zuciyarta ita ta haifar
mata da zazzabi da jiri saboda yau kwananta biyu
babu abinci da ya ga cikinta, tana kwance falo 'yan
biyunta nata zabga rigimarsu ita kuwa ji ta ke kanta
tamkar ana buga mata guduma. Nur ce in ta rarrashi
wannan in ya yi shiru sai ta juya ta rarrashi wannan
abin gwanin tausayi saboda ita kanta Nur din karama
ce, a haka Kabir ya shigo ya same su tausayinsu ya
kama shi da ya kalli 'yar uwarshi ya ga in da ta rame
gwanin ban tausayi saboda tsabar ciwon kai ko bude
ido ba ta yi haka ya tattara su su ka tafi asibiti bayan
gwaje-gwaje Likita ya sanar da shi damuwa ce ta yi
mata yawa tana bukatar mai kwantar mata da hankali,
kwarai ya dawo da ita gida sai da ya ga ta sha tea ta
hadiyi magani sannan ya ce gobe zan dawo sai mu
tattauna.
Washe gari Kabir ya iso gidan kanwarsa а
farfajiyar gidan su ka hadu da Nazir sun gaisa har da
tambayarsa mutanen gida sun dan jima suna hira ya ce
masa yazo duba jikin Shema'u ne dan juya jikin nata
ya yi zafi ya ji dam a zuciyarsa sai ya ji yara me zai ce
da Kabir can ya ce yanzu nima na fito a jikin nata da
sauki ya ce, okey su ka yi sallama.
A falo ya same ta ta warware suna kallon wani
kaset da tasa wa Nur mai suna (Ba'adal mautu) ya yi
sallama Nur ta yi tsalle ta rungume shi ta na fadin
47
aka saka sannu da zuwa uncle Kabir zo kaga yadda
hasan a wuta ba ya sallah Allah ya so ni ni dai ina
sallah, Kabir ya sa dariya ya ce su Abdul suna yi su ba
sa alwala sai sun ga mamanmu tana yi suma sai su
saka hijab su yi ya ce ashe dai suna yi ta ce Uncle
Kabir kai ma kana yi ya ce ni ina yi ba na son abin d
aya samu Hassan ni ma ya same ni Shema'u ta katse
su to sarkin surutu maza a tafi wasa maza kama
hannunsa kuje wasa, Kabir ya ce ku zo ku karba ya
raba musu ice cream da bísket su ka fita su na murna
sannan Shema'u ta zame daga kujera ta rusuna ta
gaida yayanta sannan su ka dan soma hira har dai su
ka gangaro kan abin da ya dame ta warware masa
komai ya wani zabura tamkar wanda kunama ta harba,
saki fa kika ce wallahi yaya ya sake ni yau kwana uku
kenan, saboda me ba ki je gida kin fada ba, saboda
abin da ka ce min Baba ya fada kuma idan naje na
fada mai da auran zasu yi koda ba ya so ni kuma na fi
son ko da zai koma to sai ya gane kuskurensa ya dawo
da kansa bare ma ba na fatan in koma hannunsa
saboda irin halin da na samu kaina, abin da nake so da
ke kija bakinki kiyi shiru ki zauna har in darki ta ci ka
saboda lokacin an yi bikina sai in deße ki daga ke har
yaran ki, saboda ba na son damuwa ta yi miki yawa za
ki koma karatunki da kuma koyarwarki daga nan can
makarantar da kike koyarwa zani in ji yaya zamu yi
da su sai in amiki duk wani cuku-cuku dan ki tafi
Misra amma sai kin yaye su Abdul ta ji dadi kwarai
48
C
ceE,
SO
iyasa
emm
emsa
g
yuinm
nyahyuahתa
ta
burcikin ranta ta ce to yaya na gode, Ubangiji yabar
rumunci ya ce abin ya debo kudi masu kauri ya ba ta
ce duk abin da ta ke bukatga ta ringa yi masa waya
ce, to su kayi sallama su ka tafi.
Ummu murna ta koma ciki dan ita Shema'u ce ba
so ta gani cikin gidan, to gashi an yi sakin taki
afiya, har gida ta je ta fada wa mahaifiyarta ta ja
masa kunne da cewar ta yi shiru da zan ce har iddar
Shema'u ta cika dan yanzu in Alhaji ya ji lallai Nazir
yamaida ta in kuwa Iddar ta ta ci kane suka ji tasan
Shema'u ba ta yarda ta koma.
Wata sabon gani in ji mahaifiyar Nazir da ta fito
same shi a falonta yazo, ya yi murmushi ya durkusa
ja gaida ita ya ce don Allah Hajiya ki ki yi hakuri
ayyuka ne su ke yi min yawa, ai na sani tunda akwai
ikin da zai hana mutum ganin iyayensa Allah dai ya
aimake ni ba kai kadai na haifa ba ya sa ke risinawa
Hajiya ayi hakuri ta ce in ban hakura ba Nazir ya
zanyi da kai. Sun dan jima su na hira ta tsakanin da da
mahaifi can ta ce masa Alhaji fa ya na gida ya kwana
biyu bai fita ba saboda ba ya jin dadi, ya mike cikin
Janzari ya ce bari in je in ganshi, sallama ya yi dakin
nahaifinsa ya na zaune kan dadduma da carbi a
hannunsa ya na ja, ya amsa sallamar ya samu guri ya
zauna ya gaida mahaifinsa ya tambaye shi karfin jiki
ya ce ai na warke, kwanakin da su ka shige ai na ji
gata Nazir ya ce amma Alhaji ba a aika min ba,
mahaifinsa ya ce na yi zaton saboda mu ka sake sabon
49
layi saboda kar mu dame ka saboda kai yanzu Umm
ta fiye maka komai a duniya nan dai ya zauna yana b:
wa mahaifinsa hakuri kan rashin zuwan da ya ke in
su Shema'u da ya ta ya ce su na gaishe su, insh
Allahu gobe ma za ka ga sun zo duba ka.
Shema'u dai ta koma koyarwarta dan ba ta samı
matsala ba, saboda yanzu akwai 'yar kanwar Mamant
Surayya da ta yi candy kafin sakamako ya fito ita ce:
wajenta duk wata damuwa Allah ya dauke mata ita ta
yi kalau ta yi kyau.
Yau da yamma ta na zaune a cikin lambun gidan
kana nan kaya ne a jikinta sun yi mata kyau ta harde
kafarta daya kan daya, ta na karatun jarida, Nazir da
ke can bangaran ya na kallonta cikin sha'awa dan ta yi
bala'in burge shi, ita kuwa ba ta san ya na ciki ba, a
hankali wayarta da ke yashe a gefe ta hau kara, baj
san ko me aka ce ba ta ya ji ta na cewa "Okey-okey,
gani nan zuwa nan da minti talatin." Ya ga ta dauki
abayarta tasa ta saka hijab ba zancen nikaf dan bata
sashi ba ta fita shima ya bita sai ya ji ta na kwallawa
Surayya kira kawo min jakata da mukulun mota, ta
dauko-mata ta shiga mota ta tayar, wani takaici ya kama Nazir wato ma ba za ta fada mishi ga in da zata
ba duk in da taga dama kenan, zata ko nikaf ba ta sa
kasa zata nunawa duniya wai ita kyakkyawa ce kishi
ya kusa sumar da Nazir a nan.
Nazir ya na falon mahaifiyarsa su na hira tunda a
yanzu tunaninsa ya na kan iyayansa saboda ita ma
50
mah
yarsa ba a zaune ta ke ba, yanzu al'amura sun
dsasseta, ta ce Naziru dama wani magani na Kamaka saboda tsarin jiki ya na yi irin na
sana
kaga kana samun daukaka shi ne na ce bari
in gimaka ko zaka amince a ringa kawo maka Tube
ka ringa sha saboda kar in karbo ka ki sha,
shce fa ba dole ba ne, haba Hajiya akwai abin daice in yi in kiyi ai nasan saboda lafiya ta za ki yiayi ta ce to shi kenan in dai kana gari kullum
kala sha ya ce to tare da godiya har kudı ya bata
Wiyar ayi masa addu'a yanzu kullum Nazir sai
Yajeidan su gurin mahaifiyarsa yasha rubutu kuma
Alhedulillah ya soma jin sauyi.
umar yadda ta saba duk yammaci sukan zauna
cilmbu ita da yara suyi hirarrakinsu yau ma
kam kullum ta na zaune ta na karatun littafin
gwara cikin marubuta, ta sake kallon bangon
littaja fili ta ce lallai kuwa kin ci sunanku gwanaye,
Sura da ke gefe ta ce "Anty in kin gama ki ara min
am ni labarin gwanaye ya yi dadi ni dai
marzuciyar nan ta na burge ni, ni ma haka ina son yi
matsaya ina tsoron dankaren wulakancin da aka ce
maruta na da shi, haka dai ake cewa Anty amma ni
dai nyimata text, to ta taba baki amsa gaskiya Anty
sau iya ta taba bani amsa amma nayi mata text
kusasu hamsin shima din barka da shan ruwa ta yi
min re da dan tunasar dani mahimmancin azumi da
kumaddu'o'in da ya kamata in yi su cikin watan
51
Ramadan, to zan yi calling dinta in gwada, ban karas
fadar abin da zan fada ba, na ji an cakumo ni, idanur
su ka tsaya kan wacce ta cakumo ni ba kowa ba
face Ummu na juyo na kalli Surayya na ce maza kan
hannu yara kuyi ciki ta ja hannunsu su ka nu
bangare na, na juyo gare ta na ce madam sake ni an
a sake ki, karuwa, na ce ni din ke din in ban da
karuwa ce kuma kaska ce ya za ayi a saki mace ta
tafiya gidan ubanta, kin zauna kina janye m
hankalin mijina domin nasan malaminki ya ba ki sa
shi yasa kike wannan zaman, Ummu bari ki yi ba
tsoro ko shakkar ki yanzun nan zan yi maganinki da
dama darajar Nazir ki ke ci yanzu kuwa babu wanna
darajar gid akuma da ki ke so in bar shi ai gida tu
kika makara dan ya zama gidana abu mafi sauki
nice ba kya ce son gani daga ke har mijin ki sai
tattara ina ku ina ku ku bar min gida dan yanzu ni
da gida, kar kuma ki sa ke kira na da karuwa, dan k
san kowa ce karuwa, na fi karfin mijinki bare ke de
ko a kafa aka daura min shi na kunce in gudu ina so
in ja kunnenki wannan shi ne farko kuma karshe, d
duk ran da ki ka kara yi min abu makamancin haka
ki raina kanki. Na fisge wuyan riga ta na yi gaba
barta saroro ta na kallona cike da takaici.
** **
Bikin Kabir yazo wanda ya yi daidai da gan
iddar Shema'u ta yi shiri sosai na bikin dan gaba day
52
komai tare da ita aka yi gaskiyha biki kam ya hadu a
wajan dinner ne su ka hadu da wani abokin yayanta
mai suna Najiburrahaman amma Indiya ne dan daga
ni ba sai an fada ma ka ba abin da ya bata mamaki da
ya kasance ya na jin Hausa, kai ka ce jakin Kano ne,
ko da ya ke ya ce ma ta shi haifaffan Kano ne, aiki ya
kawo mahaifinsa, naso in share Najiburrahaman
amma yadda ya ke da naci da yadda ya nuna min so
lokaci kankani sai naji ya gama dani gashi kuma naga
yaya Kabir ya ji dadin haduwarmu.
Bayan kammala biki, na dawo gidan Nazir na
hada nawa ina wa saboda a yanzu na ke da bukatar
iyaye su sani saboda haka na kuduri niyyar komawa
gaban iyayena. Yaya Kabir na fara fadawa kudurina
amma sai ya dakatar da ni in bari su dawo daga honey
moon da za su shi da amaryarsa dan dai babu yadda
zan yi na hakura.
Najiburrahaman ya na kawo min ziyara kai ba ka
ce tun daga Kano ya ke zuwa ba, yarana har sun saba
da shi dan ya ce musu shi ne sabon Abbansu zai kuma
mai da su Kano da zama, dan shima Najiburrahaman
din ya taba aure matarsa Nisha tazo haihuwa ta rasu.
Kusan shekaru hudu da mutuwar ta sai yanzu da Allah
ya hada shi da Shema'u ya ke jin zai iya zaman so da
kauna da ita don da cewa ya ke ya gama zaman
soyayya shi tunda ya rasa Nisha.
Ita kanta Shema ta kamu da son Najiburrahaman
kuma tunda ya ke zuwa ko sau daya ba su taba
53
haduwa da Nazir ba dan sam ba ta ce da Najib gidan
uban yayanta ba ne, ta ce mas agidan wanta ne saboda
haka soyayya su ke yi mai tsafta. Najiburrahaman ya
na kashe mata kudi sosai, daga ita har yaranta yaso tạ
kai shi ga mahaifinta su gana ta ce ya bari har sai
Yaya Kabir ya dawo.
Nazir ya dawo daga Dubai yau ma ya kaiwa
mahaifansa ziyara kamar yadda ya saba su na zaune
dakin mahaifiyarsa ta ba shi rubutu ya sha wanda
dama yanzu ya na sha saboda ta ce masa na tsari ne
akan dukkan lamuransa har turare ta ba shi wanda zai
turara mahaifiyarsa ta ce ban ji dadin rashin
kasancewarka gurin daurin auran Kabiru ba kuma
abin takaicin kowa ya je ban da Ummu wato ka ce har
yanzu zaman nasu babu dadi? Naziru ka ji tsoron
Allah ka tuna fa kowacce amana ce a gare ka, ina jiye
maka tsoron haduwarka da Allah don ni nasan zaman
hakuri yarinyar nan ta ke, ya yi jigum dan ya rasa me
zai ce da mahaifiyarsa, nan dai ta ci gaba da yi masa
nasiha.
A yau Nazir tunda yaje ya kwanta ban da juyi
babu abin da ya ke yi, saboda ya na son ya tuna me
ma ya shiga tsakaninsa'da matarsa yara a yau ji ya ke
kamar gari ba zai waye ba saboda ya na son ganin
matarsa, shi dai yasan sun saba to amma ya rasa
menene ma ya hada su, tsam ya tashi ya nufi
bangarenta ya dade ya na bugu amma ko motsi bai ji
ba, haka dai ya hakura ya koma bangaren Ummu.
54
Yau tun bakwai na safe su ka fice da ta tashi
daga aiki ba ta dawo ba sai ta zarce bikin da wan
babanta ba ta shigo ba sai goma washe gari ma da
wuri ta fita ranar karfe uku ta dawo, fitowarta daga
wanka kenan, wayar Najiburrahaman ta same ta ya na
farfajiyar gidan shigo ta yi ta alfarma ta nufi wajen
masoyinta, gaba daya yaran ta sun zagaye shi kowa da
tsarabarsa, sai da ya sallame su sannan su ka ci gaba
da hira, a nan ta ke sanar dashi dawowar yaya Kabir ta
ce ya na kuma nan Yola saboda haka ya ce ba zai tafi
ba zai je ya kama daki har sai ya yi yadda za su yi a
annan ma ya kira shi a waya ya ce ya jira shi ga shi
nan zuwa, ita Shema ce ta yi masa rakiya zuwa gidan
yayan nata don a can ta bar shi ta dawo gida.
Kabir bai 6oye wa Najib komai ba amma ya се
ya yi hakuri har yanzu ya na nazarin yadda zai
fuskanci mahaifinsa akan maganar ne amma ya zama
dole kafin ya tafi zai ji sahihiyar magana.
Tun La'asar Najiburrahaman su ke tare da Shema
sun kasance masoyan da suke cikin nishadi da kaunar
juna babban burinsu shi ne, Allah ya mallaka musu
junansu a nan ya yi sallar magariba nan ya dauki yarasu ka fito ya yo musu shopping bayan ya ajiye su
Shema ta fito su ka ci gaba da hira sai ga Nazir ya
shigo da motarsa, ya kuwa dallare su ya fito ya shiga
gida ya dade ya na son ganin ta ta ki ma saurarensa ya
shiga ya fito Nur ce ta fito da gudu ta ci karo da
Abbanta kc gudun me kike? Ta ce Abba Anti Surayya
55
ce zata sha min Ice-Cream dina bayan kuma sabon
Abban mu ne ya siya mana, waye sabon Abban ku?
Ga shi can yazo gurin Umman mu ba ka ganshi ba ya
na da kyau ya ce ma duk tafiya zai yi damu in dai
yazo sai ya siyo mana Ice-Cream da sweet.
Ai bai tsaya jin surutun Nur ba ya yi gaba kai
tsaye ya tsaya musu aka ya daka masa tsawa kai kana
da hankali kuwa, kazo gidana wajan matata
mahaukacin ina ne kai dan wacce kasa ne ko ko
mahaukaci ne kai? Duk Nazir ya na magana ne cikin
harshen Nasara mai jan kunne, dan shi ya yi zaton
Najiburrahaman baya jin Hausa. Ya ce haba abokina,
kayi hakuri na shigo maka gida amma saura kiris in
dauke matata in na dauke ta ba kara ganina zaka yi
ba, kai kana shan kwaya ne ka fita tun kafin raina ya
6aci kafin Najib ya ce wani abu shi Nazir ya shake
shi, ai tuni ta yiwa Yaya Kabir waya ga abin da ya ke
faruwa yau naga kishi gurin 'yan maza ai tun kafin su
Kabir su karasa barin gidan shima Nazir ya fice sai a
lokacin tunanin sa ya dawo daidai ya tuno da sakin da
ya yi mata ya ringa godiya ga Allah da Allah ya
taimake shi saki daya ya yi kai tsaye gurin Alhajinsa
ya nufa, bayan sun gaisa bai jira komai ba ya fada
masa ga abin da ya faru ya sake ta amma yanzu shi ya
gane kuransa ya maida matarsa, amma gashi har ta
janyo masa wani mai jan kunne gidan da shi Alhaji
bai dauki magaar da wani mahimmanci ba sai da ya
56
d
ya na dada jadadda maganar da tsananin tashin
hankalin da ya kc ciki.
Dattijon arziki kenan kuma aminan juna gaba
daya abin da ya faru ya ba su mamaki a lokacin can
gidan Nazir din su ka nufa dan aji daga bakin Shema,
jla kuma a lokacin ta yi parking din komai ta zuba
akwati cikin mota don yau sai gidan mahaifinta, sai
taga mota ta shigo wadanda su ka fito daga motar ne
da ta kalle su kawai sai taga mukulin tata motar ya
subuce mahaifinta ya ce ina za ki bakinta ya na
sarkewa ta ce gida nan dai su ka koma falonta dattijan
guda biyu sun so jin ta bakin su amma ganin yadda
kowa ya ke son ya nuna shi ke da gaskiya sai kawai su
ka ce basu da bukatar jin abin da ya hada su su dai a
matsayinsu na iyaycnsu sun jinjinawa Shema'u bisa
iya hakurin da tayi har ta zauna saboda haka Allah ya
yi mata albarka Allah ya sa sauranta su yi koyi da abin
da ta yi Nazir ya yi tsagal ya cc Alhaji ni fa na ce na
maida ita, Shema'u ta ce uh ka maida wa to in ba ka
sani ba ka sani ni tuni na gama idda ta a yanzu ina da
zabi saboda haka ni ina da zabi Alhaji ya yi murmushi
mahaifin Nazir ya ce ke ko mai jan kunnen shi ne
zabin ki dan ya ce wai kin ba wa mai jan kunne damar
zuwar masa zance cikin gida, mahaifinta ya ce ashsha
yaro yaro ne ke ban da sakarci ya za ki janyo masa
bazawari gidansa, ta ce baba ni gani nayi hakan shi ya
dace domin kai da kanka ka ce duk randa Nazir ya
sake ni kar in dawo maka gida in zauna a can har sai
57
na gama idda to ni kuma da na gama idda sai naga
tunda na samu wanda ya ke sona da gaskiya abun da
ya fi dacewa shi ne in yi aure tun da na wuсе
munzalin zama a gabanka kun ga Abbu Nur shi na ke
so ya zame min uba kuma madaurin aurena, tunda
mun zama jini da tsoka, domin ni tuni na maida
amincin iyaycnmu ya zama zumunci shi ne dalilin
kawo Najibburahaman gidan Abbu Nur, dan yanzu ni
ba ni da gidan da ya fi gidan Abbu Nur.
Gaba daya su ka yi shiru da jin kalamanta
mahaifinta ya ce, to yanzu duk mun ji abin da ki ka ce
a matsayina na mahaifinki kuma madaurin aure
Naziru kinga na zama sirikinki ina neman alfarmar
ban da tuna baya kiyi hakuri a yau din nan mu mayar
muku da aurcnku ki zauna ki rike 'ya'yankı shi ya fi
miki alheri amma ya za ki auri wanda yaranku ba da
ya kasarku ba daya ba ina so kiyi tunani, kuka tasa ta
ce baba ni kadai nasan irin abin da Abbu Nur ya ke
min shi da matarsa ni kadai na kunshi bakin cikin
sakin wulakancin da ya yi min, daga ni sai dan uwana
Kabir, baba ku tausaya min domin in kun maida auren
mu irin zaman za'ayi ya na bin umarnin matarsa ku
kyale ni in auri zabina tun da Najiburrahaman
Musulmi ne amma in diya ne kuma haifaffan Nigeria
ne a jahar Kano dan in ba kalarsa ka gani ba to in ya
na hausa ba ka ce daga bakinsa ta ke fitowa ba ni kam
baba na yafewa Ummu Nazir baban Nazir ya ce tunda
Musulmi ne to zamu je mu yi bincikc har can garin
58
Kano din ba za ki koma in da ba asan mutuncinki ba
ban goyi bayanki koma ba nima ban san abin ba ya
kai ya iya budar baki ya sake ki ba, baba ya ce haba
aminina ba za ayi haka mace da miji sai Allah duk
wani tone-tone mu bar shi a matsayinmu na wadanda
su ka isa da ke zamu mayar muku autenku saboda
haka ki yanke sadaki nawa kika yanka hawaye ya
zubo mata Nazir ya gurfana gabanta ya na ba ta
hakuri tare da daukar mata alkawarin dole ne rayuwar
gidansu ta sake ba za ayi irin zaman da akayi da ba,
mahaifin Nazir ne ya ce sai yanzu kasan haka ba zata
koma ba kaje ka zauna da matarka, nan ya juya ga
mahaifinsa ya na ba shi hakuri har mahaifin Shema na
taya shi to anan ya ce ya yi zai yanke sadaki take ya
yanka musu sadakin yarsa miliyan daya mahaifin
Shema'u ya ce to ai 'yar taka ba budurwa ba ce
sadakin ya yi yawa a rage mu babu ragi kar fa ka
manta akwai mai jan kune ya na kusa shi ko miliyan
biyu aka ce zai biya Nazir ya miki shi ke nan zai biya
haka ta ke ya rubuta cek na miliyan da ya ya bar nan
fa aka shiga yiwa yayan Nazir da 'yan uwansa waya
wadanda su ke manya ne ma'ana masu aure aka yiwa
yayan Shema'u Kabir shi ma ya zo abunka da 'yan
gidan yawa tuni gidan ya dunke da mutane karar
motocin da suke shigowa su suka jawo hankalin
Ummu har tasan lallai akwai abin da ya ke faruwa in
gajarce muku labari cikin wannan dare aka maida aure
Shema'u da Nazir akan sadaki naira miliyan daya.
59
A gaskiya kowa ya ji labarin abin da ya faru ya
kan tsuma shi da ba shi mamaki, Ummu kuwa ta riga
ta haukace lokacin da Anas ya sanar da ita dole in ce
ta haukace tunda zage shi ta yi tas kishi ya mantar da
ita cewa uwa daya uba daya suke da mijinta, haka
uwarsa da ta ke zagi uwa daya uba daya suke da tata
mahaifiyar, ko da ya ke shima dan ya kunsa mata
bakin ciki shi ya sa ya shiga 6angarenta. Koda ya ke
dama jikinta ya bata wani abu na faruwa amma sam
bata kawo zancen maida auransu ba dan tuni
bokayenta su ka sanar da ita Shema'u da Nazir sun
gama zaman aure, shi kansa Anas rabon sa da gidan
Nazir tun randa su ka yi sa'insa sai yanzu da Alhajinsu
ya ce maza yazo ya na gidan Nazir shi yasa ma yazo
dan shi ya ce sam ya daina zuwa gidan dan uwan nasa
matukar bai canja tsarin zamantakewarsa da iyalinsa
ba, yadda ta kasance tsakanin Ummu da Anas kuwa
shiga ya yi da fararsa ta kuma tare shi dan dama so ta
ke wani ya shigo dan tasan me ke faruwa, Hajiya
Ummu ya fada ya na dariya ta ce mai shirin zuwa dai,
ya ce ai niyya ce ba ki yi ba dan da tuni kinje kin kai
wasu ma, ta ce haka ne kasan shi zuwa Makka kira ne
na Allah, lokaci dai Anas in da rabo sai kaga na je, af
ta fada yau taron me kuke ne naga gidan namu a cike
ko lafiya? Taron alheri ne kinsan duk mugun nufin
mutum ya kan kema masa yau dai Allah ya nufa mun
maida auren ivazir da Shema'u akan sadaki naira
miliyan daya, tama manta da wanda take magana tun
60
ta dan na wan mahaukacin zagi ta ce ba a isa ba ni
Ummu babu wanda ya isa ya kawo min wargi ai
Shema'u ta gama zaman gidan nan ai dama kai Anas
babu mara mutunci kamarka zan dai daita ka, ke wai
da me kike ta kama ne ita fa duniya duk in da ka
dauke ta haka ta ke zuwar maka ina ba ki shawara ki
bi ta a sannu amma wani zafin kanki babu in da zai
kai ki, bari in fada muku duk wanda ke da hannu kan
mayar da auran nan sai naga bayansa walau mace ko
namiji ni ba zan bari in wulakanta ba, ko wacecе
munafukar da ta maida auren zan ga bayanta ne ya ce
wai ke wa kike nufi ne ta ce tsohuwarka, ya kuwa
sauke mata mari a fuska nan ta cakume shi ta na ta
antayawa iyayensa zagi har sai da aka shigo aka raba
su.
Duk da cewa Shema'u ba ta da burin da ya wuce
ace sun daidaita da Nazir to amma ta yi rabuwarta da
Dr. Najiburrahaman Ahmad Kazi tana kuma
tausayawa irin halin da zai shiga idan wannan labari
ya same shi a kuma 6angare guda ta na jinjina wa
zafin kishi irin na Nazir, haka ya shigo ya tarar da ita
gaba daya yara sun yi bacci sai ita wacce komai ya
kunce mata; sallamarsa ita ta tsinka tunaninsa tunda ta
amsa sallamar bata sake biyawa ta kansa ba, ya ce ina
son magana da ke ta kadai ta ce babu lokaci ya се
saboda me? Ba ni da bukatar sake hurda da kai kina
sane da cewar ke matata ce, kuma kinsan hukuncin
yin haka a Musulunce, ta ce na sani mana tun kafin
61
hadin aurcnmu na farko kaga ba na bukatar tuni, ya
dan yi dariya ya ce yanzu kc amarya ce ba kya laifi
taja wani dogon tsaki ta ce ta nuna masa hanya dan
Allah Abbu Nur ka yi waje yanzu kwakwalwata da
zuciyata suna bukatar hutu tun da ka riga ka hada min
zafi, au kora ta kike ai ni a nan zan kwana ta rangada
masa harara ba tare da ta