An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
MAIMUNA IDRIS SANI BELI
NA SHIGA
ALJANNA...
NA SHIGA ALJANNA...2
Na shiga Aljanna... 2
"Tashi-tashi ka taya ni jaje na haukace
Salmanu"
Cikin shasshekar kuka da nuna firgita
Adamu ya dinga dukan Salmanu wanda ke
kwance da alamun dogon bacci har yana jan
tirka-tirkan raguna, alhalin ba baccin yake ba
tsabar takaici ne ya hana shi tanka Adamu
wanda ya share guri ya fara tikar kuka tun
farkon dare.
Tun yamma da ya zo gidan ya tarar da
Adamu cikin mawuyacin hali na damuwa da
ciwon rai, ko abincin dare bai iya kai shi
bakinsa ba, hatta sallah cikin jam'i da bata
wuce shi, a jiya sai kara'in sallar isha da
magariba ya hada ya gabatar wajen karfe
goma na dare.
Abin haushi da yayi ta cizon Salmanu
shi ne, yayi-yayi Adamu ya fada masa dalilin
damuwarsa ko abinda ya birkita shi haka
amma Adamu ya kekasa kasa ya ki sanar da
shi.
4 Maimuna Idris Sani Beli
B
NA SHIGA ALJANNA...2
Damuwar ta Adamu ce ta hana shi
komawa tasu unguwar kawai yayi niyyar
kwana a nan, ba da niyyar rarrashin Adamun
ba sai dan sanin-shanun da yayi wa Adamun,
ya san da kansa in ya gama damuwarsá zai
fito ya fada masa. Sai gashi kuwa ya farkar
da shi da sigar da ta kusa sa cikin Salmanu
farkewa da dariya, amma ya kanne, ya tashi
zaune yana muttsikar ido tare da mika,
"Wai da gaske kake ka haukace
Adamu?"
Ko ma shegantaka ce Adamu ya ki
yarda da hakan, cikin hawaye da kada kai ya
amsa,
"Wallahi da gaske nake Salmanu na
haukace, kai ba ka lura ba ne?"
Salmanu ya sake murza ido yana
Karewa Adamu kallo,
"Kuma fa kamar haka ne, yaya aka yi
ka gane ka haukace?"
a
Adamu ya sake kecewa da kuka,
"Abinda nake hankali bai taba irinsa ba,
mahaukata na san sahun farko na shiga,
5 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
kaicorı rayuwata, wallahi duk cikin burikana
babu hauka Salmanu, amma ka ga Allah ya jarrabe ni da shi
Salmanu ya canja kallon dabyakedwa
Adamu saboda zaton da gaske ya haukace
din, sai tsoro ya fara kama shi, don haka ya
rasi ta cewa illa bin Adamu da kallo dokacin
da ya janyo ledar pure water ya huda ya hau
tsiyayewa a kofi ya miko masa, sUSA eeS
sedusUngò karbi ka yimin addu'a na sha kô
zarı samu kullin kirjina ya warware, ko da
ban warkė daga haukana duka ba, to wai idaň
ma iná warke illar da yayi min zata gogu ne
Salmanu? Wai zata gogu?" smas
enunSalmanu yayi tà maza ya karbi ruwan ya
hau yin mus-mus da baki yańa tofawa cikin
rtsoro,lamma yayi fuska bayan wani lokaci ya
mika wa Adamu ruwan,led umsA eweвя
"Ungo yi Bismillah ka shanye
Ba ja Adamu ya karba yal shanye ya ja jiki ya kwanta yana cigaba da hawaye.
Dakine
züciyoyinsu
iyàyicltsitleillahid
su dukarg wanda
bugawar
kunńuwansu
ilea 2
6 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
kaďai ke jiye musu, Adamu na bacin rai da
sarkewar al'amura, Salmanu na tsoro da
tunanin hanyar tserewa. Ya daga kai ya dubi
agogo sai ya tarar hudu ta karato, in ya ce fita
zai yi ya tafi gida yanzu komai yana iya
faruwa da shi ko hannun miyagu ko kuma
jami'an tsaro, kuma dai da kunya ya shiga
gida ya tayar da Hajiya y ace mata Adamu ya
haukace, in haukan karya Adamun yayi kila a
mayar da kalmar haukan kansa, idan kuma
yace zama zai yi a nan daga nan zuwa ko
wane lokaci kila Adamu ya iya ballewa da
duka.
Sun shafe mintuna goma sha biyar a
haka, ban da kuka babu abinda Adamu yake,
idon Salmanu akan sa yana tsoron ya tashi.
Can da ya ji kukan Adamun ya lafa sai ya
daga kai ya dubi agogo sannan ya mayar kan
Adamu,
"Yau ba zaka yi sallah ba ne? na ga hudu
na neman sako kai"
Cikin barin jiki Adamu ya tashi zaune,
7 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"In roki Allah me Salmanu? Husna nake
roka dama ya ba ni, kuma ya bani jiya na
tankwabe na karbi abinda kullum nake rokon
kar ya ba ni"
Tsoron Salmanu ya fara raguwa, cikin
rashin fahimta ya ce,
"Ban gane ba Adamu, ko duk a duniyar
haukan kake Magana?"
Cikin kuka da girgizar kai Adamu ya
kwashe labari ya bawa salmanu.
Shi kansa Salmanu sai abin ya bashi
mamaki, cikin jinjina kai ya ce,
"Anya? Da gaske ne zuciyarka ta fara
haukan da idan an kira shi na Allah da annabi
an yi karya"
Adamu yayi masa duban rashin fahimta,
kafin yayi Magana Salmanun ya tanka,
"Ni ban san me zan kira abinda nake
hasashe ba Adamu, abinda kawai na sani shi
ne kana son Husna kuma ba ka son Salma,
don haka abinda ka yi jiya ba zaka yi shi haka
kawai ba"
"Shiyasa ai na ce maka na haukace"
8 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Ni ma na yarda"
In ji Salmanu, wani irin takaicin Salma
na ninkaya a kahon zuciyarsa.
Har ya bude baki zai yi Magana sai
kuma ya fasa bayan wani mugun tunani ya
ziyarci ransa, tabbas in Salma bata yi wasa ba
sai ya sassaba mata kammani.
Adamu da yake jin kamar ba shi da wani
gata a yanzu ban da Salmanu a duniya kuma
shi kaďai zai iya fahimtar matsalarsa sai ya
tattara dukkan hankalinsa ga Salmanu y ace,
"Ka ce wani abu mana da zai sa naji
karfin gwiwa Salmanu"
Salmanu ya riko kafadar Adamu yana
jinjinawa cikin fuskar alhini,
"Ka share zuwa gobe, na yi alkawarin
daukar wani mummunan mataki, duk
tsinannen da ya nemi jazawa zuciyarka rudu
da hauka na rantse da Allah shi ma ba zan bar
duniyarsa lafiya ba"
Cikin tattara fata Adamu ya kurawa
Salmanu ido ya ce,
"Alkawari?"
9 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Salmanu ya jinjina kai,
"Na dauka, kai ma ka yi min alkawarin
kwantar da hankali har zuwa lokacin da zaka
ji nawa matakin"
Adamu ya koma jiki a sanyye ya kwanta
cikin dasasshiyar murya ya ce,
"Na yi"
********
Tsawon lokacin da aka ci bikin Amina
aminiyar Husna aka side, sam Husna ba ta dawalwala ko kadan, ba ma wai rashin walwala
kawai ba, duk wanda ya dube ta sai ya gane.
lallai wani murkusheshen abu ya taushe
zuciyarta da karfin hatsi, ya fi karfinta ita da
zuciyar har ya bayyana a fuska da gangar jiki.
Ba a cikin kawayenta kadai ba, hatta a
cikin gidansu ta rasa walwala a matsayinta na
mace mai kazar-kazar da shiga mutane, yanzu
ta kasalce sai son kadaici da'yan kananan
hawaye.
Matan babanta sun dan binciki
damuwarta, ba don su san ainihin matsalarta
10 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
su maganace mata ba sai don kar ace sun
ganta cikin damuwa bas u tambaya ba, wato
tambayar je-ki-nayi-ki, don haka ne ma basu
sami amsar komai daga gareta ba duk da
kuwa daidai wannan lokacin tana jin matsalar
da take ciki ta cancanci abokin tattauna ta,
zuciyarta zata babbake bata san babu ko
hakuri a a waki'ar son da ta fada ba, lallai
kenan ta nemo wanda zai taya ta nemo ruwan
da zasu kwara wa zuciyar kafin ta gama
Konewa.
Kwanan Amina uku gidan angonta
Husna ta tattara buhunhunan matsalarta ta kai
mata, bayan ta kwashe mata labari ta karkare
da Magana cikin hawaye,
"In dai yadda nake ji akan son gayen nan
haka masoya suke ji a a zuciyarsu, to ina da
tabbacin zuwa yanzu da yawan mutanen
duniya bai kai haka ba"
Cike da mamaki da alhini Amina ta
jahilci maganarta ta karshe, t ace mata,
"Ban gane ba"
Husna ta shaki hanci t ace,
11 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Eh mana, yadda rayuwa ta gaji ba
yawancin abinda kake so kake samu ba, in
dai yadda nake jin so haka kowa yake ji to
kuwa in bai samu abinda yake so din ba sai
da ya mutu, Allah na rantse miki"
Sai mamaki ya cigaba da kashe Amina,
kawai ta tsurawa Husna ido ta ma rasa abinda
za ta ce, sai juya ido da kafada kawai take.
"Abinda yake kara sakudar zuciyata shi
ne, wai duk matan da ke fadin duniya a rasa
macen arzikin da zata kwace saurayi a
wajena sai banzar kawarki Salma... shegiya
tsinanniya..."
Amina ta rufe mata baki cikin
matsananciyar dariya duk da tana yi tana rage
mata karfi kasancewar ta fahimci lallai Husna
da gaske take take, in kuwa haka ne bai
kamata ta wanko kafa ta kawo mata kukanta
ba kuma ta kasa bata muhimmanci, cikin ta
tausasawa ta ce mata,
"Kar ki rage mata alhaki don baki da
yakinin ke ya fara so ko ita, kuma shi so ai ba
ruwansa da wani kyau Husna, Salma macace
12 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
mai shegen wayo, zata iya hada kafada da ke
دو
a wajen iya jan zaren maza...
Cikin tsawa da kuka Husna ta tare,
"Wallahi karya ne ban yarda ba...., na
san so, akwai karfa-karfa cikin abinda suka
yi min.... kuma wallahi ba zan yarda ba"
Sai ta zarce da kuka.
Amina ta zurfafa a tunanin yadda zata
tunkari lamari, da gaske ne har cikin ranta
damuwar Husna ta shalle ta, Husna ba ta saba
da karya ko bata lokaci kan abinda bata
ra'ayi ba, don haka kamata ita ce duk abinda
ta yi ra'ayi a taya ta nema don da gaske take
ba da wasa ba. sbusw
Cikin bulayinta ne ma ta ji aiukawai
Adamu yana son "Rawarta, bugun eikinta
kawaf suka shirya shi da Salma tun dadama
abokin wasanta ne.
ajanyowayarta ta shigasKirám Sálma
don ita ma ta bugiscikin Snata ammaseikino2
akasita tarar da wayareakasher doleita saukesh
cikm sadudar da sanym sa jikiidóntavakan Hdsnaw
wadda ita tun dazu ta baza mata na mujiya.
6M 13 Malmuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
"Wai wa kika kira?"
Husna ta tambaya.
Kai tsaye Amina ta amsa,
"Salma сe...
دو
Husna ta banka mata harara cikin munin
fuska, kirjinta na ta faman bugawa ta ce,
"Amma dai da kin same ta kin zalunce
ni, wai ki kira ta ki ce me?"
A sanyaye Amina t ace,
"A'a bugun cikinta zan yi in ji da gaske
ne shi zata aura? Komai zamu yi yakamata
mu fara sanin wannan gaskiyar Husna"
Husna ta sawa Amina ido tana yi mata
wani irin kallo wanda ya sanya Aminar shan
jinin jikinta ta yi sararo ita ma tana kallon
Husna da fuskar nuna rashin fahimta,
Husna ta kada kai ta rausayar abin
tausayi,
"Abinda kawai na sani shi ne, Amina ina
son Adamu, sanin gaskiya zai aureta ko zai
fasa ba zai hana ni sonsa ba, don haka a bi
wata hanyar wadda ba ta shafi Salma ba, don
14 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
ni ko a lahira ba na fatan ma Allah ya hada
mu sabga daya".
Amina ta sake yin shiru cikin mamamkin
irin wannan zafin kan na Husna a yau, fada
babu gaskiya.
Can a tunane-tunanenta ta samo dabara,
"Ina kayan ankon da kika ce ya ba ki, ba
shi kayansa kika yi lokacin da suka Kuga
miki rashin mutuncin shi da Salma ko tafiya
da abinki kika yi?"
Husna ta tabe baki,
"Wallahi har zuciya ta debe ni na dire
masa abinsa sai kuma na ga asarar hakan, na
juya na tafi da abina"
Amina ta yi shewa,
"Yauwa 'yar gari, gara da kika yi hakan
ai kin ga sai ya zame mana tsanin haduwa da
shi"
Husna ta jahilce ta da ido amma bata
tanka ba.
Amina ta се,
"Da kina da lambarsa dama
kyakkayawan sakon godiya. zamu shirya
15 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
masa don bugar cikinsa mu ji inda taki
sarautar ta kwana, amma tunda babu ma sai a
tuna da, ki sami takarda 'da biro masu kamshi
ki kashe shi da baki, na san zaki iya
Hajiyata"
Husna ta 6alle da murmushin jin dan
kwarin gwiwa kadan, muryarta a bude ta ce,
"An gama, zan gwada"
Daga nan Amina tayi dabarar da suka
kashe bos din a nan saboda gabadaya lamarin
wannan murdaddiyar soyayyar ta kawarta,
aminyarta tsoro yake bata, bata taba
tsammanin Husna a irin wannan duniyar da
ake mutuwa kan son masoyi ba.
Kasancewar Husna ma'aboyiyar kaifin
kwakwalwa da iya tsara samari, wasikar da ta
rubutawa gwarzonta ta ji suga sosai, ga ta
kuma 'yar faki wadda ba yawa sai lada, rabin
shafi kwata-kwata ta ci, amma ta san in dai
akwai 6urbushin sonta a zuciyar Adamu ko
yaya son yake kamar yadda ya fara bincina
mata, to tana da yakinin sai ta shallo dukkan
sonsa da kaunarsa, sannan kasancewar Amina
16 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
ta fada mata matsayin karatun Salma, wadda
ta tsere mata don ita iyakacinta sakandare, sai
ta yi wasikar da gwanewar turancinta wanda
ba duk kai ba, don tana ja a ingilishi sosai ko
a makaranta shi ta fi kawowa sama da komai,
dalibai da Malamai kowa ya san ta akan
haka.
Da sassanyar la'asar ta so ta wanki kafa
ta kai takarda, a zuwan in tayi ruwa rijiya in
bata yi ba masai, ma'ana in ta hadu da
Adamu ta gabatar da zantukan cikin takardar
da fatar bakinta, in yaso duk ma abinda zai
biyo baya ya biyo. Idan kuma bata ganshi ba
sai ta sami yaro ta aika masa da ita.
Amma wata mace mai karbar dinkin
sunan ta da za'a yi gobe ta zo ta tsaye mata
sai da ta hada mata dinkunanta wanda ta jima
da kawowa yana kan layi, bata sallami matar
ba sai bayan sallar magariba, ita kuma ta
rantse cikin ranta wasikar da ta rubuta a
zuciyar Adamu zata kwana ba a doron tata
zuciyar ba, don haka ta shige bayan gida ta
sallo wanka ta gabatar da sallar magariba
17 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
sannan ta hau fente-fente duk da dai
kwalliyar ta fi auki a turare don rashi
tsammani za'a kawo wuta bare har wanda
tayi wa kwalliyar ya gani.
A gida tayi karyar zuwa shagon kayan
dinki ta silale unguwarsu Adamu.
*********
Duk yadda Adamu yayi Salmanu ya fada
masa inda za shi bayan sallar magariba
Salmanu ya ki sanar da shi. Ba wani abu ya
tsorata Adamu da fitar ta Salmanu ba sai
ganin Salmanu yayi wata irin shiga ta 'yan
daban zamani, har da soke wuka a kugu.
Adamu ya rikice sosai ya hau cewa,
"Salmanu 'yanci fa ba hauka ba ne, ban
biye maka don fin karfin iyayena ba balle ta
silarka na tabbata dan jeka-ka-gani, kar ka
janyo abinda za'a yi tsammanin tunkunyar
tsafinmu daya"
Salmanu ko kallon Adamu bai yi ba bare
ya tanka shi ya sa kai ya fice.
18 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Hankalin Adamu sam bai kwanta ba,
tsoron ko kashe matar ubansa da Salmanu
yake ta kirarin yi ya tafi cikawa ya kada cikin
Adamu ainun, kawai sai yayi saurin rufe
dakinsa ya tafi cikin gida wajen mahaifiyarsa
hira, abinda ya jima bai yi ba musamman a
lokaci irin wannan, shi manufarsa, idan ma
wata aika-aikar Salmanu ya je yayi ko an
kama Salmanun idan aka hado da shi zai iya
samun shaidar cewa ai dai-dai wanna lokacin
yana cikin gidansu kusa da gyatumarsa,
musamman dayake gidan nasu kafa bata
daukewa da masu siyen goro, ko wani bai
gan shi ba wani zai gan shi tare da mahaifiyar
tasa.
Salmanu na zaune a dakalin Kofar
gidansu Adamu cikin shigarsa ta Basaja
wadda idan ba farin sani kayi masa ba daga
kallo daya ba zaka shaida shi ba.
Duk da ba aikin kirki yake shirin yi ba
cikin nutsuwarsa yake, lokaci-lokaci yana
kallon hanya har tsawon fiye da mintuna
talatin. Allah ya taimake shi wadda yake jiran
19 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
karasowarta sai ga ta ya hango daidai lokacin
da aka tayar da sallar Isha a masallacin
unguwar.
Da sauri ya mike ya shiga soron gidan
wanda yake dundum da duhu ya labe. Yanzu
kirjinsa na harbawa amma ba na tsoro bane
face na fargabar kar Adamu da Sallar jam'I
bata wucewa ya fito zuwa sallar Isha ya bata
masa shiri.
Salma cike da ďoki da kumajinta ta sako
kafa soron gidan tana kokawar kunna fitilar
wayarta, tun yamma ta sami aiken guntuwar
wasika daga Adamu mai dauke da cewa,
Abin 'yar haka ne? ba ni da lafiya amma
kin kasa zuwa duba ni. To ina jiran zuwanki
bayan sallar Isha in ban ga fuskarki ba zan
iya runtsawa ba.
Ita da Anti Sa'a sun sha tsallen murnar
hakkansu ya cimma ruwa, bayan sallar isha
kuwa ta ci kwalabo ta dauko kafa ta taho ba
tare da sanin makitcin Salmanu ta ratso ba,
Adamu bai san da takardar ba kuma har zuwa
yau begenta bai yi masa yawan da zai kasa
20 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
NA SHIGA ALJANNA...2
runtsawa ba, yana kasa runtsawa tabbas
amma kuka yake sharba yana tuhumar ta
hanyar da ta bi ta shiga zuciyarsa.
Salmanu da ke labe bai bari ta kunna
wayar tata ba ya fizge wayar, lokaci guda
kuma yaya fizgi hannunta cikin zafin nama
ya jata ya makure a bango ya toshe mata baki
da hannunsa na hagu, na daman kuma ya zaro
wukar da ke aljihunsa ya dora mata a wuya,
yayi mata Magana cikin kaushin murya da
tsoratarwa,
"Bari na kashe azzaluma kafin ta kashe
wanda ta yi niyya"
Salma ta sha kwatanta yadda ake
mutuwar tsaye, amma bata taba tsammanin
haka take ba sai yanzu da ta sami kanta cikin
wannan wadin a 'yan wadanann sakannin.
Kirjinta sai bugwa yake fat-fat.
Salmanu ya sauke hannunsa da ya toshe
bakinta cikin murya kasa-kasa yace mata,
"Na rantse da Allah kika yi min ihu sai
na Burma miki wukar nan a ciki"
21 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Salma ta hadiye wani mugun yawu da
kyar, jikinta na bari ta ce,
"Wallahi ba zan yi ihu ba..... amma me
kake nufi da ni?... don Allah kar ka 6ata min
...rayuwa יל
Kafin ta rufe baki Salmanu ya kwaso
wata uwar ashar ya rusa mata, ya dora da
cewa,
"Kun ci kaza-kazanku ke da abin naki,
ke har kina da abinda za'a kwata da karfi?
Ko kyauta kika kawo min kanki zan kalle
ki?"....
Salma ta ji raguwar fargaba da wannan
kalaman nasa, don abinda ta fi tsoro kenan
fyade, gara ma ya gurza mata wukar da yake
nuna ta da ita a wuya da ace yayi mata
fyaden.
"To...to...to, me nayi maka? Allah ya
baka hakuri don Sayyidina Rasulullahi, na
bika na bi Allah"
Ba tare da Salmanu ya janye wukarsa
daga wuyanta ba ya се,
"Wanne tsubbun kika yi wa Adamu?"
22 Maimuna Idris Sani Beli
د
NA SHIGA ALJANNA...2
Hantar cikin Salma ta shiga kadawa
kirrrr! Har Salmanu na jiyo Kararta, bakinta
na sassarfa ta ce,
"Ban gane ba wallahi"
Tana rufe baki Salmanu ya tare ta,
"Zaki gane in kin ji kaifin wukar, kin ga
in kin je lahira sai ki fadawa Allah dalilin da
na turo ki can"
"Na rantse da Allah da gaske nake ban
gane ba".
Ta sake fada cikin kuka.
Salmanu ya amsa,
"Adamu ba ya sonki, kin kai shi gurin
boka ya tsafe masa zuciya, shin kin san
kuncin da kika jefa shi kuwa? Za'a iya cutata
na share mutum amma karya ne a tabа
rayuwar Adamu na kyale"
Yanzu tsoron Salma ya nunka na da, tana
fargabar ta inda aka ganta a gidan boka kuma
aka gane Adamu ta kai, sannan a daidai
wannan lokacin ta dauki muryar mai gwada
ta da wuka, abokin Adamu ne Salmanu, ta
san kuma da gaske zai iya girba mata wukar.
23 Maimuna Idris Sani Beli 1
NA SHIGA ALJANNA...2
Numfashinta sai kai komo yake tamkar
ta shide take jin kanta, sai du'a'I take Allah
ya kubutar da ita.
Salmanu ya dinga jero mata kwandon
ashar yana saukewa, karshe ya ci mata
alwashin in dai bata je ta karya asirin da tayi
wa abokinsa ba to ta tabbatar kwananta
kalilan ne a duniya.
Yana jin ya gama yi mata kashedin ya
tunkuda ta waje yana fadin,
"Bace min da gani, makira mai siffar
dutsen guga, don zalinci kuma kin ga
sambalelen yaro kin makale masa"
Kafar Salma rawa take tamkar ana kada
mata gangi, amma a haka ta suri sauri, nan da
nan sai ga ta ta bace kamar walkiya.
Salmanu ya fito kan dakali ya zauna yana
kwasar dariya har da tuntsirawa.
Ya san abinda yayi kasada ce da
zumuncin da ke tsakaninsa. da gidansu
Adamu, amma yana da yakinin sai yayi
tasirin samowa Adamu farin ciki ko kaka ne.
"Barka da dare"
24 Malmuna Idris Sani Bell
NA SHIGA ALJANNA...2
Ya ji wata zazzakar murya ta farkar da
shi lissafin dokin ranon da yake a tunanin
makomar alakarsa da gidansu Adamu, don ba
ya jin Adamu, ya san mai raba su sai mutuwa.
Ya dago da sauri ya kalli doguwar
yarinyar da ké tsaye a gabansa wadda duhun
dare bai hana shi gane ta ba, Husnan Adamu
се.
mata,
Da hanzari cikin rawar murya ya amsa
"Barkanki dai"
Cikin sakewa ta sake ce masa,
"Yauwa, ya harkoki ya ayyuka?«
A mamakance ya sake amsa mata,
"Alhamdulillahi"
Ta dan yi jim, kafin da alamun karfin
hali t ace,
"Don Allah Adamu nake tambaya"
Ya dan yi jim shi ma, har zai mike ya ce
bari a kira miki shi, me ya tuna? Oho! Sai
kuma ya fasa. A sanyaye ya kada kai,
"Ya dan fita da nisa kuma, kila ya kai
karfe goma kafin ya shigo"
25 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
Husna ta gyara tsaiwar da a bayyane ta
nuna damuwar jin Adamu ba ya kusa ne,
kamar ta rushe da kuka ta rarrashi kanta. A
sanyaye ta mika masa wasikar da ta sherowa
Adamu tana cewa,
"Kai ne abokinsa da na gan ku tare
rannan?"
Salmanu ya karbi wasikar yana amsawa'
"Eh nine, ban gane ki ba"
Husna ta dan yi hucin hadiye damuwa da
son nuna komai ba komai ba ne,
"Ka ba shi wannan takardar don Allah"
Ta fada a takaice tare da share korafinsa
na bai gane ta ba.
Ya shiga juya takardar yana saka abinda
zai ce mata, bai Ankara ba sai jin muryarta
yayi tana yi masa sai da safe tare da cewa,
"Na gode"
"To sai anjima"
Ya sami kansa da amsawa cikin
dakusasshiyar murya yana hangenta har ta
bace masa, a birkice ya sake mayar da
hankali ga kallon takardar amma azancinsa na
26 Maimuna Idris Sani Beli
,
NA SHIGA ALJANNA...2
ga tunanin yadda soyayyar abokinsa ke zuwa
a hagunce.
Salmanu ya jure boye takardar da Husna
ta kawo wa Adamu har tsakiyar dare, kuma
akan ta ne ya zauna kwana a gidan, don da
farko saboda aika-aikar da ya yi wa Salma
yayi niyyar barin gidan don bai san abinda
zata je gida ta fada ba, kila kuma Alh. ya
shiga maganar, a zo nan a same shi a titsiye
shi.
Sai da ya bari dare ya raba, Adamu ya
hau buzunsa yana kuka yana rokon Allah.
Raka'a biyu kacal yayi ya durkushe ya daga
hannaye sama cikin kuka yana cewa,
"Allah ka gan ta, sallar nan 'yar faki ce
ba yawa sai lada, gabo6ina sun yi rauni bisa
abinda ka jarrabe ni da shi, Allah ka karkato
da albarkarka da rahamarka gare ni da
zuciyata da kuma Husna da ka sa mana sonta,
Allah kar ka kwace mana sonta da ka ba mu,
27 Maimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
kuma kar ka jarrabe mu da son abinda tun fil
יי azal ba ma so
A cikin tausayi Salmanu yake amma
addu'ar nan ta Adamu tayi mugun bashi
dariya har ta tashe shi zaune, ya ce
sốKiài dan iskan ina ne da kake son kashe
ni da dariya?"
sAdámu bai kula ba ya cigaba da
addu arsa har sai da Salmanu ya furta cewa,
Kai ma ka tuna min, dazu Husna ta
kawo sako a baka"
Da sauri Adamu ya shafa addu'ar ya
dube shi cikin shakkun jin abinda
kunnuwansa suka jiye masa, ya tsurawa
Salmanu ido a birkice,
sKace me! Husna?"
Cike darjin alfahari Salmanu ya mike ya
daukowasikar a aljihun wandonsa yana
cewaid inUST İV I
oMexyeha shakkun, menene Allah ba.zaids
iya ba?i Husnagc etankawo maka wasika kumash
daganjin syaddaa takardar ke tashinshkaimshius
um sd sab statoe JABI JOBWal sa is disla
i6M28TSMaimuna Idris Sani Beli
NA SHIGA ALJANNA...2
kowa ya san sakon soyayya take dauke da
shi"
Jikin Adamu na 6ari ya rarrafo daga
shimfidar sallarsaa ya zo ya riski Salmanu.
Suka ware takarda dukkansu da dokin ganin
abinda ta kunsa, musamman Adamu, ga shi
kuma Salmanu ya kankane takardar ya hana
shi wai sai ya fara karantawa. Zuciyar Adamu
sai bugawa take saboda ganin yadda Salmanu
yayi duru-duru yana bin takardar da kallo
- cikin yatsine fuska, daga ganin abinda yake
karantawa a takardar ba mai dadin ji da gani
ba ne.
"Wai ya na ga kana ta faman tamushe
fuska kamar wanda