Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MARMUNA DRIS SAR NA SHIGA ALJANNAm Na Shiga Aljanna...1 NA SHIGA AI AN ajiya Uwa na zaune kan tabarma a H dakinta. A gahanta weni katon daro ne cike da daushen goro tana ta faman dauri tare da 'yan wake-wakenta Kamar daga sama aka watso Adamu ya fado dakin dafe da ciki yana kugi, babu batuu ma yayi sallama kenan. Ya zube gaban Hajiya tare da ambaton. "Na shiga uku Hajiya. Ta tsayar da kullin goron tana bin sa da kallon, fuskarta na nuna yanayin takaici. "Na shiga uku ce sallamarka yanzu Adamu?" Ya kwanta kan ledar tsakar dakin yana juyi cikin kama ciki, "To ina ma laifi Hajiya, ai 6arar dankali samun dama ne, ni tara ma na shiga ba uku ba don dai na soke farashin ne..." Hauşhi ya kara kama Hajiya, amma sabo da yi wai gawa da gatsine ya sanya ta yi kokarin hadiyewa har ta yi masa magana cikin mutunci da aminci, Maimuna Idris Sani Beli 4 Na Shiga Aljanna...1 "Ka shiga ukun ya fi sallamar mutunci a wajenka Adamu?" "Na fada miki tara na shiga ba uku ba Hajiya" Ya tari numfashinta tare da tankwabe hannunka mai sandan da take masa. Da takaici ya ishi hajiya kawai sai ta rausaya kai ta ce, "K! Ai shikenan." Ta mayar da kai ta cigaba da aikinta cikin 6ata fuska, Sama da minti biyu babu wanda ya tsinka a tsakaninsu, ba ta bar aikin gabanta ba shi ma bai bar juyi a tsakiyar dakin yana kama ciki yana kuma kugi ba. Hakurin Hajiya ya kai makura, ta dago a fusace ta dube shi, "Ka san Allah? Matukar ba ka tashi ka fita tsakar gida sannan ka shigo min da sallama ba, ba zan saurare ka bа". Ya tari numfashinta cikin numfarfashi, "Yanzu Haj. don Allah da me zan ji?" "Kai ka sani." Ta amsa a fusace. Maimuna Idris Sani Beli 5 Na Shiga Aljanna...1 Ya yunkuro zai yi Magana ta tare shi, "In ba haka ba kuma in tashi in bar maka gidan" Yana jin haka ya yunkura da kyar ya mike cikin kama ciki da numfarfashi, dan ya san ba karamin aikin Hajiya ba ne ta fita ta bar masa gidan. A dudduke ya fice daga dakin yana cewa, "Ai shi ya sa na ce ni gayana nake a duniyar nan ba ni da kowa" Ko kallonsa Hajiya ba tayi ba bare alamar zata tanka masa. Dan tsabar shegantaka sai da ya fice daga gidan gabadaya, sannan ya shigo ya dinga kwada sallama tun daga zaure babu kakkautawa, ya yi ta kai sha biyar, tun Hajiya na amsawa har ta gaji ta tsuke bakinta. Da ya zo kofar daki ma a jere yayi ta kai takwas. Hajiya tun da ta amsa daya ba ta kara saurararsa ba, illa cikin ranta da take nemar masa shiriyar Ubangiji. Mutum shekaru kusan talatin amma har yanzu bai watsar da tashen balaga da shaidancinta ba. Maimuna Idris Sani Beli 6 Na Shiga Aljanna...1 Ya shigo a dukensa kuma ya koma makwancinsa na dazu ya kwanta ya cigaba da kama ciki yana kuginsa. Hajiya ta so ta bata rai, amma da ta san in ma tayi a banza wai man kare sai ta hadiye kawai ta fuskanci Adamu, "Wai don Allah Adamu yaushe zaka yi hankali, kana tuna cewa a shekaru talatin watanni uku kake jira..?" Ya katse ta cikin daga murya, "Amma dai Inna kin san ita yunwa babu ruwanta da babba ko yaro ko?" Takaici ya hana Hajiya Magana sai kawai ta sanya masa ido tsawon wani lokaci sannan ta jinjina ta cigaba da sabgar gabanta. Adamu ya fahimci ta shaka saboda haka ya bar kungin da yake ya tashi zaune yana faman jan doguwar hamma, kana ya kai hannu ya dauki kwalelen goro a daron gabanta ya basga, "Waccan banzar matar Sa'adatu ce ta zuba min abinci kadan, Hajiya sai ki rantse da Allah ubanta ne ya nemo abincin ya kawo" "Da dai kana da mutunci ko cokali guda ta baka abincin sai in ga kamar ta fi karfin zagi a Maimuna Idris Sani Beli 7 Na Shiga Aljanna...1 wajenka, ai ko guga bai ci arzikin komai ba yakamata ya ci na igiya bugu da kari kuma ba Karenka ne ya kamo ba" Kama In ji Hajiya wadda da farko tayi kamar ba zata tanka masa ba. Ya fara taunar goron tamkar mai cin kashi yana kallonta uisb "Wai tsakanin ni da Sa'adatu wa kika Haifad Hajiya?" Kai tsaye ta amsa masa cikin nuna da gaske takeed swnuy sti nse nil snul isb sMA" "Kai na Haifa asuna, ammasitabmijintan kawai na Haifaosai mahaifiyarta da tai kasance yayata amma ta dauke ni mahaifiya!. sesm яүп9г "Shiyasa ta sami lasisin kashe nida yunwa kina kallo Hajiya?eda si iomidst sy umsЬА Hajiyanta sake dakatar vda kullin igorontad tana kallonsa sakare,sdaxalamantabararAdamu ta sha kanta, ta nemi abinda zata celtásrasa saib da kyar ta fizgosbs 62 161 Tsnap necsW" Yanzu donsgirman Allah ba kalji kunyarn cewa an bar ka dalyunwa ba? In zamanin bayau ne fa har jikaka kusa dauka karewar daukar nauyin mace daifya'yasl вg ni ise nionide eкяр Maimuna Idris Sani Beli 8 ile8 inc2 sinht soumisM Ya tare da kunkuni, Na Shiga Aljanna...1 "A yanzu ma ko ban dauki jika ba ya ci a ce an gan ni da mace da 'ya'ya, sai dai kawai don tawa rayuwar lito take a jikin taku. Da alama an turo ni duniyar ne domin ku zabi tsarin rayuwarku kuma ku zabi tawa" Da haushi ya ishi Hajiya kawai-sai ta nuna masa wata kular abinci, "Don Allah dauki ka ci ka tashi ka bar min daki" Bai tanka ba, cikin hanzari ya mike ya janyo kular abinci ya bude. Hajiya na lura da shi, maimakon ya ci abincin tunda yace yunwa na neman kashe shi, kawai sai ya shiga tsince nama kai yana cinyewa har ya cinye ya ture abincin. Kada kai kawai tayi ta cigaba da nemar masa shiriya. Yanzu da bata san halinsa ba, shikenan ya hada ta da surukarta Sa'adatu, don ma dai tuni an zama daya, shekarunsu sha bakwai tare, kai hasalima Sa'adatun 'yar yarta ce, duk abin na gida ne, don haka ne ma babu abinda itama Sa'adatun bata sani ba a halin Adamu. Maimuna Idris Sani Beli 9 Na Shiga Aljanna...1 "Da alama yau ma ba ka je makaranta ba" Ta fada tana duban keyarsa lokacin da ya kamfato ruwa a randa yana maka. Yana ajiye modar ya amsa mata, "Eh, ai in an hana ihu ba a hana aha! Na ce ni babu abincina a karatun boko, duk wanda ya dage sai nayi kuma, to kamar ya dage yin asarar bakinsa, lokacinsa da kuma kudinsa ne' Hajiya ta dan ja fasali sannan ta rausaya kai, "In sha Allah ba zan kara sanya bakina a maganar ka je maakaranta ba, shi ma Yayanka da ya matsu sai ka yi karatun zan fadakar da shi cewa da gaske kake asarar kudinsa yake" "Yauwa! Da kin kyauta wallahi" Hajiya tayi shiru cike da jin haushi tare da debe kaunar in Adamu zai fahimci gatan da Yayansate masa, Yayan da samun irinsa a wannan lokacin yake wahala. Ta shafa dalilin da ya sanya Adamun kin jinin Yayan nasa ta rasa. Kamar Adamu ya san abinda ranta ke rayawa sai gashi ya zo da amsar cikin yanayin halin ko in kula, Maimuna Idris Sani Bell 10 Na Shiga Aljanna...1 "Sau nawa na nemo aure ya hana ni yi, 'yar rikonsa yake neman matsa min na aura ni kuma na ce bana so, wallahi Tallahi babu shegen da ya isa ya aura min wannan kundubar 'yar" Da gudu Hajiya ta saki baki tare da kame haбa. Adamu ya mike cikin fishi, ya sunkuya ya dauki kullin goro 'yan dari uku-uku guda hudu ya sa kai zai fita. Dole Hajiya ta magantu cikin daga murya, "Ina zaka kai min goro har na dubu da dari biyu?" Ba tare da ya juyo ba ya amsa, "Kyauta zan yi da shi" Bai bata damar Magana ba ma, don tuni ya fice, dole ta sauke kai cikin yanayin alhini. Gangar jikinsa ke zaune kan dakalin kofar gidansu rike da sabon littafin Maimuna Beli mai suna MAFARKIN KHADIJA, zuciyarsa da kulliyar lissafinsa na can duniyar jaruman littafin. Maimuna Idris Sani Beli 11 Na Shiga Aljanna...1 Ya dinga cakuda rayuwarsa da ta jaruman littafin tsawon wani lokaci sannan ya koma faman tsintar abubuwan da suka yi dai dai da tasa rayuwar. Muhimmi a ciki shine, zazzafar soyayyara da ke tsakanin Sunusi da Khadija, ya hakikance irinta ce ke cin wuta a kirjinsa ga yarinyar da ko sunanta bai sani ba, shi yasa ya kuma gano bambance-bambancen da ke tsakaninsu su ne, Khadija da Sunusi tare suke son juna, amma nasa son shi kadai yake wa tsalle a kirji yana ji masa raunin da kila wadda ake wa ko ta sani ba zata taya shi jinya ba. Abu na biyu shi ne, Khadija da Sunusi Mahaifin Sunusi ne yayi musu karan tsaye, ko banza yana da kwanjin da idan yayi hakan za a zaci ya isa kuma da guminsa Sunusi ke rayuwa, amma shi fa? Yayansa ke gwada masa kwanji babu sidi ba sadada ya hana rayuwarsa rawar gaban hantsi da hujjar kawai ya dauke masa kwanon abinci ko kudin kashewa idan ta kama, sai shegiyar takurar tura shi makaranta da yake tun tasowarsa. Abu na gaba shi ne, sunusi ya dauki Khadija sun yi auren sirri saboda yana da Maimuna Idris Sani Beli 12 Na Shiga Aljanna...1 kwabbai a aljihunsa, to shi idan ya dauki hakan mafita, in ya auri matar ya boye uwar me zai dinga bata tana ci? Wai ma idan abar son nasa ta goya bayan ta zama Khadija ma'abociyar sadaukar wa so. A guje zuciyarsa ta tsinke tunanuwanta da kasafce-kasfcenta lokacin da ta hango wadda ta ke yi don ita. Can nesa ta fullo tana tafe cikin rausaya tamkar reshen bishiyar da ke jin nishadi a lokacin damina. Adamu ya ajiye littafi gefe ya rafka uban tagumi yana kare mata kallo tana kusato shi. Wankan tarwadar mace doguwa sambal, mai matsakaicin kauri komai nata matsakaici, bai yawa kuma bai yi kadan ba, mai kyakkyawar fuska dauke da madaidaicin dogon hanci..... kai kyawawan idanuwanta ma sun Kawata fuskarta. Ko hauka ne Adamu ya yarda yayi, duk duniya bai taba ganin mai kyau sama da ita ba, bai taba ganin wadda yakamata a so sama da ita ba, sai an rasa ta za a nemi da sunan maneji. Maimuna Idris Sani Beli 13 1 1 Na Shiga Aljanna...1 Ya sauke kai daidai lokacin da ta yi kusatowar da zata iya gane kallon kurillar da yake mata. Ba ya jin sautin takunta har ta bace, amma zuciyarsa na bugun da yafi na karar fasa duwatsu a nasa kunnuwanwa. Sai da ta yi nisa da wucewa sannan ya iya daga kai ya hange ta lokacin da take shigewa wani shagon sai da kayan dinki. Dama kusan kullum in ya ganta a unguwarsu shagon kayan dinkin take zuwa, duk da haka ma yana da tabbacin ko ma dai ya ya ne in ba a nan unguwarsu Kurawa take ba to tabbas ba za'a rasa ta kusa da su ba. Ta jima a shagon kamar yadda ya jima zaune kan dakali suna ta faman kokawa da zuciyarsa wadda ke tunkuda shi wajenta dan ya bayyana kai, lokaci guda kuma yana hango Yayansa ya tsare shi da kabli da ba'adin hana shi aurenta. Kila ya ci nasarar janyo wannan santalar yarinyar ta tsane shi kuma ta sanya shi kwandon shara kamar sauran 'yammatan da ya sha neman aure Yayan nasa na tankwabe masa hannun da yake mika wa neman aurensu. Maimuna Idris Sani Beli 14 Na Shiga Aljanna...1 Duk zagaye-zagayensa, a yau sai da zuciyarsa tayi nasara a kansa, ya gan shi a hanyar kantin kayan dinki ya tunkara da jarumar zuciya lokaci daya kuma yana shafar aljihunsa don tabbatar da cewa nairarsa fari wadda ta kamata ta sadar das hi da kantin kayan dinkin tana nan a muhallinta. Ya dinga hadiye barin da jikinsa yake yana bayani ga mai kantin tare da mika masa darin, "Tukur zare da allura da maballi zaka ba ni, wai kawai na fito wanka, in dauko kaya zan saka sai na tarar babu maballai. Bayan karya alkawari kuma teloli sun fara tauye mudu" Ya dauki wannan salon ne dan janyo hankalin tauraruwar tasa da ke cikin shan sharafin sayen kayan dinki iri-iri, da haka ya zaci duk yadda aka yi madinkiya ce, duk da cewa bai tantance kayan da suke zaba nata ne ko na kawarta da ya same su tare ba, wadda yake da tabbacin a katin ta same ta tunda bai ga shigarsu tare ba. Ko dai ya ja hankalinta a maganar da yayi ba ta nuna ba, sai Tukur ne ya bushe da dariya ya ce, Maimuna Idris Sani Beli 15 Na Shiga Aljanna...1 "Adamu maballi a me yake da har ya zama mudun da za'a tauye?" Kai tsaye ya amsa, "Sa wasa! Ai aikin lada da zunubi ba wahala yake ba, idan daurin aurena za'a tafi na tarar da kayan babu maballi me kake tsammani?" Yayi maganar ne yana satar kallonta bayan ya fahimci sun kawo hankalinsu kansa. Kamar wasa sai gashi ta tanka cikin fara'a da dariya' "Don ma ko babu kai ba fasa daura auren za'a yi ba in dai ka tura sadaki da waliyyi" Ya sha kokawa da nutsuwarsa kafin ta bar shi amsawa a nutse da alamar raha, "Hajjaju amma dai ba haka aka so ba, wai kanin miji ya fi miji kyau, in ji Karin maganarku ta mata ko? Duk suka yi dariya, sannan jarumar tasa ta mayar da hankali kan aikin gabanta na duba kayayyakin da take siya. : Tukur ya се, Maimuna Idris Sani Beli 16 Na Shiga Aljanna...1 "Zaka jira na karasa bata kayanta sannan na nemo maka? Allurar dinka maballin ce nake tsammanin ba ni da ita a kusa. Ran Adamu tas! Ya nemi guri ya zauna yana cewa, "In zaka yi sauri babu matsala" Nan ma ta sake tsomo baki' "Haba da ya amsa cewa a fara bashi kafin mu, da na tabbatar da cewa ko shi ya sami mudun sai ya tauye, kila fiye ma da maballi" "Allah ya sa dai ba haushi kika ji ba" In ji Tukur yana dariya kuma ya juya ya dubi Adamu, "Zata wakilci Teloli 'yan uwanta ta nuna maka su fa ba sa tauye mudu sai dai saba alkawari ko? "Shi ma Allah ya tsare" Ta sake fada cikin fara'a Murmushinta kawai tamkar ya barar da Adamu a shagon, don haka duk karfin halinsa sai ya kasa tankawa, in kuwa ya dage sai ya tanka ya tabbatar yanzu zai bayar da maza. Kila shirunsa ne ya janyo fishin kawarta, Maimuna Idris Sani Beli 17 Na-Shiga Aljanna...1 'Ke matsalarki kin cika arahar hakora wallahi' Ta ki damuwa, "A'a bari na 6ata fuska, tamkar kunun da babu suga babu gasara Adamu ya sake laluba abin cewa ya rasa, amma wannan karon faduwar gaba ce ta hana shi. Kawarta bat a tanka ba ita ta sake jan maganar, "Bakeken mata irinmu in muka ce kunu zamu dinga ci ai zamu gamu da kwantai Amina" "Eh, haka ne, gara ku dinga hadawa da tallar kai" وو" Ba na son bakar Magana" "Amma kika nema Ta sake tuntsirewa da dariya ta ce, "Ke matsalarki baki iya siyasa ba Amina, zaki rasa masu yi miki shaidar arziki bayan 99 mutuwa A sanyaye Amina ta ce, "Ai haushin da kike bani ne yake shafar kowa Husna, yanzu don Allah ina ke ina Maimuna Idris Sani Beli 18 J.aansA egide a Na Shiga Aljanna...1 sauraron Sani mai Injin markadeda sunan soyayya?" y nos inwsk iuk nus o:Guduma biyu ta dake shigaikahon zuci ta farinacikin tsintar sunanta Husna, ogaskuma waddal tà afi sta,sewátorumagánar Sanima! markadesri sgik evaat e'es sb nuler isl sie ED Sn Kwatsam! sai ga wadda ta fisu tsaurita fito daga bakin Husna,rsd szob at ebi eb enaldEkIB udf Kisbars Sanilya cigaba da amfana da furtai Kalmarı yana sona yańa cikawanicabun daga burinsa, oni kuma ya cigaba datattaro cinikini markadensal yanaabani tükwicinušoshinsaka hana masa wannanlan tauye hakkinsai da yawа tunda ba zai iya tarackudinsaurena sbajs bain kamata a hana shi furta abinda yake ji gaméda nia kirjinsa balbl sy BD Ssiem sвy аb пог sh swCikinedariya Amina tarce, ed noa Tsisddst sy sh "Barki da mutunci Husna'sied sbodsa on sd Ita ma tana dariyar ta amsaz nob ide sws stss "Barashin mutinci ba ne, saukinckai ne da iya zama da mutane. Sai dai hakan ba yà hanas kokarin cimma burinanbałzan sáuríbmára sanata baskumá ba zani auri mai karámar sana'a ni Hnans bs esi de loknoi weni taswon ds КSntin Maimuna Idris Sani Beli 19. و من sim yhsiaالمن Na Shiga Aljanna...1 ba, ban taba tunanin yin auren soyayya ba ni auren kudi kawai zan yi" Adamu ya dinga yarfe gumi a saye ba tare da lurar kowa ba. Macen da yake so sunanta Husna, yau ga shi zaune kusa da ita da tazarar da bata kai takun da za'a tsaya kirga ba, sannan tayi magana, maganar da za'a iya gane alkiblarta da inda ta dosa har karshen rayuwa. In babu irin son da yake mata lallai akwai aibu cikin maganganunta, sai dai shi mai rufaffen ido a so ya mayar da aibun nata yabo, sai ya mayar da dukkan aibun kansa da kan yayansa wanda shi ne bai so Husna ta gan shi a a layin mazan da zata iya aure ba. Rauni a zuciyarsa yanzu shi ne, yaya zai yi da son da yake mata? Da ya laluba zuciyarsa ya tabbatar son ba irin wanda ake iya yafewa ba ne, saboda haka ina za shi ya samo kudin da zata aure shi don su? A kwanakin da suka gabata burinsa daya ne, shi ne Husna amma a yau ya kara na biyu, shi ne kudin da zai farantawa Husna. Bai san hakikanin abinda yake wanzuwa a kantin ba tsawon wani lokaci har sai da Husna Maimuna Idris Sani Beli 20 2 Na Shiga Aljanna...1 ta farkar da shi da zazzakar muryarta cikin yanayin barkwanci, "Ranka ya dade za mu wuce, da fatan zakaа yafe wa telan da ya tauye maka mudun, in kuma ba zai yafu ba ka je ka kawo rigar na daura maka maballin a madadinsa". Ya dage iyakar dagiya ya wurga damuwarsa can bangon zuciyarsa, ya dago da murmushin yake, "An yafe masa" Yayi saurin kawar da kai saboda zaton dakewarsa ba ta cika mizanin da zata 6oye damuwarsa da rikitarsa ba. Ya ji wani kwarin gwiwa da kyau lokacin da cikin dariya Husna ta amsa masa, "To madalla da karimi mai kyautar yafiya" Bai shirya ba ya sami kansa da sake се mata, "Da alama kin bambanta da telolin zamaninki, ni da kin iya dinkin maza wallahi sai ki zama Telata" "Ayya ban iya ba, amma idan ka tashi kawo dinkin amaryar taka ina maraba" Maimuna Idris Sani Beli 21 Na Shiga Aljanna..,1 nixTa amsa masa lokacin da suke 'ficewa daga kantin, matakin da ya tabbatar masa dabi'ar Hisnacel kawai tayiaiki akansa ba đơn ya zamanvani abu a zuciyarta ya sanya shi samun matsayin shimfidar fuskarta basy is d a Nan ya shiga caje kansa ciki da bai, don ganirvme ya rasa a kyaunhalittagsb BY niBakinnesosai mai matsakaicin tsawo amma kakkaura, mai dogon hanci da manyan idanuwa wadanda suka dace da tsarin fuskarsa, yanasdasbtsararren Saje da hashin baki wanda yakeü saisımasa nkwarjini; musamiman saboda sumar kai da yake Tarawa wadda tun Hajiyarsa naifadaihart a gaji ta dainatirawa inaw iH sY A tsarin. halittarsas yastabbatar babu abn kušhen da Husná izata ki matsalarsa kudi ce, kuma dolebzainemoisu in dai szasu bas hi abinda yake so, wati Husna. E6 nilolst sb sinsded ail ssis idsllaw ex****** ** in blainss3 "sisisT cmes il is2 vAdamu dutkuslies gabane Malam-na-Allaň a dakinsa mai karancinahaske ko dad a hasken Maimuna Idris Sani-Beli 22 ils8 inse anbi srumisM E 2 Na Shiga Aljanna...1 rana balle daidai wannan lokacin na duhun magariba Da kyar ake iya gane abinda dakin ya kunsa, tarin litattafai ne zube a ko ina nan da can a dakin, sai kuma jeren allunan rubutun sha suma birjit jingine jikin bangwayen daki, akwai raki rataye dad a kayayyakin malamin sai kuma kala-kalar carbi manya da kanana su ma rataye a jikin rakin. Daga can kusurwa akwai wata karamar kantar katako mai dauke da kwalaban turarukan wurudi su ma kala-kala. Bayan gajeruwar gaisuwa Adamu ya gabatar da bukatarsa, "Malam zuwa na yi ni ma a ba ni wurudin nan da aka ba Sulaiman, yanzu na gane mutum bas hi taba kwanciyar hankali in ba kudi ya mallaka ba?" Malamin yayi gajeren murmushi ba tare day a tanka bay a bude wani kundi dake kusa das hi ya zaro takarda mai kunshe da rubutun ajami, da kuma bayanin da fassarar boko a bayan takardar. Maimuna Idris Sani Beli 23 Na Shiga Aljanna...1 "Gas hi, kamar dai wancan ne da nab aka ka dawo min da shi" Adamu ya karba ya shiga dubawa, sai can ya dago ya dubi Malam, "Eh na gane irin wancan ne?" Malam y ace, "Ai dama ba ka kawo min turaren ba, ko ka salwantar nab aka wani?" Adamu ya girgiza kai, "Yana nan Malam" Malam ya dubi agogo, "Shikenan sai ka je, abinda baka gane ba ka dawo gobe, yanzu dab ake da fara kiran sallar magariba. Adamu ya fara godiya yana kokawar sa hannu a aljihu,, cikin ransa yana fatan Allah ya sa kamar wancan lokacin Malam y ace ya bar shi, don Allah ya sani duk bogi ne sa hannu a aljihun, naira hamsin ce a aljihun nasa. "A'a ka bar shi kawai, zamu hadu wani lokacin? In ji Malam, addu'ar Adamu ta ci kenan. Ya kara wata godiyar sannan suka tashi gaba daya Adamu na yi masa sallama. Maimuna Idris Sani Beli 24 ร Na Shiga Aljanna...1 ********** "Na kira ka ne in ji yadda aka yi ka san gaibu" Ko gaisawa da Yayansa ba suyi ba, ya tare shi da wannan maganar cikin daure fuska, alhalin takanas ya aika aka yi kiransa. Ya zaci ma wani abin kirkin ne ashe wulakancin da aka saba za'a yi masa. Kansa na sunkuye yana zaune kan kujera yayin da Yayan nasa ke tsaye kerere a kansa. Sai dai duk bacin rai da rashin kunyarsa ya hadiye kayansa a ciki. Jiki a sanyaye ya daga kai ya dube shi, "Alh. Ban gane na san gaibu ba fa, a ina na fadi hakan?" Yayansa ya amsa masa ba tare da ya juyo ya dube shi ba, "Shekaranjiya ka fada wa Hajiya" "Na ce mata gobe za a tashi kiyama?" Ya amsa cikin cin mur da dakewa. Maimuna Idris Sani Beli 25 Na Shiga Aljanna...1 Dama tun shekaranjiya bayan ya ji kudurin Husna na kin auren mara sana'a ko kuma mai karamar sana'a ya ji-ya tsani kowa a duniyarsa, musamman ma Yayan nasa wanda ya fi kowa gina masa Katanga da sana'ar, kuma tun shekaranjiyan yake atisayen yi wa kowa bore, bai yarda a shigo rayuwarsa a tauye masa Husna a cikinta ba. "Karatu ne na bar shi kuma babu shegen da ya isa ya kuma sawa na yi" Kalmomin da yake ta maimaitawa kenan tun daga jiya zuwa yau, da ma yanzu da yake gaban Yayansa cikin zuciyarsa. Yayan na sa ya sha mamakin wannan bakar maganar da Adamu ya yarfa masa, amma dai ya hadiye yadda ta bata masa rai, yana kallonsa kai tsaye ya ce, "To ko hakan ma ka fada mata ne? gaskiya na gan ka da wannan zabgegen carbi mai 'ya'ya dubu kana neman gafarar ubangiji....." Takaici ya kama Adamu na ganin an canja masa ma'anar wuridi..... "Ni ba Istigfari nake ba". Ya tare Yayan a kuntace. Maimuna Idris Sani Beli 26 3 Na Shiga Aljanna...1 "Oh Hailala kake kenan, musamman tunda gobe za'a tashi kiyama, shi ne kake sabunta shahada?" Adamu ya sake yin fuska yana murza 'ya'yan carbin hannunsa daya bayan daya tare da yin mus-mus da baki "Kalas! Da alama ta wannan hanyar kake iya hango abinda zai faru gobe". In ji Yayan cikin nuna halin ko in kula. Har yanzu Adamu yaki ya tanka illa fuskarsa da take iyakarta na cin magani bakinsa kuma ya dukufa da motsi. Yayan ya basar inda ya jira shi yayi adadin da yake bukata yana yi masa kallon tura aniya, sai da don kansa ya gaji da kallon da kuma murza carbi sannan ya ajiye, sai dai bai ce komai ba. Yayansa ya ya fara safa da marwa a tsakiyar falon cikin yanayin mazantaka, "Hajiya ta sanar da ni cewa wai ka hango baka da abinci a karatun boko, haka ne?" Adamu ya jima kafin ya tsinka. Har yanzu yanayinsa na nuna akule yake, "Duba na yi kenan?" Maimuna Idris Sani Beli 27 Na Shiga Aljanna...1 "Ah! To wa sani? Abinda nake tambaya tun dazu kenan rashin muhimmancina ya hana ka bani amsa". Adamu ya dan fara mutsu-mutsu yana kunkuni, "Ai ka ji matsalar, shiyasa ma babu amfani na batawa kaina lokacin yin karatu,

Chapter 1 of 7