ya fahimci abinda ta fi so kenan a yanzu.
Saboda haka bai yi kasa a gwiwa ba ya kunno
wa da Adamu maganar,
"Tun kafin wannan cece-kucen yayi nisa
ina ganin yakamata manya su shiga maganar,
in da gaske kuke son juna ku fito ku fada mu
san na yi. Ni zan dauki nauyin komai har in ga
burinku ya cika, dama dukkanninku ai
nauyinku a kaina yake. Kai tunda ka ki karatun
dole ba zan zuba maka ido ba, zan baka jari
bayan kayi aure, don ba zan baka yanzu ka
shashantar min ba, in kuwa ka yi aure ka ga
nauyin iyali ya hau kanka na san dole zaka
nutsu"
Kunya ta bayyana a Salma, amma Adamu
babu abinda ya bayyana tasa fuskar sai yarda
da amincewa, duk da cewa zuciyarsa na mika
wuya tana kuma karbowa, yana so yaji
mamakin shi za'a yi wa aure kuma Salma za'a
56 Maimuna Idris Sani Beli
3
NA SHIGA ALJANNA...2
aura masa, sannan yana so yaji murnar za'a
aura masa Salman duk da cewa wata zuciyar
tasa na jin nuna an fa cuce ta,
"Ba ka ce komai ba"
Alh. ya farko da shi daga tunani.
Yayi firgigit ya dago kai ya kale shi,
"Ai babu komai Alh. duk yadda kuka yi
ina maraba, Allah bar zumunci Allah kuma ya
Kara arziki"
Cike da jin dadi Alh. ya amsa.
"Amin, ba wani dogon lokaci zamu ja ba
ma, in dai kun so hakan"
Ba tare da jin wata kumya ba Adamu ya
kalli Salma cikin murmushi ya се,
"Ba komai mun so Alh."
Cikin raha Alh. ya cе,
"To rasa kunya"
Adamu ma yayi dariya
Alh. ya dan nutsu yana duban agogo ya ce.
"Abinda ya rage min yanzu shi ne zuwa
ofishin "Yan sanda in nemi ayi wa Salma iyaka
da Salmanu"
Duk da Adamu cikin jin haushi Salmanu
yake amma sai ya ji kamar bai kyauta ba idan
57 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
aka tozarta Salmanu, cikin sanyin jiki da jin
karfin gwiwa ya ce,
"A'a ka bar ni da shi Alh. ni da kaina zan
yi maganinsa, zai fi jin hukuncina ma akan na
'yan sandan ka san shi da taurin kai"
Alh. da ya gama sakankancewa da Adamu
nan da nan ya mika wuya,
"In dai kana ganin zaka iya yi musu
tsakani ai shikenan, ni kaina bana son shaidar
zuwa ofishin 'yan sanda da mutuncina da
komai, musamman a irin wanna lamarin da
babu shaida, in ya so yana iya cewa karya aka
yi masa mu ji kunya"
A dokance Adamu ya ce,
"Hakane wallahi Alh."
Daga nan Alh. ya sallame su, Adamu da
Salma suka rabu suna kallon-kallo har Adamu
ya bar gidan.
Salma ta fada daki a guje cikin murna
kamar ta shide, Sa'a bata saurare ta ba sai da ta
je gun Alh. ta jiyo kanun zancen sannan ta
dawo ta sami Salma,
"Iye! Amaryar kwanan nan"
58 Maimùna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Salma ta kara fadawa katifa ta tana
birgima da girgiza kai, ta cc,
"Kai Anti!"
Sa'a ta dan kai mata dukan wasa ta ce,
"Me ye wani kai Anti, karya nake?"
Salma ta tashi zaune tana sussunke fuska,
"Na gode Anti...."
Sa'a ta katse ta,
"Da aka yi me? Kin fiye shirme, ki bar
murna ina ganin fa da sauran rina a kaba, har
yau Adamu bai gama zuwa hannu ba kina
ganin fa yadda ba ya zuwa inda kike in ba ke
kika nemo shi ba"
A sanyaye Salma ta dago ta dubi Sa'a,
"Haka ne Anti, to yanzu me ye abin yi?"
Sa'a ta ciji lebe,.
"Dole ne zamu koma gurin boka, Adamu
yana da taurin kai da alama, Alh. zuwan farko
da na yi masa na kama shi kirif! Amma kin ga
shi yana neman ba mu gudu"
Jikin Salma ya kara sanyi, Allah ya sani
ita ba ta je gidan Boka domin ta dauwama tana
zuwa a, ta je don Adamu ya yarda ya aureta,
kuma don Sa'a ta ce babu wata mafita bayan
59 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
wannan, amma bata taba yi wa kanta mafarkin
ta tabbata a wadanda bokaye ke biya wa
bukata ba. Amma ba yadda ta iya, Adamu take
so, har yanzu bata samu ba bare ma ta ga in
zata iya nade hannun zani ta yi wa gidan bokan
tawaye.
gida
A fuskarta ta nuna ta amince su koma.
Sa'a ta ce,
"Sai dai gobe mu je, kin ga yau Alh. yana
Salma ta amsa,
"Allah ya kai mu".
Da har Salmanu zai wuce sabgarsa ya jira
Adamu a a can, yana tuno wasikar cainan
Adamu zuwa ga masoyiyarsa. wadda ke
aljihunsa kawai sai ya saki hanya ya dauki
hanyar gidansu Husna.
Yana tsaye jiran yaron da zai aikaа
kasancewa hantsi ne kusan ko wannne yaro ne
makaranta.
60 Maimuna Idris Sani Beli
S
NA SHIGA ALJANNA...2
Yayi tsayuwa ta kusa ta minti goma, cikin
alfarmar Ubangiji sai ga Husnan ta fito daga
gidan zata siyo kayan dinki.
Tana ganin Salmanu ta saki wata
matsananciyar fara'a tamkar Adamun ta gani,
cikin 6arin jiki ta shiga yi masa maraba da
gaishe shi.
Wani mugun tausayinsu ya shige shi, bai
iya 6oyewa ba maimakon ya rama mata da nata
murmushin ko dariyar sai ya buge da yake ya
na cewа,
"Husna manyan kasa, tun dazu nake tsaye
ina jiran bullowar yaron da zan aika, sai kuma
gashi Allah ma ya bullo min ke da kanki"
Cikin kada kan farin ciki Husna t ace,
"Ka san unguwar tamu manya irinku sun
fi yawa, to bare kuma lokacin makaranta".
Salmanu ya amsa,
"Gaskiya na ga alama, to ya garin?"
Husna ta jinjina kai ta amsa,
"Komai kalau wallahi, Na yi farin cikin
ganinka, amma dai da Adamu na gan ku zan fi
haka farin ciki..."
61 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Ya katse ta saboda ya ji tausayin da yake
mata ya nunku, da gaske Husna tana son
Adamu tana son ya zo wajenta shi kuma gashi
can ya tafi gurin 'yar fashi da makamin
soyayya watakila ma ba zai tuna da ita ba bare
rainin hankalin da yayi mata a takarda.
Salmanu ya daddage dai yayi mata karya.
"Sabga c eta tare shi, kin san yana dan
koyarwa a wata makarnta mai zaman kanta,
jiya da shekaran jiya yayi fashi don haka yau
aka ki lamince masa dole ya wuce bayan ya
bani sakon amsarki, amma dai yau da dare ya
ce zai bullo.
Husna na bayyana kunya amma murna na
yin gaba da kunyar tata. Cike da farin ciki ta
ce,
"Babu laifi Allah ya kai mu
Salmanu ya zaro wasikar daga aljihu ya
mika mata, wasikar tun daga makunshinta ta
nuna da yaren da aka rubutota.
Husna ta karba cikin mamaki tana
godewa, amma dai bata yi nauyin baki bat a bi
ba'asi tana ta faman juya gaba da bayan
wasikar,
62 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Anya wannan tawa ce kuwa"
Salmanu yayi fuska,
"Taki ce mana, me kika gani?"
Ta nuna masa rubutun bayan enbilop din,
"Ka ga rubutun da ya sa ni zaton ba tawa
ba ce
Salmanu ya basar yana yarfe hannu alamar
ko in kula,
"Au ba kya jin wannan yaren?"
Husna ta shiga nazarinsa don ta gane da
gaske yake ko da wasa? Alamunsa ya nuna da
gaske yake saboda haka ta kada kai,
"Ban da a fim ni ko wanda ya taba jin
yaren ban gani ba..."
Ya tare ta da sauri,
"A'a da wasa kike"
Ta kada kai tana dariya,
"Me yasa zan maka wasa? Wallahi da
gaske nake, in kai ka taba ganin mai iya yaren
sai ka bani labari"
Salmanu ya sake yin fuska, babu ta yanda
zaka dube shi ka zaci karya yake shirgawa,
63 Maimuna Idris Sani Beli
OHN SAS A
NA SHIGA ALJANNA...2
"To ai Adamu yaren da ya fi ji kenan fiye
ma da turanci, shi ma yake koyarwa a
makarantar"
Ba karamin girgiza da jin wannan almarar
Husna ta yi ba, ta ji mamaki ta gaji, kuma
Adamu ya kara shiga ranta da birge ta, sai juya
wasikar take tana kallo tana karawa. A karshe
ta buge da kallon Salmanu cikin murmushi,
"Ya ji dadinsa wallahi"
Ta zarce da dariya cikin kallon wasikar,
a
"Amma ban da abinsa ai yakamata ya
fara sanin idan ina jin yaren, ni ko bindiga za
dora min ai ba zan iya kawo kalma daya a nan
ba".
"Kamar dai yadda kika rubuta masa yaren
da kike ji"
Salmanu ya fada cikin ransa, amma ya
kawar da fuska yana basarwa,
"Haba kar ki ba da mata don Allah, ki
daure ki buda ba zaki rasa abinda zaki gane ba"
Ya fara duban agogo yana alamar haramar
tafiya.
Husna ba don ta so ba ta kasa musawa, sai
don kar ta bayar da matan kuma kar ta cigaba
64 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
da rike shi musamman da alamunsa suka nuna
yana son ya kauce, dole ta rausaya kai ta ce,
"To babu laifi, Na gode ka gaisar min shi"
Ya yi gaba yana yana cewa,
"In sha Allah"
Maimakon Adamu ya dauki hanyar fadar
bokancinsu, kawai sai ya gan shi a hanyar gida.
Zuciyarsa ta fara rabuwa biyu ko ma fiye,
neman dalilan yin abinda yayi, nadamar
abinda yayi da kuma shakkun in ma shi din
yayi.
Wai shi ne ya karkace baki ya ce a aura
masa Salma? Wai shi ne ya zabi Salma ya
watsar da Salmanu kuma ya kware masa baya
ya goyi bayan aka aibata shi alhalin har ga
Allah ya san zuciyarsa ta fi son Salmanu akan
Salma, ta fi amincewa Salmanu akan Salma?
A yanzu ya fara jin lallai ma kawai
Sharri aka yi wa Salmanu bai aikata abinda ya
aikata ba, suna zargin Salmanu da shaye-shaye,
tabbas su ne mashayan, domin yana da yakinin
65 Maimuna Idris Sani Beli
1
C
NA SHIGA ALJANNA...2
wata hodar suka busa masa har ya zauna aka
saki wadannan sina-sinan da shi a matsayin
rayuwarsa ta zahiri, amma an ci karya an
kwana da yunwa ace cikin hankalinsa ya ce
aura masa Salma, don ma wani tsabar iya
dialogue har da fadin da gaggawa.
Duk da yana cikin matsawa zuciyarsa da
kwanyarsa mayar da abinda ya faru fim, har
yanzu kansa a rude yake, sai dai yana kala wa
zargin hodar mayen da suka busa masa ce bata
sake shi ba, sai ma ya ji kan ya rude da ciwo,
ba zuciyar tasa kawai da take zogi ba.
A daddafe ya isa gida idanuwansa na zagi
ya bude dakinsa ya fada katifa ya runtse ido,
babu abinda yake hangowa sai lokacin da Alh.
ke masa tayin auren Salma shi kuma yana
amsawa cikin murna da karsashi har ma yana
jefawa shegiyar Salma kallon so wanda sam
bata cancance shi ba, don dai kawai tayi masa
fashinsa ne.
Ya jima cikin mawuyacin hali sannan
wani mawuyacin bacci ya silalo ya sure shi
dauke da mafarkai marasa dadin ji da gani,
66 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
saboda haka da ya farka hankalinsa sai ya kara
tashi.
Dayake Allah yayi masa arahar kuka
kawai sai ya ganshi zaune yana ta sharbar
hawaye. Zuciyarsa kuma ta fara jin abinda ke
faruwa da shi cuta ce ba kaddarar haka kawai
ba, lallai kyautuwa ne ya je neman magani in
ba haka ba yayi mutuwar tsaye.
Yana nan zaune yana sharbar hawaye dajin lallai wani shaidani ne ya hau kan zuciyarsa
yake sarrafa masa ita ba shi ne da kansa ba.
Kawai sai ga kiran Salma ya shigo wayarsa,
kamar yadda ya gama hasashen kuwa sai ya ji
tilashin bashi da abu mafi soyuwa irin daga
wayar, jikinsa na bari ya daga yayi mata
Magana a ladabce muryasa har sarkewa ta ke,
"Ranki ya dade me ya faru, ko wani
99 kiran ne'
Daga can 6angaren a yangace Salma ta
amsa,
ne
"Kai haba dai wani kiran, yanzu kana ina
Ya sami kansa da jin sheka mata karya,
67 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Ina hanyar gidansu Salmanu in je mu
kwashi 'yan kallo"
Ran Salma yayi fari tas! A yangance ta
sake cewa,
"Kai Adamu wai dambe zaka yi da shi
ne?"
Ya sake amsawa cikin farin jiki,
"Sai in yi abinda ya fi dambe da shi mana
Salma, ke fa ya taba! Yau ni na taba jin irin
wanna ta'addanci ma? Don kawai ina sonki sai
abin ya tsaya masa a rai? Ai kin ga dole ma na
bi ba'asi in yake sonki na ji dalili....."
Salma ta katse shi cikin dariya,
"Kai haba! Allah ya tsari gatari da sara
shuka, ni me zan da shi?"
Muryar Adamu ta nuna tsabar jin dadinta
ga kalaman Salma, cike da zumudi ya ce,
"Ai kin ga dole na je na fada masa hakan,
in ma sonki ya dauka ba sai ya sauke ba...'
Salma ta tare,
"Eh haka ne kuma, amma dai kar ka yarda
ka yi fada da shi, ka san dan ganye ne, zai iya
Burma maka wuka na shiga uku... kawai dai
ka ja masa kunne ya fita harka ta, kai ma kuma
68 Maimuna Idris Sani Beli
3
NA SHIGA ALJANNA...2
ka fita harkarsa, ba kai ba shi, in so samu ne
ma ko hanyar da ya bi kar ka bi..... ni fa koо ya
baka hakuri kun shirya in mun yi aure kar ka
sake ka kawo min shi gidana.....
Ya tare ta cikin yanayin bin umarni da
nuna gamsuwa,
"Ni ma yaushe zan yarda da hakurinsa na
shirya da shi bare har na kawo miki shi
gidanki? Ai tunda ba kya son ganin Salmanu ni
kuma zan mutu wajen hana ki ganinsa'
Ta yi wata "Yar shewar farin ciki a
shagwabe,
"Na san zaka iya Adamu, komai ka dauka
kai Jarumi ne a cikinsa"
Ya ji matukar dadin yabon da tayi masa,
cike da fara'a ya ce mata,
"Ni jaruminki ne kawai Salma ba jarumin
kowa ba, zan iya sadaukar miki da rai, ba zan
iya sadaukarwa da kowa ba..."
Kawai sai Salma ta ji wani zazzafan
hawayen tausayinsu ya ciko mata idanuwa, wai
Adamu ne ke sakar mata irin wadannan zafafan
kalaman soyayyar ba cikin hayyaci ba? Ta ji
tausayin wannan dolen soyayya da tayi masa,
69 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
sannan ta ji tausayin kanta da bata cancanci
Adamu ya so tab a sai ta gusar masa da hankali.
"Na gode Adamu'
Ta sami kanta da fada cikin raunin muryar
da ta bayyana kukan da take.
Nan kuma hankalin Adamu ya tashi, ya
shiga barin jikin tambayarta,
"Na bata miki rai ko? Ban san Maganata
zata bata miki rai ba, don Allah ki yi hakuri ki
yafe min"
Da sauri Salma ta katse shi tana rarrashi,
"Ni ma jarumarka ce Adamu, ba zaka bata
min rai ba, hawayen farin ciki nake da jin
kamar a mafarki, wai ni-kake so haka Adamu?"
A dokance ya amsa,
"Ki bar shakku Salma, ina sonki kuma ba
יי
zan fasa ba har mutuwata"
Farin ciki ya fara korar hawayen da take,
tana gogewa tana amsa masa,
"Ni ma haka Adamu. Yanzu yaushe zaka
zo?"
Ya amsa,
"Ko yanzu kika cë na taho"
70 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Da sauri ta girgiza kai,
"Ai ba zan so abinda zai wahalar da kai
ba, yanzu ka bar gidan kuma nà ce ka dawo, ka
bari da dare ka zo"
Ya ce,
"Allah ya kai mu, In sha Allahu da vuri
zaki gan ni"
Ba don ta so su bar hirar ba sai dan kudi
wayarta sun kare, ta yi masa sallama suka rabu
dukkansu suna nuna begen juna.
Salma ta sauke waya tana farin ciki.
Adamu ya sauke tasa zuciyarsa na
kuntacewa, maimakon ya rafsa kuka kamar
yadda ya so, kawai sai ya fasa ya hau binciken
wani ruwan madubi da ba shi da amfani a
wajensa sai idan zai yi gyara fuska. Ya shiga
duban kansa a madubin tamkar yana tantamar
in shi ne Adamu dan Hajiya. Bai iya barin abin
a zuciyarsa ba sai da ya fito fili ya hau
tambayar dodon madubin da muryar tausayi,
"Don Allah fada min gaskiya kai ne
Adamu? In ka ce min kai ne, na rantse da
Ubangijin day a kage ni ka zama mugun
makaryaci, Adamu ba wawa ba ne, Adamu ba
71 Maimuna Idris Sani Bali
NA SHIGA ALJANNA...2
soko ba ne, Adamu ba Salma yake so ba,
Adamu Salma bata isa ya so ta ba....... duk
abinda ya jaza wa Adamu zama soko yanzu
Allah ya isan sa bai yafe ba!'
Bai tsaya a nan ba sai da ya zauna
musamman ya hau turawa Salma iyayen ashar,
ba ita ba hatta Alhajinsa ya sha zagi shi da
Satma, sai kuma da ya gama zagin ne sannan
ya fara kuka ya hau fadin,
"Wallahi dama na fada, na haukace, na
san na haukace dole sai an yi min Rukiyya ko
kuma Girka. Wayyo Na shiga aljanna na kasa
fita"
Yana ta faman wannan Samabatun
Salmanu da ya gaji da jira ya biyo sawu ta
waya, dama ga dokin ya bashi labarin yadda
su yi da Husa ya dame shi, ga kuma aiki
yayi musu kaca-kaca har ma suna sa ran fara
samun kostoma daga farkon sati.
Ya gintse murya ya ce masa,
"Wai har yanzu wannan
yarinyar bata bar ka ka taho ba ne?"
"Haukana ne ya tashi Salmanu"
kundubar
72 Maimuna Idris Sani Beli
A
NA SHIGA ALJANNA..2
Adamu ya amsa cikin rarraunar murya mai
son fashewa da kuka.
Salmanu ya dauke wuta,cikin rashin abin
cewa.
"Shiyasa na so ka raka ni Salmanu, na san
in kana nan komai zai iya zuwa da sauki, kila
ma ba zasu sami damar busa min hodar da suka
busa min haukan nawa ya tashi ba"
Salmanu yayi ta maza ya samo abin cewa,
"Yanzu kana ina?"
"Ina gida"
Adamu ya amsa.
A tausashe Salmanu y ace,
יי" To ka taho nan Zawaciki mu hadu"
"In zan iya ko?"
Adamu ya fada a raunane.
Salmanu y ace,
"Ai daurewa zaka yi, in ka zo din zamu
tattauna dukkan abin yi, kar ka damu Adamu,
in dai ina raye sai inda karfina ya kare a nemar
wa zuciyarka da gangar jikinka Salama, ban
taba alkawari irin wannan ba sai a kanka, ba ni
da gatan dą ya fika, ba ni da wanda ya ki
watsar da ni saboda yadda na sami rayuwa sai
73 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
kai don haka nake jin rayuwata tamkar an
samar da ita ne domin in yi maka hidima in
samar maka farin ciki.. ka zo kawai, ina jiranka
nan da rabin awa"
ba.
Ya sauke wayar ba tare da ya jira cewarsa
Adamu ya ji farin ciki da nutsuwa a
maganganun Salmanu, ko bai samar masa
mafitar da yake lissafi ba, tabbas yayi masa
abinda ake cewa zoka ci tuwo yafi tuwon dadi.
Da karamin kuzarinsa ya shirya ya dauki
hanyar Zawaciki.
Ba karamin girgiza Salamanu yayi da jin
labarin da Adamu ya bashi ba, wanda bai rage
masa komai ba tun daga kan kashedin raba sun
da aka yi masa da kuma maganar aurensa da
Salma da ake shirin yi nan kusa har ma da
wayar da suka yi da Salma daga baya.
Salmanu ya sake gaskata zaton da yayi wa
Salma na cewa sihiri suka yi wa Adamu, ya
fito fili kuma ya shaida masa cewa tabbas shi
ya tare Salma yayi mata abinda ta fada ya
kuma fadi dalilinsa na yin abinda yayi, ya kare
da cewa,
74 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA. 2
"Ko a jikinka yakamata ka ji sauyi, in ba
rami babu abinda zai kawo rami. Ko Husa da
kake so da gaske don Allah kana yi mata barin
jikin da kake wa Salma idan ka ganta?"
Adamu babu bakin Magana sai kallo.
Salmanu ya dora,
"In mun nutsu dole mu karya asirin da
suka yi maka, ni ban yarda abinda ke faruwa
daga Allah ba ne"
Adamu yayi kasake kamar ba zai tanka ba,
amma cikin yanayin kuluwa sai ya kada kai,
"Ka zauna kai ka nutsu, ni kuma zan san
abin yi
Salmanu ya dan yi nazarin Adamu da
kyau, sannan ya nisa y аce,
"Babu laifi, amma dai duk abinda zaka yi
kar na ji ka a wajen Malam-Na-Allah, don na
san kai duk duniyar nan ba ka da malamin da
ka amincewa kamarsa"
Haushi ya cika Adamu, amma dai bai
tanka ba.
Shirun da yà yayi ya tabbatarwa da
Salmanu wajen nasa zai je in dai har.zuwan da
75 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
gaske ne, dole ya shiga tunanin hanyar da zai tankwabe shi.
Da kokarin tunanin mafitar ya basar da shi,
"Ka zo mu yi katangar nan ta cikin daki, yakamata mu kammala duk wani gyara kafin
mu fara aiki"
Bai jira cewarsa ba ya bar falon zuwa
cikin tafkeken dakin ya hadu da samarin da
suka gayyato taya su aiki.
Adamu ba shi da zabi, dole ya watsar da
tunani da damuwa ya bi Salmanu, don yana jin
in bai yi wasa ba haukan nan dab yake da fara
sanya shi zabura. Sai dai fa ya kudure a ransa
dole ne da yamma ya halarci gurin Malam-NaAllah.
Salmanu ma ya kudure a ransa, duk runtsi
ba zai sake Adamu ya kubuce ya je gurin Salma kamar yadda yayi mata alkawari ba,
saboda haka ya dinga kaffa-kaffa da shi bayan
ya sace wayarsa ya kashe. Daga bisani ma sai
yayi masa dabarar cewa shi zai raka shi wajen Malam-Na-Allah su kai masa kuka.
76 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Haka kuwa aka yi, karfe shidda na
yammacin Ranar suka kwashi jiki suka tafi
Warure. Komai a gaban Salmanu aka yi, abin
mamaki Adamu bai kawo maganar Salma ba
sai ya kawo maganar neman kudinsa da neman
dafa'i.
Malam kuwa ya sake dankara masa
wurudi mai zafi, ya kuma sanar da shi a yau ba
gobe ba in yayi wurudin Aljanin kudin zai zo
masa ya nemi bukatarsa.
Salmanu da kansa ya zube wa Malam
- sadaka suka fice, a nan ne ya tambayi
Salmanau,
"Mun yi da kai zaka kawo matsalar Salma
da Husna, me yasa ka kawo zancen kudi wanda
muka kamo hanyar samunsu?"
Cikin yanayin tabbaci Adamu ya kada kai,
"Tun da sanyin la'asar ya busa na dena jin
matsalar Salma a matsala, har wacece ita da
zan aura dole?. Na ga shegen da zai aura min
ita
Salmanu ya kada kai cikin jin dariya
amma ya hadiye, ya ce masa,
"To Husna fa?"
77 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Nan ma cikn yakini Adamu ya amsa,
"Ban taba cire yakinin zan auri Husna ba,
ina jin kuma na fada maka dalilin"
Salmanu ya kawar da kai kamar babu wata
a cikinsa,
"Ai shikenan, ka je ka yi wurudin neman
kudi ka kira aljan, in na ga ka samu kuma ka
wuce lafiya sai nima na biyo hanya ko don kar
ka canja ni daga zama abokinka idan ka yi
kudin"
Ya kare zancensa cikin dariya.
Adamu ma ya dara.
Salmanu ya sake cewa,
"Ka san abinda za'ayi?"
Adamu ya girgiza kai.
Salmanu y ace,
"Don ma kar Salma ta biyo ka gida ta
shammace ka ka zo mu je gidanmu mu kwana"
Da sauri Adamu ya dube shi,
"Wanne gidan naku?"
"Wajen sana'armu nake nufi, ka ga cikin
dare kai kana wurudin neman kudinka, ni
kuma ina yi mana na neman tsari da 'yan sa
ido, kodayake babu ma wanda ya san cewa ko
78 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
ta silar sana'ar taka zamu samu kudin da
wurudin naka ya samar"
Adamu ya dan yi jimami kafin ya amince,
ya ce,
"Ni fadan Hajiya nake tsoro"
Salmanu ya shiga rarrashi,
"Kar ka damu, ka san mu da dabara dole
zamu san karyar da zamu kirkiro mata'
Da wannan Adamu ya yarda suka koma
Zawaciki.
Kafin su isa magariba ta karato. Adamu ya
tsaya masallaci, Salmanu kuma ya wuce gida a
guje ya fara shirin zama aljanin Adamu na
tsakar dare domin katange shi daga masifar da
yake shirin jefa kansa.
Salmanu ya tanadi fararen kaya da farin
bokitin fenti mai murfi, hade da fararen rawani
ya hada biyar guri daya sannan ya zauna ya
nada wa bokitin fentin nan rawani tamkar wani
jibgegen kan ifritu, yayi masa. Karamin
masakali yadda zai hau kansa kai tsaye ya
79 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
zauna daram, ya nemo zabgegiya fara jallabiya
da kuma dogon kwagiri, duk ya tura a sako ya
fara jiran dare.
Karfe uku na dare Adamu ya farka ya
dauro alwalarsa, ya zo ya sha turarensa jiki da
kuma carbi sannan ya fara aiki. Bai ja carbin
nan ya kai kwaya dari ba, kamar daga sama ya
ga dirar wata doguwar halitta mai rafkeken kai
a gabansa, sanye da fararen kaya dogare da
Sanda daya hannun kuma rike da wata
shimfidediyar bulala.
Tun yammar. Adamu ke gwajin yadda zai
yi Magana da aljaninsa cikin kwanciyar
hankali idan ya bayyana, tare da kwatanta
yadda zai yi Magana da shi da kuma abinda zai
nema a wajensa, ciki har da Husna, amma abin
mamaki lokacin da aljanin ya afko sai da fitsari
ya kubucewa Adamu, ya sunkwi da kai cikin
ransa yana cewa, Na shiga aljanna na kasa fita.
Yana ta barin jiki ba tare da razana ta bar
Adamu iya kallon aljanin ko tanka masa ba.
Aljanin ya saki tsawa cikin wata irin
razananniyar murya, ya ce,
80 Maimuna Idris Sani Beli
هر
NA SHIGA ALJANNA...2
"Kai Bil adam, wa ya kai ka karambanin
kirana?"
Jikin Adamu ya kara daukar rawa, ya kara
dukad da kai yana jan carbinsa yana kuma
ambaton wurudinsa a fili.
Aljanin ya sake daka masa tsawa, ya ce,
Dan Fatalar Gyatumarka ba da kai nake
Magana ba?"
Yanzu Adamu ya daure ya amsa cikin
harufa daidai ba tare da ya dago kansa ba,
Ranka ya dade, wai so nake na kai adadin
da aka ce sai na yi zaka bayyana da
alheri...nag a kamar yanzu da akasin haka ka
zo... a fusace kake."
Adamu bai rufe baki ba aljanin nan ya
daga shimfidediyar bulalar hannunsa ya zurara
wa Adamu, nan take Adamu ya baje a wajen,
yana shirin sumewa, Aljani ya sake daga
bulalar yana yi wa Adamu tsawa,
"Ba zaka fada min abinda kake bukata
ba?"
Adamu na neman rasa hayyaci ya ce masa,
owak Ni bukatata kawai ka bace ranka ya
idade
81 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Adamu bai rufe baki ba Aljanin nan ya
dinga shirgawa Adamu ba kakkautawa sai da
ya tabbatar ya sume sannan ya kyale shi.
A hanzarce Salmanu ya tube shigarsa
yayi saurin kawar da su daga wajen sannan ya
koma shimfidar da yayi wa Adamu basajar
yana ciki yana bacci yayi kwanciyarsa ba tare
da ya damu da halin suman da Adamu ke ciki
ba ya hau shirgar baccinsa.
Sai da sanyin asuba ya daki Adamu
sannan ya farko cikin mawuyacin hali na ciwon
jiki da razanar zaton Aljani na tsaye kansa,
Ya dinga ihu yana hurwa da neman afuwa,
tare da ambaton ya shiga aljanna ya kasa fita, a
iyakar imaninsa wannan Kalmar zata iya
kubutar da shi tunda Hajiyarsa ta sha gargadin
sa cewa, Ya shiga uku, fata nagari lamiri, in ya
shiga aljanna ya kasa fita ya fi masa.
Salmanu na jin sa yayi mukus yana
tuntsira dariya cikin mayafi.
Adamu ya gaji da hurwa ya fara neman
daukin Salmanu, cikin ihu da karaji,
"Salmanuna Salmanuna! Ka tashi ka kawo
min dauki ana zaluntata, wannan wane irin
82 Malmuna Idris Sani Bell
NA SHIGA ALJANNA...2
mugun bacci kake, wane baccin asara yau kake
alhalin ana hanyar kashe ni..."
Jin dariyarsa na neman kubucewa ya sa
shi ya bankade mayafi ya taso a gigice ya
kunna fitila,
"Adamu.. Adamu...haukan ne ya tashi?
Mun shiga uku Adamu..."
Adamu ya tattaro wasu mayun ashar ya
aunawa Salmanu cikin neman dauke numfashi
saboda wahala da fishi, bayan ashar din ya
dora da cewa,
"Kar ka kara kira mana shiga uku nan dan
kaza-kazanka, kai dan iska ne Salmanu?