zan żarce"
Cikin shegantaka Tanimu ya ce,
"Ai tuban tafi-da-gidanka zamu dinga yi,
muna aikinmu muna tuba, Allah sa su ma masu
zuwa wajen namu su dinga zuwa tafe da
tubansu"
Cikin sati daya sana'ar tasu ta shahara,
Tanimu na da ido a sanin mata da 'yan siyasa
kasancewarsa dan bangar siyasar da ya tuba ya
fada bokanci, don haka shi ne mai kawo musu
mutane, mata da Alhazai, 'yan siyasa da 'yan
kasuwa, su ma a junansu duk wanda ya zo ya
sha basaja, aka sace imaninsa in ya tafi sai ya
fada wa amininsa wani shahararren boka ya
bayyana, shi ma in yazo sai ya fada wa nasa
Aminin ta haka tafiyarsu ta fara nisa.
Tun bayan kwana hudu da auren Salma da
Adamu aka kamala duk gyaran da za'a yi wa
138 Maimuna Idris Sahi Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
gida, aka yi jere aka kuma zuba kayan kanti
aka kai wa Adamu Salma kwana goma sha
daya da auren.
Ranar da za'a kai ta da safen ne Alh. ya
shammace shi ya biyo shi gida bayan sallar
asuba, kasancewar kullum daga ya dawo sallar
asuba yake shiryawa ya fice, ba za'a kara
ganinsa a gidan ba sai bayan sallar isha,
wataran ma har karfe goma yana kai wa.
Babu ko sallama Alh. ya bankada masa
labule ya bi bayansa.
Suka yi cirko-cirko a tsakiyar dakin suna
kallon juna, fuskar Adamu da fishi, fuskar Alh.
na nuna halin ko in kula.
Alh. ya sanya hannu a aljihu ya ciro
mukullai ya mika wa Adamu,
"Don Allah ka taimaka idan ka dawo ka
zarce gidanka, yau za a kai maka matarka"
Adamu ya mika hannu saroro ya amshi
makullan, ba tare da ya tanka ba, ya dinga
motsa baki kamar yanà so ya gode wata
zuciyar na kwabarsa cewa bai kamata a cuce
ka kuma ka yi wa macucin godiya ba, da haka
ya biyewa zuciyar ya ki godewa, kuma ya ki
139 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
tankawa har Alh. ya gaji da jiran cewarsa ya
kada kai ya juya ya fita cikin kada kai da
murmushin mamaki.
Adamu ma ya dauke ido daga kallon
wucewarsa zuwa kallon mukullan hannunsa,
wasu irin abubuwa na zagaya kansa a guje,
suna raya masa cewa, ba wai rayuwarsa се
kawai take shirin canjawa ba, shi kansa Adamu
ake son a canja.
Wai shi ne da ya sha mafarkan bacci da na
ido biyu a auren mace daya kacal wato Husńa,
shi ne kuma yau da auren wata macen wai ita
Salma? Abin sa kuka amma ba hawaye.
Bai bari wata damuwa ta ci karfinsa ba ya
shirya ya fice harkokinsa. Bai sanar wa
Salmanu komai game da tarewarsa a gidansa:
da sabuwar amarya ba, sai da ya tashi tafiya
karfe tara da rabi na dare,
"Au! Kai yau fa zaka raka ni siyen baki"
Ya fada wa Salmanu cikin yake da
kokarin hadiye damuwa.
Salmanu ma ya dabe shi cikin mamakin da
yake son shanyewa,
140 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Wai da gaske kake mantawa ka yi ko
kuma tsabar basarwa се?"
Adamu ya hada da dariyar yake,
"Oho! Ni ma ban san takamaimai a ciki
ba"
Salmanu ya kame hannu ya rungume a
kirji yana bin sa da kallo,
"To Allah kiyaye hanya, Allah ba da
zuriya mai kyau"
Adamu ya yi saurin dubarsa saroro,
"Au wai ba zaka raka ni ba, haka zan tafi
zikau ni kadai?"
Salmanu yayi dariyar karfin hali,
"Kai kadai zaka tafi mana, ka manta kai
kadai Salma ke son gani, ko ka manta
sharuddan da ta gindaya maka cewa kar a sake
na zo mata gida?"
Adamu ya dinga gyada kai alamar tunawa,
وو" Haka ne na tuna'
Salmanu ya ji takaicin goyon bayan da
Salma ta samo a wajen Adamu, dubi dai yayi
masa gatse amma bai damu ba ya mayar gaske
saboda umarnin Salma ne.
141 Maimuna Idris Sani Beli
1 NA SHIGA ALJANNA...2
Amma duk da haka Salmanu bai nuna a
fuska ba, sai ya cigaba da dariya yana cewa,
"Idan gidan Salma ya zama nasu su biyu
kila a gan ni, in dai zan iya zuwa wajen Husna
ba wajenta ba"
Nan da nan fuskar Adamu ta rakito
walwala, amma dai bai tanka ba..
Salmanu bai damu ba ya cigaba da
Magana,
"Amma idan ba ka sami damar auren
Husna ba, to har mu kare rayuwarmu a idon
danginka da Salma zamu cigaba da nuna dama
mun rabu"
Adamu ya banka masa harara tamkar
idonsa zai fado sannan yayi gaba yana mita,
"Ka kwana biyu ba ka zage nib a dama,
yau in ka yi min muguwar addu'a bà laifi, to in
Allah ya ba ni Husna ka hana mana
Ba tare da sallama ba ya fice daga dakin.
Salmanu ya bishi da kallo cikin tausayi
tare da kara kullatar Salma.
"Allah ya tsine miki Salma"
Ya fada a fili kuma har cikin zuciyarsa so
yake Allah ya amshi addu'arsa.
142 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Kamar kullum duk wani abu da ya
danganci Salma zuciyarsa ba ta bashi
muhawara bare ya tantance ya zaba, kai tsaye
daga can saman zuciyar tasa wani ke bashi zabi
ya aiwatar bisa dole.
Yau ma ya so ya ji bijrewa da nuna wa
Salma iyakarta, amma ya ji wancan karfin na
son matsa masa murnar zama angon da yake
tafiya ga amaryarsa, hakan kuwa ya je mata har
da siyayyar kaji da kayan jika makoshi. Ya
dinga nuna mata doki da zumudi tamkar dama
ita kadai ce sauran burinsa a duniya ya kuma
samu.
"Ban san kana sona haka ba Adamu"
Da kalmomin da ta dinga zolayarsa da su
kenan, shi kuma yana amsawa tsakaninsa da
Allah,
"Yanzu kin sani Salma, ina son ki fiye da
son kowa a duniya"
In ya fadi haka Salma na jin wani
munafikin hawaye na kurdo mata ta samu ta
goge abinta, abinda take so kenan wato
Adamu, ta kuma samu, in ba shi kadai ne
burinta a duniya ba tana jin dai ya fi rabi.
143 Maimuna Idris Sani Beli.
1
NA SHIGA ALJANNA...2
Cikin sati biyu dukkansu rayuwarsu ta
canja, Salma ta mamaye zuciyar Adamu tsab,
duk wata mace a waje kallon Bahuwa yake
mata, bata da kyau ko bata da kwalliya ko ma
gaba daya sunan mata kawai take amsawa.
Salmansa ce kadai mace, ita ce kuma kawai
idan an so ba a fadi ba.
Duk abinda Salma ke so shi yake so,
wanda kuwa ta nuna bata so nan take yake jin
tsanarsa, saboda haka ya zama tamkar da gaske
sabon Adamu aka sake fil! Ba wancan mai
tsanar salma ba kuma ba wancan mai son
Husna a kirji ba.
Salmanu kansa ya fahimci haka, amma dai
ya shanye ba ya tanka masa maganar Salma, ko
shi ya kawo masa ma sai ya tankwabe shi da
cewa,
"Yanzu Salma iyalinka ce, bai kamata mu
dinga hirarta ba"
Da wannan hujjar suka dauke hirar Salma
a tsakaninsu, iyakaci in sun hadu su yi abinda
ya hada su su watse.
Sai dai manta Husna da Adamu yayi ba
karamin daga wa Salmanu hankali yake ba,
144 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA..2
musamman in ya tuna labarin da Adamu ya ba
shi na yadda suka yi rabuwar karsheda
Husnan, da alwashin day a ci mata na aurenta
nan da wata biyu tun a ranar.
ps
nsWannan ya sa ya cigaba da sake-saken ta
inda zai bullowa wannan bahagon lamarin, har
ya fara jin cewa a wanna gabarazaie yanke
danye hukuncin da: Zaijnunaa wai Salma
iyawarsa.
B siSanaar bokanci taincigaba hdasakawo
imanyan kudi, don haka Adamunbaii yingigin
barinta ya zauna a shago ba, kawai sai yà neii
yaro ya dora shi jira, shi kuma ya cigaba da
gashi prose sangu a Citapa ( Kows is ase
ваAbinda ma ya takaice shi shi ne, Salmanu
ba ya sakar masa kudi yayi yadda yake so ko
$dan farantawa Salma raiinemset edob sist
ei BinZasuyraba kudin rumi-rumi su uku bayan
Sun ware na sallamar yaran da ke lyi musu
hidima da kuma na siyayyar kayan aiki, amma
kawai sai Salmanu ya daka wa na Adamu
ils 145 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
wawaso, ya sunna masa abinda bai taka kara ya
karya ba, ya ce wai zubin adashi suke, kuma
wai kantinsa ya isa ciyar da Salma dai ba wata
ba.
Adamu ba ya son wannan dabi'ar, amma
dayake ba ya zargin Salmanu da cutar kudi sai
yake shanyewa, yana da tabbacin ko ba dade
ko ba jima sai ya fito masa da kudinsa.
Sati daya, biyu, uku, hudu, Husna bata ga
Adamu ba, tun tana basarwa musamman daidai
lokacin da ta ji labarin ya tare da amaryarsa a
unguwar Dorayi, ta ci kuka ta ci ciwon ranta ta
maze ta koma ta cigaba da zaman jiran ya
waiwaye ta tunda wata biyu ya dibar wa kansa
na aurenta, har aka kusa wata daya da rabi ta
fara debe tsammani, juriyarta kuma ta sare. Ta
cigaba da damuwa ta cigaba da kuka kuma ta
cigaba da ramewa tare da lissafin ta inda zata bullowa wannan mugun ciwo day a sarke ta.
146 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Rannan dai da ta ji zuciyarta na neman
bugawa kawai sai ta wanki kafa ta tafi gidan
Kawarta Amina domin neman mafita.
Ta sami Amina da makociyarta Jamila
suna hira cikin farin ciki.
Amina na ganin Husna ta hau salati da
sallallami,
"Wallahi yanzu nake zancenki Husna, ai
kawi ki zo mu fasa mu ma mu shallo Adamu"
Husna ta zauna kan kujera jagwaf tana bin
su da kallon rashin fahimta,
Amina ta shiga yi mata bayani tana nuna
Jamila,
"Kin tuna ranar da jamila ke tatsuniyar son
mai gidanta ya sai mata mota yana cewa wai
bata da hankali?"
Husna na dariyar yake ta ce,
"Na tuna, yanzu zai siya ne don ta yi
hankalin?"
Suka kwashe da dariya su duka ukun.
Jamila ta mika wa Amina hannu suka tafa
sannan ta dubi Husna tana kada mata mukullin
mota,
147 Maimuna Idris Sani Beli
1
NA SHIGA ALJANNA...2
"Tun yaushe na yi hankali, Surajo ya ji
wuya jiyan nan sai ga sabuwar mota ya samfa
min"
Husna ta zamo daga kujera tana zaro ido
cikin mamaki,
"Da gaske? To duka kika fara ne ya gane
in bai sai motar ba ba zaki warke ki bar dukan
ba?"
Suka sake tuntsirewa da dariya.
Jamila ta ce,
"Wanda ya fi shi karfi na sa yayi masa
mahangurbа"
Har yanzu Husna na cikin dokin jin labari,
ta ce,
"Don Allah ku fada min ku bar wana ni"
Amina ta hau yi mata bayani.
"Wallahi wani sabon boka aka samu mai
aiki kamar yanka wuka, saboda tsabar son
mota na Jamila sai da ta dangane da wajensa,
ba a yi sati biyu ba kuwa kin ga har ta yi
motar"
Husna ta shiga gyada kai cikin mamaki da
sha'awa,
148 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Kai! Ku dama akwai malaman Allah da
gaske a duniyar nan?"
Jamila ta kada kai,
"Wallahi ni ma abinda na yi ta cewa kenan
Husna, kawai kasada na yi na je, amma saj ka
yi ta zuwa wajen wasu asirin sai ki ga kamar an
shuka dusa"
"Wallahi tallahi"
In ji Amina, Sannan ta dubi Husna ta zarce
da cewa,
"Wai gobe zata je yi wa bokan godiya, shi
ne na ce me zai hana mu bi ta muma mu kai
tamu bukatar? Ke ki kai Adamu, ni kuma zan
kai Kamąlu a kama min shi a hannu, wannan
shegen kallon bal din nasa pa dare a hana shi,
don ni in akwai abinda na tsana a duniya ba zai
wuce kallon bal din ba"
Husna ta ji wani dum! Kamar abin bai kai
zafin haka ba, duk da ta san son Adamu ba
sanyi ne da shi a zuciyarta ha.
"Kar ki ji wani dar Husna, duniya sai da
kundumbala, ki daure ki basar ki nemi cikar
burinki, Salman banza da zata hana ki samin
abinda kike so?"
149 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA..2
Amina ta karfafa mata gwiwa da wannan
zantukan
Sai kawai ta mika wuya.
"A wane kauyen bokan yake?"
Ta tambaya.
Jamila ce ta amsa mata
"Nan nan -Zawaciki yake, hanyar
Panshekaга"
A sanyaye Husna ta се,
"To Allah ya kai mu, zan je. Karfe nawa
zamu tafi?"
Amina ta dubi Jamila.
"A motarki fa za mu, saboda haka ki zaba
mana lokaci"
Kai tsaye Jamila ta amsa,
"Mu je da la'asar"
دو" Allah ya kai mu"
Husna ta amsa a sanyaye.
Da la'asariyyar ranar yau su Adamu na
sanya ran zuwan wani gagarumin dan siyasa
mai son tsayawa takarar dan majalisar taraiya.
150 Maimuna Idris Sani.Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Ku kula da kyau fa! Yau muna bukatar
takatsantsan don kar mu yi abinda kwabarmu
zata yi ruwa, kudi muke so.. kun gane?"
In ji Oga Salmanu lokacin da suka sami
wayar cewa yammar yau ko ta gobe Honorabul
zai zo.
"Wane sirrin damfarar zamu gwada
masa?"
Adamu ya tambaya.
Salmanu ya dan yi shiru alamar tunani.
Karaf Tanimu ya ce,
"A yi masa na alkalamin nan, na ga yana
dan rudar da kwanya"
Salmanu ya bigi kafadar Tanimu,
"Yauwa! Ka kawe shawara mai kyau, a
nemo, alkaluma a fente"
Adamu ya tashi da sauri ya shige cikin
zuwa taskar ajiyarsu ya bar Salmar da
Tanimu, Tanimun na yi wa Boka Salmänu
bayanin tarihin Honorabul, nasarorinsa,
faduwarsa da kuma abokan adawarsa.
Adamu ya jima sannan ya fito,
"Akwai alkaluma, amma babu kusoshi".
151 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Salmanu da Tanimu suka dafe kai saboda
jimami, kasancewar ba a samun kusar kusa da
su har sai sun hau Mashin sun je Sabon titi.
Adamu bai shiga cikin jamamin ba, kawai
sai ya sa kai ya fice yana cewa,
"Bari na samo ta yanzun nan na dawo"
Salmanu na kiransa bai saurare shi ba.
Wannan dalilin ya hana Adamu da Husna
haduwa a wajen da dukkansu ba zasu so ganin
juna ba.
Tanimu ya shige ciki domin zama kujerar
Adamu ko da zatą kama ayi muryar aljanu.
Salmanu. kuma ya zauna a kujerarsa ta
babban Boka.
Kasancewar sun saka dokar ba a shiga
mutum biyu, Jamila ce ta fara shiga, ta yi
godiyarta ta kuma bayar da dubu goma na goro
ta fito.
Husna ce ta biyu. Ta shiga da alamun
tsoro da rashin sabo, kafarta sai rawa take jiri
kuma na kwasarta, dole ta zube a kasa ba tare
da ta karasa kan buzun da aka tanadawa masu
ziyara ba.
152 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Yadda take jin dukan zuciya Salmanu ya ji fiye da haka na ganin Husna a gabansa a
matsayinsa na boka ita kuma a matsayinta na
mai bukata a wajensa. To wacce irin bukata?
Abinda ya fi damunsa da sa shi faduwar gaba
kenan sai kuma fargabar kar Adamu ya dawo
ya tarar da ita.
Da sauri ya fara shirya ta inda zai Burma
ta.
Ko Salmanu bai ci wani Make up ba da
wahala Husna ta gane shi a yadda ta yi kasa da
kai tana jin kamar kasa ta dare ta shige. Ba sai
wani ya bude baki ya fada mata ba, ita da kanta
tana jin ta yi abin kunya, wato zuwa gurin boka
a kan saurayi.
Fahimtar hakan da Salmanu yayi ya bashi
tasa nutsuwar ta shirya yadda zai shammatota.
"Kin zo akan maganar saurayinki Adamu
ne?"
Da sauri ta dago kai ta dube shi saboda
mamaki, amma kamar an cije ta, da sauri ta yi
kasa da kai cike da jin nadamar kallonsa, to
mutumin da ba ka kalle shi ba ma shi ya kallo
abinda ke faruwa a duniyarka, ina ga ka kalle
153 Maimuna Idris Sani Beli
行
NA SHIGA ALJANNA...2
shi? Ta dai cigaba da gyada masa kai alamar
'Eh"
mata,
Ya dan shaki iska sannan a kasaice ya се
"Ba ya ce ki jira shi nan da wata biyu ba?
Ai yana can yana miki tanadi Hajiya”
Husna ta ji wani yakini da karfin gwiwa
ya dake ta, cikin rawar baki ta amsa,
"Ai wata biyun aure yake nufi, dauke
kafarsa gare ni na nuna rashin damuwarsa da ni
Malam, ni kuma ji nake ba zan iya rayuwar da
babu shi ba, don Allah ka taimake ni..."
Ta wuce da goge kwalla.
Ta yi shiru, Salmanu yayi shiru saboda
rashin abin fada.
Ita ta sake Magana cikin hawaye,
"Ina zargin ma ni asiri ya yi min, ban san
ana son mutum irin haka ba, Malam da tuni na
cire shi daga sabga ta wallahi"
Tausayinta ya kara damun Salmanu, ya
yarda Adamu ya cuci Husna, shi ya dinga
zazzafar addu'a kan soyayyarta da samunta,
gashi Allah ya amsa masa shi kuma ya juya
mata baya ya bar ta da wahala.
154 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Dole dai ya kakaro abinda zai karfafa
mata gwiwa lokacin da ya janyo kasko ya fara
yafa turare.
"Ki kwantar da hankalinki ba zai wuce
watanni biyun da ya dibar miki ba, zai zo ya
baki mamaki, ni na yi miki alkawarin sai kin
juya Adamu a tafin hannunki, sai kuma ya
ninka miki son da kike masa, amma ba wani
asiri da yayi miki.
Husna ta sake jin wata nutsuwa a
zuciyarta, ta fara godiya ba kakkautawa.
Tamkar Salmanu ya saki fitsari a wajen
lokacin day a ji tsayuwar mashin din Tanimu
da Adamu ya fita da shi a harabar gidan gonar,
ya tabbatar kuma hanyar da zai biyo ko inda
zai labe dole wadda `zai iya ganin Husna ce.
Da sauri ya mike daga. zaune ya shige
cikin dakin yana cewa,
"Ina zuwa, bari na kawo miki wani turare
da zaki zuba a cikin lallen kunshi"
Bai jira amsarta ba ya shige.
Ya yayimo Tanimu da ke lafe a duhu da
tiyo a baki yana jiran alamar da zai saki muryar
aljanu,
155 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Maza je ka ka tare min Adamu kar ya
shigo gidan nan, bi ta baya?"
Tanimu ya tsaya yana radar neman ba'asi
amma sai Salmanu ya tunkuda shi sai da ya
kusa kifawa, dole yana tashi bai nemi wani
ba'asin ba ya fice ta kofar bayan, amma tuni
Adamu ya kafe mashin cikin zafin nama ya
tunkari masaukin bakin da suke jiran shiga
wajen boka Salmanu.
Amina da Jamila na zaune suna dako,
kuma yana wuce su Husna zai tarar gaban
Boka Salmanu.
A nan zan dakata sai mun hadu a kashi na
uku.
Taku Maimuna Beli.
Ga kadan daga littafina mai zuwa nan ba da jimawa ba.
156 Maimuna Idris Sani Beli.
NA SHIGA ALJANNA...2
RIGAR SILIKI...
"Gwajin HIV?"
Mujahid ya jaddada cikin kallon likita da
haushi da kuma mamaki.
Likita ya kada kai yana tsura masa ido
cikin tabbatarwa da nuna babu fa canji.
99 "Haka na ce
Mujahid ya cakumi wuyansa kamar zai
gwara kansa da bango, amma sai ya sake shi
cikin huci ya shi hargagi,
"Haka ka ce din addini ne, ko fadar Allah
ce da ba'a gogewa?
Likita ya shiga gyara wuyar rigarsa da
Mujahid ya cukwikuya, fuskarsa na son nuna
hakuri da shanye damuwa, ya dubi Mujahid da
kyau ya ce,
"Abinda ka yi bai yi maka kyau a
zamowarka lauya ba, yanzu in na tafi neman
hakki bisa wannan cakumar da ka yi min, me
kake tsammanin zai biyo baya... a kan aikina
kake cin zarafina?"
Mujahid ya tare cikin hargagi,
"Komai ma ya biyo bayan mana, ka tafi
kotun duniya in ka so. Ban da kai dan iska ne,
157 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
matar auren zaka kawo wa maganar gwajin
HIV? In zargin hakan ne me yasa ba zaka ce ni
mijinta zaka gwada ba? In dai ba shirin tozarta
min iyali dama ka yi ba"
Likita ya dinga duban Mujahida cikin
takaici, kawai sai ya watsa masa sakamakon
gwajin HIV din da suka yi wa matarsa Binta.
"Gashi nan, ai yanzu ma bata baci ba, in
ka gama duba wannan kana iya zuwa Lab kai
ma mu gwada ka"
******
Jikin Mujahid a salube ya shiga dakin da
Binta ke kwance. Bai tarar da Salima ba sai
Binta kawai zaune kan gado ta kwanta jikin
filon da ta jingina da bango.
Fuskarta nan nuna farfadowa daga cuta,
idanunta sun yi zuru-zuru, sai dai fa ko kadan
babu wani annuri a tare da ita wanda zai sa a
zaci tana cikin tashin hankali ko kuma nadama,
kallon iskar da ta saba wa Mujahid da shi ta
karbe shi yau ma.
Shi yau tasa fuskar babu walwalar da ya
saba tarenta da ita duk irin yadda ta kai ga bori,
158 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
hasalima bata taba ganinshi cikin 6acin rai irin
na yau ba tun saninta da shi, amma a hakan ta
debe shi ta watsar.
Ya ja kujerar gaban gadon ya zauna yana
mika mata takardun da likita ya watsa masa
cikin kallon fuskarta kai tsaye.
A wulakance ta karbi takardar ba tare da
ta duba ba ta yasar gefe, kuma cikin şhan
kamshi ta dube shi da kyau ta ce,
"Ni ya fara kawo wa na gani kafin ya
baka"
Sai ya sake dubanta cike da mamaki, ya
се,
"Kin kuma duba takardar kin ga rainin
hankalin da take dauke da shi?"
Ta sake watsar da kai gefe tana cona baki,
"Na gani, ai ba rainin hankali ba ne, iyakar
gaskiyar kenan"
Yanzu duban mahaukaciya yake mata.
Dan ta nuna masa da hankalinta ta juye ta
dubi kwayar idonsa fes! Ta ce,
"To wai kai meye na tashin hankali don an
ce ina dauke da cutar kanjamau? Ko ka manta
tuni ka ci alwashin ko yaya zan kasance kana
159. Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA.,.2
so? Ai baka zabi in na zo da kanjamau baka so
ba, in kuma zaka zaba yanzu ma bata 6aci ba"
Mujahid ya jima da hankalinsa tsakanin
karya da gaskiya a tunani da hasashe, sai can
ya mike cikin nuna yakini da kumaji ya ce,
"Na tuna an yi hakan, ban zabi kanjamau
ba, amma yanzu na zaba... nan gaba ma in
zaki zo da abinda yafi kanjamau ke da su duk
ina so... kar ki damu, ki ji sauki ki zo mu
koma gida mu cigaba da jinya... in ma lahira
kika tafi zan nade kafar wando na bi ki"
Rigar Siliki...!!!
Sadaukarwa ga Mujahid Muktar Misau.
160 Maimuna Idris Sani Be
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels