da
Haule suka gaisa Ibrahim ya ce haba gaskiya mana
naga mutuniyar tawa tana ta faman washe baki, ashe
bakuwa ta yi kawa ce tazo ni nasan wannan fara'ar
76
ba a banza ba. Na ce kai yanzu har ka gane irin farir.
cikin da nake ciki? Ya ce ai ya zame min dole, nima
a taya ni farin ciki na ce na mc kuma? Ya ce Can
uwana Sadik ya kusa dawowa jibi i yanzu in Allah
yaso zai dawo ya gama karatunsa gaba daya, na ce
ikon Allah kenan, ni dai Sadik din nan tunda nake
ban taba ganinsa ba, ko a hoto ma. Ya ce e haka ne
ina kuwa da hotonsa na kawo miki ki gani sai
Nusaiba ta ce to karewar hoto ma abin da jibi zai
dawo, ta ganshi, ido cikin ido, na ce gaskiya kam,
kuma wani abin mamaki duk sa inda zai zo gidan
nan sai an sami sabani ko na tafi kauye ko kuma ina
gidan aunty Rabi. Sai dai in ji yazo ya koma kuma
tunda yake yo waya ba ku taßa yin yakanar ku ban
mu gaisa ba, daidai da rana daya. Nusaiba ta ce kin
ga kuma Allah ne bai yi ba, don rannan har zance ki
zo ku gaisa ta wayar da Yayana Sadik sai na tarar
kina barci, sai na kyale ki na ce ai ba komai in yazo
na ganshi haka muka ci gaba da hirar mu har wani
lokaci sannan muka tashi.
** **
Yau ne ranar dawowar Sadik, saboda haka
Alhaji yasa aka shirya masa yar karamar liyafa a
nan gidan domin taya murnar kammala karatunsa na
digiri, duk gida ya cika da kamshi sai gyare-gyare
muke ta yi mun gara ko in na har dakin da aka
77
mallaka wa Sadik mun gyara shi, ya yi fes muka
shiga kitchen muka kama soye-soye da hade Iemuka
kamar su inja da yake Haule na nan duk da ita
muka dinga yin aikin.
Bayan mun gama komai ne, Nusaiba ta cc, to
sai ajc a kure adaka, domin yau ce ranar da zamu
nuna wa dan uwanmu farin cikin kammala karatunsa.
Na ce, kai Nusaiba kina ji da Yayan nan naki, sai ka се
Sarki sai aman karrama shi ki ke ta yi haka. Ko dai da
wata a boye ne? Ta yi dariya a'a,a'a wallahi ba komai sai
zumunci kin san yanzu mutane sun watsar da zumunci,
sai dai dai ke yinsa, na ce haka ne kam ya kamata kam
mu dinga rike zumunci domin naka naka ne, duk tsiya
ko ka guje shi tilas ka koma masa.
Muna birar mu muna shirya wa sai ga Ibrahim nan
ya ce to ku fa yi saurin kammala komai domin Alhaji ya
ce ga su nan sun kusa isova. Ai cikin sauri muka
shisshiga wanka muka fara tsala kwalliya ke kya cе
gasar kyau ta duniya zamu shiga, sai da muka gama
shiryawa tsaf sannan muka fito muka zazzauna. Nusaiba
ta dube ni ta ce kin ga kuwa yadda ki ka hadu? Na ce kai
kema dai da zolaya ki ke ta ce ki tambayi Yaya Ibrahim
ki ji na ce ai shi dama haka zai ce mana, cikin wannan
maganar sai ga yaya Ibrahim ya shigo da camera a
hannunsa, ya fara daukarmu a hotuna gaba dayanmu
sannan ya ce in zo mu yi tare na ce a'a ka bar shi kawai
ya nace sai mun yi ganin mami ne ya sani yarda domin
kar ta ce ina wulakanta danta, sai da muka yi kusan
78
hotuna kala goma sannan ya hakura muna wannan
budurin ne sai Mami ta ce in zo ta aike ni gidan wata
kawarta, kafin su zo na'ce to na dauki mayafina ta bani
aiken, Haule ta ce in tsaya ta sai Nusaiba muka bari.
Muka tafi dan da nan muka je, muka dawo a
lokacin motar Alhaji na nan hakannen ya tabbatar mana
cewa sun dawo, haka kawai sai naji gabana na faduwa,
na ce da Haule, gabana faduwa yake yi haka kawai, ta
ce kila ambatonki aka yi, na ce wallahi kuwa, ko
ambaton Ibrahim ma kawai ya sani faduwar gaba. Muka
yi dariya baki daya, yayin da muka shige cikin gidan.
A zaune na same su a falo, yayin da bakon namu
ke fuskantar cikin falon, su kuma suna fuskantar kofar
shigowa hakanne ya samu shiga ciki domin mu sami
ganin bakon sosai, sakon Mami na fara idarwa kafin in
zauna, shi kuwa bakon yana ta zuba musu hira naji
kamar muryar wanda na sani, shekaru masu dan yawa
kamar shida, don haka nake ta Allah-Allah Mami ta
ganma fada min abin da zata fada min in juyo in ga ko
waye, mai wannan muryar Abubakar na ji Haule ta yi
kiran sunansa na yi saurin juyowa in ga wannan
Abubakar Haule ta sani cak na tsaida numfashina yayin
da naga wanda Haule take kira a daidai lokacin daya
kira sunanta sai tayo masa nuni da in da nake tsaye ya
biyo saitin hannunta da ido muka yi ido hudu cikin wani
irin mamaki ya ce "Hamdiyya." bakinsa a bude....
Kash! Ma su karatu, a kara hakurin kashi na biyu
dan jin yadda zata kasance, nasan za ku ce ina Aljanin
nan? To yana nan tare da su duk abin da ya yi a baya
79
wasa ne a yanzu ne zai fara gwara kansu, ku dai biyo ni
a cikin Sharrin Jinni kashi na biyu ku ji yadda kauna ta
ke raba kauna sannan wata da daddiyar tsohuwar kauna
tazo ta hada su bayan tsananin wahalar da aka sha kamar
rai zai fita.
Amina Abdullahi 'yar mutan Sharada.
08085389470
80
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
ZAZZAFAR KAUNA 1, 2 & 3
TALLAFIN KAUNA 1 & 2
SIRRIN JUNA 1& 2
HAKURI DA MASOYI 1 & 2
RASHIN HALACCI 1 & 2
TSAYA KALLON RUWA... 1 & 2
SHARRIN JINNI
PRINTED BY:
AL AMINNG PRINTING & PUBLISHING COMPAN
ANDAW O CITY 0802
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels