domin idan
zan zama Mongo park ba zaku taba yarda an
halicci kwanyata da iya kirkirar abin kirki ba"
Yayan ya kara janye annurin fuskarsa yana
duban adamu,
"Uhum! Cigaba ina jinka"
Adamu ya sake muskutawa rai a bace yana
gyarawa carbinsa zama, ba tare da ya dubi
Yayansa ba ya ce,
"Alh. Yadda kuke kaddarawa ni ban iya
wani abin arziki a duniya ba, haka na kalli
kwanyata da rayuwata na gane sam babu
abincina a karatun boko, don haka a daina yi
min kagen cewa na san gaibu",
"Kage? Uban wa yake maka kage Adamu?"
Adamu ya motsa ya sake motsawa cikin
dauke kai, amma bai tanka ba.
'Maimuna Idris Sani Beli 28
Na Shiga Aljanna...1 Alh. Ya jima yana yi masa kallo mai fassara
iri-iri, bai gamsu ba sai gashi a gaban Adamu
cikin zafin nama, ya sunkuya ya dago habarsa
ya shinshina tsawon wasu sakanni sannan ya
ture shi ya mike yana ja da baya cikin kallonsa,
"Babu alamun shaye-shaye a numfashinka
Adamu, amma me yake cin kanka yau?"
Adamu ya sa sake cin magani ya cigaba da
jan carbinsa, sai jikn Alh. Yayi sanyi ya jima
tsaye yana nazarinsa cikin kasa hankula, bai
kai ga warwara ba ya zauna kujerar kusa da
Adamun ya dafa hannunsa yayi masa Magana da tattausar murya,
"Ka kasa gane nufina Adamu, kudurorina
akan ka sami kyakkyawan ilmi mai zurfi duk
ba ni zasu amfana ba kai zasu amfana, babbar
sakadanre bata isa komai bad a har zaka
mallaketa ka ja ka bame, ina laifin ko 'yar diflomar ka yarda ka samu tunda ka fara?"
Yayi jiran cewar Adamu, amma har yanzu
babu alamar zai tanka, sai dai ya rage cin magani da yake.
Maimuna Idris Sani Beli 29
Na Shiga Aljanna...1
Alh. Bai yi fishi ba ya cigaba da magana
cikin taushin murya da sassaukan harshen
fahimta.
"Hajiya Uwa da mahaifinmu Mal. Musa mu
biyu kadai suka mallaka wato ni Kabiru da kai
Adamu wanda na bawa tazarar sama da
shekaru goma. Lokacin kuruciyata kafin kai
kai bai waye da neman ilmin boko sosai ba
don haka ban sami hasafinsa ba, lokacin taka
kuruciyar kuma kuncin rayuwar talauci ya
hana su maida hankali akan karatunka"
Adamu ya muskuta alamar nuna gajiyawa
da gundura da wannan dadaddan tarihi da
kullum Yayansa ya tashi yi masa nasiha sai ya
hado masa da shi, sai ka ce mai gwada masa
shiga kabari a fito.
Alh. Ya fahimci gundurar ta Adamu amma
sai ya share shi ya cigaba da maganarsa,
"Tun kana mitsitsinka na fara buga-buga ta
neman kudi, yau wannan sana'ar gobe waccan
har ajalin mahaifinmu ya riske shi. Duk da ina
da sauran kuruciya bai hana nauyinku kai da
Haj. ya dawo kaina, wanda hakan ya sa ni kara
Maimuna Idris Sani Beli 30
Na Shiga Aljanna...1
zage kwanjin neman na kai, Allah kuma ya
dafa min har ya tsayar min da sana'ar nan ta
safarar Goro daga kudu zuwa arcwa, har kawo
yau da rufin asirin Allah ya lullube mu ta
silarta har ni da Haj. mun shiga sahun wadanda
za'a kira Alhazai"
Ya dan nisa kamar alamun rashin alamun
abin fadar ne ya kare har Adamu yana murna
da tsaki cikin ransa, amma sai murnar ta koma
ciki lokacin da Alh. Ya sake nisawa,
"Ba gorin kushe nake maka ba Adamu,
amma tabbas na. ci kashinka yadda idan ka
bijire min ko kayi min butulci Allah zai bi
kadin hakkina, na soka shigen son da Uba yake
wa dansa, shiyasa burikana akan ganin cigaban
rayuwarka suka yi kamari. Burina ka zama
likita,, amma da naga hankalinka baya kan
karatun sai na sauke farashi, akalla ko malamin
makaranta ka zama. Haka kawai ni dai naji
akwai bukatar ka tanadi ilmin ko da kuwa kafi
sha'awar zama dan kasuwa, shiyasa ma na
bayar da shawarar ka karanta kasuwanci kamar
yadda ka yarda ka fara bayan ka share shekaru
da dama kana zaman kasha wando.
Maimuna Idris Sani Beli 31
Na Shiga Aljanna...1
Na ci burin ka tsaya da kafarka yadda ko
bayan raina zaka iya cigaba da daukar nauyin
kanka da mahaifiyarmu sannan ga nawa iyalin
wadanda bas u da kowa sai kai......"
Adamu ya muskuta cikin mita da kunkuni,
inda yake cewa,
"Kana tunanin abi maka kadin hakkinka a
kaina, amma ka kasa tuna za'a bi nawa hakkin
a kanka saboda takurawar da kayi min da
cukwikwiye ni sai nayi wata rayuwa wadda
bani da sha'awarta saboda kawai na dauki
nauyin rayuwar iyalinka in ka rasu....
"Me kake cewa??
Alhaji ya tambaya cikin fuskar mamaki.
"Cewa nayi Allah ne kadai ya san gawar
fari"
Adamu ya amsa cikin nuna gundura.
Alhaji Yayi kasake yana kallon Adamu, ya
shafa abin dorarwa ya rasa, sai kawai ya
rangwada kai yayi shiru.
Hakan da Adamu ya gani ya sanya jikinsa
yin sanyi, ya dan yi kame-kamensa sannan ya
fara magana,
Maimuna Idris Sani Beli 32
Na Shiga Aljanna...1
"Wallahi duk na fahimce ka Alhaji Amma
kai ma abind aka kasa ganewa shi ne, shi
karatu ba a sanya masa karfi dole sai kwanya
da ra'ayi suna da sha'awa, Ni kwata-kwata
idan ina da ra'ayin karatun boko Allah ya tsine
min, shiyasa ma shekarun nan biyu na dinga
samu n kari oba, kuma wannan shekarar ma
idan an matsa min kila abin sai yafi haka.."
istAllah ya kyautam BRESE
uAlh.Yafada cikin alamun gajiya da takaici.AE
no Sukajima cikin shiru kafin alh. Yamisa, susI
Shikenan maganar karatu an barta in Allah
ya so, amma fada min, menene kudurinka
menene burinka, menene abindaskwanya da
ra'ayinka
eys
suke sha'awa
one is
baswanda
As sape
As
ake musus
Kingi Asgo
Da sauri adamu ya amsa, 626П
Nilsana'a make so, Allah yausani ina so
nayi aure3 вр якпог sn smls? iA sks sweС
Zuciya ta zo wa Alh. Wuya, amma ya dingav
shanye kayarsa harya hadiye fiye da rabintáA
"Na san kana sonsaure Ctunsfuni, amma a
tsammanina zan iya tare ka har lokacin da idan
Maimuna Idris Sani Beli
ewеlUь сsa sY IA
33E iled ins2 ainht sauoisM
Na Shiga Aljanna...1
kayi ba zai zame mana matsala ba, ban sani ba
دو
ashe karya naci na kwana da yunwa"
Adamu yayi shiru.
Can.jimawa Alh. Ya sake nisawa,
"An ce min Salma na sonka, in haka ne gara
ayi 'yar gida musamman da yake baka da
kwakkwarar sana'a sannan ka san komai
akanta, 'yar yar mahaifiyarmu ce da ta rasu tun
tana karama rikonta ya dawo hannuna don
haka ta san ciki da bai a samu da rashinka kafin
sana'arka tayi kwari".
Ba don wata fuskar tafi gaban mari bă babu
abinda zai hana Adamu tura ashar. Sai kumburi
yake kamar ya fashe ya tari numfashin yayan
nasa,
"Wa yayi min sharrin cewa ina son Salma?"
"Cewa aka yi Salma na sonka, ba cewa aka
yi kana son Salma ba"
Alh. Ya amsa cikin tausasawa.
Adamu ya kara bata rai,
"Wa ya fada? Ni bata taßa fada min ba"
Alh. Ya sake daurewa,
こ
Maimuna Idris Sani Beli 34
"Sa'adatu ta sanar da ni
Na Shiga Aljanna...1
Babu kunya Adamu ya sake tare numfashin
Alh. a sike,
"Gaskiya ni bana sonta, ba mace nake so da
aure kawai ba, wata yarinya nake so na aura'
Alh. Ya gama kai wa bango, tsawon lokaci
yana jinjinawa,
"Ba ka sonta?"
Adamu bai tanka ba, iyaka ya cafko
carbinsa ya fara ja.
Alh. Ya sake kada kai,
"To da kyau! Nan ma an wuce, na yarda
kaje ka auro yarinyar da kake so kuma kake
son aure. Sai mu fado maganar sana'a, wacce
kwanya da ra'ayinka suke sha'awa?"
Hantar cikin Adamu ta kada day a fahimci
turin Jeka-ka-mutu Alh. Ya shirya yi masa, ko
kuma debi in ga hankalinka. Ta ina zai sami
sana'a babu hannun yayan nasa a ciki, in
sana'ar ba ta aikin karfi bace ina zai nemo jari?
Yana tuno tauhidi sai ya sami harshensa na
bawa Alh. Amsa,
"Muna nema wajen Allah?"
Maimuna Idris Sani Beli 35
Na Shiga Aljanna...1
"To babu laifi, Allah ya zaba mafi alkhari.
Idan an samo sana'ar a sanar da mu mu taya
murna. Tashi ka je"
*** *********
Garin Kano garin kasuwanci, unguwar
kurawa unguwar sarakai kuma unguwar
makotaka da kasuwar rimi bakin asibiti.
An ce duk mai makotaka da kasuwa baya
tsiya, amma da alama wannan kaulin ya tsame,
Adamu ciki, domin a Kurawa aka haife shi, ya
girma a cikinta amma yau ya laluba sana'ar yi
ya kasa ganowa ko kuma ita ta kasa ganinsa,
saboda haka kamar makotaka da kasuwar ta
kasa yi masa rana.
Bayan alhinin awa daya kacal~ wanda yayi
bayan turin je-ka-ka-mutun da Alh. Yayi masa,
ya dawo gida ya dinga cakuda rayuwa da
mutuwa a hakuri da son Husna da kuma sauran
rayuwarsa, da kyar ya wafto jarumtar tashi ya
nemo sana'a don kar ya mutu a matsayin ragon
soyayya da rayuwa, tunda aikin malam ba lallai
nan take zai ci ba.
Maimuna Idris Sani Beli 36
Na Shiga Aljanna...1
Amma kaico! Kwana da yini kenan ya kulla
lissafin sana'o'l sun fi a kirga amma har yanzu
ya kasa fitar da amsar ko guda, ba don rashin
iyawa ko rashin sanin makamarta ba face don
wadanda suke da saukin samu shi sam! Basu
dace das hi ba kamar dai yadda me markade
bai dace da zama mijin Husna ba.
Ya yarda tun daga yammacin jiya bayan
sallamar da yayansa yayi masa kawo
yammacin yau, kwakwalwarsana ajin washi, ta
fara karaiun nemo mafita, har tayi digirgir
amma ta fito fanko!
Kwance yake rashe-rashe kan doguwar
kujerar dakinsa da yammacin ranar cikin tunani
a halin yanzu, sai gashi a halin zahiri an
wangale kofar dakinsa an shigo
"Ho! Gayun gidan nan suna kusa?"
Wani shegen takaici ya kume shi, amma a
halin shanye shi ya dago kai ya dubi mai
shigowar lokaci daya kuma zuciyarsa ta rubuto
wata addu'a tana biyawa,
"Ya Allah ka tsari gatari da saran shuka,
Ubangiji ka tsare ni ko hada hanya da gajeriyar
mace bare ta kai ga gina mata gida in ajiye a
Maimuna Idris Sani Beli 37
Na Shiga Aljanna...1
matsayin matar aurena, Allah ka san ni baki ne,
amma bana son macen da ta fiye baki Allah ka
tsare ni da ita. Idan na ga 'ya'ya masu idanuwa
dakwa-dakwa Allah ka sani har jaje nake wa
iyayensu to Allah ka tsare ni da macen da zata
haifa min irinsu. Duk mace mai saurin murya
bana kaunarta, Allah ka san wannanin ka
jarrabe ni da irinta zuciyata zata iya fashewa....
Gaba daya Allah ka san doguwar mace nake so
wankan tarwada mai kyakkyawar fuska da
kyakkyawan murmushi bana son mai yake, ina
son mai kyawawan idanu mai dogon gashi, mai
fara'a in so samu kuma mai suna Husna.... Ita
nake so, Allah ka mallaka min kayi min tsari
da wannan da take tsaye a gabana yanzu
Salma ta karasa shigowa dakin sosai tana
nazarisa tamkar wani bakonta. Dakin ya
wadata da duk wani kayan more rayuwa daidai
matashi mai matsakaicin rufin asiriirin
Adamu.
STEVIOUS Saul sysh igndol mewogida Dakin na shimfide da shudin kafet, akwai
dindimemiyar katifar sauko mu gaisa daga can Kuryar dakin waddaEDSIT ta cika OELI da shirgi kama da bargo, kayan sawa wankakku da masu dauda
Malmuna Idris Sani Beli 38 RON HML
2
Na Shiga Aljanna...1
litattafai har da wasu allunan rubutun sha guda
biyu kamar yadda suke watse ciki da gefen
akwatunan dake jere a nasu gefen ba.
Daga wani gefen kuma ga fakej din kayan
kallo masu dirma-dirman sifiku da kuma
karamin firji a gefe. komai dai a dakin baya
cikin hayyacinsa duk kyau kuwa da tsadarsa,
can kwalbar turare nan filasan abinci, can bel
nan kwalaben lemo. Abu bako a idanun Salma
cikin dakin shi ne, wata shimfidaddiyar sallaya
daga can bangaren gabas a karshen dakin
sannan ga wani jibgegen carbi zaune kan
salllayar yana shan nasa sharafi.
Kodayake iyakar sanin da tayi wa Adamu
ma abocin son ibada ne wato sallah akan
lokaci da kuma yawan nema a wajen Allah,
idan duk halayensa na kushewa ne to tabbas a
nan bangaren ya sami na yabo. Ta dade da
sanin Adamu tun suna yara, in dai yana jarabar
son abu, to ya dinga kafa goshi yana fadawa
Allah kenan ba dare ba rana.
Lokacin da yake neman tsarin Allah da ita
cikin zuci, ita kuma daidai lokacin take nazarin
dakinsa, sai aka yi sa'a suka gama kusan lokaci
Maimuna Idris Sani Beli39
Na Shiga Aljanna...1
guda, kuma kamar masu tseren Magana suka
dago suka fuskanci juna,
"Ke matsalarki fadowa dakin mutane babu
sallama"
Ya riga ta Magana cikin matukar daure
fuska.
Duk da kusan a tare suka yi maganar ita ma
ce masa tayi,
"Lafiya kai da dakin naka na gan ku duk a
hargitse?"
Dayake kafin ta dire taji nasa furucin sai ta
zarce da amsa masa,
"Au yanzu ban yi sallama ba na shigo?
Kawai dai ka ce baka ji ba ka lula cikin tunana
di".
Haba ya ji kamar zai tura mata ashar, amma
ya maze ya kawar da kai,
"Kin manta ne, ai ba daki kika shigo ba,
Turu kika shigo...
Ta wuce ta zauna kujerar dake kusa da
kafarsa tana dariya,
"Allah ya baka hakuri Akaramakallahu..."
Ya tare ta a kufule, don bai gama fanshe
maganarta da ta zoza masa gyambo a kirji ba,
Maimuna Idris Sani Beli 40
Na Shiga Aljanna...1 "Tunanainki? To kila ma ni gabadaya ba a
halicce ni da zuciya ba bare a bata lokacin da
zata bata wajen tunaninki"
Salma ta katse si cikin dariya da mayar da
komai ba komai ba,
"Kar ka damu, tawa zuciyar ta ishe mu
tunana komai da ya shafe mu, yadda nake bata
lokaci wajen tuna ka haka nake bata lokaci
wajen tuna maka kaina......"
"Ba na son iskanci da wulakanci Salma..."
Ya sake tare ta a zafafe saboda tsakani da
Alla hadiyar bakin cikinta ya fara gagararsa.
Salma ta shafe sama da minti biyar tana
dariya cikin kallonsa kafin ta shanye dariyar
cikin goge hawayen da dariyar ta samar mata.
Ta jima tana kallonsa a nutse sannan ta tanka,
"Komai ya ji a kai Adamu, gaye har gaye
matsalarka daya baka san wasa ba. Wai kai a
zatonka ko daura min kai a kafa aka yi zan ja?
Ai gara na yanke kafar ko ta katako ce na aro
na yafa"
Ya tashi zaune cikin rage damuwar fuskarsa
yana sauke numfashi,
Maimuna Idris Sani Beli 41
Na Shiga Aljanna...1
"Ai kece kike neman zunguro wa mutane
sama da kara, 'yar wannan rahar da kike kin
janyo manya sun sa mana ido, suna zaton son
juna muke. Abin ma sam babu tsari, ko ina zan
dauki gundumemiyar mace irinki in kai a
matsayin mata?".
Duk kawaici da kai zuciya nesa irin na
Salma sai da wannan maganar ta Adamu ta
bata mata rai, don haka ta jima kafin ta gama
hadiye ta. Cikin murmushin yake ta ce,
"Kar ka damu, kai zaka samo wanda zai iya
daukar irina a matsayin mace ka aura masa, na
san kila kai ne waliyyin don haka in ka tashi
tallata ni sai ka dinga dawajewa, Baka ce kuma
gundumemiya"
Adamu ya dan yi saroro da jin wannan
bakar maganar tata, amma dai ya takura
fuskarsa kar ta bada maza, sai ma ya kada
kafada nuna halin ko-in-kula,
"Ba ba'a ce ta kar uwar gizo ba karar kwana
ce, ni ba kushe ki nayi ba, ainihin halittarki na
fada menene na jin haushi na? in ni baki yi min
a matsayin matar aure ba wani ai yana nan
yana cin layar in ba ke ba sai rijiya"
Maimuna Idris Sani Beli 42
Na Shiga Aljanna...1
Salma ta so ta hasala, amma sai ta binne da
siyasa,
"Haushinka na ji Adamu?"
"Ni bana son janjanin magana don Allah"
"To an bar maganar"
Ta fada cikin saduda sannan ta koma bin
dakin da kallo kusurwa bayan kusurwa
musamman shimfidar sallayarsa mai jibgegen
carbinsa a kai.
Adamu na biye da ita da nasa idon tamkar
yana gadinta ne, zuciyarsa a kuntace domin
yakinin wannan kallon Allah tsine uwar mai
karyar da take wa dakinsa sai ta jangwalo
abinda sam bata da ruwa a cikinsa. Don haka
ya katse mata hanzari,
"Kin ga malama duk maganar da zata fito
daga bakinki ya zamana ni da ke duk muna da
hakki a cikinta, idan ba ruwanki ko ba ruwana
to kar ki kawo mana ita, ato!"
Ta sauke ido a kansa cikin murmushi tana
jin ciwon hanzarinta da ya katse. Idan ba
idonta ke gizo ba a can kusa da jibgegen carbin
nan ta hangi kwalbar turaren wurudi, cike take
da fargaba, amma dokokin Adamu na mata
Maimuna Idris Sani Beli 43
Na Shiga Aljanna...1
burkin tambayoyin da zata fanshe, dole ta
tattare ta hadiyc da cin alwashin jiran wata
haduwar kafin ya kafa dokar.
Ta ciro Jakarta da ke rataye a kafadarta ta
zaro wasu kyallaye guda biyu na les da na atamfa ta mika masa,
"Amina kawar nan tawa! To bikinta ne ya
taso saura sati biyu, wannan anko ne na kawo
ka sai min, kunyar Alh. nake ji wallahi kullum
na dinga damunsa da dawainiya”
Da Adamu ya kalle ta sai ya fahimci
tsakaninta da Allah take Magana, don haka ya
yayyafawa ashar din da ke turereniyar fitowa
daga makogwaronsa ruwan salama ya hadiye
su. Yana bin hannunta da kalllon gefen ido ya
се,
"To ajiye su nan, dama jiya-jiyan nan na
siyo sabuwar Gariyo tare da AK 47, dare kawai
nake jira ya tsala na fita"
Duk da ta gane bakar maganar da ya cinna
mata sai tayi fuska,
"Ban gane nufinka ba"
Kafin ta rufe baki ya mayar mata,
Maimuna Idris Sani Beli 44
Na Shiga Aljanna...1
"Dama kin zo ne ki gane nufina ko kuma
dan na sai miki anko?"
"Anko ya kawo ni"
Ta fada a sanyaye.
Ya nuna mata kofa,
"To ki ajiye ki je za a siyo"
Ta bi umarninsa ta hanyar mikewa tare da
yi masa sailama, amma maimakon ta nufi kofa
kai tsaye sai ta zarce kan sallayar nan ta
sunkuya ta dauki turaren wurudin nan ta hau
sunsuna.
Adamu ya kara cin magani ya kawar da kai
daga kallonta, can ta juyo ta dube shi, tana
kallon fuskarsa ta tabbatar ashar dinsa a kan
harshe take karamin motsi bakinsa yake jira ya
antayo ta waje.
Ta so su hada ido ko dan ta gaskata zatonta,
da ya ki sai ta hakure tare da ajiye turaren ta
juyo a sanyaye kai tsaye kuma ta nufi kofa ta
fita ba tare da ta sake tankawa ba.
A soro ta tšaya domin bawa kwallar da ta
cika cikinta dammai fitowa ta wataya. Wane
irin mugun ciwo ne ya kama kirjinta? Ta
tambayi kanta ba tare da sa ran samun amsa ba
Maimuna Idris Sani Beli 45
Na Shiga Aljanna...1
don ta sha kai wa kirjin nata duk wani lissafi a
akan Adamu. Adamu ban da son sallarsa
kulliyarsa bai cancanci a so ba, ashe ma bayan
wannan ita kanta bai dauke ta a matsayin mace.
ba, Baka gundumemiya, wannan ce inkiyarta a
wajen Adamu wanda ta kwashe shekaru da
saninsa saboda haka ta ga ko wane irin aibu
nasa daga halittar jiki zuwa hallitar hali amma
duk da haka ko kadan kirjinta bai ji rauni a
sonsa ba.
Ta ci kuka mai hadiye shassheka a ciki
sannan tà goge hawayenta daidai lokacin da
zuciyarta ta cilla lissafin Adamu da zabgegen
carbi hadi da turaren wuridi, nan da nan
kwanyarta ta rushe da canki-cankin Allah ya sa
ba zargin da zuciyarta tayi ya tabbata da
Adamu ba.
Tana cikin share hawaye Adamu ya fito
daga dakinsa da nufin shiga cikin gida. Ya kula
hawaye take tana sharewa, amma sai ya basar,
"Au ashe ke ce baki tafi ba, haba tun dazu
nake jin kwashar-kwashar".
Maimuna Idris Sani Beli 46
Na Shiga Aljanna...1
Ta fara girgiza kai cikin rudewa da kokarin
kwato furuci daga kwanyarta, amma ya gagara
kawai sai ta sa masa ido da kallon kurilla.
Suka yi kallon-kallo tamkar kowa na hango
cikin zuciyar kowa, amma shi sai ya basar ta
hanyar kawar da kai yayi fuska,
"Ina abincina, kin taho min da shi?"
Ta amsa da kyar cikin numfarfashi tana
nuna masa cikin gida,
"Tun dazu Sajida ta kawo maka ina
tsammanin ba ta san kana ciki ba ta kai wa
Hajiya"
Ya kada kai ya wuce cikin gidan ba tare da
ya tanka mata ba, ita kuma ta bishi da kallo
zuciyarta na kade-kade iri-iri wanda ko daya
gangar jikinta ta kasa zabar daya ta taka masa
rawa, sai daga karshe ita ma ta zabi kada kai ta
fice tana kara goge hawaye.
**********
Yana ta faman wurga loma tamkar mai shiri
hadawa da harshensa ya hadiye, idan ya ajiye
cokali kuma kafin ya cinye na bakinsa sai ya
Maimuna Idris Sani Beli 47
Na Shiga Aljanna...1
cafko carbinsa ya hau ja, a haid
kuma mafici ne yana ta faman firfita.
agu
Ga kwanon abincinsa ga kyallayen ankon
Salma a gefensu, shaida ce ta ya kuduro batu a
akansu ya kawo wa Hajiyarsa wadda ke ta 'yan
hidimominta daga tsakar gida zuwa daki.
Da alama ita ma Hajiya hankalinta a kansa
yake, tun bayan da babban danta ya je maía da
batun ya sallama Adamu da maganar karatu sai
duk hankalinta ya bi ya dugunzume, ta san
Adamu da kyau! Bai iya zaben komai ba bare
ya zabi makoma tagari a rayuwarsa wadda
babu hannun yayansa a ciki, sannan ta san
kafiyarsa kan abinda ya zabowa kan nasa
komai muni shi baya gani. Kari kan damuwarta
bayan wannan shi ne yadda ya zaune mata
yanzü yana cin abinci bakinsa a dinke, ta dade
da sanin shirun Adamu sai da dalili don haka
tuni ta fara neman tsarin Allah da jin dalili
wanda zai shafi farin cikinta ko wanda zai
sanyata zance da karkata kai.
Ta cigaba da shige da ficenta tana sakar
abinda zai bugar mata cikinsa ta ji me ya hadiya, bata yi aune ba kawai sai ta ji ya
Maimuna Idris Sani Beli 48
Na Shiga Aljanna...1
kwarma ihu tare da furzar da shinkafar bakinsa
kana ya furta,
"Na shiga uku!"
Ta girgije tsoron da ta ji karon farkon
ihunsa a hasale ta yi kansa da tsintsiyar
hannunta,
"Menene haka, kai wane irin mahaukaci
ne?"
Ya nuna mata shinkafar day a furzar daga
bakinsa,
"Wata shegiyar tsakuwa na gurza, in
Sa'adatu ta iya girki Allah ya tsine min"
Hajiya ta dinga motsa baki alamar takaici na
neman hana ta Magana, amma dai ta daure ta
warto,
"Wato Adamu bakinka ba zai zama mai
yawan ambaton alkhairi ba ko? Ka kwarma ihu
ka biyo shi da na shiga uku an bi ba'asi kuma
ka nemi Allah ya tsine maka. Adamu fata
nagari fa lamiri ne...."
Alamar nasihar tata ta bayan kunnensa take
shiga, kawai sai ya hau kakari tamkar mai
shirin finciko 'ya'yan cikinsa a matsayin amai
sun ki fincikuwa.
Maimuna Idris Sani Beli 49
Na Shiga Aljanna...1
Da haushi ya ishi Hajiya kawai sai ta bi
bango ta yi zaman dabaro tana kallon Adamu
har ya gaji da kakarinsa ya dago ya dube ta ido
jawur,
"Wai Ibtila'I ya afkowa mutum amma sai ki
ce sai ya ce ya shiga aljanna a madadin ya
shiga uku, aljanna ba dadi ba ce? Wata masifar
kuwa in ana shiga dubu mutum ma ba sai ya ce
dubu ya shiga ba..."
Cikin sikewa Hajiya ta katse shi,
"Ka'idar daidai ce sai ka ji dadi zaka
godewa Allah Adamu...?"
Shi ma tare ta cikin nuna mata carbin
hannunsa,
"Mu da muke neman kusaci da Allah har a
fada mana godiyar Ubangiji Hajiya? Ai kar ki
damu kawai, Allah na kowa ne kowa ma
azurtawa yake. Aljanna kuma ta mai rabo се"
Furucinsa da carbin hannunsa ya sanya
shakku ya dabaibabye zuciyar Hajiya ta ji
numfashinta ya fara gudu a guje! Nan da nan
Shazali dan gidan Hajiya Dudu da Malam mai
almajirai suka fado zuciyarta.
Maimuna Idris Sani Beli 50
Na Shiga Aljanna...1
Wani malami ne a Warure da labarinsa
tsakaninsa da matasa ya fara karade bakunan
jama'a, ana zarginsa da neman matasa maza,
wadanda yake yaudara da basu wurudin neman
kudi, an ce wasu na tsallakewa su yi kudin
wasu kuma su zama bayinsa da sai yadda yayi
das u yayin da wasu idan sun kuskure wurudin
suke haukacewa kamar yadda Shazalin ya
haukace kuma kwararo-kwararo yake bawa
mutane labarin abinda ya faru da shi a daren
wurudin tare da bayyana matasan da suka yi
kudi ta hanyar wurudin, kowa a Kurawa da
zagayenta ya san da wannan batun ciki kuwa
har da Adamu wanda bai dauki hakan abin
kyama ba don lokacin da labarin ya zo musu
suna tare da Hajiya da yayansa da Sa'adatu har
ma da Salma. Suna ta jinjina labarin amma
budar bakin Adamu sai cewa yayi,
"Ni ban ga abin jinjina lamarin nan ba
wallahi, ai wurudi ka nemi kudi ba laifi ba ne
in dai ba shirka zaka yi ba, shi ma Shazali
akasi aka samu"
Salma t ace,
Maimuna Idris Sani Beli 51
Na Shiga Aljanna...1
"Ko babu laifi Yaya Adamu ai kasada da
rayuwa ganganci ne, yaushe mutum zai saka
hankalinsa a caca yana ji yana gani a bashi
zabin kudi ko hauka...."
Ya mike yana amsa mata cikin gwasalewa,
"Ke ai wata Dumfa ce wallahi, ai dai kin
san matsaroci baya taba zama gwani. Dama
rayuwar ai kamar caca ce, zubi ake ko a samu
ko a rasa....
"Sannu Kala-Kato!"
In ji Sa'adatu
Adamu ya so ace ba Yayansa a wajen ya
yarfa wa Sa'adatu Magana, idon yayan nasa ya
sa ya bige da cewa,
"Yauwa akarambana, sarauniyar shiga
abinda babu ruwanta".
Ya sa kai ya fice daga gidan.
Hajiya ta dawo daga tunaninta cikin taruwar
fargaba, ta dade tana duban Adamu wanda
yake ta faman tsince-tsince a abincin da yake ci
cikin yatsine fuska har ya kamala cin abincin
ya ture kwanon.
"Wai me kake ja da carbin nan Adamu?"
Maimuna Idris Sani Beli 52
Na Shiga Aljanna...1
Ta ji muryarta na tambayarsa ba tare da tayi
shawara da zuciyarta ba.
Ya dan yi jim, sannan ya amsa cikin
murmushin da-biyu mai alamar waskiya,
"Waccan Kundubar yarinyar ce tana gani na
ba Cas! ba As! Wai ta kwaso kyallayen anko
har guda biyu ta kawo min, dan kar aji kunya
na karkade kundi na dukufa gaban Allah
rokonsa ya hore abinda za'a fita kunyar..."
Har ga Allah Hajiya ta yarda da shifcin
gizonsa.
"Wacce Kundubar yarinyar?"
Ta tare shi cikin rashin fahimta
"Salma mana".
Ya amsa mata cikin karsashi tare da mika
mata kyallayen,
Ta karba ta shiga juya su tana kallo. Zahiri
kwayar idonta ce kawai take kallon kyallen
amma zuciyarta da kwanyarta sun fi na'ura mai
kwakwalwa tara aiki. Can jimawa suka samo
matuntuba daya, cikin raunin murya ta daga
kai ta dubi Adamu,
"Yanzu kai tsakani da Allah da ka san
akwai addu'o'in da zaka yi domin canja hagu
Maimuna Idris Sani.Beli 53
Na Shiga Aljanna...1
ta zama dama amma ka kasa yi wa kanka
gatanta a rayuwarka da neman ilmi wanda
kamar ya zama shi ne tsanin sana'ar mutanen
wannan zamanin in ma an ture wayewar
rayuwa?"
Yana sane ya mike yayi kicin-kicin yana
fuffukar tafiya,
"Ni wallahi Allah ne gatana, kar a daga min
hankali akan batun da tuni nayi jana'zarsa na
binne"
A gajiye da takaici Hajiya ta yafito shi
sannan ta shafa hannu a fuska,
"To fatiha, an gama binne karatun boko, zo
mu yi wata maganar daban"
Ya dawo ya zauna yana kumburin karya.
Sai kawai Hajiya ta watso masa tambayar
da ta kusa tarwatsa masa numfashi duk da ya ji
alamar ita kanta Hajiyar tambayar bata shirya
mata ba ta fado harshenta.
"Ina fatan ba ta tsanin Malam-Na-Allah ka
hau domin kusaci da Allah ba...."
Ragowar maganar ta makale a
makogwaronta shaidar a cikin tsoro ko abinda
yayi kama da shi tayi maganar.
Maimuna Idris Sani Beli 54
Na Shiga Aljanna...1
Ya jima yana tattare yawun bakinsa yana
hadiyewa da kyar ko dan ya sami kofar da
sautin zance zai fito daga huhunsa. Ba ya
shakkar Hajiyarsa ko kadan amma ya tabbatar
a cikin sha'anin Malam-Na-Allah ko tsoron
sata ne ya sami kansa