aką matsawa cin kashi?"
Adamu ya kaşa hakuri sai da ya
tambaya.
A sanyaye Salmanu ya mika masa
takardar yana sakin damarar da ya yi wa
fuskarsa yana cewa,
"A'a babu komai, karatun takardar ne ya
fi karfina saboda da harshen Ingilishi ta
66.
rubuta. Sai dai kai ka karanta mana
29 Maimna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Kirjin Adamu ya barko wata shegiyar
kara saboda jin wannan samu da rashi, shi ma
ba iya turancin yayi ba, karatun da yayi duk
bige ne, kuma tun tuni ya sha rantsuwar ba
zai bata lokacinsa a boko ba saboda babu
abincinsa a ciki, ban da gaisuwa da kananan
kalmomin turancin yau da kullum da ake ji
har a bakin wanda bai je makaranta ba ma bai
san komai ba, saboda haka a kawo masa
maganar ya karanta wasikar turanci ma ya
zama.wani yarfa masa yaji a gyambo.
Ya sauke wani irin gwauron numfashi ya
ajiye takardar jiki a sanyaye ya koma ya hada
kai da gwiwa.
Salmanu ya cikin shiga mamaki kwarai,
ci-da-zuci ya dafa kafadar Adamu y ace,
"Ina fatan ba zagi ta antayo maka ba?"
Adamu ya hadiye kunan ransa y ace,
2
"Ba na tsammanin zagin ne
"Yaya baka tsammmanin zagi ne, baka
karanta ba ne?"
Salmanu ya sake tambaya a kagauce,
Adamu ya daure dai ya fito da shi haske,
30 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Ni ma ban da gaisuwar sama ban gane
komai a turancin nata ba"
"Ba ta iya ba ko, amma dole sai ta yi
mana fafa"
Salmanu ya fada iyakar gaskiyarsa, don
shi kansa bai san Adamu bai iya turanci ba,
musamman dayake in yana Magana yana jefa
na kare yawa.
Haushin Salmanu duk ya cika Adamu
fiye ma da haushin yadda ya kasa sanin
menene sakon da masoyiyarsa ta aiko masa.
Salmanu ya sake daukan wasikar da
Adamu ya ajiye ya hau dabura karatunta a
fili.
Kawai sai Adamu ya ji kuka na neman
kwace masa, amma ya daure ya hadiye shi ya
fanshe da cewa,
"Allah ka tsinewa wadanda suka kawo
mana turanci suka ce mu dinga karatu da
rubutu da shi, ko kowa ya yafe musu Allah ni
ba zan yafe musu ba"
31 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Salmanu ya saki takarda, dariya-dariya
da kuka-kuka na damunsa, cikin hadiye su
duka ya dubi Adamu ya ce,
"Au ko kai ne baka iya turancin ba ne?"
"Eh mana!"
Adamu ya amsa a fusace.
Kawai sai Salmanu ya saki dariyarsa son
ransa. Ya dinga yi babu kakkautawa, tun tana
kular da Adamu har shi ma dariyar ta fara
kama shi ya shiga taya Salmanu har suka ci
suka koshi sannan suka dawo neman mafita.
kai,
"Wai yanzu yaya za'ayi ne?"
In ji Salmanu.
Adamu ya dan ja fasali sannan ya girgiza
"Ni wallahi gaba daya kaina ya kulle sai
dai zuwa gobe"
Salmanu ya fara gyara filonsa yana shirin
kwanciya ya ce,
"Allah tashe mu kalau, ko wani ne sai mu
99
nema ya karanta mana ya bayar mana da amsa
A kufule Adamu ya tare shi,
"Allah ya kiyaye, ai gara har in mutu ban
san abinda ta rubuto ba..."
3
32 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Shi ma Salmanu ya tare shi,
"In haka ne babu wata mafita kenan"
Adamu y ace,
"Mu dai jira goben mu gani"
*********
Hankalin Anti Sa'a yayi mugun tashi bisa
labarin da Salma ta kawo mata, ta rasa inda
zata bullowa lamarin ta wanke kanta idan dai
har da gaske ne wani basa'iden ya gan su a
gidan boka har ya fesa labarin yadda ya koma
kunnensu, hukuncin da za'ayi musu shi ne kisa
da wuka?
"Anya ba hasashe ba ne kawai Adamu da
Salmanu suka yi Salma?"
Da ta gama walankeluwar hasashenta ta yi
wa Salma wanna tambayar da safe.
Salma har yanzu a tsorace take, don haka
bata iya tankawa ba face ta dinga ringima kai
kamar kadantare tana yarfe hannu,
Anti Sa'a ta sake girgiza kai,
"Ina shakkar hakan, amma dai zan yi
kunar bakin wake in gwada wata dabara"
33 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Salma ta dago ta dube ta cikin zare ido,
baki na rawa ta ce,
"Me zaki yi? A tsorace nake wannan
maganar ta je kunnen Hajiya, ina da yakinin
wani ne ya gan mu ya je ya fada. Ni dai na
shiga uku, ban fara bin boka a sa'a ba....”
Kawai sai ta zarce da shasshekar kuka.
Wani mugun takaici ya tokare wa Anti
Sa'a a makoshi, ta kashe Salma da harara cikin
mugun kunan rai,
"Ke fa wallahi wata muguwar jaka ce, in
an hada abin kirki da ke sai. kin tankwabe
kokari mutum..."
Salma ta katse ta cikin goge hawaye,
"Ni ba haka nake nufi ba Anti, kawai dai
abin ne ya firgita ni kuma dole ma kin san na
yi ta hasashen ta inda suka gano mu, bugu da
kari ma ban sani ba maganin ya kama Adamu
ko bai kama shi ba tunda har suka sami damar
tattauna na yi masa asiri shi da Abokinsa, kalli
lamarin da kyau Anti dole ne ya firgita irina"
Anti Sa'a ta yi shiru tsawon lokaci, can sai
ta mike ta tafi Dakin maigidanta tana cewa
Salma,
34 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Bari na gwada dabarar da na ce miki zan
gwada mu gani"
Salma bata iya tankawa ba, illa ta bi Antin
da kallo cikin shanye baki da bugawar zuciya.
A mugun tsorace take, tana fargabar abinda zai
bityo baya idan kwai ya fashe, akwai zallar
kunya a ce wai ita ce budurwarta da ita kuma
'yar uwar Adamu a ce ta kai kanta gurin boka
neman soyayyar saurayi, saurayin ma dan
uwanta. Haba wannan abin kunyar har ina!
Anti Sa'a ta sami Maigidanta kishingide
yana hutawa, akwai alamun. hankalinsa a
G kwance yake, don haka ta karawa fuskarta da
furucinta nutsuwa, amma fuskarta a bace ta yi
sallama, hakan ya sanya ya karkato da
hankalinsa gareta fuskarsa babu yabo babu
fallasa,
C
"Ke da wa na ga fuskarki da fishi?"
Ta nemi kujerar da ke fuskantarsa ta zauna
tana ajiyar zuciya,
"Ba fishi ba ne 6acin rai ne Alh. wani
ta'addanci Abokin Adamu ya kwaso ya kawo
mana, wanda idan an bar shi ya sha gaskiya ba.
a kyautawa kai ba"
35 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Alh. ya tsura mata ido cikin kallon rashin
fahimta, ya ce,
"Abokin Adamu wanne, me yayi?"
Kai tsaye ta amsa,
"Ka san dai me ke tsakanin Adamu da
Salma, yau ya kwaso soyayya ya ya kawo
tnata, gobe idan sun yi fada y ace ya fasa haka
su ke, dama dai shi ka san shi, kuli-kuli ne ba a
gane gabansa. To kwanan nan sai ya fara
maganar aure muna dai ta yi masa tsiya har ita
Salman na cewa da me zaka aure ni? Ana ta
wasa da raha, amma dai na fahimci shi wannan
abokin nasa Salmanu ba son abin yake ba, ban
dai san dalili ba,....."
Alh. ya ji ya gaji da wannan dogon sharhin
kafin furta laifin, kawai sai ya tare ta cikin
tuna kaguwa da sikewa,
"Bar wannan labaran don Allah ki fada
min gudarin abinda ya faru"
Nan da nan ta yi fuska ta furta,
"Ai kai ka nake Alh. kawai jiya Salmanu
ya fitar da maitarsa a fili, inda na aiki Salman
gidan. Hajiya da dare ya makure ta a soro ya
dora mata wuka a makogwaro yana tuhumarta
36 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
da cewa wai asiri tayi wa Adamu yake
sonta,wai in ba hakan ba bábu yadda za'ayi
Adamu ya so ta, wai in bata je ta karya asirin
ba sai ya kashe ta
Duk da maganar ta zo wa Alh. a ba zato
kuma ta firgita shi, amma dole wani gurin ya
bashi dariya, ya dan murmusa ya ce,
"Yaya ba zai so ta ba, saboda ita ba mace
ba ce?"
Sa'a ya ji takaicin rashin daukar maganar
da muhimmanci da bai yi ba, amma dai ta
hadiye ta yi fuska tana dan taya shi dariyar a
yake, ta cе,
"To abinda na gani kenan Alh. salmanu
dan iska ne kawai"
Alh. yayi shiru cikin tunanuwa barkatai,
shakkunsa shi ne, ya san Adamu da kyau, bai
cika boye so ko ki ba, sun yi maganar Salma
da shi ya nuna babu soyayya tsakaninsu,
sannan duk labarin soyayyar Salma da Adamun
da ake karade dangi da ita daga bakin Sa'a dai
take fitowa kamar dai yadda ta zayyano yanzu,
sai Alh. ya ji kansa ya kulle ya ma rasa abinda
37 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
ya kamata ya yi nazari a kai ko kuma ya
maganta, sai ya ci gaba cikin shiru.
Cikin bugun kirji Sa'a ta dube shi ta ce,
"Alh. ka yi shiru"
Ya dan yi murmushin yake,
"Abin ne ya daure min kai, ribar me
Salmanu zai ci in ya raba Salma da Adamu,
kuma me zai rasa idan sun auri juna?"
Sa'a ta kawar da kai tana dan bata fuska,
"Oho masa! Ni ba abinda ya dame ni
kenan ba, ni abinda ya dame ni shi ne
ta'addancin da lamarin ya zo das hi, Alh. dole
ka dau mataki gaskiya"
In Sa'a ta yi irin wannan bata ran Alh. ya
sani bata bukatar musu, abinda take bukata
kawai shi ne a aiwatar da abinda ta nufa. Вa
wai in bai aiwatar din tube masa jiki zata yi ta
zane ba, a'a kawai shi ne yake jin ba daidai ba
ne ya ki bin umarnin nata ko aiwatar da abinda
take so, don haka kawai sai ya kada kai cikin
sanyin jiki,
"Ai dama zan dau mataki, raba su ma zan
yi gaba daya
38 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Yauwa yanzu na ji Magana Alh. shegen
yaro kawai ya gagari iyayensa sun sallama shi
mu zai shigo namu dangin mai doka da oda ya
fata mana tarbiyya"
Ta fada cikin jin dadi da karsashi saboda
yakininta na sanin mijinta, tabbas zai dau
matakin kamar yadda ya sanar.
Suka yi shiru tsawon lokaci su duka kowa
da sakar zuciyarsa. Alh. ba a son ransa zai
shiga lamarin Adamu ba, domin tun lokacin da
ya nuna masa iyakarsa akan karatunsa yayi
niyyar fita harkarsa har sai duniya ta jima shi
ya nemo shi da kansa, to amma Iyalinsa ta
shiga lamarin, shi kuma ba ya iya ja da abinda
ta zo da shi, kenan a dole zai bi.
Ita kuma Sa'a tana can duniyar shirya
yadda zata bullowa da Alh. dabarar yadda zai
tunkari Adamu da batun auren Salma, ta saka
wannan ta kwance ta kulla wannan, har dai a
karshe ta zabi fadin abinda ya zo bakinta.
Cikin dakewa ta daga kai ta dube shi,
"Ni ina ganin me zai hana ka tuntube shi,
in suna son juna kawai ayi abin nan mu huta,
sai ka sami 'yan wasu kudi masu kauri ka bashi
39 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA.. 2
ya ja jari tunda ya ki karatun ai bzi kamata a
bar shi ya lalace a banza ba, yana faman bin
'ya'yan iska irinsu Salmanu"
Game da maganar bayar da jari ya ga
gaskiyarta, don shi kansa ya lura Adamu ya
kama turbar lalacewar tunda ba shi da abokin
da ya wuce Salmanu, kullum kuma sai an gan
su sun sha wanka sun fice tare, to amma batun
a yi masa maganar auren Salma shi bai ga
dabara ba don yayi masa maganar kuma bai ga
wani hasken son salma a fuskar Adamu ba, sai
dai ba yà son gwale Sa'a, don haka ya dan
gyara zama ya cе,
"Haka ne, ni ma na lura ya dauko turbar
lalacewar, dole hannunka ba zai rube ka yanke
ka yar ba, zan yi wani abu akan sana'ar tasa,
maganar Salman ma zan kira shi mu yi
maganar. Ni abin ne yake ban shakka, ranar da
na yi masa maganar ba ki ga bakar maganar da
ya zabga min ba, kin dai san shi"
Ta yi fuska ta tare shi,
"Alh. in kana shakka ka hada su tare ga
shi ga Salman, ai maganin karya hallara"
Cikin fuskar jimami ya girgiza kai,
40 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Ni ba nufina kenan ba, ba na son shiga
shirgin da zan zama karamin mutum, shi
Adamu ba ya jin komai in yayi karanta, ba zai
ji kunyar in na hada su gabana ya keta idon
Salman y ace ba ya sonta ba, ai kin ga in an yi
hakan ba a kyauta ba"
Ya kare da zura mata ido.
Ta tamke fuska ta shiga kallon gefe, ba
tare da ta tanka masa ba.
Dole ya saki nasa ra'ayin ya bi nata ta
hanyar kada kai cikin sanyin jiki ya ce,
"Amma shikenan yadda kika fada din
haka za'a yi, ki sanya Salman ta kira min shi a
waya"
********
Salmanu ba yadda bai yi da Adamu kan su
je su sami wani ya karanta musu wasikar
Husna ba amma fur Adamu ya ki, a cewarsa
cin amanar kauna ne wannan ya kai wa wani
ya gane masa sirrin mata, ya kara da cewa,
"Kai ko surar zagi Husna ta sauke min a
wasikar nan cin amana ne na kai wa wani ya
41 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
karanta min, ni a wajena daidai ne da na bashi
damar ya kare mata kallo ita Kanta..."
Salmanu ya tare cikin mamaki,
"Zagi fa ka ce? In nine duniya zan nunawa
don in na rama kar san zalinci na yi"
Kai tsaye Adamu ya amsa,
"Kai da idan ta zage ka zaka dena sonta
kenan, ni zaginta gareni ba zai rage komai a
son da nake mata ba shiyasa in na tona sirrinta
nake jin So ba zai yafe min ba"
Cikin dariyar keta Salmanu y ace, "Shikenan ina jiran ganin ta yadda zaka kwaci kanka, ka san me ke cikin wasikar har ka sami damar bada amsa"
"Don amsa zan bayar da amsa, ka zuba ido ka sha kallo malam, cutar da aka min daya ce, kawai ban san me ta rubuto min ba, ko zagin
ne hakika in a son in sani"
In ji Adamu.
Salmanu ya ce,
"An ji an cuce ka baka san abinda aka
rubuta ba, ni kuma ina nan ina jiran ganin
yadda zaka amsa alhalin ba ka san abinda aka
rubuta ba"
66
42 Maimuna Idris Sani Beli
fita.
NA SHIGA ALJANNA...2
Adamu bai tanka ba, kawai ya mike ya
Salmanu ya bishi da mita,
"Malam kar ka dade, yau yakama ta muje
da wuri mu kammala shirya gurin nan, na fada
maka mun baza neman kostomomi daga jibi
Kila zamu fara zama"
Adamu dai bai tanka ba ya fice abinsa ya
bar Salmanu na dariyar shegantaka.
Sawon mintuna goma sai ga shi ya dawo
rike da Biro da doguwar takarda. Ya nemi guri
ya zauna Salmanu na bin sa da Ido,
"Wato kintatar amsa zaka yi ka bata
kenan?"
Adamu yayi fuska ya zura hannu a aljihu
ya dauko tiger balm sabo a takardarsa, yana
cewa,
"Ka tsaya ka yi kallo kawai, yadda ta sa ni
a duhu wallahi sai na sa ta ba tare da ta canki
yarenta ne ban gane ba"
Har yanzu Salmanu bai fahimci inda
Adamu ya dosa ba, yayi sakare yana kallonsa
yana farke takarda taigan, ya kasa hakuri sai da
ya ce masa,
43 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Wai man zafin zaka shafa a takardar
maimakon ita da ta feso turare?"
Adamu ya ki tankawa face ya cigaba da
aikin gabansa, wato zaro takardar bayanin da
ke kunshe cikin taiga wadda ke dauke da
rubutun yaren China ya gwafe ya fara kwafewa
a doguwar takardar da ya shigo da ita.
Sai yanzu Salmanu ya ankare, ya saki ihu
yana kai wa Adamu bugu, ya ce,
"Shegen kasa! Wato yaren China kai
kuma zaka yi mata idan ita ta yi maka turanci
ko?"
Adamu ya saki dariyar keta ya се,
"Ashe ka gane, idan ita gama-garin yare
take ji wato turanci to ni ina jin wanda kila a
fadin Najeriya ba mu kai mu dari ba?"
"A hasahenka kenan"
Salmanu ya fada cikin tsananta dariya,
shegantakar ta Adamu ta yi mugun birge shi,
salin alin ya kubuta daga tozartar bai iya
turanci ba, kuma ita ma Husna ya sat a a
kwanar bat a iya cainanci ba, yana da tabbacin
gaba ba zata yi gigin sake rubuto wa Adamun
44 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
takarda da turancin ba don kar a bata amsa da
yaren da bata iya ba.
Adamu ya kwafe takarda tsab yayi mata kyakkyawan ninki ya nade a enbilof hankalinsa
a kwance, in dai wannan tararradin amsa
wasikar ne ya gama da shi, sai dai ya jira wata,
wadda yake da tabbacin da yaren da zai iya
zata iso.
Sun karya kumallo suna ta tattauna zancen
cikin dariya, a fakaice Salmanu na yi wa
Adamu hudubar kwantar, da hankalinsa ya
manta da wasu mata ya kama sabgar gabansa,
ya ce masa,
"Ka manta da su, ka nemi kudi, wallahi in
ka same su mace sai ka ture....."
Cikin kada kai Adamu ya tare shi,
"Husna nake so ba mace ba Salmanu"
Salmanu ya ce,
"Na sani, ita ma din cikin sauki zata zo in
dai kana da dan karansinka a aljihu. Abinda
nake so ka gane shi ne, sana'armu tana son
nutsuwa da kirkirar basaja da dabaru, in kuwa ka cunkusawa. kwanyarka mata don Allah
45 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
yaushe zaka sami nutsuwar aiki bare tuna abin
kirki?
"Ba don Adamu ya gamsu ba said an
gajarta zancen ya kada kai,
"Babu laifi zan kwatanta, musamman
dayake daga yau ma zaman kashe wando ya
Kare"
"Yauwa ashe ka gane"
Salmanu ya fada da farin ciki.
Suna shirin fita sai ga wayar Salma, da
Adamu yaga
sunanta sai da ya ji gabansa yayi
mummunan faduwa.
Cikin wani irin barin jiki ya daga wayar
muryarsa na rawa y ace,
"Ran Gimbiya ya dade"
Salma ta ji kamar an tsoma ta a ruwan
sukari, ta saki wata ajiyar zuciya, fargabarta da
tsoronta suka gushe, a ranta ta raya, cib! Ashe
har yanzu maganin na aiki! Amma a fili sai ta
tausasa murya ta се;
"Wacce ni ni mai ido ba dan ciki?"
Da sauri Adamu ya katse ta,
46 Maimuna Idris Sani Beli
3
NA SHIGA ALJANNA...2
"Da gaske wallahi, ai ni kin fiyc min duk
matan duniya?
Dadi ya sake kashe Salma, ta sauke
katuwar ajiyar zuciya ta ce,
"Kamar gaske"
"Me zan yi ki yarda da ni?
Ya tamabaye ta cikin raunin murya.
Ta dan ja fasali sannnan ta amsa,
"Mu bar maganar, yanzu dai kiran ba
nawa ba ne, Alh. ne ya ce na kira ka, wai ko
me kake yanzu ka katse shi ka zo"
Adamu ya dan yi dum! Ransa bai so
wannan titsiyen ba, sai dai ba shi da zabi tunda
ta bangaren Salma kiran ya biyo, ba don haka
ba wallahi mazewa zai yi. Duk da haka said a
ya dan tirje.
"Kash! Anya ba zan share kiran nan ba sai
na dawo? Ina da wani uzuri wallahi"
Kamar Salma zata biye masa saboda
rashin son bacin ransa, sai kuma ta ji yakamata
ta motsa kwanjinta akan sa, cikin basarwa.t
ace,
"Haka dai zaka daure ka zo, in ka zo ma ai
ma samu mu gaisa".
47 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Nan da nan ya amsa,
"To babu laifi zan zo yanzu tunda ke ma
kina son ganina"
Ta sha mur ta sake cewa,
"Yauwa kar ka dade"
"In Allah ya so ba zan jima ba"
Ya sauke wayar tare da sauke ido akan
Salmanu,
"Salma ce ta ce Alh. na kira na yanzun
nan, ka zo mu je sai mu wuce daga can"
Ran Salmanu yayi mugun baci, ya dorawa
Adamu Ido tsawon lokaci sannan ya girgiza
kai,
"Ka na rawar kafar tafiya ka je. ne don
Alh. ne yayi kiran ko kuma don Salma ce ta zo
da sakon kiran?"
Abin tausayi sai Adamu ya yarfe hannu a
sanyaye ya ce,
"Ni ma ban sani ba Salmanu"
Wani haushin ya sake cika Salmanu,
amma dai bai tanka ba sai yayi zuguri yana
kallon Adamu.
、
Adamu ya figi mukullin dakin yana
yafitarsa,
48 Maimuna Idris Sani Beli
"Zo mu
NA SHIGA ALJANNA...2
je mu da sauri mu gama da shi mu
wuce don Allah, ko wacce tsiyar ma zai min
oho masa"
Salmanu da yake tsakiyar shaka ya fashe,
"Ni fa ba zani ba, kawai ka je in kuka
gama ka same ni a can"
Jikin Adamu yayi sanyi, ya dan yi saroro
yana kallonsa, sannnan ya ce,
"Ko gidansu Husnan ba zaka raka ni kai
takardar nan ba?"
Salmanu yayi fuska,
"Kai da zaka gidansu Salma me zaka je yi
gidansu Husna?"
Adamu ya debo murmushin yake ya
sauke,
"Ka manta ni mijin mata biyu ne? ai kayan
nama ba ya kasha kura"
"Sai ka je ai kai daya, don ni kyanwar
lami ne ko 49ay bana ci bare naman"
Bai jira cewarsa 49ay a kada kai yayi
tafiyarsa.
Adamu ya girgiza kai yana murmushi ya
janyo kofar dakinsa ya garkama mata mukulli
49 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA.2
sannan ya shige cikin gida domin yi wa
gyatumarsa sallama.
***********
Salma na sauke waya ta saki ihu ta bazama
dakin Antin Sa'a tana bat a labarin yadda aka
yi.
Anti Sa'a bata yi mamakin abinda ta ji ba
domin ita tayi wa aikin bokanta farin sani, ta
jima da imanin ko ba dade ko ba jima sai
Adamu ya kamu a tarko Salma kirif! Ta nuna
jin dadinta ainun Sannan ta cewa Salma,
"Kin san Allah? Da mun sani ma ba mu
shigo da Alh. cikin maganar nan ba, ke kanki
kin isa raba raba Adamu da Salmanu, Na rantse
miki da Allah idan kika ce kar ya sake kula shi
sai ya hanu"
Salma ta cika da jin mamakin jin abinda
Antinta ta ce, cikin sakin baki ta ce mata,
"Da gaske Anti?"
Sa'a t ace,
"Har fa rantse miki na yi"
Salma ta rausaya kai,
50 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Ai al'ajabi ne yake neman kashe ni,
yanzu duk fandarar Adamu zan iya
dankwafewa?"
Sa'a ta jinjina kan jin dadi hirar, ta ce,
"In kina shakka ki gwada daga kan
maganar Salmanun nan, kar ki bar shi da
maganar Alh. da zai iya watsarwa idan ya tashi
daga gabansa, ki shiga maganar zaki ga abinda
zai faru"
Salma ta kasa Magana sai jínjina, kai
kawai, lamarin ya girmi tunaninta, in a da can
wani ya sanar mata Adamu zai iya zama haka a
hannunta-zata musa masa ko da kuwa tsafe shi
za'a yi ba wai karamin alhaki boka ba.
Babu fargaba ko kadan a tare da Adamu
ya shiga falon Yayansa domin dai shi ya san
bai yi komai ba bare ace akan sa aka kira shi a
balbale shi da fada, amma ga mamakinsa
Salma na shigowa dakin ita ma ta zauna sai ya
ji gaba daya kwanjinsa ya zube, ya dinga jin
rashin katabus hade da faduwar gaba
51 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
musammman da ya saci kallon Salma ya gán ta
tana kuka, sai ransa ya ji a duniyar nan bai taba
cin karo da wani abu mai ciwo irin zubar
hawayenta ba, amma dai haka ya daure ya
sunkwi da kai gaban yayansa wanda ya dauko
jawabin da ya fi zubar, hawayen Salma buga
masa zuciya,
"Da kai Salmanu ya hada kai ya kawo
mana ta'addanci gida? Kana sane da ya tare
Salma jiya ya aza mata wuka a makogwaro
yana mata kashedin ta fita hanyarka"
Adamu ya ji kansa yayi masa wani mugun
nauyi, da kyar ya cire kai ya dubi Alh. sannan
ya mayar da ganinsa ga Salma wadda ke ta.
faman matsar hawayen karya. Da sauri ya
girgiza kai ya ce,
"Salmanun? Wallahi ban san da maganar
ba Alh."
"To yanzu ai ka sani"
Alh. ya fada cikin daure fuska.
Adamu bai damu da cin maganin Alh. ba
shi ta masoyiyarsa Salma yake, wadda yake jin
kamar ya shiga zuciyarta ya sanyaya mata rai
ya hana ta kukan da take, ko kuma ya nuna
52 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
mata lallai ba da hadin kansa aka cutar da ita
ba kuma ba za a taba hada kai da shi a cuce ta
ba bare har da hukuncin dora mata wuka a
wuya, shi mai dora mata wukar a wuya ma ya
gani ba sai inda karfinsa ya kare ba ko kuma
ayi mutuwar kasko.
Cikin mugun sanyin jiki ya mayar da kai
ga Alh. ya се,
"Wallahi Alh. ba ni da masaniya, to wai
laifin me tayi masa da har zai tare ta da wuka
kamar wani shirin fim?"
"In kana shakkar karya ta yi masa ai ga ka
יי
nan sai ka tambaye ta...
A ladabce Adamu ya tare shi,
"Ni ba haka nake nufi ba Alh. tsabaragin
beken Salmanu na gani da haukansa wai zai
zuga shi tare mace da wuka, macen ma wai
Salma wadda ya san dangantakata da ita"
"Kila sholishon nasa na sabo ya sheka"
Alh. ya fara sakkowa saboda imanin da
yayi babu hannun Adamu a abinda Salmanu
yayi tunda yake wannan fitittikewar, sai ya hau
bashi labarin abinda ke akwai kamar yadda
Sa'a ta sanar das hi, ya karkare da cewa,
53 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Ni mamakina shi ne, menene ribar
Salmanu in ya raba ka da Salma? in kuma ka
aure ta me zai rasa?"
Adamu ya rausaya ka, ya rasa abin cewa, a
can cikin kansa ya ji wata shegiyar gada ta
barke, ya rasa me ya tashe ta, amma dai
haushin Salmanu ma ya kunno, don ya ji
mugun ciwo abinda yayi, ji yake kamar ma
abotarsu ta zo karshe daga yau din nan. Yana
can duniyar tunani da lissafi ba ya tare da
dogon sharhin da Alh. ya kunno wanda yake
nufin lallai ya fita hanyar Salmanu ba mutumin
kirki ba ne, kuma dama hausawa sun ce zama
da madaukin kanwa yana kwo farin kai, lallai
ko yanzu bashi da irin tarbiyyar Salmanu idan
suka cigaba da tafiya nan gaba za a wayi gari
babu abinda ya bari na batattun halayen
Salmanun.
Alh. ya karkare da cewa,
"To ka fita hanyarsa, kar na sake ganinka
da shi, in ba haka ba ranka zai yi mummunan
басі"
Adamu bai ji komai ba a kokarin raba shi
da amininsa da ake, shi ma haushinsa ya ji
54 Malmuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
sosai don bai ga dalilin wannan danyen
hukuncin da Salmanun yayi ba. Hankalinsa ba
sosai yake tare da Alh. ba yana can ga Salma
da tayi kicin-kicin cikin hawaye,
A dan raunane ya ce mata,
"Wai da yaushe ne hakan ta faru?"
Sai da tayi ta faman goge hawaye sannan
ta amsa,
"Jiya da dare ne ya kira ni a waya ya ce
min kai ne baka da lafiya wai na zo da sauri"
A rikice Adamu ya cе,
"Kin gani ko? Ke ma da laifinki, ko nine
babu lafiya me ya kai ki fita da dare? Lallai
Salmanu ya isa makiri"
Babu wanda ya tanka tsakanin Alh. da
Salma. Salma goge hawaye take amma tsakiyar
zuciyarta bata taba samun kanta da farin ciki
irin na ranar yau ba.
Alh. kuma kallonsu kawai yake cikin
nazari, sai yanzu ya gaskata maganar
soyayyarsu da ya sha ji a bakin Sa'a. cikin
ransa sai yaji gaba daya haushin Adamu da
yake ji ya gushe, ya ji ma kawai ya yafe masa
bata masa ran da yayi a kan maganar karatu.
55 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Cikin ransa yayi ta bitar Allah ne kadai ya san
abinda ya boye game da lamarin, aurensu zai
masa dadi don shi dai yana alfahari da auren
zumunci, ya gwada ya ji dadinsa, abu na biyu
kuma shi ne, auren nasu zai farantawa Sa'a rai,
don