Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
tayi tana cewa," duk abin da zai rabani da su Ummi baby bana kaunarshi, amma shi Zakariyya yana kiran kanshi ustaz amma ya kasa gane wannan irin jahadin da nake , kullum sai wa'azi Allah ya ce, malam wa ne ya ce , gaskiya ni bazan iya auren Zakariyya ba", da babbar murya mai cike da mamaki Zainab tace ,"tab! Yaushe kika koma haka Fadeela? gaskiya zamanki da karuwai bai amfane ki da komai ba , kin bani mamaki", Fadeela na kokarin maida mata da martani taji wayarta ta fara ruri , ganin wanda ke kiran wayar yasa murmushi da far'a suka bayyana a fuskarta, "wannan kai ne babban burin da nake so mallaka a rayuwa", Fadeela ta fad`a cikin shauk`i dajin zanen Zainab tasan cewa Aliyyu ne ke kiranta . Bayan wasu kwanaki Zainab da Fadeela ne zaune cikin ajinsu fuskar Zainab murtike ita kuwa Fadeela sumul sai shauk`i take domin tana sauraran zuwansu Ummi baby zasu kawo mata ziyara ganin kiran wayar Ruma ne ya tabbatar wa Fadeela sun iso , hakan yasa ta kalli Zainab tana cewa," mu je mana Zainab ", ba tare da Zainab ta kalli inda Fadeela take ba tace da ita ," ba inda zani , a dawo lafiya kije ki tsaya dasu students suna muki wani kallo", kawai Zainab ta yi tsaki ta fice Fadeela ta fice ita ma tare da nufar inda take da tabbacin za ta ga su Ruma , tana isa suka rungume juna suna murna "Aliyyu yace duk yana gashsheku ", Fadeela ta fad`a musu cikin girmamawa " a'a gaskiya ba ma amsawa , kullum sai gaisuwa ya kasa zuwa a gaisa",Farida tayi maganar cikin ya tsine fuska , yayin da Ruma ta ce,"ai kuwa dai", Fadeela tayi murmushi tana kallon hagu da damanta yayin data kula idanun wasu d`aluban a kansu yake, ba tare da yanayinta ya canza ba ta sake kallonsu tana cewa, "to naji insha Allah zaku gaisa da shi , amma ni bama wannan ba , yau idan na koma gida zan yi tafiya", " toooooooo"๐Ÿ˜ฏ Ummi baby ta fad`a ba tare da Fadeela ta jira sun tambayi k`arin bayani ba ta sake cewa,"zani biki kwana biyu zan yi na dawo", jin wayarta ta fara ringin yasa ta saurin cirowa wayar a rigarta mai tafe da aljihu , kallon fuskar wayar tayi ta saki dogon tsaki ๐Ÿ˜‘ yayin dasu Ruma suka kalli juna lokaci guda kuma suna shirin jefa mata tambaya. share and comment๐Ÿ™K`AWAR KARUWAI ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ BY AUTAR MARUBUTA _____________________________________ page 7&8 "mene ne hakan kuma, wake kira ",? Ruma ta tambaya , Fadeela cikin yatsine fuska tace ," wallahi Zakariyya ne ",ta aje maganar tana ajiyar zuciya sake kallonsu tai tana cewa," bari nai shirin komawa gida domin kar nai dare", Farida tace, "eh haka ne , mu ma bari mu koma", a lokacin Amina Umar tazo wuce wa ita da wasu k`awayenta yayin da take kallonsu Fadeela tana cewa," abokin b`arawo dai b`arawo ne , ato a fito kawai a ce anason karuwanci ", tana aje maganar sauran k`awayenta suka shek`e da dariya , suka wuce abin su ajiyar zuciya Fadeela ta sake yi tana kallonsu cikin rashin jin dad` yayin da wayar Ruma ta fara ringin , hakan yasa kowannensu bai ce komai ba ya maida hankali kan Ruma , Ruma murmushi tayi tana kallon fuskar wayar lokaci guda kuma tana cewa dasu ," Mubarak ne nasan akwai harka yau ", wayar ta kara a kunne tana cewa," bani nasha mutumin ",๐Ÿ’ƒ daga can bangaren aka ce ," Ruma akwai wani Alaji yana hanyar zuwa kano yau , kuma zaki debe masa kewa , amma bari zami magana anjuma ", tace ," ok ", yayin da ya kashe wayar " harka tazo ko",?Ummi baby ta jefa mata tambayar d`aga mata gira Ruma tayi alamun eh, Fadeela kawai ta zuba musu idanu . Bayan Fadeela ta koma gida sukai sallama da Inna , nan Inna ta bawa Fadeela sak`o wanda zata kaiwa k`awar Fadeela da zata bikinta , bayan Fadeela tasa k`afa ta fice duk jikin Inna ya yi sanyi ya mutu .๐Ÿ˜’ daga cikin adai-daita Ruma ta fito yayin da ta dubi babban gidan da akai parking d`in ta a kofar, taku ta farayi tana dosar gidan tare da duban girmanshi , harta shiga cikin falo , tsayawa ta kuma yi tana duban falon tana murmushi da jin dad`in yadda iska mai sanyi ke ratsata , ba tare da ta ankara ba taji ana kokarin kissing d`in ta, da sauri ta juya tana kallon waye , gajeren wando kawai yasa , ba bak`i ba ne can yana da suma a kanshi mai kimanin shekaru 40 ajiyar zuciya tai tana cewa, "haba Alaji! Ai saika sa na tsorata , ko ciniki ba ai ba kake kokarin cin gyara", murmushi yayi yana kallon ta sama da kasa ," haba baby nifa cikakken d`an bariki ne , kuma nasan farashinki, shi yasa na fara abin da ya kawoni", ya matsa kusa da Ruma ya rik`e hab`arta yana cewa, "karki nunamin kin fini bariki domin zaki sha wahala , ba a maneji dani kad`an daga cikin mata ne ke dawowa gare ni bayan munsan juna", duk Farida jin shi take domin ko tsoro bata ji ba a cikin ranta tace," baka san wace Ruma ba ", Zainab ce zaune a falon gidansu ta kara waya a kunne ga dukkan alamu waya take , daga can bangaren aka ce, " wallahi Zainab, sam Fadeela bata sona , amma ni ina tausayin Fadeela, domin nayi alwashin share mata hawayenta na rashin iyaye amma sam tak`i bani had`in kai ", ajiyar zuciya Zainab tayi cikin muryar tausasawa tana cewa," ka yi hakuri Zakariyya, wallahi kullum ina fad`a mata wannan, amma insha Allah wata rana zata gane ", Zakariyya yace ," to Allah yasa Zainab, yasu umma da yaran", Zainab ta bashi amsa tana cewa, "wallahi lafyar kalau," yace "to Masha Allah aunty Zainab a gashshe mini dasu sosai", Zainab ta d`anyi jimm sannan tace , " uhumm aunty kuma "? Zakariyya yace ," eh mana bama wannan ba bani labari", abin ya sake ba Zainab mamaki tunani tai to kodai ya zata da Fadeela yake magana ne , domin ya tab`a fad`a cewa muryarsu iri d`aya ce . Ni kam nace oho๐Ÿ‘ a rungume take jikinshi yana bin laushin fatarta yana shafawa da gani babu tambaya wanka sukai , yadda yake jin laushin fatarta yasa yake yawo da hannunshi ko'ina cikin jikinta ,"I love you Ummi baby ", ambassador ya fad`a yana murmushi " gaskiya babu ta biyunki cikin mata , ban ga wacce ta kama farcen ki ba", Ummi baby tai tsaki ta mike tare da sake tamke towel din dake jikinta , kallonta ya yi yana cewa, "mene hakan", fari tayi da ido tana cewa," dad`in baki ambassador, duk matan da kake nema haka kake fad`a musu , sannan kuma karka mance akwai alkawarin aure da kai mini", murmushi ya yi yana mikewa ya sake kanannad`ota jikinsa yana cewa, "haba baby a kan wannan zaki b`ata ranki, to yi hakuri ki murmushi", baki ta sake tab`emai tana cewa," to idan da gaske ne ka fito mi auren", "haba Ummi kinsan yanzu abubuwa sun cakud`e, amma komai yana daidaita zami aure", cikin shagwaba tana girgiza jikinta tace ", to shi ke nan", ambassador ya fara bin kamshin jikinta yana shaka tare da ajiyar zuciya, kai ambassador ko maye ko kadan baya gajiya da kusantar Ummi baby.๐Ÿ˜‚ Yanzu wajen karfe 11:20 na dare , amma Farida tana tsaye bakin titi tana neman abin hawa , har da 40 tayi amma babu wani abun hawa da ya tsaya da nufin d`aukarta . Daidai da lokacin da tai ajiyar zuciya wata farar mota tai parking a gefenta ko kallan motar bata yi ba sakamakon wani huci da take , sanadi kuwa Alaji Nuhu ne ya b`ata mata rai tunda ta baro gidanshi yake ta kiranta a waya harta gaji ta kashe wayar, wani mahaukacin mutum ne Alaji Nuhu da sam ba ya da hakuri a kan abin da ya keso. " yan mata lafiya kuwa", saurayin dake cikin motar ya zuro kanshi yana fad`a dogon tsaki taja tana sake kau da kanta "yan mata bai dace ba kina mace ,amma kina waje a irin wannan lokacin , ki shigo na rage muki hanya", Farida ta kalli saurayin wanda lokaci guda taji ya kwanta mata tayi murmushin takaici tana cewa," a'a na gode", rufe bakinta ke nan motar Alaji Nuhu tayi parking duk hankalinsu ya karkata wajen , da sauri ya fito yana cewa, "ni zakiwa haka farida? to wallahi baki isa ba, yau ina san kwana dake kuma ina yunwarki dole ki bani hak`k`ina",๐Ÿ˜ saurayin dake cikin motar ya saki baki cikin ranshi yake cewa", a she matar aure ce , amma wannan mijin nata ba shi da hankali", Farida ta sake kicin-kicin da fuska cikin isa ta fara cewa. share and comment.... my fans K`AWAR KARUWAI๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ BY FATIMA ABDALLAH KANO (Autar marubuta) ____________________________________ Page 9&10 "wallahi Alaji Nuhu ka kiyaye ni , dube ka shirgege da kai amma neman mata kamar jaraba , to wallahi ko mutuwa zakai saidai ka mutu amma ni bazan sake mu'amala da kai ba", Alaji Nuhu cikin rad`adin abin yace ," wallahi kin yi karya farida kizo mu wuce kije ki sauke nauyin dake kanki tunkan raina ya b`aci wallahi ", Farida kawai ta bud`e kofar motar wannan saurayin ta shige , shi kuwa saurayin ganin yadda Alaji Nuhu yake zak`ewa yasa shi saurin jan motarshi ya tafi , Alaji Nuhu yabi motar da magana yana cewa," zama ki dawo ki sameni tunda kike mini shocking d`in da ba macen da ta iya wallahi sai kin dawo , ai ba hauka ake ba", ya koma motarshi cikin huci . saurayin tuk`a motar yake yana satar kallon farida a fakaice , zuwa can ne kuma ya fara cewa ,"ki yi hakuri ke irin kaddararki ke nan", Farida tayi shiru jin hakan yasa saurayin sake fad`in, "mijinki ne ko",? Lokaci guda Farida ta kece da dariya ๐Ÿ˜‚ murmushi ya yi yana sake kallonta ," haba mene ne abin dariya", Farida tace ,"Hmmm amma ka bani dariya in rasa wanda zan aura sai wancan bagidajen mutumin, to ka b`ude kunnuwanka da kyau kaji , suna na Farida kuma ni Karuwai ce , abin dana fito yi ke nan ", cak ya tsayar da motar ya tsaya yana kallonta, " karuwa kuma",ya fad`a cikin mamaki Farida had`e rai tayi tana cewa, "oho kana shakka ke nan to wacce macen tarbiya ce zaka ganta a titi yanzu? ai sai mu ", ba tare da ta jira abin da zaice ba ta bud`e kofar zata fita ," tom ni zan wuce na gode da taimako", mutuwar zaune yayi yana binta da kallo harta tsallaka titin ta shiga gidansu, yay ajiyar zuciya. Anan gidan Inna kuwa baba Aminu ne da matarshi suka kawowa Inna ziyara nan suka sha hira sosai . tafiya suke cikin mota yana mata wani kallo Fadeela saidai kawai ta kalleshi tace "uhum", magidanci ne sanye da shadda jaah yake tuk`a motar ," zan yi kewarki Fadeela dan ma Allah yasa nima zan kwana biyu a kanon da bansan ya zan yi ba", Fadeela cikin kunya ta kalleshi tace "haba Alaji sani ai naga ba wani shakuwa mukai ba", " keeeeeeeeh",Alaji Sani ya fad`a "soyayya ke nan , cikin kwana biyu kin mamaye zuciya, gaskiya Fadeela ina sanki", kallon shi tai ta rufe fuska tana cewa," har kasa naji kunya", Alaji Sani ya yi murmushi yayin da ya yi parking kofar gidansu Fadeela "har naji wata kasala da mutuwar jiki ya kamani , bana san na barki Fadeela", ya fad`a yana kallonta ajiyar zuciya tayi lokaci guda tana kallon kofar gidansu tana cewa," to ni dai bari na shiga domin na gaji sosai", yace ,"to shi ke nan sarauniyata ki gashshe mini da Inna kafin nazo", Fadeela ta fice tana masa bye -bye yayin da ya murza kan motarshi yay gaba to ni ko nace zan ga yadda Fadeela zata kai Aliyyu da Zakariyya da Alaji mansur ga kuma Alaji Sani๐Ÿ˜‚ Inna tayi murnan dawowar Fadeela sosai musamman yadda take korafin gida ita 1 "kai duniya ambassador jarababbe ne", Ummi baby ta fad`a tana rike da kugunta tana kallon madubi dariya Farida ta kwashe da ita tana cewa", hhhh dan Allah Ummi baby kije wajen Alaji Nuhu nan ne zakiga masifar jaraba , wallahi Ummi baby ko Alaji Nuhu zai mutu ya dena kusantata", " wai ke farida ba kye yafiya ne tun da ya fad`a miki wannan maganar fa kika tsane shi", Ruma ta kwashe da dariya tana cewa... yanzu wajen karfe ukun asuba Fadeela ta fito daga wanka , b`urun-b`urun din ta ne ya tada Inna zaune tana tsaki "Allah ya yaye miki wannan wankan daren, ace kullum ta Allah saikin tashi irin wannan lokacin kina wanka",๐Ÿ˜  Fadeela tai ajiyar zuciya wanda jikinta duk a ma ce ta kalli Inna tana cewa," ki yi hakuri Inna wallahi na saba idan ban yi ba jikina ciwo yake", "to shi ne kuma sai dare abin ya fara damuna kuma na fara jin tsoro , haka mahaifinki fa ya ringa yi kullum wanka a rana sai yay wanka sau nawa , a karshe likita yace mana yana da kansa haka ya mutu muna gani", Fadeela ta fad`i jikin Inna tana kuka๐Ÿ˜ญ " Inna na tuna Abbana , yana fadan kullum cewa yanzu ake yi anjuma sai labari, duk lokacin da ya fad`a dariya nake mai ", Inna ta fara rarrashin Fadeela cikin karyayyar zuciya๐Ÿ’” DA sauri baba Aminu ya farka a bacci yana cewa," Jamila ina jaririn yana ina , bani shi bani shi Jamila", hakan yasa matar shi Jamila saurin tashi tana cewa, "lafiya Aminu ?wanne jariri",? baba Aminu yay ajiyar zuciya yana cewa ," yi hakuri Jamila wallahi mafarki nayi mun haifi jariri", Jamila tace ,"Hmmm " Fadeela ce tsaye kofar gidansu Ummi baby ita da muradinta Aliyyu wayarta ta dauka ta kira Ruma "Hello Ruma muna waje fa", Ruma tace ," to ki shigo da shi mana ai kinsan bama shakkar maza ko", "ke dallah dakata mini , aka ce miki shi kwarto ne ko me? idan zaku fito ku fito ko mu tafi", Ruma tai ajiyar zuciya ta kashe wayar Aliyyu yay murmushi yana cewa," Fadeela ta ke nan , sai kin yi hakuri kuma duk gudun mawar da kike so daga guri da ya shafi shiryuwarsu zan baki", murmushi tayi tana cewa, "na gode", Farida ce ta fara fitowa, sa'ilin da Ummi baby ta biyo bayanta sannan Ruma Aliyyu bin su yake da kallo cikin ranshi yake mamaki wai Karuwai ne๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ˜’ " Aliyyun Fadeela ya kake ya shagali", Farida ta fad`a murmushi yay yana cewa, "Alhamdulillah fatan kuna lafiya", Ruma tace", lafiya kalau mu ke", nan suka ringa hira ana wasa da dariya har cikin hikima Aliyyu ke sake Jan hankalinsu a kan kudirin Fadeela, inda su kuwa suke shek`e mai da dariya. su Ruma manyan 'yan duniya ne , niko zanga yadda zasu dawo kan hanya๐Ÿ˜‚ Bayan Fadeela ta dawo gida ta tadda Zainab zaune tana zaman jiranta Inna ce ta fara cewa", kin tafi shiru dake Fadeela, sai kace anyi biyan bashi dake", murmushi Fadeela tayi kafin tace uffan ", taji an kwasheta da wani gigitaccen mari, fad`awa tai kan kujera cikin tashin hankali ", Aminu! Mene ne haka", Inna ta fad`a tana mikewa, yayin da ita ma Zainab ta mike tsaye cikin huci da tsananin b'acin rai baba Aminu ya fara cewa ," koki yarda Fadeela ko karki yadda ni ubanki ne , na gaji da zancen da mutanen gari suke kawowa a kan ki , ni wallahi sam bana yadda da duk wani motsinki, to wallahi na baki wata da`ya ki shirya Zakariyya ne zaki aura", sai a lokacin Fadeela ta fashe da kuka inda Inna ta titsiye baba Aminu da tambaya, "mene aka ce ta aikata haka Aminu",? Inna tai tambayar tana rike da hab`a cikin wannan huci baba Aminu ya fara cewa," Inna matukar na tuna Fadeela na gabana hankali tashi yake , ni yanzu ma wallahi na fara zarginta, kullum sai an kawo mini maganarta taya ne hankali zai kwanta , tunda ta fara mu'amala da wannan yaran duk hankalina atashe yake", yay ajiyar zuciya yana cewa, "na dai fad`a miki ki shirya auren Zakariyya nan da wata d`aya kacal", yana gama fad`a ya fice cikin huci ya tafi gidansa Fadeela ta fad`a jikin Zainab tana wani rurucewa da kuka ", Zainab wannan wacce irin rayuwa ce , mene ne mutane suka gani ina aikatawa, yanzu shima baba Aminu yana mini kallon da wasu mutanen suke mini har ya furta yana zargina", Zainab cikin karyayyar zuciya idanunta sun ciko da kwalla tace ", kiyi hakuri Fadeela, wallahi baba Aminu yana da gaskiya, ki daure ki auri Zakariyya zaki samu farin ciki", Fadeela ta bar jikin Zainab ta doshi inda Inna take ta durkusa kasa tana cewa cikin gagarimin kuka mai gwanin ban tausayi," wallahii Inna ki hana baba Aminu aura mini Zakariyya, ya bani lokaci zan fito da wanda nake so," Inna tace ,"babu abin da zance Fadeela kibi umarninsa , ni barin duniya zan na barku tare duk yadda yay da rayuwarki cigaba yake nema maki", Inna tana gama fad`a ta tashi ta shige dakinta, kuka Fadeela ta sake rurucewa da shi tana kallon Zainab. "lallai ma ambassador ya raina miki hankali, to wallahi idan zaki nemi wani namijin ma ki nema , zama dana miji d`aya asara ne", Ruma tayi maganar tana kallon Ummi baby jin Ummi baby bata ce komai ba yasa Ruma cewa," ni kinga ma anjuma wani sabon chairman nake da shi , zamu je muji irin nashi salon,"ta karasa maganar tana dariya๐Ÿ˜‚. baba Aminu cikin hucin ya koma gida zama ya yi a falo yana ajiyar zuciya Jamila ce ta fito fuskarta cike da farin ciki da annushuwa, ko tambayar halin da yake ciki batai ba ta kama hannayensa ta mik`ar da shi tsaye tana sumbatarshi murmushin yak`e yay mata kawai yana cewa,"mene yake faruwa", rungume shi tai ajikinta cikin wani rurucewa da kuka tana cewa. kuna tare da Autar marubuta share and comment.... my fans๐Ÿ™. K`AWAR KARUWAI๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ BY AUTAR MARUBUTA _____________________________ page 11&12 ,"ciki ne dani mijina , wallahi ciki ne dani "๐Ÿ˜ญ shima baisan lokacin da yaji idanunshi sun ciko da kwallaba zameta yay a jikinsa yana kallon fuskarta bai iya cewa da ita komai ba , kawai ya sake rungume matarshi yana zubar da hawaye. Anan kofar gidansu Ruma kuwa ,wani saurayi ne tsaye wanda ga dukkan alamu yana jiran wani abun ne, zuwa can Farida ta fito ta tsaya gabansa tana cewa," a she kai ne kake kirana", saurayin yay murmushi yana cewa, "a she zaki gane ni ke nan ", Farida tace ," me zai hana,to amma meke tafe da kai", murmushi ya sa ke yi yana kallon fuskar Farida yana cewa, "kin barni cikin zulumi tun ranar da muka had`u", murmushi tayi tana cewa," Hmmm, nifa malam karuwa ce na fad`a ma gaskiya dan haka ba wani mamaki ba ne", cikin karyayyar zuciya yace ,"kina kama da mahaifiyata Farida, wallahi tun a daren dana ganki kwana nayi ina tunanin mahaifiyata, muna kaunarta sosai amma Allah ya raba mu da ita," Farida sake kallonshi tai tana murmushi sannan tace ,"mene sunanka", cikin girmamawa yace ,"suna na Khalid ". Yanzu misalin karfe 8na dare , Inna na zaune a falo, Fadeela tazo ta wuce ta rufe gida , inda Fadeela ta kalli Inna tana cewa", saida safe Inna", sauri Inna tayi tana kallon Fadeela," yau kuma tun yanzu zaki kwanta", Fadeela tace ,"eh Inna kaina yana ciwo", Inna tace ,"nima kuwa zuwa zan yi na kwanta , domin kwana biyu ina yawan jin Ana hauro mana gida ina jin tsoro," murmushi fadeela tayi tana cewa, "ke dai kawai Inna ki ce matsoraciya ce ke," Fadeela ta shige dakinta tana dariya Inna tace ",kin ji mini yarinya tsoron gidanku ",๐Ÿ˜‚ Inna ta dauro alwala ta shige dakinta Fadeela na shiga daki aiko kiran wayar Alaji Sani na shigowa nan suka sha wayarsu har yake tambayar yaushe zasu had`u, bayan su gama wayar sai ga kiran Zakariyya, amma Fadeela kawai tayi blocking d`in shi , kawai ta kira Alaji mansur, suka sha soyayya bayan duk ta gama abin da zatai wani matsanaicin ciwon mara ya riketa gamm, ta jima tana shan bakar wahala kafin ta samu sa'ida. Ruma ce kwance kan wani had`ad``en gano tana shan ๐Ÿฆ babban hotel ne na masu abin๐Ÿ’ด zuwa can saiga gogannaku ya fito daga bathroom , goge jikin shi yake da towel yana kallon Ruma , harararshi tai tana cewa," to mene kake kallona", tsalle yay ya hau kan gadon yana cewa, "karki sake hararata ko kisha wahalar da tafima ta d`azu, domin ni chairman a kujerata ma ina basu wahala bare a gun mata", tab`e baki Ruma tayi tana cewa," ku fa maza kuna bani mamaki , kawai wannan d`an abin da kamin shi ne shan wahala , to wallahi ko a jikina chairman", haushin maganar yaji ya mike yana kokarin caf kota yana cewa, "to bari ki gani ", da gudu ta tashi ta cillar da bargon dake jikinta tana dariya , shima dariya ya kwashe da ita katan banzan yana cewa," zo kisa kayanki Ruma",ya d`ebi kayan yana mika mata , fari tamai da idanu tana cewa, "mene amfaninka", cewa yay "haka ne ta inda aka hau tanan ake sauka ",ya mike da kayan ya nufi inda take.๐Ÿ˜Ž Zainab na shiga lungun gidansu Fadeela taji Ana kwala mata kira, tabbas idan ta gano muryar Zakariyya ce , aiko tana juyawa ta ga bawan Allah sanye da jakar goyo. Fadeela ce kawai cikin gidan , sakamakon Inna tana gidan baba Aminu, tunda taji Jamila ta samu ciki bini-bini ta shirya ta je yanzu haka ma tana can Fadeela tasa hijab tana shirin fita taji sallama juyawa tai daidai lokacin da take amsa sallamar had`e rai ta yi taja dogon tsaki tana kallonsu Zakariyya da Zainab suka kalli juna cikin mamaki Zainab ce ta karasa gabanta tana cewa", haba Fadeela mene haka ke nan", Fadeela hankad`e Zainab ta yi gefe cikin mummunan bacin rai su ma cikin gagarumin mamaki suke kallonta ", daman ke ce babbar munafukar da ki ke shiga kina fita kan dole baba Aminu ya auran Zakariyya, to wallahi kin bani kunya Zainab", Fadeela ta juya ta kalli Zakariyya tana nunashi da yatsa๐Ÿ‘‰ ", tom ka ji ni da kyau kai kuma maye , na tsaneka Zakariyya bana kaunarka bana sanka , ku fi ce mana a gida", tsananin mamaki ne ya kama Zainab saboda a iya zamanta da Fadeela tasan da cewa Fadeela ba ta da aljanu , to amma mene wannan abun da ta aikata, tsananin fusata Zainab ta yi , amma ba tare da tace komai ba tasa kai ta fita , ganin hakan yasa Zakariyya bin bayanta da 'yar jakarshi da aka zo za'a kwana biyu๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ bayan sun fita Zainab tayi nannuyar ajiyar zuciya tana kallon Zakariyya," dan Allah ka yi hakuri Zakariyya ", murmushi yay bawan Allah๐Ÿ˜‚ yana cewa," babu komai Zainab ni yanzu zan koma", sakin baki ta yi cikin tsananin jin tausayinshi sa'ilin da tai ajiyar zuciya tana cewa ",zuwanka fa ke nan Zakariyya dan Allah kayi hakuri, kaje gidanmu ka huta ai kaduna ba wasa ba", shi ma ajiyar zuciya yay yana cewa", da kin barni Zainab hankali duk ya yi gida wallahi", cikin murtuke fuska tace ", to tunda gidan namu ne baka san zuwa , sai mu tsallaka mu je gidan baba Aminu", a ajiyar zuciya Zakariyya ya kuma yi yana kallon Zainab cikin tausayin kanshi , sannan yace ," tom shi ke nan , mu je gidan naku", sannan suka dauki hanya suna tafiya suna hira . Ita kuwa Fadeela cikin b`acin rai ta fita waje , sakamakon Alaji mansur dake jiranta, Farida ce da Kalid a kofar gidansu , suna cikin mota suna hira Kalid ya kalli Farida yana cewa ",gaskiya ke Farida mutuniyar kirki ce, amma ban so kika jefa kanki a irin wannan yanayin ba", kallon shi tai tana cewa," Kalid ke nan ", fuskar shi babu wasa ya kalleta ", zan so ki bani da ma cikin rayuwarki , na zamto miki jigo na ma ye maki gurbin da kika rasa , ya zamto jinina yana yawo cikin jikinki Farida wallahi Farida ina sanki", shiru tayi tana kallonshi๐Ÿ™Ž ganin bata ce komai ba yasa Kalid cigaba da cewa ," zan nunawa dangina ke ce nake so , zan baki gudunmawar daidaita rayuwarki, wallahi har zuciyata nake kaunarki Farida ", nannauyar a jiyar zuciya tayi jikinta duk a ma ce , wani kwarjini Kalid yake mata , hakan yasa ta kasa cewa komai ta b`ude murfin motar ta fita da sauri ya fito shima ya sha gabanta yana cewa", Farida", juyawa sukai baki d`ayansu sakamakon k`arar mota da suka ji a bayansu", motar Alaji mansur ce tai parking shi da Fadeela, suka fito yayin da Alaji mansur ya jingina jikin motar tashi yana gyara babbar rigarshi, share and comment.... . K`AWAR KARUWAI๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ BY FATIMA ABDALLAH KANO (Autar marubuta) _________________________________ page 13&14 Murmushi Fadeela tayiwa Farida tare kuma da d`aga musu hannu ta shige cikin gidan tana shiga ta ga Ummi baby tana gyaran

Chapter 2 of 6