maimaita
tambayarsa cikin fishi.
Bayan sun shiga ma Adamu na neman guri
musamman ya zauna sannan ya fito da kudin
don ya san ba karamin aikin Salmanu ba ne in
Maimuna Idris Sani Beli 109
Na Shiga Aljanna...1
Barnar da yayi wa kudin ba ta yi masa dadi ba
yayi masa mahangurba yanzu.
Ilai kuwa, hana shi zama Salmanu yayi sai
ture shi yake yana hayaniya.
Haka dai ya daure ya fito da ragowar kudin,
sai ga shi dubu uku, wato ya ba Husna dubu
takwas.
Salmanu ya kasa Magana don haushi, sai
kawai Adamu ya basar ya ce,
"Mu cancana wannan mu yi da su, na san
albarkacin sadaukarwar da na yi wa soyayya
وو
zaka ga Allah ya buda mana....
Bai kai ga rufe baki ba Salmanu ya sakar
masa wani wawan naushi a ciki, wanda ya
sanya shi zubewa kasa wanwar a sume, jini na
fitar masa ta hanci.
Ko kadan Salmanu bai yi nadama ba, domin
neman guri yayi ya zauna yana ta kunno ashar,
"Dan iska, wannan dukan ma ka
sadaukarwa soyayyar"
Maimuna Idris Sani Beli 110
Na Shiga Aljanna...1
Ba a son ran Salma ta bi Anti Sa'a unguwar
da ta gayyace ta ba saboda saka ran Adamu
yana dab da iso mata da ankon da ya sai mata,
kamar yadda ya sanar da ita. Ta yi gardamar
zuwa unguwar, ita ma Anti Sa'a ta yi lallashin
har sai da ta kai ga zagi sannan Salma ta
hakura ta shirya suka tafi.
Anti Sa'a na ta faman mita,
"Banza ce ke wallahi, na rantse miki da
Allah idan muka je muka dawo, zai yi wahala
Adamu ya kwanta bacci ba tare da ya dawo ya
nemi inda kike ba"
Wasi-wasi da mamakin duniya ya ishi
Salma, bayan wani tsantseni da bai taka kara
ya karya ba wanda yake kawo wa zuciyarta
shawagi.
Antinta ta wayar mata da kan inda zasu kai
Adamu, gidan wani boka ne mai aiki kamar
yankan wuka. A duniyar soyayyar Salma
Kauna bata ce haka ba ko da kuwa haramci ya
kau, to amma dai tunda mutuwar yawa kaka ce
sai ta bi ayari, a yadda Anti t ace mata duk
matar da ba kai mijnta ko saurayinta gidan
Maimuna Idris Sani Beli 111
Na Shiga Aljanna...1
boka a wannan marrar to tabbas ita take zaman
hakuri da shi.
Da alama kalaman karfin gwiwa ne Antin
ke mata, amma tsoronta ya ci dubu sai ceto,
don ta shafa karfin gwiwar ta rasa.
"Kuma mutane ba zasu ga bekena ba idan
aka gan ni budurwa wai na kai saurayi gurin
boka dan ya so ni?"
Ta furta cikin rawar murya bayan ita da
zuciyarta sun gama sakankancewa sun shiga
uku.
Anti Sa'a ta tuntsire da dariya tana yi mata
kallon mamaki, ta ce,
"Lallai Salma kanki a tukunya yake har
yanzu. Shin baki san yanzu 'yammata ma sun
fi matan aure gane aikin boka ba? Zura ido ki
kirga min matan aure da 'yammata in mun je"
Da haka Salma ta saduda ta bayar da gari,
yayin da bangaren shirya mafarki a zuciyarta
ya lula shirya mata auren Adamu da kama mata
shi a hannu yadda zai amince su shirya iyali
masu kyau da soyayya.
A can cikin kauyen Bunkure suka iske gidan Bokan. Kamar yadda Anti ta labarta
Maimuna Idris Sani Beli 112
Na Shiga Aljanna...1
mata yammata sun fi matan aure yawa a
wadanda suka tarar a alayi, sai ko dima-diman
motocin da suka cika farfajiyar unguwar
bokan. Da Salma ta tambayi Anti Sa'a game da
manyan motocin sai ta amsa mata da cewa, ai
motocin 'yan siyasa da 'yan kasuwa ne, don ko
'yan siyasa sun fi mata lakantar zuwa gurin
boka da matsafa, ta kare da cewa, "Mata na
hada kafada da 'yan kasuwa da kuma 'yan
sane"
Sai Salma ta ji zuciyarta ta yi wani irin
rauni, kamar hawaye ya zubo mata jin cewa
har da 'yan sane tana hada kafada ba ma 'yan
kasuwar ba, kai! Maza ba su yi ba aradu tun da
ba sa abinda ake so sai an shako su ko an biyo
musu ta bayan gida.
Ta bar damuwarta a zuci da fuska kadai, ba
tare da gangar jikinta ta kasa aikin bin Anti
Sa'a ciki suka hau layi a bencinan dake jere a
soro cike da mata. Akwai kuma wani Katon
soron wanda maza zalla ke bin nasu layin.
Salma na ta rarraba ido tana shan kallon
kosassun matan da idan ta gan su a gari sai taci
layar duk inda matsala take ba su san ta bare su
Maimuna Idris Sani Beli 113
Na Shiga Aljanna...1
je gurin boka neman warakarta, a ganin Salma
ga su da kyau, ga kudi, to me suke nema?
Kamar Anti Sa'a ta san abinda Salma take
rayawa a ranta sai ta hau kara mata bayani duk
dai dan ta karfafa mata gwiwa.
"Wasu matan ba wai matsalolin miji kadai
kan kawo sun nan ba, zaki sami ma'aikata da
masu matsala da dangin miji ko kuma son
mayar da kishiya bora, kai wata ma bata
dakishiyar sai 'ya'yan miji, sabda haka su ne
kishiyoyinta kuma in ba shan kansu tayi ba to
ba zasu ta6a barinta shakar numfashi a gidan
aurenta ba... Kin ga, dubi waccan!" ta katse
bayanin da take mata tana nuna mata wata
zankadediyar farar budurwa cikin rage murya,
"Kin gane ta?"
Cike da mamaki da shakku Salma ta kada
kai,
"Na gane ta, shahararriyar "yar fim din nan
ce, amma na yi mamaki.. kodayake kila ta kusa
دو
aure
Anti Sa'a ta tuntsire da dariya tana cewa,
"Ana baki kin a kin karba, maganar me
nake miki yanzu? Ba batun da ke sa mutane
Maimuna Idris Sani Beli 114
Na Shiga Aljanna...1 bin malamai muke ba? Kuma n ace miki ba
wai sai matsalar miji ko ta saurayi kawai ke
kawo mutane ba, na saba ganin 'yan fim maza
da mata a wajen nan suna neman daukaka da
farin jinni, ke fa nake gaya miki wallahi wata
ma mijin makociyarta zaki ga ta kawo.
Rayuwar ta yanzu gaba daya ta neman dafa'I
ce, in kuma ka matse hannun nema to kuwa sai
dai ka zauna a rayuwar kana ji gani gani ka
zama mara sa'a, talaka mai bakin jinni da
mummunar fuska"
Sai da Salma ta daga kai ta dubi Anti Sa'a
bayan ta diga wa zancenta aya, ta dubi fuskarta
da kyau sai ta tabbatar da gaske take a maganar
da ta karkare batunta da ita, Salma ta ji hanjin
cikinta na wani mugun kadawa da dalilai biyu,
na farko in bata nemi wannan dafa'in na zuwa
irin wannan kazamin gurin ba zata zama talaka
mai mummunar fuska da bakin jini kuma mara
sa'a a rayuwa, na biyu idan ta nemi dafa'in
tabbas tana shirin canjawa ne daga asalin
Salma da ta dade da sanin kanta zuwa wata
daban da ba ta gama ammana da irin rayuwar
Maimuna Idris Sani Beli 115
Na Shiga Aljanna...1
da ta tsoma kafa ba kuma bata san inda zata
riska in ta nade hannun zani ta fara tafiya ba.
Tana ta wannan tuntuni har layi ya zo
kansu, kuma karin gargaba da bugun zuciyarta,
mutum daidai ake shiga dakin bokan, bare ta
shiga da Anti Sa'a tayi mata jagora. Haka dai
Anti Sa'ar ta yi ta tausar ta sannan ta tura ta.
Daga bakin kofa kafin ka shiga akwai wani
dogari tsaye rike da wani bakin koko cike da
kananun layu, duk kostoman da zai shiga sai
an bashi guda ya hadiya sannan ya shige ciki.
Har ga Allah ba da son ran Salma ta hadiyi
layar nan ba, don dai kawai ta kawo kanta ne,
kuma ma dai ta ga gomomin mutane sun
hadiya sun shiga sun fito kalau, kuma gobe ma
suna dawowa kamar dai Antinta Sa'a.
Tun daga kolin kanta har tafin kafarta
karkarwa suke, ta bankada labulen dakin ta
shiga tare da rafka sallama.
Ba kamar yadda ta tsammaci ganin bokan
ba, wato sanye da kayan tsafi ko tarkacen
kayan bori rakwacam! Maimakon haka sai ta
ganshi hakimce kan kujera ya ci manyan kaya
tamkar wani saraki har da rawani, fari tas da
Maimuna Idris Sani Beli 116
Na Shiga Aljanna...1
shi kamar shi ya zabo kansa musamman da
yake yana da alamun yanzu yake dosar
shekarun tsufa ba a cikinsu yake ba.
Sai dai fuskarsa a matukar murtuke ya zubo
mata ido ba tare da ya amsa sallamarta ba.
Tamkar Salma ta yi girgiza ta zama ba ita
ba saboda tsabar firgici da fargaba, ta yi diradira tana cigaba da yi masa sallama.
Ya ci gaba da kallonta rai a bace ba tare da
ya tanka mata ba, har sai da dan kanta ta yi wa
kanta wajen zama ta kuma ja bakinta ta tsuke
kai a kasa, amma tana samun damar kalle nan
da can a kusurwoyin dakin wanda yake shaida
kasancewarsa dakin bokanci.
Bangwayen dakin duk an lanyace su da
zannnuwan shudin saki da fari, ga kuma
hatimin gidan sarauta a guraren da ba su sami
adon zannnuwan sakin ba, abinda kuma ya
daure kan Salma kenan. Amma dai ta ci gaba
da kallon yadda dakin ya sha korai masu fenti
shantuna da sauran dangin kayan duma, sai
layu bankwala-bankwala rarrataye bakake da jajaye hade da wuri tare da wasu karafa da Salma ba ta san sunansu ba. Sannan akan ko
Maimuna Idris Sani Beli 117
Na Shiga Aljanna...1
wacce kusurwa ta dakin daga kasa akwai
katuwar kwarya zaune kuma daya cikinta wani
hayaki ke fita tamkar dai an kunna turaren
wuta, wannnan gaskiya shi ya fi tsorata Salma,
dan tana da yakinin sai tsabar sihiri ne zai
zaunar da garwashi cikin kwarya ba tare day a
kona kwaryar ba....."
Bata gama shan kallonta da nazarin dakin
bokan ba gajiyayyiyar muryar bokan ta katse
mata hanzari,
"Yanzun haka Adamu na kwance gadon
asibiti"
Abinda bokan ambata kenan ya sanya ta
razanar dagowa ta kalle shi duk da kuwa
kunnuwanta ba su gama tantance abinda ya
fada ba illa sunan Adamu da ya bata mamakin
ji a wannan muhallin.
Ta zuba masa ido da kallon tsoro da rashin
fahimta, shi kuma bai yi kasa a gwiwa bay a
sake maimaita mata,
"Masoyinki Adamu a halin yanzu yana
kwance a gadon asibiti bai san inda kansa yake
ba"
"Inna lillahí wa inna ilaihi raji'un"
Maimuna Idris Sani Beli 118
Lusensita de БИ Na Shiga Aljanna
a, lada.bda munacrazanale fuaka
amma cikin zuciyarta tana karyata bokan jayas
Adamun da suka sabusdafiyalafiya zabaidada
mata mummunan labari a kansa mara dadiр
irin haka Wai me har da maĝailar bai gaida
kansa yake ba saboda tsabaririuguh fatab sb s
ksasbi ki je gida shi kinhtarar da abinPA
faga kinigamsu sannan kindawo kisan sitrd
kike nemaja kansab ustsm aianij s ibl aa sdst iss
evSalinacta kara rudewa dastargane bakan ha
gang har ahinda ke cikin ztrciyarta, mirda niad ta hayicin laya Sa shud as staddst st
ideWallahisgrapkaa yas dads stin ifyanzusgisb
gamsnu ka yi min rai karsaurafisabindalzts
shi" serbleds s usber usbA asnue siasl
Ya jimathaintankaaibmyeammiasidonsalda
kantabrs os kr agked iomidst sT
sDuksta bii td lirkiaes ndiyaetasvhausonnilsd
kamo tashar dana-sanin zuwanta, amnd ca
tsoron hatsabibin bokan: ya shigalzudkiyasta ya
gang abindasta erayeh doio hakaura oicanaHsy
kakkacewa tashoshi dåssuky dongandsd
bokankarshevmarkawaiisailtayl dabaarea
76267 68 sinobi s vist st sliswal ted SPISTIOUS
Maimuna Idris Sani Beli 110lsd ia62 zirbI GnumisM
Na Shiga Aljanna...1
tashar mafarkin soyayya da Adamu ta zama gaskiya.
Dai-dai wannan gaßar ne kuma Bokan ya tanka,
"Adamu ya fada wata zazzafar soyayya ba
tare da dalili ba, duk wata mace a duniya yana
kallon kawai wadda yake so ta rako duniya,
lallai ba don kin zo nan ba har abada Adamu ba
zai taba sa ki a jinsin matan da zai so ba"
Yanzu tsakani da Allah Salma ta ba wa
Boka dukkan imaninta, ko bai san gaibu ba to
ta tabbatar an buda masa wani abu da ya
dangance shi. Ta zo wajensa ba sanar da shi
abinda ya kawo ta ba, amma ga shi yana batu a
kanta, sunan Adamu radau a abakinsa.
Cikin sakankancewa ta muskuta ta ce,
"Na fahimci hakan, ranka ya dade tunda da
bakinsa ma ya sha fada min ni ba irin matar da
99 za'a so ba се...
"Ki bar shi kawai, da mu yake zancen. Ba shi
yau ya farfado zuwa gobe duk tsiyarsa sai kin
yagi wani abu a soyayyarsa"
Salma ta ji wani irin rauni ya mamaye
zuciyarta har kwalla ta taru a idonta. Ba yagar
Maimuna Idris Sani Beli 120
Na Shiga Aljanna...1
wani abu take son yi a soyayyar Adamu ba,
kulliyar soyayyarsa take so saboda haka ta ji
sanyin gwiwar yadda bokan nan mai gani har
hanji yake batun zata yagi wani abu
soyayyarsa.
"Kin fiye garaje"
a
Bokan yace mata lokacin da ya miko mata
wani kunshin hoda da ba ta san yadda aka yi ya
zo hannunsa ba.
"Duk mai hulda da ni sai ya yi yadda yake so
a rayuwarsa kar ki dinga zatawa aikina
ragontaka, Ungo nan!"
Ya cilla mata kunshin hodar.
Jikinta na karkarwa ta sa hannu ta dauka tana
bin sa da kallo,
"Ta zama hodar sawar ki duk lokacin da ki ke
hasashen zaku haďu da shi"
Ya sake cillo mata wani daurin magani.
"Wannan duk yadda za'a yi ki bashi a abinc
ko a ruwa ko da sau daya ne, Adamu ya zama
naki in kin yi wannan... ajiye sadaka ki tashi-ki
وو tafi sai kin kawo min goron daurin aure'
Jikin Salma sai bari yake ta zuge jaka ta
kwanto dubu biyar din da Anti Sa'a ta bata ta ce
Maimuna Idris Sani-Beli 121
Na Shiga Aljanna...1
ta bashi, ta mika masa yayi mata inkiyar ta zube
kan dardumar gabansa. Ta ajiye ta mike tana
faman sharara masa godiya ta fice yana bin ta da
wani irin kallo da har keyarta ta ji shigar kallon.
A waje ta yi jiran Anti Sa'a wadda layin ya
zo kanta, ta dinga mamaki da al'ajabin jin cewa
ashe wai duk so da kyautatawar da Alh. ke wa
Anti Sa'a ba so da kirkinta ne ya janyo mata ba?
Dama wajen boka ta ke kai shi? Shiyasa ake
ganin tana samun kudi amma a rasa inda take kai
su? Yanzu ita ma haka zata sami irin wannan
gatan na kwatance a Adamu? Amma kuma ta
rasa ajiye abin kanta?
Ta binne wannan mamaki da tunane-tunanen
bayan Antin tata ta fito, suka dauki hanya cikin
tattauna tadin Bokan, a nan ne Salma ta ji abinda
ya ruda zuciyarta ya kuma so ya sanya ta sauka
daga wannan turbar ta bin bokan, wato Anti Sa'a
take kara mata bayanin dalilin da ya sanya aikin
bokan ke matukar ci kamar yankan reza, inda ta
ce mata,
"Na taba jin bayanin cewa aljanu na yi wa
bokaye biyayya ne gwargwadon yadda suka
shata maka sharadi ka bi, shi wannan Bokan
Maimuna Idris Sani Beli 122
Na Shiga Aljanna...1
babban hadimin aljaninsa dan sarkin agadas ne,
an ce kafin ya bashi aljanun da zasu dinga yi
masa hidima suna yi masa biyayya ido rufe sai
da ya ba shi sharadin zai daina sallar la'asar
kwata-kwata kuma zai daina halartar sallar
juma'a cikin jam'i sai dai yayi tasa a gida,
sannan wannan karagar da yake zaune a kai
karkashi shimfidar akwai kur'ani izifi sittin.
Wannna shi ne sharadin da ya cika ake biya
masa bukata, don haka duk wanda ya ce miki ya
zo wajen malamin nan bukatarsa ba ta biya ba,
na rantse miki da Allah ya ci karya ya kwana da
yunwa"
Wannan bayanin sai da ya so sanya jiri ya kai
Salma kasa, duniyar ta dinga juya mata cikin jin
tsananin mamaki tana duban fuskar Antinta
wadda ke halartar islamiyya duk asabar da
lahadi, amma wai ta dage tana yi mata bayanin
bajintar nan ta boka a wajen saßawa Allah da
sunan labarin birgewa.
Ba ta farko daga rudaninta ba Anti Sa'a ta
sake kashe ta da wani labarin takaicin,
Maimuna Idris Sani Beli 123
Na Shiga Aljanna...1
"Amma dan tsabar son yada jita-jita irin na
mutane, rannan na ji wani malamin addini a
radio yana ba da misalin bokan a fakaice ba tare
da kama suna ba, wai shi a dole masanin bokaye
da sirrin aljanu, yake cewa, wai layun da
maziyarta gurin bokan nan ke hadiya kafin
ganawa da shi ta wannan hanyar yake zaunar
musu da aljanu a zuci da sauran sha'anoninsu
wadanda zasu zama 'yan sa ido kansu da
wadanda suke son a yi wa sihiri, kuma wai ta
wannan hanyar ne yake sanin abinda ya faru da
mutum kafin ya sanar da shi, kuma ta wannan
hanyar ne bokan ke ribace imanin masu zuwa
gurinsa har suke ganinsa kamar wanda ya san
gaibu, ... ki ji don Allah, hassada kiri-kiri, shin
Allah ba zai yi baiwa ga mutum ba sai da wani
dalili?"
Wani tsinannen takaici ya cunkushe wa
Salma a makoshi, ta yi kokarin ta hadiye shi ya
faskare, dole ta ji ko yaya ne yakamata ta rage
wa bokan nan karfi a fuskar Anti Sa'a ko da
kuwa da fatar baki ne kuma ko da ragewar ba
zata tsinana komai ba na janyewar su ga bokan,
ita kanta ba ta fara mafarkin ta guji bokan ba,
Maimuna Idris Sani Beli 124
Na Shiga Aljanna...1
musamman saboda furucinsa na cewa duk mai
hulda shi sai yayi abinda yake so a rayuwarsa,
ita Adamu take so a rayuwarta kuma da alama ta
hanyarsa zata same shi.
"Kila maganar malamin da kika ji a radion
gaskiya ce, tunda ko kin ce ai ajanu ne suka
tsaya masa, mu dai mu je ya biya mana tamu
bukatar in ma da laifi sai mu dawo mu yi
istigfari
"Ai shiyasa nake yawan sadaka Salma, ni ma
ai na san akwai laifin, akwai lokacin da nake jira
na dena musamman kwanaki da boka ya sa ni
hada wani asiri, ni da kaina na san akwai
kaucewa a ciki, sai dai kawai mu yi ta rokon
29
Allah ya yafe mana
"Amin"
Salma ta fada a darare, domin ita kanta ta san
wannan ta'addaci ne aka kinkimo aka kai wa
Allah
b "Ko me ya sami damu? A tsorace nake
wallahi"
b In ji Anti Sa'adatu, kum fadar tata ce ta
dawowa da Salma damuwarta da ta sanya ta kasa
ko tankawa.
Maimuna Idris Sani Beli 125
*******
Na Shiga Aljanna...1
Salmanu yayi jiran farowar Adamu tsawon
fiye da mintina talatin, da bai farfado din ba ne
kuma hankalinsa ya tashi har ya fara sambatu.
"Ka ga dan iska, idan ka zarce ai ka yi wa
soyayya asara, ni kuma ka janyo min jafa'i a се
ni na kashe ka"
Yana ta faman irin wadanna sambatun ya
debo ruwa ya shafawa Adamu amma kamar an
shuka dusa, sai hankalinsa ya kara mungun
dugunzuma, ya kame kugu yayi tsaye tsakiyar
dakin yana shawarwari, duk hange hangensa ya
rasa tudun dafawa, can sai ya sake debo wani
sambatun,
"Dama ni bokan gaske ne ba sai na fara
aikina ta kan wanna shegen ba, daga wasa sai ka
kama ka macewa mutane, tun farko ma ban da
kai wani shegen tunku ne uban waye yace ka
bayar da kudin, yo ko ubana ne yayi min abinda
ka yi ba sai na dirka masa naushin da zai ziyarci
Maimuna Idris Sani Beli 126
☑
Na Shiga Aljanna...1
barzahu bai shirya ba, kai ma sa'a ta ka ci wallahi"
Maganganun da yake fada ba su yi kama
da fuskarsa mai nuna tsananin tsoro da fargabar
yadda abokinsa ke kwance hanyar rasa rai ta
dalilinsa ba.
Ya sha hange-hange kafin ya kullo
dabarar da zai je Hajiya da ita, ya fito dakin yana
hawayen karya amma bakinsa bai fasa kuri ba,
"Dan iska kawai, na rantse da Allah ban
da wancan furojet din namu na sana'a in ka mutu
zan jima kafin in samu madadinka, Kur'anin
Ubangiji da bar ka zan yi ka tafi kawai"
Ya karasa maganarsa a ciki lokacin da ya
shiga cikin gidan, aka yi sa'a suka yi kacibis da
Hajiya ta fito daga kicin rike da galan din
kananzir,
Tana kallon Salmanu idonta ya shaida
mata tashin hankalin da yake ciki, ita ma nata
hankalin a tashe ta hau baibaye shi da
tambayoyi,
"Lafiya kuwa, ina Adamun?"
"Yanzun nan wani la'anannen tsinannen
matsiyacin direban babur ya make shi ya tsere,
Maimuna Idris Sani Beli 127
Na Shiga Aljanna...1
na kwaso shi mun taho gida bai san inna konsa
yake ba saboda sisin kobo babu a aljibuna
Sai ya karasa maganarsa ta hanyar barkewa da kuka.
Kafin ma ya dire Hajiya ta yi hanyar soro
tana rafka salati gami da hirji.
Salmanu ya bita a baya yana ta faman kwashe wa direban babur albarka kuma yana
kuka haikan tare da bawa Hajiya labarin Karya
akan hatsarin, ya ce mata ta cikinsa ya kusa bi da
tayar mashin din, duk yadda-aka yi a ciki ya sami matsalar.
Hajiya na jinsa tana ji da danta, ba ta
tankawa Salmanu ba sai da ta bugawa Alh. waya
ta sanar masa komai ya taho daga unguwar da ya
je a gigice sannan ta juyo ta fuskanci Salmanu
cikin tausayawa ta ce,
"Halinku daya dai da abokin naka Salmanu,
kun fiye amfani da munanan kalmomi, yanzu
don Allah wadannan alkaba'in da kake janyo wa
mai laifin nan da wannan tsine-tsinen da kake
masa duk ya cancance su, yaushe laifin nasa ya
kai haka Salmanu? To ka yi hakuri don Allah ka
yi masa addu'a tagari wato addu'ar shiriya, shi
Maimuna Idris Sani Beli 128
Na Shiga Aljanna...1
kuma abokinka sai ka dinga yi masa ta fatan samun sauki"
Salmanu ya hau matsar hawaye yana kada
kai ba tare da ya tanka ba.
Alh. na zuwa aka kwashi Adamu asibitin
Murtala a sume.
"Kar mu ce bigewar mashin ce, yanzu sai
su sanya mana ka'idar sai mun zo da 'yan sanda"
Alh. ya kawo shawarar nan, ta yi wa
Salmanu dadi ainun, cikin doki da garaje ya ce,
"Nima na yi wannan tunanin Alh. kawai
sai mu ce faduwa yayi kan kwalbar lemo"
"Haka za'a yi"
Alh. ya amsa zuciyarsa daya.
Bayan sun kai asibitin Salmanu na kan
gaba wajen kurda-kurda da kuka shaße-shaße da
hawaye, babu wanda bai ji tausayinsa, don haka
ne ma da aka baAdamu gado, Alh. ya bar
Salmanun ya tafi gida shaidawa iyalinsa da kuma
kwamtar da hankalin Hajiya wadda yayi dabarar
kin tafiya da ita don kar ta zo ta daga hankalinta.
To ya manta ma iyalin nasa ta je unguwa, don
haka kawai sai ya je ya kara rarrasar Hajiya
sannan ya koma asibitin.
Maimuna Idris Sani Beli 129
Na Shiga Aljanna...1
Har yamma suna tare da Salmanu wanda
ya fi shi tarin damuwa da cutar, don haka ne ma
sai ya zama kämar shi ne dan uwan Adamun a
idon likitoci shi suke kira don karin bayani ko
neman wani abu kasancewar asibitin ba'a ganin
mara lafiya sai lokacin ziyara. Wannan ta sa shi
kansa Alh. a bakin Salmanu ya ji cewa Adamu
ya farko kuma jikinsa da kyau yana baccin
gajiya, duk suka taru suka yi ta farin ciki.
"Sun ce zuwa dare ma zasu sallame mu
In ji Salmanu.
Alh. ransa yayi dadi, ya ce
"Abin yayi kyau, dama ina zaman asibiti ya
ga dadi, ga mahaifiyarsa can hankali a tashe,
gara a kai mata danta ta ga lafiyarsa
Lokacin ziyara na yi Salmanu ya yi dabarar
silalewa ya riga Alh. shiga dakin da Adamu ke
kwance, ya same shi zaune jingine da filo yana
kurbar maltinar da Salmanu ya siyo masa tun
yana mace.
Ya zauna bakin gadon daga gefensa suna yi
wa juna kallon kuda, da alama kowa bakinsa cke
yake .da zance, amma sai Salmanu ya riga shi
Maimuna Idris Sani Beli 130
Na Shiga Aljanna...1
furtawa cikin murya kasa-kasa kasancewar
dakin ba Adamu kadai ba ne mara lafiya.
Babu alamar ciwo a tare da shi yanzu amma
fuskarsa ta nuna jigata da farkowa daga ciwo.
"Malam ka daga min kafa, na ce Mashin ne
ya bige ka, banza kawai daga naushi daya sai ka
macewa mutane?"
Adamu ya jima bai tanka ba. Salmanu ba ya
shakkar in Adamu zai kasa goya masa baya, ba
yau yake da shi ba ba jiya ba
Hasashensa kuwa ya ci, domin sai gashi cikin
murmushiAadamu ya се, еек y en t
"Ка сci sa'a ban mutun ba Salmanu, in na
mutu ni đa Hüsna ba zamu taba yafe maka ba,
don ba ka bar mu a duniya mun auři juna ba
ihu,
Salmanu ya kai masa bugu cikin murna da
ed uobs'2
"Au har ita ba zata yafe min ba? Ita da bata
ma san kana yi ba?"
revAdamu ya kawar da kaiyslaw i umbA
EhAmana, ruhinta ba zai yafe ba domin
akwai ranar da zai san a duniya yayi rashin
wanda ba zai taba samun wanda ya so shi haka
ba sy sb diA ad in sted sy sbbsy blerd no
Maimuna Idris Sani Beli 131
Na Shiga Aljanna...1
Shigowar Alh. ba ta hana Salmanu ya ansa
masa cikin murya kasa-kasa ba,
"Da ka mutun ai zan kai mata wannan canjin
a matsayin diyya, su suka kashe ka su suka hana
ka auren abinda kake so"
Suna dariya tare da tafawaAlh. Ya karaso
cikin fara'ar nuna farin ciki da murnar yadda ya
sami jikin Adamu,
"A lallai jiki yayi kyau, Alhamdulillahi"
Cikin ladabi Adamu ya rusuna kai ya gaishe
da yayansa.
Salmanu ne ya amsa,
"Wallahi kuwa jiki yayi kyau Alh, kawai su
יי
zo su allame mu a kai wa Hajiya danta"
Suka yi dariya su duka.
Alh. ya duba agogo y ace,
"Sa'adatu ba ta gida ne tún safe, amma mun
yi waya da ita ta ce min ta dawo gida har sun yi
abinci suna hanyar zuwa ita da Salma"
Adamu yayi walankeluwa da bayanin yayan
nasa don ya ji suna Salma a ciki, har ga Allah ya
tsani Salma, tsana mai yawan da ya sha tambayar
kansa dalilinta alhalin ta kasance 'yar'uwarsa.
Don haka yadda ya bata rai ba Alh. da ya san
Maimuna Idris Sani Beli 132
Na Shiga Aljanna...1 akwai tsama a tsakanin Salma da shi ba, hatta
Salmanu da yake daukar tsanar da Adamu ke wa
Salma a matsayin shakiyyanci sai da ya lura da
hakan,
Suna ta 'yan hirarraki a tsakaninsu, Da
Adamu aka taru aka dinga zagin mai mashin da
ya buge shi har Allah ya kawo su Sa'adatu.
Aka gaisa a mutunce tare da yi wa juna jaje
da Allah kiyaye gaba.
Kasancewar akwai Alhaji a wajen Adamu ya
dake bai nuna tsama ba, Salma ma ta rakuye a
can gefe rungume da hannu tana satar kallon
Adamu wanda ta lura yana ta faman buga mata
shan kamshi ko kadan bai yarda ma sun hada
idoba, alhali a yanzu babu abinda take nema irin
su hada idon ko hodar Boka zata rallo mata shi,
tana son ta ga yadda za'a kare saboda haka
zuciyarta ta kasance cikin matsanancin bugu.
"Zo ki zuba masa abinci Salma, mun gode
Allah Adamu an auna arziki"
Anti Sa'a ta farko da ita daga fargabarta, a
hanzarce ta yunkura ta nufi ledar kayan abincin
ta janyo.
Maimuna Idris Sani Beli 133
Na Shiga Aljanna...1
Tana zuba abincin cikin kasala da fargabar
yadda maganin zai yi aiki akan Adamu kadai
duk da ba shi kaďai zai ci abinci ba, Anti Sa'a ta
fada mata a tukunyar gidan yawa ma ana zuba
maganin Boka kuma ba wanda zai kama sai
wanda aka nufa.
Adamu bai yi niyyar kin karbar abincin ya ci
ba, sai da Salmanu ya zolaye shi ta hanyar yi
masa inkiyar ga amaryarshi fa na hidimar zuba
masa abinci.
Da Salma ta mika masa filet din abincin sai
ya kawar da kai yana cin magani,
"Ke na koshi"
Suka dubi juna ita