domin shan iska domin abin da ta gani ya bata mamaki
shawara ta yanke kawai ta kirasu a waya duk inda suke su zo
daidai lokacin Kalid yay parking da motarshi ya sakko cikin shigar kamala suka gaisa kafin ya tambayi Ummi baby shin ko'ina Faridan ,
wayarta ta fara ringin murmushi tai tana d`aga wayar tare da karawa a kunne
,Hello Ruma kuna ina ne, to wallahi duk inda kuke ku dawo gida , ga Kalid ma yana jiran Farida",
daga can bangaren Ruma cikin tashin hankali ta fara cewa ," haba Ummi wacce irin magana ki ke, to kingan mu Alji Nuhu ne bansan mene yay wa Farida ba tana kwance kamar ya kashe ta ",
ita ma Ummin cikin sabon tashin hankali tace ," ban gane ba ku na ina , ina Faridan "?
bayan Ruma ta fad`a mata komai hankalin Ummi baby ya sake matukar tashi , nan ta sanarwa da Kalid shima
hakan yasa suka shiga motar Kalid suka bi adireshin
suna isa da gudu Kalid ya banka cikin gidan yana kiran sunanta
yana zuwa babu abin da ya canza ko shurawa babu
hakan yasa Ruma suka sa ta a mota suka nufi asubiti ,a cikin tashin hankali suke dukkansu
asubitin kudi Kalid ya wuce dasu aiko suna zuwa aka basu taimakon gaggawa.
Alaji Nuhu yana cikin mota yana ta nazari "shin ko mutuwa tai , haba ba zata mutu ba ai karuwai suna da tsawon rai , to idan kuma ta mutu aka sami gawarta fa a cikin gidana",
kawai Alaji Nuhu ya juya motarshi ya koma gidan,
yana zuwa ya shiga, kai tsaye dakin nasa dariya ya kece da ita yana cewa," ai ni na sani da man kawai salo ne , ga shi ta tafi ,
amma yarinyar nan ta cuce ni ai dana sani nayi abina a hakan amma ba komai gobe ma rana ce",
ya cire kayansa ya fara bacci .
Inna gobe take son zuwa kaduna domin ma harta shirya kayanta tana son taje ai maganar auren Zakariyya da Fadeela
ita kuwa Jamila ciki ya tsufa sosai yau kwananta 1a Jos
sakamakon 'yan uwanta sun zo sun tafi da ita amma Inna sam bata ji dadi ba ,
Fadeela tana cikin daki a kwance cikin ranta take cewa ,"haba Inna bana san Zakariyya ne saboda komai yace Allah yace annabi yace , kuma idan ma ya aure ni , ni bazan fasa fita duk inda nake so ba
ita kuma Farida da ta dena karuwanci mu yanzu muka sa kafa duk da na dade a ciki",
Inna ce ta yanke mata tunani sakamakon kiran sunanta .
Alaji Sadi ne zaune cikin farfajiyar babban gidansa , yayin da wayar shi ta fara ruri yay saurin dauka don ganin mai kiran
dillalinsa ne Junaidu yana dauka ya fara cewa ,"Junaidu ya akai ne , kasan bana san matsala domin ganin kiranka ba ya wuce an samu matsala ",
daga can Junaidu ya fara cewa ," ai Alaji babu wata matsala tunda sun amshi kudin gida kawai ranar tashinsu ce ya rage ,"
Alaji Sadi yace "yawwa!
Lokacin su na cika karsu sake mini ko minti guda domin rushen gidan za'ai samfari za a canzan",
Junaidu yace ," babu komai Alaji Allah ya kara daukaka",
Yau Zakariyya kamar farin ciki zai kashe shi , ya rasa yadda zai sa ranshi saboda murna dalilin wannan murna kuwa dawowar wakilansa ke nan yanzu daga kano gidansu Zainab, an ba shi aurenta , dalili kuwa ta tabbatarwa iyayenta shi ne zabinta .
Anan cikin asubiti kam sai kai kawo suke cikin tashin hankali wajen minti talatin da shigar likitocin amma har yanzu basu fito sun basu wani bayani ba
kai kawo suke yi cikin damuwa bari ma ita Ummi baby ga zancen Fadeela na cinta
a yanzu dactor John ya fito daga dakin da Farida take shi da wata nurse
hakan ya basu damar shan gabansa da sauri don jin wanne hali take ciki
Doctor John cikin kwarin gwiwa da hausarshi da bata wadace shi ba ya fara cewa.....
Share and comment.π K`AWAR KARUWAIπππ
BY
AUTAR MARUBUTA
_____________,___________________________
Page 23&24
"Ina baku hakurin rashin sister na ku , ta rasu ta mutu sai dai Allah yay mata afuwa , ku yi hakuri ",
yana gama fad`a ya wuce zuwan sauran ayyukan da yake da su,
Da gudu Ruma ta fad`a dakin cikin tashin hankali , jikin Farida ta fad`a cikin mummunan zautuwa da tashin hankali
ita ma Ummi baby cikin mummunan yanayi ita da Kalid suka shigo dakin
Ruma ta bude fuskar Farida cikin tashin hankali ta sake rurucewa da kuka tana cewa," mene haka Farida da man mutuwa zaki yau amma kin kasa sanar dani , mene amfanin zaman taren da mukai da har za ki mutu babu mu ,"
Ummi baby ta zo ta hankade Ruma gefe cikin tashin hankali tana cewa, "ba mutuwa tai ba matukar kika sake cewa ta mutu ke ma sai na kashe ki , Farida samm babu iinda zata ta barmu",
Ummi baby ta koma jikin Farida tana cewa," tashi farida, tashi mana dan Allah, na faje na samo wani abin mamaki zan sanar dake yanzu ki tashi mu tafi gida ",
tana jijjigata tana dukanta
wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Kalid, wani kundululun bakin ciki ne ya tokare masa mak`ogaro tabbas da zai hadiye shi , to shima mutuwarsa ce
Ruma cikin sabon tashin hankali ta cigaba da cewa ," Allah ma ya sawwake ki mutu yanzu ,"
da sauri Ummi baby ta tashi ta fad`a jikin Ruma tana cewa, "Farida taki tashi Ruma wallahi ta mutu wallahi ta mutu , tafa mutu wallahi Ruma ",
da wata mutuwar kauna da tausayi suka rungume junansu suna ambaliyar kukaπππ
" me yasa zata mana haka , wannan shi ne shiryuwar da tai , ta koma ga Allah me yasa",
inji Ummi baby Ruma ta cireta a jikinta tana sabon kuka ba tare da ta iya cewa komai ba
duk idanunsu jajir sukai zai zafi suke musu duk sun fita daga hayyacinsu
Allah sarki Kalid kawai fuskar Farida yake kallo yana tuna farkon had`u warsu ya matukar girgiza a halin yanzu.
Bayan sun koma gida
a kaiwa Farida dukkan wani abu da addini ya tanadarwa mamaci , lokacin da za a kaita makwancinta sabuwar tashin hankali suka sake shiga domin Ruma sammm ta hana a dauke mata Farida , da mar da aka samu lokacin da ta yanke jiki ta fad`i sannan aka tafi da Farida
ita Ummi baby ma da zata yanke jikin ta fad`i ma iya cewa tafi jin sauki domin kawai dai gatanan ba gunki ba ,ba mutum ba, bata gane komai da kowa .
Da ma duk mai rai lokaci yake jira , kowa na haka ne , amma Farida tayi sa'ar tafiya domin dukkan abin data aikata tsakaninta da mahalicci ne kuma ta ne mi tubarsa
sai dai muce Allah yasa idan tamu tazo mu cika da kyau da hasken imani wanda suka rigamu gidan gaskiya kuma Allah ya sa sunje a sa'a.
Washe gari
Inna da zazzabi ta kwana sakamakon tun jiya da dad dare aka musu waya cewa an sa ranar bikin Zakariyya abin ya d`aga mata hankali
yanzu Fadeela ta samu labarin mutuwar Farida aiko cikin tashin hankali ta nufi gidan nasu
cikin kuka ta fad`a cikin gidan ,
duk su Ruma su na kwance mummunan zazzabi ya kamasu
haka Fadeela ta zauna tana musu kuka , amma Ummi baby kawai tana kallonta da abin data ji ta gani ba tare da ta sanar da komai ba ,
Fadeela tayi matukar kukan gaske da rashin Farida.
Bayan kwana biyu
Kalid da Ruma da Ummi baby ne zaune cikin gidansu, bayan sun gaisa yay musu ya karin hakuri da jiki
sai ya fara cewa,"yau kwanan Farida uku da komawa ga Allah, Allah ya kara haske cikin kabarinta ,"
suka ce ,"amin ,"
sannan yaci gaba da cewa ,"sai dai akwai nauyin da ya kamata mu saukewa Farida, sabida dole mu fitar da zancen Alaji Nuhu kuma mu kaishi kotu , sannan mu ne mi 'yan uwan Farida mu sanar dasu halin da take ciki, domin bukatar addu'arsu",
Ummi baby ta kalli Ruma yayin da tai mata murmushin da ya fi kuka ciwo
Ruma ce ta bude baki tana cewa, "wallahi ni ma Kalid ko da baka zo da wannan zancen ba , sai nayi duk inda nayi dan Alaji Nuhu ya fad`i ta yadda ya kashe Farida, kuma koda zan tafi tsirara sai naga an hukunta shi mene tai mai zai kasheta ",
ta fashe da kuka
Kalid yace ," kiyi hakuri ba zamu yi sanyi ba dole a hukuntashi ko waye ",
ita ma Ummi baby taji wasu hawaye sun zubo mata
Kalid yace," karku damu kawai ku nemo family dinta ko da yake nasan tsawon rayuwarku da ita kun san hakan ",
Kalid ganin suna kuka yasa yabar maganar yace idan ya dawo zasi maganar
bayan ya fita Ummi baby tai nannuyar a jiyar zuciya tana share hawaye
sannan ta kalli Ruma tana cewa", Ruma sai na wulakanta Fadeela a duniya sai nasa an gujeta an tsaneta ,sai na rabata da duk wani saurayinta dake son aurenta ",
cikin mamaki ita ma Ruma da hawaye ta kalleta ," mene ne kuma Fadeela tai miki Ummi , gaskiya karki mata haka ",
murmushi Ummi baby tai tana cewa," naso Farida na duniya domin ta ga yadda Fadeela ta ci amanarmu ta yaudare mu ",
Ruma ta sake fuskantar Ummi baby cikin rashin fahimta tana cewa," wai ki mini bayani mana ",
da mummunan bacin rai Ummi baby tace," na shirya komai na yadda zan tozarta Fadeela kawai wasan za a fara , Ruma wallahi Fadeela karuwa ce ",
wani faduwar gaba Ruma taji
cikin mamaki ta kalli Ummi baby
nan Ummi baby ta sanar da Ruma komai da kuma karin hujjojin da suka tabbatar mata Fadeela karuwa ce
wata ashar Ruma ta murgino tana zagin Fadeela
" amma yarinyar nan taci abinci a kan mu , wato har legos tana zuwa
tabbb to ni ma wallahi ina bayanki don ganin mun yaye mata rigar mutuncin da take yafawa a idon mutane , sai mun kwance mata zani a bainan nasi wallahi ".ππ
yau ake sanar dasu Inna cewa Jamila ta haifi na miji , Inna tayi murna sosai π
"ai wallahi ma Zainab kin yi kokarin zama da Fadeela domin ni wallahi tunda take kula karuwai kallon karuwa nake mata",
Amina salisu ta fad`a tana gyara zama a kan gadon Zainab
Zainab tace ," a'a Amina ki ringa kyautata mata zato ",
Amina salisu ta tabe baki tana cewa", ni fa wallahi ma kawai damuwata mu kai mata ankon ki da Zakariyya domin nasan har yau bata san shi zaki aura ba , naga yadda idon shegiya zai koma ",
Zainab dariya tai tana cewa," gaskiya kina da abin dariya ",
daga can wajen gidan kuwa mahaifiyar Zainab taji sallama yayin da taga wasu 'yan mata su biyu , suka gashsheta ,
ganin gun Zainab suka zo yasa ummansu Zainab cewa su shiga Zainab d`in na ciki
Sallama suka yi cikin dakin da Zainab da da Amina suke ciki
duk mamaki ne ya kashe Zainab da Amina
," innalillahi ",
Amina ta fad`a
murmushi Ummi baby tai tana kallon Ruma
Ruma ce ta kallesu tana cewa ," haba dan Allah sai kace kinga shedanu , muna tafe da muhimmiyar magana ne a kan K`AWAR ki Zainab, wato Fadeela ",
Amina Salisu tace ," K`AWAR ku dai ai mu tun tuni mun mance da shafinta domin bata da banbanci da ku , domin abokin b`arawo to shi ma barawon ne ",
murmushi Ummi baby tai tana cewa," gaskiya ne sister, amma akwai abin da baki sani ba bayan wannan ",
Zainab tai a jiyar zuciya tana cewa ," ku zauna domin maganar zata fi ",
murmushi sukai suna cewa ," mun gode ",
Anan kuwa Fadeela ce tare da wani saurayi a cikin gidansa,
tana zaune a falon gidan amma hankalinta duk a tashe yake domin Alajin da sukai magana zai siya mata gida ba ya d`aga kiranta ya juya mata baya hakan yasa take cikin tashin hankali,
ji tai ana shafa mata bayanta , ta kalli kyakykyawan saurayin tana mai murmushi , zama yay jawota ya dorata a cinyarsa yana cewa," baby Fadeela ina sanki sosa",
murmushi Fadeela ta kuma yi mai na yake da damuwa tana cewa, "Sadiq ni ma bani da wanda nake so kamar kai , amma sai dai ni Ina yin karuwanci ne saboda jin dadi , amma yanzu dole nai karuwanci mai yawa ba dare ba rana zan yi yawon bariki domin na sami kudin da nake nema ",
a jiyar zuciya Sadiq ya yi yana cewa ," wallahi Fadeela da ina da kudi sai na share miki hawaye, amma kinsan yadda nake ",
kallonshi tai tana cewa," na sani amma bari na tafi yanzu ",ta mike tsaye
saurin jawota yay yana cewa," haba ya za ki to kuma ki tafi , gaskiya ni ban yadda ba ",
rigar dake jikinsa ta fara cire mai ta fara gogar bayansa tana sumbatarsa a hankali yake jin shigar sautinta sakonta na kaiwa dukkan ilahirin jikinsa
hakan yasa ya rungumeta yay daki da ita ya banko kofar ππ
to babu hanyar da zamu leka bare mu kai rahotoπ
share and comment..........π
K`AWAR KARUWAIπππ
BY
AUTAR MARUBUTA
_____________________________________
Page 25&26
Ruma ta kalli Zainab tana cewa, "mun zo da maganar da muke son fad`a muku wanda babu wanda ya sani a kan Fadeela, muna fatan zaku am she mu ku fahimta kuma ",
Zainab tace," dan Allah mene wai ",
Ummi baby ce tace ", Fadeela karuwa ce ",
dauu Zainab taji a ranta cikin fad`a ta fara cewa ," wato kuna san b`ata mata suna ke nan saboda kun jawota taki sauraranku ko ",
Ruma da Ummi baby suka kalli juna cikin rashin jin dadi
Amina ce tace ," haba Zainab ni kam su bamu shaida a baza mu karyata su ba",
cikin jin dadin maganar Ruma tace ,"yawwa!
Gaskiya ne wannan muna da hujjoji da irin mazan da Fadeela take mu'amala dasu , da hotunanta ke har ido da ido muna da yadda za a kamata ",
.
Zainab tai a jiyar zuciya cikin kasala da mamaki
yayin da Amina tace su gabatar da dukkan abin dake tafe dasu ...........
har wajen magariba su Ruma suka kai gidansu Zainab suna ta tattaunawa har suke fad`a musu mutuwar Farida
Amina da Zainab duk sun sha jinin jikinsu
sun yarda da maganar su Ummi baby sai dai abin ya matukar tada musu da hankali ba kadan ba
haka su Ummi baby suka koma gida yayin da sukai musayen numbobinsu
suna isa gida sukai sallaπ
mutanen ku an fara komawa ga Allah bayan an yi salla wayar Ruma ta fara ringin tana dubawa ta ga Kalid ne nan ya sanar da ita an tafi kama Alaji Nuhu
Ummi baby tace," tsinanne kawai ni wallahi ma Ruma wannan harkar duk ta fita a raina tunda Farida ta bar duniya, ambassador tun shekaran jiya yake kirana ",
Ruma tace ," Hmmm Ummi baby ke nan , wallahi nima tsoro nake ji , amma anya kuwa zan dena ",tana dariya
Ummi baby tace "yanzu kinsan mene shirin da nake",
Ruma tace ," fad`a mini dai naji ",
Ummi baby tace" yanzu haka ina bibiyar Alaji mansur da Aliyyu wato samarin Fadeela , saboda su ne take ganin zata yaudara ta auri wani a ciki",
Ruma ta girgiza kai tana cewa, "tabbas kinyi tunani idan ma ta kama wallahi kawai mu aure su ",
Ummi baby taiwa Ruma wani kallo tana cewa", wane zai auremu bayan sun san mu su waye ",
Ruma tace ", Hmmm, mu yi kokarin hakan dai domin zuciyar Fadeela zata fi ciwo , ni kam na dau damarar bakanta mata rai , ai wallahi yarinyar nan ta yaudare mu mene ne ta rasa , gara mu koba komai babu yadda zami ",
Ummi baby tace ," Hmmm ".
Yanzu'yan sanda suka tafi da Alaji Nuhu suka tabbatar masa da ana tuhumarsa da kisan kai, sai dai yace babu wanda ya kashe , sun yi kuskuren adireshi ππ
yanzu misalin karfe 12na dare , sako ne ya shigo wayarta sakamakon ko kwanciya ma batai ba hakan yasa ta duban wayar rubutu ne da manyan baki ,
" Fadeela ki fito ina waje yanzu ",
Fadeela ta tashi cikin nutsuwa da iya takunta ta dauki mukulli cikin iyawa ta fita ba tare da Inna ta farka ba
tana fita ta tadda Alaji Shehu a waje , cikin bacin rai ta fara cewa haba Alaji ai yanzu dare bai yi ba 12fa mutane zasu iya fitowa ",
Alajin da idanunshi jajawur ya kalli fadeela yana cewa," ni fa bazan jira dare sosai ba , yanzu nake so domin ko bacci na kasa , kuma tun tuni na miki transfer na kudi , don haka babu jira ",
Alaji ya fara kokarin cire kayansa, yana ajewa a gefe
Fadeela ta waiga ko'ina da ina tana cewa," ni wallahi bana san kofar gida da kazo da mota kawai mu tafi gidanka ",
kafin ta rufe ba ki kawai taji Alaji a kanta , cikin ranta tace ni da jaraba
Alaji Shehu sai da yay mata ......π
sun jima a kofar gidan har Fadeela ta matsu ya tafi ,
ni ko wannan wacce irin jaraba ce ita Fadeela ma abin Nata a cikin dare ne kuma kofar gidansuππ
ai shi ke nan Allah yana ganin kowa da komai ,
misalin 1:20
fadeela ta shiga gida yayin da shi kuma ya koma inda ya fito ,
wanka ta shiga a lokacin yayin da Inna ta farka tana tsaki da wannan hali da Fadeela.
Washe gari
Ambassador ne tare da Ummi baby a kofar gidansu
juya masa keya tai cikin fushi , ambassador yace, " Haba baby kiyi hakuri mana ".
Ummi baby tace , " Nifa wallahi bazan hakura ba sai ka mini abu guda".
Ambassador yace, "To zan yi fadi".
Ummi baby ta kalleshi tana cewa, " Wannan yarinyar ta wayarka nake son ka mini abu a kanta".
Ambassador yace, "Au wai Fadeela, to me kike so za ai".
Ummi baby ta fad`a masa komai na yadda take son ai , aiko Ambassador ya yarda ya amince , to Ummi baby ko me take son ai wa Fadeela???
mu dai namu idanu ππ
" Wallahi officer ban kashe wannan yarinyar ba, tana nan da ranta ku bincika."
Officer da ranshi ya 'baci da maganar Alaji Nuhu ya mike ya fita ya bada umarnin tura shi kotu.
Alaji Nuhu cikin zuciyarshi yake tunanin to idan Farida ta mutu wa ne yasan da ita a gidan da har za a shigo a dauketa , kuma bisa hujjojin da 'yan sanda suka gabatar masa ,ya wadatar masa Farida ta mutu , to tabbas kashinsa ya bushe,
ba jimawa yayansa yazo aka tabbatar masa da abin dake faruwa , garin bin matansa ya yi kisan kai,
Yayan nasa haka ya juya domin ba shi da wani gwarin gwiwar kare Alaji Nuhu.
Fadeela na zaune ta ga kiran sabuwar number a wayarta
kiran ta d'aga tana cewa, "Hello."
Daga can 'bangaren taji ana cewa, "Fadeela ke nan shi ke nan kuma sai a mance damu , bayan an lasa mana zuma."
Murmushi Fadeela ta yi tana sake sai ta zaman wayar a kunnenta tana cewa, "Hmmm amma waye yake magana."
"Lallai ne Fadeela to wanda ku ka had'u a legos ne."
A jiyar zuciya ta yi tana cewa, "To ai mutanen da muka had'u a legos suna da yawa."
"To tunda kin kasa ganewa Ambassador Umar ne."
Fadeela ta kwashe dariya tana cewa, "Ashe kai ne ."
Aiko dai nan suka sha hira har suka sa ranar had'uwa.
Ummi baby ce ta kalli Ruma tana cewa, "Ni fa wallahi tunda na gano Fadeela da irin wannan halin duk yanzu na tsani kai na."
Ruma kawai ta kalleta tai shiru .
Zainab sosai hankalinta yake tashe tunda komai ya tabbatar da Fadeela karuwa ce , to amma tun yaushe Fadeela take aikata wannan abu, ni ko nace wannan amsar sai gun Fadeela .
Inna tasa rana zata je ganin jariri ta zauna har suna , Fadeela ta yi kokarin hanata duba da bata jin dadi, amma Inna da gardama tace sai taje,
Yanzu labari ya fara jita-jita cewa Fadeela karuwa ce , sai dai mutane da dama suna karyatawa sakamakon an sabai mata wannan 'kazafi,
yanzu misalin karfe 8 na dare Fadeela ta dan fita zuwa shago
Inna kuwa tana cikin tashin hankali tana tsaye cikin falo tana jiran shigowar Fadeela ,
Fadeela na shigowa taji Inna ta kwad'a mata mari,
abin mamakin ma maimakon Fadeela ce zatai kuka kawai Inna ta fashe da kuka tana zamewa a kasa
cikin tashin hankali da rashin sanin abin dake faruwa Fadeela ta kalli Inna tana cewa, "Mene ne Inna, mene yake faruwa."
Fadeela idanunta sun ciko da kwalla,
Inna ta fara wani irin tari lokaci guda kuma tana kokarin fara magana
........shareπ
'KAWAR KARUWAI πππ
BY
AUTAR MARUBUTA
_______________________________
Page 27&28
"Fadeela yanzu so kike ki tozarta mana rayuwa? mene abin da kika aikata ke nan , yanzu wani ya zo yake sanar mini gobe zzamu tattara kayanmu , wai kin saida gidan, hankalin ki ya kwanta idan muka koma kwanan titi."
Fadeela ta durkusa gaban Inna tana cewa, "Wallahi Inna ban yi dan tozarta...."
Inna ta dakatar da ita tana cewa, "Yanzu ina kud'in gidan yake." Fuskar Inna cike da hawaye tai maganar
ita ma Fadeela fuskarta cike da kwalla ta fad'a mata yadda Alaji Sani ya yaudareta
Inna ta sake fashewa da kuka tana cewa, "Wallahi kin cuceni Fadeela, kin cuceni."
Fadeela na kokarin bawa Inna hakuri, amma Inna ta shige d'akinta cikin mummunan yanayi tana kuka .
Kamar tun d'azu dai Ruma da Ummi baby suna zaune , ita Ummi baby ta durkusar da kai kasa koma take tunani?
Ruma kuma tana danna wayarta , yayin da ta kalli Ummi baby tana cewa, "kinga Kalid yana fad'a mini Alaji Nuhu ya amsa laifinshi kotu kuma ta yanke masa hukunci , gaskiya Kalid yaron manya ne ya taimake mu ."
Ummi baby ko d'ago kai batai ba , hakan yasa Ruma shafa mata fuska tana cewa, "Magana fa nake Ummi."
Ummi baby ta d'ago idanunta sharkaf da hawaye tana kallon Ruma
Ruma ta aje wayar dake hannunta tana cewa, "Me ke faruwa kuma ."
Murmushi Ummi baby ta yi tana cewa, "Wallahi kanwata Aisha na tuna yarinyar nan tana so na , haka Dady da momy , ban ta'bajin ina kewarsu ba kamar haka ,sai yau , ko wanne hali suke ciki oho , a gaskiya ahali sun yi a rayuwa."
ta share hawayen fuskarta tana murmushi
Ruma ita ma murmushi tai tana kallon Ummi baby da cewa , "Idan kuwa haka ne ,to lokaci ya yi da zamu tuba."
Da sauri Ummi baby ta kalli Ruma da idanunta da tasha kuka.
Fadeela ce kwance a kan gado tana takaicin irin halin da Alaji Sani ya jefata
amma taci alwashin dole taci gaba da neman kudinta don kada su rasa matsuguni
tashi tai taje ta rufe gida ta kwanta
Inna kuwa matukar tashin hankali take ciki da wannan hali da Fadeela ta jefasu
hakan yasa ta kasa bacci har zazza'bi ya sake rufeta duk da haka kuka take tana tunanin
tsawon lokacin da ta share a duniya da irin 'kalubalen da ta fuskanta na rashin 'ya'yanta
Inna kuka tai ta yi tana zubar da hawaye har wajen kimanin karfe 12:30 na dare
motsin Fadeela taji
babu jan lokaci taji ta 'bude gida ta fita ,
hankalin Inna tashi ya sake yi cikin tsananin fargabar Inna Fadeela zata a wannan daren, ta fito falo ta zauna cikin tashin hankali
Fadeela kuwa na fita gidan Ambassador ta wuce tana zuwa ya yi mata marhabun da zuwa suka shiga cikin d'aki
d'aki ne mai matukar hasken gaske tare da had'ad'd'en gado
tana shiga tai murmushi tana cewa, "Gaskiya wannan d'akin ya burgeni."
Ta karasa maganar tana cirea babban hijab d'in dake jikinta tana wata irin kwanciya a kan gadon , babu komai jikin Fadeela a halin yanzu take kwance a kan wannan gadon
Ambassador zama ya yi a kan kujera yana kallon Fadeela yana murmushi
yadda taso take juyi a kan gadon tana shashshafa jikinta tana kallon Ambassador
Ambassador ba tare da ya taso ba ya fara cewa, "Baby me yasa kika za'bi wannan rayuwar ko dan baki da kowa ne ko kuma kina neman kudi."?
Fadeela cikin shagwa'ba tana girgiza jikinta tace ," Ni ka taso , dare fa yayi Inna tana gida yanzu bata jin dad'i."
Ambassador yace , "Au kina nufin ba ta san kina fitowa ba."
Da sauri Fadeela ta