kafa gurin Nazir
kai ka cc ba a taba yi masa haihuwa ba ya ringa Garin
kudi kamar bai san zafin su ba sai da yayi mata
akwatina dozin nata shida na fanta shida ko tsinke bai
ba wa Shema'u ba itama ba ta damu ba dan ba ta sa rai
ba aikin bikin nan Shema'u ce ke yi tana cikin yin
wani ya acc ga wani irin da Ummu ta haihu hutu kam
Shema'u ba ta same shi ba, matan gidan da kansu su
ka yi wa Hajiya maganar aiki ya yi wa yarinyar nan
yawa ta yi wannan ta yi wannan ita kadai sai ka се
mai hannun gizo-gizo, gaskiya tunda gida da yawa
gamu ga 'ya'yanmu ai sai a sakar mana wani aikin
muyi, Hajiya ta ce sam abokiyar zamanta ce dole ta yi
mata aikin biki har na kwana arba'in, a'a Hajiya ba
kwana arba'in ake yi ba sati daya ake kuma na sati
zata yi, ai itama 'ya ce Hajiya ta ce ni kuma na haifi
mijinta sai in ga mai mai iko ni ko ku, jin abin da ta ce
ya sa su ka ja bakinsu su ka yi shiru.
Ranar kwana biyar da haihuwa a ranar aka yi
Kauri sai da ya yanka manyan raguna biyu na kauri
Shema'u ita ce Karfin aikin naman sai Aysha da
Aina'u da su ka taya ta bayan sun kammala su ka
mikawa Hajiya ai kuwa su an basu har da rabon
mazajen ita kuwa ko yanka daya, abin ya ba wa su
Aysha haushi amma ita kuwa ba ta yi mamaki ba
tunda kuwa kullum ita take gasa naman ga shi ko
yanka daya ba a ta6a bata ba ko ita ko 'yarta, da
daddare ne Dayyib kaninta ya kawo mata aiken da
16
tayi masa, atamfa ya siyo mata phoenix da kayan
jariri kala shida amma da ta kai kayan barkar ta watso
mata aka yi aka ce Ummu tafi karfin daura phoenix
atamfar dubu biyu da dari biyar ce wani wajen ma har
dubu uku amma an raina ta tsinci kayan ta hawaye na
bin fuskarta wajen Aysha ta zauna tasa kayan a gaba
tana kuka, haushi ya kama Aysha to dan ba a karba ba
sai me, ni ba rashin karbar ke damuna ba illa na rasa
me na yi wa Ummu aka tsanc ni aka tsani abin da na
haifa, ta kalli Aysha da jan ido ta ce, wallahi Aysha
tun da na ke ban taba yi wa wani yasin ba ya za ayi
ma in yi mata yasin ke kika dami kanki komai mutum
ya ga zai iya ya yi duniya ce ta ishi kowa.
A yau ne sunan jaririn da Ummu ta haifa wanda
ya ci sunan mahaifinta Suraj an yi suna na kece raini
dan irin ragunan da aka yanka masu kama da shanu
guda uku kayan ciye-ciye kala-kala da na shaye-shaye
ni ma dai ba abarni a baya ba dan nayi shiga mai kyau
da gani har 'yata nasha bakaken maganganu gurin
dangin Ummu haka dai taro ya watse.
Washe gari suna muna zaune tsakar gida 'yan
uwan Ummu su na ta aiki naman suna kun san yaro
babu hankali sai Nur ta ringa rigima wai ita nama zata
ci kin basu aikin ta ce da ya ta ce in kin ci naman nan
kici hantar uwarki shegiya 'yar masu tsafi naji haushi
amma sai na kasa ce mata kome, Aysha ta ce ai kuwa
Nur sai ta ci nama tunda ubanta ya siya aka kuma,
yanka nan dai na dauki 'yata nayi gaba suna ta cacar
17
baki da Aysha can itama ta taho ta bar su, abin ka da
yaro me kafa sai ta koma su ka yi ma ta kcta su ka
dauko nama daga wuta mai dankaran zafi aka danka
mata, ai kuwa yarinya ta shide, jin ihunta ya sa ni da
Aysha fitowa sai mu ka same ta hannun Alhaji ya na
ta fada ashc tun abin da ya fai ya na ji har sai da su ka
danka mata naman nan ya dauke ta hannu har ya tashi
nan fa Alhaji ya ce duk masu suya nama su tafi ba ya
son zaman kowa, Hajiya kuwa ta ce ba zai yiwu a kori
'yan uwanta ba, ya ce wallahi sai sun tafi wai ai in ba
haka aka yi mata ba tashi zata yi da roko nan fa Alhaji
ya hau fada in da ya ce dukl fa abin da ya ke faruwa
na sani tsaf kyalcwa nake saboda anga iyayanta ba sa
yin magana to ni daga yau na zama wakilin Shema'u
cikin gidan nan duk wanda ya yi mata sai na yi masa
ni nasan abin da ya sa mahaifanta su ka yi shiru
saboda sanin darajar zaman tare, haba Alhaji in ji
Hajiya ai saboda sun san 'yarsu ba ta da gaskiya ne
nan dai ya yi musu kaca-kaca ya kore su dole Hajiya
ta fito ta soya nama ko da aka raba Alhaji bai ci ba
bare ni dama da ba aban ba tun da ga ranar kullum sai
Alhaji ya aikowa da Nur nama (balangu) ko (tsire).
Yau dai yamma mu ka samu kiran Alhaji, da
gaggawa wannan karon na samu mahaifana falon
Alhaji ga iyayan Ummu ga Nazir ga wani bawan
Allah wanda kana ganinsa kasan Malami ne ya na
zaune, bayan mun zauna Alhaji ya ce wannan shi ne
Malam Sani shi ne Malamina shi na sa ya yi min
18
bincike kan gobarar da aka yi wacce Ummu ta kasa
tawakkali ta yi wa 'yar uwarta kazafin ta yi mata yasin
Malam ina so ka warware mana komai.
Malam ya yi gyaran murya sannan ya ce abu irin
wannan in ya samu mutum ya yi tawakkali ko da aiko
maka aka yi to ka kaddara daga Allah ne sai Allah ya
sauya maka da alheri, a gaskiya a iya nawa bincike da
na yi da kuma istihara da na yi ya nuna min cewa
gobarar nan da ta faru ba daga Allah ta ke ba domin
yasin din aka yi aka aikowa da Shema'u ita dan ta
tarwatsa ta ta fita daga hayyacintga ta rasa hankalinta
ta rasa dukiyarta koma ta rasa ranta gaba daya to
amma Allah cikin ikonsa sai ya takaita aiken da aka
yo mata ya juya kan wanda ya aiko shi domin ita
Shema'u yarinya ce mai addu'a kuma iyayenta na yi
mata saboda haka wannan aken kan ita wacce tayi ya
dawo ina kuma ba ki shawara addu'a in ba wacce za ki
sa ayi miki saboda kare kanki ba ne to kar ki sake yin
irin wannan domin kin ga abin da ya same ki, shi yasa
Malam Bahaushe ya ce in za ka gina ramin mugunta
ka gina shi gajere wala Allah kai za ka fada gani ga
wane dai ya-ishi wane tsoron Allah, nan fa maman
Ummu ta hau masifa wai an tara mutane an ci musu
mutunci ita wallahi ba zata yarda ba sai ta shigar da
kara kotu tai ta babatu babu wanda ya tanka mata
Ummu kuma tana ta kuka tana cewa Umma Hajiya sai
da na ce karki yi mata yasin da ma ai an ce ta ci gaba
ta ci baya ne yanzu fa komai nawa ya ci wuta ga
19
kudına duk wuta ta cinye, baban Ummu kuwa ya rasa bakin magana saboda tsabar takaici.
Ita kuwa Shema'u sai kukan murna ta ke yayin
da Alhaji ya kalli Nazir da ya yi tsu ru ya ce ka nemi
afuwar matarka domin ka zalince ta, kuma sai Allah
ya saka mata da niyyata zaka koma gidan da na gyara
wa su Rufa'i, amma yanzu na fasa ban gyara na za ku
koma har lokacin da ka ga ma sason gini tun da naga
an soma aiki kuma ina so kowacce ayi mata part dinta
daban, ya juya kan Ummu ya ce Gani ga wane dai ya
ishi wanne tsoron Allah daga ke har mahaifiyarki ku
sake hali da tsari ku sa tsoron Allah a zuciyarku
Shema'u dai ta fi karfin ku tunda dai ita yarinya ce
mai Ibada babu yadda zaku yi da ita sai dai shi
wannan sokon sai kuyi ta gara shi in kun nutsu kun
daina kanku in ma baku daina ba kanku, Allah dai ya
fi ku, sai zancen kayi da na ce zan sake to jiya kunnen
ko da lis dan har na ce jibi a zo a karba to na fasa sai a
nan Alhaji Jibrin ya yi magana a'a Alhaji Yusif ba a
haka a girma ya fi gaban komai wallahi Allah kenan
tsinke ba zan siya ba, Babanta ya ce kayi daiai ni
kaina da nace tazo ta karbi miliyan daya da rabi ko
sule mba zan bayar ba, Ummu ta kurma kuka ta na
bada hakuri, wai ba ita ta yi ba Umma Hajiya ce ta
tuba ba za ta kara ba, nan dai aka yi ta sa in sa
kwandala babu mai bata har mijinta haka taro ya tashi.
Kan kace meye wannan zance ya karade ko ina
Ummu ta yi wa Shema'u yasin ta dawo kansu, ai kuwa
20
a
a
e
a
fi
i
e
Kil
a
a
n
a
n
ณ
te
in
n
ת
n
ta
a
na
va
EEeEiiבaaבiυeannnaaaa
abin ya dame su ko suna ko biki bata iya zuwa saboda
nuna ta da ake yi akan ta yi asiri ya koma musu, Nazir
dai ya rasa ta ce wa yara da idon da zai kalli matarsa
ko da ya ke namiji ba kunya ce da shi ba yana iya
mutsittsekewa to hakan ce ta faru ga Nazir ita kanta
Hajiya abin ya tsimata dan dai babu yadda zat ayi 'yar
uwarta се. A yanzu mun ce Nazir ya samu 'yuar nutsuwa
saboda ya koma Business dinsa a yanzu yakan
kwatanta adalci dan ya na jin kunyar Shema'u saboda
abubuwan da ya yi mata amma fa karkace su Ummu
sun hakura a yanzu ne ma su ka dauki tsana su ka sa
wa Shema'u saboda sun da sia sun ga bayanta daga ita
har 'yarta Nur yanzu ne ita kuma ta sake dage dantse
saboda ganin yadda addu'a ta yi ma ta rana dan ita
Shema'u gani ta ke yi iyayanta ba sa sonta shi ya sa
ma ba sa kula da duk wani abu da zata fada gara ma
mahaifiyarta ita zata ba ta shawara amma babanta sai
ya ce jeki ai muna yi miki addu'a insha Allahu babu
abin da zai same ki.
Yanzu suna zaune part din Alhaji saboda haka su
na da katon falo da one room megidan ne ke bin daki
yanzu saboda haka yanzu kowacce na dakinta kuma
tan kula da mijinta tsaf yanzu kissa da iya
kwarkwasa ke kwatar kowa da kuma iya tarairayar
miji yanzu fa Ummu ta raina kanta dan bata iya komai
ba sai dai tana nan san gam gam kama tabaryar dan
madai ita Shema'u ba ta da sha'awar dan ne wa yar
21
uwarta hakki amma duk da haka Ummu sai tabi ta
lalace saboda sa bakin kishi a zuciya.
Yanzu dai Shema'u ta murmure daga ita har Nur
ga Nur a har an shiga makaranta dan tana playgroup
tunda shekarunta uku ga Ummu nan ta sake samun
wani cikin yanzu har ta yaye Suraj ginin da ake musu
kuwa ya yi nisa, Ummu dai ta soma raina kanta don
yanda ta zata za ayi mata ba shi ya ke samu wasa dan
wannan cikin nata duk abin da take so sai dai ta tashi
ta yi da kanta tunda ba na dai kukanta ta samu 'yanci.
Ganin zaman banza da suke ne ya sa Shema'u ko
kar arzikin gurin Nazir domin taje ta koyi dinki ai
kuwa ban yi mata gardama ba cikin watanni shida har
ta kware Shema'u na iya dinki ko wanne iri ne da
yake tana da nasibi a dikin in kaga yanda dakinta ke
cika da dunkunan mutane sai abin ya baka mamaki,
cikin azimi tana tara dunkunan Sallah Nazir na
gefenta ya na yi mata hira me zai faru sai ta ga wani
abu ya bude labule ya shigo tana fadin innalillahi
wa'inna ilaihir raji'un ashe shima Nazir ya ganin ya na
fadin Hasbinallahu wani imal wakil kawai sai abin ya
fada akan keken dinki keke ya kama da wuta karar
faduwarsa ya yi wuri gida Shema'u kafin ka ce kaso
an sauya mata kamanni baki ya koma gefe idanu sun
juye kamar na kutare fatar jikinta ta yi wani iri kai in
ka kalle ta ba zaka ce shema'u ba ce duk abin da ya
faru ya faru a gaban idan Nazir abin da ya tsorata shi
da ya ga keken ya kama da wuta amma ya na gama
22
cinyewa sai wutar ta mutu murus kamar ba yanzu
wuta ke ci ba sai a lokacin Allah ya ba shi ikon daga
Shema'u da aka yi wurgi da ita sai a lokacin yaga
yanda aka canja mata halitta ya rike ta ya na kuka ya
na tofa mata addu'o'in da su ka sawwaka a gare ta tun
cikin dare aka kirawo mahaifinya kwana su ka yi
akanta shi da mahaifinsa amma ina bata san wanda ya
ke kanta ba.
Abu kamar wasa ciwo ya ci gaba da zafi domin
gaba daya hankalin iyayanta yana kanta kowa kokari
ya ke ya kawo mata magani, Nazir dai ya kidıme wai
sai ya fita da ita Saudiyya mahaifinsa ya ce a bari dai
a gani wanda aka mata yanzu mahaifinta da kansa ya
nemi izinin tafiya da ita gida saboda ba ta iya komai
da kanta wasa wasa sai a ta smau wata daya a kwance
bata san wanda ya ke kanta ba komai sai anyi mata
duk me Imani in ya ganta ya tausaya mata haka dai
iyayanta su ka dukufa nema mata magani a kanta
wannan asibiti duk in da aka ji me magani sai an nema
an bata amma har yanzu ba ayi katari ba.
Mahaifiyarta ce ta ce ya kamata a nemi mata
maganin sammu saboda yanayin ciwonta kamar jifa
nan fa ya hau fada wai wa zai jefe ta ciwo ne dai
Allah ya kawo shi sauki kuma sai a hankali, Alhaji
Yusuf ma ya fadi haka amma shima haifenta ya се
Allah ne ya dora mata ba zai zargi kowa ba ba kuma
zai bawa zuciyarsa damar zargin wani ba idan Allah
ya nufe ta da warkewa to in kuma kwananta ya kare
23
Allah ya sa ta jikawa da Imani, Alhaji Yusif babu
wani malami da ya amince wa kamar Malam Sani me
ishiriniya ga shi ba ya nan ya na kasar Sengel to cikin
hukuncin Allah, Allah ya nu fushi da dawowa ya
kuma zo yaga jikin na ta ya kuma fassara ciwon nata
ya kuma yi niyar taimakonta haka dai ya shiga kawo
mata rubutu da turarruka cikin hukuncin Allah har in
an zaunar da zata zauna takan yi magana amma ba
kowa ne ya ke ganewa ba saboda yadda harshen ta ya
karye in zata yi magana sai ka ji kamar da hanci ta ke yi.
Ganin ta soma samun sauki sosai shi ya sa ga
yadda Nazir ke sintiri a gidan koda ya ke har yanzu
hannunta da kafarta ba sa motsi ma'ana ba sa wani
amfani har yanzu bakinta bai dawo daidai ba, haka
Alhaji Jibrin mahaifinta ya ce a maida ita gidanta,
Nazir ya ne mi alfarmar a kyale ta saboda ya
kammala jininsa har furtuniture ya zuba musu hatta
showglass duk ya yi musu komai iri daya da Ummu,
kowa iyayensa yaje ya gani kayan Shema'u su aka
siyar aka sai mata irin kayan decroction na kawata
daki da wani shegen labule falon nata an kwatashi
sosai dan komai na ta ya fi na Ummu, saboda Ummu
duk'wani abu da zata samu gurin miji, to suna raba wa
Malamin da bokaye ne su sami rabonsu saboda haka
Ummu yanzu dai babu abin.
Ummu dai ta sake haihuwa wannan karon ma
namiji ta haifa saboda haka ita ana ta tunanin tafa
24
gama da Nazir saboda gashi basawanta biyu wannan
karar an samu Lukman. Bayan suna da sati biyu ne
aka tare a sabon gidansu, ita Shema'u saboda ba ta da
cikakkiyar lafiya sai wata 'yar kanin Babanta ta zauna
tare da ita tana taimaka mata tana kuma kula da Nur
Shema'u ba ta fi wata da dawowa ba to soma zazzafan
zazzabi kamar wasa suna zuwa asibiti ba wan awun
fitsari aka tabbatar da ciki wanda bai fi sati uku ba, ai
kuwa hankalin Ummu yata shi domin a yawon bin
Malamansu an fada musu wai zata haifi 'yan biyu
duka ma maza wai kuma su za su gaji mahaifinsu in
dai ba ta tashi a tsaye ba yayanta za su zama ko kai ya
basu.
Kai wannan ciki na Shema'u da fallasa ya ke
dama ita ba lafiya ba gashi kowa yasan da cikin dan in
baka sami ba Ummu zata fada wai mutum ba lafiya ba
amma saboda tsabar na ci sai da ya samu ciki aikuwa
cikin nan na Shema'u ya wahalar da ita tunda kuwa
komai ta ci sai ya dawo gashi ciwonta ya tashi dole
iyayenta su ka ce amai da ita gida Nazir ya ce a'a shi
kam zai yi jinyarta mahaifinsa ya ce ya yi hakuri a tafi
da ita randa aka maida ita gidansu ranar cikin ya
lalace nan da nan asibiti aka tafi da ita sai da aka
kenta robar jini uku Malam Sani yaje duba ta anan
ya yi wa Alhaji Yusif alkawari zai karya duk wani
sihiri da ke jikinta zai kuma yi mata wani da fa'ida ba
da mutan ba sai Allah.
25
Wannan jinya ta Shema'u ta tashi hankalin
danginta dan har ta fita farko zafi kowa gani ya ke
lokaci ne kawai bai yi ba, kamar yanda Malam Sani
ya yi alkawari zai yi mata dafa in da babu mahalukin
da ya isa ya taba ta da izinin Allah to a yau Malam ya
na zaunc a falon gidan su ya yi wa mahaifinta da
sirikinta cikakken bayan yayin da ya ce a kawo masa
manyan zakaru shckararru na Hausa guda bakwai ya
ce zai yi rubutun suratu yasin kafa saba'in da suratu
jinni ita ma saba'in idan an wanke ruwan rubuta za'a
yanka mata zakara da ya ayi mata farfesunsa kafin nan
za'a sami ganyen tumfafiya guda bakwai za'a rubuta
sunan Allah guda casa'in da tara a saka su su bushc a
daka za a zuba cikin romon rubutun da kuma gayan
magarya da kaikayi koma kan mashekiya shima duk
za'a zuba cikin romon za ayi romon daidai wanda zata
iya cinyewa ita kadai ba tare da wani ya ci ba idan
zata ci to karta karya kashin naman idan ta cinye tas
sai aje a kona kashin sannan sai a binne shi haka zata
yi kullum har kwanaki bakwai, kun fahimta kun ga ya
kama zata cinye zakarun nan guda bakwai a kwana
bakwai in da aka yi wannan to tabbas zata fi karfin
duk wani man kawo mata hari, duk wannan zafin
ciwon idan sihiri ne to zata samu sauki gaba dayan su
su ka yi masa godiya tare da tambayar nawa ne sadaka
ya ce duk abin da Allah ya hore musu su biya sai
kudiri ladan rubutu da za asa masu yi su yi a biya su
sai kuma abubuwan da za a siya take Alhaji Yusif ya
26
zare dubu hamsin ya ba shi ya ce gashi nan komai ake
da bukata sai a siya cikin kudu, sadaka kuma zan zo
har gida in baka.
Jiki kan ya warke dan kafin kwana uku ta soma
tashi zaune har in 'yan dubiya sun zo za ka ji hirar ta,
Nazir kuwa nan ya tare saboda kula da ita satin ta biyu
ta murmure ba ka ce ita ce ta yi wannan jinyar ba.
Shema'u ta na kwance cikin daki a gidan su Nazir ya
yi sallama ya shiga, ta dan yi murmushi ta ce Yayana
barka da zuwa, ya ce yauwa ta ce saukar yaushe ai na
yi zaton kana Dubai ya ce saukar yanzu dan ko gida
ban je ba na ce sai na dawo na ga sweet darling, ta yi
murmushi ta dan yunkura bari in kawo ma ka abinci
yau gidan ni kadai ce nan ta mike kafa babu kwari
kamar mai koyar tafiya taje ta kawo masa kayan
abinci sauri ya yi ya mike ya karbe ta dan ya ke
tsaf sai ta mbar.
Sun kasance cikin so da kauna don s.a sake sosai
tunda gidan babu kowa, ya danyi gyaran murya ya ce
ya kin samu sauki cikin kidima ta ce ina ya ce gida na
mana ta kalle shi ta ce Yayana ina son raina ina son
lafiyata ba zan iya zama da kai ba kuma ko ba ka
kawo min wannan maganar ba nima ina son yin
magana da kai, yayana Musulunci ya bamu dama in
har mace taga zamanta da miji akwai kwaruwa to fa
akwai hanyar warware ko ita macen gani tayi ba zata
iya zama da mijin ba akwai hanyar warwara hanyar
kuwa ita ce yayana zan yi maka aure don in fanshi
27
kaina ina son muhi hulki ni da kai ya zuba mata ido
saboda ya kasa magana cam ya ce, kin manta cewa da
gani har ke muna son juna shi kuma hulki idan har
ma'aurata su ka yi shi to aure ya haramta har abada ya
zaki yi min hulki mana yi miki wanda har zan ki yi
min wannan hukunci Shema'u ta kalle shi kafin ta
sake magana tuni shi ya fice daga ganin ta maida kai
ta kwanta ta ce Allah kaga ina son Nazir dole ce tasa
na ke son neman rabuwa da shi dan in tsira da
lafiyarta.
Nazir mahaifinsa ya samu ya fada masa cewa
Shema'u ta ne me shi da suyi hulki, shi kuma ya na
son matarsa ba zai iya rabuwa da ita ba mahaifinsa ya
ce da wanne dalili ko hujjar ta ke so ku rabu, Nazir ya
sunkuyar da kai ya ce Alhaji nima ban sani ba, to tashi
jeka bayan sallar Isha sai ka dawo lokaci Alhaji Jibrin
ya dawo daga kasuwa, wannan magana ta manya ce
ya mike ya ce to Alhaji na tafi sai nazo din.
Bayan sallar Isha ina zaune dakin da nake tunda
har yanzu kafofina ba su yi kwari sosai ba, na mike su
Nana mahaifiyata na shafa min wani magani a kafar
da ya ke kullum sai an kaini gashin kafar asibiti,
mahaifina ne suka shigo shi da Alhaji ko da ya ke
wannan ba sabon abu ba ne saboda haka ban kawo
komai ba bayan na ganshe su can sai ga Nazir ya
shigo shima ya gaishe su ya samu gefe ya zauna sun ci
gaba da tattaunawa duk akan ciwo na kafin daga
bisani su dawo kan maganar da ta kawo su maganar
28
mahaifina na tsinta ya na cewa, mun ji abin da ki ka
shiryawa kanki na san rabuwa da mijinki wato ni ban
isa kiyi shawara da ni ba ko da mahaifiyarki gaban
kanki kawai kika yi, har kin kai matsayin da za ki
nemi mijinki kuyi haka da shi ko, to ba ki isa ba a
gidan nan ba, ya hau fada ta in da ya shiga ba ta nan
ya ke son fita ba, ni kuwa a lokacin da ya ke fadan
nan ji nayi zuciyata ta yi bakikkirin saboda bacin rai
sai da ya yi fadan sa dan kansa ya yi shiru sannan
Alhaji Yusuf ya yi magana saboda a gaskiya babana
ya na da zafi sosai shi yasa duk wani abu da zai zama
bacin rai ba ya shigarsa shi ya sa duk wanda bai san
halinsa ba ake ganinsa mai shiru-shiru, to shi bacin
raine baya so, a'a Alhaji Jibrin ba za ayi haka bna, a
ba ta da marta ta yi magana ta kuma fadi hujjojinta
nasan rabuwa da mijinta, sai a lokacin mu ka hada ido
da Nazir, Alhaji Yusuf ya ce ke na ke saurare na
sunkuyar da kai na zuba wa kafafuna ido wandanda
ake nema anakasa ni can naji ai dama ce ma yanzu na
samu, cikin muryata wacce harshena bai fiye fita ba
saboda har yanzu ban koma normal ba, na ce, Allah
(SWT) shi ya bamu dama-mu ne mu a gurin
mazajenmu idan bukatar hakan ta taso a iya nawa dan
sanin da nake da shi sai na fahimci zaman da Nazir
akwai cutarwa mai yawa, kuma idan har akayi min
dole sai na zauna dashi to nasan watarana za azo a
dauki gawata domin ni ina da hujjoji masu mutukar
karfi akan rabuwarmu, wanda ko da alkali ne zai raba
29
auranmu, babana ya daka min tsawa munji hujjojin
naki muke so mu sani, na saki kuka mai ban tausayi
na ce baba shi ai yasan, tunda shi ya sani dole muma
ki fada mana don mutum uku ba a boye musu magana
Likita ko Malam, ko alkali dole ne ki fada musu
gaskiyar abin da ya ke damun ki, na ci gaba da kuka
ina fadi ai Allah shi ya bamu dama to tunda Allah shi
ya ce a nema baba ku kyale ni in nemi 'yancina fadar
Ubangiji zan bi, jikin Baba ya yi sanyi ya ce to, na ji
abin da ki ka fada ina so kije kotu ki shigar da kara ni
zan tsaya masa, kuka na ya ci gaba da karuwa na ce ai
Baba abin ba na kotu ba ne masalaha na nema a kashe
maganar a gida ya nemi aure ni zan biya masa sadaki
don in fanshi kaina, Alhaji Yusif ya ce kan Nazir kaje
ka nemi aure ni zan zamar mata wakili ko nawa za a
kashe wajan neman auren zan biya, Babana ya ce shi
fa sam sai ya ji hujjojin rabuwarmu, Alhaji Yusif ya
ce mace da miji sai Allah tunda ta ce shi ya sani to shi
ya fada mana in dai har ya na da gaskiya.
Magana fa ta yi tsamari ni na dage ba zan fadi
dalilina ba amma dan ina kan bakana nasan rabuwa da
shi shi kuma ya ce sam bai yarda ba aure ni da shi
yanzu aka fara duk yanda Babana ya ke da zafi in ya
hau fada na ringa kawo hujojina na ayoyi da hadisan
sai in kashe bakinsa, Babana da Babata sun sani a
gaba sun ko ki arzikin kar in kunyata su saboda yadda
Alhaji Yusif ya tsaya shi sai ya karbar min 'yancina
idan na tuna yadda Alhajin ke