An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
SHARRININNIF
NA
AMNA ABDULLAHI SHARAБА
(MRS AHMED YUSUF)
SHARRIN JINNI
1
NA
AMINA ABDULLAHI
Hakkin Mallaka (m) Amina Abdullahi
Copy right (c) Amina Abdullahi
GODIYA
Godiyata ga Allah Madaukakin Sarki da ya nufe ni
da rubutu wannan littafi mai suna SHARRIN JINNI.
Tsira da aminci su kara tabbata ga Shugaban halitta
kuma cikamakin Annabawa (S.A.W), Alayensa da
Sahabbansa.
GODIYA TA MUSAMMAN GARE KU
Nafisa Abubakar Shaba
Binta Bello
Suwaiba Yahaya
Nafisa Dahirı
Maryam Abdurrazaka (Gandu)
Binta Bature
Surayya Auwalu
Balaraban Jamilu
Da sauran irinku, wadanda ban sami damar shigar
da sunayenku ba.
JINJINA
Gare ka Jamilu Ali Indabawa, Allah ya kara
zumunci amin.
KUMA BAN MANTA DA KU BА
Ummi Ali Indabawa Da Sadiyatu Ali Indabawa
2
ITA TARI DA KU 'YAN'UWANA
Umar K.B Sharada
Kabiru Bullet (Bulman) Sharada
Abdullahi Muhammad Yakubu Bauchi
Yaro Abbas Sharada
Aminu Samarat Sharada
Babanji
Salisu Sanin karfi
TUNASARWA
Wannan littafi Sharrin Jinni, ban rubuta shi domin
wani ko wata ba, na rubuta shi ne domin nishadi,
Kagaggen labari ne don haka a guji zargi.
Amina Abdullahi Sharada
GABATARWA
Sharrin Jinni, labari ne da wani gawurtaccen Aljani ya kulla soyayya don cimma burnsa, ya dinga
haddasa musufu kala-kala wanda ya kasance duk wanda
ya kulla alaka da cu sai ta shafe shi. Bayan kuma yana
son yarinyar sosai, hakan ne yasa duk wanda ya yi gigin
taba ta, da sunan duka ko yasa ta a wani bacin rai sai ya
sami horo mai tsanani a gurin Aljanin, Karshe ya shiga jikinta.
Kaddai in cika ku da surutu ku biyo ni ku sha labari.
Amina Abdullahi Sharada
3
SHARRIN JINNI 1
Y
au kauycn garin Zanzari, an kwana ana tafka
ruwan sama kamar da bakin kwarya, ya kasa
ta juku ni ima ta sauka gari ya yi dadi, sai gajimare ke ta
wuccwa da yayyafi lif-lif, yayin da duk wani magidanci
ko saurayi tsoho da yaro da mata masu karamin karfin
ke ta faman fafutukar zuwa gona shuka, tuni masu hali
daga cikinsu sun sa an nome musu gonakinsu wasu da
motar noma wasu da garmar shanu wasu kuwa karti
suka sa majiya karfi ya danganta da ra'ayin mutum.
To a daidai wannan lokacin da kowa ke fafutukar
yin aikin da ke gabansa, ni kuma ina can nasa Babana a
gaba ina ta faman sharar hawaye don tausaya wa ganin
ccwa kowa na fafutukar kauda aikin da ke gabansa, shi
ko na kwance rai'ga Allah, bai ma san wanda yake
gunsa ba.
Ni kadai ce 'yarsa ni ce ta fari ni ce auta, duk kuwa
da cewa mahaifin nawa tsoho ne tukuf mai kimanin
shekara tamanin da biyar a duniya. Itama dai Innan zata
yi hamsin domin daga ninta za kasan ta kwana biyu duk
da cewa wahala ma ta isa ta kara musu tsufan
kasancewar ba wasu mawadata ba ne, abin da za a ci ma
ba dan da noma da yake ta ba wa ba da kansa yake
zaune. Kar ku yi mamakin jin cewa ni ce ta tarin nice
kuma auta wannan ya samo asali daga rashin haihuwar
da suka samu tun farko, sai da girma ya kama sai da
gima ya kama sannan Allah ya azurta su da ni.
4
"Hamdiyya ki yi shiru ki daina kukannan haka kar
kanki ya yi ciwo." Na dubi Inna dake gefe daya ta yi
tagumi, na ce "Inna gani nayi garin nan kowa ya tafi
gona domin yin shuka, ba wanda ke zauke sai mu, ga
Baba ba lafiya ga abincin ma na waccen shekarar ya
kusa karewa, gashi bana ba zamu noma ba. Inna ya
zamu yi.?" Itama ta sharc hawaye ta ce "Haka Allah
yaso damu, sai hakuri. Ai cuta ba mutuwa ba ce, sai
kwana ya kare." Na mike gami da sharc hawayc na ce,
"Inna zanje in zaga gonar Baba in gani." Ta ce "In kinje
me zaki yi, tunda ga mai aikin a kwance ba lafiya?
Nasan dai ke ba iyawa zaki yi ba, amma jeki sai kin
dawo, kya iyo mana abin wuta ma daga can, ki taho
mana da gwandar daji ki dubo nunanniya kar ki debo
danya." Na cc "To." Na kama hanya na tafi.
Tun daga hanya nake ta faman murza ido danganin
abin da ke gonar ko idona ne yake gizo wato yake zagi.
Haka dai na karasa gonar zuciyata cike da mamakin
abin da na gani. Gonar na gaki an yi mata (haro) wato
huda kenan, kuma har an shuke iya ganina ma'aikata ast
gonar su suna ta aiki abinsu, na hango wani dan makotanmu shima a tasu gonar yana cire ciyawa, na isa
gare shi a banya ye na yi masa sallama, domin Baba
yana cewa dani "duk in da naje in dinga sallama, sannan
in gaishe su kafin in fadi aiken da aka yi mini." Ya amsa
sallamar, sannan muka gaisa na ce "Sule don Allah ko ka ga wanda ya yi aiki a gonar Babana.?"
Ya ce "Wallahi kamar yadda ki ka gani, nima haka
na gani. Sai dai ki tambayi Malam Shehu gashi can a
5
tasa gonar ko ya sani. Ni da ina cewa ma ko ku ne ku
kasa aka yi muku.?" Na ce "A'a, wallahi ba mu ba ne,
Baba dake ta kansa yaushe zai sa ayi masa noma da
shuka, shi da bai san ma wa ke gunsa ba." Na ce, bari
inje in tambayi shi Malam Shehun ko ya sani."
Ina zuwa na tambaye shi, shima ya cc bai sani ba.
Abin ya yi min dam! Na yi masa sallama na tafi gida ina
cike da mamakin wannan abu.
Ni kadai akan hanyata ta komawa gida, ina tafe ina
ta tunani, kwatsam! Naja na tsaya cikin tsananin tsoro da
fargabar ganin wanda ke tsaye a gindin wata bishiyar
dorawa gashi na bar mutane, ni kuma ban karaso cikin
gari ba, cak! Na ja na tsaya domin in na ce zan gudu
ma, ba iya tsere masa zan yi ba, sai faman tsuma nake yi
saboda da in ganshi gara in ga kumurcin maciji baki,
Abubakar kenan saurayin da na tsana in gani saboda
tsananin tsana da izayar da yake nuna min.
A hankali ya tako yazo in da na ke yayin da ya
tsare ni da ido, yana kallona, sama da kasa sbaoda
tsananin firgita ban san hawaye na zuba a idona ba, sai
da naga yana diga a hannuna, sannan na lura da cewa
kuka nake yi, ya ce cikin dacin rai.
"Ke me yasa ba kya gaida mutane in kin gansu?"
Ban za ci a iya nan abin zai karc ba, don haka sai
na ji wani dadi ya lullube ni, na ce "Ina gaishe ka
wallahi mantawa kawai dai ka ke yi....." "Shceet! Rufan
baki." Na yi saurin sunkuyawa "Ina kwana.?" Ban sani
ba, ni kam na shiga uku na ce a raia, take na kakalo
kalmar "Abubakar ka yi hakuri in wani laifi na ke yi
6
maka, wallahi in ka gaya min ba zan sake yi maka ba."
Sai naga kawai ya lumshe ido ya bude ya girgiza kai.
"Sai kin gaya min dalilin da yasa ki ke jin
tsorona.?" N ayi shiru na rasa abin da zan ce masa, daga
can sai na hango wata kawata mai suna Haule, tana ta
sauri da ke a kanta ita kadai muna nan gurin har ta
karaso ta same mu, ta ce "Hamdiyya lafiya na ganki,
kinyi jigum.?"
Na ce "Wai saboda bana gaishe shi, shi ne yake
tuhumata."
Ta cc "Abubakar ka yi hakuri, kasan Hamdiyya ba
mai yawan magana ba ce, ina ga shi yasa bata gaishe ka.
Ke Hamdiyya ki dinga gaishe shi, duk sanda ki ka
ganshi. Zo mu tafi." Ta kamo hannuna, muka wuce shi
ka fuskarsa ban kalla ba, gudun ban san me zan ga ni a
fuskar tasa ba.
Muna cikin tafiya ne, na k ce mata "Haule wallahi
na rasa abin da nake wa Abubakar, kullum ya ganni sai
ya tare ni daga yau ya cc nai masa kaza, sai gobe ya ce
abu kaza na yi m2a. Yau ma kina ji wai gaishe shi ne
bana yi."
Ta ce "Rabuwa zaki yi da shi, ki dinga gaishe shi
tunda hakan dai yake so, ko kya tsira da mutuncinki
tunda dai shi namiji ne ke kuwa mace ce, bai kamata ace
ma kuna wata gaba a tsakaninku ba."
Na ce, "To sau nawa ina gaishe shi baya amsa min?"
Та се "Кe ana baki kina kin karba, ko ba zai amsa
ba, sai ki gaishe shi. Menene yafi ki yi shiru ya ci
7
mutuncinki daga gaisuwar sai mc." A haka muka yi la hirarmu har muka isa gida abinmu.
Iona na zaunc na ta yi wa Baba ſirfita, na shiga na yi sallama ta amsa min, sannan ta fara yi min fada.
"Yanzu Hamdiyya me yasa ki kaje ki ka y
zamanki, kinsan dai na ce ki komo da wuri ko? Kuma
ina abin wutar da gwandar dajin?" Sai sannan na tuna da
abin wuta gashi bana son in sanar da ita halin da muke
ciki ni da Abubakar. Sai kawia na labarta mata a yadda
na sami gonarmu. Ta yi mamaki matuka, amma sai
kawai ta ce "In bar maganar domin tana zata wani ne ya
yi shuka in ya girbe sai ayi kashi mu raba, (wato ya
bamu kaso daya bisa uku na amfanin gonar).
Yau kwana biyar da zuwana gona, ban kuma
komawa ba saboda kullum sai an tabka ruwan sama.
Yau ne aka samu ruwan ya yi sauki, gari ya yi sarari, saj
na shirya domin in je jeji amma wannan karon ba gona
zani ba, abin wuta zan yowa Inna, sannan in samo mana
ya'yan itatuwa.
Ni kadai na ke ta sauri domin na biya wa Haule,
ko zata je. Babarta ta ce, "ta tafi tuni." Shi yasa ma nake
sauri ko zan ganta, sai mu taho tare da ita. Ina cikin
lafiyata, kwatsam! Sai ga tawagar 'yammatan kauyanmu
sunyo abin wuta, gabana ya yi mummunan faduwa,
domin nasan abin dake tsakanina da su, ba ko wani abu
ne ya jawo rashin jituwarmu ba, illah halayyarmu da
tasha banbam, Su basa karatu koda Islamiyyar nan ma,
ni ko ina zuwa makarantar boko da Islamiyya, har ma na
gama firamare zaman jiran fitowar jarabawa ta nake yi
haka Haule Kawata makarantarmu daya, tare muka gama
su kuwa in ban da tallace-tallace da kokaye kokayen
samari babu abin da suka iya, ni ko bana talla sai dai
zama a gida ko in je abin wuta ko in zauna taya Inna
aiki. To wannan kamewar kan da nakc da ita, shi ya
janyo min tsangwama a cikinsu, musamman irin kyaun
da Allah ya bani, duk cikinsu babu kyakkyawa kamata.
Ga fari da hanci ga uwa uba gashi har baya, abin da ya
sa ma ba na yarda su ja ni muyi fada da su saboda ja min
gashi suke yi da karti in yi ta ihu, saboda tsananin zafi.
Ina ganinsu, sai na kara azama domin kar su tarar
da ni, nasan ba zamu rabu kalau ba. Da saurinsu suka
Karaso in da nake, suka tare ni daya daga cikinsu ta ce
"Ke Hamdiyya wato shi ne don rashin mutunci kina jin
muna kira ki ka share mu.?"
Na ce "Lah! Wallahi ban ji ba." Tas! Na ji sąukar
mari, fayar ta ce "Yau sai kin gaya min abin da ki ka je ki ka ce wa Bala mai kifi rannan." Na ce "Me naje na ce masa?" Dayar ta ce "Kin fi kowa sani munafuka, ba
zuwa ki ka yi kika soki Mairo a gabansa ba, kin san dai
sani sarai saurayinta ne, shi ne ki ka ce wai wani kin gansu suna kokawa da Musa mai manja ko.?"
Kai da jin zancen kasan an yi ne don aci min mutunci kawai, sai kawai na ji ta sake kwada min mari, daga nan sai suka hau ni da duka. Ba zan iya ramawa ba, domin an ce 'Sarkin yawa ya fi sarkin karfi.' Suna cikin dukana, sai ga tawagar su Abubakar nan sun danno, suma suna zuwa suka raba mu, na koma gefe ina ta harar hawaye, a kaina a sunkuye duk suka watse suka
bur ni ina ta faman kuka, motsi na ji a bayana, a firgice
na juya don ganın mai motsin, Abubakar ne tsaye Kyam
ya zubo min ido, na yi baya cikin dimauta take na zube
ina gaishe shi, sai kawai na ji ya ce "Me ki ka yi
nrusu.?" Cikin shesshekar kuka na ce "Babu abın da na
yi musu, kawai don suna son su dake ni ne." י
Ya yi shiru, sai can ya ce "Yanzu ina zaki je ?"
Na ce, "Inna zairsamo wa abin wuta."
"Zo ki wuce ki tafi."
Cikin sauri na fice na ta rawar jiki. ina yi ina
waiwayen sa, da na waiwaya mun hada ido sai in yi
saurin dauke kaina, don kar ya ga ina kallonsa, shi kuwa
ya zubo min ido har sai da na yi nisa, sannan ya lafi.
Nayo itace mai yawan gaske, da kyar nake dauka
saboda nauyi. Tun daga nesa na fara hango mutane a
kofar gidanmu, sun taru ga tabarmi an shimfida, ga
bokiti da ruwa ana ta alwala. Gaba daya jikina ya yi
sanyi da kyar nake tura gwiwa duk da ban san me yake
faruwa ba. Na karaso.
Ina shiga cikin gidan, sai naji ana cewa "Uwani ba
kuka za ki yi masa ba, addu'a za ki yi masa domin irin
wannan jiyar an yi kankarar zumubi ansha jiya." Abin
da narji wasu tsofaffin mata ke fada kenan, yayin da na
shiga dan da nan naga ne abin da ya faru, wato dai Baba
ya mutu kenan.
Nan da nan na yi jifa da iccen, na fara kuka ina
kiran "Wayyo Allah Babana ka tafi ka barni, Allah ya
jikan ka da rahamarsa." 10
Inna ce zaune, can gefe kuma kanwarta ce Baba
Mairo, da kanwar Baba Hajiya Tasalla, suke tattaunawa
akan batun gadonmu.
Hajiya Tasalla ce mai cewa " Yo ke Uwani tunda
dai gida za ko koma, ai ba kya tafi mana da 'ya ba, tunda
ta isa aure kawai in yaso ta dinga zuwa tana ganinki ko
ke kizo." Ta cс "A'a, ba wani abu ai kuma 'yarku сс,
gata nan kun fini iko da ita. To yanzu batun gona sai
muje mu sami Maigari (Dagaci), mu gaya masa halin da
gona take ciki, in yaso sai ya karbar mana a nemi mai
saye a sayar don kar wani ya sake kwacewa. Inna ta ce
"To yanzu me muke yi, mu tafi kawai muje mu safe shi,
abin da za ayi ai maganinsa yi." Suka mike sai gidan
Maigari game da zancen gona.
Bayan sun kwashi gaisuwa, suka yi masa bayani
daya bayan daya, duk yana saurarousu. Hajiya Tasalla ta
cc "Kaga bawan Allahn nan babu abin da ya mallaka sai
gonar nan, ya kamata ace an binciko wanda ya aikata."
Maigari ya syara zama, ya dube su daya bayan
daya ya ce "Y anzu shi Malam Musan kafin ya mutu bai
sanar da ku abin da ake ciki ba ne?"
Suka dube shi cikin rashin fahimta, suka ce "Ba
mu ganc ba.?" Ya cc "Ai wannan gona da ku ke zancc,
bata Malam Musa ba ce, gonar Babana ce har wannan
gidan da ku ke ciki shi ya mallaka masa tun sa'adda
mahaifinsa yazo garinnan. Ke Tasalla don ke macece shi
yasa ina ga bai miki bayani ba, amma ai yasan komai
saboda haka gidan ma barinsa zaku yi, kunsan lamari ne
na da can duk shedun da aka gabatar ada sun mutu
saboda haka sai ku dau hakuri, shima Malam Musa
ya sani ai ya sanar da ku tun katin va mutu, don guрп
rigima, domin babu shaidu."
Tasalla ta ce "Yanzu shi kenan gidan tashi zamuy kenan mu bar maka ko ?"
Ya ce "Ayo, ai tashi ya zama dole dama baku
ba zan tura ayi kiranku in sanar daku." ta yi murmushin
Karfin hali "Ai shi kenan 'Yalla6ai, zamu bar muku gidan, ba komai."
Hajiya Tasalla ce ke taya Inna hada kayanta, zata
tafi garinsu, ga 'yan'uwanta duk sun zo suna taya su
duka ka kwashe kayanta aka barmin nawa Hajiya
Tasalla ta bada min nawa kayan kaf ta daure ta ce in je
in raka su Inna in yaso na dawo da yake daga garinsu
zuwa garinsu Inna ba shi da nisa da Kafa ma mutum in
ba mai son jiki ba ne zai iya zuwa, dama garinmu daya
da Hajiya Tasalla yar Babana duk unguwa daya muke
gidan da take aure babu nisa da gidanmu tana auran
wani mutum mai suna Baba Sani yana sana'ar kasa
kayan miya a nan maciyar unguwar. Kwanana biyu a
gidan su Inna ta tarkato ni na dawo gidan Baba ba abin
da nake kiranta da shi kenan.
**
Hajiya Tasalla su su uku ne a gidan mijinta, matan
wa da kani wato dai mazansu 'yan uwan juna ne, amma
ba sa zaman lafiya kuma babbar masifaffiyar ita ce
Hajiya Tasalla, duk tsoranta suke ji duk ranar da taje
12
unguwa ranar kamar Sallah a gidan amma in ta dawo ta
dinga dube-duben abin da zata yi bala'i a kai, duk da
bata taßa haihuwa ba ita ke juya 'ya'yan gidan, tana da
tsafta sosai haka nema yasa komai nata a killace yakc,
bata bari yaro yaje ya taba mata kaya kofin da take bai
wa yara ruwa ma daban yake, in kuwa ta yi shara to ko
ke wace ba ki isa ki shiga dakin ba sai ta baki ruwa kin
wanke kafa ga shi ta rangada kunshi ya yi jawur da ke
tta fara ce tas gata kyakkyawar mace doguwa mutane
suna yawan gaya min muna kama da ita, shi yasa ma
take sona, tun kafin in dawo hannunta duk Sallah sai taje
birni ta sayo min kayan Sallah sannan ta bayar a yi min
Sinkuna masu kyau, ta kawo min gami da kayan
kwalliya tun kafin Baba ya fara cuta take cewa ya bar
mata ni ya ce shi ba zai iya rabuwa da ni ba, sai dai in in
zauna a tsakaninsu bani nan bani can shi ne ta yarda а
kan hakan, a yanzu kam muna zamanmu lafiya da Baba
babu abin da na nema na rasa a wajenta, don haka
hankalina kwance.
A zaune nake gaban Baba muna hira, ta ce
Hamdiyya maganar gaskiya ba zan zauna in zuba miki
ido kina gabana gododo dake babu sana'ar komai ba, ke
fa marainiya ce yanzu in auranki ya tashi mai za a kai
miki in ba mu nema ba gashi Yaya Musa ba rai, ita
kuma Uwani ba wata sana'ar kirki ba, haka kurum in ruwanka bai isa alwala ba sia kayi taimama ka taşhi yaushe don girman kai kace 'yarka ba za ta yi tallaba, sai
karatu, in auran ya tashi karatun za a jera a dakin? Ni dai jin Baba nake kawai tana ta faman masifa, sai da ta
23
gama na ce, to yanzu Baba me zamu dinga yi na
savarwa? Та сс, rogo za ki dinga sarowa rafi kuna
dafawa ki dinga kaiwa tasha, an ce akwai riba sosai
kinga sai ki dinga tara kudinki a banki." Na ce to kuma
in jarabawata ta fito fa? Ta ta fito mana, kin san dai
babu maganar karatu domin ba za ki yi ba wanda ki kaа
yi a baya ma ya wadatar.
Tafe nake da farantin tallan rogo akaina, ya dahu
ya yi fari sal ga gari sai kamshi yake bulawa, dama Baba
ta haddace haduwar rogo na dure shi a wata katuwar
leda na dora bisa tray ga wasu 'yan kananan faranta
masu kyau tun itip na auran Baba na debo su guda biyar
ya wanke su na dora bisa ledar rogon gami da wata 'yar
wuka, bayan na yo wanka nayi kwalliya na sanyo
kayana na saka hijabi na fito Baba cewa take Allah ya
bada sa'a 'yar gidan Baba, don Allah a tsaya a yi ciniki
kar a dawo da kwantai." Na ce To ina tafe ina cewa a
gaskiya Baba ta fiye san kudin tsiya ni wallahi har
kunyar tallan nan nake ji, abin da ban saba ba, yanzu in
wadannan marasa mutuncin suka ganni shi kenan na
kade, dagangan ma zasu takale ni domin su 6arar min
da kayan sana'ar bare kuma uwa uba Abubakar, Allah
dai yasa har in gama tallana ba zan ganshi ba.
"A hayye jama'a ku zo ku yi kallon 'yar makaranta
da tallan rogo, la yau me zamu gani?" Dayar wato
Jimmala da ta fara magana ta ce karya ce, ta kare wai
bori ya kashe boka, sauran suka ce ai dama karyar da
14
farar duk na banza ne, wannan sabon salon ba zai yiwu
ba dole a dawo hanya. Duk wadannan maganganun da
suka yi ban ko kalle su ba, na nemi guri na zauna nima
don da nan kuwa mutane suka rufe ni da sayen rogo mai
cewa in bashi na ashirin nayi mai na goma nayi, kafin
maye wannan rogo ya kare, sai kudina a hannu, kun san
mutane suna son su ga abu mai kyau ga kuma tsafta ga
shi dai suma rogon suke sayarwa amma sai da nawa ya
Kare sannan nasu ya kare, ni kuwa ma tuni na taho gida.
Baba saboda murna har rawa ta yi, ta ce, to gobe sai kije
ki kuma kaiwa can.
Tofa, yau da gobe sai da ya kasance in bani na
kawo rogo ba, ba a saycn na kowacce a gurin nan sai ya
zamana har da masu daukar min su kai min gurin
sayarwa, domin ba zan iya dauka ba. Manyan, kwanika
irin na mai saida gurasa da nama sai an cika, min shi har
uku asa almajirai su kai min, idan na zauna bana hutawa
sai ya kare, saboda masu saye Takar kudi kuwa wata
katuwar lalita ce aka dinka min nake daurawa, a ciki sai
na cikatą da kudi tun ban saba ba har na zo na saba, na
dake bana jin kunya kuma na yi suna sosai kowa sai
Hamdiyya a mutunce da girmama juna buna ciye ciyc a
titi bana kokąwa da samari bana kallon fada bana yawan
surutai ba kuma na fushi da mutane, baka ne ya jawo
min matukar farin jini a gurin mafiya yawan saonn da
ke gurin, kowa yana so ya gabatar da kansa gare ni ana
shayin irin amsar da zan bayar. Al'amarin da ya kara
rura wutar gaba tsakanina da 'yammatan kauyanınu har
15
suka fara shawarwarin daukar mataki a kaina, ba tare da
na sani ba.
A tafe nake na tura ayi min gaba da kayan domin
dama sai an kai an diddire sannan nake zuwa, sai nayi
kicibis da Abubakar sai na dan yi dam naja na tsaya, ya
karaso dab danı ya tsaya na kalle shi a tsorace na ratse
zan wuce sai ya ce "Yau ba gaisuwar?" Na ce au na
manta, na dawo na gaishe shi ya amsa sannan ya dube ni
ya ce wai me yasa ki ke jin tsoro na ne? Na sunkuyar da
kai na ce ba komai ya yi murmushi sia kin fada min za
ki bar nan." Na ce, gani na yi in ka ganni ba ka yi min
dariya sai ka daure fuska, shi ne nake jin tsoro kar ka
dake ni." Sai ya yi dariya ya ce dama shi kenan abin da
ya jawo tsoron? Na cc E, ya ce to shi kenan daga yau na
daina daure miki fuska, shi kenan kema ki daina jin
tsorona na ce to na daina, ya ce to yi murmushi in gani,
sia na sa hannu na biyu na rufe