Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
ka gabana, amma abinda ya fi damuna shi ne ganinka hankali a tashe, wai a haka ka taho tun daga gidanku?" Kulawarta ta sa ya dan sami karfin gwiwar kada kai yayi murmushin yake, "Ban ji nauyin ki gan ni a haka ba sai wasu mutane?" Ta kaďa kai ba don gamsuwa ba sai don son ta yi masa gwaninta, 110 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 "Na ji, me ya faru?" "Bai yi kasa a gwiwa ba ya amsa mata, "Burikana ne suka tarwatse a kasa, na san in na tsinto su ba za su yi miki kyau ba, ba zasu dace da irin son da nake miki ba... shi ne kawai na debo tsawo na zo neman afuwarki, son da na yi miki ba tare da na samu ba" Husna bata fahimci komai a maganganun Adamu ba sai ba zata same shi ba, cikin kura masa ido ta ce, "Dan kara bayani ko zan fahimce ka" Kai tsaye ya amsa, "Na jima ina sonki baki san ina yi ba, ranar da Allah ya hukunto kuma zaki sani sai aka yi fashin zuciyata da makami ba tare da imani ba, abinda ya faru da mu a ranar nan babu shi a tsarina, kawi mafarki ne daga cikin munanan mafarkai..." "Wacce ranar" Ta tare shi cikin ci da zuci. Adamu ba ya son hada shirgin lissafinsa da waccan ranar, ba ya son tuna ta kuma baya son abinda zai tuna masa ita, amma tunda shi 111 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 da zuciyarsa ba sa zuwa wajen Husna da wasa, sai kawai ya ji ya amsa mata kai tsaye, "Ranar da kika kawo min dinkin nan na bayyana miki abinda ke zuciyata game da ke, zuwan Salma kuma ya sanya na rusa abinda na fada da karfin hali ba da karfin imani ba... wallahi bakina karya yayi min Husna ban tabа son Salma ba, ke na taba so son da ban taba yi wa ko wacce mace irinsa ba..." So da tausayi da rashin madafa sun fara gajiyar da Husna dole ta dakatar da shi, cikin sanyin muryar da ta 6oye ciwon ranta, "Kar ka damu da abinda ya faru ran nan, ni tuni ya wuce a gurina" Adamu ya mike cikin rangaji ya fara dan kai komo a gaban Husna kasancewar soron gidan nasu yana da yalwa. Idon Husna na kansa bata ko dauke fuska, kwayar idon nata na nuna jiran furucinsa take amma a zahiri lissafin yadda zata nada gammon daukan jidalin rasa shi take, tana son Adamu irin Son da ba ko wane mutum ake wa ba, kai ba ma ko wacce irin zuciya ce yi ba, sai 112 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 irin Adamun na musamman da irin tata zuciyar ta musamman. Adamu ya dage ya tsayar da hawayen fuskarsa ya kuma kawo wa fuskarsa jarumta, sannan ya daga ido ya kalli Husna. Suka dubi kwayar idon juna tawalli! Sai duk wata shakka ta debe musu, Adamu ya fara jin yayi Magana cikin kwarin gwiwa da zallar gaskiya, Husna ta fara jin sauraron Adamu cikin yakini da gaskata shi. "Furucin da na yi rannan a gabanki a gaban Salma ya tabbata, bayan balaguron da na yi na sati guda, a yau na dawo na tarar an daura min aure da Salma, yanzu na kawo kokon bara ta gurin ki, ki ba ni dama na tafi, amma idan na dawo da wani karfin gwiwar don Allah ki karbe ni a haka ki yi maneji da ni" Ba don idanuwanta da ke kallon Adamu tsaye gabanta ba, da kuma iskar da take shaka mai alfarma Adamu na shaka ya fesar ba ce, jin wannan labarin ya isa kai Husna kasa, amma ta dake tana kallo Adamu cikin rashin hayyaci wani malalcin hawaye na sirnano mata. Ta ci guru da kyar ta tanka masa, 113 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 "Allah sanya alkhairi" "Ban fada don ki yi min addu'a ba, na fada ne don ki san abinda na tawaye ki da shi na auren wata alhalin ke nake so, na fada ne domin ki ji tausayina akan kaddarar da ta afko min, na fada don in kin yarda kaddarar ce ki karbe ni a haka ki yi maneji da ni..." Ya fada cikin son koma wa hawayen da ya baro. Husna ta sake cin wani gurun ta girgiza kai. "Ai duk ba zasu gagara ba. Yanzu me ka fi bukata daga gare ni?" Ya karaso gabanta murya kasa-kasa ya amsa mata, "Nan da wata biyu zaki karbe ni a matsayin miji? Wata rahma ta tsirgowa Husna tun daga Kolin ka har yatsan kafa, amma dai ta shanye nunawa a fuska bare barin jiki. Cikin nutsuwa ta gyada kai, "Ina jiranka" "Da gaske kike?" A rikice Adamu ya tambaye ta. 114 Maimuna Idris Sani Beli $ NA SHIGA ALJANNA.2 Tayi murmushin da ya fi kama da yake, ba tare da ta tanka ba. "Na gode" Adamu ya dinga ambata cikin kada kai har bai san adadi nawa ya fada ba, sannan da baya da baya ya dinga tafiya yana godiyar har ya fice daga soron cikin daga mata haninu.T Sai da ya gama ficewa sannan Husna ta ji kukabya zo mata a guje, tuni ta durkushe a gurin ta soke kai a gwiwa tana kokari hadiye Kararsa. Jin zuciyarta take kamar an bulbula fetur an kyarta ashana*** E sWannanwaneinsirin.arsoswne keshan sharafinsa a Kirjinta? Wa ya taba irinsa ya bata labari? Jiya ta gama karatun wani littafi wai shỉ Mafarkin Khadija, tá rantse a fili ta rantsea zuci son Adamu da take ji cikin ranta ya ninka wanda Khadija jarumar littafin ke wa mijinta Sunusi. on ide sos idavad sisd it sy sbridA Ta ci kukanta as soro ta koshi sannan ta goge ido jiki a sabule ta ikinkimi kujera da tambulan ta shiga gidasusd osanew isb ni" "B2 Idono Hajarai karaf al kantadlokacin da ta janyo ruwa ta hau wanke fuska, 115 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 "Kar dai ke ma zuwa kika yi ku ka haďu ku ka yi ta kukan?" A kufule Husna ta masa, "Kuka mu ka yi amma ba ki jiyo tumaminmu ba?" Umma ta wuce tana ce mata, "To uwar bakar Magana, in ma haukacewa kuka yi ai ku ta shafa" Husna ba ta tanka ba, don dama don ta kashe bakin tsanyarta ta fada mata haka. Yana fitowa masallaci ya canja riga ya fita ba tare da ko sallama yayi wa Hajiya wadda sarm bata yi kwanan kwanciyar hankali ba saboda halin da ta ga Adamu ciki, jiya ko abincinsa bai karba ya ci ba, illah dai ta san a gidan ya kwana. Abinda ya fi bata haushi ma shi ne, da ta kira Alh. ta yi masa wannan korafin sai ya nuna halin ko in kula. "In dai wannan banzan yaron ne mai halin canje-canje ki bar shi kawai, ni ne maganinsa" 116 Malmuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Kalaman da ya fada mata kenan wadanda haushi ya sanya ta shiru ba don wai ta sallama ba. Da safe ta yi ta zuba idon ganin shigowar Adamu bayan dawowarsa masallaci sallar asuba kamar yadda ya saba, sai ta ji shiru. Haka ta zauna cikin fargaba da ci-da-zucin kallon kofa har hantsi ya daga bata ga Adamu ba, ta lallaba ta je dakinsa sai ta tarar a garkame da kwado, nan fa ta fara tsoron ko ya koma gidan jiya ne, sai sannan ma ta tuno ko tambayarsa inda ya shiga tsawon sati ba a bata damar ta yi ba. Da hantsin Alh. da kansa ya kawo mata abinci. Ya gan ta cikin rashin walwala amma sai ya share don ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta koki. "Daga nan dorayi zan wuce" Ya kamo bakin zarenta da haka bayan ya lura cin maganin nata yayi yawa. Ta motsa baki da kyar t ace, "Me zaka yo?" Ya amsa mata 117 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 "Gidan da wadancan yara zasu zauna zan sanya a yi wa gyara, Adamu gata yayi masa yawa, jiya na yi masa maganar ya karbi mukullin ya je ya dubo... kai har maganar kudin da nace zan bashi ma bai bi ta kai ba, na 66. rasa wane irin yaro ne Adamu... Haushi ya hana Hajiya barinsa ya kai karshe, "Idan bai koma inda ya fito ba ko? Ni tun safe ban gan shi ba" "Zai dawo ne, ai giji lahira ce" Alh ya fada cikin halin ko. in kula don ya fahimci Hajiya bayan Adamu take son bi akan maganar auren nan, shi kuma jin kansa yake akan maganar auren nan babu wanda zai saurara ya tankwabe shi. Jin hakan ya sanya Hajiya jan bakinta ta tsuke, don dama ita mace ce mai kawaici da hadiye damuwa, in dai ta lura za a daga matahankali sai ta sakar wa mutum. Alh. ya gama kame-kamensa ya mike yana ce mata, ""Dorayin zan je na kula da komai, har kayan shagon zan siyo komai in zuba masa, 118 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Allah basshi idan ya zo in ba zai gode min ba ya tsine min" "To Allah tsare" Hajiya ta fada a gajarce. Adamu ya tarar Salmanu ya ci Make Up ya zama rikakken boka yadda in ba su da suka yi masa farin sani ba kuma suka san dawan garin ba, ba za a gane shi ba. Yayi tirgijijin a cikin rigunan shudin saki hade da wando, an masa tafka tafkan kwalen farin fenti da ja a goshi da kunci, haka ma kansa ya sha askin kwalkwal an adance shi ta tattoo din kan mutum. Salmanu ya canja kala daga Salmanu zuwa wani shaidanin boka duk aikin Tanimu ne. Suna tsaye da Tanimu yana yi masa lissafin mutanen da ya gayyato masa yau Salmanu ya shigo, "Ka ga akwai matar Aramman unguwarmu, wai ta ji labarin zai dauko uwarsa daga kauye, uwar tasa kuma muguwar 119 Malmuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 masifaffiya ce ga jarabar sa ido, shi ne wai take so ta zo a toshe zuciyarsa a hana shi kawo ta.... Salmanu ya tare shi cikin yamutse fuska, "Matar Alaramma kuma Tanimu zaka kawo mana? Mijinta malami sannan kuma na san ba karafa garesu ba, mu fa manyan harka mu ke so Cikin tsananta dariya Tanimu ya tare shi, "Kai matsalarka gajen hakuri aradun Allah, yo malanta ba yana kan tasa kujerar ba ne kai kana taka?" Salmanu ya sake tare shi rai a bасе, "An ji, ni fa ba zan yi harkar naira hamsin ko dari ba" "Shiyasa ai na ce ka fiye gajen hakuri, in ka ga dama idan ta zo ka caje ta dubu talatin, na rantse da Allah zata baka... abincin siyarwa fa ta ke, duk eriyar nan ba kamarta, motar doya ake sauke mata duk wata, buhun shinkafa kuma kwana biyu yake mata. ay amise Fuskar Salmanu ta washe, "A zamu tafi da ita, ta zo kawai"g Suka tuntsire da dariya suka tafa. gg 120 Malmuna Idris Sanl Bell NA SHIGA ALJANNA...2 Tanimu ya cigaba, "Sai Alh. Habu mataimakin sakataren kamafanin tabarma wanda yake son wai ka kashe masa sakataren shi ya samu ya hau kujerar" Salmanu ya doko wata katuwar ashar, "Wannan da zan iya Allah shi zan kashe" Tanimu na dariya ya amsa, "Tunda ba zaka iya ba, sai ka karbi kudinsa ka sallame shi yayi gaba, randa Kwanan sakataren ya kare sai Allah ya kashe masa shi" Salmanu ya сe, "Wannan rike shi zamu yi, in bai wasa ba Allah sai na talauta shi" "Oho maka kuma" In ji Tanimu, sannan ya cigaba, "Sai kuma Hajiya Kumbo, ita kuma Mijinta ne yayi mata kishiya a 6oye, bayan ta sakankace wani boka yayi mata alkawarin daga ita ba zai iya kallon wata mace da sunan so ko aure ba, kwatsam sai ga mijinta yayi aure a boye, bayan ta gano shi kuma yake son raina mata hankali wai amaryar zata tare, ta ce zata 121 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 zo wajenka da neman taimakon, har abada kar Amarya ta tare, ya bar ta tayi ta lilo a gidansu in ma rabon 'yan dozin ne a tsakaninsu duk tayi ta haihuwarsu a gida..." Ya sauke numfashi ya dubi Salmanu, "Ita ma wannan matar tana da Dala. "To an gama, ta kawo kuka gidan mutuwa. Suka sake kwashewa da dariya. Sai lokacin Salmanu ya kula cewa Adamu fa ya shigo da wata irin fuska wadda ta kamata a saurare shi, musamman da ya kasance duk hirar da suke ya ci magani ya ki sanya musu baki alhalin da idan ana yi ya fi kowa shan dariya, "Kai kuma fa?" Tanimu ya tambayi Adamu, da alama kuma ba jiran amsarsa yake ba, don bai jira cewarsa ba ya fice da sauri yana cewa, "Ni fa ban karya ba, bari na zagaya wajen mai shayin can" "Salma ce ko?" Tambayar da Salmanu ya yi wa Adamu kenan. 122 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Adamu da yake jin ya zo da kwrin gwiwa ya yi taku gaban Salmanu ya tsaya cikni nuna da gaske yake, "Ban taba nutsuwa da sana'ar nan da ka kira ni mu yi ba sai yau, na zo da imanina da yarda ta duka, ba mai yi muku maganar aljanu ba, ba yi muku basaja ba, ba dan koren boka ba, komai ake so na yi zan yi, don na shirya in zama ko mai zan zama in dai zan sami abinda zai shigar da Husna rayuwata, nan da wata biyu ina neman kudaden da zasu aura min ita a matata tą biyu, an min danyen hukunci a jiya an aura min Salma a matsayin ta daya...." "An aura maka Salma?" Salmanu ya tambaya cikin karaji tare da jin wani irin mugun takaici ya naushe shi a kahon zucі, Adamu ya fara naushin hannu cikin alamar fishin da yake ji yafi na Salmanu, kuma danyen hukuncin da yake son dauka zai iya fin nasa in da sarari zai samu. Ya сe, "Eh. Salma suka aura min don su nuna sun ciyar da ni na girma, ba ni na wayi gari na ciyar da kaina ba" 123 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Ganin nasa fishin ya kai haka ya sanya Salmanu rage nasa, ya kawar da kai yana kadawa, "Ban cika ganin laifinsu kamar na Salma ba..." Cikin sikewa Adamu ya tare shi, "Don me? Don in ba su aura min ita ba zata iya aura min kanta? Kar idonka ya rufe Salmanu don kana kin Salma bisa kiyayyar da na yi mata a baya, amma in neman me laifi ake ba sai an wani sha wahala ba ana samun Alh an وو gama. Ya zarce da yin kwafa cikin kufula, "КК! Аmma ba komai zan nuna masa tawa iyawar wallahi" "Ni kuma zan nuna wa iyawar" Salma tawa In ji Salmanu da haushin Salma ya sake kashe shi, wato har Adamu ya daina ganin laifinta da zargin ta yi masa wani siddabarun? In haka ne ta ina ma zai faro wa wannan matsalar tasu tunda mai matsalar bai dauke ta matsala ba? 124 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Adamu sai yi wa Salmanu duban rashin fahimta yake bisa furucinsa na nuna wa Salma iyakarta, har dai da Salmanu ya ki kara masa haske cikin raunin murya, "Ka da ka manta fa yanzu Salma matata ce Salmanu ya bugi kafadarsa cikin nuna halin ko in kula, "Oh na tuna fa! Kuma ba zan sake mantawa ba” Adamu zai yi magan Salmanu ya tare shi, "Mu share wannan hayaniyar Adamu mu zo mu yi abinda ya fi kamatarmu, ba kai kadai zaka nemi kudin da zaka auri abinda kake so ba, har ni idan na nema zai iya zama naka, saboda haka ka kwantar da hankalinka in dai matsalarka a Husna ita ce kudi to zamu taru mu yi ta nemansu ko ido rufe ne, ka cire damuwa ka ji gwarzon aminina?" Ya kare maganar da zolaya. Dole ba don Adamu ya so ba ya yi dan yake, sannan ya fitar da dariya da karamin sauti. 125 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Salmanu ya mika masa hannu suka tafa sannan suka saki ihu. "Kafin wancan Tanimun ya dawo daga shan shayin ni bari na zagaya baya na yi wani abu..." In ji Salmanu Adamu ya tare shi, "Ka zagaya baya ka sha Sigari..." "Allah ya kiyaye, ji nake na ci maka alwashin na daina tunda kai daga kauye kake ko warinta baka so. Kai dai ka zauna nan ya dawo yayi maka naka Make Up din" Dole Adamu ya dara yana bin Salmanu da kallo cikin wani irin kaunarsa, ji yake ban das hi da Husna ba shi da kowa a duniya wadanda suke iya son abinda yake so, suke kuma iya yunkurin ba shi abinda yake so. Karfe góma sha biyu da rabi daidai bakuwarsu ta farko ta zo, maimakon matar Alaramma Hajiya Kumbo ce ta fara zuwa. 126 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Salmanu na hakimce kan shimfidar buzun da suka lullbe da fatar Maciji, ya wadatu da wani irin kwarjini irin nasu na bokaye, sai muzurai yake. Adamu kuma na daga can uwar dakin riker da tiyon da suka huda bango suka zura daidai saman kan Salmanu amma sun yi wa gurin basaja da adon kayan tsubbace-tsubbace. Ba kadan ba Hajiya Kumbo ta ji shakkar wannan Boka, sannan ta ji yakinin tabbas in wannan bokan yayi aiki ba za a tarar da wasa ba. Tunda ta shigo Salmanu bai daga kai ya kalleta ba, illa ya kurawa fararen takardun gabansa idon. Hajiya sai dan nishi take na bakunta da nuna sallamawa wannan hamshakin Boka, wanda a labarinsa da aka bata an ce ba a fara yi masa Magana, shi yake fadar dukan abinda ya kawo mutum sannan ya magance masa damuwarsa. Kamar Salmanu ya san abinda take tunani ya dauko daya daga cikin fararen takardun nan ya mika mata. 127 Maimuna Idris Sani Beli Π NA SHIGA ALJANNA...2 Tun da safen suka samu kyandir suka rubuce sunan mijinta da na kishiyarta da rowan kyandir din yadda ya saje da farin takardar babu yadda za'a yi farat daya a gano rubutun. Hajiya ta karbi takardar cikin ladabi da 6arin jiki. Salmanu ya cilla mata kullin nikakken gawayi wanda suka gauraya da garin dayis. Ta hada su duka biyun tana juyawa a hannu tana kallonsa cikin rashin fahimta. "Ki bude wannan maganin" Boka ya fada mata cikin murya mara karfin sauti, sai da ma ta nutsu sosai sannan kwanyarta ta ruwaito mata abinda ya ce. Da sauri ta shiga warware kullin gawayin da suka nade da takarda, ta daga kai ta dubi Boka cikin rawar murya t ace, "Na ware Malam" Salmanu yayi shiru tamkar yana karbar wani sako daga sama, sai can ya sauke gani a kanta, "Ki barbada garin maganin nan kan wannan takardar ta hannunki" Jiki na bari tuni Hajiya ta idar. 128 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 "To karkade" Nan ma ta karkade sai ga zanen sunan mijinta da na kishiyarta ta dinga bi da kallo cikin dukan zuciya. "Ba ni nan mu gani" Boka yayi mata umarni Ta mika masa jikinta na bari, ta kasa magana. Salmanu ya kura wa takardar ido sannan ya ya mayar da kallonsa gareta, "Wane ne Usman?" Ya tambaye ta, Cikin sallamawa da rawar murya ta amsa masa, "Mijina ne' "Hadiza fa?" Sai da ta bata rai sannan ta amsa, "Ita ce kishiyar tawa' Salmanu ya dinga gyada kai nuna al'ajabi da mamaki. Hajiya Kumbo duk ta bi ta tsure. Ya sake mika mata takardar, "Ungo juya bayan takardar ki sake 99 barbada maganin nan 129 Maimuna Idris Sani Bell NA SHIGA ALJANNA...2 "Boka me ka gano? Na shiga uku!" Da kyar ta karbi takardar saboda rudewa. Salmanu y ace, "Abin babu kyan gani, amma sake jarrabawa mu ga sunan wanda zai fito" Da ta sake sai ga Usman da Hadiza sun sake fitowa, ta mika masa hannunta na karkarwa. Ya duba na wasu sakanni yana kada kai sannan ya ajiye takardar gefe yana cewa, "Lallai wadannan mutanen da gaske suke" Ya janyo wani kasko a gefe wanda ke cike da rushi ya bude wani kuttu ya duntso garin magani ya yafa wa wutar, wani irin hayaki gauraye da kauri ya tashi a dakin, shi kuma ya runtse ido yana ta faman mus-mus da baki tsawon wasu mintuna marasa yawa. Can kamar daga sama sai ga Adamu ya fara wani irin nishi a Tiyo, Ba Hajiya Kumbo da nan take suka gama siye imaninta ba, hatta Salmanu da ya kwana da sanin basajar sai da salon na Adamu ya so tsorata shi da zargin wani aljanin na gaske yayi musu kutse a aiki, amma dai haka ya cigaba da 130 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 mazewa yana gurnanin da ke kara ruda Kumbo. Sai da Adamu ya gama nishinsa can kuma yayi dif! Tsawon wani lokaci sannan ya dage ya kwararo wani ihu mai gigitarwa wanda ya sanya Hajiya zabura zata arce sai da Salmanu ya dakatar da ita da hannu tare da dora yatsa a bakinsa alamar ta yi shiru, nan ta zube jikinta na bari. Adamu ya zarce da Magana cikin nishin da ya fara da shi, "Bisa wane dalilin ka taso ni ina baccina, me yasa ku bil adama ba ku cika tausayi ba ne?" Salmanu ya marairaice murya cikin ladabi ya ce, "Wani bahagon aiki ne ya zo gabana ranka ya dade, dole na kira ka, ka zo ka sanya hannu وو ka ceci mutuncin baiwar Allah na... Kafin ya rufe baki Adamu ya amsa da watą irin dariya, ya се, "Wai Kumbo da ke zaune gabanka?" Salmanu ya dago ya kalli Kumbo wadda razana ke sa ta jin neman sakin fitsari a wajen, 131 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 sai dai can cikin zuciyarta cike take da farin cikin abinda ke faruwa, wannan sabon bokan nata da manyan aljanu yake aiki wadanda suka sanka da matsalar da ka zo da ita. Salmanu ya ce, "Ita ce ranka ya dade" "To ka fada mata ta tashi ta tafi gida, da mijinta aka hada baki aka cuce ta Salmanu ya marairaice Murya, "Ita da ta zo neman waraka wajen manya irinku ai ba kwa kora ta ba Ranka ya dade" "A taimaka min" Ta shiga maganar cikin barin jiki. Adamu ya се, "Ina buhun dankalin turawan da ya kawo miki kamun azumi?" Hajiya Kumbo ta shiga tunani. Ta tuna cewa duk wata mijinta buhun dankali yake direwa kasancewar gidansu na mutane, amma watan azumi har buhuna hudu yake direwa a raba wa makota buhu biyu, azumin da ya gabata satin kama azumin ya kawo dankalin. Nan da nan ta gyada kai, "Eh na tuna, buhu hudun nan ko?" 132 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Adamu ya amsa cikin dariya da ihu. fito?" "Yauwa su! Kin san daga hannun wa suka Ta gwalo ido tana girgiza kai, "Ban sani ba ranka ya dade" Adamu ya amsa, "Daga hannun Hadiza matar mijinki suka fito, shiyasa na ce duk abinda aka yi miki da sanin mijinki..". ce, Hajiya ta saki wani irin nishin fargaba ta "Oh ni Allah! Alh. ya ci amanata..." Adamu ya tare ta, "Duk asirin da zata yi miki ta hannunsa take kawo miki shi take bawa ya kawo miki a zuwan daga gare shi ne, amma lamfa kawai suka yi miki dukkansu, suna nan suna niyyar יי tarwatsa miki rayuwa... Sai ga Hajiya na son barkewa da kuka, "Na lura da haka wallahi, don a da Alh. komai na gindaya ba ya musawa amma yanzu ko jinjirin jaki haka ya gan shi akan yadda yake jayayya da ni" 133 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 "Ai ta gama da shi,kiris take jira ta karasa kassara ki, ko yanzu gata can na hango ta zaune gaban wani matsafi suna shirin yo miki aike... Hajiya ta dora hannu aka tana ambaton shiga uku, Adamu ya cigaba da ruda ta, "Rannan da kika tsefe kai an turo Duna ya saci gashin kanki, gashi can ana kullewa a cikin kwai za a jefa teku, in har hakan ta kasance to ke da mujiya ba bambanci a idon mijinki" Hajiya ta sake rikicewa ta cigaba da kuka haikan tana roko da hurwar a taimake ta. Sai da Adamu ya gama tabbatar da imaninta sannan ya ce mata, "Zauna ki dakata a nan, na san Aljan Cunkokuwaso za su tura ya jefa tekun, ni kuma zan tura Migadir ya kwato ya kawo miki nan ki gani" Da haka Adamu yayi musu Sallama yayi nishi ya bace. Hajiya ta kife kai wajen tana ta faman kuka, Salmanu kuma yayi kus yana sauraronta 134 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 a zuciyarsa yana saka yawan kudin da zai wafta. Damuwarta ya sanya bata kula da lokacin da Salmanu ya dauko farin kwan kazar gidan gonarsu ba wanda suke da irinsa ya kai hamsin, yadda suke wa kwan shi ne, suna tsaga shi daga kokolinsa cikin hikima da wata siririyar aska yadda ba zai fashe yayi baraguzai ba, sai su zazzage ruwan su cusa tarkacen da suke so, wani su sa gashi wani allurai, wani su cusa danyen nama wani kyanyasai, wani kuma su hada gashin da rowan kwan, sai su mayar da murfin su like da gam ko super glue yayi tamkar ba a taba bude shi ba. To Hajiya mai gashi hade da rowan kwai aka dauko mata wanda zuwa yanzu yayi wari. Salmanu yayi tafi da hannu dan janyo hankalinta kasancewar ta kife kai tana ta faman kuka shi kuma yana ta faman Magana ba ta san yana yi ba, "Magadir har ya kawo kwan ya wuce kina faman kuka, ban da abinki meye na kuka bayan kin gamu da Sarkin Aljan Shakakiriro ya shiga aikinki da kansa?" 135 Maimuna Idris Sani Beli NA. SHIGA ALJANNA..2 1GN Hajiaya ta hau múrzargido Salmanu, tana kallon SEVI nion Yà mika matad kwan ya mika mata wata tasa yana céwa fasa shi mu ganiy mesig sb Tа karba da kwatin gwiwarta eikin dokin fasawar, don Allah Allah take ta fasa shi ta san fasawar ce tarwatsa asirin da kishiyar tata ta yi mata ko take shirin yi matal isx sd sbbay eles 02 Bayan ta fasaşibazita ba hatta Salmanu sai dá ya toshe hanci saboda azabar doyi, ya dinga tarsmyahaurkarawavdashegantakas ita ma hancinta toshe tana bin fasasshen kwan da kallo?sai ta ga tabbas ma gashin kanta ne, hatta kududunen da tayidmàsa kafin ta watsa shara iyana manbandu ware baeny ism sviish oT risMalam kaytaimakebni mana, me ye abin yiryanzu? Ga sharrinsu dai an dauko shi nomeTana nuna rubab6en kwan daita fasalued nse siʻKitashi ki je gida zaki ga aiki da cikawa, Shakakiriro ya zuciya sosai, na san ba sai an bashi zabi baj ba żai wa Hadiza ba kyau ba" asyadCikini farinciki daidokita of sut itemst sgida "Allah ya saj ni ko kaslie annamimiya ma ils yayi ita ta sai wa kanta" ksnesS" qs sikioki 2136 Malmuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 "Na fada miki ba sai kin bashi zabi ba, ke dai ki dawo nan da sati guda" Ta shiga zuge jaka cikin jin kwarin gwiwa. Salmanu ya dinga satar kallonta yana tunanin ta inda zai bullo mata in ta ba shi abinda ba shikenan ba. "Malam nawa zan bayar kafin alkalami" Salmanu yayi fuska iyakar fuska, "Ki bada dubu hamsin" Ta dan ji dukan zuciya, amma da ta tuna bokan tana baya wanda ko kama kafar wannan bai ba shi kansa yana cajar sama da haka kawai sai ta zage jaka ta ciro ta mika masa, ya tura mata wani faifai ta ajiye a kai sannan ta tashi tana yi masa godiya ta fice. Sai da ta jima da fita sannan Adamu da Tanimu suka fito maboyarsu suka shiga hayaniya da ihun murna tamkar sa balla dakin. Tanimu ya dubi Salmanu y ace, "Yanzu kai Salmanu tuni ka san da wannan sana'ar ka bar mu muna ragaita a titi?" "Rabonmu ne ke nesa" Salmanu ya amsa cikin farin ciki. 137 Maimuna Idris Sani Beli NA SHIGA ALJANNA...2 Adamu kuma ya ce, "Ni kam yanzu na nade hannun riga zan fara sana'ar nan, ko kun tuba ni kam

Chapter 5 of 6