kula da duk lamurana
30
ba sai dai Allah, wai duk ta ji in je in ji da dogarа
sanda da nake da kuma magana da hanci da nake,
kuma wai in Allah ya yarda na zauna a haka kenan, na
yi murmushi na ce Allah ya fiki na rike hannun 'yata
mu ka fice saboda naga take-takenta.
Sannu-sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba aje ba,
yanzu gashi na samu cikakkiyar lafiya, yawo da sanda
ya zama tarihi magana ta ta dawo ras in ba ka san nayi
wannan jiyar ba in na fada ba zaka yarda ba a yanzu
Nur ta na Primary one yanzu ina dauke da wani cikin
wanda yanzu ya sami watanni biyar Nazir yakan
kwatanta adalci domin yanzu tsakanina da Ummu
babu bambanci muna cin abincin rana ni da Nazir da
Nur mu ka ringa jin ihun Ummu daga ni har shi mu ka
mike muka yi bangaran ta me zan faru mun same ta ta
rike suraj jini ya wanke falonta lafiya muka tambaye
ta wai showglass dinta ta fado masa aka ga shi har
kunnansa daya ya fita inalillahi wa inna ilaihir raji'un
ban taba ganin tashin hankali irin wannan ba, nan da
nan aka dauke shi sai asibiti nan da nan sun yi masa
taimakon gaggawa amma fa kunne an rasa shi domin
sun ce bazai koma ba, sai dai ayi hakuri da shi, Nazir
ya ringa yi mata fada yana cewa sau nawa zan yi miki
magana akan wasan da Suraj ke yi da show dinki har
cewa na yi ki mai da ita wani dakin kin ki ke duk abin
da yaro zai yi bakya kwabarsa wai kar ya yi kuka, to
ke ai gashi nan ya saki kuka ko banza ya nakasa ita
dai babu bakin magana sai kuka ya ci gaba da cewa da
32
Nur ce taje wajan yanzu kin rufe ta da duka kice
uwarta ta turo ta tayi miki bari gashi nan yanzu ai kin
ga sakayya duk wanda ya ce tukunyar wani ba za ta
tafasa ba to tasa ko dimi ba zata yi ba, nan dai muka
barta asibiti dan an kwantar da su, kullum ni da kaina
nake zuwa kai abincin dare in kuma duba su har aka
sallamo shi, memakon ta bar wa Allah amma sia ta ke
ganin ni nayi mata asiri saboda 'yata daya ta kuma
dauki aniyar sai taga bayanta, har cikina ya shiga wata
tara bata san ina dashi ba, a lokacin ita kuma ta sake
samun na uku, Nazir baya nan ya na Dubai saboda
haka tun safe na ji alamar haihuwa ban fada wa kowa
ba na kwashi kayana sai asibiti da kaina na tuka kaina
saboda a lokacin ciwon ba wai zafi yayi ba sai da
ciwo ya kankama sosai sannan nayi waya gidanmu na
kuma sanar da gidan su Nazir ina asibiti da ya ke sun
san asibitin da muke zuwa.
Ban haihu ba sai bayan karfe biyar na haifi yan
biyu duka maza nan da nan har an yi wa Nazir waya
an sanar masa sai washe gari muka dawo gida, sai da
muka dawo gida Ummu ta ji na haihu ai kuwa ta kadu
tunda ba ta ban da ciki ba sai haihuwa kuma 'yan biyu
duka maza, asali bai ta shigo gurin taga yara, hankalin
ta bi sake tashi ba sai da taga yanda Nazir ya ringa
rawar jiki ya kashe kudi sosai ban taßa tunanin Nazir
zai iya yi min abin da ya ke min yanzu ba. Ni da kaina
nake cewa lallai mai hakuri ya na tare da Allah, an yi
suna lafiya yara sunansu Abdullah da Abdurrahaman,
33
na ci gaba da rainon yara na mijina kuma yana nuna
min so da kulawa dai dai gwargwado. Ranar da na yi arba'in na ji hargowa a farfajiyar
gidanmu na saka hijab na fita na sami Police ne guda
biyu wai nan ne gidan Nazir Yusif? Na ce E, nan ne
su ka ce suna son magana dashi na ce baya nan yana
Dubai, su ka ce to matarsa ce Ummu su ka yi hatsari
suna asibiti tun jiya, ban san ba sa nan ba na ce to ita
da wa ina yaran ya ce ki zo muje duk sai kiji bayanin
komai na ce ina zuwa na koma falo na yi wa Hajiyar
su Nazir waya ta cc ai Alhaji ya na nan ga su nan na
fito na baiwa mai yi min raino yaran gaba daya na fito
sai da muka yi jiran su Hajiya sannan muka nufi
asibiti, kai abin babu kyan gani, sun tafi wajan yawon
asirinsu a nan su ka yi hatsari a hanyar su ta dawowa daga Gombe zuwa Yola domin yaranta yayeyen shi ya
rasu mahaifiyarta kuwa ta karye a hannu ita kuwa
saboda razana cikin da take dauke da shi ya bare shi
kuwa Suraj bai ji wani ciwo ba amma babu wanda ya
ke hayyacinsa abun gwanin tausayi.
Saboda bacin rai Alhaji Yusif ya ce ba za ayi wa
Nazir waya ba-duk san da ya dawo ya ji rasuwar
dansa lokatin da 'yansanda su ka sa da kayansu da aka
samu a wajan hatsari ba komai ba ne in banda jarkokin rubutu sai garin magunguna Hajiyan Nazir
ban da kunya babu abin da ta ke ji, wai kanwarta ke
wa dan cikinta haka kai albasa ba ta yi halin ruwa ba
da ta yi da batai yaji ba, sun kwanta asibiti amma ita
34
Umma Hajiya mahaifiyar Ummu gida aka dawo da ita
dan ayi mata dorin gargajiya.
Wannan karon Nazir ya dade fiye da lokacin da
ya saba bayan ya dawo ya samu labari daga bakin
mahaifiyarsa a gaskiya fadar bacin rai ma bata baki
ne dan ransa ya baci sosai har Allah ya isa ya yiwa
Ummu dan ya ce ita ta kashe masa da zaman da
Ummu da Nazir suke zama ne mara dadi dan ya share
ta tamkar ba ita ce ta musamman dinsa ba, dan ma ni
ba irinta ba ce nasan hakkin zaman takewa shi yasa
duk sanda ta ke da girki sai na yi 'yandabaruna ya
tafice.
Ummu duk ta kade ta fige tayi lakwas domin
bahaushe ya ce in duka ya yi yawa naka kan kare to
wannan abu dai haka ya ke domin Ummu abin ya
mata yawa ga dai mutuwar da ga shi Suraj ya nakasa
cikin da ake takama da shi ya bi rariya kai wannan
abu ya yi ma ta yawa amma tasan wannan ba komai
ba ne in banda sa hannu da Shema'u ke mata a cikin
lamuranta, kan jama'ar musulmi muyi hattara wai duk
wadannan abubuwa da suke faruwa har yanzu kunne
ta bai yi laushi ba har yanzu ita dai ba ta daukar
kaddara duk abin da ya sa me ta wani ya yi mata, to
mata muyi hattara gani ga wane dai ya ishi wane
tsoron Allah.
Burin Ummu bai wuce tsohuwar ta ta warke ba
su sake sabon lale muje zuwa, ko zasu yi nasara akan
Shema'u, Shema'u a yanzu ta mike kafa gidan mijinta
35
dan tana yin rayuwar yanci ba wai ta mallaka ba, ita
da yaranta gwanin sha'awa ita kuwa Ummu ta kalla fa
kanta saboda miji ya juya mata baya dan ya nun amata
bacin ransa kan irin mugun halinta, a yau ta samu
Nazir zaune bakin ga do a master room dinsa ta shiga
ya daka mata tsawa meye haka za ki shigo min daki
babu sallama, uhm wai ni Nazir ya yiwa tsawa ta fada
cikin ranta sai ka ce da sallamar nake, lallai Shema'u
ta yi min illah ta fada a zuciyarta a fili kuma ta yi
murmushi ta ce darling mace da dakin mijinta dan
zata shiga sai ta yi sallama, ka ji jahilci, Allah dai ya
raba mu dashi, haushi ya kama shi ya ce dan dakin
mijinki ne mijin naki ba Musulmi ba ne, sorry darling
naga kamar ranka ya 6aci in dai sallama ce bari in
koma in yi ta juya samgamgam da ita amma ita ba ta
yarda ba wai nan kwarkwasa ta ke, ta yi sallama ta
shigo ya amsa a dakile ta samu gefensa ta zauna ta
soma magana darling nazo muyi magana akan abin da
ya ke neman shiga tsakaninmu domin wallahi na gaji
da abin da kake min kasan dai ita mutuwa guda daya
ce, sababinta da yawa Lukman ko muyi atsari ko kar
muyi lokacinsa ya yi ya daka mata tsawa na ji amsar
da kika kasa bani ita har yanzu ita ce ina kuka je? Wa
kika tambaya? Rubutu da magunguna na menene? Ta
zumbura baki baka nan ban tambayi kowa ba rubutu
da magani na tsarin jiki ne sanin kanka ne Shema'u ba
ta kauna ta duk hanyar da zata ga bayana so ta ke to
36
sai in zauna ta kashe ni da raina, dole ne in nemi tsari
da ita.
Ido kawai ya zuba mata har ta gama surutunta ya
ce ke dai wallahi shedaniya ce in Shema'u ba ta nemi
hirji akanki ba ai ke bakin nema ba mutanen kirki su
suke neman tsarin jiki ba wai irinku marasa imani ba,
maganar ta yi mata ciwo saboda haka ficeva ta yi,
daga dakin ta na kunkuni.
Mahaifiyar Ummu hannu ya warke saj dai ya
karkace sun koma gurin mai gyara ya ce sai dai a sake
karya shi sannan ya koma daidai da ta tuna azabar da
ta sha sai ta ce ta hakura a bar mata shi a haka
memakon wannan abu da ya fa ru ya zamar musu
hanyar shiriya ina sun sake fantsama.
Rayuwa jin dadin da Shema'u da mijin ta suke yi
ta yi kalau dan sun sabi sasan su yi haka kawai
megidan ya tashi ya bi bai kaunar ya bude ido yaga
uwar 'ya'yansa kai hali dai na da ya dawo domin ba ta
sami tafiyarsa Dubai ku dawowar sa kai zancen wai
yau girkin ta ne ya kare domin dai da ita da babu duk
daya, kai abubuwa iri-iri sukan faru amma ita
Shema'u ta kasa wani yunkuri saboda sauyin yazo
mata ne a bazata daga ita har yara babu shi babu su
kai wannan abu na Nazir na lafiya ne kuwa, kullum
dare takan hana idanunta bacci wajen gayawa Allah
matsalolinta takan yi kuka saboda tausayawa yaranta
ganin irin maraicin da ya kama su ba wai saboda
rashin uba ba dan sau da yawa suna san ganin abbansu
37
amma sai kika da sun shiga can 6angaran Ummu ta
koro su yanzu Ummu ji ta ke da kanta dan abin da
take sa Nazir yi abin ya shalle ke kan matarsa har ya
kai kan iyayensa domin sai ya yi watanni ba su ganshi
ba sai dai in su suzo gida su ritsą, shi, wannan abu ya
damu Hajiyarsa ta rasa yadda zata yi shi kuwa Alhaji
ido ya zuba masa dan yasan wai arina an saci zanin mahaukadya.
Kun san an ce zuciya bata da kashi, to hakan ce
ta faru da Shema'u ta kasa daurewa yau har falon
Ummu ta higa don tana son ganin mijinta ta yi
sallama ta siga babu kowa falon kasancewa ta riga
tasan kan wan master room ta yi ta yi sallama ta
shiga ya na une ya yi zukudin kamar mai tunani
suna hada ido Shema'u ya ci na kyamis ta kai ci ya
kama Shema'u boda yanda taga yada da kyau wato
shi ba shi da danwa kenan, ya juyo ya kalle ta lafiya
kuwa ta mayar nsa da amsa ito ina son magana da
kai jeki zan zo sia lokacin ta san cewa Ummu ta
shigo Ummu ta nummata hanya zo ki fice ni bana so
kina shigo min wajetomin nasan duk wani abu da zai
same ni ko ya samiyyana ke ce saboda haka karki
kara shigowa wajena Sema'u ta shige ba tare da tayi
mata magana ba abin y kuma ba wa Ummu haushi
don taso ta tanka mata amma ba ta kula ta ba da sauri
ta shaki wuyan Shema'utana cewa duk san da ki ka
Kara shigo min sai kinga abin da zan miki Shema'u ta
juyo ta kalli Nazir ta ceanin matarka ko sai a
lokacin ya mike tsaye ya ce Ummu meye haka sake ta
ta sake ta tana cewa daga yau sai yau in dai ta karа
shigo min zan karya kafarta ne, Shema'u ta yi
murmushi ta ce kamar yadda hannu tsohuwa ya karye
ta kuwa zabura ta kawo mata damka ita kuma ta zille
ta yi wajanta ita kuwa sai kumfar baki ta ke ta na
cewa ki tsaya mana kiga yadda zamu yi da ke dan
ubanki, abin haushi Nazir sai wani bata baki ya ke dan
ba ya son 6acin ranta musamman da ranta ya baci
gwara na kowa ya bаcі.
Gaba daya yau daga Ummu har Shema'u suna
family house ne domin halartar sunan dan da
Babangida ya haifa, ganin Nazir ne sunan sa na ainihi
Yusif shi ne su ke kiransa da Babangida, Shema'u ta
yi mamaki yadda dangin Hajiya suka sakar mata fuska
hatta Hajiya kaffa-kaffa ta ke yi da ita.
Gaba daya matan 'ya'yan gidan sun hadu suna
cin abinci suna ta hirar fahimtar juna saboda su babu
wani faccalanci a tsakaninsu, saboda Usaini mijinsu a
tsaye ya ke duk wacce ta kawo abin d aya ga zai
riguza musu zumunci 'yaya yanzu zai yi maganinki
saboda haka da fahimtar juna a tsakaninsu, Hajiyar su
Nazir ta leko ta ce idan kun gama cin abinci kizo ki
same ni 6angaran Alhaji ina son magana da ke,
Ummu ta yi tsagal ta ce to Hajiya ta ce ba da ke nake
ba da Shema'u na ke Shema ta ce, to yayin da sauran
su ka fashe da dariya su ka shiga zolayar Ummu.
39
Bayan sun kammala har ta wanke hannu ta nufi
in da ake kiranta falon babu kowa in ka dauke Hajiya
da ta ke zaune ta ke jiran karasowar ta, ta yi sallama ta
shiga ta sami Kasan kafet ta zauna sannan ta ce Hajiya
gani.
Hajiya ta bi ta da kallo na tsaf sannan ta ce dama
ba wani/abu ya sa na kira ki ba saboda ganin yadda
kika sayya bai kamata in yi shiru ba a matsayina da
mahaifiyar mijinki, Shema'u kowa ya ganki zai san
kin sauya domin kin rame na kuma san cewa abokiyar
zamanki te shiga hakkinki, Shema'u ki gafarce ni sai
yanzu na e nadama da da na sanin hada auren Ummu
da Nazir, domin ina ta kaicin ace dan uwanka na uwa
daya uba daya shi ya ke neman juyar maka da
hankalin dani a tunanina Hajiya Umma ko babu raina
zata rike minabin da na haifa, ashe abin ba haka ya ke
ba, ina so ki fito fili ki fada min me ya ke faruwa
tsakaninku da mijinki da abokiyar zaman ki? Shema'u
ta yi shiru ta na tunani can ta ce Hajiya babu komai
kin san yanayin shayar da tagwaye kadai zai iya sani
rama, tunda ba sabawa na yi ba. Hajiya ta ce na ji
wannan abin da ya sa kika ga na tambaye ki shi ne, ko
kin san daga ni har Alhaji mun kai wata uku ba mu sa
Nazir a idanuwanmu ba, wani abin takaici ba ya barin
wayarsa a bude, ko da yaushe a rufe take abin da ya
sani cikin kokonto shi ne sau biyu ina aiken Surayya
gidan Hajiya Umma sai ta ce taga yayanta Nazir a
can, hawaye su ka zubo wa Hajiya, kin ga ya tabbata
40
ita ta janye min da kenan, ni mahaifiyarsa kenan ina
ga ke matarsa nasan kina kunsar bakin cikin da ya fi
nawa tun da dai mahaifinki saboda aminci irin na da
ba zai saurari wannan ba, Shema'u idan ba mu dauki
mataki ba mun ci amanar amincin da ya ke tsakanin
Alhaji da mahaifinki, tamkar yanda na ke ji da Nazir a
zuciyata haka nake sonki ki fito fili ki fada min abin
da ya ke damunki, Hajiya ni abin da nake so a gare ki
shi ne addu'a ki ringa yi wa Nazir addu'a sai kiga duk
wani kulli nasu Allah ya rusa shi amma ni yanzu
tsakanina da shi babu komai sai dan abin da ba a rasa
ba, su ka yi sallama su ka rabu.
A gaskiya yanzu abin na Nazir ya shige hankali,
domin ya watsar da Shema'u tamkar Ummu ce kawai
matarsa, ba shi da aikin da ya fi nata bai isa ya gabatar
da abu da kansa ba sai abin da mahaifiyarta ta ce sun
tare a jikinsa dan yanda ya ke musu facaka kan baka
ce ya na da uwa da uba ba tuni Alhaji ya fita harkarsa
tun Hajiya na yi masa nacin bai kamata ya ce ya cire
hannunsa akansa ba har itama tazo ta ce ta fita
harkarsa har da ta iyalinsa, gaba daya Nazir ya zama
tamkarm waina a tanda sai yadda aka juya shi, Ummu
kam an yi kudi da Nazir yadda ransu ke so sai dai ta
in da aka samu kudin ta nan su ke tafiya domin dai
Bokaye da 'yanbori da Malamai 'yantsibbu su suke cin
kudinta, ashe gaba daya maganar da Hajiya da
Shema'u su ka yi duk a kunnan Ummu su ka yi ta dan
sai da tazo ta labe ta ji duk abin da su ke fada ta
41
kwashe ta fada wa uwarta ita kuma ta ce zata yi maganinsu.
Shema'u ta shiga damuwa fiye da da saboda
yadda Nazir ya banzatar da su a yau daga ita har
yaranta a gidansu za su yau, ta shirya su su ka nufi
can, saboda yau ake sa ranar bikin Yayanta Kabir. Sun
je gidan da wuri saboda sunan yan zuwan farko ita da mahaifiyarta sun kule da a dakin suna ta hira ta
bazawa mahaifiyarta irin halin da ta ke'ciki ta ce kiyi
hakuri wata rana sai labari ina tausayawa rayuwar
Ummu da mahaifiyarta saboda raba da da mahaifi sai
Allah, aka raba mace da miji kinsan mahaifinki kiyi ta
hakuri watarana sai labari, cikin kuka ta ce to yanzu
Nana duk fa wasu bukatuna da kaina nake yi, ni kuma
ba kudi ba ba aiki ba ya zan iya daukar nauyin kaina
da na yarana, musulunci fa bai bar komai ba komai sai
da ya bayyana shi yanzu Nana rayuwa zata yiwu a
haka, Nana ta ce baya baki abinci ta ce abinci kam a
kwai a store duk wata zai zuba hatta kaji da nama
kwai komai a kwai shi amma rabon da kiga ficikarsa
tazo hannuna zamu kai watanni biyar dai ma Allah ya
sa ina da 'yan kudadena a banki kuma kinsan wancan
watan na dauki kudin hayar gidana, sai kiyi wa Allah
godiya tunda ya rufa miki asiri, ni kam Nana ina so in
koma karatuna in kuma ci gaba da koyarwata tunda
Annabi ne ya ce mu nemi ilimi ko da kuw aa birnin
sin ne, ni dai ina son in koma makaranta, sun jima
suna tattaunawa mahaifiyarta na bata shawara mai
42
kyau sai da mutane su ka soma zuwa su ka hakura da
hirar.
Kusan sha biyu zata yi na rana, Shema'u ta fito
daga bangaranta dan ta fadawa mai wanki cewar ya yi
sauri ta na son zata aike shi sai ta hangi Ummu ta rako
Nazir mota ko ina zai fita? Oho! Dama ta na son
magana dashi saboda kudin makarantar Nur jiya sun
ba ta takardar dakatarwa in dai ba a biya ba ta dan
tsaya ta na san Ummu ta gama abin da ta ke yi amma
taga ba ta da niyya sai ta karasa, ta dan risina ta
gaishe shi ya kalle ta fuskarsa dai babu yabo babu
fallasa ya ce Ummu Nur ya aka yi ne, ta ce AbuNur
wajan ka nazo ya ce ina jin ki ta ce kudin makarantar
Nur ga shi jiya har an dakatar da ita oh ya dafe kai ya
ce na sha'afa bari in baki sai kije ki biya mata, na ce to
ya zura hannu a aljihu ya laluba bai dauko komai ba
ya bude jakar da ke gefensa ya zaro rafar 'yan dubu
dai dai ya bani ya ce gashi ki biya ragowar ayi cefane
wani dadi na ji har ina ganin addu'a ta ce ta karbu na
yi masa godiya mai tarin yawa, a lokacin da ta ke yi
masa godiya kuwa ita Ummu ta hade fuska yayin da
tausayin Shema'u ya kama Nazir har ya ke ganin
wautarsa na banzatar da matarsa da ya yi ya kuma
kudiri aniyar kawo gyara.
Shema'u ta na zaune a falo ta gama kirga kudi
dubu dari da hamsin, washe gari taje ta biya kudin
Nur na makaranta ta shiga super market ta dan yi
musu sayayya ita da yara ba ta koma gida ba sai da
43
taje banki ta zuba kudin ragowar da zata yi amfani da
su ta bar su a jakarta sannan tayo gida.
Me zai faru? Kofar wajanta ta gani an tuttula
rubutu ga garin magunguna nan bakinta dauke da
addu'a ta shige wajanta falon duk ta gani a hargitse
wannan ya tabbatar mata Ummu ta shigo ta yi mata
bincike, ta shiga gyara dakin ta ta tsinci layu sun kai
biyar kafin ta gama gyarawa ta kyasta musu wuta ta
kone su duk da cewar Nazir ba ya shigowa wajen ta to
amma ya na kula da yara in kuma zai tafi zai basu
kudi na yi mamakin wannan sauyi ko da ya ke addu'a
maganin komai ce.
Kamar yadda na saba in ina son ganin maigidan
zan tsayar da idona ne farfajiyar gida in zai fita in yi
magana da shi muna tsaye ina gaishe shi Ummu ta
karaso in da kuka san wata taba6biya ta taka ni ta
wuce na ce Ummu ya za ki taka ni ki wuce sai cewa ta
yi an taka in kina da abin yi ki yi na ce ba ni da shi
amma na barki da Allah, ji na yi ta falla min mari
kafin in dawo daga gigin marin nima na rama tuni ta
kama ni da kokawa tana zagina zagi na cin mutunci,
Nazir ya na yi mana tsawa tare da cewa shi-fa ya gaji
na ce amma dai kaga abin da ta yi min abin mamaki
sai ga Nazir ya goyi da bayan Ummu har da shi a ci
min mutunci zuciyata ta yi baki na kasa hakuri na ce
na gaji da irin wulakancin da kake min a gabanka tazo
ta yi min wulakanci ga zagi da wulakanci to ni ba zan
varda ba dole ne ka bi min hakkina dan na zagi tsohon
44
banza mai dankaran kwadayi shi ne za ki damu na
kada baki na ce me kanannadeddan hannu ita ki ka
zaga nasan dama irin wannan addu'ar ya dace da ita
domin irin tarbiyar da ta ke miki kenan babu kunya
Nazir ya rufe ido wai tunda na zagi uwar Ummu zan
zagi tasa nan fa ya shiga ci min mutunci itama tana yi
min na juya zan bar wajan ta figo ni nan fa kokawa ta
dawo sabuwa, ni dama nasan ta fi ni karfi amma dai
Allah ya bani karfin zuciya da kyar ya raba mu ta fada
in fada ya ce kar wacce ta kara magana a cikinmu, ni
tuni naja bakina na yi shiru dan in ji hukuncin da zai
yanke mana, sai cewa ya yi Shema'u na gaji da halin
tsiya irin naki duk abin da ya ke faruwa ke kike
janyowa saboda haka yau zan yada kwallon
mangwaro in huta da kuda, Ummu sai wani karkada
kafa take yi tana cewa in b an da jarraba ma mutum
an nuna ba ayi da shi ai sai ya tafi gidan tsohonsa ko
yau dai dubu ta cika sai a tattara a koma in da aka fito,
darling fada mata ta ji Shema'u ki tattara ina ki ina ki
ki bar min gida na sake ki saki daya bani da bukatar
sake ganinki a gidana, abin ya zo wa Shema'u a bazata
saboda haka da farko rudewa ta yi amma da ta soma
jan innalillahi sai ta sami nutsuwa nan take ta ce ni ka
saka Nazir? Ya ce kwarai to na ji amma bari in fada
maka, zama dam in ji mara zuciya saboda ni yanzu ka
zama ubana yara uku ai mun zama daya zan yi zaman
'ya'yana saboda haka ka iya zaga rabon 'ya'yana ka
bani in zauna in yi musu tarbiya ta gari amma ni ba
45
zan haifi da a cikina in ba wa Ummtu ta yi rainonsa ba
saboda itama ba ta da tarbiyar bare ta yi wa wani ni
yanzu ko miji na samu ai kaine waliyina kai zaka
daura min aure saboda haka zugu ne ba ta kare ba
Ummu muna tare ina so ki rike wannan yanzu ne za
muyi zama yanzu za ki san shema'u da ba ni kika sani
ba saboda da igiyar aure akaina yanzu kuwa babu
nauyin kowa a kaina, ta juya.ta tafi ta bar su a bushe a
wajan dan ba haka Ummu ta zata ba.
Falonta ta nufa ta na zuwa ciki ta shige gado ta
fada ta na kuka wai ni Nazir zai saki ta shiga hada
kayan ta da na yara ta na fadin ai gidan ka ba aljanna
ba ce ba zan zauna ba ta gama hada ko ma maganar
yayanta Kabir ta dawo mata kamar yanzu ya ke fada
mata, nasha jin mahaifinmu na fadin bai haifi 'yar da
zata zo masa yaji gida ta zauna ba, shi ko auranta ne
ya mutu sai ya tabbatar ta gama idda gidan mijinta ji
ta yi jiri na dibarta wai wane irin hali ne da
mahaifinsu ta yi shiru ta na tunanin yanzu in naje ma
dawo dani za ayi in na zauna burin Ummu kawai ya
ishe ni waya ta dauka ta yi wa yayanta Kabir bayan
sun gaisa ta ce Yaya ina son ganinka yanzu dan Allah
kazo ya ce ga shi ba na gari ina Kaduna ina duba
ginina, da ya ke a can ya ke aiki kuma in an yi bikinsa
can za su zauna, Yaya yaushc za ka dawo? Zuwa jibi
zan dawo, lafiya in kuna da damuwa ki fada min, ina
son magana da kai amma sai ka dawo din, yinin ranar
46
nan ta yi zuru-zuru saboda in da ta tsinci kanta cikin
damuwa.
Damuwar da tasa cikin