Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
ganyen magarya ",Assalamu alaikum", Ruma ce ta riga amsa sallamar daga fitowarta daga toilet Ummi baby murmushi tayi tana cewa", ai na dauka shuka mu kikai ba zuwa za ku yi ba", durkusa Fadeela tayi gabanta tana cewa", mene zaki da wannan", ta nuna ganyen magarya Ruma ce tai dariya tana cewa", wai maganin sanyi da kuma matsi , ni kam dai bazan amfani da shi ba", Ummi baby harara ta dokawa Ruma tana cewa," rabu da waccen matar, to wallahi wannan ganyen babban magani ne a gurin mata , idan kika bazashi ya bushe ki daka , kina tsarki ko shiga ciki , yana maganin budewar gaban mace", Fadeela tace ",ikon Allah su Ummi baby masu gargajiya", tana dariya ita ma Ummi baby dariyar tayi tana cewa", ke kuwa ba dole ba , ina san nake kashe ambassador da dadi", Ummi baby had`e rai tayi tana cewa", a'a to barni haka", ta mik`e tsaye tana cewa," ni wallahi ma maganin ciwon mara nake so , domin kwana biyu ina shan wahala kuma dah bana yi", Ummi baby ta mik`e tsaye tana cewa ",zan baki wani sirri", ta je kofa tana kokarin fita tsayawa Fadeela tayi tana cewa", ina za ki ne", " waje mana ke ce fa kika ce Alaji mansur yazo", Fadeela tace ",haba sa hijab mana , ke ma Ruma ki fito ku gaisa", ta karasa maganar tana fita . Bayan Tsawon Lokaci yau kimanin sati uku ke nan da mutuwar baba Aminu๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ ya yi jinya ne Allah ya dauki ransa ba tare da ya ga matarshi ta haihu ba๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ tabbas wannan mutuwa ta girgiza mutane, Inna taci kuka sosai mara misali, haka ita ma Fadeela, uwa uba kuma Jamila๐Ÿ˜ญ wannan rayuwa haka take duk sanda lokacin ka ya yi babu jira , Allah yasa mu dace baba Aminu Allah ya yafe maka ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ bayan Fadeela ta fito daga wankanta na kaddara(Dare) ta fad`a gado tana murk`ususu mararta kamar zata fita, to banda abin Fadeela taje asubiti mana asan meke faruwa, niko nace waya sani ko wankan darenta ne yaja mata.๐Ÿ˜’ Wayar Zainab ce take Ring da sauri ta nufo wayar domin tunaninta kiran da take jira ne , tana isowa ta ga Zakariyya ne, tai ajiyar zuciya ta zauna tana kara wayar a kunne, ", Assalamu alaikum ma a bociyar hankali da ilmi", taji Zakariyya ya fad`a wani d`an yammm taji haka , kafin ta amsa sallamar bayan sun gaisa Zakariyya ke cewa", Zainab na gode da dukkan gudun mawar da kika bani dan ganin na auri Fadeela, amma a yanzu ina tabbatar miki na fahimci Fadeela bata kaunata , dan haka na sake sabuwar rayuwa tare da wata , na mance da Fadeela", Zainab tace ", Alhamdulillah, Allah yasa hakan ne yafi alheri, ita ma Fadeela Allah ya bata miji na gari", dariya Zakariyya yay yana cewa", to Amin zainabata, amma bari na fad`a miki wata gaskiya, Zainab yanzu ke nake so , kuma nake son aura, zuciyata ta kamu da sanki Zainab", darau damm dumm Zainab taji a ranta , a take taji kanta ya sara, " kasan dawa kake magana kuwa",Zainab ta fad`a cikin mamaki murmushi Zakariyya yay yana cewa",na sa ni mana Zainab, dan Allah karki mini hali irin na Fadeela ki share mini hawayena da rad`ad`in da nake ciki, ki amshi soyayyata", tsawon minti guda sukai shiru suna sauraran numfashin juna daga bisani Zakariyya tace",dan Allah Zainab ki yarda dani ", Zainab taja dogon numfashi mai zafi tana cewa", Fadeela fa Aminiyata ce kuma dan mu samu matsala da ita hakan ba yana nufin naci amanarta ba", wayarshi ya sake daidaitawa a kunnenshi yana cewa," na nemi Fadeela da aure Zainab tace bata kaunata , to mene abin cin amana dan na soki", a ajiyar zuciya tayi tana cewa",gaskiya bazan iya wannan abin ba kayi hakuri ", ta kashe wayar yayin da Zakariyya ke kiran sunanta. Yanzu misalin karfe 8na dare Ruma da Ummi baby sun gama cin abinci , yayin da Farida ke kwance tana kallonsu ", wai kwana biyu meke faruwa ne Farida? duk kin canza mana fa lafiya kuwa",? Ruma ta fad`a murmushi farida tayi ma ta tana cewa ", kawai yanayi ne", Ummi baby tace " tom ni dai gaskiya zan je taron karuwai na legos , idan zaku sai ku shirya", Farida ce ta kalleta tana cewa ",au haka ne fa , ai nasan ambassador zashi sai ki bishi", ", auuuuu๐Ÿ˜  kina nufin ba za ki ba farida",? Ummi baby ta fad`a tashi Farida tayi daga kwanciyar da tai jikinta duk a mace tare da wani yanayi na kasala tace ", a kwai abin da na keson sanar daku", kallonta sukai a tare lokaci guda kuma suna kallon juna , kafin wani yace komai suka ji hoonn d`in mota mai karfi daga kofar gida dogon tsaki Farida taja tana cewa," kunji banza Alaji Nuhu ko, to wallahi ba inda zani tsinan ne", dariya Ummi baby ta keece da ita tana cewa ",bari naje na ce masa ba kyenan", Ummi baby ta ziri mayafi ta fice cikin rawar jiki, tana fita ta karasa wajen motar tunda Alaji Nuhu ya hangota ya fara sid`e baki๐Ÿ˜‹ sauri yay yana fitowa daga motar daga shi sai singlet da gajeren wando, ga shi luk`uti bak`i baki d`aya ita ma Ummi baby taji tsanarshi ta kamata ", Alaji Farida bata nan fa ", ta fad`a ba tare data karasa inda yake ba sauri yay yana takowa inda Ummi baby ke tsaye yana cewa", toooooo,yanzu ya zan yi ke nan kuma wallahi a matse nake , baki d`aya K`AWAR taki ta kaurace mini kuma naga kema ba lefi ko zaki fansheta ne yau kawai", had`e rai Ummi baby tayi tana cewa", me kake nufi Alaji", Alaji Nuhu yay dariya yana cewa", haba yarinya sai kace ba 'yar hannu ba", ya karasa maganar yana aje hannu a kan kirjinta yana cewa", a taimaka mini", mari ta falla masa tasa karfi ta wurgar da shi gefe kawai ta shige gida๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ tana shiga ta fara cewa", gaskiya Farida kina fama da wannan gardin mutumin", dariya suka shek`e da ita yayin da ta basu labarin abin da ya faru , Ruma harda tintsirawa tana dariya cikin b`acin rai da haushi Ummi baby tace ," to dariyar ta isa haka Ruma ", Ruma tana kokarin shanye dariyar tace", sorry na dena", lokaci guda kuma tana sake tintsirewa๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ Ummi baby duka ta kai mata yayin da Ruma tai saurin kaucewa, bayan sun yi shiru ne Ruma ke cewa", to Farida mene ne zaki fad`a mana? muna ji Allah yasa cigaba ne", cikin kasalalliyar murya Farida tace ", NA DENA KARUWANCI", sauri sukai suka hada ido cikin tsananin mamaki da rashin gane inda maganar ta dosa, duk ji sukai maganar na musu amsa kuuwa a kunnuwansu, Na dena karuwanci_na dena karuwanci. ...........comment and share my fans K`AWAR KARUWAI๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ BY AUTAR MARUBUTA _________________________ page 15&16 ",nifa ban gane me kike fad`a ba Farida", Ruma tai maganar cikin tashin hankali, kawai Farida ta tashi ta bar musu d`akin yayin da suka bita da kallon mamaki da rashin fahimta. Washe gari๐ŸŒž Inna da Jamila ne zaune suna falo, sakamakon tunda Allah yay wa baba Aminu rasuwa Jamila ta dawo gidan , Fadeela kuma tana madafa tana had`a musu abin kari ๐Ÿดโ˜•๐Ÿฒ taji wayarta na ringin , dubawar da zatai kawai ta fara murmushi , Alaji Sani ne ke kira , wayar ta d`aga tana karawa a kunne daga can Alajin yace", barka my sweet", murmushi Fadeela tayi tana cewa", ina kwana fatan ka tashi lafiya", ", kin ganni nan tun asuba nake tunaninki da kewarki, kuma ina son na zo na gaida Inna , ko ya kika ce", a jiyar zuciya Fadeela ta ja tana cewa," ban da abinka kai ne fa zab`ina kuma Inna zata so ganinka ai, kawai kasa rana", murmushi yay yana cewa ",kwanannan zan se miki mota Fadeela, ke dai ki cigaba da mini addu'a", ", da gaske Alaji!,Gaskiya idan haka ne zanji dadi ka ga na koma 'yar bata", Alaji Sani yay dariya yana cewa", to mene ? nawa motar take da bazan siya miki ba , a cikin watannan ma kuwa", a jiyar zuciya mai sanyi ta sauke tana cewa", wallahi ka farantan rai, amma bari zami waya, yanzu ina son kaiwa Inna kayan Kari", Alaji Sani yace"to shi ke nan", tana aje wayar ta doshi inda su Inna suke da nufin tambayar Inna ina sugari yake domin zata zuba a cikin kunu๐Ÿบ tana shiga falon Inna ta rufeta da fad`a ", gaskiya Fadeela kin bani mamaki, Zakariyya yazo har kano amma ki saka masa da wannan rashin mutuncin, duk a cikin samarin naki wayakai nagartarshi da ilminsa , daman da Allah bai jarabemu da rashin Aminu ba dah tuni kina d`akinki, to amma yanzu zan tsaya tsayin daka wallahi don ganin kin auri Zakariyya", Inna cikin tsananin fusata ta ci gaba da cewa", uban mene ai bunsa? tom yanzu ni zan tsaya miki uwa uba don ganin kinyi aure ko dan shed`anun๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ zan je har kadunan zan yi magana da iyayen nashi na basu hakuri, ko kina so ko a'a Zakariyya ne mijinki, ana kokarin sama maki nagartacciyar rayuwa kina hauka", kuka Fadeela ta fashe da shi mai gwanin ban tausayi, tabbas k`in Zakariyya ya ratsa zuciyar Fadeela Jamila ce ta fara bawa Inna hakuri lokaci guda kuma tana rarrashin Fadeela. A cikin bargo suke ,rungume da juna suna shakar kamshin jikinsu, dukkan ilahirin jikinta yake bi yana shafawa yadda yake so ya gadama, Ummi baby murtike fuska tayi tana cewa", ambassador bana san wannan iskancin naka yau", sakin baki yay yana kallonta๐Ÿ˜’ murmushi tayi tana cewa ",yau baki d`aya ka gajiyar dani ko tausayina baka yi , idan nazo hannunka yadda kaso dani haka kake", hannunshi ya cire a kan jikinta ya d`orasu kan fuskarta yana sumbatarta, yanayin yadda ya kama harshenta ne yasa ta tureshi gefe , baki d`aya ranshi ya b`ace ", me yasa kike son b`atan wannan yanayin ne baby, kin ce kuma ba za ki kwana a nan ba , amma kink`i bari nai abin dana keso", ", auu duk abin da kai dani d`azu bai isheka ba, ai wallahi indai yau na kwana da kai sai naci ubana domin yau na ga wani karfi kake ji", sakin fuska yay yana murmushi tare da had`awa da dariya ๐Ÿ˜‚ rungumota yay yana shafa lafiyayyen gadon bayanta da yake masa dad`in shafawa tare da zarcewa inda yake so ", to ki bani kanki , saboda idan na tafi legos za ki kewata", da sauri ta kalleshi tace", ina son zuwa wannan taron gaskiya, kuma zani , sai kana mini wayo kana zuwa gun wasu matan ni kuma ko oho", kallonta yay shi ma yana cewa", to ai kinga ni namiji ne, duk da taron karuwai ne bana san ki je", ", to wallahi sai naje , indai kaga banje ba to Allah ka fasa zuwa", jimmmmm ambassador ya yi na d`an lokaci sannan yace", to naji ba za ni ba , shi ke nan",? ta girgiza kai alamun ehhh jawota ya yi yana cewa ", to mu kwanta na minti uku ",yana d`aga mata gira๐Ÿ˜ฌ๐Ÿƒ๐Ÿƒ๐Ÿƒ๐Ÿƒ๐Ÿƒ๐Ÿƒ๐Ÿƒ Anan kuwa Zainab ta rasa yadda zatai da Zakariyya, domin kuwa kullum kira a kan neman yardarta da ta nunashi matsayin muradinta , amma Zainab ta rasa inda zata sa kanta, tana neman shawara , ya za tayi shin idan ta amshi Zakariyya Fadeela mene zata ji , zatai Mata kallon mai sonkai ko mayaudariya mai jiran a rabu ta samu??? misalin karfe 11na dare yanzu mutuminku Alji Nuhu ya kasa kwance ya kasa zaune yay ta kiran wayar Fadeela amma taki d`agawa harya yanke shawarar zuwa gidannasu, amma sai ya tuna da abin da ya faru a wancan zuwan uban tagumi ya kafta ", gaskiya Farida ba kye kauta mini , na saba dake ba maรงen da nake jin dadinta kamar ke , amma kin barni cikin tashin hankali", mikewa yay tsaye yana gyara zaman wandanshi yana cewa", kann uba ai wallahi bazan barki ba Farida wasa farin kirki, amma yau duk inda karuwa take sai na nemo nayi maneji", ya zura kayanshi ya fice . Farida ce kawai cikin gidan sakamakon sauran suna can barbad`arsu kuka take yi mai gwanin ban tausayi mai kuma cike da nadama๐Ÿ˜ญ ", na tuba ya Allah, ka sake bani da ma na canza rayuwa๐Ÿ˜ญ tabbas Kalid bana a kan daidai na gode Allah da zuwanka cikin rayuwata", kuka ta sake fashewa da shi da majina tana fitowa kalaman Kalid take tunawa , idanunshi sun yi jajir ya ke kallonta, ga dukkan alamu kad`an yake jira ya fara hawaye", wannan wacce irin rayuwa ce Farida? ba dai kudi ne ba ina da kudi Farida, babu abin da za ki nema ki rasa na miki alkawari, zan sama maki ahali tare da Farin ciki Farida, ki gyara rayuwarki da tsakaninki da mahaliccinki", ya miko ma ta hannu yayin da hawaye suka zub`o masa yana cewa๐Ÿ‘‹ki mini alkawari Farida, ki mini alkawari Farida kin dena wannan rayuwar", kara zaucewa tai da kuka tana shashsheka da wannan abin da ta tuna ", tabbas Kalid ahali na rasa da kudi, a yanzu nayi nadama ya Allah", gwanin ban tausayi matuka๐Ÿ˜ญ " ina tsoron mutuwa ya Allah, ka bani da mar gyara rayuwata", ta kwanta cikin mummunan yanayi na kuka. "me yasa ba za ki kwana anan ba ne Ruma",? chairman ya fad`a cikin tashin hankali zame towel d`in dake jikinta tai tana share ragowar ruwan da ya rage da tai wanka , bata ce mai komai ba chairman ganin Ruma a wannan yanayin yasa shi saurin tasowa yana janye towel d`in yana yarwa, kafin tace uffan ya jefata kan bed๐Ÿ’ƒ๐Ÿƒ๐Ÿƒ Washe gari tunda Farida tai sallar asuba take zaune a gurin, har bacci ya sake kwasheta su Ruma suna mata ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ Fadeela ce a da`akin Inna tana dube-dube duba can duba can ga dukkan alamu akwai abin da take nema , garin hawa saman kwallar Inna ta hard`e da babban hijab d`in dake jikinta sauran kadan tasha kasa , nan mararta ciwonta ya motsa amma ta daure da kyer ta dauki abin da take nema ta fita . comment and share......๐Ÿ’– K`AWAR KARUWAI๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ BY AUTAR MARUBUTA ______________________________ page 17&18 Jamila na zaune a falo tana waya da 'yan uwanta daga Jos, Fadeela ta wu ce zuwa d`akinta , tana rik`e da mara to wai Fadeela zuwa hospital ne aiki?tabbb๐Ÿ˜’ wajen kira biyar ya yi mata , amma Zainab na zaune tana kallon wayar ta kasa d`auka , domin ba ta da kalmomin da za ta bayyanawa Zakariyya shigowar kira na shida ne yana kusan tsinkewa Zainab ta kai hannu ta d`aga shiru tai ta kasa kunne tana jiran abin da zai ce murya taji can kasa kamar zai kuka ",haba Zainab dan Allah me yasa za ki ke mini haka? soyayyar dana ne ma ce tasa kike a zabtar dani",? A jiyar zuciya Zainab tai tana cewa ," ka yi hakuri Zakariyya ban san mene ne zan ce ba , amma ka bani lokaci", yay a jiyar zuciya yace ,"to shi ke nan Zainab ", Zainab taji duk tausayinshi ya rufe ta to idan ke ce Zainab mene ya kamata ki yi??? Ruma ce da wani Alaji muhd a kofar gida, ya jingina jikin motar shi yana cewa da ita ", to ya za ki zo da daren ne ko mu tafi yanzu", kallonshi tai tace," sai daren amma gaskiya hotel nake so yau", Alaji muhd yace ,"ba ki da matsala zuwan naki shi ne wahala ", a lokacin Farida ta fito daga gida tasa luk`af da babban hijab girman hijab d`in ne yasa ba zaka iya hangen carbin dake hannunta ba , kai tsaye ta wuce gidansu Fadeela yayin da su kuma suke bin ta da kallo. Fadeela tana d`akinta tana shirya kayanta cikin jakar goyo , sakamakon wani discussion da zasu je a makaranta na kwana biyu Farida tai sallama yayin da ta bud`e fuskar ta suka gaisa da Inna da Jamila dake falo, Inna ba tare da ta gane wace ba tace mata ta shiga ciki domin Fadeelan na ciki duk a tunaninta abokiyar tafiyar ce Farida na shiga d`akin , Fadeela ta kalleta cikin tsananin mamaki ", Farida", Fadeela ta fad`a tana girgiza kai cikin mamaki mai girma murmushi Farida tai tana zama bakin gado haka ita ma Fadeela ta zauna tana kallonta murmushi Farida ta kuma yi yayin da take cewa", na tuba Farida, na dena karuwanci, na koma rayuwata kamar ke , ina kuma rokon Allah ya yafe mini , ina matukar godiya da nasiharki da ke da Kalid ba zan taba mancewa da ku ba", Farida tai maganar idanunta sun ciko da kwalla matukar mamaki ne ya sake rufe Fadeela hakan yasa ta kasa magana Farida ganin haka ya bata da mar cigaba da cewa", na zo ne domin ki magana a sani a islamiyyar ku", ita ma fadeela cikin yanayin fara kuka tace ," kai na ya kulle Farida, a she zan ga wannan ranar , tabbas Allah abin tsoro ne idan da rai akwai rabo", murmushi kawai Farida ta kuma yi yayin da Fadeela tace, "na matukar ji dadi Farida, kamar mafarki duk jikina ya mutu, Allah shi ne abin godiya, amma yau zamu discussion na kwana biyu, matukar muka dawo , zan same ki mu gyara komai", Farida tace ," to Allah ya dawo da ke lafiya ", cikin sabuwar kasala da mutuwar jiki Fadeela tace," wallahi kamar na fasa tafiyar nan , duk jikina ya mutu", cikin kwarin gwiwa Farida ta ta shi tsaye tana murmushi, "to mene ne abin fasawa , kin ga tafiyata Allah ya tsare hanya ", Farida ta fita zamowa Fadeela tai daga kan gadon cikin tsananin mamaki zuciyarta na kiran uku , uku tace ," ya Allah ". Bayan Farida ta koma gida taci karo da Kalid yana zaman jiranta . Washe gari Zainab ce kanta ya kulle hakan yasa ta tafi gidansu Fadeela a yita a gama sai dai tana zuwa Inna take tabbatar mata bata nan sun yi tafiya , nan Zainab take sanar da Inna cewa ba department d`in su d`aya ba hakan yasa ba ta san da tafiyar ba, Zainab ta koma gida tare da alwashin idan Fadeela ta dawo za a yi ta a gama , ko ita ko ita Ummi baby ce ke waya da ambassador cikin bacin rai ," amma wallahi ka bani mamaki ka yaudare ni , shi ne za ka tafi legos bayan mun yi da kai babu wanda zai je", ambassador yace ,"haba baby wallahi ji nai bazan iya ba amma kiyi hakuri ai yau zan dawo", cikin tsananin fusata Ummi baby tace ,"to wallahi za ka zo ka same ni", ta kashe wayar. Kwana biyu Fadeela ta dawo da mugun zazzabi har su Inna sun cire rai da ita , tasha jini tasha ruwa duk ta rame Inna tace babu wani discussion da zata sake zuwa domin sauro ne ya cijeta๐Ÿ˜‚ sai dai a bangaren Fadeela sam ba haka ba ne , ita tasan abin da ke damunta, domin kuwa tayi babban kuskure Alaji Sani ya yaudareta ta biye zancen shi ta d`ebi takardun gidanta ta siyar ta ba shi kudin , da zummar zai sa hannun jari kuma yase mata mota , saidai har yau shiru babu shi babu labarin shi , wanda aka sayarwa da gida akwai wa'adin da ya basu zasu ta shi su ba shi gidansa , sai dai Inna da Jamila ko kadan basu da wannan masaniyar idan Fadeela ta tuna hakan yasa take kwanciya jinya har asa mata jini, wannan babban rashin hankali ne Fadeela ta aikata kuma tana cikin tashin hankali mummuna tana neman mafita . share and comment....... K`AWAR KARUWAI๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ BY AUTAR MARUBUTA ________________________ page 19&20 Tunanin Fadeela kawai yanzu ta ya za'ai kar Inna su sami labari, ta bawa Alaji sani yarda amma ga abin da yay mata , wajejen biyar na yamma ta samowa kanta mafita, wayarta ta dauka ta kira wata number da ba ai saving d`inta da suna ba . Anan kuwa Farida da Ruma ne a gida suna zaune saiga sakon Alaji Nuhu sakamakon Farida bata d`aga kiranshi , hankalinta ya ta shi hakan yasa ta sanar da Ruma , Ruma ta amshi wayar tana karantawa, "to bari kiji Farida, tunda ba yadda ban yi dake ba kan ki bani kanki kin ki , kinsan ina da hotuna da video naki da kika yi kina tsirara, to wallahi ko ki zo nan da minti talati ki biya mini bukata kona sa a watsa ki a duniya, minti 30 gare ki", Ruma ta saki wata uwar ashar " lallai ma mutumin nan tsinan ne ne , yanzu abin da za ai ta shi za ki muje gidan nasa ni zan tsaya a waje ki yi duk yadda za ki ki dauko wayar tashi ki fito idan kina bukatar taimakona kawai ki kwallan kira", Farida ta kalli Ruma cikin mutuwar jiki tana cewa, "kina ganin hakan za ai", Ruma tace," kinsan mutumin ba shi da hankali wallahi zai aikata miki", Farida ta tashi suka tafi . Ummi baby ce gaban ambassador da wasu fitinannun futsararrun kaya shi kam yana kan gado kugu ta rike a gabanshi tana harararshi ,"na ce ki hakuri na amsa laifina naje legos na sab`a alkawari", ambassador ya fad`a kan gadon ta matsa kusa da shi tana cewa, "aikin banza , kuma ni tafiya ma zan sai ka koma legos din ka samo wata", ambassador ya mike cikin rawar jiki sakamakon tunda tazo gabanshi hankali ya tashi ," na ce ki hakuri ai kuma tunda naje legos din matan duk kin fisu kuma kawai da mace d`aya na kwana", dogon tsaki Ummi baby taja ta juya tana sa kayanta cikin fusata ambassador ya ciro wayarshi a aljihunsa na jus yana kokarin shiga gallery cikin fushi yasha gabanta yana cewa, "to kiyi ta tafiyar kuma zan je gurin wannan domin ta fiki", ya nuna mata photo da sukai shi da yarinyar cikin futsara ya janye wayarshi wani dauu Ummi baby taji a ranta , hakan yasa cikin tashin hankali ta sake karbar wayar tana kallon photon tsananin mamaki ne ya rufeta da tashin hankali, hakan yasa tace ," ina kasan ta", ambassador saboda ya motsa mata kishi yace ,"yarinyar legos can muka had`u so sweet Babyn", kallon photon ta sake yi tana cewa, "Inna lillahi wa Inna........ wannan ia Fadeela ce ," ambassador yay murmushi yana cewa, "kinsanta ashe", mummunan tashin hankali ta sake jin kanta a ciki, Fadeela ce wannan me hakan yake nufi kawai Ummi baby ta tafi gida cikin mummunan yanayi domin sanar dasu Ruma. Anan kam ba a cewa komai domin fadeela ce da wani Alaji a cikin hotel cikin bargo suke tsirara suna yin yadda suka so, " gaskiya Alaji har naji bani da damuwa , ina sanka, " Fadeela ta fad`a cikin sake rungumeshi ,"haba Fadeela ta ai bani da amfani idan ban saki farin ciki b, kuma maganar gida zansa yadda za ai a se wani kinji my baby," Fadeela ta hard`oshi tana dorashi saman kirjinta tana cewa, "to my," typing ba yawa kamar yadda comment ba yawa.๐Ÿ˜› K`AWAR KARUWAI๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ BY AUTAR MARUBUTA ________________________________ Page 21&22 murmushi yay mata yana cewa, "ki tashi ki tafi gida nafi son had`uwar dare domin nafi aiki Fadeela", Fadeela kallonshi tai tana cewa," na fara gajiya kullum fitar dare nafison kazo kofar gida muyi abin mu, kuma kullum na koma sai nai wankan dare Inna ta fara gajiya kuma wani lokacin ma da zan fito kona koma Inna tana jin motsina , sai tace wai Ana hauro mana ", dariya Alajin yay yana sake cakumota jikinsa . Ummi baby har wani layi take a hanya , ya za ai ta ga Fadeela a haka to kodai mafarki ne ko me , abin ya matukar daure mata kai sosai waiiyo duniya . Bayan su Farida sun isa kofar gidan Farida ta shiga Ruma ta zauna tana jiranta ganin motarshi a waje ya tabbar masu yana ciki , Farida na shiga d`akin ta ganshi sanye da gajeren wando kawai ya kece da dariya ," ai nasan za ki zo shi yasa na shirya zo mu shiga ciki ,"yana jawo hijabinta fincikewa tai cikin fusata tana cewa, "ba shi ne abin da ya kawo ni ba , kai azzalumi ne kuma kai da ka sake amfani da ni har duniya ta nade ", Alaji Nuhu yana mata dadin murya ya fara cewa," haba Farida minti uku kawai babu mai sani kuma kema kinsan dadin abun fa, ki zo muje ," Farida kawai duk hankalinta yana kan wayarsa bata da wani da ma da ya bata da zata dauki wayar, ,"haba Farida ta so muje ," ya cacumota yana janta Farida ta mare shi ta gasa masa cizo kawai Alaji Nuhu ya wurgar da ita jikin bango ko shurawa Farida ba tai ba hakan yasa ya nufi inda take yana cewa "Farida, Farida", ko motsi ba tai ba hakan yasa Alaji Nuhu tsorata kawai ya zura kayansa ya fita ya hau mota ya tafi Ruma da sauri ta shiga cikin gidan tana kiran sunan Farida amma shiru ,ta fara dubawa daga bisani ta samota a cikin dakin kiran sunanta take tana tashinta amma shiru . Ummi baby na isa gida ta ga duk basa nan hakan yasa ta fito waje

Chapter 3 of 6