Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
zaiyi magana ba kuma sai ya ce.  Bhatool. Ya kira sunan a wani irin voice. Ji tayi babu wanda ya kai shi iya kiran sunan ta, a wani irin yanayi ta kalle shi ta furta.  Na am Senate. Tsayawa cak suka yi babu wanda ya motsa, kafin ya ce.  Kina da wanda kike so ne?. Girgiza kai tayi, wani naunauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya saki murmushi ya ce.  Muje ko. Suka cigaba da tafiya babu wanda ya cewa wani kala. A bakin get ya tsaya ta shiga, ganin ya tsaya yasa ta ce.  Ka shigo ku gaisa da Yaya mana. Girgiza mata kai yayi ya ce.  A a yanzu kunyar ta nakeji, akwai lokacin da zan shigo har mu gaisa muyi hira da ita.  Ok nagode ka gaishe min da Momi. Ta fada tana masa bye bye ta shiga falon. Har sai da ta bace kafin ya sauke numfashi yana furzar da iska ya ce.  Yau na mata magana, yesss God kasa kar tayi wani saurayi har ta gane inason ta. Ya fada yana tsalle da murmushi kafin ya koma gida. Tana shiga falon ta fara ihu wanda ya tsorata Yaya Karima ta fito da gudu daga kitchen.  Wallahi sona yake, yess na kamu da soyayyar Kyakkyawan saurayi fari ajin farko irin na fita cikin kawaye da shi, na kece raini. Cike da haushi Yaya Karima ta ce.  Shi ne zaki shigo da ihu?.  What the fuck, Yaya Karima ki barni kawai. Ta fada tana fadawa akan three seater ta lumshe ido. Filo Yaya Karima ta dauka tana buga mata, da sauri ta tashi tana dariya ta nufi dakin da ta sauka ta ce.  Sai hakuri idan zaki iya, kisan wanda ya fada soyayya baya jin shawara. Yana komawa gida ya shigo falon da gudu yazo ya rungume Momi.  Babana Lafiya? What s wrong?.  Momi babu wanda ya kai ki sona a duniya, ina kaunar ki Momi. Dariya Anas yayi yana ciro waya ya fara musu video yana fadin.  Cigaba mana da maganar, irin yau kaga bugun zuciyarka, ai har yaran ku sai sun ga video nan In Sha Allah. Turo baki gaba Senate yayi yana hade fuska ya nuna Anas yana kallon Momi ya ce.  Momi ki ce ya daina bana so.  Anas ka daina baya so. Cewan Momi tana dariya.  Ke ma dariya kike min Momi?.  A a kuka nake. Juyawa yayi ya tafi dakinsa yana guna-guni kamar yaro karami. *Bhatool* Tun bayan da ta shiga dakinta bacci ya dauke ta, sai kusan mangarib ta fito tana bata fuska. Yaya Karima ce da Barrister a falon yaran sun tafi wasa, kallon ta Barrister yayi yana cewa.  Yar dakina nazo kina bacci. Sakin fuska ta yi tana cewa.  Uncle ina wuni?.  Lafiya ya gajiya.  Alhamdulillah. Tashi yayi yana cewa.  Ni kam na wuce masallaci kar na makara.  A dawo lafiya. Yaya Karima ta fada tana masa murmushi, da haka ya fice. Duban Yaya Karima tayi tana yamutse fuska ta ce.  Yaya abinci.  Ni zan kawo miki kenan?.  Ni bance haka ba, naga bakon ka Annabin ka. Da mamaki Yaya Karima ta ce.  Ke ce bakuwar kenan?.  Eh mana. Jinjina kai tayi tana danna wayanta, zama Bhatool tayi a kasan tana fadin.  Nikam gurin Abbana zan tafi, duk babu wanda yake so na sai shi, abinci ma ana ma mutum yanga, abun duniya da za a mutu a barshi ana hana ni. Ta fashe da kuka. Jikin Yaya Karima ce yayi sanyi ta tashi tazo gurin ta tana durkusawa ta jawo ta jikinta, tana bubbuga bayanta ta ce.  Bhatool kiyi hakuri mana, ba fa hanaki abincin nayi ba, amma ai kema ba bakuwa bace.  Babu wani nan, kawai bakya sona ne, amanan da Abba ya baku kukeson ku ci. Ta kuka take maganar.  Wallahi Bhatool ba haka bane, bari na dibo miki abincin kiyi hakuri. Ta mike ta nufi kitchen din. Bata dade ba ta dawo hannunta rike da tray da abinci a ciki. Mikewa Bhatool tayi tana karba ta nufi daining table, zama tayi ta fara cin tuwo miyan egusin tana mita wai yaji yayi yawa, Yaya Karima bata kula ta ba ta nufi dakinta tana cewan Momi ta kawo mata masifa. Tana gama ci ta tashi ta dauki ruwa a fridge ta koma dakinta, salla tayi kafin ta dauki waya ta fara charting da friend s nata kuma duk hiran akan auren da suke dashi ne, tana zaune aka kira Isha ta tashi tayi, sai kusan goma kafin tayi bacci. *Yaya Karima* Kallon mijin nata tayi tana cewa.  Barrister sai ina ganin kamar Senate zai sha wahala a hannun yarinyar nan, dan ko mu da muke yayunta muna shan wahala bare kuma mijinta da zasuyi zama na har abada.  Karima bana jin zaman Bhatool dashi akwai matsala, Bhatool tana da hakuri sannan kuma tana da tsoro, kuma miji ai ba wasa ba, ni a ganina a musu fatan alkhairi idan har auren nasu alkhairi ne.  Hmmm! Barrister Bhatool fa& . Dakatar da ita yayi yana cewa.  Karima kar baki yayi yawa a ciki, Allah ya tabbatar. Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa.  Amen. Kasan zuciyarta kuma yana raya mata cewa akwai matsala. 'ýÿLegends pen 08129553971. 11- *HASASHEN SOYAYYA*d'þ =Ø%Ý>ØyÝ _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen) 'þ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)=Ø‹Ýþ=ØÚÜ* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =ØOÞ=Ø«Ü* _Page 11_ Ajiyar zuciya ta sau™e tana cewa.  Amen. ˜asan zuciyarta kuma yana raya mata cewa akwai matsala. Murmushi yayi ganin ta tafi duniyar tunani ya ce.  Mar atussaliha!. Juyowa tayi tana kallon shi ta ce.  Na am Hayati.  Kar ku saka damuwa a ranki kinsan ciki ne dake, yanzu ba lokacin tunani bane, yanzun lokacina ne. Ya daga mata gira. Dariya tayi tana fadawa kirjinsa. *Senate* Yana zaune a tsakiyar gadonsa shi da Anas suna video call da Juraij da Salman. Salman ya ce.  Senate soyayyar yarinyar nan ya saka baka gane komai. Anas ya ce.  Hmm!! Ku da bakwa tare dashi kenan amma har kun gane, idan zaku bawa yaron nan shawara tun wuri ku bashi, bayi da magana sai na Bhatool. Rai a bace ya kalli Anas yana cewa.  Na fada maka ka daina kiran sunanta tsirara kana cewa Anuty Bhatool. Dariyar rainin hankali Salman yayi yana cewa.  To kaji dai ko Anas, saboda haka take note.  Ni fa bazan ce mata Anuty ba, after all na girme ta.  Wallahi da Anuty zakana kiranta. Senate yayi maganar yana hararan shi. Dariya kawai yayi yana kallon Juraij ya ce.  Ya kayi shuru fa?.  Hmm!! Ba shuru nayi ba, lamarin Senate ke ban tsoro, nifa nasan yarinyar kuma akwai rawan kai, ga rigima, kaga Senate kuma bai iya ba, shine nake tunanin soyayyar nasu. A tsawace ya yi maganar wanda yasa dukan su yin shuru.  Ina ruwanku idan tana da rigima, ko ku zaku zauna da ita ne? For the last time idan daya daga cikin ku ya sake embarrassing din matata ban yafe ba, kuma sai mun rabu dashi.  Gaskiya ne baka so kuma dole sai mun fada maka. Cewan Juraij a fusace yana disconnecting din nasa, Salma ya ce.  Mun ji ayi hakuri. Shima ya kashe. Anas ya tashi ya nufi kofa yana fadin.  A dakin k asa zan kwana sai da safe.  Ku kuka sani kuma. Ya fada yana jan bargo ya rufe fuskarsa. ~~~~~~~Washe gari Tana tashi da safe ta shirya dan yau suna da lecture na karfe takwas kuma tana so tayi attendance, shiryawa tayi cikin abaya blue mai ratsin fari, sai sheki da daukar ido yake, tayi roiling din veil dinsa. Handbag dinta ta dauka ta saka perfume nata da lips glow ta jefa biro a ciki, kafin ta dauki wayanta tana bud e wardrobe ta dauki kudi ta zuba. Sauri sauri ta fito, a daining ta hangi Yaya Karima da mijinta suna breakfast, isa gurin su tayi ta gaishe su tana cewa.  Na tafi muna da class eight. Barrister ya bata kudin machine, ta karba tana godiya ta fito waje. Tana tsaye machine yazo ta hau, a bus stop ya ajiye ta ta bashi kudinsa ta hau wani machine zuwa Makarantar. Tana shiga Makarantar ta kira number Amrah, bugu daya ta dauka tana cewa.  Billahil lazi kiyi sauri wai test zai yi. Kashe wayan tayi tana sauri ta isa department nasu.  Excuse. Ta fada cikin sanyin murya. Kusan duka ajin sai da suka juyo da hankalin su zuwa gare ta, a hankali Lecturer ya sauke glass din idanunsa ya zuba mata ido. Magana class din ya dauka wasu na fadin bazai barta ta shiga ba wasu na cewa ya fada soyayya da ita. Muryansa taji yana cewa.  Ki shiga test zanyi. Da mamaki team nasu suka kalli juna, Jannah ta ce.  Kun ga kallon da ya mata kuwa?. Amrah ta rage murya tana murmushi ta ce.  Ni kuwa na gani. Suhaima na fadin.  Ku bari sai mun fita kafin muyi magana, yanzu any slice of mistake zai fitar damu. Shuru suka yi suna zubawa Bhatool ido. Duk taji wani iri, a sanyaye ta soma tafiya zuwa gurin su ta zauna, paper ta ciro ta rubuta reg no ta, kafin ta fara rubuta question din, question biyar ya rubuta ya ce a amsa duka kuma 30 minute, sannan ko wanne da a and b. A hankali ya soma zagaye class din yana kallon su daya bayan daya, dai-dai bayanta ya tsaya yana zubawa yatsunta kallo ganin yanda take rubutu a natse. Ji tayi kamar an tsaya a kanta hakan yasa ta juya ba shiri, karaf suka had a ido, da sauri ta janye idanunta tana kallon Amrah ta gefen ido, murmushi kawai suka yi wanda iya sune suka gane abun su. Sai da ya tabbata ta gama kafin ya ce.  Submit, before I count 1 to 5. Kafin ka ce me har kowa yayi submitting. Suna fitowa daga ajin Amrah ta ce.  Guys I don t get rite, me hakan ke nufi?. Tafiya suka cigaba da yi zuwa wajen garden Jannah na cewa.  Maybe kawai ya taimake ta ne.  Wannan ba taimako bane, ko kin manta waye Dr Hashim? Ranar fa bani da lafiya nazo amma ya hanani shiga lecture dinsa, yau kuma Bhatool tazo kuma tayi letting amma ya bar ta ta shiga. Suhaima ta fada tana zama a kujera bayan sun iso garden din. Kallon su kawai Bhatool tayi kafin ta gyara murya ta ce.  I don t think that so, maybe kawai ya taimake ni ne kamar yanda Jannah ta ce. Tabe baki suka yi suna chanja hira, a cikin hiran ne Amrah ke cewa.  Yau ban ga wannan kyakkyawan saurayin yazo ba. Lokaci daya Bhatool ta hade rai tana cewa.  Ina ruwan ki dashi?.  No kawai tambaya nayi fa, naga ya saba zuwa ne, kin ga dole na tambaya ko lafiya. Ba ta bata amsa ba suka wani yazo gurin su yana cewa.  Bhatool tazo inji Dr Hashim nan da minti biyar. Ya karashe yana juyawa ya tafi. A tare suka hada baki gurin furta.  Whatttt!!!!. Amrah ta ce.  Wallahi na fada muku dama kallon da ya mata ba a banza ba akwai dalili, ya fola. Ta karashe suna tafawa ita da Suhaima.  Kai dalla shut up, ku fa kun zare I swear, kun san me nayi ne?. Tayi maganar tana duba gefe da gefe kafin ta cigaba da cewa.  Amma idan ya nuna alamun soyayya, to idan mun kara yin karatun shi make i bend, ai na banza ya samu. Ta mike da wuri tana cewa.  Bari naje kar na makara.  Bhatool idan kin ga ruwan sanyi ki kawo mana. Cewan Jannah suna dariya. *Senate* Ko da suka hadu da Anas a daining babu wanda ya yi wa wani magana, har sai da Momi ta lura da haka ta ce.  Naga yau baku yiwa junan ku magana ba, is that any problem?. Girgiza kai Anas yayi yana cigaba da cin abinci, mikewa Senate yayi ya koma perlo ya zauna yana kallo amma rabi da kwatan hankalin shi yana gurin Bhatool. Sallaman abokanan shi yaji, da sauri ya juyo dan tabbatar da su din ne. Salman ne da Juraij kowa rai a hade, suna kallon shi suka dauke ido, gurin Momi da Anas suka nufa suna murmushi. Da mamaki Senate ya mike yana kallon su, kamar zai yi kuka ya ce.  Ni kuke sharewa? Then sai me idan kun ki yimin magana, Mtsw. Ya dauki key din motansa ya fice daga falon Momi na cewa ya tsaya bai saurare ta ba. Salman yayi murmushi yana cewa.  Momi zafin soyayya ke rudar shi, yanzu ba a isa a fada masa gaskiya ba inde akan Bhatool ce. Fuskar Momi da damuwa ta ce.  Me ya faru ne?. Juraij ya ce.  Hmm! Momi dan kawai mun ce yarinyar tana da rigima shine yayi fushi damu, shi ne muma muka yi fushi da shi. Bata ce komai ba ta nufi dakinta dan dauko wayanta ta kira shi. *Bhatool* Da sallama a bakinta ta shiga office din nasa, yana zaune akan gujera mai juyi yana facing din kofar shigowa. Bayan ya amsa sallaman ne ya nuna mata kujera yana cewa.  Have a seat. Zama tayi tana sunkuyar da kai, bata ankara ba taji maganar da ya kusa toshe mata kunne da ganin ta& . '<Øüß Legend's pen 08129553971. 12- *HASASHEN SOYAYYA*d'þ =Ø%Ý>ØyÝ _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen) 'þ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)=Ø‹Ýþ=ØÚÜ* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =ØOÞ=Ø«Ü* _Page 12_ Bayan ya amsa sallaman ne ya nuna mata kujera yana cewa.  Have a seat. Zama tayi tana sunkuyar da kai, bata ankara ba taji maganar da ya kusa toshe mata kunne da ganin ta.  Za ki aure ni?. Da sauri ta dago da manyan idanunta ta zuba masa, kamar wacce aka ce an aikowa da sak on mutuwa, muryanta har rawa yake gurin cewan.  Sir Ina da wanda nake so.  I don t care >Ø7Ý B&þ, ba shawaran ki nake nema ba umarni na baki. Ya fada yana nuna ta da yatsa, kafin ya cigaba da cewa.  If not duk abunda kika gani ke kika jawowa kan ki, na baki nan da gobe kadai. Wani yawu mai kauri ta hadiye, tun da take ba a taba yi mata barazana ba sai yau, hakan kuma ba karamin tasiri yayi ba a kanta.  You can go. Ya fada yana juyawa akan kujera. Da sauri ta tashi ta fita daga office din har tana k ok arin fadi. Gudu yake tsulawa akan titin, horn kawai yake yi sai motoci su matsa, da gudu ya shigo YSU yana parking a tsakiyar Makarantar. Ya dade a ciki kafin ya fito yana bata fuska saboda zafin ranar yau din daban ce, gurin garden ya fara nufa amma sai yaji zuciyarsa bata canja bugu ba, da mamaki ya furta.  Bata nan kenan.. Bai karasa ba ya hango ta tana nufo garden din duk a burkice. Duk da ya ganta a burkice amma sai da murmushi ta kufce masa, cike da k asaita ya fara nufo inda take yana murmushi, wanda ita ko lura dashi bata yi ba. Tana shirin shiga garden ne tayi tuntube za ta fadi, cikin zafin nama ya taro ta ta fada kirjinsa, yana furta.  Subhanallah tunanin me kike yi haka. Sai da ta runtse ido kafin ta bude tana zuba masa, duk a tunanin ta zata fadi, janye jikinta tayi tana dan yin baya kafin ta ce.  Thanks.  Tunanin me kike yi?. Senate ya fada yana duban fuskarta. Girgiza kai tayi tana cewa.  Babu. Bai ce mata komai ba har ta isa gurin su kawayen ta ta zauna. Dukan su ita suke kallo, kafin Suhaima tayi magana a sanyaye.  Me ya faru Bhatool?. Shuru ta musu bata ce komai ba, ganin kamar bata tare dasu ne yasa Amrah taba ta tana fadin.  Bhatool!!!. A furgice ta juyo tana kallon su. Jannah na fadin.  Me ya fada miki?. Girgiza kai ta shiga yi tana kallon inda Senate yake tsaye ya zuba mata ido, duk kuma maganar da suke yi yana jin su. Kamar baza tayi magana ba sai kuma ta ce.  Babu abunda ya faru, just kawai gaisawa muka yi. Dariyar rainin hankali Jannah tayi tana cewan.  Wallahi karya kike Bhatool, tun yaushe muke tare da ke, mun sanki ciki da bai fa. Hararan ta Amrah tayi tana cewan.  Barta ta raina mana hankali ne, idan bata yarda damu bane ai shikenan damuwar ki. Amrah ta mike a fusace zata tafi. Tashi tayi kamar zata yi kuka ta rike ta tana fadin.  Ba wai ban yarda da ku bane, after all kun fi kawaye a gurina kun koma jinina ne. Suhaima ta girgiza kai ta ce.  Idan har kin dauke mu jininki ai zaki fada mana ba wai kice ba komai ba. Wani yawu ta hadiye mai kauri, kafin ta juya ta dubi Senate da ya hade hannun a kirji ya zuba mata ido yana jiran yaji me zata ce, kafin ta sunkuyar da kai ta ce.  Wai sona yake yi, dana ce masa ina da wanda nakeso shi ne ya ce ya bani daga yau zuwa gobe wai na yarda, ko kuma duk abunda ya faru ni na jawo. Maganar da ya kusa hargitsa zuciyar Senate kenan, bai san sanda ya bar gurin a furgice ba. Kusan a tare suka furta.  Whatt!!!. Jinjina musu kai tayi tana cewa.  Bansan me yake nufi ba, and& . Ta juya taga baya gurin hakan yasa tayi shuru tana tunanin ina yayi. Amrah ta ce.  Dama kwarto ne, ai na dade da fada muku kune baku yarda ba.  Yanzu ya zamu yi Bhatool?. Cewan Suhaima a dan tsorace. Numfashi ta sauke ta ce.  Duk abun da zai yi yayi, karshe dai ya ce bazan yi passing din course na shi ba ko.  Ni fa ba wannan ba ne tsoro na. Cewan Jannah tana cigaba da cewa.  Kin san duk yarinyar da ya ce yana so sai ya same ta, idan kuma bai same ta ba to ya saka ayi raping na ta. Dukan su shuru suka yi kowa da abun da yake tunanin a zuciyarsa, kafin ta kalli agogon hannunta tana fadin.  Ni zan koma gida. Suhaima tayi magana a sanyaye cike da damuwa.  Ki bari mu gama lecture mana.  A a akwai abun da zanyi ne. Ta karashe tana daukar handbag din ta. Har bakin get suka raka ta ta hau machine kafin suka dawo cikin Makarantar ita kuma ta nufi gida. *Senate* Bai san sanda ya isa gurin motarsa ba ya shiga ya mata key ya fice a 360, idanunsa yayi ja ga wani ruwan da ya kwanta a ciki, fuskarsa tayi ja abunka da fari, jijiyoyin kansa sun fito rad a-rad a. Gudu kawai yake zubawa akan titin kalamanta yana masa yawo a kwakwalwa. < Wai sona yake, ni kuma na ce masa ina da wanda nake so.> Bai lura ba da machine din da yake gabansa har ya kusa bugawa, wani burki ya danna da karfi ji kake chusssss, buga kansa ya soma da stirring yana fadin.  Why? Why!!!! Waye wanda take son? Dama tana da wanda take so ban sani ba? Ba zai yu ba, ni zan aure ta ba kowa ba! Ni neeeee!!!. Ya karashe da karfi. Wayansa ce ta soma ruri ya duba, Momi ce hakan yasa ya ki dauka dan yana kusa da gida, tada motan yayi ya karasa gida yana horn da karfi wanda ya saka mai gadi lekowa dan yasa waye ne. Yana kallon motan yasan Senate ne hakan yasa ya bude da sauri, cilla hancin motar yayi ba tare da yayi parking dai dai ba ya fito ya nufi ciki. Duk suna tsaye a parlon Momi na fadin.  Yaki picking fa, me ya& .. Bata k arasa ba ya shigo falon.  Subhanallah. Kusan a tare suka fad a, kafin Momi ta nufi gun sa da gudu tana kama shi ta soma furta.  Me ya faru da kai? Hatsari kayi ne? Kai da waye?. Ido kawai ya zuba musu, kafin ya janye jikinsa zai haura sama ya ce.  Duk wanda zata aura ni ne ajalin shi, idan kuma ban aure ta ba to ni zan kashe kaina. Ya karashe yana shiga dakinsa ya rufe da key. Duk sakin baki suka yi Juraij na cewa.  Ta haukata shi, saboda yarinyar nan Senate ya zare, idan ba a aura masa ita ba Wallahi zamu rasa shi kamar yanda ya fada din. Ya karashe yana kallon su. A hankali Momi ta tako ta zauna tana had a tagumi, ta rasa ta ina zata fara duk kanta ya dau zafi. Anas ya zauna kusa da ita yana dafata ya ce.  Momi the best solution shine a kai kudin auren yarinyar nan. Salman ya ce.  Ita ta ce muku tana son shi ne?. Ajiyar zuciya Momi ta sauke kafin ta ce.  Ita fa bata ma san yana wannan shirmen ba& . Bata k arasa fad a ba suka ji karar fashe-fashe a dakinsa. A guje suka haura upstairs har Juraij na buge Momi dan sauri, buga k ofan suka shiga yi Momi na kuka tana fadin.  Senate kar ka kashe kan ka dan Allah. Legend's pen 08129553971 13- *HASASHEN SOYAYYA*d'þ =Ø%Ý>ØyÝ _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen) 'þ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)=Ø‹Ýþ=ØÚÜ* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =ØOÞ=Ø«Ü* _Page 13_ A guje suka haura upstairs har Juraij na buge Momi dan sauri, buga k ofan suka shiga yi Momi na kuka tana fadin.  Senate kar ka kashe kan ka dan Allah. Magana ya soma musu yana kuka.  Kun ce HASASHEN SOYAYYA na ke, gashi ina ji ina gani za a kwace min ita, dukan ku babu wanda zai iya kwato min ita.  Senate ka bud e kofan nan, ka daina fashe-fashen nan, ka kasa zuwa ka tunkare yarinya ka fada mata kana sonta, wai kai tsoro. Cewan Anas kamar yayi kuka dan haushi. Bai kula su ba ya cigaba da buge-bugen da yake yi. Salman ya dube su ya ce suyi baya, suka matsa da karfi ya buga kofar sai gashi ya fadi, inda yake tsaye suka nufa duk dakin kwalba ga hannunsa din da yake digar jini alamun ya tsage. Cikume rigarsa Juraij ya yi yana cewa.  Mad kawai, akan mace kana k ok arin halak a kanka da rayuwarka. Kafin ya sake shi yana shafa gashin kansa ya ce.  Ka je ka same ta kace kana sonta mana. Bai bari yaji

Chapter 5 of 8