Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels GaniGa Wanes NA ZAHRA U BABA YA (Mrs. Dan Ringim) GANI GA WANG.. 2 NA ZAHRA'U BABA YAKASAI (Maman Shureem) 08020863615 1 Copy right © ZAHRAʼU B. YAKASAI Mallaka (m) ZAHRA'U B. YAKASAI SHEKARAR BUGU: 2008 2 GANI GA WANE...2 Y adda wutar ke ci bababa, ita ta sanarwa da jama'ar da ke unguwar cewa wannan gida ana neman taimako, duk da cewar unguwa ce ta ma su ido da kwalli ba wasu jama'a ba ne da yawa a wajan hakan bai hana taruwar Jama'a ba, nan da nan sun soma zuba ruwa domin ganin sun kashe wutar, amma wani abin mamaki yadda wutar ta ke sake ci gaba da ci tamkar fetur su ke zubawa, tuni makocinsu ya yiwa jami'an kashe gobara waya don su zo su taimaka. Ummu da ke harabar gidan ta zare kamar wata mahaukaciya fadi ta ke "mijina, mijina ya na ciki ku taimake ni ku fito dashi." Sai a lokacin aka san da mutum a ciki, yadda wutar ke ci ya sa mutane kasa shiga don duk wanda ya ga yadda wutar ke ci zai tabbatar ba za ta bar komai a ciki ba, saboda haka kowa gani ya ke duk wani abu da ya ke mai raine to ba zai fito a raye ba tuni har 'yan gidan su Nazir sun zo Anas tare da Yayan Shema'u Kabir da ya dawo daga karatu su su ka fara zuwa, Kabir ya ce "Ina Shema'u, ina Nur?" Yayin da Anas ke kiran su, nan dan'uwansa ai sai a lokacin Ummu ta ce itama tana ciki wani kukan kura ya yi tare da nufar cikin gidan nan da nan aka rike su domin daga shi har Anas sun fita hayyacinsu, sai a lokacin 'yan (fire service) su ka iso isowarsu ke da wuya su ka soma abin da ya kawo su bayan shigarsu cikin gidan sun yi nasarar dauko Shema'u da Nur da hayaki ya sumar da su abin zai ba 3 ku mamaki in na ce muku 'yan kwana-kwana sun kasa kashe wutar nan an dai samu an dauko Nazir shima tuni har an yi asibiti dasu, gobarar tun bayan sallar isha ta faru amma har karfe dayan dare wutar tana ci wutar ba ta daina ci ba sai da ta cinye dukiyar gidan tsaf an yi nasara dai ba ta ci rai ba shi kuwa maigida da matarsa tuni sun ya da zango a gadon asibiti. Duk da cewar wutar ba ta kona su ba, amma jikinsu ya yi wani irin dabbara-dabbara gaba daya ba sa cikin hayyacinsu dan Shema'u daga ta farko ża ka ji ta ihun wuta wuta sai da ta kwana uku aka samu ta dawo cikin hayyacinta tun da aka kaisu asibiti Ummu ba ta taba leka in da Shema'u da Nur su ke ba bare asa ran za ta yi musu sannu, ita kuwa Ummu babu abin da ya same ta sun ci gaba da karbar magani na sha da na shafawa satun su biyu sannan aka sallame su dan yanzu fatar jikinsu ta soma koma wa normal. Bayan an sallame su gidan su Nazir su ka nu fa wato family House wayansu na da dai yanzu anan Anas da matarsa su ke kuma duk dakunan gidan da mutane saboda yanzu samarin gidan yawancin su anan su ke zaune da iyalinsu, dan sun-yi aure daki daya ne babu kowa a ciki bedroom ne da toilet, Nazir da matansa biyu ga daki daya ne ya za'ayi wannan zaman ko da ya ke ya na da gidajen da ake haya a ciki amma ai ba aje a tashi mutum katsan ba, Anas ne ya ce ya kamata a cika gidan haya tunda gaskiya waje ya yi 4 kadan, amma sai Hajiya ta ce ba zai yiwu ba, a bari Alhaji ya dawo tun da baya nan gobarar ta faru. Shema'u da Umma suna zaune a dakin da ya ke nasu katuwar katifa ce a shimfide a kasa, Nazir ya shigo hannunsa rike da carbi alama ce daga masallaci ya ke, ya samu gefen katifa ya zauna, Nur ta tafi cinyarsa ta zauna ta na son yin wasa da carbin hannunsa ya sakar ma ta ya na yi mata wasa, Shema'u ce ta katse shirun ta ce Yayana, wata muguwar harara ta saki tare da jin tsaki ba ta kalle ta ba bare ta tanka ma ta, ta ci gaba da maganarta in da ta ke cewa, yayana yanzu dai kana ganin zama cikin gidan nan haka zai yiwu daki daya, kasan dai zaman Musulunci mu ke yaya zamu ringa kasancewa in lokacin bacci ya yi? Nazir ya yi gyaran murya ya ce, ni da nufina in dare ya yi sai in tafi cikin kannena samari, in ringa kwana kunga sai ku sake, Ummu ta zumburi baki ta ce ba zai yiwu ba, Shema'u ta ce gaskiya kai ma za ka takura me zai ha na kowacce ta tafi gidan su in ya so duk lokacin da Allah ya nufe ka da gyara gidan sai mu dawo, hauka ma kenan in ji Ummu, ke tafiya ta kama amma ni zama daran, Nazir ne ya ce, ku meye haka kun manta cewa yanzu ba a gidanmu mu ke ba, ba zan dauki kananan maganganu ba, ta zumburi baki ta ce to kai darling ya ma haka zata yiwu ya ce ai shawara ce kowa ya kawo tasa tunda ta bayar ke ma ki ba da taki ta ce darling ni ina ganin abin da ya kamata shi ne wacce ta ke da miji sai ta kwana tare da shi wacсе 5 kuma ba kwanan ta ba ne sai taje dakin 'yanmatan gidan ta kwana amma mu tafi gida ko kai ka kwana wannan gurin ai babu tsari, ta na jin Nazir ya amince da hukuncin Ummu tasan an yi niyyar wulakantata, shiru ta yi ba ta ce komai ba, sai ji ta yi ya ce gobe ku shirya muje can gida don kowa ya ga irin 6ar nan da wuta ta yi mana, kowacce ta aika gidansu gobe so mu hadu aje ko wacce ta ce to, da ya ke tun da gobarar ta samu hankali bai kwanta ba tunda dai masu gida na asibiti. Washe gari da safe misalin karfe goma 'yan uwan kowacce sun zo aka cika mota aka tafi, sun shiga harabar gidan mota daya ce ta kone motar Ummu ce sun yi mamakin konewar motar saboda san da wuta ta tashi ba ta yi harabar motoci ba, aka shiga cikin gida falo ya yi baki kirin, rufin gida ya cin ye shi kansa gidan wani waje duk ya rufta saboda a zabar cin wuta, wani abin mamaki da ya faru shi ne 'yan uwan Shema'u su na bude dakinta da ya ke rufe ko alamar hayaki bare ka sa ran dakin ya na cikin gidan nan aka yi gobara gaba daya salati su ka saka su na fadın ikon Allah, nan fa hankalin 'yan uwan Ummu yayo wajansu su ma dai abin ya tsima su da gudu ta yi kicin nan ma komai ya na nan kamar yadda ya ke ta yi garcji in da kayanta su ke a jibge nan ma su na nan tsaf! Wannan gobara da ta faru Shema'u ba ta yi asarar ko yanki ba babu wani abu nata da ya yi wuta, haka motocin mijinsu su ma su na nan in ka dauke wannan 6 kayan Ummu babu komai sai toka duk uwar dukiyar nan wuta ta cinye su ikon Allah kenan. Ai kuwa jikin Ummu ya dauki tsima ita da mahaifiyarta yanzu Ummu ba ta da komai nan fa su ka ce sam su ba za su yadda ba Shema'u ta aiko musu da yasin mai fuka-fukai, kan kace meye wannan waje ya yamutse da fadace-fadace saboda yadda 'yan uwan Ummu su ke 6arin bakaken maganganu don masu zafin rai irin sun soma ba wa hammata iska Shema'u kuwa ban da kukan takaicin kazafin da aka yi ma ta ba ta komai, nan da nan Hadiza kanwar Nazir ta yi waya gidansu ta fadi abin da ya ke faruwa, nan fa su Hajiya su ka taho an yi sa'a su Anas su na nan da su aka taho nan dai su ka ba da hakuri aka tattara aka taho gida. Abu kamar wasa magana ta yi tambar kc'ina Shema'u ta yiwa Ummu yasin mai fuka-fvkaj igima ta tsananta dan wannan karo Kabir YayShenz'u ya yi aniyar karbar mata 'yancinta Shema'u ta yi matukar takura cikin gidansu Nazir domin abun ya shafi 'yarta Nur babu mai daukar ta duk gidan sun yarda in ka dauke wan mijinta da matarsa sai ko Anas da matarsa, abun ya yi tsamari gurin mijinta dan ya tattara ta yawatsar shi ko kunyar iyayana baya yi dan Shema'u ta koma kwana cikin kannansa mata Ummu ce kawai me miji dan abin haushi ba ta cas bare as, Shema'u ce baiwa ita ke musu girki saboda su dama can gidan su Nazir ba sa hada girki da surukansu, wannan abu ya 7 kan damu Shema'u saboda ba ta da takamaimai gurin zama sai dai cikin dare ta kwana tana kuka, abin ya damu Aysha matar Abubakar ta fada masa da ya samu Nazir ya yi masa nasiha, sai cewa ya yi yaya ba na son katsalandan a rayuwa ta abu wanda ya shafi zumunci mu yi shi amma ni ba na son shisshigi cikin harkar iyalina, saboda haka yau shi ne karshe kar ka sake saka bakin ka cikin abin da ya samu iyalina, ai kuwa Abubakar ya yi fushi sosai har ya gargadi matarsa kan shiga harkar Shema'u, nan fa Aysha itama ta fita harkarta don ta ji haushin abin da Nazir ya yi wa mijinta. Shema'u ta sami Nazir cikin daki ya na kwance ta na shiga ya hada girar sama da ta kasa ya ce lafiya ki ka shigo ba na fada miki zaman wucin gadi kike kafin Alhaji ya dawo ba ta ce na ji nazo neman alfarma ne ya zuba mata ido ba tare da ya bata dama ba ta ce ka ga Musulunci bai bar komai cikin dubu ba, sai da ya bayyana komai kuma ni ba jahila ba ce nasan komai tun da a iya dan nawa sanin........ya daka mata tsawa ya ce, sai ki fada min jahili, ta dan yi murmushi mai kama da yake, ta ce ni a iya tarbiyar da iyayena su ka ba ni ba su ce in daga muryata fiye da taka ba, ya yi tsaki ya mike daga kwanciyar da ya ke dai dai lokacin Ummu ta fito daga toilet ta kama kugu ta rike, tarbiyar banza har wata tarbiya ce da ke tarbiyar zuwa gidan 'yan bori da bokaye, an fada miki duk yawon asiri dca kuke yi bamu sani ba a yau an wayi gari ki 8 rasa abin da za ki yi wa bakin ciki sai kayan daki to ina mai sanar miki sai na ninka mata wanda ya fi na da, saboda haka ki fice min daga daki kar ki sa ke shigo min, Ummu ta ce 'yar mutsiyata masu shegen kwadayi da bin 'yan tsibbu ba su san komai ba, Shema'u wacce hawayen ta ya ke zuba ta ce Nazir Allah ya na jin duk irin tijarar da ku ke min ni kuma nasan Allah zai sai min kuma shi ya yi alkawarin duk wanda aka zalinta in ya roke shi zai saka masa, ta daga hannu ta ce Allah na roke ka ka gaggauta bayyana gaskiya kowa ya gani ta juya har zata fita ta juyo su ka hada ido da Nazir, Nazir a yau ni Shema'u ni ce makiyarka ko za ka gane kuranka, ta juya ta tafi. Cikin hikima ta dauke kayanta daga dakin da suke ta maya 6angaren matar Anas, a nan ta zauna kamara me gyarawa shiga kicin da Aina'u ta yi shi ya ba ta damar ficewa daga gidan ta kofar baya, gidan iyayanta ta nufa, Shema'u ta kuduri aniyar rabuwa da Nazir, don ba shi ba ne dan autan maza ba. Shema'u ta shiga gidan su dauk da akwatinta a hannu ta samu mahaifiyarta tana aikin tsintar shinkafa, Yayanta Kabir ya na zaune su na hira ta yi sallama ta shiga su ka zubo ma ta ido saboda ganin ta da aklwati da rana fatsal-fatsal ga wata uwar rama da tayi, koda ya ke duk halin da ta ke ciki sun sani, amma suna jiran Alhaji su ke dan ganin an kawo karshen rigimar, ta durkusa ta gaida Nana mahaifiyarta sannan Yayanta Kabir ya ce lafiya kuwa 9 na gtanki haka, uwa wacce aka kore ina ki ka baro Nur? Sai a lokacin ta tuna ashe fa ta bar Nur, take ta ji hawaye ya sako ma ta, ta saki kuka mai ban tausayi Kabir ya daka mata tsawa ya ce ki juya ki koma gidanki mai kika taho yi, jikinta na rawa ta fadi halin da ta ke ciki shi ya ce ki taho, ta ce a'a to saboda me ki ka taho kin san Allah ban da ina jin tausayinki da sai na zane ki, ya ji ba a gidan nan ba tun kafın Baba ya dawo ki juya don nasha in ya na cewa bai hafi 'yar da zata yi yaji tazo ta zauna masa ba, in kuwa ta zauna ya tabbatar auranta ya mutu har ta gama idda a gidan miji, maza ki juya kun san mu mata nan fa Nana mahaifiyarsu ta hau shi da fada wai ai sai ya bari Babansu ya dawo, domin abun da ake mata ya yi yawa, ko da ya ke shima ya ji haushi amma dole ne ya sa shi yi ma ta haka don yasan Babansu babu wasa a al'amuransa. Ai kuwa Shema'u da tasan abin da Babanta zai mata da ba ta soma fitowa ba, bayan dawowar Babanta ya ci abinci mahaifiyarsu ta sanar da shi zuwanta, ya yi kiranta ya tambaye ta itama ta sanar da shi dattijon arziki ta in da ya shiga ba ta nan ya ke fita ba, ya ce sai ta bari Alhaji Yusif din ya dawo in yaso komai ma sai ayi shi amma yanzu ta tashi ta tafi Nana ta ce ba ta koma ita kadai ba, ai sai a rakata ya kwalla kira Dayyib, Dayyib, dan matashin saurayi ya taho wanda ba zai fis ha bakwai ba, ba shi ya ke bin ta ba da wani a tsakaninsu Dayyib ya durkusa ya ce gani 10 Baba, ya ce yayarka ce tayi yaji ina so kazo ka mai da ita gurin mijinta, ka kuma ba shi hakuri saboda fitowar da ta yi ba tare da izininsa ba. Dayyib ya ce, Baba Yaya Kabir ya na nan fa ya ce tsarina kenan duk wacce ta yi yaji kaninta ne zai mai da ita, in taji haushi gaba ba za ta kara ba, in kuma ta kaso auran randa ta samu miji sai kaninta ya yi mata waliyi Dayyib daga yau na wulakantaka kai ne waliyinta, Dayyib ya na dariya ya ce taso in maida ke ta mike ta na ta kuka wai ya zata yi da rayuwarta ne yanzu Dayyib kaninta shi zai maida ita lallai kam daga yau ba za ta kara ba sun zo soro Nana na bata baki ta daina kuka yayansu ya yi kiran Dayyib sai cewa ya yi Baba ne ya aike ni yaya ce tayi yaji zan maida ita, Kabir ya leko ya na dariya cikin ransa da zuciyarsa san ban ji dadi ba amma shi kansa tsarin Baban nasu ya yi masa dadi. Dayyib har cikin gida ya shiga ya gaida Hajiya sannan ya tambaye ta ko yaya Nazir ya na nan ta ce e ya na nan ya ce ya na san magana da shi, falon Hajiya suka zauna a nan Dayyib ya gaishe shi tare da ba shi hakuri akan tafiyar da ta yi-ba tare da izninsa ba amma yarar ya na da fasa ba dan ya yi wa Nazir jirwaye mai kamar wanka san nan kuma ya ce ga matarka ne komai kayi ma ta kai da Allah, ba dan ba ma santa mu ka dawo da ita ba a'a illa saboda abu uku, na farko darjar aure na biyu aminci iyayanmu na uku, hakkin makota in ka cutar da ita Allah ba zai 11 kyale ka ba ya mike ya yi musu sallama jikin Nazir ya yi sanyi knain kanin bayansa shi yazo ya ke tunasar da shi abubuwan da ya kamata ya duba, a ranar da da daddarc Nazir ya kira Shema'u ya bata hakurı tar da cewa ita zata kwana dashi, ai kuwa jin ccwa Ummu za ta tafi dakin yara ta kwana sai ta langwane wai ba ta da lafiya kan in kaga yadda ta ke murkususu ai ka rantse haihuwa zata yi a ranar dan akanta su ka kwana sai asuba ta warke. A yau da yamma Allah ya yi dawowar Alhaji Yusif mahaifin Nazir da ga Cairon ai tun cikin dare ya samu labarin yasin mai fuka-fukai da Shema'u ta aikawa Ummu, Dattijon arziki ya yi murmushi ya ce Allah ya kiyaye tunda dai fuka-fuukan basu tafi da ran ba Hajiya da ke ba da labari ta cika ta yi fam ta ce kai fa Alhaji ba a taba hira mai dorewa da kai ba sai ka ba wa mutum haushi ya kalle ta ya ce Hajiya haushi na baki tace wallahi na ji haushi ya ce to shi kenan ya miko hannunsa ya ce to bani abina ta ce me? Ya ce haushin mana, ai ba ta san sanda ta sa dariya ba. Jin dawowar Alhaji ke da wuya sai ga mahaifiyar Ummu ta bayyana ina ta ce san ita wallahi sai ambiyata dukiyarsu da wuta ta cinye saboda yasin aka aiko musu, Alhaji Yusif ya ce wai wa ya ce muku yasin aka yi muku ta ce ga shaida nan ita me yasa ko tsinken ta bai kone ba, sai na Ummu? Ya ce, wai ba ki san kaddara ba, ai Alhaji wannan ba kaddara ba ce, ya ce yanzu ni wannan magana na kashe ta kije kiyi 12 total ko kayan sun kai miliyan nawa zan biya, amma. daga yau kar in kara jin wannan magana, Hajiya ta ce ta yi wannan amma yarta ba za ta zauna da Shema'u ba don ta tabbatar dan suma ba a zaune suke ba da tuni wutar har Ummun sai ta ci ai kishi ba hauka ba ne, ran Alhaji ya 6aci ya ce to shi kenan ni ban gane abin da kike nufi ba, kina nufin ko wacce a bata gidanta ko kuwa ai in anyi wannan ma ba tsira aka yi ba, ina jin ki fadın abin da kike so ina son Nazir ya rabu da Shema'u ko kuma ni ya sakar min 'ya don yanzu kafarta kafar 'yarta, Alhaji ya yi murmushi ya ce to kin yanke naki hukuncin kenan a matsayinki na uwar Ummulkulthum ko to ni mahaifin Nazir ina tabbatar miki ni ba irin iyayan da za ki juya ba ne, abin da naga zan iya ce miki shi ne, in kin tafi da Ummu to wallahi kin yanke igiyar auranta kaf don kuwa ta rabu da Nazir rabuwa ta har abada saboda haka ni na gama magana ai kuwa sai Umma Hajiya ta saka kuka wai saboda bare ya ci mutuncin ta ya cе Shema'u ba bareba ce in da kika san 'yar cikina haka na dauke ta da ita da Naziru babu banbanci. Abu kamar wasa Alhaji tunda ya ke da matarsa ba su taбa sabawa ba, sai akan wannan magana sabodo ta ce ya ci mutunci 'yar uwarta akan 'yar aboki sa'ar da akayi Alhaji tsayayyen mutum ne kuma kaifi daya, abu fa ya yi tsamari saboda Hajiya tasa 'ya'yanta kaf sun daina kula Shema'u kuma ta dawo da Ummu kwana dakin ta sannan ta yanke duk wata hulda ta da 13 mijinta ita kuwa baiwar Allah Shema'u ba ku ga irin cin mutuncin da Nazir ke mata ba, amma ya zata yi haka ta zauna har su Aysha haushin ta suke ji saboda gani su ke in su ake wa abin da ake mata ba za su zauna ba, sai dai in dare ya yi ta yi ta kai kukanta ga Allah, Nazir fa ya rikice saboda ba shi da nutsuwa kawai shi ya rabu da Shema'u shi ne burinsa saboda yadda Hajiyansa ta takura shi. Duk fa wannan abu da ya ke faruwa iyayan Shema'u sun sani saboda ga gida ga gida fa amma mahaifinta bai yi magana ba saboda gani Alhaji Yusuf bai yi masa ba, Anas shi ya fada wa Alhaji cewa ya na gani raba auran Nazir da Shema'u zai fi ya ce saboda mc? Ya cc Alhaji a gaskiya hakkinta kawai ya isa ya kai Nazir wuta, nan fa ya fada masa abubuwan da ya sani har da yajin da ta yi da saka kaninta ya dawo da ita, Alhaji ya ce shi kenan Anas zan dauki matakin Karshe. Alh. Yusif ya tara Nazir da iyalansu kuma kowa da wakilinsa in da Dayyib ne ya je da Alhaji Jibrin kin zuwa ya yi haka ya ki wakilta Kabir a gaskiya wannan abu ya sosa ran Alhaji Yusif saboda shi a ganinsa ba su dauki maganar da muhimmanci ba, tunda kanin ta ne yazo amma sai ya danne, bayan an yi addu'a Alhaji Yusuf ya ce abun da ya ke faruwa nasan saboda na ce zan biya kayan da su ka kone dai magana ta mutu, amma abu ya ki yanzu ni na yanke magan zan sa wani Malami da ya ke min addu'a ya yi istihara a gano 14 dalilin tashin wutar saboda naga basu yadda da Kaddara ba abin da ya sa na taraku shi ne idan wuta Allah ne ya aiko da ita shi ke nan idan kuma ta na da wani sababi to kusani wallahi kowa musabbabinta zan daga maganar kowa ya ji saboda ya kunyata mutuncinsa ya zube mahaifin Ummu ya ce shi duk bai san wannan badakala da akc yi ba, in dai kayan daki ne zai sake mata wani a bar maganar Hajiya ta се wallahi sai an yi ai dole ne ma a gano ko waye in Allah ya yarda sai Allah ya toni asirin mutum Alhaji ya kalli 1Dayyib ay ce kai ba ka ce komai ba Dayyib ya ce ai i babu abin da zan cc sai dai in yi addu'a akan kowa ye ya yi sanadin faruwar hakan addu'a Allah ya shiryc shi ya kuma ganar dashi tun da daga yaya har ita Ummun an zama daya kaga ko wayc abu ya faru akansa ba zamu muso ba saboda haka Allah ya shiryi kowa ye a cikinsu in kuma daga Allah ta ke Allah ya maida nunkin din abin da aka rasa gaba daya su ka сс amin, Alhaji ya ce Nazir ba ka ce komai ba, Alhaji duk abin da zan ce kun riga kun fada a nan dai su ka yi addu'a kowa ya kama gabansa. Alh. Ya fadawa Malaminsa abin da ya faru ya ce shi kenan zai zo amma yau da yamma zai tafi Umara sati biyu zai yi in ya dawo zai ja da masa ya ce to. A yau tun safe Ummu ta ke nakuda babu yadda Nazir bai yi a kaita asibiti su ka ce a'a wai a gida zata haihu, ai kuwa ba ta haihu ba sai bayan magariba Allah ya ci ka mata burinta ta sami abin da ta ke 15 kwadayi wato namiji, kunga rawar

Chapter 1 of 5