na ce ta yaro fa
kyau take bata karko. Nan dai suka yarda suka tafi
amma zuciyar wasu bata so ba, sun dai tafi ne dai kawai
tun daga wannan runa aka dauki tsanar duniya aka
dorawa Abubakar ba mai kula shi in abu zai saya sai dai
ya yi ake amma in shi yaje da kansa ba za a sayar mása
ba, haka ya zauna cikin takura ba shi da abokin hira
daga mahaifiyarsa sai mahaifinsa gaba daya mutanen
unguwa sun yi mitin akan cewa duk wanda yaga
Abubakar zai daki wata ko ba yar uwarsa ba ce ya yi
masa jina jina. 30
W
C1
k
ir
S
k
C
1
Yana cikin tafiya sai ya yi kicibis da wani tsoho
mutum maiı bayar da magungunan gargajiya ya gaishe
shi zai wuce sai ya ce masa ji mana samari, ya dakata
gami da risinawa ya ce gani baba, ya dube shi ya ce kash
wallahi yaro ina tausaya wa rayuwarka, ya cc baba me
ka gani? Ya ce wato samari wani abin al'ajabi na hango
maka amma kafin in ce maka komai bari in yi maka
wata tambaya guda daya, ya ku ke ciki da mutanan
Kauyenku a game da abinda ake zarginka aikata? Ya ce
to Baba ya ko mike ciki lamarin ai sai ddai addu'a, a a
kai dai bari in baka wata shawara kunya da ya ya ciro jakar bayansa ya fara ciro magunguna ya mika masa
wani bakin magani ya ce ungo wannan ka jika shi kasha
in Allah yaso sai yadda ka juya mutanan kauyan nan naku, yasa hannu ya karba ya yi godiya sannan ya ce gashi ban ſito da kudi ba ko zaka biyo ni muje gida in
baka dan wani abu? Ya cc ina yaro ai kyauta na baka, kai dai ka yi abin da na ce ba a karbar maganina a zubar da ka zubar gara kar ka karba in har kasan zubanva zaka yi ka bani abina in ba haka ba kuwa zaka yi da na sani,
ya ce ai ba zan zubar ba Baba, suka yi sallama ya wuce zuwa gida shi kuma ya zage bayan wata bishiya ya girgiza ya koma kamarsa ta asali ya fara tuntsura dariyar mugunta har sai da dajin ya dinga amsa kuwwa. A da kam Abubakar bai yi niyar shan maganin nan ba, zubar wa zai yi sai kuma aka kwaße shi don haka sai ya hakura akan zai sha din in yaso Allah shi ne mai kiyayewa yana zuwa gida sai ya sami kofi ya jika
31
magani ya kafa kai ya shanye abinsa, daga nan sai ya
kwanta sai barci ya kwashe shi.
Ta leko daga ba wanda ta gani sai tsoho tukuf a
tsayc ta Karasa gurinsa ta ce dama kai ka ke sallama? Ya
ce ni ne abin da yasa na zo gurinki shi ne, fazun nan
naje cikin unguwa sai naji ana zancen wat kece ummul
aba'isin da Abubakar dan dagaci yake dukan 'ya'yan
mutane, shi ne naga ya dace in zo in tamaka miki da
maganin baki kinsan fa baki shegen abu ne, yanzu kya
lalace in jama'a suka sako ki a gaba ta dafa kirji na gode
baba bani ina so nima dama wannan abu yana damuna,
ya kwance jaka ya fiddo magani ya ce gashi ki jika shi
kisba, kar ki nuna wa kowa abin asirrance yake, in kin
jika za ki sha sai ki ambaci sunansa sannan kisha zai
daina wannan mummunan halin na ce to muka yi
sallama na shiga gida ina shiga shi kuma ya bace, ba
tare da na sani ba.
Abubakar ya farko daga barcin da yake wanda bai
san dalilin yinsa ba ya yi juyi ya ji duk jikinsa a mace,
zumbur ya mike jikinsa na rawa ya fara tunanin da bai
taba mafarkin yinsa ba wato tunanina in ban da son
yaganni ba abin da yake yi, wuf ya fita da sauri ba
wanda ya ganshi sai gidanmu a lokacin nima ina soro
ina tunanin zuwa wajensa domin babu wanda nake so da
gani in ba shi ba. Muna yin arba da juna sai muka saki
wata irin ajiyar zuciya a tare muka kuma kura wa juna
ido Abubakar ya ce "Hamdiyya wallahi duk duniyar nan
ba ni da wadda nake so in bake ba, inhar aka ce ba za a
bani ke ba wallahi raina zai iya salwanta, na ce wallahi
32
Abubaka r kai nake so da kauna muddin aka hana nı kai
an iya rabuwa da duniya muna cikin fadar haka sai ga
wani yaro nan dan cikin gidanmu yazo zai wuce yana
ganınmu sai yaje ya sanar wa baba Tasalla, ccwa ga mu
can muna zance a soro haba wa sai ga ta nan babu ko da
mayafi ta shigo ban yi aune ba sai jina yi ta kwadan
mari ta jani cikin gida ina ihu haba da Abubakar ya rasa
yadda zai yi sai ya bini ciki yana cewa don Allah haba
ku yi hakuri ku kyale ta, wallahi Baba ina kaunarta ba
zan iya rabuwa da ita ba, ni kuma sai ihu nake ina kíran
Abubakar, baba na ganin ya shiga sai ta ce au har ciki ka
shigo domin ka 6ata min 'yar? Ta kurma ihu wai azo a
taimaka mata zai lalata mata 'ya haba kafin a ce ma yi
wannan gida ya cika da samari dan da nan ta ce zuwa ya
sake yi domin bata ma ta 'ya suka rufar masa da sanduna
suna ta duka da naga suna dukansa sai na kwalla kara
gami da cewa wayyo Allah na za su kashe min
Abubakar na fisge na kifu a kansa sai lugudan sanduna a
bayana shi ko Abubakar har ya galabaita ma sai
numfashi yake yi dai dai suka dinga kokarin janye ni
ina ibu ina cewa sai du ku kashe mu tae, baba cewa take
ba za ku janye ta ba sai ka ce tafi karfinku? Suka ja ni da
karfi wasu suka rike ni wasu suka janye Abubak ar aka
fita dashi aka yar a waje, sai ka ce mushen dabb a, haba
wa ina ganin an janye shi a kasa an fita da shi na kara
gunjin kuka ta karfi aka kaini daki aka rufe &ofa na yi
kuka iya kuka ba abin da naka tunani sai At ubakar da
halin da ya shiga.
33
Labarı ya iske Dagaci cewa an yi wa Abubakar
duka yana can kwance rai ga hannun Allah a kofar
gidanmu da kansa ya taso domin yaga abin da ke faruwa
yana zuwa da yaga halin da Abubakar ya shiga saı ya yi
salatı ya tambayi ba'asi aka ce har cikin gidan su ya
shiga shi ne suka yi masa haka,. dagaci ya ce ba ni da ta
cewa tunda kai ka shigar musu gida, ka taka shari'a da
ace a kwararo suka yi ma wannan dukan wallahi wallahi
da ran kowa ma sai ya 6aci yasa aka tai tayi Abubakar
sai gida.
Kuka nake sosai duk idona ya kumbura sakamakon
kwanan da na yi ina kuka a kan lallai sai an bami naje
naga halin da Abubakar yake ciki na yi ku ke iya kuka
ko kallona ba ta yi ba danga bata da niyar barina sai na
yanke shawarat zuwa ba tarc da ta sani ba, don haka na
faki idanta fice ina ta gudu har kofar gidan su dagaci,
nazo zan sl
da cewa ina
ga sai dagaci ya tsaida ni da saurinsa gami
ki je? Na ce gurin Abubaka r za ni ya cе
me za ki yo? Na ce jikinsa zan gani dagaci ya ce wannan
ko tsinannivu
Abubakar
arinya mara mutunci duk halin da
ya sliga a dalilinki ne wallahi in har ki ka
kara zuwa kof dannan da sunan gurin Abubakar ki
ka zo sai na ka ya ki shegiyar yarinya shedaniya. Ina
ganin ya hana ni shiga na durkusa ina kuka ina faman
rokonsa ya barni in je in ganshi, ya ce maza ki bar kofar
gidan an ko kuma in sa a yi miki abin da aka yi wa
Abubakar a gidanku na ce ni wallahi ko kashe ni za ayi
ba in da zan je sai naga Abubakar na yi kuka iya kuka
amma ya ki barina, in shiga ina nan zaune sai ga baba ta,
34
ta biyo sawuna, da bulalarta a hannun tana zuwa ba abin
da ta fara sai dukana, na zunduma ihu zan shige gidan
Dagacı ya tare hanya ya ce wallahi ba za ki shiga ba, ki
yi can ku karata ni ba za ku tara min mutane a ka ba.
Haushi ya turnike Tasalla ta jani tana duka tana
cewa ku taimaka min in kaita gida shegiyar yarinya
mara mutunci ke dai Allah wadanki yar banza, da karfin
tsiya tasa wasu samari suka jani har gida tun daga
wannan rana ta sa mata kan tsaro akaina ba shiga ba fita
ido akai.
Abubakar zaune a kofar gidansu ya yi tagumi
hannu biyu shi kaďai yana tunanin halın da yake ciki, na
rashin ganina, ransa 6ace bai damu da wahalar da zai
sha ba, muddin zai yi ido biyu da ni, don haka ya shirya
zuwa gidanmu ko za a kashe shi yana gama wannan
tunani sai ya mike zumbur ya nufi hanyar gidanmu yana
zuwa daidai kwanar gidanmu kafin ya karasa sai ya hango wani mutum a tsaye a kofar gidanmu sai ka ce
Abubakar din shi kansa take ya ji gabansa ya fadi,
wannan wanne irin mutum ne haka maı kama da shi? Ya
tambayi kansa take ya kara sauri domın yaga ko waye,
kafin ya isa sai yaga mutumin ya bi wani lungu da gudu
Abubakar ya karasa ko zai ganshi bai ga kowa ba, yaja ya tsaya yana mamaki domin hatta kayan da yake jikinsa irin na wannan mutumin ne sak.
Yana nan tsaye ya rasa dabarar da zai yi, ya tura in fito sai ga Dagaci nan a fusace shi da wasu kartin samari
yana zuwa ya ce ku kama min shi maza in ya ki ku dake shi, nan suka dinga titirniyar kokawa dake an ce sarkin
35
yawa yafi sarkin karfi, sai da suka kada shi suka sa igiya
suika daure shi kamar yadda ake daurin huhun goro,
hayaniya ce tasa mutanen gidanmu lekowa suga abin da
ke faruwa ciki kuwa har da Baba Tasalla, tana ganin
abin dake faruwa, sai cewa ta yi au dawowa kayi tsohon
dan iska to Allah ya ara maka rana mahaifinka ya ganka
da sai dai uwarka ta haifi wani." Ina cikin gida ina jiyo
abin da take sai na gano da wanda take don haka sai na
fito da gudu ina ihu kafin su cafke ni tuni na nufi in da
Abubakar yake a daure, kafin in kai in da yake sai
samaron nan suka yi ca akaina da nufin su kama ni,
nima dagaci sai cewa ya ke kar ku bar ta tazo, nan kafin
su kama ni wuf nayi na fisgi wani lauje a hannun wani
yaro ya yi wo ciyawa ya tsawa kallo na dubi samarin
nan na ce duk wannan ya karaso sai na farke shi ana duk
sai suka yi cirko-cirko suna kallona, na kuwa yi wa
laujan rikon tsauri ina matsawa kusa da Abubakar da
yake a daure wuf na yi sauran datse igiyar da yake
laujen mai kaifi ne dan da nan sai ya warware igiyar ya
fisgi hanuuna ya jani muka danna a guje suma a gujen
suka rufo mu, Baba cewa take cikin daga murya jama'a
ku taimaka ya sacen 'yar ku bi shi mu kam sai gudu
muke iya karfinmu muka nufi hanyar dahi suna biye
damu kamar kuraye, shiga nan fita can fada nan haura
can sai da muka basu rata sannan muka sami wata
duhuwa muka buya gami da rike numfashi sai da suka
gama dube-duben su har suka gaji muna jin daya daga
cikinsu yana cewa tunda ba mu gansu ba kawai mu yi
tafiyarmu in yaso duk sanda suka ga dama sa dawo
36
sauran suka ce mu dama mun gaji muna jin sawun
tafiyar su raf raf raf, sai da muka ji sunyi nisa guri ya yi
tsit sannan muka fito, ashe suna nan labe suna ganin mu
suka taso mana suka kama ni, to dama na riga na gaji
don haka shima ya tsaya yana ganin an kama ni.
A gaban Dagaci aka zube mu ya dube ni ransa a
басс уа се cikin tsawa, ke dai wannan yarinya akwai
shedaniya, haka kurum kin yarona sakewa. Wallabi ki
fita daga shirgin yaron nan in ba haka ba zan dauki
kwak kwaran mataki a kanki, Baba Tasalla ta cc yau zan
ji ikon Allah, wato kai har laifin ta ma ka ke gani, baka
ganin laifin naka dan da yazo har gida ya tafi min da 'ya
zai lalata? Wallahi duk sa in da ya kuma zuwa gidan mu
ya dauke min 'ya sai na sa an tattaka shi, in yaso duk
abin da za'ayi sai dai ayi yana gama fadar haka ta juya
abinta gami da jan hannuna ina tuje wa ina kiran sunan
Abubakar shi ma yana ganin haka sai ya mike ya nufe
mu da gudu yana cewa baba don Allah ki yi hakuri
wallahi ina kaunar ta ba cutar ra zan yi ba Dagaci yasa
aka jawo masa shi cikin fushi ya fada shi da fada yana
cewa wallahi Abubakar zan tsine maka wai wannan
wanne irin yaro ne? Sai nema yake ya tsunduma ni cikin
masifa?.
Duk gari labarin wannan abu ya bazu har ta kai da
mutane suna zuwa gidan Dagaci su ci masa mutunci
akan abin da fansa ya yi ko yake yi, haba wa rai in ya yi dubu duk ya baci zuciyar Dagaci kamar ta fashe don
tsananin bakin ciki, dan kuka ce mai ja wa uwarsa jifa, ya ce a ransa wannan yaro ya zan 6ullo masa a gaskiya
37
ba zan jure wannan abu ba gara in je in sanar da Kanina
Alhaji Lawan duk abin da ake ciki, in ji in da wata
shawara da zai bani to, domin abin nan ya isa haka.
A Sannu motar take tafe duk da cewa ba bakuwa
ba ce, motar a garin domi motar Alhaji Lawan ce Rane
ga Dagaci, wanda yake zaune abirnin Kano can unguwar
noman sland, mai kudin gaske ne domin idan ana
lissafin mashahuran masu kudin garin nan za'a ıva saka
shi a ciki da matarsa daya da 'yayansa bıvu mace da
namıji Namijin shi ne babba macen take binamar suna
Nusaiba shi kuma namijin Ibrahim.
Alhaji Lawan din ma'aikacin banki ne domın yana
ma rike da mukamin Chairman din bankın da vake aiki.
Suna matukar kama da Dagaci sai dai shi da zamu iya
cewa dan hutu ne jikinsu ba zai zo daya da Dagaci da
yake zaune a kauye ba, amma da ka ganshi zaka gane
matsananciyar kamar wanda in ka hada su da abubakar
zaka za ci shi ne auta a dakin nasu saboda tsananin
kama. Ga kyau domin Allah ya yi su kyawawan gaske
ne musamman ma shi Abubakar da yake da kuruciya a
jikinsa domin yaro ne dan misalin shekaru ashirin da
uku da haihuwa.
A kofar gidan Dagaci ya yi fakin yayin da Dagaci
ya fito da hanzarinsa yana murnar ganin fan'uwansa,
suka rungume juna kamar yara. Nusaiba ta fito ta fada
gidan da gudu tana murna, Abubakar na ganinta ya tashi
da sauri yana cewa Nusaiba yaushe ku ka zo? Ke da wa
38
ku ka zo? Ta ce ni da Daddy ne ga su can a waje, уa сс
ina Ibrahim fa? ta ce shi yana gida ya ce wai zai zo shi
kadai ya yi murmushi ya ce shiga Umma na ciki ai ta
shiga tana zuwa ta fada kan cinyar Babar Abubar wato
Hadiza da suke kira da Umma, shi ko Abubakar ya yi
waje aka sa shi jido tsaraba daga but din mota yana
kawowa gida, duk zuwa tsarabar nan sai ya yi musu ita
kamar an shekara ba aga juna ba, nan ko ba ya wata uku
sai yazo wannan karon ne ma ya yi wata biyar bai zo ba
saboda sha'anin aikinsa, ya yi tafiya duka duka
kwanansa uku da komowa daga tafiya shi ne yazo yaga
lafiyar dan'uwansa wanda shi ma yake ta kuzun gaje
gurinsa shima.
Bayan Dagaci ya kai shi dakin sa sun zauan sun
gaisa, gami da tambayar juna bayan rabuwa, itama
Umma tazo suka gaisa ta tambayi mafarsa Hajiya Lami
da kuma Ibrahim yake cewa sunanan kalau itama Hajiya Lamin ta cc zata zo in an kwana biyu shiru sai can
Dagaci ya dubi kaninsa Alhaji lawan ya ce dama ina son
in je gıdanka akan maganar yaron nan Abubakar, al'amarin ya dame ni matuka daga nan ya kwashe abin da ya faru tun daga farko har karshe ya sanar wa Alhaji Lawan, abin ya girma a zuciyarsa ya ce yaya kar ka ji haushina duk wannan abu da yake faruwa rashin ilimi ne da ace yaron nan ya yi makarantar gaba da sakandire da abin zai dan yi sauki, anma ka rike yaro ba karatu tun daga sakandare ya ki ci gaba ga zaman kauye duk abokansa ma ba wani mai ilimki ba dole ya dinga abin 39
da yaga dama ba, ka ma yi arziki da ba a koya masa
shayc-shayen nan na banza ba.
Dagaci dai ya yi shiru kawai yana sauraronsa, ya ci
gaba da ccwa abin da ya kamata ayi ka bani yaron nan in
tafi da shi can birni in tura shi makaranta kai ma sai ka ji
saukin bacin rai kan kararka a kunne ba mai sake
tarenka da wata magana.
Dagaci ya ce to ai bani da wani dan a gabana shi
yasa bana son baka shi tuni ka ke nacin in bar maka ya
cc haba Yaya, wai ya za'ayi ka dinga tauye wa yaro
rayuwa nc? Shi kansa yanzu in ya dandana dadin zaman
can din ba zai iya zama a wannan kuncin ba, dakc ta
dakata kai mayc asalinka in ba kauyen ba a a kaga sha
sha sha zaka kawo min rainin hankali, ko don ka yi kupi
zaka fara gujewa kauye? To ba zai yiyu ka wulakanta
mana kauyc ba, kai dam ma ba dan darajar dan nan
abokinka dan gidan yawale mai gyada da yake abota da
fan gidan Hakimin garin nan aka biya masa kudin
makaranta ya jaka ku ka je godiya yallaßai ya tambaye
ka in da ka ke aka ce dan gidan dan Kande ne dagaci
Allah ya jikan rai Baba shi ne ya biya maka kaima
darajar baba ai da yanzu muna nan tare muna noman in
na mutum ana da ka dagacin domin nanne asalinka.
Alhaji lawan ya c e yaya kenan to Allah ya huci
zuciyarka ni bana fada don in raina kauyc ba ne sai don
in nuna maka irin ci gaban da muke samu in munyi
karatun." Ya çe to ai shima ya yi karatun domin shi yake
karanta min takardu in hakimi ya aiko da kafin ya iya ai
yaron nan dan gidan Asabe mai dambu nake sa wa yake
40
karanta min, Allah sarki kaga yaron nan shima shiru
ya bata abinni baya ko zuwa ganin iyaycnsa, da an
yi magana sai ace karatu sai ka ce alhuda huda, kat
ma haka ka ke so ka dauke shi ku nausa sai sanda
ku ka ga damar dawowa. Haba Yaya yausbe ayi
cikakken wata bai zo gida ya ganka ba, ai in A'lah
yaso da wuri zai dunga zuwa kuna ganawa, da kyar
dai ya samu ya shawo kansa zasu tafi tarc, dan da
nan Abubakar ya shiga hada shirgi za su tafi.
** **
Wayyo Baba, baba na tuba ba zan kara ba ji ka
ke wani tau fau rim za ki kuma binsa dan ubanki?
Wallahi ba zan kara ba, shegiya 'yar kundų gurun
buhun uba yau din nan zan maida ke gidan uwarki
ba zan iya ba, kije ki jawo min abin kunya yaran da
kowa yake shedarsa dan iska ne ki like masa sai
yaje ya yi miki ciki sannan ki bar mu da abin kunya,
wallahi ba za ki jawon abin fada ba. Ta shiga hada
shirgi na sai da ta gama sannan ta ce in tashi ta
maida ni gurin uwata na fara bata hakuri, ina kuka
amma ina sai da ta tilasta min na dauki kayan muka
tafi tana tafe tana ta faman masifa akan hanya ita
kadai, ni kuma ina biyc da ita har gidan su Innata, ta
sami Innata ta labarta mata abin da yake faruwa tun
daga farko har karshe. Inna ta ce to Hajiya aike ma
'yar ki ce yanzu ace a matsayinki na kanwar
41
mahaıfiyarta ba za ki iya hukuntata ba sai kin kawo
min ita? Ni din to wanne irin hukunci zan yi mata
wanda za fi naki? Ai kawai ki daukc ta ku koma
duk irin kukuncin da ya dacc kiyi mata domin kema
yarki
Haiva Tasalla ta ce, a'a, a'a babu abin da zai sa
in maida ita gata nan kema kya ga halinta tana gama
fadar haka ta tashi gami da cewa ni na tafi sai an
kwana biyu.
Inna ta na kiranta haka ta kada kanta ta fice ko
waiwaye. Innata ta juyo kaina ta kama min fada
abin da bata taba yi min ba, na yi kuka har na gaji
na yı shiru.
Kwanana biyu da komawata hannun Innata sai
wata matar kanin Inna ta ce da za'a kai ni can binni
kawar in ci gaba da karatuna da ya fi min wannan
shiraritar. Inna ta ce gaskiya bani da halin da zata yi
karatu sai dai in je in yi aiki a gidan masu hali ana
biyana albashi duk wata in yaso sai in dinga ta rawa
tana saya min kayan daki in an yi shekara biyu sai
in dawo gida ayi min aurcna. Matar kanin Inna wato
Gwaggo Halima ta ce shi kenan ai hakan ma ba zata
gagara ba tunda suna da yan uwa a can birni gidan
wata 'yar wanta zata kai ni can a samo min aikin.
Ba a dade da wannan magana ba, Goggo
Halima ta shirya ta ce nima in shirya muka tafi da
'yan kayana a leda sai birni. Muna zuwa gidan 'yar
42
wan nata muka sauka a nan mandari na ko yi sa'ar
matar gidan wata 'yar wan goggo Halima mai kirki
da ita ga fara'a sannan da son Jama'a ta karbe ni
hannu biyu goggo ta yi mata bayanina da abin da ya
kawo ni ta ce ito a yanzu dai kam babu wani aiki sai
dai ta zauna a nan in an sami mai neman mai aiki
koda reno ne sai a kaita goggo ta yi godiya sannan
ta ce in zauna a nan gidan nata tunda kila ba za a
daďe ba zan sami aiki.
Kwanan goggo biyu aka hada mata sha tara na
arziki ta koma gida, ni kuma na ci gaba da zama a
gidan ina taimaka mata da su shara wanke-wanke
wankan yara da sauran aikace-aikace ta ji dadin
zamana sosai don haka sai itama takc kyau tata min
sosai sunanta Rabi amma Aunty naji 'yayanta suna
kiranta da shi, shi ne nima nake kiranta da Aunty
Rabi.
Rannan Aunty Rabi ta yi kiran wata 'yar
makotansu budurwa kamar ni,m domin zami yi
sa'o'i da ita, ta ce wa ta dinga zuwa muna tafiya
makarantar Islamiya da ita in zata je ta yamma
domin da safe tana zuwa makarantar sakandare
amma day take yi, ta kuwa amsa kullum sai ta zo
mu tafi a haka har muka saba da ita na san sunanta
Safiyya. Tun muna haduwa lokacin makaranta
kawai har na fara zuywa gidansu hira gurinta har
muka saba in za'a aike ta mu tafi tare har muka
43
zama kamar shakikan Kawaye, barci ni kadai yake raba mu.
Wata rana muna zaune a gidan su Safiyya muna ta
hira ta ji komai ina fadar sunansa daidai sa6anin da
da ban san sunayen wasu abubuwan ba ga maganar
Kauycnci a bakina kasancewa ta 'yar kauyc fitik
domin Safiyya ta sha fama da kawayenta akaina
wasu sun bata wasu kuma sai sama-sama suke
magana domin a yadda suka dauke ni 'yar kauye ba
su so Safiyya ke kula ni ba duk sa in da na yi musu
magana sai su kama gwale ni da hantara da kyara
sai Safiyya ta nuna musu in har zasu dinga
wulakanta ni, to itama ta daina yi musu magana ba
ruwanta da su domin nima ai mutun ce kamar su na
ce ta kyale su ba komai rashin sabo ne, watarana
zamu saba da su ne. Ta ce, ai ba zai yiwu ba to shi
ne sanadin 6atawar ta da wasu kawayen nata.
Muna nan zaune sai ga wata bakuwar mata nan
ta yi sallama, muka amsa mata, da gudu naga
Safiyya ta karbi jakar dake hannunta ta kaya, suka
shiga daki Babar Safiya da muke kira da Umma ta
fito cikin murna ta ce, in je firji in debo mata lemo
da ruwa, na tafi da hanzarina na debo mata na
durkusa na ajiye mata sannan na gaishe ta. Ta dubi
Umma ta ce, wannan kyakkyawar yarinyar fa?
Umma ta bata labarin wato dangane da tahowata
neman aiki ta ce kash dadina da kauye kenan, ke da
44
acc 'yar nan ce yadda take da tsananin kyan nan ai
da ka samu jari in 'yarka ce, Umma ta yi dariya ta ce
ke kuma gaki mai idon cin naira ko? Ta ce A'a ba
haka ba ne yarinyar ce na yaba da kyanta ne so ai,
ta ce tsaya ki gani in ta samu hutu ta goge sai kin
nanteta in kin ganta, ta ce da ace Hajiya Lami
Kawata zata dauke ta wallahi da yarinyar nan ta huta
domin ba ruwanta masu aikinta suna jin dadinta
sosai ta ce a to ba sai ki yi mata maganaba in tana
sosai a kaita, ta ce to shi kenan a cikin satin nan
zanje dama ma yi maganar in yaso ni kuma sai inje
in sami Rabin ba? Ta ce yauwa shi kenan kinga ta
san da maganar itama bayan sun jima suna suna hira
ta gabatar da abin da ya kawo ta ta mike zata sai da
ta sake kirana ta ganin sannan ta ce kai wannan
yarinya Umma da ace