da Anti Sa'a fuskokinsu na
aika sakon karaya.
"A'a me ka ci? Kai da tun safe kake sume?"
In ji Alh.
Adamu ya tattara hankalinsa ga Alh.
maimakon kallon Salma wadda ta nace da mika
masa farantin abinci duk da ya ce ba zai ci ba.
"Ba na jin ci ne Alh. maltina da madarar da
na sha sun gamsar da ni, bakina babu dadi"
Karaf Anti Sa'a ta shiga maganar,
Maimuna Idris Sani Beli 134
Na Shiga Aljanna...1
"Ai ba daka ta bakin naka zaka yi ba Adamu,
ko loma biyar ne yakamata ka karrbi hatsi ka
watsa a cikinka, ga rowan zafi ma idan shayi
zaka sha"
Adamu yayi fuska,
"Tun da kin matsu kawai sai ki yi min dura"
"Wacce ni? Wannan sai dai Salma, ita zata yi
maka durar"
Salmanu ya tuntsire da dariyar da ta kara
hasala Adamu. Idon Alh ne ya sanya bai kashe
Salma da harara ba sai kawai ya shaye ya kawar
da kai.
Salmanu ya mika hannu ya karbe abincin
hannun Salma yana cewa,
"Kin ga ni ko Maltinar ban sha ba, manta da
shi ki ba ni na ci"
Dole Salma ta sakar masa abincin ta ja baya a
muzance zuciyarta cike da kaďe-kade, tsakaninta
da Allah ko hanyar son abokin Adamu ba ta
dauka ba, idan ya ci abincin shi kadai sihirin
sonta ya kama shi fa?
Anti Sa'a ta lura da wannan tashin hankalin
na fuskar Salma don haka ta dinga rarrashinta da
ido tana nuna mata kwantar da hankali.
Maimuna Idris Sani Beli 135
Na Shiga Aljanna...1
Dai-dai wannan lokacin aka yi kiran Alh. a
waya ya sa kai ya bar dakin domin ya amsa, da
sauri Anti Sa'a ta yi wa Salma inkiyar ta saki
fuskarta ta matsa kusa da Adamu.
Ba karamin karfin hali Salma ta yi ba na bin
umarnin Anti Sa'a, musamman da ta dubi
Salmanu ta ga ya aika da rabin abincin kuma har
yanzu yana kan ci.
Anti Sa'a ta fara yaudaro Adamu da cewa,
"Ni fa na zaci kun shirya da 'yar tawa har na
ji ka sai mata anko, amma yanzu takanas mun zo
duba ka kana ta faman wani shassharewa, wai ko
kallon fuskarta ba zaka yi ba bare ka ci abincin
da ta kawo maka?"
Adamu yayi fuska ya tsurawa Anti Sa'an ido
maimakon Salma da suke son ya kalla,
"Menene sabo a fuskar tata da ake son na
kalla? Ga abokina nan ya fanshe ni ya kalla, ba
shikenan ba"
Duk su biyun suka ji kamar ya rusa musu
guduma a kahon zuci, na Salma dai yafi bayyana
saboda dama a tsorace take da cewa ta zubawa
Adamu tsafaffen maganin bokan da ba ya karya,
abokinsa ya ci abincin.
Maimuna Idris Sani Beli 136
Na Shiga Aljanna...1 Sun kara rikicewa lokacin da Salamánu ya
debo murmushi ya ce,
"Ga shi yau Salma ta yi kyauwun da bata taba
yi ba, kuma ta yi girkin da ban taba cin mai dadi
irinsa ba"
"To ai sai ka yi mata abinda suke son ni na yi
mata כי
Adamu ya kara yin fuska ya fada.
Sawu a likkafa Salma ta sa kai ta fice daga
dakin, inda Salmanu da ma Adamun suka bi
keyarta da kallo.
"Babu dadi cin fuska"
Anti Sa'a ta fada cikin takaici, ta kara da
cewa,
"Duk tsiya mai sonka ya fi mai kinka"
"Me ya kawo wannan maganar?"
In ji Adamu rai a bace,
Anti Sa'a ta ce,
"Abinda ka yi ne ban ji dadi ba, Salma fa ba
neman kai muke da ita ba, kuma ba wani laifi ba
ne dan ta nuna sonka a matsayinka na dan gida
wanda ba wani abu ya mallaka ba bare ace ba
son Allah da annabi take maka ba, ka je ka tuna
wannan".
Maimuna Idris Sani Beli. 137
Na Shiga Aljanna...1
Tsaki kawai Adamu yayi ya kawar da kai.
Hakan ya sanya Salmanu yin shiru alhalin da yayi niyyar saka baki.
"Ina ankon nata"
Ta tambaya.
Da sauri Salmanu ya kalli Adamu yana dokin jin Karyar da zai zabga.
Kai tsaye Adamun ya amsa,
"Wa yake ta wani anko? An sace shi a nan
inda hadarin ya faru. Ai maganinta kenan ma da
na ce ta zo ta karfa ta ce min sai ni zan kawo
mata, Allah kara"
Murmushi kawai anti Sa'a ta yi ta basar da
zancen suka kamo wani, har lokacin ziyara ya
kusa karewa sannan ta yi masa sallama ta tafi.
A waje ta ci karo da Salma zaune a baranda
cikin damuwa. Ta ce mata,
"Yi maza ki kara goga hodar ki je ki yi masa
sallama kar ki damu"
Cikin sanyin jiki Salma ta goga ta shiga
dakin, tana rike d karfen gadon Adamu t ace,
"To yaya Adamu zamu wuce, Allah kara
lafiya"
Maimuna Idris Sani Beli 138
Na Shiga Aljanna...1
Ya dago ya dube ta fuskarsa babu yabo babu
fallasa ya dago ya dube ta, ita kuma ta sakar
masa wani murmushi, sai ya ji wani dum! Tun
daga idonsa har cikin ransa, amma dai bai bayar
da maza saboda canjin da yaji ba, cikin nutsuwa
ya amsa mata,
"To sauka lafiya, na gode"
Ta dan yi dum! Da zaton bai kalle ta da kyau
ba, musamman da yake ya kawar da kai. Amma
babu yadda ta iya haka ta juya tana ficewa.
Salmanu ya bi ta da kira,
"Ki zo ki tafi da wannan abincin da yaki ci
kin ga yau za'a sallame mu"
Salma ko ta juyo bare ta nuna alamun ta ji
abinda yake cewa.
Adamu ya saba tsayuwar dare, amma yau bai
yi niyyar tsayawar ba dan har yanzu jikinsa ba
kwari, sai dai kuma baccin ya gagari idonsa da
ma zuciyarsa gaba daya, wadda ta kuntkce
iyakar kuntacewa, haka kawai ransa ya dinga
mugun baci cikin daren nan ba tare da dalili ba,
Maimuna Idris Sani Beli 139
Na Shiga Aljanna...1 ya kuma rasa wa yake jin haushi ko kuma abinda ke bata masa rai. Haka kuma Salma da Husna suka dinga tsere cikin zuciyarsa suna nuna masa kansu.
Ya san cewa shi ma'abocin tunani ne, amma
na Husna zalla! Salma ba ta taba samun ko a
bonus ya zauna musamman ya tunana ta ba, tunaninsa a lokutansa na rana na yadda zai
mallaki Husna ne da mafarkin yadda zasu shifida
rayuwarsu, tunaninsa da lokutansa na dare na
mika dukkan imani ne ga ubangiji da rokonsa ya
mallaka masa ita yana mai cike da fatan Ubangiji
ba zai juyar da rokonsa ba saboda haka yake yi
cikin dadin rai na jiran lokaci.
Amma yau komi ya canja, shi da zuciyarsa
neman sa karfi suke su bar Allah, ba don su sami
Husna ba sai dan su sami Salma ba tare kuma da
sun dena son Husna ba, abin da bayar da
mamaki!
Fiye da rabin dare haka yayi ta juyi. kan
katifarsa rayukansa babu dadi suna kuma ta
damfara masa kala-kalar mamaki. Bai tashi yayi
sallar ba bare ya fadawa Allah, bai ma yi
sha"awar hakan ba saboda kasala da rashin dadin
Maimuna Idris Sani Beli 140
Na Shiga Aljanna...1
zuciya, kai da ma rashin tabbas din in ya tashi
me zai cewa Allah? Shi da ya shafe watanni yana
neman Husna a wajensa yau kuma sai ya
durkusa neman abinda baya so wato Salma? Ita
wadda yake so ya kai ta ina, kuma Salman ma
yaya zaı zai yi da ita?
Duniyar ta taru tayi masa zafi har karshen
dare, musamman da ya Ankara duk yadda ya so
ya nesanta ransa da kKawancen Salma hakan yaki
samuwa, kara haka muhalli take mai shegen
zurfi a cikin zuciyarsa. Sai ga shi zaune da kuka
shaбe-shabe da hawaye har da sauti, yana yi
yana ambaton,
"Na shiga uku!"
Ya ci kukansaya koshi,, amma Salmanu da
ke kishinire kan Kafet yana sharar bacci bai gan
yana yi ba.
Kasancewar ba'a sallamo su kan kari ba neya
sanya shi kwana a nan, abinda ya cewa su Hajiya
kenan, amma gaskiyar ita ce, sammakon aikinsu
suke son dokawa, a cewar Salmanu, ko babu
kudi yakamata su fara aikin da ba kudin yake
bukata ba.
Maimuna Idris Sani Beli 141
Na Shiga Aljanna...1
Musamman Adamu ya tashi zaune yana
zungurinsa cikin kuka.
A firgice Salmanu ya farka ya tashi zaune,
"Adamu jikin ne?"
Adamu ya sake carkewa da kuka,
"Zuciyata 'yar ta'adda ce Salmanu, ta kwaso
ta'addanci ta kawo wa raina, sun hana ni bacci
da Alama ma har karshen rayuwata suke bukatar
kar na runtsa"
Salmanu duk da bai gama fahimtar Adamu ba
fuskarsa ta nuna iyakar damuwa, ya ce,
"Wai me ya faru?"
"Wai Salma mu ke so"
Ya amsa cikin shassheka.
Salmanu ya sake tare gira nuna alamun rashin
fahimta,
"Kai da wa?"
"Ni da banzar zuciyata mana"
Kamar Salmanu zai tuntsire da dariya, amma
har ga Allah ya ji tausayin Adamu musamman
yadda ya ga yana kuka da hawayensa, a sanin da
yayi masa jarumi ne daidai misali, kadayake shi
halittar so na saurin sanya shi kuka, haka wancan
Maimuna Idris Sani Beli 142
Na Shiga Aljanna...1
neman auren da ya taba rakitowa karfi da yaji ya
mayar da shi wani Baure.
Ya jima yana kallonsa cikin nazari sannan ya
tanka,
"Da mamaki gaskiya, to me ya janyo hakan?"
"Oho! Nima na sani! Zagi nake so in rusa
amma na rasa wanda zan zaga, ni ko zuciyata da
haka kawai muka rakito son abinda bai cancanta
ba? Allah ya tsine wa Salma wallahi, ni ban san
abinda zan so a ita ba"
Ga dariya ga kuma son yin nazari suka taru
suka murkushe Salmanu, sai ya hada su duk
biyun yana ji das u,
Cikin tsananin dariya ya ce da Adamu,
"Jiya Salma ta sako kwalli? In ta saka sai mu
yi tsammanin Kifil ta sako maka"
"Allah ya isa ban yafe ba wallahi"
Saļamanu ya sake tuntsurewa da dariya yayin
da Adamu ya sake sakin shasshekar kukan da ya
tsayar da Salmanu dariyar da yake,
"Wai baka yi bacci ba? Na san ka da sallar
dare yau me ya hana ka? Ai da ka kai wa Allah
karar Salma yayi mana maganinta"
Ya kara da tuntsirewa da dariya.
Maimuna Idris Sani Beli 143
Na Shiga Aljanna...1
Adamu ya tsayar da hawaye yana duban
Salmanu,
"Ka bar mayar da lamarin nan wasa Salmanu,
wallahi da gaske nake zuciyata ta ci amanarmu"
Sai abin ya fara bawa Salmanu mamaki, yayi
suguri tare da laluben tashar da zai kamo, amma
ya rasa har lokacin da ya ga Adamu ya mike
daga kan katifarsa ya fara kaiwa da kawowa a
tsakiyar dakin, Salmanu ya daga kai ya bi shi a
kallo yana sauraronsa a nutse,
"Lallai akwai wani abu da ke shirin faruwa da
mu ni da rayuwata, abu mafi daure kai shi ne, ta
inda makomar Husna zata bullo a rayuwar tawa,
abu mafi muni shi ne kaddarar rayuwata ta
zamanto babu Husna cikin rayuwar, duk da ina
cike da yakinin da wahala Husna bata zamto
mata gare ni ba...."
"Me ya kai ka cin wannan alwashin don
Allah"
Salmanu ya tare shi cikin mamaki da al'ajabi
tare da zaton kamar ba cikin hayyacinsa yake
ba"
Adamu ya amsa cikin murmushin yake,
Maîmuna Idris Sani Beli 144
Na Shiga Aljanna...1
"Akwai kyakkyawar alaka tsakanina da
Ubangjina Salmanu, in dai na yi masa irin rokon
da na yi akan Husna yana ba ni abinda na roka,
shiyasa nake cike da fatan kutsen da Salma ta yi
cikin zuciyata ba zai hana ni zama mijin Husna
ba"
Har yanzu Salmanu cikin mamaki yake, sai
ma ya rasa abinda zai ce.
Adamu ma ya kulle hira daga haka, ta hanyar
ficewaya dauro alwala ya tayar da sallah.
Yayin da Salmanu ya koma ya kishingida.
Duk sammakon ficewar da suka doka sai da
Salma ta riske su da farfesun dubiya ga Adamu.
A bakin kofa suka yi kacibis da Adamu
bayan Salmanu ya fice waje, duk suka dubi juna
da wani bakon kallo wanda ba su saba shi
tsakaninsu ba, a cikin wasu sakanni kalilan,
Salma ta riga shi tankawa,
"Sai ina da sassafen nan?"
a
Ya so ya tara gira ya kuma daure murya
amma sai ya ji kasa. Ya jima bai tanka ba cikin
Maimuna Idris Sani Beli 145
Na Shiga Aljanna...1
kallonta a sassauce sannan ya nisa cikin sanyin
murya yа се,
"Ke ma me ya fito da ke da wannan
sassafen?"
Ta fara kokarin shiga dakin da yake son
rufewa kamar zata ture shi, da sauri ya bata
hanya sannan ya bita cikin dakin yana sauraron
amsar da take ba shi,
"Dan abin sashe baki na kawo maka a
matsayinka na maras lafiya"
"Uhm"
kawai ya iya tanka mata da 'ita.
Ta zauna kan kujera shi ma ya nemi
dandaryar kafet ya zauna suna fukantar juna,
"Ya jikin?"
Ta tambaya tana dubansa kai tsaye.
Shi ya kawar da nasa idon ya amsa,
"Alhamdulillahi"
Ta cigaba da kallonsa tana son kore mamakin
sauyawarsa don ita ta san dalilin sauyawar,
"Kuma daga fitowarka jiyan nan daga asibiti
Yaya Adamu sai ka kwashi jiki ka fice yanzu da
sanyin safiya ba zaka bari ka warware ba? In
Maimuna Idris Sani Beli 146
Na Shiga Aljanna...1
baka damu da lafiyarka ba fa akwai irinmu da
muka damu da ita"
Yayi kokarin fada mata mai dací ya ji
harshensa ya kulle, mai dadi yake son furtawa
zuciyarsa kuma tana kyashi, don haka ya kyale
aka yi biyu babu.
"Yau wai ya na gan ka duk a sanyaye?"
Ta tambayae shi cikin dariyar da biyu.
Ya dago kai ya dube ta kawai, amma bai
tanka ba.
Haka ta yi ta 'yan sambatunta yana bin tad a
ido hart a sauke kular farfesunta ta samo filet ta
zuba masa ta kai masa har gabansa,
"To dan taba wannan tunda sauri kake in ka
dawo ka Karasa sauran"
Ya dubi agogo sannan ya mike yana cewa,
"To bari na kira Salmanu ya taya ni"
Ta yi kokarin shan gabansa,
"A haba dai ka ci mana ba sai ka zuba masa
wani ba tunda farfesun da yawa?"
Fuskarsa ta dan nuna damuwa duk da yana yi
mata fada kar ta batawa Salma, ya kewaye ta ya
nufi kofa yana cewa,
Maimuna Idris Sani Beli 147
Na Shiga Aljanna...1
"Ai ba za'a yi wasa tare ci bamban ba, bari
dai na kira shi"
Ta bi shi suka bar dakin tare tana cewa
"Shikenan, ni ma zan koma Allah ya kara
lafiya"
Ya amsa cikin fara'ar da Salma ba ta taba
gani a wajensa ba.
A kofar gida suka tarar da Salmanu zaune
kan dakali, suka gaisa da Salma ta wuce, shi
kuma Adamu ya shi cikin gida suka fara
kwasar garar farfesu.
Wai sai da suka ci suka side sannan Salmanu
ya ce cikin zolaya,
"Mu fa samari a irin wannan kwadayin namu
ake neme mu,'ka san mata da barbade-barbade"
Da takaici ya kulle Adamu sai ya rasa da
abinda zai fanshe ie kai wa Salmanu wani
wawonkmari, Allah taimake shi ya kauce yana darrya
"Kai wallahi kwankwararren mugu ne, ka san
da hakan sai da muka cinye zaka fada min?"
Salmanu yа сe,
Maimuna Idris Sani Beli 148
Na Shiga Aljanna...1
"Kai ma yakamata ka san hakan don kai
kadai ka san abinda kake ji a kirjinka game da
Salma"
Sai kuma Adamu ya ga gaskiyarsa, amma
daga daren jiya zuwa yau zuciyarsa ba ta da
zabin tunani na kanta sai abinda aka zaba mata,
ko ta fara sai ta tsinke, don haka yanzun ma
tsinkewa tayi daga gaskata Salmanu da ta fara.
Sai Salmanu ya canja bari,
"In muka fara sana'ar nan zaka ce na sanar da
kai, zaka gane halayen mata da yawa"
Adamu dai yayi shiru, daga shi har zuciyarsa
ba a nutse suke ba, ko ragon tunani ba za su iya
ba bare su yi wanda za'a yaba.
Sati daya a tsakani Adamu na shan wahala
iyakar wahala, tun daga zuci har zuwa gangar
jiki. Duk wáni tsari da fata wanda yayi shekaru
yana shiryawa a matar aurensa da iyalinsa cikin
sati daya sun bi ruwa. Zuciyarsa ta zama fanko
babu wani tanadi a cikinta sai jiran tsammanin
abinda rayuwa zata zabar mata.
Maimuna Idris Sani Beli 149
Na Shiga Aljanna.....
Zuciyasa ta bude makeken fili ta share a son
Salma ko ciwon shigowarta rayuwarsa, Husna na
can loko sakaye da tata matsananciyar kaunar
wadda ya fara jin yawa ne da ita kawai, amma
tabbas zuwa yanzu ba ta da tasiri, tare da yakinin
rashin tasirin nata nakasu ne a kulliyar tasa
rayuwar. tS ts RO
Abin ya zo masa da sauki ne, kasancewar
tsawon satin suna ta fama da kujiba-kujibar
harkallar da suka cacimowa kansu, shiyasa dare
kawai yake mallaka yayi kukansa yayi rokonsa
ga ubangiji kuma ya tunana abinda zai iya
tunanawa a mafiyayyen son
KOIS
Salma da kuma dan
asalin son Husna. se sbnsw ty na sied sd
Sun gyara muhallin da zasu fara bokancinsu,
yanzu suna cikin atisaye ne na dabarun karbar
kostomomi yadda bokayen gaske suke, da kuma
koyar rufa idon da zasu dinga yi wa maziyarta,
ga Adamu kenan wanda bai san kan garin ba.
Zuwa yanzu dai ya haddace rufa idon da ake
da kwai, Tiyo, kyandir da kuma karkashi.
Sun samo wani abokinsu takadari irinsu mai
suna Tanimu, tafiyar ta koma ta mutum uku,
Salmanu ne Boka, Adamu zai dinga aiki biyu,
Maimuna Idris Sani Beli 150 ls8 in62 ainbI snumisM
Na Shiga Aljanna...1
muryar aljanu yayin da yake boye, in ya bayyana
kuma ya zama dan kore ga Boka, Tanimu kuma
shi ne mai nemo kostomomi, wataran kuma yayi
shigar burtu a zuwan kostoma ya yi ta koda boka
a gaban bakin kostomomi, sun shirya in harka ta
kankama zasu nemai karin yara.
Yadda suka dauko tafiyar sun hango mata
samun tsabar kudade da nasarori, don haka
dukkansu hankalinsu kwance suke komai.
********
Ranar juma'a da yamma yana zune a dakalin
kofar gidansu zuciyasa a mugun kuntace, ya
dinga ayyana, ina ma shi yaron goye ne, tabbas
yau da uwarsa ta shiga uku da tsinannen kukan
da zai balle mata hancinsa, a yau sai ta
gwammace bata haife shi ba: Kuma da girman
nasa ma ya so ya kwantanta har ya shiga daki ya
fara gwaji, amma da ya fahimci aikin baban giwa
yake babu wanda ya san yana yi kawai sai ya
share hawayensa ya fito waje yana rarraba idanu.
Kamar daga sama ya hango Husna ta nufo shi
kai tsaye, ta ci kwalliyar da bai taba ganinta
Maimuna Idris Sani Beli 151
Na Shiga Aljanna...1
cikin irinta ba, kai bai ma taba ganin wata 'ya
mace mai daura zani a hannun hagu ta yi ba.
Kawai sai ya saki baki yana kallonta cikin
matsanancin bugun zuciya har ta karaso gare shi,
sannan ne ya lura tana dauke da wata leda
kunshe da kaya.
Ya sauke wata wawuyar ajiyar zuciyar da ya
so hadiye ta amma ta sanya masa karfi, ya kawar
da kai cikin jin gaba daya ma ya san ya gama
bayar da maza.
Da sassanyar muryarta ta yi masa sallama.
Ya amsa da tasa dakusasshiyar muryar ba tare
da ya dube ta ba, ya kuma rasa dalilin da ya sa ya
kasa duban nata.
"Ranka ya dade wannan gimbiyar taka kuwa
tana gari? Na ga ba ka nemi dinkin nata ba gashi
kuma tun jiya muka fara bikin"
Ta fada cikin matsananciyar fara'ar da tayi
awon gaba da dukkan fargabar da ke kakale a
zuciyarta
Cikin kumaji ya juyo yana dubanta kai tsaye, kirjinsa na dakan uku-uku amma karfin halinsa
ya gama bayyana ilahirinsa, yayin da soyayyarta
ta fito daga sakon da kaddara ta bayar da ajiyarta
Maimuna Idris Sani Beli 152
Na Shiga Aljanna...1
tayi awon gaba da ta Salma wadda ta yi gida ta
tare,
"Duk wata gimbiya ai bayanki zata bi ranki
ya dade"
Ya fada cikin sanyin murya yana yi mata
kallon da shi kansa ya san karya ne a ce bai
bayyana tsantsar kaunar da yake mata ba.
Ta dora dan alinta a kirji tana bude da baki
cikin shauki da yi masa kallon mamaki, amma
bakinta ya kasa furta kalma,
Ya kada kai mai nuna tabbatarwa,
"Na rantse da Allah dama kayanki ne
Ta ji tsaiwa na neman gagararta, sai ta doge,
ta rausaya kai har yanzu ta rasa bakin Magana.
"To yaya hidimomi?"
Da kyar cikin sarkewar numfashi yanzu ta
daure ta tanka,
"Alhamdulillahi, komai na gudana yadda ake
So
"To masha Allah, dama yanzu da nake zaune
tunanin yadda zan riske ki gidan bikin nake"
Ta sake dubansa galala.
Shirunta ya cigaba da bashi karfin halin
Magana, musamman yadda take dubansa cikin
Maimuna Idris Sani Beli 153
Na Shiga Aljanna...1
sanyin jiki yana da yakinin tabbas ita ma So yayi
mata wawurar da yayi wa zuciyarsa da ilahirinsa.
"Zuwa yanzu na gama juriyar hadiye
soyayyar da zuciyata take miki, in ban samu na
furta ba ina da tabbacin zamu iya shari'a da
zuciyar"
Tamkar jiri zai tika ta da kasa ya fasa, garin
kuma ya dauki haramar zagayawa da ita.
Cikin haka ta kwato furucin,
"Ni ka ke so?"
Ya amsa,
"Menene na shakka?"
Ta yi saurin girgiza kai.
"Ba shakka nake ba, amma me yasa sai na zo kofar gidanku zaka fada min? ka ragewa son da
ka ce kana yi min daraja"
Ya girgiza kai cikin sanyin jiki,
"Kar ki fadi haka, son da nake miki ina da
yakinin ba a taba irinsa ba, amma sai jiya na san
gidanku kuma a yau din nan naked a niyyar
zuwa"
Farin ciki ya rufe Husna, sai ta kasa tankawa.
Suna tsayen nan kowa sai numfarfashi da
murmushi.
Maimuna Idris Sani Beli 154
Na Shiga Aljanna...1
Kwatsam sai ga Salma tamkar an jefo ta, ita
ma ckin kwalliya tana sanye da irin kayan dake jikin Husna.
Adamu na ganinta ya ji tamkar an ruguzo
masa dutsen dala a kirji, jikinsa yayi sanyi kalau,
zuciyarsa kuma ta dakata da zabі,
Aka yi gaisuwar mutumci tare da ambatar
sunan juna tsakanin Husna da Salma na shaidar
an san juna, kai tsaye kuma Salma ta fara gabatar
da Adamu a wajen Husna a matsayin dan
uwanta, sannan ta zarce da cea,
"Kuma shi ne wanda zan aura in Allah ya so"
Duk da Husna macace mai siyasa, amma
siyasar tata ta kasa galaba a wannan muhallin,
sai da idanunta suka kankance suna shirin fara
zubar da hawaye, ta bi Salma da kallo wadda
fuskarta ta nuna alamar da gaske take. Da ta juya
ta dubi Adamu shi nasa arzikin ma sai ya ci uban
na jiya, domin kada mata kai yayi cikin
tabbatarwa ya kuma amsa mata da baki.
"Haka ne, za mu yi aure cikin kankanin
lokaci"
Maimuna Idris Sani Beli 155
Na Shiga Aljanna...1
Husna ta dauke kai daga kallonsa lokacin da
wani malalacin hawaye ya sulmiyo mata ta yi
dabarar goge da mayafi.
Ko Adamu ya san tarkon sonsa ta fada ne
shiyasa takanas ya shiryo mata wannan cin
fuskar?
Sai ta daga kai ta cigaba da tsura musu ido su
duka dan ta gane siyasar ce, cin fuska ce ko
kuma iyakar gaskiyarsu kenan?
Kamar sun manta da ita sai suka lula cikin
hirarsu da ke bayyana son da suke wa juna kai
tsaye.
Zan cigaba a kashi na biyu.
Taku Maimuna Beli
Ga kadan daga littafina mai zuwa nan ba da
jimawa ba.
RIGAR SILIKI..
"Gwajin HIV?"
Maimuna Idris Sani Beli 156
Na Shiga Aljanna...1 Mujahid ya jaddada cikin kallon likita da haushi da kuma mamaki.
Likita ya kada kai yana tsura masa ido cikin tabbatarwa da nuna babu fa canji.
"Haka na ce
Mujahid ya cakumi wuyansa kamar zai gwara
kansa da bango, amma sai ya sake shi cikin huci
ya shi hargagi,
"Haka ka ce din addini ne, ko fadar Allah ce
da ba'a gogewa?
Likita ya shiga gyara wuyar rigarsa da
Mujahid ya cukwikuya, fuskarsa na son nuna
hakuri da shanye damuwa, ya dubi Mujahid da kyau ya ce,
"Abinda ka yi bai yi maka kyau a zamowarka
lauya ba, yanzu in na tafi neman hakki bisa
wannan cakumar da ka yi min, me kake
tsammanin zai biyo baya... a kan aikina kake cin
zarafina?"
Mujahid ya tare cikin hargagi,
"Komai ma ya biyo bayan mana, ka tafi kotun
duniya in ka so. Ban da kai dan iska ne, matar
auren zaka kawo wa maganar gwajin HIV? In
zargin hakan ne me yasa ba zaka ce ni mijinta
Maimuna Idris Sani Beli 157
Na Shiga Aljanna...1
zaka gwada ba? In dai ba shirin tozarta min iyali
dama ka yi ba"
Likita ya dinga duban Mujahida cikin takaici,
kawai sai ya watsa masa sakamakon gwajin HIV
din da suka yi wa matarsa Binta.
"Gashi nan, ai yanzu ma bata baci ba, in ka
gama duba wannan kana iya zuwa Lab kai ma
mu gwada ka"
Jikin Mujahid a salube ya shiga dakin da
Binta ke kwance. Bai tarar da Salima ba sai
Binta kawai zaune kan gado ta kwanta jikin filon
da ta jingina da bango.
Fuskarta nan nuna farfadowa daga cuta,
idanunta sun yi zuru-zuru, sai dai fa ko kadan
babu wani annuri a tare da ita wanda zai sa a zaci
tana cikin tashin hankali ko kuma nadama,
kallon iskar da ta saba wa Mujahid da shi ta
karbe shi yau ma.
Shi yau tasa fuskar babu walwalar da ya saba
tarenta da ita duk irin yadda ta kai ga bori,
hasalima bata taba ganinshi cikin bacin rai irin
Maimuna Idris Sani Beli 158
Na Shiga Aljanna...1
na yau ba tun saninta da shi, amma a hakan ta
debe shi ta watsar.
Ya ja kujerar gaban gadon ya zauna yana
mika mata takardun da likita ya watsa masa
cikin kallon fuskarta kai tsaye.
A wulakance ta karbi takardar ba tare da ta
duba ba ta yasar gefe, kuma cikin shan kamshi ta
dube shi da kyau ta се,
"Ni ya fara kawo wa na gani kafin ya baka"
Sai ya sake dubanta cike da mamaki, ya ce,
"Kin kuma duba takardar kin ga rainin
hankalin da take dauke da shi?"
Ta sake watsar da kai gefe tana cona baki,
"Na gani, ai ba rainin hankali ba ne, iyakar
gaskiyar kenan"
Yanzu duban mahaukaciya yake mata.
Dan ta nuna masa da hankalinta ta juye ta
dubi kwayar idonsa fes! Ta ce,
"To wai kai meye na tashin hankali don an ce
ina dauke da cutar kanjamau? Ko ka manta tuni
ka ci alwashin ko yaya zan kasance kana so? Ai
baka zabi in na zo da kanjamau baka so ba, in
kuma zaka zaba yanzu ma bata baci ba"
: Maimuna Idris Sani Beli 159
Na Shiga Aljanna...
Mujahid ya jima da hankalinsa tsakanin Kary
da gaskiya a tunani da hasashe, sai can ya mike
cikin nuna yakini da kumaji ya ce,
"Na tuna an yi hakan, ban zabi kanjamau ba
amma yanzu na zaba... nan gaba ma in zaki zo
da abinda yafi kanjamau ke da su duk ina so..
kar ki damu, ki ji sauki ki zo mu koma gida mu
cigaba da jinya... in ma lahira kika tafi zan nade
Kafar wando na bi ki"
Rigar Siliki...!!!
Sadaukarwa ga Mujahid Muktar Misau.
Maimuna Idris Sani Beli 160
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke