bakina ina dariya, a ciki
sai ya yi murnushi ya ce yanzu ina zaki je? Na ce
kasuwa zani gurin sayar da rogo, ya ce to sai kin dawo
na ce to, har na tafi sai ya tsayar dani na tsaya ya ce ki
taho min da alakoro na ce to zan kawo maka amma sai
na dawo.
**
Yau ba mu da abin wutan dafa rogon gobe, don
haka Baba ta ce in je in yo abin wuta maza in dawo na
ce to, na dauki wata doguwar igiya na tafi domin dauro
abin wuta, Dab da dajin da muke dauro abin wuta naga
su Jimmala sun taru sun kai su goma suna zaune duk da
16
gabana ya fadi ban fasa karasawa ba, domin in na ce zan
koma kafin inje kauyenmu sun kamo ni na yi imanin
wannan zaman nasu bana lafiya ba nc, akwai abin da
suke jira. Ina karasawa na yi musu sallama ba wanda ya
amsa min, don haka sai na wuce su ban saurarc su ba,
gaba dayansu suka tashi kamar hadin baki suka tsaya
wasu a gabana wasu a bayana, na yi matukar jin tsoro
amma sai na daurc na ce ku bani hanya mana in wuce
suka ce dama ke muke jira yau kwananmu uku kullum
sai mun zo nan nemanki, ba ki zo ba, to yau Allah ya
kawo ki, sai kuma mun raunataki muga ta tallan rogo, ke
ga mai kasuwa har wata takama ki ke yi kin kashe mana
kasuwa ko? Na ce ni wallahi bani na kashe muku
kasuwa ba, amma don Allah ku yi hakuri, in dai tallan
rogo ne ni ba a son raina nake yi ba, wallahi in naje gida
zan ce da Baba ta sauya min wata sanar......Ban rufe baki
ba sai ji nayi sun rufe ni da duka, ta ko ina, da
tsumagiyar lalle tun ina iya ihu har na kasa suka jani ta
karfi suka kaini cikin dajin suka daure ni da igiyata a
gindin wata bishiyar tsamiya.
Wannan shi ne farkon labarin
Mummunar hallitar tasa, ta saua lokaci daya, girgizar da ya yi ta koma siffar Abubakar sak, babu banbanci ya doso in da nike a daure idanuna a rufe ban
san abin da yake faruwa ba, ya kwance min daurin na bude ido da kyar, na dube shi cikin tsamin jiki na ce Abubakar yaushe kazo nan? Ya c e yanzunnan na zo na
same ki a daure shi ne nayi mamakin abin da ya jawo
17
haka. Ta yi murmushin karfin hali ta ce, wallahi ba wasu
ne suka aikata min haka ba sai su Talatu da Jimmala, ya
girgiza kai cikin tausayi ya ce'muje in raka ki gida.
Baba Tasalla sai fannan fada take kamar ta ari baki,
wallahi tunda haka ne, kin daina dauko rogon dagayau
gara ki sake wani abun, har yausbe su dinga yi miki im
wannan dukan wata rana ma ai sai sun 79ma sanadin
ranki gara ki saro goro shi yafi miki sauki kawai, na ce
Baba da ki ka je gidajen nasu mai suka ce, iyayen nasu?
ta ce me zasu ce, kuwa cewa suka yi ayi hakuri ba za su
Kara ba.
Abubakar na fa gode sesai, kaga ba đon kai ba
wallahi da ban san halin da zan shiga a wannan dajin ba,
domin yamma ta riga ta yi ga shi ba kowa." Ya yi shiru
yana mamakin wannan godiya, shi dai ya ji labarin wai
yan matun unguwar sun dake ta, har ma sun daure ta a
jikin bishiyar tsamiya, amma shi sam bai je dajin ba ma
a wannan rana, ko dai tsananin firgita ce da azabar duka
tasa ta mance wanda ya taimaka mata, ko ta kasa gane
shi don haka ya ce a ransa gara kawai ya amsa mata a
cewar shi ya taimake tan, ya c e ai ba komai da ya same
su ma a gurin sai ya hukunta su sosai, nan suka yi
sallama ta tafi saro goranta, dama a hanya suka hadu.
Usaina ce tsaye daya daga cikin 'yan matan da
suka yi min duka, yau ita kadai zata je ta samo abin
wuta, tana tafc ita kafai yayin da shi kuma ya tsago kasa
ta bayan ta cikin mummunar balittarsa mai kama da
bakin goggon biri, ya yi girgiza ya juye kamannin
Abubakar sak ba wani bambanci ya biyo bayanta ya
18
kirata ta juya da sauri ta tsaya ta ce au la Abubakar ina
za ka je kaima icen zaka samo?" Ya ce cikin fushi, me
yas aku ka daki Hamdiyya? Ta cc a'a ka ji mu. da
Abubakar dinnan ni kadai na dake ta zaka wani tsare ni
ka ce me yasa na dake ta? Tana gama maganarta ta ci
gaba da tafiya cikin isa da rashin kunya, ya sami irin
tsafgar da suka dake ni da ita, ya kama dukanta tun tana
ihu tana neman taimako har ta suma, ya daure ta da
igiyar hannunta a jikin dorawa ya koma kamarsa ta asali
ya бace.
Wani mutum ne mai saran itace ya ganta daure
tana numfashi dai dai, ya kwance ta ya tafi da ita cikin
kauyen, yana tambayar gidansu, har ya samu ya sami
iyaycnta ya yi musu bayanin yadda ya same ta, a halin
neman taimako shi ne ya taimaka mata don kar ta
halaka. Iyayenta suka yi matukar godiya sannan suka
shiga taimaka mata don su samo kanta ko sa ji wanda ya
aikata mata wannan mugun abu.
Bayan an kwana biyu ta samu sauki, shi ne take
gaya wa iyayenta cewa, Abubakar ne ya dake ta wai
akan sun doki Hamdiyya, haba wa, ai sai gidan dagaci,
suka kai masa karar dansa Abubakar, akan abin da ya
aikatawa 'yarsu, nan da nan ya kira dan dan tambayarsa
dalilin da ya sa ya daki 'yar mutane, kuma ma
mummunan duka irin wannan wanda ba dan da
kwananta a gaba ba sai ya halakata. Da Abubakar yazo
aka gaya masa laifinsa, sai ya yi mamaki wai da aka ce
shi ne ya doki Usaina, ya dubi Usaina ya ce, yanzu
Usaipa tsakaninki da Allah kin ganni a dajin ma? Ta cе
19
ba kai ne ka dakeni ba wai don mun daki Hamdiyya."
Ya yi salati ya ce ki ji tsoron Allah Usaina, ta ce wallahi
kai ka dake ni, ya rasa abin da zai ce kawai ya yi shiru
yana mamakin irin sharrin da ta kulla masa.
Uban ya ce, kaga kar na kara jin ka yi irin wannan
ranka zai baci, ya basu hakuri matuka gami da cewa in
Allah yaso ba za su kara ba. Suka tashi suka tafi, shi
kuma ya yi wa dannan sa fada kamar yadda ya kamata,
shı dai yasan ba shi ya dake ta ba, haka ya hakura ya
amsa laifinsa.
Dan da nan zance ya cika gari Abubakar ya daki
Usaina akan sun daki Hamdiyya, hakanne ma yasa
Hamdiyya samun Abubakar din na ce Abubakar ka da
ma kyale ta ka yi ya wuce duk abin da suka yi Allah zai
saka min kaga irin wannan bai da amfani a dinga zagin
ka a gari ana cewa saboda ni ka daki wata ya ce ai ba
komai insha Allahu daga wannan na daina.
** **
Sauri nake tayi faram-faram da farantin goro a
kaina na dawo daga talla ga magariba ta kusa Baba ta ce
kar in zauna. Tun daga nesa nake hanmgo duhun abin
kamar mutum kamar ba mutum ba, na dai daure na ci
gaba da tafiya, domin ita kadai ce hanyar da zata kaini
gida. Ina zuwa gurin sai naga ba komai sai nace a raina
ashe dai idanuna yake yau dara ta. Na wu ce abina
kwatsam sai in nayi ta bayana an ce malama Hamdiyya
gida za'aje ne nayi firgigit na juya domin ganin mai
maganar, sam ban san da mutum a bayana ba, na san dai
20
ni kadai nake tafe, hakannc ya sani mamaki da sauri
juyawa Abubakar nc yana tafe yana murmushi na ce
Abubakar wallahi ban san da kaine ba." Ya ce ai tuni na
hango ki shiyasa na ce bari in zo mu gaisa daga talla ki
ke ne? Na ce e, har ma na dawo. Ya ce ina alakoro? Na
ce dauki wanda ka ke so ya sa hannu farantin na bisa
kaina ya dauko wani farin goro kalle babba wanda a iya
sanina dai bani da irinsa a farantin domo gorukana
jajaye ne duk da dunbun mamakin da na yi sai na boye
na ce wannan din ya yi maka? Ya ce ya yi min wannan
din ma zan bara shi biyu ki ci bari in ci bari, na ce to me
aka yi kenan? Ya ce kyautar ki gudan da kika bani ni
kuma 6arin da na baki shi ne kyautata da ke na yi
murmushi na cinye barin nan take duk da ba cin goro
nake yi ba,,ban yi mamakin cinyc 6arin da nayi ba. Ya
kira sunan Hamdiyya na amsa ya ce ina son in baiyana
miki wata magana amma ina tsoron irin amsar da za ki
bani, na ce fadi mana ai ba komai ya ce wallahi ina
matukar kaunarki sai dai ina tunanin ko kuma kina
sona? Na yi murmushi na ce wallahi ina kaunarka
Abubakar kar ka ji komai." Ya ce, to shi kenan na yi
farin ciki da wannan kauna da ki ka nuna min ya zaro
wani zobe na gold ya miko min in go saka a hanunki na
kar 6a na sanya a hannuna ina mamakin irin kyau zoben
na ce, ni ko ban taba ganin ka da shi ba, ya yi murmushi
ai zoben aurena igiya goma sha biyu, na yi dariya
dom,in a zatona wasa yake yi min ya yi murmushi to sai
yaushe kenan matar?m Na ce au har na zama matar? Ya
ce tun yaushe na ce to sai na ganka ya ce zan zo gobe da
21
yamma, na ce Allah ya nuna mana, ya juya ya tafi ni
kuma na karasa gida.
Da saurin ta fici-fici ta doro buhun nikanta aka
tana ta saun ta biyo labiba kowa sai ita kadai ga yamma
ta yi mata da yake yau ayi cikawa a in jin sai tana cikin
tafiya sai ta ji an kwada mata mari, take dan buhun
nikan ya fadi can gefe ta dafe kumatu ta ce kai kai kai
Abubakar me nayı maka? Yana tsayc a gabanta ya cе
Sa'ade dan ubankı me Hamdiyya ta yi muku ku ka kama
ta da duka, har da dauri? Kafin ta yi magana yasa irin
tsafgar da suka dake ta da ita ya fara dukanta, tana ta
faman tsandara ıhu ba mai ceto sai da yaga ta galabai ta
sannan ya daure ta a bishiya ya aje mata nikan ta kusa
da ita ya yi girgiza ya bace, ba tarc da tasan ko waye ya
dake ta ba Sa bayan magariba ubanta ya biyo sawunta
yazo da dai in da take ya ji nishinta ya haska ya ganta a
guje ya kwance ta yana salati ya tambaye ta wa ya yi
mata wannan aika-aika ta ce Abubakar dan gidan dagacine, ai ko a wannan daran uban bai zame ko ina ba sai
gidan dagacin ya sanar da shi abin da ya faru ran Dagaci
ya yi mummunan baci, ya sa aka yi kiran Abubakar ya
tamnaye shi dalilin da yasa shi wannan aika-aika, yana
jin abin da mahaitiusa ya ce, ya yi salati ya ce wallahi
Baba yau ni ina ma filin ball kuma ban baro filin ball ba
sai bayan magarıba zuwa na gida kenan na yi wanka na
ji alwala zan yi Sallah aka ce in zo in ji ka Daga ci yalce
da uban sa'ade to kai ka ji abin da yake ya certhaba
'Yallabai da bai aikata ba, ai ba zan yi masa sharnv bà
yau mike da shi? Da can ban yi masa ba sai yanzu?
22
1
Dagaci ya ce kai ka gaya min gaskiya, ba kai ne in kuma
ba kai ba ne ka fada ya ce ni ina da sheduna, wadanda
muka je filin ball din tare da su. Ya dubi shi Baban
Sa'adan ya ce a kira su yanzu ko zaka bari sai da safe
Ya ce a yi kiran su yanzu mu ji ta bakinsu kawai." Take
Abubakar ya fita neman shaidu.
Dan da nan ya juye kamannin Isına'il babban
abokin Abubakar wanda da shi ne suka je ball din da
yamma ya tsaya a kofar gidan su Abubakar din yana nan
sai ga Abubakar ya fito a fusace yana ganinsa ya ce
yauwa dama kai na fito nema, ya ce gani nima yanzu da
zan tura a yi min sallama da kai sai na ji maganar ka a
zaure gurin su ba ba," Ya ce haba ai abínne'da bakin
ciki, shigo daga zauran shaida zaka yi min." Ya сe "Tо
muje." Suka shiga suka zauna, bayan ya gaishe su sai
Dagaci ya ce Isma'il dama tambayarka nake so in yi, ya
ce to Raba Allah yasa na sani ya ce wai da gaske kunje ball yau kai da Abubakar? Ya ce yau da yaushe fa'? Abubakar ya yi saurin cewa da yamma ba muna tare a
filin ball na yamma da gari ba? Ya ce labbas mun yi ball
amma ba kai Abubakar ba zan goya maka baya ka dinga yi wa Baba karya ba, naga cewa ka yi ka tafi unguwar kudu gnrin Tsalha abokinmu." Baban Sa'a ya ce to ka ji gaskiya ko Allah ya taimake ka? Na gaya na shi ya yi dukan nan ya musa mana unguwar kudu nan Sa'a ta kai nika, gu yaro ya fadi gaskiya. Abubakai ya ce ekin tsananin mamaki yanzu Isma'il ni zaka yi wa kaharu ko, amma da yammar muna tare ka ce ban yi ball ba Ya damki kwalar rigarsa yana huci da kyar aka banbere shi. 23
Dagaci ya ce je ka abinka Isma'il Allah ya yi maka
albarka kai kuwa yau sai ka gaya min hadinka da
yarinyar nan Hamdiyya, har ka kc bugun 'ya'yan mutane
domin sun dake ta daga yau ka daina in Allah yaso ba
zaka maida ni mutumin banza ba sakarai kawai. Isma'il
ya yi ficewarsa ya na fita ya girgiza ya koma
kamanninsa na gaskiya ya yi tafiyarsa.
Dagaci ya dubi Baban Sa'ade ya ce ka yi hakuri in
Allah yaso daga wannan karon ya daina, ya kawo kudi
masu yawa ya ce ga wannan a saya mata magani. Baban
sa'ade ya karba ya yi godiya ya tafi. Dagaci ya dubi
dansa Abubakar ya ce mayc hadinka da Hamdi yya? Ya
ce wallahi Baba ba abin da ya hada ni da ita, abin da ko
kulata bana yi sai dai ita duk in da ta ganni sai ta yi min
magana, to ni kuma bana iya kin yi mata magana, domin
ba kyau wulakanta mutum amma ban da haka ba wata
alaka da ke tsakanina da itą. Dagaci ya ce to daga yau ka
daina yi mata maganar ma in ba baka ba sai ta jefa ka a
masifa, ka ji ko? Ya ce to Baba in Allah yaso ba zan
kara koda kallonta ba ma." Ya ce to shi kenan tashi ka
je."
Abubakar, Abubakar, Abubakar, aka ji dan iska
ashe kana ji ina yi maka magana ka yi banza da ni,
dakata Isma'il kar ka maida ni wawa ban san abin da
nake ba, daga yau wallahi kar ka kara cewa ka sanni
bare har ka yi kuskuren yi min magana, bayan ka riga ka
gama tozarta ni a gaban Baba jiya sannan yau zaka zo ka
24
yi min wani dadın baki? Ai ni ban san dama irin zaman
da ka ke yi da ni ba sai yanzu." A da isma'il ya dauka da
wasa Abubakar yake yi masa, daga bisani ya gano abin
nasa da gaske ne, ya ce Abubaka r wai mc yake
damunka jiya jiya mu rabu lafiya amma yau kazo min da
wata fuska kodai ka shiga shayc-shayc ne, ban sani ba?
Ya damki kwalarsa kai wayc dan shayc-shayen sharrin
da zaka kara dora min kenan? To wallahi mu zuba
wanda bai fasa ba baya kaunar uwarsa ba abin da Isma'il
yake ja sai Innalillahi, domin abin ya wuce hankali, ya
ce to na ji cika ni ka yi hakuri yasa mu ya banbari
wuyan rigarsa da kyar, ya kama gabansa yana mamakin
abin da ya faru a yau din nan tsakaninsa da babban abokinsa Abubakar.
Haba Abubakar me na yi maka zaka ce kar na kara
kula ka? wa ba ka ji yadda nake mutuwar kaunarka ba,
in wani abu na yi maka ai sai ka fada min in yaso in kiyaye gaba, ni ba abin da ki ka yi min kuma haka ake yi ni ban ce ina sonki ba sai kawai ki ce min wani kina
sona ke ko kunya ma ba kya ji a matsayinki na mace mai mutunci ai sai ki bari in ma ina son naki in fara furta miki, ta ce au ni ce ma na fara cewa ina sonka ba kai ke
fara cewa kana sona ba? Yacca gidan uban wa? Abin
ya bata mamaki ta ce ai har da zagi baga zoben ka da ka bani ba ka ce min na aue ne? Ya kalli zoben ya ce wai ni
me yasa ku ke raina min hankali ne? A yaushe na ba ki zoben? Ta ce, ka raina min hankali ka bani abu ka се wani ba ka bani ba, to amma shi kenan ta zare zoben ta cilla masa ga kayan tsiyar ka nan nima bana so kuma kar
25
ka kara kula ni ya dube ta ya cc au kayan tsiya ta ko dai
ke kayan tsiyarki, ni ban baki wani zobe ba, sai ki mayar
wa mai shi yana fadar haka ya juya abinsa ya bar zoben
a gurin itama ta yi shigewarta cikin gida ranta a басе.
Suna barin gurın ya tsago kasa ya dauke zoben yа басс.
Ina ta sharar bacci na yi nisa a cikin barcina dakin
da duhu domin na rage fitilar kafin na kwanta na yi juyi
gami da jan dogon minshari a fisge na ji kamar na
dunguri mutum na alhalin ni daya nake kwana, na yi
saurı na tashi na Karo fitila ba kowa don haka na koma
na kwanta jim kadan barci ya sake fauka ta juyi na biyu
sai na ji ni a jikin mutum yana rungume da ni ga wani
daddadan kamshin turare wanda na tabbatar turaran da
Abubakar ke amfani da shi ne, na kuwa kwala ihu gami
da neman- taimakon jama'a wuf na ga an yi hanyar fita
daga dakin da gudu, mutane suna fitowa suka ga an
tsallaka ta katanga a guje kafin a bude kofa a bishi ko
sama ko kasa ba wanda ya ganshi don da nan kowa ya
hallara a tsakar gida daga masu gora sai masu sanduna
aka tambaye ni waye ya hauro ya shigo dakina na сe ba
kowa ba ne sai Abubakar dan gidan Dagaci, domin irin
Kamshin turarensa naji kuma sannan ga zoben sa da ya
bani ya barshi, mutan gidan suka ce iskancin da yaron
nan yake yi ya fara isa da safe zasu je su gaya wa
Dagaci. In bai ſau mataki a kan dansa ba to su za su
dauki doka a hannunsu ma'ana za su hukunta shi don rai
nin hankali ya shigo musu gida da tsohon dare zal lalata
musu yarinya? Masifa kuwa gurin Hajiya Tasalla
bakinta har kumfa yake yi, saboda fada, cewa take yi
26
ل
3
t
wallahi in har dagaci bai yi wani abu ba a kai to zata kai bırni gurin Hakimi domin ba za a lalata min 'ya ba, ina ji ina gani.
Kashe gari da misalin karfe bakwai na safe mutan
gidan mu ne maza da kuma ni da baba da mijin baban
zaune a kofar gidan maigari yayin da suka baiyana masa
abin da ya faru, sai Dagaci ya cika da mamakin wannan
abu ya kira dan nasa domin wannan magana ce mai
girma. Yana zuwa ya ganmu a zaune alamar mamaki ya
baiyana karara a fuskarsa, ya sunkua ya gaishc da 'yan
gidan mu amma ba wanda ya amsa masa, ya yi kasa ke dan jin kuma abin da za ace ya yi
Dagaci ya karanta masa laifinsa yana ji ya mike a
fusace yana cewa wai me ake so da ni ne? Haka kawai
kowacce irin shara sai a dinga kwasowa ana zuba mon
sai ka ce wanda ba shi da galihu? Ke yanzu Hamdiyya
irin sakamakon da za kı yı min kenan? Na ce aí da ba ka
aikata ba ba zan ce kai ne ba, d ya ji abin da na ce sai
ya fashe da kuka, na ce in karya na ke maka ai ga zoben
kama jiya jiya muka yi fada da kai na baka kayan ka shi
ne ka je dashi cikin dare don kar esirinka ya lonu ka bar
min shi ka gudu. Saboda tsananin bacin rai Dagaci ya zari wani katon katako ya fara maka wa Abubakar da kyar aka kwace shi, duk kansa ya fashe va umbura saboda duka, dagaci ya dinga basu hakuri va, ve haifi da ne amma ban haifi halinsa ba, nar da kuka dorkin ciki ya dubi Abubakar ya ce wallahi in ba ka gyara halinka ba sai na tsing maka ka lalace gaba dayanin ba ka da wani amfani a tare da ni saboda bakin ciki ka
27
sa magana Abubaka r ya yi suka tashi suka yi sallama da
dagaci ya dinga basu hakuri akan in Allah yaso ba za a
sakc ba.
Su su tara ne cif suka nifi rafi domin yin wanka
sunc ya rage wadanda basu sha bulalar Abubakar ba, to
su goma sha daya ne dama ya daki uku wanda iyayensu
sun hana su zuwa ko ina dan gudun kar a kuma ta cikon
goman kuwa ni ce ni ko dama bana shiga cikinsu, dama
abokiyar yawan nawa Haula c e ita kuwa tana can bimi
tana karatunta tunda ta tafi bata dawo hutu ba. Suna ta
faman facakar su a cikin ruwa da iface-iface sai ya faso
ta bayan wata katuwar bishiyar kuka, ya tsaya sai da ya
koma siffar Abubakr sannan ya isa bakin ruwan a
lokacin sun gama wankansu sun fito sun sanya kaya
suna shirin tafiya, sai kawai ya ya hausu da maka ihu
kake ji ta ko ina sai daya ga ya yi musu lilis sannan ya
juya ya bace, ya barsu anan kwance a galabaice,
kamannin Isma'il ya koma ya nufi cikin garin in da
mutane ke taruwa dattawan garin ya karasa da hakinsa
jiki na rawa ya ce maza ku je ku kwaso yayanku a bakin
rafi Abubakar ya yi musu rotse yanzu yanzun nan gaba
daya aka tashi da salati duk mutanc suka bazama bakin
rafin, suka sami yayansu fululu a kwankwance kamar
shanya suka kwaso yayansu suka nufo gida.
A zaune Abubakar yake ya hada kai da gwiwa
yana tunanin abin da yake faruwa, gefe kuma Dagaci ne
zaune shima zaune yana zancen zuci, daga can ya dubi
28
dan ya ce Abubakar ni dai ina gaya maka ba danni ba
don Allah ka nutsu ka daina abin da ka ke yi, kaga fa
wannan abin da ka ke yi ba karamin bakin jini zai jawo
mana ba, wai ace duk tadan nan da nake maka babu
dayan da yake shiga kunnenka? Abubakar ya ce wallahi
baba duk laitin nan da ka sani babu wanda na taba yi,
koda sau daya duk sharri ne na rasa me yasa ake min
wannan sharrin, suna cikin hirar ne sai suka fara jiyo
hayaniya mutanc an doso nan gidansu, to dama a zaune
suke sai Abubakar ya ce bari in leka in gani hayaniyar
me ake yi? Har ya tashi sai dagaci ya ce a'a zauna ni in
je kasan me yake faruwa kafin ya rufe baki tuni jama'ar
sun karaso suna ta faman zagc-zage ga sanduna da
gorori rike a hannunsu wasu ma har da sanduna suna c
ewa a fito mana da Abubakar yau mu sassara shi mun
gaji da rashin mutuucin da yake mana, ai kuwa sai
maigari (dagaci) ya fita yana lambayar abin da ya ke
faruwa, wani saurayi ya cebkagmalam in zaka fito
mana da shi ka fito mana daashi yau ba zamu bar kofar
gidan nan ba sai mun du fansa.
Dagaci ya eub kursanar dani laifin da ya yi muku
mana, in bah Nanlaifin bi rayazan ba ku shi ku hukunta
shi? Wani daga cikin su ya ce da Allah kar ku saurare
shi kulsa wagidah wota in yaso ya fito ko ya kone dama shl'yake yaña jihsu ya ma rasa ta cewa sai can wani
dattijo ya fito ya bayyana masa laifin da Abubakar ya yi
dagaci ya ce tun yaushe aka yi wannan aika-aikar? Suka
cc misalin hudu na yamma ya ce to wallahi tun karfe biyu muna nan tare da Abubakar ni dama nasan wannan
29
abu da akc yi da wata makarkashiya so ake yi a raba ni
da dana Kwaya daya tilo, suna jin haka suka afka masa
kai duka shi shi yake tura shi ya yi wannan barnar,
mutane suka afka wa maigari da bugu ya shige gida da
kyar wasu suka ba da shawarar a shiga a fito dashi wasu
suka ce a sa wa gidan wuta, wasu kuma suka ce a kyale
su sai in sun kuma ayi duk abin da aka yi niyya, wasu
sun yarda wasu kuwa suka kafe sai sunyi abin da suka yi
niyya, yana can bayahsu ba wanda ya lura dashi ido ya
rufe ya juye kamannin dan tsoho tukuf bakinsa daga jaja
da goro yana ta Kara sandarsa ya dinga ratso mutane har
ya kai tsakiyarsu ya ce yana da magana aka yi shiru ana
sauraransa sannan ya c e a yanzu dai ayi hakuri amuna in
har ya kara nan gaba sai a yanke hukunci take wasu sun
yarda da wannan shawara wasu. kuma suka ki
musamınan ma wadanda aka taba nasu 'ya'yan da yaga
haka sai ya ce cikin gyaggyabin tsofa aiko dan darajar
tsufannan nawa kwa yarda da abin da