sake furta komai ba.
Ya na master room dinsa da ke bangaren Ummu,
Ummu ta shigo babu sallama ta tsaya ta na kada
kafada to munafiki yau dubu ta cika ka maida
Shema'u sai hankalinka ya kwanta, babu yadda ban yi
da kai ba akan ka korata gidansu amma ka ki wai har
miliyan daya ka ba da sadaki dole ne nima ka bani kai
wallahi in kana son zaman lafiya har gyaran daki sai
kayi min, kai ni dama nasan sai ka mai da ita sau
nawa muna kwance za ka ringa kiran sunanta, kai kun
yi karya daga kai har irin munafukan da suke: goya
maka baya, tunda ta ke da Nazir ba ta taba ganin irin
fushin da ta gani a yau a fuskarsa ba ya na dago wa ya
wanke mata fuska sannan ya ce ian so ki kula ki kuma
san kalaman da ya kamata kiyi amfani da su wajen
fada min magana ki kiyayen ba ki sanni ba ne rainin
har ya shige kaina da kannena ya kuma gangarat kan
iyaycna a hir dinki yanzu da da ba daya ba ne iria so
ki gane haka kin ji ko, in za ki zauna ki zauna in kuma
ba za ki zauna ba babu wanda ya rike kafafunki kuma
ke ba makauniya ba ce kinsan hanya, kuma ina so in
sanar da ke Shema'u matata ce wacce nake so kuma
62
ita ce uwar 'ya'yana, in kina son zama da ni ki bita ku
zauna lafiya, ya juya ya fice ya barta ta na cizon yatsa
ta fadi lalle dole in sake shiri Shema'u wannan karon
da shirinta ta dawo.
Ya na zaune falon Shema'u wanda ake ta gyara
shi saboda dama ta riga ta yi pakin din kayanta,
Surayya ce ta ke aikin Surayya ya kirata kirawo min
Anty ki ta ce yau tun dazu ta tafi can makarantar da ta
ke teaching saboda suna da meeting, cikin ransa ya ji
ya yi masa zafi wato ba za ta fada masa ba illah
Shema ta sake hali kuma fa in bai was aba ya na da
sauran aiki ya samo kiran Number dinta amma layin a
kashe yake, ko da ya ke batun yanzu ya ke kiran layin
ba ya ji haka, saboda haka tuni ya soma tunanin ko ta
sake layi ne da wannan tunanin ya yiwa surayya
magana bani number dinta ai ba ta fita da handset din
ba, ina ga garin sauri ta manta shi maza dauko min ta
je ta kawo masa nan ya shiga yi mata bincike, fuskar
wayar ma hoton Najib ne da ya shiga inbox din ta
kuwa duk wasikun Najib ne, haushi ya kama shi gaba
daya ya yi delete din su har numba dinsa ya goge ya
tashi ya shige master room dinsa nan ma wani abin
haushi ne dan ya yi kura sosai da alama ba ma ta
amfani da shi wato yarinyar nan tama goge shi ababin
rayuwarta.
Alhaji Jibrin da Alhaji Yusif na zaune suna
zantawa kan abin da ya faru na mayar da auren da su
ka yi Alhaji Yusif ya ce ni kam ban san yadda zan
63
nuna farin cikina ba kaga fa gwara da ta zauna da
yaranmu zasu ringa haka a yau da mutuwar aure ta
ragu dan kasan fa da haushi kaga wani yazo zance har
gidanka wai kuma wajen matarka ba ma dole takaici
ya sa ka ka maida ita ba, Alhaji Jibrin ya ce haka ne
amma fa kasan akwai wadanda in sun saki mace an
ringa ci mata mutunci ka ji ya na cika bakin kafin yaje
ya dawo ko tsinkenta ba shi da bukatar gani ai kasan
wargima guri yake tararwa kasan akwai macen da zata
so ta zauna har ta gama idda to amma cin mutuncin da
tijarar da mijin zai yi mata ne ya kansa ta tafi gidan
iyayenta, wani laifin a mace ne sai kaga dama can
bata samu tarbiya ba, Allah-Allah ta ke ayi sakin ta yi
shewa ta yi dariya ta hada inata ina ta ta fice dama a
gidansu ta na da daki tana zuwa share shi kawai zata
yi ta zauna, Alhaji Yusif ya ce zaman ne yanzu wasu
iyayen idanunsu ya rufe saboda kudi sai kaga uwa
tasan 'yarta tana fasikanci amma saboda dan wani
kaso da zata bata na abin da ta samo sai kaga ta daure
mata gindi kai dai wannan zamani Allah ya ba mu
wucewa lafiya.
Hajiyan su Nazir kuwa tun dare kasa rintsawa
tayi saboda tsabar mamaki wai Nazir ya iya sakin
Shema, kai wannan yarinya 'yar albarka ce ko ni da
nake uwarta aka sake ni gidanmu zan tafi amma sai
gashi yarinya karuna ta iya daurewa ta zauna ba tare
da ta senar da kowa ba kuma tabbas da ta sanar din a
iokacin ko ya na so ko ba ya so zai maida ita amma
64
sai ga shi ta yi shiru har sai shi da kansa ya nemi ta
koma kai dan da ya sami tarbiya daban ya ke.
Mahaifiyar Shema itama ta jinjina abin, ta kuma
sarawa 'yarta tare da yi mata addu'a da ita da ziri'arta
ta kuma jinjinawa maigidanta da ya fi karfin iyalinsa
da kuma shimfida musu doka da yake wanda babu
mai tsallake abin da ya fada duk wannan nasara da
'yarta ta samu tatattara ne bisa iko mijin nata, iyaye
mu nutsu musan irin shimfidar da zamu ringa yi wa
'ya'yanmu domin su kasance masu tarbiya a tsakanin
al'umma.
Anas da Kabir kusan in ce sun fi kowa murnar
wannan kome dan har wata walima su ka shirya
wacce isu isu ne familes su ka hadu dan taya
ma'auratan murna walima ce wacce hatta iyayensu tun
daga kan maza har mata sun halatta, amma wani abin
takaici Ummu fita ta yi ba tare da izinin mijin ta ba ta
tafi gidansu saboda ba ta da bukatar zama wajan
walimar an yi wa'azi an yi ciye ciye da tande tande
har da lashe-lashe, da shaye-shaye, sannan kowa ya
koma in da ya fito.
Ango Nazir ya na zaune a falo saboda duk in da
ya yi da Shema ta saurare shi ta ki daga karshe da ya
ga wanki hula ya na nema ya kai shi dare sai ya shirya
musu honey moon da farko ki ta yi wai ita ba zata ba
da kyar ta amince ba dan ta so ba, saboda ya ce in ba
ta shirya ba zai fadawa mahaifinta, lokacin da ya
sanar da Umınu kwalarsa ta ci ita sam sai dai itama ya
65
tafi da ita ko kuma ya sake ta dan ita ba za ta zauna ta
zama bora ba wani kallo ya yi mata ta saki rigar tasa
ta na kuka ya ce kiyi lis din abin da kike so dan ina jin
in mun tafi zamu yi wata daya ko biyu dan daga nan
har dubai zamu zarce saboda harkar kasuwancina.
Surayya ita aka bar wa yara sai kanwar Alhajinsu da
mijinta ya rasu ta dawo gidansu Hajiya ta ce ta dawo
ta zauna da yaran kafin su dawo.
Kasar South Afrika muka nufa garin Capetown
mun sauka a wani kayataccen hotel rayuwar da muka
gudanar a wannan Kasar abu ne wanda ba zai fadu ba
dan na tabbatar wa da zuciyata lallai ina tsananin son
Nazir kamar yadda ya nuna cewa a iya lokacin da ba
ma tare ya yi missing dina, munje kasashe sun kai
goma sha hudu dan ban taba tsammanin zanje su a
rayuwata ba, kwannanmu uku a London muka tafi
kaiwa wani abokinsa ziyara mazaunin can ne amma
ba dan kasar ba ne ya na zaune a wata unguwa mai
suna Bourne street mun isa gidan sai dai matarsa
muka samu ta sanar mana ya tafi asibiti gurin dan
uwansa a gaskiya gidan ya dauki hankalinsa sosai,
wanda ita matar nayi min hira amma hankalina ba
agun ta ya ke ba. Nazir ya zungure ni to sarkin
sha'awa shi ma wannan gidan ya baki sha'awa ne, ko
shi za'a gina miki an fasa wancen ta yi murmushi
Abbu Nur gidan nan ya yi min sosai, nan dai muka yi
sallama da ita akan gobe zamu dawo in ya zo ta fada
masa gobe karfe hudu ya jira mu.
66
Washe gari taxi ta ajiye mu karfe hudu daidai
mun yi sa'a mun samu El-Bashari a gida sun yi
matukar murnar haduwarsu domin sun dade ba su
hadu ba nan fa suka yi ta hira yau zamu wuce karfe
bakwai dan daga nan ma Dubai zamu daga nan sai
gida a nan ya ke tambayar sa waye ba shi lafiya ya се
kanina ne dan wan baba na ne ya masa mi sauki dan
muna sa ran sallama gobe, Allah ya kara sauki sai
kazo muje mu duba shi daga nan mu tafi dan fam mun
gama shiri Nazir ba ka da kirki memakon ka sauka a
gidana kayi hakuri wani lokacin in mun dawo sai mu
sauka a gidanka nan mu ka shirya har matarsa dan su
daga sama muka fito dan zuwa asibiti sai da ya je ya
yi mana siyayyar yara sannan muka nufi asibiti, mun
shiga wajan mara lafiyar kasancewar lokacin ziyara ne
ya na sanye da kayan majinyata ya rame matuka kallo
da ya nayi masa na dauke idona ba kowa ba ne fa ce
Najiburrahaman da sauri ya sake juyowa dan ya
gaskatga abin da idanunsa suka gani, duk daga ni da
ya Nazir ya yi masa amma ba zai taba manta
kamannin mai jan kunnunnan ba, su ka gaisa tare da
tambayar jikinsa ya ce da sauki El-Bashir ya gabatar
da shi wajen kaninsa ya kuma gabatar da kanin nasa
gurin abokin nasa, Nazir ya ce Shema ba ki gaishe shi
ba ta ce sannu ya jiki? Da kyar ya iya amsa da sauki
Nazir mutum ne mai zafin kishi ko cikakken minti
goma ba su yi ba su ka bar Hospital din, karfe bakwai
jirginsu ya shilla Dubai. 67
Mun zauna a hotel din da yasa ba sauka kullum
da yamma yakan fita da ni yawo wani lokacin ma har
wajan harkokinsa ya kan fita dani kudin da Abbu Nur
ya kashe min Allah ya yi yawa dashi, har furniture ya
sake min na isa wanda ni Shema'u ban taba ganin
irinsa ba hatta kujeru da kirin set da dukkani nau in
kayan alatun da za su yi kyau da furniture din tun
kafin muta ho kaya suka yi gaba.
Ana i gobe zamu dawo muka yo wayar gobe a
tare ma washe gari karfe biyar da rabi na yamma ta yi
mana ne cikin garin Yola mun sami yara da surayya
da Goggo sun tare mu amma shiru naga ta
musamman, amma ko leke. Bayan ya yi mun yi
wanka mun ci abinci zaga yayi 6angarenta can ya
dawo ya ce wa Goggo ina Umma ta fita ta ce ai tun
safe suka fita ita da Hajiyan ta ni nayi zaton ta dawo
bai kara cewa komai ba ya juya, ya ce min ya tafi gida
na ce ya gaishe su kafin nima in zo gaida su, bai dawo
ba sai bayan goma. Muka yi sallama da shi sai gobe
saboda yau dakin Ummu zai sauka, har lokacin ba ta
dawo ba in da ya tafi ya bar dakinsa haka ya same shi
da kansa ya zage ya gyara sannan ya yi wanka ya
kwanta, sai bayan sha daya na dare Ummu ta shigo
kafadarta rataye da sury dan ta tunda taga wayanta a
sude tasha jinin jikinta a falo ta shimfide shi kamshin
turaren Nazir ya bugu hancinta master room ta nufa da
murnarta taia fadın darling saukar yaushe, shiru ya yi
mata ta kai hannu zata taba shi a tunaninta bacci ya ke
68
ya yi saurin murginawa, darling meye haka ta fada
cikin muryar shagwaa, cikin dakakkiyar murya ya ce
ki koma in da ki ka fito ki duba agogo sha daya da
kwata ki ka shigo ke ga mara kamun kai ko, na mijin
arziki ba zai kai sha daya ba bai doshi iyalinsa ba
cikin kukan kissa ta ce haba darling ya zaka fadi haka
ya kamata ka tsaya ka ji hujjar kai wa ta iyanzu ko
lafiya ko ba lafiya ba, Ummu ki fita idona in rufe
kinsan tun sanda na dawo tun yaushe nake kiran
lambarki, kin kashe wayarki kuma kin san cewa yau
zan dawo tunda na sanar da ke na tabbata cewa tunda
na tafi kema yawonki kike, to ki sani ba zan dauki
raini ba, nan dai su ka yi ta taska tsiyarsu har asuba
suna sa-in-sa in da ya kafa mata dokar rashin fita ya
soki in taga ta fita to asibiti ne.
Rayuwa gidan Nazir a yanzu komai ya sauya
dan halin kowa ya fito an gane kowa yanzu duk wata
fawa da Ummu take da ita babu ta dawo abin ban
tausayi, duk dangin miji sun dawo daga rakiyar ta duk
wani abu da tasa mu gurin miji ta rabar wa 'yan tsibbu
dan darajarta ta daukaka amma a banza a yanzu ko
cikin gidan-su Nazir sai abin da Shema'u ta ce domin
mijin ta ne mai naira dan a yanzu ya fi mahaifinsa
naira, sannan ita Shema'u ba mai bakin cikin b a duk
abin da ya cancanta ba wai sai ka tambaya ba ita ta ke
ba da shawarar yin komai dangi kowa santa ya ke,
Ummu kuwa ta zama kamar wata mujiya gurin dangi
da mutane dan da kanta ta ce ita dai ta gaji da wannan
69
aure Nazir ya sawwake mata ya ce saki ki ke so to
kije ki fadawa wadanda suka hada auren sai su
warware.
A yau mahaifiyar Ummu ta kawo mata ziyara ne
ta kawo mana labarin wani sabon boka ta ce kawai ta
fidda kudi su kashe Shema'u da 'ya'yanta su huce
takaici, Ummu ta ce dakata Hajiya ni yanzu ba ni da
kudi ba ni da kuma hanyar samunsu abin da mu ka yi
da bai kama Shema'u ko 'ya'yanta ba ko mun samu
nasara sai abu ya lalace ni yanzu na gane komai ya
same ka ka tsakake zuciyarka shi ya fi Shema ni na
tabbatar ba na gabanta babu irin kunci da bata shiga
ba same ni a yau Allah ya fitar da ita komai ya same
ta ta dangana shi da Allah ai Hajiya gani ga wane ya
ishi wane tsoron Allah, ko abubuwan da su ka ringa
samun mu ya ishemu tunani amma ina wallahi Hajiya
da ina da ikon sake uwa ni kam da na sake ki dan sam
irin tafarkin da ki ka dora ni kin cutar dani ina amfani
bin bokaye da 'yanbori na dawo kamar mujiya cikin
dangina, ni wallahi kin cuce ni a yanzu ni na gane zan
nemi gafarar abokiyar zama na da na mijina zan kuma
koma ga Allah, Allah ya shiryi duk mai hali irin nawa
da naki Hajiya dan ganin abin da ya same ni ya ishi
duk mai irin halina ishara, jikin Hajiyarta ya yi sanyi
ce to Ummu nima na yi nadama kiyafe ni, ni a
tunanina ina son ki zama tauraruwa gurin mijinki shi ta
ya sa na shigo hanyar bata amma nima yanzu na gane
70
zan je mu sasanta da 'yar uwata gaba daya Nazir ya
tausaya musu don duk abin da suke fadi a kunnensa.
Oder furniture din Shema'u ya iso dan dama irin
wannan oder sai ta yi watanni uku ta ke isowa to kaya
dai sun iso lafiya har an shirya su tsaf abin gwanin
sha'awa nata na da ta mayar da su dakin mahaifiyarta
gaba daya 'ya'yanta har dan gidan Ummu Abba su ya
bude musu account duk wata akwai kudin da ya ke zuba
musu ga hannun jari da ya siya musu abin nasu gwanin
sha'awa.
Hankalin Ummu ya kara tashi ganin cikin da
Shema'u ke dauke da shi domin ita shiru babu wani
labari gashi duk in da taso su shirya da 'yan uwan
mijinta kowa ya watsar da ita bata da wani mutunci a
idanunsu wani lokaci takan yi kuka ne da kanta domin
ita ta jawa kanta da ta zauna tsakani da Allah tun farko
da hakan ba ta faru ba ga shi da wanda ya isa da wanda
bai isa ba kowa wani gani gani yake mata.
Mahaifin Shema'u da sirikinta suna aifahari da ita
domin ita ta kawo wa families dinsu sabon sauyi dan
yanzu duk wata ya da ta kwana ta tashi cikin gidan su
Nazir ba ta isa ta yi yaji ba ko ta kaso aurenta ta dawo
domin Alhaji Yusif ya bi ra'ayin amininsa wajen sarrafa
'yayansa duk wacce ta yi yaji to kaninta ke maida ita
saboda haka yaji ya kare cikin zuri'arsu.
Shema'u na zaune cikin lambun gidan ta ita da
kanwarta da take riko Surayya, hankalinta na kan
rubutun da ta ke Surayya ta ce Anty wai yau rubutun me
kike littafi zan rubuta kan labarin rayuwa dan mun yi
magana da Zahra'u Baba har ta ce zata duba min idan ya
71
yi sai ta hada ni da Lis Computer daga nan sai ta hada ni
da babbar harka Al-amin Bookshop babban dila, ni
kuwa Anty sai naga da ya wa duk wani littafi ta Al-amin
ya ke fita, tun da ki ka ga haka to mutum ne mai aminci
kinga ya ci sunansa Aminu, gaba daya su ka sa dariya,
sai Antina babbar marubuciya in ji Surayya, ke dai ta
yani da addu'a nima zan fasa cikin marubutan zamani
don in ba za tawa basirar.
Kasancewar bikin Surayya ya zo kwata-kwata
Shema ba ta samun zama, don a gaskiya Nazir ya yi
mata komai ita kuwa ta hada ta mata kicin abin sai
wanda ya gani gaba daya duniya ta yi wa Shema dadi
yadda mijinta ke ji da ita haka dangin miji gashi uwa
uba dole Ummu ta yi saranda dan yanda ta ke mata
biyayya har abin mamaki ya ke ba ta dama hausa sun cе
komai ya yi farko zai yi karfe.
TAMAТ
Allahumma sali ala Muhammad, wa ala ali
Muhammad, kama sallaita ala Ibrahim wa ala ali
Ibrahim innaka hamidul majid.
Mu hadu a:
--1. GWANAYE 2. 'YA'YAN HAJIYA
3. ZUBAR HAWAYE 4. DANGANTАКА
Suna nan fitowa ku taya ni da addu'ar Allah ya
sauke ni lafiya.
Mai Launarku: ZAHRA'U BABA YAKASAI
Maman Shurem)
72
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
UWAR MIJI KO KSHIYA? 1 & 2
BAN SAN HAKA KAKE BA! 1 & 2
HADIYYA 1, 2 & З
TARKON SO 1, 2,3 & 4
FUREN KAN JUJI 1, 2 & 3
ZUMUNCI KO ANINCI 1, 2 & 3
HATTARA MATA 1,2&3
HUDUBAR MAZA 1, 2 & З
HUZAYYA 1 & 2
GANI GA WANE...
AWARWARO
PRINTED BY:
AL-AMIN B/PRINTING & PUBLISHING COMPANY No.; 156 S/TITIN MANDAWARI KANO CITY. 08028411703
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels