Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
Na hadu da masifa tun dazu amma kana kwance wai kana bacci?" Salmanu ya cigaba da hadiye dariyar da ke neman kashe shi, cikin hanzari ya karasa wajen Adamu yana marairaice murya, "Bacci ne mai nauyi ya dauke ni Adamu, Barayi ne suka shigo? "Uban barayi ne suka shigo, zo ka daga ni 83 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Taga-taga Salmanu ya daga Adamu ya ja shi bango ya jinginar, har wannan lokacin idon Adamu yana runtse yana ta faman nishi. Salmanu ya zauna a gabansa yana dubansa da fuskar tausayi, murya cike da jimami ya ce, "Wai me ya faru, yaya na ga fuskarka a kumbure? Kai duk jikinka ya yi suntum wani gurin har da jinni, mun shiga aljanna Adamu me ya same ka? Bude idonka mana" Adamu ya soma neman barkewa da kuka yana cewa, "A'a fara duba min ya tafi?" Salmanu ya ce, "Ya tafi? Waye ya tafi" Adamu yа сe, "Aljanin da na kira, daga kai ka dube shi gashi nan akanka da rafkeken kansa" Salmanu ya shiga waige-waige kamar gaske, sannan ya dawo da ganinsa ga Adamu, "Ban ga komai ba Adamu, ko dai mafarki kake?" Adamu ya barke da kukan da yake son yi tun dazu, 84 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 "Ni kadai nake ganinsa kenan, gashi nan kuma ina ganin inuwarsa" Salmanu ya ci laya, "Wallahi ba komai Adamu, ka daure ka bude idonka" "To ka roke shi ya tafi" Salmanu ya shiga hurwa, "Bawan Allah kai kake ganina ba ni nake ganinka ba, Adamu ya kira ka shi ma yana neman alfarmar ka bace, in kudi ne ya fasa nema ka tafi da abinka" Ya katse maganarsa ya juyo ga Adamu ya ce, "Ko Adamu?" Cikin rawar jiki Adamu ya kada kai ya ce, "Eh wallahi, ya bar ni ma da bante" "To ka ji ta bakinsa Bawan Allah" In ji Salmanu yana gintse dariya. Can kuma sai ya ce, "Bude idonka Adamu, ina jin ya tafi, na jiyo wani huci" Adamu bai iya bude idon kai tsaye ba sai da ya kankame Salmanu yana ta faman karatun ayatul kursiyyu sannan ya bude idon yana 85 Malmuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 zazzarewa cikin bin dakin da kallo a tsorace, sannan kamar zautacce ya hau sambatu yana tambayar Salmanu, sy nitands2 "Yanzu ashe da gaské baka gan shi ba Salmanu?" "Ban gan shi ba Adamu aon ак оТ "Ta daidai nan ya faso Salmanulds2 Yana nuna wa Salmańu daidai gurin da ya tsaya, sannan ya cigaba da sambatunsasanttаg "Kamar saukar aradusnauji dirarsasYiff! Dogo tokarere da shi ya kusa tarar da rufin kwanon nan, kai ina jin ma kansa yana wajen kwanon, ko da yake nayi arba da kansa sinke da farin rawani...." "TumsbA О 9 Кa ce ka sha kalloA Dii TEws ahliD Salmanu ya tare shi yana son fitar da dariyarsaisILA neWad seniled t il вя оТ" n Adamu ya cigaba yda numfarfashi yana cigaba da sambatu, 00 BY IAE so En Nasha kallo ko na sha wahala Salmanu? Na ci bakar wuya na ci dukan aljan yau na sha bulalarsa sai ka ce shi ne walakiri, mutůwa се kawai ban yi ba Salmanu Kila ma na mutun ha dawohobi BY ЕДИВИ 86 Malmuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 A wannan gabar Salmanu ya sami sararin sakin ragamar dariyarsa iyakar karfinsa. "To kuma jaka nawa ya baka? Na zaci ai duk bulala daya a matsayin wasu makudan miliyoyi take" Adamu ya dauke wuta dif! Sai can ya nisa ya dago sosai ya dubi Salmanu, "Ai da kai muka je wajen Malam ko? Don Allah ka ji sharadin aljanin nan zai dake ni a wajensa?" Salmanu ya kanne, "Wallahi ban ji ba kam, amma ko baka yi daidai ba ne?" Adamu ya sake rafkewa, "Wallahi iyakar iyawata na kiyaye sharudan da ya ba ni, kuma in da na san da duka ba zan taba karba ba" Salmanu ya sake kannewa, "Shiyasa ai nace kila kuskure ka yi baka san ka yi ba" A tunzure Adamu ya се, "To tsakani da Allah ni dai ya zalunce ni, Allah ya isa ban yafe ba, kuma na dauke masa. 87 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Kafata wallahi ko karin bayani ba zan koma in ラクラク masa ba tunda abin nasa mugunta ne "Amin" Salmanu ya fada a gajarce, yayin da wani farin ciki ke cika zuciyarsa. Wasa-wasa sai da Adamu yayi sati yana jinyar dukan da ya sha wajen aljanninsa ba tare da ya leka gidansu ba, yana kwance Salmanu na jinyarsa, yana yi masa famfon kin zuwa gidansu ko sanar da su halin da yake ciki, wayarsa na hannun Salmanun shi yake zuwa ya ce Hajiya na gaishe shi wai kafarta ke ciwo shiyasa bata zo duba shi ba kasancewar Alh. yayi tafiya zuwa Enugu. Ba wannan ne kadai aikin da yake da wayar ba, yayi blocking din hanyar shigowar ko wane kira, duk sanda ya bushi iska kuma ya kan tafa maganganun cin mutunci da cin fuska hadi da nuna kiyayya ya tura wa Salma a zuwan shi ne Adamu. 88 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Salmanu ya dauki wannan matakin ne dalilin abubuwa uku, na farko jin haushin yadda Alh. ya runtse ido ya ce ya raba shi da Salmanu, shiyasa a tasa iyawar yayi niyyar nuna musu tasu iyakar. Sannan abu na biyu ya san tabbas idan Adamu na gida sai an yi yadda aka yi ya ga Salma, abinda kuma Salmanu yafi tsana kenan yanzu a filin duniyarsa, Salma ta shiga jerin mutanen da ya tsana, saboda haka yake iyakar yin sa ya hana ta rayuwa da Adamu. Sai dalili na karshe, ya sami wani Alaramma ya sanar da shi matsalar Adamu ta zargin da yake na an masa Sihiri, saboda haka kullum yake bada rubutu ana kawo wa Adamu, Salmanu na yi masa karyar ai maganin bibikon aljanin da ya make shi ne. Adamu bai taba shakkar abinda Salmanu ke fada masa ba don Salmanu ya iya hila, saboda haka hankalinsa kwance yayi zamansa a gidan gonar nan, kuma gidan sana'ar bokancinsu da cutarsa ta dakatarsu farawa. A can gida hankalin Hajiyarsa ne kadai yayi kololuwan tashi saboda rashin ganin 89 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Adamu, amma Alh. ya rantse ya kuma wallahi Adamu yana sane ya buya, kawai so yake ya nuna musu iyakarsu, don haka babu inda zai je nemansa. Hajiya ta so ta musa, amma kasancewar Alh. na iyakar kokarinsa akan Adamu, kuma yawancin abinda ke hado su ma Adamun ne bashi da gaskiya, sai kawai ta daure ta cije domin kar ta kware wa Alh. baya, musamman da yake yana ta kumfar bakin don shi Adamu ya buya, sai da ya sanya shi karade dangi da maganar aurensa da Salma sannan zai juya baya ya zo masa da rainin wayo, ya bace kowa in ya buga lambarsa ba zai same shi ba, sai shi idan ya ga dama ya bude ya dinga aikawa da Salma bakaken maganganu da'nuna kiyayya. "Na rantse da Allah, sati daya na cika in ma bai dawo ba sai na daura aurensa da Salma sai dai idan ya ga dama y ace ni ba jininsa ba ne mu raba hanya" Wannan ne alwashin da Alh. ya dinga ci cikin tsananta fishin da ke kara tashin hankalin Hajiya mai son ta kare Adamu ko tayi umarnin a yi cigiyarsa. 90 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Amma dai dole haka ta hadiye ta cigaba da kawaici, shi kuma Alh. ya cigaba da shirye shiryen aurar da Adamu cikin sati dayan da ya kudurta, kuma ya himmatu cikawa, ya kuma cika a ranar da Adamu ya cika kwanaki bakwai da bacewa, ba tare da an yi gangamin tara mutane ba, hasalima su isu danginsu suka hadu da makwabta aka daura auren. A wannan sati dayan duk zirga-zirgar da su Salma zasu yi gidan bokansu sun yi abinsu, shi ya tabbatar musu aure an yi an gama, shi ya ingiza Alh. rasa kwnciyar hankali har sai da ya daura auren, sannan ya tabbatar musu Adamu idan ya dawo ba shi da wani katabus na yunkurin bijirewa. Ranar da Adamu ya cika sati dayan, da kansa ya ji hankalinsa yayi mugun tashi a bukatar zuwa gida. Tun da sanyin asuba ya gallabi Salmanu tafiya zai yi. Ba tare da son rai ba Salmanu ya dinga karfafa masa gwiwa, amma cikin siyasa ya dinga ribatarsa har ya kai azahar sannan ya bar 91 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 shi ya tafi gida bayan sun ajiye ajandar cewa gobe da sanyin safiya zai fito aiki. ********* Ba cikin karfin gwiwa sosai ya tunkari gidansu kai tsaye zai shiga ba, yana dab da shiga soro suka yi kacibis da Alh. ya fito daga gidan shi kuma zai fita. Adamu ya ji wata irin mummunar faduwar gaba ta daki kolin zuciyarsa. Gaskiya ba haka ya so ba, ba Alh. ya so fara gani ba, Hajiya ya so fara gani yadda duk yadda ya tsara ta zata tsaru, ashe yau Allah ya hukunto masa haduwa da abinda ba ya so. Kawai sai ruďewa ta sanya Adamu zubewa kasa yana gaishe shi saboda tsabar rudewa, musamman da ya gan shi cikin fishi. Alh. yayi masifar cin magani, maimakon ya amsa gaisuwar kawai sai ya yafice shi ya се masa, "Zo mu je" 92 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Tsoro ya kara kashe Adamu da ya ga ba cikin gidan Alh. ya dosa ba, hanyar gidansa ya dosa. Wani karfin gwiwa ya shigi Adamu da wani tunani ya zo masa kahon zuci, don me ma zai dami kansa da tsoron Alh. sai ka ce wani Ubangiji? Bakinsa na rawa ya tambayi Alh. wanda ya riga yayi gaba, "Alh. ina za mu?" "In mun je sai ka gani” Ya amsa masa ba cikin dadin murya ba. Adamu ya kara dakewa, "To ba zan iya shiga na gaisa da Hajiya ba tukunna? Gara na shiga ta gan ni hankalinta ya kwanta.." Cikin juyawa ya kale shi fuska a tamke Alh. ya amsa, "In kwanakin sati da kayi ba ka gida ba ta fadi ta mutu saboda bata ga fuskarka ba ai, rabin awa ko awa daya da zaka yi yanzu ba zai sa ka dawo ka tarar ta mutu ba" Adamu na jin haka ya san Alh. ya hadiyo, don haka sai ya ja bakinsa ya rufe, a ransa 93 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 kuma ya kudurta rashin kirkin da zai yi in an nemi raina masa wayo. Ya tarar da gidan da hayaniya, amma dai suna shiga aka hau kallonsa saroro yana bin Alh. a baya yana ta faman yake yana gaisawa da mutane har suka shige dakin Alh. Alh. ya shige bandaki shi kuma ya nemi kujera ya zauna ya ci magani yana ta faman muzurai da sake-sake har Alh. ya fito daga bandakin ya hakimce a kujera cikin kalar nasa nuna bacin ran, "Ba na so in ce daga ina kake Adamu, don kar in ji amsar rainin hankali ta janyo in tashi in kashe ka da mari" Adamu yayi fuska iyakar fuska, "Ni dai namiji ne, bare a ce yawon duniya na tafi" Mamaki ya cika Alh. wannan fa shi ake kira karfin hali wai barawo da sallama, daga bisani kuma sai ransa ya baci ya kura wa ido Adamu cikin bacin rai. Adamu ya muskuta ya sake muskutawa yana wani basarwa, "Wallahi fashina aka yi" 94 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Alh. ya jima bai tanka ba saboda tsabar haushi ya ma rasa me zai cewa Adamu, dama abinda ya guda kenan, ya san Adamu zai iya zuwa masa da rainin hankalin da zai tunzura shi, ilai kuwa. Sai faman kokawar hadiye fishinsa yake, har ya samu ya hadiyu, ya sassauta fuska ya dubi Adamu, Fashi wane iri, su waye suka yi fashin naka?" Adamu ya sake kawar da kai yana cin magani, "Masu fashin mutane mana, sun ga ba zan yi musu amfani ba suka dawo da ni" Wannan tatsuniyar ta gajiyar da Alh. sosai, ya ga kawai mafi a'ala ya rufe babinta ya dauko babi na gaba. Ya girgiza kai cikin halin ko in kula, "Allah sarki, to Allah kiyaye gaba" "Amin" Adamu yayi fuska ya amsa. Alh. ya sake gyara zama sannan ya gyara murya, "Na zaci lafiyarka lau ka guje mu shiyasa har na yi maka wani karambani" 95 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Adamu ya dube shi cikin rashin fahimta, amma bai tanka ba. Alh. bai damu da shirunsa ba ya cigaba da Magana. "Kodayake ba za'a kira shi da karambani ba illa son in faranta maka ko kuma in cika maka wani burinka da kake fatan tabbatuwarsa" Yayi shiru yana jan iska. Yanzu Adamu ya tattara masa hankalinsa gaba daya, cikin jin dokin jin burin da Alh. zai ce ya cika masa, shi dai ya san a duniyar nan ba shi da wani buri da ya wuce mallakar Husna da kuma zama attajiri domin ya jiyar da ita dadi, su ne manyan burikansa, duk sauran da zasu biyo baya kanana ne mahadın rayuwa kawai, amma me!? Kawai sai Alh. ya kunno masa da hagun wannan buri. "Maganar da muka yi kwanaki kai da Salma, cikin ikon Allah na yi iyakar Kokarina na cika muku wannan buri, da safiyar yau aka daura muku aure" Adamu ya ji tamkar Alh. ya wurga shi a tekun ruwan zafi, nan take ya fara hada gumi 96 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 tamkar fankar da take juyawa ita ma zafin take bayarwa sai dai harshensa ya sarke, duk kokarinsa na yayi furuci sai ya kasa illa sa wa Alh. ido yana kallo. Alh. ma ya kura masa ido, "Yaya lafiya na ga kana hada zufa?" Da za a sakar wa Adamu barshe babu abinda zai hana shi tura wa Alh. ashar, amma an daure harshen don haka ba shi da baka sai kunne. Alh. ya sake kada kai yana cigaba da nuna mamaki, "Na san ban maka ta'addanci a Adamu, godiya na cancanci ka yi min ba wannan kallon ba" Har yanzu Adamu ya kasa tankawa, lokacin da ransa ya raya masa ya tashi ya sa wa Alh. naushi ma sai ya ji duk lakarsa ta mutu, tamkar ko hannunsa ba zai iya dagawa ba. Da Alh. ya karaci nuna mamakinsa sai ya daga waya ya kira Sa'a ya ce ta turo masa Salma. Kafin Salma ta zo sai da ta gama tsubbacetsubbacen da boka ya bata, ta taho da maganin 97 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 da ya sanya ta barbadawa a inda Adamu zai taka, ta barbadada a kofar dakin sannan ta yi fuska ta shiga kai a kasa tana sallama. Har yanzu harshen Adamu a daure yake, amma idon zuciyarsa bai kasa ganin mugun kyan Salma ba, ya ji a guje wani irin shauki yana zagaye ilahirinsa, sai dai ba bakin tankawa. Ya dauke ido daga kanta bayan ta zauna ya mayar da ganinsa ga Alh. wanda ya fara koro musu nasiha. Ya yiwa Salma shaidar hakuri, ya yi wa Adamu ta mayar da kai ga abinda ya sanya gaba, ya ce, "To ke Salma ina fatan ki dore da hakurinki da na san ki da shi, kai kuma Adamu ina fatan za mu ga jajircewarka da taurin kanka wajen kula da iyalinka tare da yi musu adalci" Ko nishi Adamu yayi yunkurin yayi ya kasa, ya dai bi Salma da kallo wadda farin cikinta ya kasa boyuwa lokacin da take kada kanta a kasa alamar bayar da amsa cikin kunya. Wannan shirun da kallon galala din na Adamu ya ishi Alh. amma babu yadda ya iya haka yayi ta yi musu nasiha kana ya sallami Salma ya kara mayar da hankali ga Adamu, 98 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 "Karamin gidan nan nawa da na siya kwanaki a Dorayi, anjima zan baka mukullinsa ka je ka duba 'yan gyare-gyaren da ba zai ci kudi da yawa ba a samu a kwaskware shi ku tare nan da sati guda" kyar. ko?" "Hmn!" Wannan karon Adamu ya kwato nishi da Alh. ya sake shanye haushi ya cigaba, "Ka san gidan akwai shago a kofar gida Gyada kai kawai Adamu yayi. Alh. y ace, "Na lura dan zagayen unguwar gaba daya babu shagon sayar da kayan masarufi, saboda haka tunanina ya fada kan cewa sai na baka jari ka zuba kaya ka dinga saidawa, daidai talaka dai ya ishe ku cin abinci da toshe wata 6arakar" "To" In ji Adamu Alh. ya dan ja fasali yana kallonsa, yanzu ya fara zargin anya kansa daya kuwa? Kodayake kafin yayi masa zancen aurensa da 99 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Salma ya zo da bakinsa da cin maganinsa har ya dan sassaki rashin kunyarsa da rainin hankalinsa. Kenan karamin tabin kwanyar da ya same shi na nan take ne bayan jin an aura masa Salma. To bakin alkalami dai ya riga ya bushe, aure ne an riga an daura, yayi haukansa ya warke. Don haka Alh. ya share shi ya cigaba da yi masa bayani, "Ta bangaren Salma kuma kar ka damu, na bawa Sa'a 'yan wasu kudi ta y mata siyayya, babu abinda na ke nema a bangarenka sai halarci ta hanyar yi wa Salma adalci da rike ta bisa amana, ka ga marainiya ce bata da kowa sai mu wanda ko ba kai ka aure ta ba kai mai tsayawa ne ciki-ba-hatsi ba ka kwatar mata 'yancinta idan mijin da ta aura ya danne" Da wannan nasihar Alh. ya sallami Adamu ya fito yana layi ya doshi gidansu. Zuciyarsa fanko ce a tuna komai ko saka komai, amma dai wani radadi-radadi daga can kasa yana fuzgarta, sai dai ba ya nisa yake cin tuntube ya nuna ba komai. Kafin ya je gida ya dinga jin kansa yana wata irn kara tamkar yana shirin bindiga ko 100 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 kamawa da wuta, kawai sai ya tsaya wani kanti a unguwarsu ya sai fuyo wata mai dankaren sanyi har leda hudu ya shiga da shi gida. Hajiya na kakabin murnar zuwansa da kokarin fashewa da kuka saboda ganinsa a hargitse, shi kuma yana mika mata ruwan ya tsuguna a gabanta cikin raunin murya yana cewa, "Hajiya zuba min ruwan nan a tsakar kaina kar ya kama da wuta" Jikin Hajiya na bari ta karbi ruwan ta dinga fashe masa su a aka har leda hudu ba tare da ta damu da jika falonta da take yi ba ta dago kansa cikin fuskar alhini da jimami tana kallonsa, sannnan cikin raunin murya ta ce, "Adamu ina ka shiga ka bace?" Maganar da tayi cikin rauni ta karasa raunata tasa zuciyar, ya ja jiki da kyar ya isa kan tabarma ya zube yana shasshekar kuka. Hankalin Hajiya ya kai kololuwan tashi, da sauri ta durkushe a gabansa tana tambayarsa cikin rudewa, "Adamu me ya same ka?" 101 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Ya ji tausayin kansa da na Hajiyarsa wadda ta damu da shi ya mamaye ransa, ya saki kuka mai nuna tsanantar kunan rai, "Hajiya Alh. yayi min auren da ba zan taba farin ciki da shi ba har abada" Kafar Hajiya na rawa ta silale ta nemi gurin zama tana sauke nishi cikin sauri, "Dama ba kai ka bashi damar ya aura maka Salma ba? Dama baka sonta Adamu?" Ta tambaya a rikice, Ya amsa mata da rauninsa da kuma iyakar gaskiyarsa, "Nine, amma ban san abinda ya shiga cikin kaina na fadi hakan ba, wallahi ba Salma ce zabina ba, ban taba zabarta ba, ban taba mafarkin aurenta ba, kuma ban taba fatan ko a mafarkin in aureta ba" Kan Hajiya ya so ya shiga duhu duk da a iyakar imaninta ta san iyakar gaskiyr Adamu kenan tunda yake furucinsa cikin kuka, sai ta rasa da Kalmar da zata yi amfani wajen karfar wannan kalubalen nasa. Ta cigaba da zura masa ido galala shi kuma ya cigaba da shasshekar kuka kafin ya zarce da cewa, 102 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 "Na kasa cewa Alh. ba zan iya rike auren da yayi min ba, amma duk lokacin da kika sami sarari ki sanar da shi, ni dai ya tawayi rayuwata ya kuma cutar da ni, ba Salma nake so ba, wadda nake so ina yi mata son da ko wane hali aka rataye zuciyata ba za'a iya raba ni da son ba... kuma in na sami sarari zan iya ko ma menene da zai iya samar min da ita" Bai jira cewar Hajiya ba ya mike yana niyyar barin dakin. Gabadayan kan Hajiya ya kulle, a gigice take kwarai, amma dai maganganunsa na karshe sun zabure ta karfin halin mikewa ta riko rigarsa kafin ya ficė, cikin rawar murya ta се, mata, "Adamu zo ka fada min, wa kake so?" Ya dakata ba tare da ya juyo ba ya ce "Husna nake so" "Wacece haka?" Ta tambaya cikin nuna rashin fahimta. Ya kada kai idanuwansa na cigaba da zubar da hawaye, zuciyarsa na wani irin kuna, 103 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 ya koma ya zauna yana kallon Hajiya da ta tsaya kansa hankalinta a tashe, "Ita ce wadda tun tuni nake maganar ina so, akanta na ki karatun boko don in sami kudin d azan rike ta.... Kai Hajiya ko me na zama akanta na zama, ko kuma nake shirin zama... ina fada miki wannan ne dan ki gane ban fara sonta don in daina ba..." 'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Kawai Hajiya ke Ambato cikin tafa hannu mai nuna alhini da nadama, tamkar ita ta yi wa Adamu auren dole take ji cikin ranta, ta kasa yafewa kanta sakacin da tayi aka aura masa abinda ba ya so. Ta matsa can jikin bango ta jingina da shi, "Adamu ni ban san abinda zan ce maka ba, hakuri zan baka ko kuma sakacinka zan nuna maka?" Ya sake mikewa tamkar kunama ta dalle shi yana girgiza mata hannu, "Kar ki ba ni komai Hajiya, ko Husna kika ba ni a yanzu ba zaki birge ni ba, don na san Husna zata rage darajar son da ta ba ni in ta tarar da wadda kaddara ta aura min wato 104 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA.,.2 Salma, duk ku rike abinda zaku fada min don ban ki karbar abinda aka ba nib a wato Salma, amma dai ba zan kasa sanar da ku an cuce ni ba, ba zan kasa fadar ba a yi min daidai ba...." Ya sake ficewa daga dakin cikin fishi. Wannan karon Hajiya bata iya riko shi ba, duk da ta fahimci ba cikin hayyacinsa yake ba, yakamata ta ma ta bar shi ya huce, yadda zasu fi fahimtar juna. Haka dai ta zauna tana ta kakabin alhini da fargabarta har lokacin da ta yanke shawarar daukar waya ta kira Alh. su tattatuna. Adamu bai damu da goge hawayen fuskarsa ba ma bare ya kintsa tafiyarsa ta 6оуе rashin nutsuwarsa ko tashin hankalinsa. a A dazu ya gama kaddara kwanyarsa ta tashi daga aiki, amma a yanzu da ya gan shi hanyar gidansu Husna ya tabbatar ko kwanyarsa zata manta komai ba zata taba manta Husna da abinda ya shafe ta ba. 105 Maimuna Idris Sani Beli 1 NA SHIGA ALJANNA...2 Har ya isa kofar gidan bai san abinda ya kawo shi gurinta ba, amma yayi imanin tunda zuciyarsa ta kawo shi ta san abinda zata fada. A hargitsensa ya sami yaro ya tura shi gidan yayi masa sallama da ita. Husna na kan kekenta da ta fito da shi tsakar gida tana ta faman dikin, yaron ya shiga da sallamarsa, ta toshe kunnuwanta da head phone tana sauraron wakokin da ba su fice na soyayya ba, zuciyarta a rube take da tunanin Adamu har kwalla na tsattsafo mata tana goge abarta a saye. Kuma da yake tana hadawa da dan rausaya alamun tana jin dadin wakar da take sauraro babu wanda ya damu da gane cewa wuya take sha. "Wai Husna ta zo" Yaron ya sake maimaitawa bayan yayi Sallama duk Husna bata ji ba, sai da Hajara at fito daga kicin ta tambayi yaron, "Wanene yake kiranta?" Yaron da yake irin fadi ba a tambayeka bane ya ce, "Wani saurayi ne, baki mai dan kauri da tarin gashi, kuma na ga ma kamar kuka yake?" 106 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Kukan da aka ce yana yi ne yayi mugun jan hankalin Hajara ta yafito Husna cikin firgita, "Ke shashasha, ki saurari yaron nan ya zo da maganar a kasa kunne a saurara" Husna ta ji haushin kiranta shashashan da Hajara ta yi, ta debo mita zata sauke Hajara ta tare ta, "Yanzu haka shi ma me neman naki rashin kunyar kika yi masa, na san yanzu sai ki zage ni... Sai kawai Husna ta saki baki tana kallonta cike da kunan zuciya. Hajara ta juya tana cewa yaron, "Ga ta nan ka sanar da ita sakon" Tana rufe baki yaron ya furta, "Wai Husna ta zi in ji wani..." Shi ma Umma ta tare shi, "Shi wai wa? Ka sanar da ita waye" Yaro kuwa ya gyara murya ya kwatanta mata Adamu. Tunda ya ambaci mai tarin gashi ta ji numfashinta na neman daukewa, zuciyarta ta 107 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 dinga bugawa da sauri da sauri tamkar tana ambatar mata, Adamu ne! Adamu ne! Hajara ta zuba idon ta ga Husna ta kora mai kiran sai ta ga nan da nan ta saki dinki tat fau janyo ruwa tana wanke kafa, a gurguje ta auki hijabi ta yi waje. Kamar yadda ta zata, Adamu ta tarar wujiga-wujiga da shi tamkar an finciko shi daga bakin kura ba, ga shi ba, ba ga zuciyarsa ba wadda fuskarsa ta nuna alama, sannan ita ma kanta bata sha wahalar gane cewa kuka yake ba. Ai jikinta na bari tamkar ta riko hannun Adamu ta yafito shi, "Shigo shigo nan Adamu" Ba ta yi gaba ya biyo ta a baya ba sai ita ta anya shi gaba suka shiga soron. Da sauri kuma ta shige cikin gida ta nace masa, "Bari na kawo maka kujera" Adamu ya kasa Magana ne saboda yadda kuka ya kara cika kansa. Ya tabbatar barin jikin da Husna ke yi da shi na so ne, to yaya zata ji idan ta ji cewa an aura masa kundubа Salma? Duk yadda yayi kokarin ya dake wa 108 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 wannan tausayin sai da ya ci karfinsa, hawayensa suka kara araha a fuskarsa dan ma yayi namijin kokarin hana sautin kuka fitowa. A haka Husna ta fito ta same shi, tana dauke da kujerar zaman dinkinta da kuma pure water mai dan Karen sanyi hade da tambulan din roba. Ta kula da karuwar damuwarsa kuma zuciyarta ta kara rauni, sai dai bata nuna hakan ba. Ta dire masa kujerar cikin kuzari ta nace masa, "Zauna Adamu" Ba musu ya zauna. Ta huda pure water ta tsiyaye shi a tambulan din ta mika masa, "Ungo sha ruwan sanyi hankalinka ya dan kwanta sai na ji me ke akwai" Adamu ya kasa Magana, kirkin Husna ya sanya shi jin lallai an tafka masa asarar masoyiya, asarar da ba zai taba fanshewa ba. Sai da ya shaye ruwan tas, bata bar shi ya ajiye kofin a kasa ba ta mika hannu ta karba idanunta akansa tamkar in ta rufe ido zata bude ta ga ya bace, 109 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 "Adamu me ya faru?" Ta tambaya cikin raunin murya bayan ta fahimci ba shi da alamar niyyar tanka mata, da alamar kuka ya zo yi mata ba Magana ba. Ya daga jajayen idanuwansa ya dube ta, "Kin karanta takarda ta?" A nutse ta girgiza kai, "Ba na jin yaren China" Yayi kasa da kai cikin tunani. Ba don shegantaka yayi mata wannan tambayar ba, yayi mata ne domin ya kamo bakin zarenta, don ta haka ne zai gane matsayinsa a zuciyarta. Ta dan ja fasali tare da sauke numfashi ce masa, ta "Mu bar zancen takarda tunda ga

Chapter 4 of 6