828 iles ins aist souris
Na Shiga Aljanna...1
Ba wannan sharhin Hajiya ta so ba wanda
ke nuna abinda take wa har yanzu gefensa ma
Adamu bai bi ba, wato kulla kauna tsakanin
Adamu da Salman, musamman kuma a daidai
wannan lokacin da yake ta yi mata kururuwar
aure yake so, tana da yakinin in dai an so zama
lafiya to gara ma ayi masa auren a kuma zuba
wa saraut Ubangiji ido.
Cikin sanyin jiki ta mika masa nairarta dubu
da take makale a hannunta,
"Ungo wannan ka rike a hannunka ko zata
bukaci kudin dinki, ka ga ba sai ka bada maza
ba"
Ya sa hannu ya karbe kudin ya kalmashe a
aljihu yana tura wa Salma ashar cikin
zuciyarsa, ya rasa da abinda wannan tulun
yariyar ta rudi su Hajiya har'suke ganin bata da
abokin rayuwa sai zukeken saurayi irinsa.
Ya sake jaddada wa Hajiya godiya sannan
ya sa kai ya fice da kaya a hannu zuciyarsa
barkatai da tunani iri-iri duk na ba'a ga Salma
wadda ya dinga rantsewa ko tayi kwalliya ba
kyau take ba, lallai mijinta zai sha barnar kudi
Maimuna Idris Sani Beli 83
Na Shiga Aljanna...1. kuma babu obiyan bukata, don ko Zinärin duniyar nan zata sanya ba zai mata kyau ba.
YDSAEE s siluil otaw sd id lad uosbA
ebinb s *********mis sb wsbA
Tewwnd iy selay sb ginlol nsnnsw
Husna kyakkyawar doguwar yarinyar da ta taso cikin s maraicias sakamokon rashin mahaifiyarta Zainab sanadiyar haihuwarta
kuma haihuwar fari, ta sha hannun raino iri-iri
tun daga kan hanun Kakarta Innaa mahaifiyar Zainab odin wadda ta dauke tat a cigaba da
rainonta tare dastare da dan da take goyo
Yunusa. Ita ma Allah ya karbi ranta Husna ná
shekaru hudu, sai rikonta ya koma gurin yar
mahaifiyarta mai suna Rakiya wadda shekaru
biyu kacal tayi Allah ya raba zaman dalilin
mutuwar auren Rakiyar kuma bata da Karfin
cigaba damrikonta, wannan yasa ta danka
amanar Husna ga autarsu Jamila, la, amımma ba'a yi sa'a ba halin Jamila tamkar ba ciki daya süka
fito das'yan uwanta ba, sai ta dinga gasa Husna
tamkar ba vjininta ba, yadda take matukar
gallaza mata tun idaga unguwa här kafatin
交
Maimuna Idris Sani Beli 848 i net enhi srunish
Na Shiga Aljanna...1
dangi babu wanda bai san irin mawuyacin
halin da Husna ke ciki ba.
Mahaifin HUsna Malam magini mutum ne
mai tsananin kawaici, shi ne dalilin da yasa ma
ya dauke hankalinsa daga kan Husna duk da
kasancewarta 'yar fari kuma 'ya daya tilo day a
mallaka a duniyarsa. Gashi kuma dangin
Zainab sun baibaye shi da karamci, kana sun
baibaye shi da lissafin hakkin rikkon Husna
ahannunsu yake.
Bayan rasuwar mahaifiyarta yayi aure har
sau biyu, farko Suwaiba wadda da alama bat a
da rabon haihuwa, suka shekara biyar tare
kanwar son 'ya'ya ta kais hi auren Jummai,
amma muguwar fitiharta ta sanya yayi mata
saki uku da tsohon ciki ta koma gidansu ta
haifo 'yan biyunta. 'Ya'yansa uku kenan a
dangin matannsa matatciya da rayayyiya.
Da aka sake diban shekara daya da
rabuwarsa da Jummai sai ya sake auro Hajara,
wadda tana zuwa ita ma ta ci karo da nata
rabon, a auren Hajarar ne kuma ya fahimci
ashe akuyar Jummai ce tayi kuka kawai,
bambancin ya saba da rike mace daya ne
Maimuna Idris Sani Beli 85
Na Shiga Aljanna...1 Zainab sannan Suwaiba, lallai rashin kyawun halin mace yafi bayyana idan tana da kishiya,
wato dai ya yiwa jummai bahaguwar fahimta
ita kanta Suwaiba baa rasa nata laifin. Wannan
dalilin ya sanya ya rike su da halinsu ya kuma
cigaba da hakuri haka.
A shekarar da Hajara ta haifi 'yarta Khadija
hakurinsa da kawaicinsa akan rikon da Jamila
take way a gaza, ya shafe wa idonsa tokay a
karbi 'yarsa, babu wani jan ido Jamila ta bashi
abarsa, dama ba Kaunar rikon take ba
kasancewarta mai muguwar karaya da kyashi.
Da babu gara babu dadi, amma Husna ta
baro wata wuyar ne ta fado wata, duk da akwai
dan sassauci kasancewar a tsakanin kishiyoyin
da ked a migun kishi take, wadanda kulawarsu
gar eta bata motsawa sai idan zasu cutar da
juna, in bah aka bata da sauran wani gata ko
amfani a wajensu, sannan ko da sun cutar da ita
idan idon mahaifinta ya kai kan cutar ya ka
tsawatar daidai gwargwado.
Sai dai wannan halin ko in kula da tare da
Kalubalen da rayuwarta ta taso a ciki ya koyar
da ita dabi'a gwagwarmaya tare da koyar
Maimuna Idris Sani Beli 86
3
Na Shiga Aljanna...1
tsayuwa da kafafu., ta taso mace mai jarabar
neman kudi kamar tayi sata, it ace wannan
sana'ar gobe waccan, karshe dai ta tsayar da
guda wadda ta fi kwarewa a kai kuma wadda
tafi ko wacce kawo mata kudi wato dinkunan
mata, kai har na mazan ma tabawa take idan ta
sami rarar lokaci tun da dinkin matan yafi sauri
tare da kawo kudi masu kauri.
Wannan jarabar neman kudin nata ne ma ya
sanya dakatar da karatu daga kamala babbar
sakandare kawai, a cewarta ai karatun book
dan sana'a kawai ake saboda haka ai ita ta sami
sana'a yi.
Sai dai nakasun da za'a duba a rayuwarta da
gwagwarmayarta it ace, shegen sabo da kasha
kudi, tana da kirki sosai amma yawancin
alfarmarta ta kudi ce da kokarin kere sa'a. gat
a 'yar kyakkyawa mai kyan diri don haka ta
budi ido da farin jinin samari fiye da kima, ita
kuma tayi amfani da wannan dammar ta dinga
yashe duk saurayin da tsautsayi ya kawo shi
shirgin ta saboda tana da dankaren wayo da iya
tsara kalami bugu da kari gat a mace mai
sanyin murya.
Maimuna Idris Sani Beli 87
Na Shiga Aljanna...1
Wannan dabi'ar tata ta dami mahaifinta
kwarai, kullum cikin fada da nasiha gareta
yake tare da fatan ganin ta tsayar da miji ya
aurar da ita amma ita sam hankalinta bay a kan
auren, ta ci alwashin sai tayi wanki zata yi aure
kuma ma dai har zuwa yanzu bata ga saurayin
day a kwanța mata a rai ko kuma ya cika
sharudan zamowarsa miji gareta ba.
Amma wani hukuncin Ubangiji wanda ya
sanya ta sakankancewa tabbas rayuwa ba
abinda ka tsara tun fari zuciyarka ke dorewa a
kanta ba kuma ko ana yi wa komai tsari to
tabbas So ba a yi masa tsari kuma ba zabа
masa muhalli ake ba, kawai shi yake canka ya
zuba sheka. Tun ranar da ta hadu da Adamu a
shagon kayan dinki sai ya bi zuciyarta ya
mimmike, ya zamana dukkan mafarkinta a
mijin aure kan Adamu yake fadawa da kudi ko
babu, in ta wassafa shi a mai kudi sai ta hango
musu wata aljannar duniya mai cike da
kyawawan 'ya'ya da rayuwar jin dadi, in ta
wassafo shi a talaka kuma sai ta hango
rayuwarsu mai mutumci da karrama juna tare
da son juna tsakani da Allah. A wannan gabar
Maimuna Idris Sani Beli 88
Na Shiga Aljanna...1
har hango kanta take yi tana daukar nauyin
gida a sana'ar da take shi kuma Adamu na ta
kara sonta yana shi mata albarka tare da cin
alwashin daga ita babu kari, kuma duk lokacin
da Allah ya yassare masa sai ya jiyar da ita
dadin da babu wanda ya taba jiyar da matarsa
ko masoyiyarsà irinsa.
Wannan jumurdar da ta sami kanta ciki ta
rage mata kuzari ainun, so take ta fasa wannan
son da zuciyarta ta kinkimo mata amma duk
yadda ta kwaso fasawar sai ta ji ta kasa, sai
fasawar ta rikede dubunnan soyayyar Adamun
su hadu da fatan samunsa su yi ta faman
wahalar da ita. Musamman idan taji faduwar
gaban yadda za'ayi ta samu din tunda ba ta
cikin duniyar da ake mutunta matar da ta ga
namiji tace masa tana son sa.
Cikin kwana biyun nan haka ta dinga tsirar
zuwa shagon kayan dinki musamman dan ta
ganshi, ko akan allura ne bazata aiko yaro ba
sai dai ta wanko kafa ta taho amma bata taba
katarin sake sanya shi a ido ba, kuma duk
yadda sonsa yake gasa mata gujjiya a hannu ta
kasa samo dabarar da zata yi wa mai shagon
Maimuna Idris Sani Beli 89
Na Shiga Aljanna...1
kayan dinki ta nemi Adamun ko kuma ko da
sunan Adamun ya tuna mata wanda ya kwanta
mata a rai kafin zuciyarta ta zabe shi
gwarzonta na har abada.
*******
A gurguje kafin karasowar Salmanu
Adamu ya fada wanka sai dai bai yi katari ba
ya fito ya tarar da Salmanun har ya ya karaso
yana kwance kan kujera yana jiransa tare da
rera wakarsa ta Dauri kasancewarsa mai son
wakokin mutanen Da.
"Haba ashe ba banza ba Allah yayi maka
ajiyar son wakokin su Dan anaci da su Duna,
ashe Boka mai gani har hanji zaka zama"
Da shegantakar da Adamu ya tare shi
kenan.
Suka tuntsire da dariya suka tafa.
Salmanu ya ce,
"Malam da fa kai na yi niyyar ka zama
Bokan"
Adamu ya kai masa duka a fusace,
Maimuna Idris Sani Beli 90
Na Shiga Aljanna...1
"Ba na son rainin hankali, saboda ni na
kawo shawarar kuma na san yadda ake yi?"
"Saboda kai baki ne ni kuma fari, ka san
ba a saba ganin bokaye farare ba..."
Adamu ya sake kai masa duka cikin
dariya,
"Shege! Ni ne bakin? Ai nima ba baki ba ne
malam"
Suna kacamewa da dariya su duka Salmanu
y ace,
"Amma ai baki za a kira ka a kaina"
"An ji, kuma nine mai masoyiyar da babu
irinta ko, Husna mai sunan laarabawa"
Adamu ya fada cikin raha.
Salmanu ma ya zolaye shi bayan ya kawar
da kai yana kunshe baki,
"Allahu Akbar! Na rantse da Allah na zaci
Salma zaka ce, ita ke sonka, waccan ba ta san
bikin da kake ba kila ma matar aure ce ma'ana
an yi mata miji".
Fuskar Adamu ta nuna damuwa amma sai
ya girgaza kai ya jefar da comb ya yi gaba ya
dauko man shafawa ya nemi gurin zama, sai da
ya fara shafa man ya amsa wa Salmanu,
Maimuna Idris Sani Beli 91
Na Shiga Aljanna...1
"Salmanu, addu'ar da nake wa yarinyar nan
ina tsaya wa dararena akanta, idan ka ga ban
aureta ba ko kuma Allah bai jefa mata sona
cikin zuciyarta ba, to ka tabbatar Allah ya ajiye
min wadda ta fita wadda kuma zan so fiye da
ita din"
Salmanu ya saki wani ihu sannan ya dora da
cewa,
"Ka san abinda ya fi birge ni da kai?"
Adamu ya girgiza kai.
Salmanu ya ce,
"Yarda da kanka wallahi"
Adamu ya sake kada kai,
"Ai ba yarda da kai ba ne, yarda da wanda
ya ce idan an kira shi zai amsa ne, idan kuma
aka tsaya a kofarsa ya ishe mu ne, shin a kai
wa kuka na kuma ina da yakinin ba zai
tankwabar ba. Irin wannan addu'ar na yi a
karatun bokon da aka yi niyyar mayar min
addni, ka ga cikin sauki Allah ya raba mu'
Jikin Salmanu a sanyaye ya amsa masa,
"Ai game da karatun nan gata ne yayi maka
yawa Adamu, in ni na sami wannan gatan
Maimuna Idris Sani Beli 92
Na Shiga Aljanna...1
wallahi ba zaka gan ni a wannan kwararon ko
wannan sana'ar ba"
Sai jikin Adamun shi ma yayi sanyi, ya
basar lokacin da Husna ta mamayo zuciyarsa,
wadda ya hakikance in dai akwai karatu nan a
gabansa tabbas sai aurenta ya tsere masa.
Zai yi Magana kenan ya jiyo motsi kamar
daga cikin gida, zargin ko Hajiya ce zata leko
ya sanya ya mike da sauri ya zo wajen
Salmanu ya hau yi masa radar yadda suka yi da
ita akan sabuwar sana'ar da suke son farawa.
Cikin sakkani kadan Salmanu yayi hadda
kuma zo aka wuce ne ma suka gane cęwa yara
masu siyen Goro ne.
Salmanu ya mike,
"Bari na je na gaishe ta kafin ka shirya.
Cike da fargaba da wasi-wasi iri-iri Adamu
ya shirya har Salmanu ya fito.
Salmanu ya nemi guri ya zauna ya fito da
kudin aljihunsa ya hau kirga, kana ya daga kai
ya dubi Adamu,
"Ni an sami dubu goma ba dari daya a
jikina, kai nawa aka samu a jikinka?"
Maimuna Idris Sani Beli 93
Na Shiga Aljanna...1
Maimakon Adamu ya amsa kai tsaye sai ya fara kalubalantarsa.
"Dari dayan ma na san fasa dubun ka yi ka
sha sigari.
Salmanu yayi dariya,
"Kamar ka sani?"
"Yo kama ce ma? Ai sani nayi kawai"
"An ji, kar kuma ka ja mana zance mu yi
abinda ya kawo ni lokaci na kurewa"
Adamu ya kawar da kai,
"Haka ne, to ni ban tara komai ba"
Salmanu yayi masa wani kallon banza,
amma ganin bai san yana yi ba sai a hasale ya
ce,
"Ba ka tara komai ba fa ka се?"
Adamu ya juyo ya kale shi,
"Eh, na je ba sa'a na matsa layar zanar na
kasa bata"
Salmanu ya shanye haushi ya dan yi
murmushi, kamar zai basar amma sai ya yi
dabarar tashi ya shammaci Adamu ya dakumi
aljihunsa ya zaro naira dubu biyun da Hajiya ta
ba shi kudin dinkin Salma,
> "Makaryaci, wannan fa?"
Maimuna Idris Sani Beli 94
"Tsakaninku kallo"
Na Shiga Aljanna...1
Adamu ya kawar da kai ya fada.
"Wallahi bata isa ba, sai ka bayar das u sun
shiga cikin 'yan uwansu, na karba a haka ai da
hanau gara mannau"
Ya hada su da dubu goman wajensa ya
mikawa Adamu,
"Ungo ajiye mana ka zauna ka ji bayani"
Ba musu Adamu ya karba ya cusa aljihu
sannan ya gyara zama yana duban Salmanu.
Salmanu ma ya zauna zaman nutsuwa ya
fara koro jawabi.
"Abu na farko da zamu tanada shi ne, Guri,
wato muhalli da ya dace da malamai ko
bokaye, dan guri kebаббe nesa da mutane, ko
kuma cikin mutane inda ba a san mu ba"
Adamu ya ci gaba da kallon Salmanu saroro
da alamun rashin fahimta, kuma cikin alamun
son nuna juriyar a dire ya fahimtar.
"Wannan bos din na gama kashe shi tun
daren jiya, ina gidan gonar Ogana da nake
kular masa da shi na nan Zawaciki kusa da
mu?"
Maimuna Idris Sani Beli 95
.
Na Shiga Aljanna...1
Da kyar Adamu ya daure ya kada kai saboda tsabar rudewa.
Salmanu bai damu da rikitar Adamu ba ya cigaba da ba shi lissafi,
"To dama tuni Alh. ya daina zuba Kaji a
nan, sai kawai ya ce na sawa gidan ido na
dinga kula da shi, ai mun taba zuwa ka ga girman gidan ko?"
Nan ma Adamu ya kada kai,
"To daya 6angaren za mu iya mayar da shi
fadar tsubbunmu ba tare da wata mishkila ba,
dama gashi Alh. yana shirin zaune wa a Japan
har na tsawon shekara hudu, abin Allah jiyan
nan yake min wannan albishir din"
"Ikon Allah"
Adamu ya daure ya tanka.
Salmanu ya janyo jug ya tsiyayi ruwa ya sha, sannan ya dubi Adamu da kyau,
"Wadannan kudin ko basu hada dukkan
siyayyarmu ba na san zasu kusa, zamu sai
kayan saki irin na 'yan bori, har da su tabarmi, kore, shantu da kaskwayen wuta, kai har da su tsaintsiya da faifai duk masu fenti irin na masu
girka...."
Maimuna Idris Sani Beli 96
Na Shiga Aljanna...1
"Har girkar zamu dinga yi kenan?"
Adamu ya fada cikin tsura wa Salmanu ido
yana hadiyar yawun fargabar yadda Salmanu
ke son aikensu zunguro sama da kara.
Salmanu ya tuntsire a dariya ya amsa,
"Haba wa zai aike mu wannan danyen
hukuncin? Mu fa Jabun ne, masu girkar asalin
ne Orijinal, hanyarsu daban tamu daban kawai
dai sunan sana'a kusan daya mu ke"
"Shikenan, ina jin ka".
Adamu ya fada cikin sallamawar da bata kai
zuci ba.
"Kana ji ko?"
In ji Salmanu. Bai jira cewar Adamu ba ya.
cigaba.
"Wadancan kayan 'yan borin ba su ne
kayan sana'ar ba, su ne dacoration din wajen
yadda zai dace da sana'ar, amma dai zamu dan
yi hake-hake a wajen yadda zamu jona
butotanmu...."
"Meye wani butotai?"
Adamu ya fada kamar a kule. Har ga Allah
maganar ba karamin gundurarsa da batą masa
rai take ba.'
Maimuna Idris Sani Beli 97
1
Na Shiga Aljanna...1
Salmanu ya buge shi a kafada.
"Kai dallah malam ka ware, duk ka bi ka
wani cukwikuye"
"Ai kai ka cukwikuye ni, malam in zaka yi
sauri ka ware ni, ka yi wallahi ka fara sa min
ciwon kai"
Salmanu ya dinga tuntsira masa dariya har
sai da Adamu ya dinga barazanar bar masa
dakin sannnan Salmanu ya riko hannunsa cikin
tsananta dariya,
"Ka ga in ma'anar Butotai ne zo in fada
maka mu kashe wannan bos din mutumina"
Yana cigaba da dariyarsa bai jira cewar
Adamun ba ya cigaba,
"Tiyo nake nufi da butotai, ko baka san an
ace masa bututu ba? In ka je makaranta ai ka
san za'a iya kiran jam'insa da butotai. To ba
wai amfaninsa kawai tarar ruwa daga famfo
zuwa tanki ba, a'a, a tamu sana'ar da shi ake
maganar aljanu duk zaka gani idan mun je
wajen"
"To"
ciAdamu ya fada domin ya hutar da zuciyarsa
Maimuna Idris Sani Bell 98
A
Na Shiga Aljanna...1
da-zucinta na jiran fahimtar Salmanu tare da
kokarin cirewa ransa damuwar da ta addabi
ransa. Amma sai ya dage ya mayar da
hankalinsa ga Salmanu wanda ya zage yana yi
masa bayanin yadda ake wannan sabuwar
sana'a ta wankin ido ba tare da an je wajen
wani malami neman sa'a ko siddabarunsa ba.
Hankali kwance kuma a wanke bayin Allah.
Adamu ya kwashi gayar mamaki da yadda
salmanu ya kwatanta masa yadda ake binne
hankali da azancin masu yawon neman asiri,
yadda ko shi aka yi wa wannan siddabarun sai
ya yi muguwar bayar da gaskiya. Kai tsaye
Adamu ya gane wannan sana'ar sunanta
damfara hakkun, amma tunda da tsoka kuma
Salmanu ya baibaye shi da hujjar dama duk
wanda zasu cuta ko su damfara Allah ya bari
ya kama gaibu, ba laifi in an nuna masa yadda
ya kama kafar wala. Wata hujjar da Salmanu
ya gabatar masa it ace, sana'ar na kawo
kazaman kudi, a saukake zasu kawo masa
kudin da zai auro masa Husna cikin wata daya
kacal!
Maimuna Idris Sani Beli 99
Na Shiga Aljanna...1
Ko an juyawa dukkan hujjojin baya wannan kadai ta ishi Adamu, domin yana jin HUsna da darajar da ko ta wane hali ne ma ya kamata ya
sami aurenta, kuma in ya samu shi ne abinda
ya dace da shi duniya da lahira.
"Amma idan Goranmu ya kamo katon kifi, akwai wata hanyar mai 6ullewa, ita ce ta
tsakurar wani kaso daga abinda muka caji kostoma mu nemi Bokan gaske mu bashi aikin
ya gabatar, maimakon namu da yake iska, ka
gane?"
Salmanu ya karkare dogon jawabinsa da
wannan karin hasken.
Cikin karsashi Adamu ya kada kai, zuciyarsa na kara karfin bugu tana hango masa
samuwarsa Husna a duniyarsa.
Ba su bata lokaci ba suka mike don fara
daura damba, daidai lokacin kuma Salma ta
kira Adamu a waya, kafin ya daga ya antayo
mata ashar ta kai goma, sannan ya daga murya
a cushe y ace mata.
"Malama lafiya?"
Ta hadiye jin haushin tambayar tasa ta
amsa masa cikin tambaya,
Maimuna Idris Sani Beli 100
"Lafiya da aka yi me?"
A kufule ya amsa,
Na Shiga Aljanna...1
"Da kika ishe ni da kira kamar ke kika sai
min wayar"
Ta yi dariya,
"Ai ban san a saukar da ka'idar sai an sai
waya ake kiran mai ita ba, in haka ne ni da
nake da burika kan kiranka ai yakamata na sai
99 maka waya...
Yayi tsaki cikin gundura,
"Sai ki hada har ni ki siya, don in kin sai
wayar ai kamar kin yi baki yi ba"
Zata yi Magana ya tare ta,
"Malama don Allah kar ki cika ni da
hayagaga, me nene dalilin kiran?"
Kai tsaye ta amsa,
"Ankon nan, sati na sama ne bikin..."
Kafin ta dire ya tare ta,
"ki aiko a karbar miki zan fita"
Ta dan yi ihun murna,
"Da gaske, kudin ko kayan?"
"Oho!"
Ya amsa mata.
Ba ta damu ba ta sauke ajiyar zuciya,
Maimuna Idris Sani Beli 101
Na Shiga Aljanna...1
"Wallahi ga gidan babu kowa Yaya Adamu,
ai na san hanya ne, me zai hana ka daure ka
biyo min da shi?...""
"Ashe ba zaki sanya ba kenan"
"To in fito kenan yanzu na karba? Gaskiya
ina son karba yau na mik wajen dinki"
Adamu yayi jim, ya tsani zuwan gidansu,
haka kawai shi ko son ganinta ba ya yi bare ace
wai takanas wajensa ta zo, saboda haka nan da
nan ya tare ta a cunkushe,
"Uwar gantali kenan, zan biyo miki das hi,
mu kar ki wani kwaso kafa ki zo mana gida"
Cike da murna Salma ta shiga gyada kai
tamkar yana ganinta,
"Haba dan albarka ko kai fa"
Bata jira cewarsa ba ta sauke wayar.
Shi ma ya ajiye cikin bata fuska yana sauke
idonsa kan Salman wanda ya ishe shi da fuskar
tambaya, ya hau bashi labarin abinda ke akwai
game da Salma da ankonta.
Suna ta hirarsu suka fito dan fara shiryeshiryen sana'arsu Adamu dauke da ledar kayan
Salma.
Maimuna Idris Sani Beli 102
Na Shiga Aljanna....1
Zancen Husna ne a bakinsa yana jaddada
irin kaunar da yake mata.
Salmanu ya fahimci lallai da gaske Adamu
yake sai ya shiga karfafa masa gwiwa cikin
karsashi.
"Ka kwantar da hankalinka, mace fa ba
wani wahalar farauta ne da ita ba, ko baka da
ranyo in kana dad a tsari ka gama da ita"
Cikin nuna karaya Adamu ya ce,
"Ayya! Don kana da kyau ne ba sa yi maka
wahalar shiga tarko Salmanu, amma ni, ai sai
aikin sa'a kawai..."
Ya katse maganarsa zuciyarsa na bugawa
fat-fat har Salmanu na lura da dagawarta, ya
daga kai da sauri yana kallon saitin da Adamu
ya shanya ido da baki yana kallo, sai ya ga
wata kyakkyawar doguwar halitta tana ratsowa,
.shi kansa Salmanu sai da tasa zuciyar ta buga
ko da kuwa ma'anar bugun tasa da ta Adamu
akwai bambanci.
Bakinsa na rawa ya ji yana tambayar
Adamu,
"Ba dai wannan ce Husna ba?"
99 "Ita ce
Maimuna Idris Sani Beli 103
Na Shiga Aljanna...1
Adamu ya amsa a hanzarce kuma cikin nasa
karkarwar harshen zuciya cike da debe kauna
da fata, saboda.yadda ya ga Husna rai a bасе
kuma sun hada ido ta kawar da kai, kawai sai
ya kaddara fishinsa ne, ya shiga uku! Ta fara
kin sa tun kafin ma ya furta yana sonta.
Ya sami bakin Magana gareta karo na farko
a matsayin yada manufarsa tun da sonta ya
tsira a zuciyarsa,
"Ranki ya dade"
Ya ambata mata lokacin da ta zo giftawa, a
idonsa tana ta faman shan kamshi kamar jira
take a kula ta, ta zabga mari.
Ga mamakinsa da raguwar fargabarsa sai ta
dan dakata ta juyo kuma tana masa duban ina
na san ka?
Kwakwalwarsa ta yi shawagi kafin ta cafko
makama,
"Ko ba Telar nan ba ce?"
Ta kada kai cikin saurin da ba dan Adamu
ma a rude yake ba zai gane fuskarta daban,
zuciyarta daban.
Salmanu dai na kallonsu da nazari su duka.
Maimuna Idris Sani Beli 104
Na Shiga Aljanna...1
"Ai na jima ina nemanki Hajiyata
In, ji Adamu, yana Magana cikin wasa da
zolaya.
Husna ta yamutsa fuska da nufin dan rage
damarar da ta yi wa fuskarta, ta yi murmushi
sannan ta rausaya kai ba ta ce komai ba.
"Halan baki gane ni ba"
Ya fada da alamu karayarsa na nema ta
- bayyana.
Wannan karon kai tsaye ta amsa kuma a
yangace,
"Na gane ka maña, ba Malam mai maballi
ba ne wanda muka hadu a kantin kayan dinki"
Ya tari numfashinta da karsashi,
"Yauwa kin tuno ni da kyau, to ya yau?"
Ta dubi tsawon hanya da fuska mai nuna
kosawa,
"Alhamdulillah. Neman me kake min?"
"Dinki ne da ni".
Kai tsaye ya amsa.
Ta ji kirjinta ya amsa, don ba ta so neman
nasa gareta ya tsaya a dinki kadai ba, sai dai ta
yi saurin jin cewar in dinkin yayi sanadi ma
kila wancan ya zo da sauki.
Maimuna Idris Sani Beli 105
Na Shiga Aljanna...1
Ta murmusa ta dube shi ta cе,
"Na fada maka ba na dinkin maza"
"Ai na mata ne, kin gan su ma
Ya amsa kuma ya mika mata kayan Salma
da zai kai mata.
Salman yayi ta zarya cikin wata irin
muguwar dariya, sai da Adamu ya yi masa
alama sannan ya kama kansa cikin tu'ajibi ya
cigaba da kallon wannan dirama.
Husna ta karbi kayan ta buda cikin mugun
sanyin jiki, tamkar ta bace a wajen take ji
saboda tsabar fargaba da jin an ci ta da yaki.
Ta sake daga kai ta dube shi ranta a dan
bace.
"Wa za'a dinkawa, ko kuma in ce ina
measurement?"
Adam ya dan yi turus sannnan ya waske ta
hanyar kare mata kallo sama da kasa,
"Ki yi kamar na jikinki komai d komai"
Ta kasa daurewa sai da ta bi ba'asi cikin
tsuke gira,
"Kamar ni take kenan?"
"Wace cе?"
Maimuna Idris Sani Beli 106
Na Shiga Aljanna...1
In ji Salmanu da ya ji ya kasa hadiye dariya
ko saka baki.
Adamu ya saci idon Husna ya watsa masa
harara, sannnan cikin tsabar yin fuska ya gyada
wa Husna kai alamar amsarta Eh kenan.
A
ciwon matukar gajiye da zuciya da
takaici Husna ta sake bude ledar kayan ta gani,
sai sannan ne ma ta lura ashe ankon bikin
aminiyarta Amina ne, wani mugun takaici yayi
masifar turnuke ta, ba dan ba ta sai ankon ba,
a'a wajen samari hudu ta karbi kudin ankon a
wajensu amma a ganinta babu na birgewar da
ya kai na Adamu wanda dinki ma sai ya kai wa
budurwarsa don tsabar gatantawa. Kodayake
ita kanta ta san a baibai ko a tarkon So take
yanke wannan hukuncin, in kai dinki gata ne,
fiye da shi ma tana samu a a wajen masu sonta,
amma dai ta ji yaji da bata sami ko kasa da
haka a wajen wanda ita take so ba.
"Ai ankon aminiyata ne ma
Ta hakura da kallon kayan ta mayar da
ganinta gareshi tana hadiye hawayen da ke son
kunno mata.
Maimuna Idris Sani Beli 107
Na Shiga Aljanna...1
Cikin zumudi Adamu ya ce,
"Allah ko? kawai k ice an sara akan gabа?"
Ta koma duban hanya cikin cin magani. A
zatonta duk wannan fara'ar tasa ta zai bayar da
dinki masoyiyarsa ne. Ta nisa ta се,
"To ni zan wuce, yaushe ake son dinki?"
"Kin fi ni sani tunda kin san ranar bikin"
"Haka ne, to yanzu yaya za'a yi? Baka san
gidanmu ba bare ka zo karba, kai ko tsoron in
gudu maka da kaya baka ji ba?"
Ta daure ta karasa maganarta da dariyar 5
zolaya.
Kai tsaye kuma fuskarsa na nuna yakini ya
amsa mata,
"Haba dai, wallahi kin fi karfin wannan. Ke
dai kawai ki je da kaya ki yi min dinki mai
dankaren kyadaidai jikinki, yadda za'a yin
a karba na san Auah zai kawo"
Ta yi saroro tana kallonsa.
Abinda ya sanya numfashin Salmanu
bugawa. Sai ga Adamu ya kutsa hannu a aljihu
ya dumbuzo kudin da ya bashi riko ko kirgawa
ba yi ba ya mika mata.
"Ga kudin dinki?
• Maimuna Idris Sani Beli 108
Na Shiga Aljanna...1
Ta dan rusuna kadan ta karba fuskarta babu
walwala ta yi musu sallama ta wuce.
Adamu ya bita da kallo cikin shanya baki
Salmanu ya danki hannunsa wanda ya mayar
aljihu suna taba ragowar kudin da ya bari.
Cikin fishi ya ce,
"Ina fatan wannan matsiyaciyar dubun naka
ka bata?"
Adamu bai bashi muhimmmanci ba sai daya
tabbatar Husna ta gama bacewa idonsa sannan
ya juyo ya dube shi,
"Me ka cсе?"
"Nawa ka bata?" Salmanu ya tambaya
cikin fishi.
Tun daga zuciya Adamu ya fara shiryawa
rikicin Salmanu, cikin dakewa y ace,
"Sai dai mu koma ciki a kirga"
Bai ma jira cewa Salmanun ba ya wuce ya
koma cikin soro ya hau buďe dakinsa.
Salmanu ya biyo shi yana