je gidanmu. Ya yi murmushi amma
dai ba ki yi wata biyu ba? Na ce uhm zancen ka ke
so, kaje ku gaisa da Aunty sai in fito mu tafi ya ce
61
to ya bi bayana har ciki ya shiga Aunty ta yi masa
sannu da zuwa suka gaisa sannan na ba da kayana
ya taimaka min muka yi sallama da Aunty Rabi
muka rankaya.
Tunda muka koma makaranta karatu muke yi
gadan-gadan da mun taso kuma a gida Ibrahim ke
mana lesson, yana kuwa koya mana abubuwa da
dama, ta yadda zamu dinga fahimta, haka dai muka
dings katu ba ji ba gani, duk lokacin hutu a gida
nake yın sa wato can kauyenmu gidan su Inna.
Hakika vanzu ni kaina nasan na hadu sosai don in
kin gan mu ba za ki banbance mu da Nusaiba ba,
domin sar k za ci nima 'yar gidan ce, gashi Mami
da Ahaji suna matukar kaunata saboda akwai
biyuyya ga ladabi da hakuri.
Ira zaune ni kadai a falo ina karatu yau Mami
sun fita ita da Nusaiba, da yake lahadi ce ranar hutu.
Shi kuma Alhaji ya yi tafiya kusan kwanansa hudu
baya nan sai Ibrahim wanda yake dakinsa a zaune
yana nazarin wasu takardu da Alhaji ya ba shi. Can
sai gashi ya fito ya same ni a falon shima ya zauna
ya dube ni muka hada ido ya yi murmushi ya ce yau
ina kawar taki? Na ce sun fita da Mami yanzu ta ce
ma in ka fito in fada maka kar ka fita tana dawowa
yanzu, tana son ganiuka. Ya ce shi kenan ke me
62
yasa ba ki bisu ba? Na ce bana son zuwa ko ina nc,
ya ce rabon mu yi hira ne, ya hana ki fita domin na
fuskanci Allah ya zuba miki kunya duk lokacin da
nazo domin in taya ki hira sai ki dinga nuna jin
kunyar Mami to yau dai bata nan, na yi murmushi ai
kasan kunya wata aba ce da Allah ya halicci mutane
da ita musamman ma ga mu mata, domin duk
yarinyar da bata da kunya kai koma matar aurc in
ma takaice maka kowacce irin mace ce aka ce bata
da kunya sai kaga darajarta tana zubewa, ba ma ga
mazan ba har ga matan ma, ya yi murmushi nima
ina son yarinya mai kunya kamar ke, na dube shi na
yi murmushi na ce, sai ka yi kokari ka samu, ya сe
ai na samu, na ce ya yi kyau au ba ki tambaye ni
wacece ba? Na cc ai ba sauri ake ba, zan sani ko ba
yanzu ba, ba ki dai damu da sanin ba kenan, uhm
Ibrahim kenan to wacece? Wallahi wata yarinya ce
tana nan doguwa amma ba can ba fara sosai, tana
da dogon hanci da manyan fararen ido bakinta dan
karami la66anta masu matukar laushi ga wushirya
nan siririya a bakin in ta yi murmushi kumatun ta
yakan lotsa tana da dogon gashin kai mai santsin
gaske, ga muryarta mai dadin sauraro kuma......na
dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu domin na
gano da wacce yake wato da ni yake saboda duk
kamannin da ya zana kamannina ne, don haka na
mayar masa da martanin cewa, a ita wannan da ka
63
ke so din tana da masoyinta wanda zata aura. Sun
riga sun yi alkawarin aure ba tun yanzu ba, don
haka sai ka yi hakuri ka nema a gaba, ya rumtse ido
cikin rashin jin dadin abin da na ce ya ce tabdijan
aiko ban ga abin da zai raba ni da ke ba, na yi
dariya, au yanzu ka fito fili kuma ka fada min, to ai
shukar dusa ka ke yi domin an riga ka. Waye ya riga
ni? baka san shi ba a garinmu yake, koma waye ba
abin da ya yi min zafi dashi, sai na kafa
gwamnatina, na ce amma kana da babban aiki a
gabanka ya ce wannan aiki ne? Abin da na sa kaina
ne fa? Na ce zan sa ido in yi kallo.
Tun daga ranar da muka yi wannan magana da
Ibrahim sa na shiga 6oye masa kaina bana yarda ma
wani abu ya hada mu domin mun fi sati biyu ba mu
ga juna ba bare ma wata magana ta kara hada mu,
haka muka zauna har tsawon wannan lokaci.
Rannan ina zaune a dakinmu yayin da Nusaiba
ke ta fafutukar hada mana kayanmu tana jerawa a
cikin wardrop dinmu, an ga mu mana guga ni kuma
ina warc uniform din mu daga cikin gugar sauran
kayan sai ga Yaya Ibrahim ya shigo fuskar nan tasa
a daure ya ce da ni maza ki je ki gyara min dakina
yanzu, ba musu na ce to, na mike na ce da Nusaiba
ci gaba kafin in dawo ta ce to na bi bayansa zuciyata
cike da tunanin nasan ba gyaran dakin zai sani ba,
domin bai taßa sa ni ba, sai da naga alamar mamaki
64
ma a fuskar Nusaiba, domin itama tasan ba ya sa ni
aiki.
Ina shiga dakin naja na tsaya, domin shima
tsayawar ya yi, ya juyo ya kalle ni zauna ga kuj era
nan magana nake son mu yi na ce to kawai na sanmi
guri na zauna ina fuskantarsa ya ce Hamdiyya ba ki
san abin da yake faruwa ba ko? Na cc cikin fargaba
me yake faruwa? Ya yi murmushi ba komai da wasa
nake miki amma wallahi naje gidan Aunty Rabi ta
ce babu wari saurayi da ki ke dashi, har ku ka yi
alkawari don haka ni dai in ma jamin rai ake yi don
Allah na jemu haka a daure a karfi soyayyata, na ce
kaima dai da komo da hannun agogo baya ka ke
wallahi, na gaya ma ina da saurayi kuma shi zan
aura to a name zaka damu kanka, to ai an gaya min
abin da ki ka fada ba haka ba ne. Na ce wallahi
itama Aunty bata sani ba, ni fa ban yarda ba saboda
haka ni dole ma a soni. Uhm shi kenan tunda ana
soyayya dole ma ji ma gani.
Ina tafe a harabar gidan ni kadai sai ga Ibrahim
nan da saurinsa, ya karaso in ia nake ya ce tun dazu
fa nake miki magana kina jina wai me na yi miki
ne? Na juya na kalle shi na ce, haba Ibrahim wallahi
abin da ka yi min ban ji dadin shi ba, ko kadan ya
ma za'ayi kaje ka sami Aunty ka hada ni da ita haka
kawai yau naje ta kama ni da fada har tana cewa
zata je gida ta hada ni da Innata, bayan na gaya
65
maka gaskiyar lamari wai ana soyayya dole nc? Ya
ce na gaya miki ana yi kuma koma ba a yi daga
kanki za'a fara bari ma Alhaji ya dawo sai na sanar
da shi kuma in ce kin amince min, ban san sa in da
hawaye ya zubo min ba, na ce shi kenan da ma ba
kauna ta ka ke yi ba domin da kana sona zaka so
abin da nake so, shi so duk sona ana sonkai ya fi
saboda haka ba zan faranta wa wani ni kuma nawa
ran ya yi baki ba, a nan na bar shi saboda takaici na
sami guri na kebe ina ta faman kuka saboda 6acin
rai.
** **
Aunty Rabi ce zaune ni kuma ina gefenta can
waje da ya kuma Ibrahim ne Aunty Rabi ta ce
Hamdiyya har yanzu na fuskanci akwai kuruciya a
tare dake yaron nan tsakani da Allah yake kaunarki
shi ko Abubakar kila ma yanzu ya mance da ke
banga dalilin da zai sa ki like masa kamar kaska ba.
Ibrahim ya ce wallahi aunty irin kaunar da
nake wa yarinyar nan ba zan iya misalita ta ba da
zan iya hakura da Hamdiyya da tuni na hakura da
ita saboda haka ni ki hada ni da wani muje in sami
Innar da kuma Baba Tasalla in yi musu bayanin
abin da ke faruwa tunda ke ta ki jin maganar ki kila
su taji tasu dan dai ma ban san garin ba ne da tuni
naje, Aunty Rabi ta ce ai hakan ma za'a yi kawai ina
66
jin haka sai na sa musu kuka domin na san in har ya
je gurin su Inna za su ba shi goyan baya. Rabi ta cс
ai kuwa komai kukan ki dole aje ka bari ni zan kai
ka da kaina." Ya ce shi kenan Aunty zan zo mujc,
ya dube ni ya ce taso mu tafi gida." Na ce cikin
kuka ka yi gaba zan taho Aunty ta ce ai dole ne ku
koma tare tunda tare kuka za kaje ka jira ta a mota,
ba musu ta tashi ya fita Aunty ta ce ke dai kam
wallahi ban san irinki ba, ban da abin ki ga yaro
kyakkyawa dan manyan mutane ga kudi har kika
samu ma ya ce yana sonki ai kin yi barka amma
komai mai ki kishi kuma kina zaune a gidansu da fa
aiki a ka kai ki ki yi ya hana ki aikin yasa ki a
makaranta gashi saura shekara biyu ki gama sannan
ga dadin duniya ya mallaka miki amima duk a banza
ki tsaye jiran wanda bai ma damu dake ba ba a
masan in da ya kc ba na ce ai duk in da yake nasan
yana nan yana tunanina. Shi kenan tunda ke duk
fadan da ake miki, ba kya ji ni daga yau ruwana da
ke kar ki kora zuwar min gida sannan kuma sai na
yi kutu kutun da aka hada auran naku muga tsiya,
fuuu, na mike cikin fushi na fita bako sallama sai ita
ce ma ta leka ta ce dashi sai an jima ranta a ba ce
har ya tada motar ta sake leko wata ce yazo ya fita
da saurinsa yaje sun dan jima suna magana sannan
ta koma shi kuma ya dawo a lokacin idona akan
kofar gidansu kawata Safiyya, na dinga tunanin da
67
tana nan da ta bani wasu shawarwarin akan wannan
lamari amma yanzu tana makaranta har ya ja motar
bai juya in da nake ba nima kuma ban ko kalle shi
ba sai da muka yi nisa muna tafiya sannan ya dan
juyo ya ce ina son in biya gidan wani abokina za ki
raka ni? Na cc Allah ya kaimu lafiya ya cc amin.
A kofar wani gida muka yi parking gidan ya
hadu sosai ya fito ya bude min bangaran da nake na
dauke kai ya ce, fito mana, na ce a'a ka je ka dawo
ina nan, abin ma ya zama abin dariya don haka sai
ya yi dariya kawai ya tafi abinsa, jim kadan sai
gashi da wani hadadden saurayi amma duk da
haduwar sa bai kai Ibrahim ba suka karaso ya zo in
da nake ya yi min sallama nima na mayar masa
sannan ya dan ran kwafa yayin da shi kuma gogan
yakc can gefe daya ya zubo mana ido. Ya ce yaya
bakuwar tamu ta cije daga nan ba za ta karaso ba?
na dan yi murmushi tunda ka karaso ai sai mu gaisa
daga nan din ma kawai ya isa. Ya ce ai ba
mutuncina ba ne na yi bakuwa amma na barta a nan
kinga ban yi adalci ba. Na ce ai ni nasa kaina ba sa
ni aka yi ba, ai ya kamata ki zo ko don ruwa kya
kurba kinga ba ki taba ganina ba in ba ki zo dan shi
ba kya zo danni. Na yi murmushi na ce dan ka r ka
ce na yi maka wulakanci zan je mu gaisa amma da
bazan fita ba ina gama fadar haka na fita ya сe
yauwa ko ke fa wallahi kin kyauta na bi bayansu
68
muka shiga har falon gidan na sami guri na aena
aka kawo min lemo juice da ruwa ina nan zaune sa
ga wata tsohuwa fara daga ganin matar tana da
kamala ga alama ma tana da rikon addini domin ina
ganinta na shaida hakan. Da fara'arta ta yi min
sannu da zuwa na amsa sannan na durkusa ra
gaishe ta tace min dama Ibrahim yayo min waya da
zu ya ce zaku zo na cce wallahi ta ce to yaya kuma
lamarin naku yake tafiya haka ne? Sai na yi dam
dani domin nasan Ibrahim ne ya bayyana mata halin
da muke ciki, na dai yi shiru domin na rasa amsar
da zan bata gashi matar tana da kwarjini a idona, na
ji kin yi shiru ba ki ce komai ba duk dai da nasan ya
kamata in dan baki lokaci ki yi tunani te kafin ki
fara tunanin ina so in dan ba ki wasu shawarwari
tukunna, ta dubi su Ibrahim da ke zaune ta се
Al'mustapha ku dan ba mu guri da Allah sukata shi
ba ko musu suka fice sannan ta dube ni, ta yi
murmushi mayafin da ta yi lullubi da shi ya dan
zama sai naga gashin kanta ya dan leko gaba da ya
babu ba ki sai fari wata furfura waunan furfura tata
daga gani ta nuna yawan shekaru ce ta ce da ni 'yan
mata ya ma sunanki? Na ce "Hamdiyya." Та се
Hamdiyya karar ki fa aka kawo min, na yi
murmushi na sunkuyar da kai kasa don kunya ta ce
kafin in fara cewa komai sai na tambaye ki tukunna
abin da yake faruwa tsakaninki da Ibrahim kar ki
69
boye min komai, nan takc na shiga mata gaya
gaskiyar lamari da kuma wanda nake kauna sai da
naga tas tana jina ba tare da ta katse ni ba, sannan ta
numfasa ta ce duk abin da kika fada min na gamsu
da su, domin dai ita kauna daya ce kuma in har
zuciya ta riga ta afu akan abu ta fa mai zare wannan
abu sai ya yi kamar me kuma ba lallai ba ne ya
samu nasara akan hakan don haka sai dai abi abin a
hankali shi Ibrahim yaro ne da in ya kafe a kan abu
duk abin da za a yi masa ba zai bar wannan abu ba,
to bare kuma abu ya kasance Kauna ce kun ga kuwa
sai dai abi a hankali kin ganni din nan ni Kakarsa cc
mahaifiyar uwarsa wadda ki ke gurin ta, wato
Hajiya Lami to kin ga dai in san raina zan bi zan
goyi da bayan jikana ne to amma da yake nasan
wahalar so nasan zakin kauna yadda takc a cikin
zuciya ba zan goyi da bayan jikana ba domin shima
yabe yazo zai yi a kan tsohon gini, wanda tun farko
ba shi ya gina ba tarar wa ya yi an yi saboda haka
shawarar da zan ba ki, ki janye wannan ra'ayin na
kin yi masa magana da kin kulawarki a kan
soyayyarsa ki ba shi hadin kai ku dinga gudanar da
soyayyarku amma fa wannan batu naki yana nan a
zuciyar ki kafin nan kafin ki kare makaranta, in
yaso in an gama karatun sai aje a binciki shi wancan
din in yana nan kan bakansa shi kenan, in kuma ya
sami wata to shi kenan sai an gon nawa ya fita, to
70
kunga komai yazo da sauki kenan, amma yanzu in
ki ka ce kin daina kula shi kuma haukaccwa zai
dinga yi akan ki wanda a karshe giyar so zata iya
tunzura shi ya shiga cikin wani halin na daban kuma
duk wadannan maganganun da ta yi na yi kasake da
kunne ina sauraronta, sai da ta gama na ce mata pa
yarda da abin da ta ce, na kuma dauki wannan
shawara tata, da hannu biyu. Ta yi farin ciki sosai
sannan ta ce in je in kira su, na fita na same su a
waje suna ta hira na ce su zo tana kira gaba daya
suka taso idon Ibrahim a kaina na yi saurin shigewa
cikin gida na same ta suma suna shigowa suka zobe
ta ce angon Hajiya ga amaryar taka nan sai ku tafi
ko? Ko ba amaryar ta saba ce, na ji kunyi shiru? In
dai amaryarta sa ce za ki yi murmushi, yanzu na
sunkuyar da kai kasa ina murmushi na rufc fuskata
da mayafina ta yi dariya ta ce to shi kenan sai ku
shirya maza ku je gida kar aga kun dade. Batun
farin ciki kuwa a gun Ibrahim ai ba bayani, bare da
ya fuskanci hakarsa ta cimma ruwa, ai nan take ya
fara baiyana farin cikinsa a fili, ya ce in zo mu tafi
ni na ce to muka yi wa Hajiya sallama muka tafi a
kan cewa sai an kwana biyu zamu dawo.
** **
Ina zaune ni kadai sai zancan zuci nake yi, ba
abin da nake tunani sai Abubakar, ko a wanne hali
יר
yakc? oho, in da haka ne ai sai yayo mın aikc da wasika to ta wacce hanyar? Na tambayi kaina to ko da ya janye ne? Na fara juyayin lamarin aiko in har ya yi min haka bai kyauta min ba, ga Ibrahim mai kaunata da gaskiya ban ji ina sonshi ba ne abin da zuciyata ta aiyana min kenan, ai kawai kokari zaki yi ki cusa kaunar sa a zuciyarki in ji wani bangare daga zuciyata, to ta yaya? Wancan 6angaren ya tambaye ni.
Ina cikin wannan batun zucin sai jin kamshin
turarc nayi ya daki hancina, na yi saurin juyawa ashe Ibrahim ne a tsayc take ya zauna dab dani jikinsa yana gugar jikina na yi saurin matsawa na ce haba Ibrahim wannan wanne irin abu ne ni gaskiya ka daina yi min irin wannan zaman. Na zakuda ya kalle ni kawai ya ce to mai na yi miki kuma? Yanzu
dan na zauna sai abin ya zama laifi? Ki tuna fa mu masoyan juna ne, wata rana muna sa ran kasancewa ma'auratan juna. Na tabe baki na ce a wai to kuma shi kenan don nan gaba zamu yi aure....na sake jan wani tsakin ba tare da na gama fadar abin da nayi niyya ba, na mike domin haka kawai sai na ji yana bani haushi, ya mike shima ya tsaya kusa dani ya kira sunana na amsa a ciki ya ce wai don Allah dan Annabi me Abubakar din nan yake miki wanda yaja hankalinki haka da yawa? Nima in dinga yi miki ko na samu nima a dan Gantarar min kaunar nan nima
72
in dan ji sanyi a raina. Na juyo a fusace na ce kaga
ni dai na ce ka kyale ni na ce ka kyale ni ka ki
wai ya ka ke so in yi da raina ne? Sai muka ji ana
cewa kai ka Ibrahim yaya nc? Me yake fanuwa
dukkanmu muka juya ashe Alhaji ne yake kallonmu
ta barandar bene, kuzo nan dukkanku, take muka
nufi ciki, kafin mu karasa ya dakatar dani na Ki
tsayawa ya ja mayafina cewa yakc don Allah in
Alhaji ya tambaye ki waki ke so ki ce ni don Allah,
wallahi ni ne mai kaunarki da gaskiya, na yi masa
banza na ci gaba da tafiya ta abina.
A zaune muka same shi yana jirarmu, cikin
sanyin jiki na durkusa na gaishe shi ya amsa cikin
fara'a sannan ya tambaye ni me ya hada mu da
Ibrahim? Zai yi magana yasa hannu ya dakatar da
shi, da cewa ba kai na tambaya ba, a gaskiya da
kunya in ce don ya ce uana sona ne don haka sai na
sauya dabara na ce Alhaji cewa ya yi yana son shi
ne na ce ya tsaya in yi shawara shi ne yake jin haushina, yana jin haka ya yi murmushi ya ce to kai
in ban da shirme irin naka don ta ce zata yi shawara
maye laifinta? Kai ba jika yi ta ce bata sonka ba ba
sai ka bata lokaci ba? Ka sani ma ko ta gama shawarar ta zabe ka? Na yi murmushi a boye ya ce Alhaji karya ne wai cewa ta yi tana da....ya katse shi dancewa kai kai kai yi min shiru da Allah, tashi bani guri kar in kara jin ka tsare ta da wannan
73
in dan ji sanyi a raina. Na juyo a fusace na ce kaga
ni dai na ce ka kyale ni na ce ka kyale ni ka Ri
wai ya ka ke so in yi da raina ne? Sai muka ji ana
cewa kai ka Ibrahim yaya nc? Me yake faıwa
dukkanmu muka juya ashe Alhaji ne yake kallonmu
ta barandar bene, kuzo nan dukkanku, take muka
nufi ciki, kafin mu karasa ya dakatar dani na ki
tsayawa ya ja mayafina cewa yakc don Allah in
Alhaji ya tambaye ki waki ke so ki ce ni don Allah,
wallahi ni ne mai kaunarki da gaskiya, na yi masa
banza na ci gaba da tafiya ta abina.
A zaune muka same shi yana jirarmu, cikin
sanyin jiki na durkusa na gaishe shi ya amsa cikin
fara'a sannan ya tambaye ni me ya hada mu da
Ibrahim? Zai yi magana yasa hannu ya dakatar da
shi, da cewa ba kai na tambaya ba, a gaskiya da kunya in ce don ya ce uana sona ne don haka sai na
sauya dabara na ce Alhaji cewa ya yi yana son shi
ne na ce ya tsaya in yi shawara shi ne yake jin haushina, yana jin haka ya yi murmushi ya ce to kai
in ban da shirme irin naka don ta ce zata yi shawara
mayc laifinta? Kai ba jika yi ta ce bata sonka ba ba sai ka bata lokaci ba? Ka sani ma ko ta gama shawarar ta zabe ka? Na yi murmushi a 6oye ya ce Alhaji karya ne wai cewa ta yi tana da......ya katse shi dancewa kai kai kai yi min shiru da Allah, tashi bani guri kar in kara jin ka tsare ta da wannan
73
magana, shi so ai ba a dole, take na ji wani dadi ya
lullubc ni na mike Alhaji ya ce i tafiyarki kin ji, kai
kuma dakata ina da magana da kai, na yi ficewata
abina ban san me zai ce masa ba ni dai a ganina
cewa zai yi ya kyale ni kawai in na nutsu ya furta
min.
Yau gidan Aunty Rabi na nufa ban jira Ibrahim
ya kai ni ba, domin ban nuna masa za ni wani guri
ba. Nusaiba ce kawai ta sa ni sai Mami. Na san
kuma in har ya dawo yaga bana nan ya tambayi in
da naje aka gaya masa cewa zai yi zai je ya dauke
ni, da isa ta gidan kamar kullum Rabi na ganina da
murnarta ta tarye ni ta ce yau kuma ina mutumin
nawa? Na ce ai baya nan ta ce gaskiya man na ganki
ke kadai, na zauna muna gaisawa da ita kwatsam
kamar daga sama sai ga Haulc nan tazo, haba wa
murna a gurina kamar me take na afka jikinta
saboda murna itama sai faman murna take yi mukа
zauna na kawo mata abinci da ruwa, da lemo sai da
taci ta nutsu sannan muka shiga sabuwar gaisuywa
da tambaye-tambayan mutanan gida, ta ce duk suna
nan lafiya bata je kauye su Inna ba, Baba Tasalla
ma bata san zan zo ba na ce kuma kinga ne
kwatacan da na yo miki ta ce na gane mana ban ma
wata sha wuya ba, tasa hannun ta dafani ke na ta
baki da alheri na ce ya aka yi ta zuge jakarta ta ciwo
wata wasika ta ce gashi in ji Abubakar din ki ya ce
74
SL
in kawo miki, na ce ke don Allah take na karba na
wara jikina na Gari na bude domin in ga abin da a
ka rubuta min haba wa ga abin da ya rubuto, bayan
na duba adireshinsa.
Gare ki abar kaunata har kullum.
Tunaninki da shi na kc kwana da shi nake
tashi, Allah yasa kin rike alkawari kamar yadda
nima na rike alkawari?
Bayan haka wallahi Hamdiyya ban ji dadin
zuwa gida da na yi ban same ki ba, ina sanar miki
wannan shi ne zuwana can kauye na uku ba tare da
na bi ta gidan Alhaji ba, sai ace min kina Kano
kema, kina karatu, to a nan nayi matukar farin ciki
sai dai na rasa hanyar da zna bi mu hadu, to shi ne
na yanke shawarar rubuto miki wasika in bai wa
kawarki Haule ta kawo miki. Da yake na tambaye ta
ko tasan in da ki ke? Ta ce min ta sani, domin kin yi
mata kwatance.
A karshe nake cewa a rike min amanar
kaunata hannu biyu kar a sake wani abu ya jangwale ta.
Daga karshen nake cewa ki huta lafiya.
Mai Kaunarki, Abubakar Isa Dagaci.
Na rungume letter nan a kirjina ina ihun murna
kamar an yi min gafara, Aunty ta shigo da sauri
domin da suka gaisa da Haule fita ta yi ta bar mu a
dakin. Ta ce mayc haka kuma? Na ce Aunty wallahi Abubakar ne ya yo min wasika, kin ganta karanta ki
ji, taje wani dogon tsaki ta galla min harara ta ce ke dai wallahi ta ki ji dadin halinki ba, ga yaro dan mutunci karıar ya mutu a kan kaunarki kin like wa
wani banza wanda ba abin da yake ransa sai
yaudara, to wallalii ki kiyayi kanki, domin wannan
ba zabin arziki ki ka yi wa kanki ba. Duk abin da
Aunty ta ke fada jinta kawai nake yi, kamar busa
dama na ji ta dame ni da masifa sai na ce da Haule
tazo mu tafi can gidan su Ibrahim kawai, muka yi
wa Aunty sallama muka tafi.
A falo muka sami Mami a zaunc tana ganin
mu ta tarye mu da fara'arta, bayan mun gaisa ne
take tambaya ta a ina ki ka samu kawa? Na ce ai
Haulatun da nake gaya miki ce, tazo gurina ta yi
farin ciki da ganinta sannan ta sa na kawo mata
kayan ciye-ciye, da su lemo ta ce ta fara tabawa
kafin a gama abinci. Nan muka zauna muna ta hira
har wani lokaci na tambaye ta yaushe zata koma ta
ce min kwana biyu zata yi muna nan zaune muna
hira sai ga Nusaiba ita da Ibrahim, sun shigo dama
ashe Mami ce ta aike su nan na gabatar musu