da yafitowa.
Lokaci guda ya nemi danshi a
makogwaronsa ya rasa, don haka lamarinsa ya
zame wa Hajiya bambarakwai tunda ta san ya
saba fadin gaskiyarsa kai tsaye in yaso ko me
za'a yi, a yi.
Cikin sabbata juyyata ya aro fuskar kunu ya
yafa,
"Me yasa kika yi min wannan tambayar?"
Ta rausaya kai cikin yanayi na saduda a
matsayinta na 'yar masani a cikin halayyar
Adamu, zuciyarta ta tsinke. da ambaton sai
yadda Allah yayi shiyasa gangar jikinta ta
dauki barin jimamain abinda Allahn ya 6oye
mata, hakan ya sa duk da ta nemi guri
musamman ta zauna bata kasa jin jiri daga
zaunen ba.
"Shazali na tuna"
Maimuna Idris Sani Beli 55
Na Shiga Aljanna...1
Ta fada cikin rawar murya tare dą kurawa Adamu ido saboda ta canki amsa da kanta ko
da shi zai mata karya.
Ya kawar da kai yana sake cin magani.
"Nima Na-Allahn kaina ne Hajiya, bana son zarge-zarge"
Sai Hajiya ta sa masa ido sagwalo tana
kallonsa amma zuciyarta cike da hirji da
neman tsarin ubangiji.
Suka dauki tsawon wani lokaci a haka kowa
da abinda cuciyasa ke sakawa.
Can Adamu ya dago ya dubeta fuskarsa na
kokarin shaye fargabarta ta dazu,
"Yanzu yaya zamu yi da maganar sai wa
Salma ankon nan, hakuri zan bata ko kuma za
ki ara min na sai mata kafin na fara aiki?"
Kirjin Hajiya a nauyayae ta kada kai,
"Ba komai zan bayar a siyo sai ka karba ka
kai mata, don kar na baka kudin ka kashė ka ki
sai mata"
Ya mike yana dariya ba tare da zuciyarsa ta
iya tantance abinda yake ji cikin ransa ba.
Maimuna Idris Sani Beli 56
Na Shiga Aljanna...1
"Dama haka rayuwa take, in baka da kudi to
duk zantukanka kila-wa-kala ne wajen
mutane
Cikin yanayin tunani ta amsa,
"An ji, je ka"
*******
Da sanyin yamınacin Alhamis ya dogara ya
fito waje da kwalin sugansa mai kwara-kwara
a hannu. Ban da dolen an ce a yau din nan
kafin faduwar rana zai yi sadakar babu abinda
zai fito da shi har sai ya sha ruwa.
Shi dama can a ibada ba mai bashi wahala
irin azumi, don haka ban da azumin Ramadan
da ya zama farilla baya taba tarkar wani na
Nafila, to yau neman rufin asirin duniya ya kai
shi ka'idar da ta gindaya masa azumi bayan
kwanan zaunen wurudi, sannan ya rufe ranar
azumin da wani raya daren wurudin.
Wuni yayi yana bacci amma abin mamaki
bai hana shi jin wuyar azumin ba, in ma ba
rudewa yayi ba sai ya rantse da Allah bai taba
azumin da ya bashi wahala irin wannan ba.
Maimuna Idris Sani Beli 57
Na Shiga Aljanna...1
Gashi dai a kwance yake, amma a kwancen
yake jin zai fadi.
Kamar ya kwanta a dakalin kofar gidansu
yayi rabon sugan a haka lokacin da ya sanya
yara suka yi masa layi, haka dai ya daure ya
cije yayi rabon sannan ya raba ya kwanta.
Kwanciyarsa ke da wuya ya hango abokinsa
Salmanu na doso shi cikin kuzari kamar ya
tashi sama. Shi ma wani matsanancin kuzarin
ya motso masa bai san lokacin da ya gan shi
zaune ba.
Salmanu abokinsa ne na bani da wani sai
shi, asali a nan unguwar suke zaune kafin
Allah yayi wa mahaifiyarsa rasuwa mahaifinsa
ya auro wata fitinanniyar mace, wadda babu
shakka dalilinta Salmanu ya kangare har ya
gagari kowa.
Karshen barinsa gidan mahaifin nasa ma
wuka ya dauko sai ya yanka matar uban
nasa da kyar mahaifin nasa dad a jama'ar
unguwa suka taru suka karbe matar, dalilin day
a sanya ita kuma t ace in dai da Salmanu zata
ci gaba da zama a cikin gidan to ta gama auren
ubansa. Ta yi yaji ta tafi gidan ubanta, daga
Maimuna Idris Sani Beli 58
Na Shiga Aljanna...1
bisani ta dawo bayan Uban Salmanu ya tara
mutane har da 'yan sanda ya sanar musu ya
sallama Salmanu ya yanke diyancin da ke
tsakaninsu komai, ya dauko babu hannunsa,
ciki kuwa har da sharadin ko gidansa aka gan
shi ya shigo zai iya zuwa hukuma ta bi masa
hakkinsa.
Hajiyan Adamu da ta san ciki da bai na
maraicin Salmanu da kuma sanin wani abu
daga cikin muguntar matar babansa, sai ta
- amince da zaman salmanu cikin gidanta tare da
yarda ai Da na kowa ne, kuma idan da rabo in
Salmanu ya sami rikon kirki kila ya shiryu.
To amma me? Ba a shekara ba sai
maimamkon Salmanu ya shiryu' sai ya kasance
ya fara bata mata Adamu da tsayayya, don
haka babu shiri ta sallami Salmanu cikin dadin
rai inda ta kora shi dangin mahaifiyarsa can
hannun kanin mahaifiyar tasa a Unguwar
Panshekara.
Amma wannan bai raba zumuncinsu da
Salmanu ba wanda lokaci lokaci yana zuwa
gaishe ta kuma bashi da abokin sirri sai
Adamu.
Maimuna Idris Sani Beli 59
Na Shiga Aljanna...1
Tun kafin ya karaso wajen Adamu ya fara kora masa kirari,
"Ruwan rijiya mai wuyar raba gado.
Gawo ba a hawanka ta reshe.
Gonar nesa mai wuyar kai taki.
Buhun Kaya ba a cika ka a danna.
Buzun Bushiya Malam na kallonka yake
salla a kasa.
Gonar nesa mai wuyar kai taki.
Dakalin majina a hau ka a zame, ka hau
mutum ka zauna daidai.
Kutu-kutu mugun Icce, tsohuwa na kallonka
ta kwana da yunwa.
Fagen gyada ba a rasa kala....."
Salmanu ya karaso suka tafa cikin ihu irin
nasu mai bayyana murnar ganin juna.
"Ya aka iya, ya za a yi?"
Inji Salmanu lokacin da ya zauna kan
Dakalin kusa da Adamu.
"Ka zo a lokacin day a dace Salmanu, Sama
ta turnuke da hazo, kasa ta dauke ni ta cilla
mata
Maimuna Idris Šani Beli 60
3
Na Shiga Aljanna...1
Adamu ya fada cikin gyara zama zuciyarsa
na farin cikin jin kamar matsalolinsa sun zo
karshe.
Salmanu ma ya tari numfashinsa.
"Nima da tawa na zo, shiyasa kirarin da
kake min bai taba yi min dadı irin na yau ba,
lallai ka sami guri ka adana shi, domin
amfaninsa ya zo.
"Allah ko? To da me kazoo?
Adamu ya tambaya cikin zumudi.
Salmanu ya kada kai,
"Ai kai zaka fara saukewa, don da alama ka
fi ni abin fada, ni nawa Caca ce kawai, ko a ci
riba ko kuma a fadi... me ya faru ma nag a
idonka ya fada? Kai ka ma rame gaba dayanka
fa!"
Adamu ya kai hannu yana shafar
kundukukinsa tare da kurawa hanyar da yake
yawan ganin Husna ta bullo ido tsawo wani
lokaci sannan ya juyo ya dubi Salmanu,
"Kududdufin soyayya na fada, wanda kifin
da ke cikinsa giwaye ne....."
Salmanu ya kawar da kai cikin bata fuska,
Maimuna Idris Sani Beli 61
Na Shiga Aljanna...1
"Ka ji wani Ajawo! Kai baka dauki kanka
Zaki bane shiyasa kake tsoron Giwa. Macen
banza da har zata iya zama kududdufi a
duniyata, dan uwar kakanta ta ma isa..."
"Kar ka ja ta da nisa cikin rashin sani
Salmanu"
Adamu ya fada cikin jin ciwon zagin mata
da salmanu ke yi, da ma ya tsame Husna cikin
zagin to kalas! ya mayar da matan zogale idan
ya so.
Salmanu zai yi Magana Adamu ya tare shi,
"Kar mu ja ta da tsawo, ka tsayar da zafin
kanka dan mu fahimci juna"
"A'a tafi kawai, na ji ka fada maliyan so,
kar a raina son in ka ce kududdufi"
Adamu ya kada kai cikin murmushin
shanye ba'ar ta Salmanu, a takaice kuma ya
kwashe labari tsab ya bashi. Babu abinda yayi
wa Salmanu dadi sai ritayar Adamu daga
karatun boko, labarin ya yi masa dadi ba dan
kadan ba har bai iya boyewa ba ta kansa ya
fara sharhi,
?
Maimuna Idris Sani Beli 62
Na Shiga Aljanna...1
"Gaskiya barinka karatu yayi min mugun
suga"
Adamu ya sanya masa ido kawai.
"Zuwanka wajen Malam-na-Allah kuma ya
bakanta min, da gaske ne fa shegen Malamin
nan fa yana sunkuyar da 'ya'yan mutane, ni
kuma ko komai nama ne a wajena wannan
harkar ina mugun ganin kazantarta"
Fuskar Adamu ta fara nuna jimami, nan da
nan ya ci laya,
"Na rantse maka da Allah ni bai taba yi min
maganar ba, na san dai fara'arsa da habahabarsa ta sanya ni jin lallai banza bat a kai
zomo kasuwa, na kuma yi kudurin da zarar
bukatata ta biya zan ari takalmin kare, nima ina
ganin kazantar haka Salmanu ka yarda da ni"
"To ka manta da shi, azumin nan ma ka
karya shi, ba fa karya ba ne wurudin nan na
haukata mutane, don in baka tsinto kudi ba na
rantse da Allah hauka zaka tsinto, kuma a
daren irin wannan ranar ne a zaman wurudin
nan suke haukacewa"
Sai wani mugun tsoro ya runtse Adamu, ko
kowa yana karya a wajensa to ban da Salmanu,
Maimuna Idris Sani Beli 63
Na Shiga Aljanna...1
ba a bakinsa kadai ya fara jin maganganu a
akan Malam-na-Allah ba amma shaci fadi ya
dinga daukar maganganun. Ba wai tsarkin
niyya ko ayyukan Salmanu ke janyo masa
yarda a wajen Adamu ba face don ya hakkake
babu matsi a ra'ayoyin Salmanu, saukakan
fatawoyi yake bi wadanda ba zasu matsa wa
numfashinsa da farin cikinsa ba.
Adamu ya lula can duniyar canki-canki ya
balla azuminsa wanda bai rage masa
cikakkiyar awa daya ayi kiran sallar magariba
ba ko ya bar abinsa?
Sai juyowa yayi ya ga Salmanu da karan
sigari yana zuka, a firgice zai yi Magana
Salmanu ya riga shi tare da miko masa sigarin
yana dariya cikin karkace lebe,
"Don Manzon Allah kafa tarihi ka ja abar
nan sau daya ka karya azumin nan da ita, nima
agurina ta tarihi ce don karan karshe nake
zuka".
Adamu ya fizga yayi cilli da ita cikin tsoro
da 'fusata yana kallon soron gidansu kana ya
dubi hanya,
Maimuna Idris Sani Beli 64
2
Na Shiga Aljanna...1
"Zaka janyo min masifa Salmanu, ka manta
sa idon unguwar nan....
Salmanu ya tare,
"Shikenan ya wuce, yanzu mu koma abinda
دو
ya fi kyau da mu...
Adamu ma ya tare,
"Mu fara ta kan yadda Husna zata shigo
rayuwata cikin sauki, don kirjina na fada min
kamar gaba daya ita ce rayuwar tawa ma
"Macen ka mayar haka? Na fada maka in ka
basar su da kansu suke kawo kansu in dai mata
ne, kawai kai dai ka nemi karafa"
In ji Salmanu cikin Gadara.
Adamu ya dinga kada kai cikin jimami,
"Ni ba fari dogo kyakkyawa kamar kai ba
ne da mace kalar da nake so zata kawo kanta
gurina, duk sai jagwal irin su Salma. Kai na ma
fada maka ni ba mata nake so ba, Husna kawai
יי nake so
Suka tuntsire da dariya su duka sannan suka
tafa.
Salmanu ya yafito wani mai lemon fata da
ya zo wucewa ya sai musu. Cikin saduda da jin
ba shi da zabin da ya fi wannan Adamu ya
Maimuna Idris Sani Beli 65
Na Shiga Aljanna...1
karbi lemo ya karya azumin musamman da
Salmanu ya cigaba da kururuta masa yawan
mutanen da suka haukace bayan sun kai
azumin sun kuma zauna lazumin dare.
Salmanu ya cigaba da ce masa,
"Kai ni fa duk namijin da na ga ya kwanta
yana jiran arziki daga kwance kallon gara nake
masa, Allah Wallahi, Kwanji ai ba karya ba ne
nemowa kai ake har a sam wa wasu,
دو
musamman kai da kake da wasun...
"Kai baka das u?"
Adamu ya tambaya yana dariya.
Salmanu ya dauke kai yana cin magani,
"Ni babban burina in na yi arziki shi ne in
dinga tula wa wancan tsohon banzan kura da
mota, ita kuma wannan kilakin da ya 6оуе а
gidansa yake wa kallon mace sai na ci kan
ubanta wallahi, na rantse sai nayi sanadin da
zata mutu a daure shi kuma mijinta ya mutu a
hanyar zaryar ganin ta kubuta, na rantse da
sarkin da ya kage ni"
Dariya kawai Adamu yake idan Salmanu na
cin irin wadannan layun mahaifinsa da
Maimuna Idris Sani Beli 66
?
2
Na Shiga Aljanna...1
matarsa, da can yana dan kwabarša, amma tun
da suka raba gari akan haka yà sanya ya daina
kula shi sai dai kawai ya dinga yi masa
dariya.
Suna ta hirarsu har magariba ta karato, bisa
dabi'ar Adamu da sallah bata wuce shi
Salmanu da sallar ma gaba dayanta bata dame
shi ba dole ya bishi masallaci. Dukkansu dama
suna da kiyaye girmama bukatun juna.
Bayan sun dawo suka wuce cikin gida
Salmanu ya gai da Hajiya, suka dan jima tare
da ita suna hira tana kara yi musu nasiha kamar
yadda ta saba, ta yau har ta fi ta kullum
kasancewar tana cikin firgicin halin da Adamu
yake shirin fadawa.
Bayan sun dawo dakin Adamu suka ci
abinci suka cigaba da hira.
"Wai me yasa na ga Hajiya a firgice? Ina
fatan ba zuwana ba ne?"
ne"
Salmanu ya tambaya.
"Kan zargin na je wajen Malam-na-Allah
Adamu ya amsa.
Maimuna Idris Sani Beli 67
Na Shiga Aljanna...1
"Tana da gaskiya, kuma da na san haka ne,
da na kwantar mata da hankali na fada mata
gaskiya"
"Gara da baka sani ba din, yanzu mu je ga
abinda ya kawo ka"
Salmanu ya gyara zama cikin jin kumaji da
nishadi,
"Faduwa ce fa ta zo daidai da zama, hanyar
neman kudi da samunsu cikin sassaukar hanya
na kawo mana, dabararmu ce kawai zata yi
aiki.."
"Kai da ka ce baka son ganin Kato na jiran
kudi a huce?"
Adamu ya fada cikin gwasalewa.
Salmanu ya girgiza kai,
"Ai ba irin naka ba ne Adamu, ku da kuke
jiran Aljanu su sato na mutane su kawo muku
kuna kwance, akwai bambanci da sana'ar da
kana zaune mutane ne zasu tako sayyadarsu su
kawo maka, hasalima sai ka zuba jari, ka ga da
bambanci?"
Adamu ya rausaya kai,
3
Maimuna Idris Sani Beli 68
Na Shiga Aljanna...1
"Uhum ina jin ka, kar ka manta ka dai sa ni
na karya azumi, da ka bar ni na kai abina ai in
nayi kudin kai ma ka huta...."
"Allah ya kiyaye, me zan yi da kudin jini"
Suka sa dariya sannan Salmanu ya dora,
"Ka na ji ko? Muma malaman tsubbu zamu
zama a yanzu babu sana'ar da ta fi ta kawo
kudi...."
An ki cin Biri an ci Dila...."
Adamu ya fada cikin dariya.
"Na fada maka da bambanci, mu fa har jari
zamu zuba, kuma harkar mu ba ta shirka ba ce"
"Hmn" Ragon nishin da Adamu ya iya
saukewa kenan.
Salmanu yana dubansa y ace,
"Allah kana daukar lamarin nan wasa, ka yi
shahada ka sa kai kawai, a gaba zaka yi dariya
ka gode min'
Adamu ya yamutse fuska ya mike tsaye,
"To ni wallahi kaina ya fara ciwo, kawai ka
je gobe ka dawo, ga kiran sallar isha can ma an
fara"
Maimuna Idris Sani Beli 69
Na Shiga Aljanna...1
Salmanu ya daga kai ya bi shi da kallo
kamar zai kulu, amma sai ya dake, shi ma ya
mike tsayen,
"Banza gwangwani kawai"
Adamu ya ki tanka shi, don tsakani da Allah
da gaske kansa ya fara ciwon, wannan saki na
dafe da Salmanu yayi masa ya rasa da abinda
zai gwada shi.
Salmanu ya kulun, a fusace ya nufi kofa.
Adamu ya daga murya,
"Sai ka zo da wuri goben
Salmanu yayi tsaki,
"Zuwa goben kai ma ka tanadi dubu goma
wadda za mu hada mu zuba jari" Ya shafa
aljihun wandonsa, "Ni kaga tawa na tanado"
Adamu ya kebe baki,
"To babu laifi. Ga duhun dare ga bindiga,
al'amuran duk sun zo da sauki..."
"Ga kuma layar zana ba"
Salmanu ma ya rama bakar maganar.
Adamu ya tuntsire da dariya yana cewa,
"Allah baka hakuri, ka jira mana mu je
sallar Isha sai ka wuce
Maimuna Idris Sani Beli 70
Na Shiga Aljanna...1
"In na je tamu Unguwar na yi, dama bana
son bin sallar 'yan kabalu".
*********
Salma ta kwana da damuwar halin da take
zargin Adamu na neman jefa kansa, ta yi
tunanin duniyar nan dan samo masa mafita ko
kubutar da rayuwarsá daga mutuwar tsaye a
duniya tare da zuwa lahira fankan fayau ta
rasa, shi dai Adamu ba wani yake shakka ba
bare ta dogara das hi ta kai masa kararsa. A
zahirin ido Alh. yake tsoro amma shi din ma
tuni ta fahimci tsoron na ta gina bata shiga ba
ne, domin duk abinda ya hana shi ko kuma ya
sa shi a gaban idonsa zai nuna ai ya hanu har
abada, amma Alh. na 6acewa zai hau mita da
jefar da bakar Magana har da cin alwashin in
yayi kashe shi za'a yi? Wai ma Alh. haifarsa
yayi da zai dinga sa masa ido alhalin uwarsa da
ubansa basu sa masa idon ba? Kai kankat ma
yadda ya ci lagon Alh. akan gudun makaranta
ya tabbatar mata babu abinda Adámu ke bukata
illa addu'a.
Maimuna Idris Sani Beli 71
Na Shiga Aljanna...1
Kwana biyun nan Sa'adatu ta fahimci sam
Salma ba ta cikin walwala, kuma dama tuni ta
dade da sanin matsalarta bata wuce Adamu ba,
amma abinda yake shake mata makoshi bai
wuce kaukauce wa iyakar hanyar da zata iya
taimakonta ba. A wajen Sa'adatu duk abinda
kake so a rayuwa ko wani baya so zaka iya
samun abin in dai ka san hanyar da ake bi a
samu, to ita ta san hanyar saboda haka duk
abinda ta nema a rayuwarta ita ta same shi, ta
sami mijin nuna wa sa'anni wanda bay a
tsallake bukatunta, ta sami kudi ta silarta da ta
silar sana'o'inta, ta sami 'ya'yan da ko
mutuwa tayi dole an san ta bar Iyali, 'ya'ya
takwas ba wasa ba, ta cusa wa kowa
soyayyarta yadda mutane na nesa da na kusa ba
sa ganin laifinta ko da tayi.
Duk da dai ta hakkake ba waccan dabarar
tata kadai ta bata ba har da Kokarinta na
kyautata kowa daga fuskarta zuwa aljihu.
Hakan ya toshe ko da zaginta wani zai yi a
gaban mutanen da take kyautatawa sai ta sami
me karba mata.
Maimuna Idris Sani Beli 72
Na Shiga Aljanna...1
Ta zari jiki ta sami Salma kwance kamar
ruwa a daki.
"Waj Adamun ne yayi miki irin wannan
raunin haka?"
Saima ta dago ta dube ta a jahilce, duk da ta
san ta dauki turbar kwance abinda yake faruwa
a ainihin zuciyarta.
"Wanne rauni kuma Anti?"
Sa'adatu ta nemi guri na zauna.
"Na fahimci son da kike wa Adamu ya fara
kai wa mizanin da ba zaki iya rike shi ba"
Salma ta kawar da kai ba dan ta saduda da
fasawa Anti Sa'a cikinta ba sai dan tana jin
kunyar ta karyata abinda yake gaskiya.
A labarai da fina-finai ta saba ji da ganin
irin son da ke makare cikin zuciyarta bata taба
tsammanin ko da mafarki akwai shi a zahirin
rayuwa ba.
"Haka ne?"
Anti Sa'a ta sake tambaya da fuskar neman
tabbaci mai kuma bayyana ta riga ta tabbatar
tuni.
Maimuna Idris Sani Beli 73
Na Shiga Aljanna...1
Salma ta tashi kwance daga kwanciyar da
take cikin matsanaciyar kasalar da take tasowa
tun daga zuciya.
"Ba ni da tabbas Anti Sa'a, har yanzu cikin
karyata zuciyata nake, abinda nake ji a cikin
raina kamar ba shi ne son da aka saba ji ba, in
ma an saba ba'a taba tarar wa mace ce take
irinsa a inda ba a san darajarta ba".
"Kar ki sare wa kanki gwiwa da wannan
hasashe-hasashen Salma, ni ban goyi bayan
mutum ya tauye wa zuciyarsa abinda take so baa
matukar zai amfane shi. Adamu yà cancanci a
so shi kuma ya cancanci zama miji saboda
haka sarewa kai gwiwa ne ki dinga sonsa tare
da kallon taki gazawar ko wacce iri ce"
Tun da Sa'adatu ta ambata Adamu ya
cancanci a so shi Salma ta saki baki tana
kallonta cikin shakku da alamun neman ba'asi.
Sa'adatu ta lura da ita don haka ta amsa mata
kai tsaye,
TEROL"Kyautata wa iyali a tsatso Alh. ya tsinta,
haka kakansa yayi, haka babansa yayi shi ma
gashi ina sahun farko na matan da ke jin dadin
miji, ina kuma da yakinin Adamu ba zai yar a
Maimuna Idris Sani Beli 74
Na Shiga Aljanna...1
kasa ba, wannan yasa tun kafin ma ki fara
sonsa nayi miki sha'awar aurensa.
Salma ta rausaya kai kawai ta nemo abin
cewa ta rasa, amma dai zuciyarta na raya mata
ko babu abin moro a Adamu ita dai ta fada
tarkon sonsa ba tare da sa ran ko a tukwici ya
kyautata matan ba.
"In kuma kin ga na kyale tawa hobbasar
shikenan, amma ina da yakinin in na sa hannu
ko Adamu ya ki Hajiya sai ya aure ki...."
Cikin faduwar gaba da dukan zuciya Salma
ta sami kanta da rawar jikin kada wa Sa'a kai
baki na rawa ta ce,
"Na amince ki sa hannun Anti..."
"To ba ni sati biyu ki gani"
Anti sa'a ta fada cikin karsashi da yarda da
kai.
Sai karfe sha daya na şafiya ya sami shiga
gidansu don ya gaishe da Hajiya, suka gaisa ya
ci abińcinsa suna hira.
Maimuna Idris Sani Beli 75
7
Na Shiga Aljanna..3.
Wajen sha biyu sai ga kiran Salmanu ya
shigo, sai a sannan ma ya tuna yadda suka
rabu. Yana ta faman tuntsira dariya ya daga
wayar,
"Malam gobe-da-nisa"
Salmanu ma ya tuntsire da dariya y ace,
"Kai na fi haka mukami, Malam ba-jira
kawai zaka kira ni"
Adamu ya sake tuntsirewa da dariya,
kafin yayi Magana Salmanu ya tare shi,
"Kai babu sanya fa! Ina hanyar gidanku
da fatan ka tanadi kudin nan?"
"Sai dai in ni zaka kai kasuwa ka siyar,
amma ko na tauna goro ni kam ba ni da shi"
Salmanu ya sauke dogon tsaki y ace,
"Malam Yawa kake wallahi"
Kafin Adamu yayi Magana ya kashe wayar.
Shi ma Adamu ya sauke tasa yana bin ta da
kallo da murmushi.
ido,
Jikin Hajiya a sanyaye ta kurawa Adamu
"Da wa ka yi waya?"
"Salmanu ne"
Kai tsaye ya amsa
Maimuna Idris Sani Beli 76
2
"Salmanu da ya zo jiya?"
Na Shiga Aljanna...1
Ta sake tambaya cikin alamar tuhuma.
Cikin dauriya Adamu ya kada kai. Ya san
Hajiya na son Salmanu amma sam bata son
mu'amalarsa da danta don haka yanzu duk sai
ya tsure, gani yake kamar zata iya shiga
zuciyarsa ta ramfo kasuwancin da suke shirin
Kullawa ta kafa musu kusa.
Hajiya ta sake sanya masa ido cikin shakku,
"Amma maganar kudin me na ji kuna yi?"
Ya fara hirji cikin zuciya kuma yana iyakar
kokarinsa na boye damuwar fuskarsa lokaci
guda kuma zuciya da kwanyarsa na saka wa
Hajiya amsa,
"Kamar ya san ina cikin halin ha'ula'in
neman sana'a, jiyan nan sai gashi ya zo min da
maganar mu fada aikin gini maná? Shi ma ana
samu kudi musamman na kwangilar tituna ko
gine-ginen gwamnati da ake samu, a wuni daya
kusan kullum sai
66
mutum ya sami dubu biyar
zuwa sama....
Hajiya ta ji hawaye na neman kece mata
amma ta danne shi.
"Sai kai kuma ka ce masa me?"
Maimuna Idris Sani Beli 77
Na Shiga Aljanna...1
"Ni kawai sai na amince, don dama akan
gwiwa nake da neman sana'ar
Hajiya ta sake jin wani yaji ya shake ta na
tausayi da takaici, ba tare da ta shirya ba ta ji ta
tambaye shỉ,
"To kudin da naji yana Magana na meye?
Cin hanci zaku bayar kafin a dauke ku aikin?"
Nan ma bai yi kasa a gwiwa ba ya amsa
mata yana dariyar yake,
"Haba dai, wannan ai sai aikin gwamnati.
Wukar sumunti zamu siya kwangiri da sauran
kayan aiki, in masu daukar aikin suka gan mu
da shirinmu sai sun fi gane cewa da gaske
muke, saboda ba ma so mu je a kananan
leburori"
Hajiya ta saci idonsa ta goge kwalla. Cikin
shanye damuwa a murya ta juyo ta dube shi,
"Wannan sana'ar da wannan rayuwar sun
fib aka sha'awa ko Adamu? Kaico baka iya
zabi ba kuma tsaurin ra'ayinka aikin banza ne
da wofi tun da bai san inda gata da kamata
وو suke ba bare ya nemo maka su
Yayi fuska ya kawar da kai, kamar zai yi
Magana sai kuma ya hadiye abarsa.
Maimuna Idris Sani Beli 78
Na Shiga Aljanna...1
Hajiya ta daure shakar hanci.
"Menene wahala a karatu da yi wa kai
kyakkawan gini har da ya fi aikin leburanci
wahala ko jiran tsammani..."
Kamar Adamu zai cigaba da yi mata kunnen
uwar shegu, amma da ya tuna cewa in ya dauki
wannan matakin ita kuma zata cigaba da
kwakkwafarsa sai kawai ya murje ido ya fara
shirin yi mata bore,
"Sau nawa kika yi min alkawarin cewa ba
zaki sake yi min maganar karatu ba? Hajiya in
gani na ne ya isheki ki sha kuruminki ina fara
sana'ata sai ki wuni ki kwana ma baki sanya ni
a ido ba...."
Ya fara kokawar tashi yana barazanar tafiya
kamar yadda ya saba yi mata.
Da alama ta rasa abin yi yau, a maimakon
kira shi tá lallaba kamar kullum yau kawai sai
ta sanya masa ido.
Shi da kansa ya ji kamar bai kyauta ba sai
ya dan dakata a kofar daki yana cigaba da mita
cikin yanayi kamar zại yi kuka.
"Ko ban fada wa kowa dalilina ba aike dai
ban boye miki ba Hajiya, na ce aure nake so an
Maimuna Idris Sani Beli 79
Na Shiga Aljanna...1
ce sai na yi karatu, shin a duniyar nan ni kuwa
in ban tsani karatu na tsine masa ba anya akwai
wanda zai tsine masa?"
Har yanzu kwányar Hajiya ta kasa dawowa
kan doka da oda bare ta yanke hukunci, kallon
Adamu kawai take zuciyarta cike da fargaba iri-iri.
Shiru duk sun yi jingo-jingum shi yana dogare nauyi da kunya sun hana shi tafiya ita
kuma tana ta faman kallonsa cikin hada kan
kare da na doki. Sai daga can ta nisa,
"To kayi tafiyarka mana"
Ya ji wani turus don bata taba yasar da
fishinsa ba sai yau. Har yayi gaba kamar zai
tafi cikin rashin kkwarin gwiwa sai kuma ya
dawo cikin sanyin jiki, da muryar tausayi yace
mata,
"To kin amince in je?"
"Ina?"
Ta tambaya cikin rashin fahimta.
Ya amsa,
"Kwadagon ginin "
"Ina da wannan mutuncin ne?"
Ya dube ta saroro,
Maimuna Idris Sani Beli 80
Σ
ス
Na Shiga Aljanna...1
Ta kada kai mai nuna yakini,
"Kwarai da gaske, na san da ina da wannan
mutuncin ko alfarmar a wajenka da kafin ka
zartar da hukuncin sai ka zo ka same ni ko ka
99 sami yayanka, to yanzu me kake son in ce
Ya dawo cikin karfin gwiwa ya nemi guri
ya zauna yana dubanta kai tsaye,
"Idan na ci baya a rayuwa ko na kasa
albarka ina da yakinin da sanya hannunki
Hajiya, duk al'amurana sai kin kushe kin
turbuda musu kasa kuma ba haka na ga kina yi
wa Alh. ba......"
Sai ya zarce da shasshekar kukan da yanzun
nan yaji zuwansa makogwaronsa, ba dan
tausayin Hajiya ba sai Husna da ta dan kawo
shawagi kirjinsa daidai wannan lokacin.
Dole ya baibaye Hajiya da tausayi ita ma ta
ji kukan na neman kamata, nan da nan ta hau
girgiza kai t ace,
"Sam ba haka ba ne karka tauye wa kanka
99 albarkar mana...
Ta katse maganarta saboda shagala da
kallonsa yana matsar hawaye, sai ta hau
Maimuna Idris Sani Beli 81
LGugsilA suide З Na Shiga Aljanna...
tunanin me ya sarsh kakanBuka gina shaka
har egaji yoishareshawaydnsa etkinmatitwa
kuma ya,dube da yafara yismatá kalalmaionutum
Tamikaeikin sanyini jikiitanaiedakatasrda
shi, "ao m uoe ekak em usnsy of sinevay ime2
"Tsaya ka karbi wani sako"
Batarjira cewatsagbaita: fashlita ownde aiwar
daka. Ba jimawa ta fito dankoldå lodamainyaky
da bakis da alamatufa ce eveikiidlana ankiä ta
mika mase. svnea sb ainidsy sb sni asds
Ya karba fuskarsa cikerda lalamun rashini
fabimia ya karbesya buda, saesyh tarar sordin
atamfa da na leshi ne. ya sake, dawo daAido
kanta çikinalamar tarnbayada sh sOTSX BY In2
Da alamuna kassashi Hilajiyazta.coms
OYAnkon da Salmadalbakaskassiysi mateszre
wanda nadauki nauyin sai makska jbnlaggashia
nan sai kai kai mata kar ma kaooedidassiyaö
Zuciyarsa eta hugatdasjimswanann siyashr
amma fuskarsa ta shanye, nan domnisyasfarag
murmushin yakeuvarsamadrawhadye?"
"Ai kuwa kin ceto ni Hajiyaşnmı sanradis
zhumet ffe wabwdnnapmlar şatrihyad ta
kawa min kyallonwanko ets susy sanolis
Maimuna Idris Sani Beli