bani da mai taya ni aiki ni zan
dauke ta, kai Hajiya Laraba wallahi kin rude a kan
'yar nan lallai to ki karbe ta man ki hada biyu, a'a
gara dai in kai ta gidan Hajiya Lamin, wai wacce
Hajiya Lamin ba dai ta noman sland ba kawar nan
ta ki? Ta ce ita mana, E, gaskiya na goyi da bayan a
kai ta can din.
Abubakar ne zaune a falon Alhaji Lawan shi
da Ibrahim yayin da Aihajin ya dubi Ibrahim ya yi
murmushi ya ce yaro dai yaro ne, in ban da abinka
45
ga dan uwanka Abubakar Sadik ba sai ku yi
zamanku ku biyu ba a can din, ya ce ni fa Alhaji ba
zan je ba a nan Kano nake son yin karatuna bana
son zuwa ko ina ya ce shi kenan, kai kumka fa ina
ka ke son zuwa? Ya ce ni ko ina ma zan je amma na
fi son zuwa can Zariya A.B.U ya ce to shi kenan sai
ku fara shirye-shirye domin nan ba da jimawa ba za
ku tafi, kai sai kaje B.U.K din kai kuma sai in kai
ka zariyan. Suka tashi suna farin cikin abin da
Alhajin ya ce musu, sai da suka fita falo Abubakar
yakc cewa Ibrahim me yasa ba zaka je can zariyan
ba? Ibrahim ya ce in haka ne kai me yasa ba zaka zo
mu yi B.U.K din ba? Ya ce, ai kowa da irin nasa
ra'ayin ya e to ka gani, nima nan nafi kaunar zuwa.
Haka suka ci gaba da hira kowa na bayyana
dalilansa na son zuwa in da yafi ganin ya yi masa.
Yaya Abubakar wai kazo in ji Mami, ya amsa
da to ya tashi ya fita ya same ta a falo tana zaune ya
durkusa ya gaishe ta sannan ya ce gani Mami, ta ce
to dama abin da yasa na yi kiranka shi ne kaga dai
gobe in Allah ya kaimu zaka taíi makaranta, nasan
duk fadan da zan yi maka Alhaji ya riga ya yi maka
shi saboda haka abin da zan Kara maka shi ne ka
tabbatar abin da kaje nema ka tsaya ka yi shi, kuma
ka samo shi, kaga in ka tafi sai dai hutu zaka dinga
zuwa gida, sai dai in ko Alhaji yaga yana da lokaci
ya kai maka ziyara, don haka ka lura ga tawa
46
Isarabar ta mika masa waya Nokia mai kyamara ta
ce ma dinga gaisawa ya karba cikin farin ciki ya
bude ta sabuwa ce dau, akwalinta irin ta Ibrahim ce
sak ya yi matukar godiya sannan ya tashi ya tafi
nuna wa Ibrahim.
nake ta faman Tunda muka shiga cikin gidan
zarc ido ina kallon ko ina ban gaji da kallon harabar
gidan ba, muka shiga ciki. A falo muka zauna yayin
da matar gidna tazo da saurinta cikin fara'a tana
cewa, Hajiya Laraba sannunku da zuwa, ta zauna
bayan sun gaisa ne nima na gaishe ta, ta amsa min
cikin fara'a. Sun jima suna hira sannan ta ce dama
wannan ita ce yarinyar da nace zan kawo miki 'yar
makotan kanwata Umma, ta ce to gata kuwa
kyakkyawar yarinya kai wannan yayarinya da kyau
take lallai na yarda Laraba ai da na dauka zugugun
ki ne kawai ta ce ato ga shi dai idanki ya gani,
yanzu dai gata nan zata zauna ta dinga taimaka miki
da wasu ayyukan, ke dama nasan halinki ba ki da
wani aibu ita ce dai ban san halinta ba, amma da
gani yarinyar zata yi hakuri da hankali Hajiya Lami
ta ce ai da ganinta nutsattsiya ce, sai dai yanayi na
kauye sai da Hajiya Laraba ta yini da yamma ta tafi gida, ita kuma matar gidan ta nuna min dakin da zan
kai kayana sannan ta ce in je in yi wanka ta sa 'yarta
47
Nusaiba ta bani kaya har kala uku domin ta fuskanci
bani da wasu wadatattun kaya masu kyau sai
tsumma kawai. Ta nuna min duk irin aikin da take
son in yi mata cikin ladabi da biyayya na amsa
mata.
Kwanci tashi na zama tamkar 'yar gida a
gidansu Nusaiba, itama Nusaiban ta dinga koya min
wasu abubuwan da ban sani ba, misali girki irin
nasu da sauran soyc-soye su hada lemo da sauransu
abinci kuwa sai na bar shi, duk kalar da suka ci da
ni za aci kafin mayc wannan na goge na yi fes da ni
baske na ya fito sosai har na kusa sajewa da 'yar
gidan ko sakan zata je sai ta ce in tsefe kaina mu yi
nan da nan sai gashina ya muke har ba ya domin
nafi Nusaiba gashi sosai ita kanta tana sha'awar
gashina.
Ina kitchen ina wanke kwanoni da safe na
gama na shiga goge-goge har na kare na share
kitchen din na goge sai na ji yo kira daga falo da
sauri na na fita domin Mami ce take kira kamar
yadda na ji Nusaiba na kiranta na je na durkusa na
ce gani Mami, ta cc kin gama ne? Na ce na gama ta
cc da Allah ki dorawa Ibrahim ruwan zafi ki juye
masa a flask zai zo ya dauka yanzu na ce to na tafi
ina tunanin wanene kuma Ibrahim ni dai tunda nazo
gidan nan naji ana yawan ambata Ibrahim amma
ban san shi ba, yau dai na ganshi na yi sauri na
48
tafasa masa ruwan ina durawa a flask sai na ji an ce
yi a hankali kar ki kana cikin tattausar murys na
dago kaina da sauri sai muka yi ido biyu da shi ya а
tsaye a bakin kitchen din na ya zubo min ido sai ne
yi saurin yin kasa da idona ina tunanin ko dawa ya
dade a tsaye ne ban sani ba oho, na gama durawa na
durkusa na mika masa yasa hannu ya karfa yna
murmushi ya ce thank you yana yi min wanı tr.n
kallo da na kasa fahimta har ya tafi kaina a duke
yake, na ce a raina kai ina jin dai wannan yayan
Nusaiba ne domin naga suna kama sosai amma fa
kyakkyawa ne sosai.
Ina cikin wannan tunanin sai na jiyo kara din
Nusaiba tana kiran uwar Mami, Mami kizo Yaya
Abubakar ya yo waya, maza kizo ta fito da sauri
nima kuma falon naje na zauna ina ta gyare-gyare
na naji suna gaisawa da wanda ya yi wayar Mom na
tambayarsa karatunsa da kuma hira da suka dan
taba da tambayar mutanen gida sai na ji tana cewa
ai lbrahim yana nan ta ce, ta ce ai nasan kuna
gaisawa amma baya gaya min kasan Ibrahim da
zurfin ciki, wato har can yaje ko? Oho to ya ji ga
Nusaiba ku gaisa, suka gaisa da Nusaiba suka dan
taba hira sannan ta bai wa Mami wayar suka yi
sallama.
49
** **
Yau mai wa su Mami sharar harabar gidansu
baya nan duk ganyayyakin bishiyoyin dogon yaro
ya watsu a harabar gidan, ga shi kusan duk irin
kananan duwatsun nan ne farare sai Mami ta yi
kirana ta ce da Allah in share iya in da zna iya nace
to, na fara shara sai da na yi yafi rabi sai ga Ibrahim
a motar sa maigadı ya bude masa ya shigo ya ganni
ina ta faman shara ya nufo in da nake ya tsaya ya ce,
ina yaran da suke wannan aikin? Na ce basa nan, ya
ce to waye ya ce ki yi ai bai ai bai kamata a bar ıniki
duk wannan sharar ba, na ce ai ni ce nasa kaina ba
sa ni aka yi ba, ya ce to ki daina ki bar musu in sun
zo sayi na ce to ban ki maganarka ba amma ka yi
hakuri, in karasa wannan in yaso gaba sayi, ya
girgiza kai alamar a'a na ce sai na gama ya ce to ba
ke kuka sa kanki ba saki aka yi amma bari in je
gidan in ji wanda ya sa ki, sai na yi saurin yar da
tsintsiyar na ce na bar shi ya yi murmushi ya ce,
haba ko ke fa, amma yadda ki ka hadu din nan ace
kina irin wannan aikin ai sai ki jigata kanki, na cе
a'a ka ji ka fa wacce haduwa ce a nan? Kai dai ka sa
mi wacce ta hadu amma ba a nan ba, sai dai in ko
ba a zaka yi min ya ce wallahi ba wasa nake miki ba
da gaske nake, na ce uhm kawai na juya na tafi na
bar shi tsaye.
Ina ta faman kai ruwa sama cikin toilet din
Mami da yake famfo an dauke ruwa sai masu tanka
50
batikka
inashk
yaلSΠ
water suka kawoi ruwa, shi ne nake jida ina kai wa
ciki ina juycwa a manyan robobi sai da na gama da
kasa su kitchen tukunna sannan na fara kai wa sama
ina cikin diba sai ga Ibrahim nan ya dawo sai nagan
shi zaunc a falo a lokacin zan shige da ruwa sai ya
kira ni na ji ya ce, ina ki ke kai ruwa? Na ce sama
ya ce daga wannan ki bar shi kar ma ki sake
daukowa, wannan din ma maida shi toilet din kasa,
sai na ce ai Mami ce ta ce in kai mata sama sai ya
mike zumbur ya nufi saman yasa mi Mami a zaune
ya cc cikin fada fada haba Mami ya ma za'a yi ku
dinga sa ta daukar ruwa?" Gaskiya daga yau ku
daina sa ta ai ba daukar ruwa aka dauko ta ta dinga
yi ba, kin san fa daukar ruwa abu ne mai cin rai, da
yake Mami mace ce mai hakurin gaske, sai ta yi
murmushi ta ce Ibrahim kenan to an daina sa ta
daga yau, tun daga wannan lokacin ta daina cewa in
kai ruwa sama sai dai tasa wadannan samarin gidan
masu yi musu wanki da guga da share-sharc.
Na gama aikina da wuri ina zaune ni kadai sai
ga Nusaiba nan tazo ta same ni, muka zauna da ma
ta kan zo gurina mu zauna muna ta hira har ma na
kan dan sami littafi a gurin, na Hausa in dinga
karantawa yana dan debe min kewa, domin in ba ku
manta ba, na yi makarantar primary baba Tasalla ta
hana ni tafiya sakandire da yanzu ina can.
51
Ta dube nr ta ce, wai Hamdiyya me yasa ba za
ki dinga bina makarantar Islamıyyar mu ba ne? Nu
ce, au a ina ku ke makarantar? Ta co Nan ne fa ba
nisa makotanmu na ce to zan tambayi Mami ta barni
nima sai ta dinga zuwa, in za ki je ta ce ai gara kı
dinga zuw a kya rage wani abin domin zaman haka
ba a rabi ba baka ba shi da dadi na yi murmushi
kawai ina mamaki a raina na fa girmi Nusaiba sosai
amma in ta yi magana sai ka ce babba a gaskiya
tana da hankali da tarbiya maganar da zata tsaro ba
zan iya tsaro ta ba. Haka muka je gurin Mami ta
gabatar mata da wannan magana ta ce to ai ba wani
abu ku dinga zuwa taren dukkanmu muka dinga
murna saboda ta barni. Tun daga wannan rana nake
zuwa makarantar Islamiyya
Hamdiyya na gaya miki ki dinga barin aikin
nan yana fa yin yawa, na daga kai na dube shi na ce
Yaya Ibrahim abin da fa aka kawo ni yi kenan,
kuma kasan fa biyana ake yi duk wata, to ya zan ce
aikin ya yi min yawa ai sai dai in ba aikin zan yi ba,
kuma ma ni ban ga abin yawa a wannan aikin ba,
domin ni bana girki daga in yi wanke-wanke sai
goge-goge sai kuma sharar kitchen shi ne fa aikına
kawai."
"Ke gaskiya fa ba za ki sake wani aiki a
gidannan ba."
52
Na cc "A'a to sai dai in so ka kc yi in tafi." Ki
je ina? Na ce in je in da na fito." Ba kya son zaman
nan din ne? Na ce to ka ce in daina aiki kuma shi ne
ya kawo ni, ka ce in bari.
"Ai aikin Ki da ne da wahala, kuma kamar
tsarinki bai kamata ace kina wani aiki ba." Yaya
Ibrahim in har kana son zamana a gidannan to ka
daina yi min zancan in daina aiki domin shi ya
kawo ni." Ya yi shiru ya zuba min ido kawai har na
gama magana ta na mike zan tafi ya kira sunana na
amsa na juya muka hada ido, ina sauraron abin da
yake son gaya min sai na ji ya yi shiru kawai sai
kallona yake yi, sai na ce Yaya, Ibrahim in na Sata
maka rai ne to ka yi hakuri ni wallahi ba da wani
abu na gaya maka ba, iya gaskiya ta na fada, sai ya
girgiza kai ya ce ko kadan ba bata min rai ki ka yi
ba ki dawo kawai ki yi zamanki mu ci gaba da hirar
mu, na yi murmushi na ce gurin Nusaiba zani mu yi
haddar Hadisin da aka bamu a makaranta jiya ya ce
to shi ke nan.
** **
A gaskiya Mami na tsani in ga yarinyar nan
tana aiki, ya kamata ace kun daina ba ta aiki sam
sam. Ta ce to ai ba aikin girki take yi min ba, daga
wanke-wanke sai shara, ai su din ne bana son in ga
tana yi, saboda me? Bata dace da aikin ba ne
53
kawai" Oho ai haka zaka ce ka tsaya kana wasu
kewaye-kewayc, kace kawai da abin da yake cikin
ranka? Shi kenan sai kaje ka sami Alhaji domin shi
ne da magana kasan dai ni ba zan je in yi masa wata
magana ba, ya ce ni fa ba wani abu nake nufi ba, ta
ce kai tafi can sakarai kawai. Ya mike yana ta
dariya ya fada dakin Alhaji Lawan dake yau yana
gari.
A zaune ya same shi shima ya zauna ya dube
shi ya aka yi ne Ibrahim? Ya ce ba komai ya
karanınka da wata matsala ne? Ya ce babu wata
matsala, ya ce ai jiya naje gurin Abubakar ya ce in
gaishe ka da zai zo ma ni na ce kar ya soma zuwa
daga fara karatun zai fara yawo a hanya? Ya ce
nima zau je ne ni da Nusaiba sai week end ya ce shi
kenan kaga kuwa zai yi farin ciki sosai. Ya dauki
Jaridar da Alhajin yake karantawa ya fara dubawa
daga can sai ya ajiye ya yi tsaki ya dubi uban Alhaji
ya kira sunansa ya ce na'am ya ce nifa Alhaji
yarinyar nan tausayinta nake ji, ya dube shi a
hargitse domin yana zaton Nusaiba yake nufi yana
matukar ji da 'ya'yansa kwaya biyu rak shi yasa ma
duk abin da suka ce suna so yake yi musu komai
kuwa wahalarsa, ba ya fasawa shima Ibrahim din
sanin hakan ne yasa shi yin wannan maganar,
Ibrahim ya ce ba ka gane ba wannan yarinyar da aka
kawo aiki nan gidan, ya ce oho ai na ga zata iya
54
domin da wayanta tausayınta nake ji, ya ce ai in an
ce ta daina an sallame ta iyaycnta za su kai ta wani
gurin za su yi ta aikin kuma kila in da za su kai tan
ba za ta sami sakewa kamar nan ba. Ya ce to me zai
hana ta yi zamanta ba sai ta yi aiki ba? Tun da Allah
ya hore maka sai ya zamo kamar ka taimaka mata
ne ya ce ai ba ka ma ba cc ba ma taimako ne tsakani
da Allah ya ce to kaga ni sai a samo wata ta ci gaba
da aikin ita kuma ta yi zamanta kasa ta a makaranta
tunda ta yi primary, sai ta ci gaba da sakandire
kawai. Ya ce shi kenan ba wani abu kaje ka turo
min Mamin naka zan yi mata bayani ya fita ya
dinga murna kamar wanda aka yi wa wani
daddadan albishir.
Haba Yaya Ibrahim ni dai ban ji dadin wannan
lamari ba wallahi, a gaskiya ni ba ka burge ni ba,
haka kawai ka tilasta musu abin da ba su yi niyya
ba? Ni ban ga abin tilastawa a nan ba, wallahi da
ace lokacin bayi ne in nace da Alhaji ya 'yanta ba
wa wak baiwa zai iya domin yana san mu baya son
abin da zai 6ata mana rai ko kadan shi yasa duk
abin da ki ka ga na ce ayi ma'ana ana yi mana na ce
shi ke nan na gode Allah ya saka da alheri, ya ce na
manta ma ashe ban gaya miki ba jiya Alhaji ya сe
zai sayo miki fom din makarantar gaba da primary
za ki dinga zuwa na dafa kirji Allah da gaske ka ke
yi? Ya ce sai in kin soma zuwa za ki fi gaskata ni,
55
na ce kai amma na rasa kalmar godiya da zan yi
maka, ya yi murmushi ba shi ne nake so in fito dake
ba amma ke sai faman ga cewa ki ke yi, na ce ai
abinne ni da na aiki sai in wuce makadi da rawa
kuma? Ya ce don kin shige makadi da rawa ai ba ji.
Tuni har na fara zuwa makaranta abina, kullum
Yaya Ibrahim ne yake kai ni kuma ya dauko ni, ita
kuma Nusaiba direban su ne yake kaita ya dauko ta
yau da gobe har na fara saba wa da karatun komai
yana tafiya min daidai ba wata matsala kuma а
gurin Alhaji kamaı 'yarsa na dawo haka ma Hajiya
Lami wato Mami itama ta dauke ni kamar 'yarta
Nusaiba dinki ma iri daya ake yi mana ba wani
bambanci tuni yaya Ibrahim ya sa aka kai ni dakin
Nusaiba na bar wannan dakin shirgin mai sauro da
sauran Kwari.
Muna zaune da Nusaiba muna ta hirar
makaranta na ce ni ko Nusaiba in an bamu hutu zan
je garin mu ta ce, Allah na ce Allah kuwa, kinga da
za'a bar ki sai mu tafi tare, ta ce ina ai Alhaji ya ce
gidan Yayansa can kauye zani in yi hutuna a can, na
ce au dama kuma kuna da kauye? Ta сe E, mana
garin su Alhaji fa in da wan Alhaji yake babansu
Abubakar." Na ce yauwa wai ni waye Abubar din
nan ne, da na ji kina yawan ambatarsa ko kuma ku
yi masu waya ko shi yayo maku a ina yake da zama
ne? Ta ce ai dan wan Alhaji ne a kauye yake shi ne
56
Alhaji ya taho da shi domin ya yi karatu, kin an
kauyc ba a damu da karatun ba kamar nan. Na ce
haka ne kam, ta kc tunanin nawa Abubakar fin ya
fado min nace a raina Allah Sarka Abubakjar ko
yaya yakc ciki oho, nan take wani irin dafin SO
harba a zuciyata na ji wani irin shauki so kawa
nake u ganshi na mi je wuf na ce da Nusaiba ina
zuwa ta ce io na mike na je na zare hotansa ba tar
da ta lura da abin da nake yi ba domin ina tashi ta
fara Game a wayarta, sai da na gan shi sannan na yi
ajiyar zuciya hawaye ya nemi tona min asiri, sai na
yi waje kawia bayan na lallaba na mayar da hoton
ma'adanarsa. Na jima ina kuka sannan na sbare
hawaycna, na wanke fuskata don kar a gane ne, na
yi kuka na dawo ciki zuciyata da radadin kaunar
Abubakar ga Gacin ran raba mu da aka yi.
** **
Kwanci tashi muna zuwa makarantar mu
kullum har muka yi jarabawą na sami kyakkyawan
sakamako a wannan jarabawa, ta canja aji na zo ta
daya a ajinmu, murna gurina da su Ibrahim Alhaji
da Mami da Nusaiba ba a magana har kyaututtuka
na samu shima Alhaji sai da ya dan hada min fati
bayan mun zo hutu. Muna gama fatin da kwana
daya Alhaji ya ce ibrahim ya maida ni gida in
hutuna a can in yaso aka koma sai ya dawo dani.
57
Haka kuwa aka yi, da Ibrahim ya dauke ni gami da
kayan tsarabar tawa sai gidan Rab, wato Aunty Rabi
ita kuma ta ce ya barni a nan ma ita zata kaini gida
da kanta, sai da ya nace a kan sai ya kaimu ta ce ai
ba dan rakiya sai dai ita in mijin ta ya dawo ta
tambaye shi sai ta raka ni washe gari haka ya
hakura akan tilas.
Da gari ya waye, ita ta shirya ta raka ni har
kauyenmu, murna a gurin Inna kamar me, da taga
na goge na kara kyau sosai. Kwanan Aunty Rabi
daya ta koma a kan cewa in an gama hutun na taho
tun da yenzu na gane hanya. Sai da na kwana uku
sannan na tafi can zan zari guri baba Tasalla itama
ta yi farin cikin ganina ta ce lallai birnin ya karbe
ki, kin dawo-sai ka ce wata 'yar Turawa ai wannan
tafiyar tak: ita tafi maki alkairi, shima yaron nan
dan gidan Dagaci na ji ana rade-radin wai kanan
uban wannan mai kudin yazo ya tafi da shí gurinsa
ya sa shi a makaranta. Na tabe baki kawai don kar
na yi wata magana ta balbale ni da masifar tata da ta
saba, nan ta kasa min tsaraba duk na kai wa mutane
sai faman mamakin kyan da na yi suke yi wasu har
da taba min gashi wasu ko zuwa suke ganina
takanas da zance ya bazu wai nazo ga yadda na
sauya, Baba ta ce in je gidan kawata Haule itama
tazo hutu, na kwashi tsarabar da naje musu da ita
zan kai wa Haule gidan su hanyar gidan Dagaci nc,
58
don haka sai na sayi goro mai kyau farare a boye
don kar Baba ta gani na tafi dashi in na gan shi a
wajc in ba shi. Na kuwa yi sa'a na same shi bisa
kujera shi kađai ba kowa, na durkusa na gaishe shi
ya amsa da fara'arsa amma bai gane ni ba, na mika
masa goron ya sa hannu ya karba ya ce ban shaida
ki ba daga ina ki ke? Na ce Baba nice fa Hamdiyya
yar gidan Tasalla, my maya, ce oho sai yanzu na
ganc kina ina ne shiru na raby da jin duriyarkı Na
cc ai ina cikin gavi ina karatu ya ee koda naji, shıma
Abubakar din ai yana сaр, па се Allah Sarki to ni
zan tafi ya ce to na fa gode, yaushe za ki koma ne?
Na c e sai na gama butu ya ce a nan za ki ga? Na
ce a'a gidan su Inna nake da zama ya et m za ki
koma gidan su Ipnau ki zo in bakinta wa tsarabar ki
tafeda ita, na ce to na gode muka yi sallama
wuccne
גת
gidan su Haulé la tasolda
muk. Ina isa gidan su Haule ta taso da guda ta tare ni
mukat rungume juna muna ma, Haule la ce
wallabi kin yi bala'in hadawa Hamdiyya, a aua ki kẹ
yanzu? Na ce uhm, ke da bari Haule bayan
afiyarkin ni naga abu, muje mu gaisa da Baba,
tukunna mu zauna kisha labn daab H на
subasu I Bayn mun gama gaisawa da Babar Haul cet
basu tsarabar murdan (aba bira sai Hauie ta
muka kebc a wan deki ta kawo min madararshant
mai dumi dake su. fylani ne kuma tasan inasoplati
ys 39
oted n
הה
madarar shanu a lokacin muna tarc. Bayan na zauna
na sha na nutsu na shiga bata labarin komai tun
daga farko har karshe ta yi matukar mamaki ta ce to
yanzu a ina ki ke a can Kanon na gaya mata in da
nake a zaune, ta ce in bata a rubuce insha Allahu sai
ta nemi in da nake na ce ba zan iya yi mata
kwatancen gidan da nake ba, zama ba amma zan yi
mata kwatancan gidan Aunty Rabi sai tasa a rakata
tunda ni ba zan gane gidan ba bare in yi mata
kwatance. Ta ce shi ke nan in Allah yaso sai ta je
nan muka ci gaba da hira har wani lokaci, sannan
muka yi sallama ta rako ni gami da tambaya ta me
nake so ta kawo min in zan koma? Na ce ina son
nono mai kyau, ta ce to sai lokacin da zan koma
Kano zata kawo min can gidansu Inna domin kar ya
lalace.
Satina daya a gidan Baba sannan na koma
gidan su Inna, hade da tsarabata niki-niki da Haule
muka tafi ta raka ni har gidan su Inna, sannan ta yi
ni ta kamo gida dake bani sa sosai daga kauyanmu
zuwa kauycn su Inna, sai da na gama hutuna cif
sannan na koma gidan su Aunty Rabi can Kano.
Inna ce ta raka ni da kayan tsaraba ta niki-niki.
Daga ci kwan zabi ya bani mai yawa domin shi
mutum ne mai saukin kai bare kuma yaga an rabu
babu wata hayaniya a yanzu hankalinsa a kwance.
60
Kwanana biyu a gidan Aunty Rabi sai ga Yaya
Ibrahim yazo daukata, Aunty ta ce ai yazo ya fi sau
goma sai in ce ba ki dawo ba, na ce lallai Ibrahim
akwai himma. Ta yi dariya akwai himma kdai
akwai wata a boye? Na ce haba Aunty ba komai
wallahi yana dai tausayina nc kawai, ta ce ai in ta yi
wari ma ji, au ke an bar dan mutane a wajc a tsaye
je ki ce masa ya shigo daga ciki, a tsaye jikin
motarsa yana ganina sai na ji ya saki wata ajiyar
zuciya mai karfi ya karaso cikin murmushi ya ce
wai Hamdiyya me yasa ki ka je ki ka yi zamanki ne
a can? Na ce kasan an jima ba a ga juna ba shi yasa
ina can yaran gida da 'yan uwa da abokan ariziki da
aminiyata, ya yi dariya suna nan lafiya ko? Na ce
duk lafiya ya ce to shiga ki fito mu tafi. Na ce au
yau ba za a shiga a gaida Aunty ba? Ya yi
murmushi bari dai in shiga da sauri nake yi wallahi
daga zariya nakc don na mayar da Sadik kin san
shima yazo hutu satinsa biyu na ce au yazo Allah
bai yi zan ga Sadik din nan naka ba, ya ce wallahi
kuwa, sai dai wani hutun na ce to a ina zan gan shi
bayan duk hutu kauyenmu zan dinga tafiya, ya ce
kai ina ai daga wannan kin daina zuwa, na yi dariya
haba sai ka ce wata matar aure? To ko aure ma nake
yi ai dole ne in