An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
DAN KARUWA
writen by zahra surbajo
Page 1
"Mummy don Allah kiyi hakuri ki rufamin asiri kar kije club dinnan don Allah ki tausayawa rayuwata da taki"cewar wani matashin yaro da shekarunshi bazasu wuce goma sha biyar ba,
Tsugune yake rike da kafafuwanta yana kuka,kallo daya zaka masa ka fahimci yana cikin tashin hankali me tsanani.
Cikin halin ko in kula matar ta fara magana cikin isa da izza tace. "Sultan kenan,wlh lamarinka ya fara bani tsoro,taya ina kasuwanci dan in rufa maka asiri amman kai kullum kawo min nakasu kake ga kasuwanci na," Hawaye ya share yace bakinshi na rawa. "Mummy kiyi hakuri don Allah abokaina tsokanata suke suna kirana DAN KARUWA, sunce kin cika yawo mummy ki zauna agida don Allah ki taimakeni"yakarasa maganar cikin matsanancin kuka.
Murmushi tayi sannan tace. "In kace ta mutane zakabi zaka mutu da talauci, niko yau wlh ba abinda ze hanani fita,in zakaje ka kwanta kaje ka kwanta,danni se dare"
Bin jikinta yayi da kallo yana kuka,sanye take cikin riga da wando masu matukar bayyana surarta,wanda sam bedace ta fita dasu ba.
Baki na rawa yace. "To mummy kidaura zani akan kayan kan ki fita kinji"
Dariya tayi tace. "Sultan problem,je ka daukomin zanin"
Ba musu ya mike da gudu yaje dakinta ya dauko mata zanin harda hijabi ya mika mata.
Bata musa mishi ba ta daura zanin tasa hijabin sannan ta dauki handbag dinta ta shafa gefen fuskarshi tace. "Ka kulle kofa kayi addua kaji,se na dawo"
Jiki ba kwari yace "Adawo lfy mummy"
Yanaji yana gani ta fice daga gidan,rushewa yayi da kuka ya fada kan kujera yana kuka me tsuma zuciya.
Ita ko tana fita, wani lungu ta samu ta cire zanin da hijabin daya bata tasa ajaka tayi gaba abunta.
Tana tafiya tana juya jiki,har ta isa bakin titi ta hau mashin.
Tana isa gurin club din tundaga bakin kofa matasa ke mata ihu suna kiran. "Lokacinki ne khady baby," Gaba daya gurin se tafi ake mata itako se juyi take cikin kartin mazan suna tafawa wasu kuma su rungumeta.
Cikin gurin ta karasa shigewa,inda ta nufi mashaya,
Kwalba uku ta siya na cordine bata bata lokaci ba ta shanyesu,mintuna kadan ta mike ta fara hada hanya,
Isa zakara ne ya hangota tana hada hanya da sauri ya nufeta,
[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:DAN KARUWA
Writen by zahra surbajo
Page2
Yana zuwa janyota jikinshi yayi yana dariya,yace. "Khady baby kinyi wuyar gani"
Murmushi tayi tace tana kara shigewa jikinshi. "Zakara,kacika takura ne yasa nake maka wasan buya,kai bakasan kayi abu na marmariba,kai cinye du ne shiyasa bana son alaka dakai wlh,gaka da hannun yan dambe"
Murmushi yayi ya fara shinshinata yana laso wuyanta kamar wani mayunwacin kare,yace. "Khady baby yau zan miki biya me kyau dan akwai kudi ajikina,karkiji komai,wlh kishin ruwanki nake narasa ina zan ganki se yau Allah ya hadamu"
Dariya tayi ta lakace mishi hanci tace. "Shaidan de ya hadamu ba ruwan Allah"
Dariya shima yayi yace. "You are right"
Daga haka jan hannunta yayi suka nufi gurin masu bada daki,biyan kudin yayi ya karbi key suka shige dakin.
Suna shiga dakin suka shige jikin juna,kowa na kokarin nunawa dan uwansa shi gwanine.
Sautin numfashinsu kawai kakeji yayinda suka isa kan gado.
Sosai zakara ya dirji kudinshi dan sun kwana biyu basu hadu ba.
Itako tuni bacci yay gaba da ita me nauyi bata farka ba seda garin Allah ya waye.
Koda ta tashi wanka tayi tai sallah,sannan ta tashi isa zakara dan ya sallameta zata wuce.
Koda ya farka,yaganta sabuwar shaawarta ce ta kamashi,duk yadda taso ya barta yaki seda ya sake kauda bukatarshi.
Mikewa tayi ta maida kayanta,isa dubu talatin ya bata.
Wanda sosai taji dadin su.
Sallama tai masa ta dauki jakarta ta fice ta nufi gida.
Tana isa unguwarsu yara suka fara mata ihun karuwa,itako ko ajikinta,haka ta dunga wuce mutane sanye cikin shigar diban albarka.
Sultan dake cikin gida yana mata wanki,jiyo hayaniyar yaran dayaji ne yabashi tabbacin mahaifiyatshi ce ta dawo.
Jikinshi ne yayi sanyi,sanda ta shigo gidan batare da zani da hijab din daya bata ba.
Wasu hawaye ne masu zafi suka fara biyo fuskarshi.
Dakyar ya iya yima ta sannu da zuwa.
Amsawa tayi cikin walwala,tace. "Sultan ka ganni se yanzu ko wlh wani sabon kamu nayi shine na tsaya tare dashi kayi hkr kaji yarona,Allah yayi maka albarka"
Shuru yayi yakasa bata amsa,yana kallo ta shige dakinta baa jimaba yafara jiyo karar ruwa alamun wanka takeyi,
Rasa abunyi yayi dan haka kawai rushewa yayi da kuka,
Muje zuwa.
.surbajo for life.[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*DAN KARUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Writen by zahra surbajo*
*Page 3*
Seda yayi kuka me isarshi sannan ya mike jiki ba kwari ya shiga cikin dakin nata.
Kamar kullum kayan data cire suna zube akan kujera a falon.
Kwaso kayan yayi,yauma har da pant da bra din data cire duk ta ajiye masa ya wanke.
Yana fitowa ya fara wankesu,batare da kyamar komai ba,duk da cewa pant din kallo daya mutum ze masa yasan me aka aykata dashi,hakan be hanashi wankewa ba.
Tsaf ya wankesu ya shanya mata a igiya,sannan ya wuce dakinshi yayi wanka ya kimtsa,ya fito ya nufi dakin mummyn tashi.
Sallama yayi ta amsa sannan ya shiga,.. Tana zaune kan kujera,tana latsa waya,gefe daya kuma tana zukar shisha tana fesar da hayakin.
Dagowa tayi tana kallonshi fuskarta dauke da murmushi tace.
"Yarona dan albarka,Allah ya tsaremin kai yabaka mace ta gari yarona,"
Murmushi yayi na karfin hali yace.
"Amin mummy"
"Se ina kuma zaka danaga kayi kwalliya?"mummy ta tambaya.
Cike da ladabi da biyayya yacs.
"Zanje cikin kasuwane indan samu ayki ko na dako ne insamu insami kudin abinci,sannan inason intara kudin makaranta na kinga na samu admission dole indage"
Murmushi tayi ta shafa kanshi,sannan ta zuge jakarta ta zaro wasu kudade masu yawa,tace tana mika masa.
"Yarona dan albarka kenan,ka kwantar da hankalinka Allah ya baka uwa jaruma,dan haka bakai ba kuka,ga kudin makarantarka nan na tanajesu,gasu ka ajiye agurinka"
Wasu hawayene masu zafi suka zubo masa yasa hannu yashare yace bakinshi na rawa.
"Kuka kuma na nawa mummy,ay kullum cikin sani kuka kike,mummy inason ki ayadda kike,ina alfahari da zamanki mahaifiyata, mummy bana danasani gameda haka,amman bazan yafewa kaina ba in na amshi kudin da mahaifiyata ta fita yawo ta zubarmin da mutunci da nata da sunan kasuwanci ba,mummy ki daure ki rufamin asiri,kidena gurbatamin rayuwata data zuriaar da zan samar agaba,nifa danki ne mummy me alfahari dake amatsayin uwa,kiyi hakuri ki fadamin nawa kike samu aduk fita idan kinyi,namiki alkawarin ayki tukuru in kawomiki kudin"
Tasss ta daukeshi da mari,ta fara mgn tana hawaye.
"Sultan ni kake cewa ina yawo,inma yawon nake anfada maka jin dadi nakeyi nima in inayi,kasan balain da nakeji idan banyiba,koma me nakeyi Ay dan kai nakeyi,akan me kullum zakasani agaba kanamin fada kaine ka haifeni konice na haifeka,kasan wahal danasha dan ganin kazama mutum kasani nace?"ta karasa maganar cikin matsanancin kuka,
Kan kujera ta fada ta rushe da kuka me tsuma zuciya,da ganin kukan kasan an fama mata tsohon ciwone.
Sultan gigicewa yayi yama rasa abinda zeyi,kifa kanshi yayi kan cinyarta yana kuka yana fadin.
"Mummy kiyi hkr don Allah kar fushin Allah ya kamani,kukanki masiface agareni,kigafartamin mummy kiyi hakuri nadena bata miki rai kiyi shuru"
Rungumoshi jikinta tayi gaba daya rana cigaba da kukan,yana share mata hawaye.
Cikin kukan take fadin.
"Sultan kaine kawai gatana se Allah,bani da kowa da komai sekai,wannan sanaa da nakeyi sultan har cikin raina banaso,narasa taya zan dena wlh ba dadin yi nakeba kawai masiface don Allah kar hakan yasa watarana kaima kace zaka gujeni,in ka gujeni munin abinda zan aykata seyafi wannan da nakeyi"
Rufe mata baki yayi yace.
"Mummy bazan gujeki ba,har abada inasonki,mummy zan miki addua Allah zesa kidena mummy na kidena kuka"
Haka yay ta rarrashinta,dakyar tai shuru,suka fara hira dan ya sake kwantar mata da hankali.
Duk yadda taso ya amshi kudin yaki amsa dole ta hakura ta kyaleshi.
Kitchen yashiga ya dafa mata abinci me dadi dan tuni ya jima da kwarewa gurin girki.
Yana gamawa ya zubo mata yazo yazauna ya dunga bata abaki tanaci tana sa masa albarka har ta koshi ya kwashe kwanukan yakai kitchen.
Yazo yay mata sallama ze fita,dakatar dashi tayi,tasowa tayi ta karaso kusa dashi tace tana murmushi.
"Sultan ko abincina bakaci duk abinda na siya da kudina bakaci,base kamin bayani ba nasan kana gudun cin haramunne,"
Murmushi yayi ya dukar dakai kasa.
Dubu biyar ta mika masa tace.
"Ka amshi wainnan kudin,wlh tlh blh ba ta haramtacciyar hanya nasamesu ba,na halak ne,kai amfani dasu koda gurin jari ne kafara seda wani abun kaji dan albarkan dana"
Murmushi yayi yasa hannu biyu ya amsa dan yasan mahaifiyarshi karuwace de amman tana sawun gaba gurin mutane masu gaskiya.
Godiya yay mata yasa kai ya fice ta bishi da adduar samun nasara.
Kasuwa ya wuce,inda yasai abinci yaci sannan,ya shiga bangaren yan saida turare,ya saro su kala kala,
Muje zuwa
Surbajo for life.[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*DAN KARUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Writen by zahra surbajo*
*Page 4*
Cikin kasuwa yashiga da turarukan yana saidawa.
Kamar wasa segashi da kudinshi cas a hannu turarukan sun kare.
Sosai yaji dadin hakan yayiwa Allah godiya,dan haka komawa yayi yakara saro wasu yacigaba da saidawa.
Seda yaga gari yafara duhu jamaa sun fara watsewa,ya hakura yabi hanyar komawa gida.
Yana shiga gidan ya fara jiyo karar mummynshi alamun dukanta akeyi.
Da gudu ya watsar da kayan hannunshi ya fada dakinta.
Agigice ya juya ya fito yana maimaita duk adduar da tazo bakinshi sakamakon arba da mahaifiyarshi da yayi tsirara tare da wani kato yana dukanta.
Jiri yaji yana daukarshi dan haka zamewa yayi yazauna agurin yana jiyo kalar zagi da cin mutuncin da mutumin yakemata.
"Banza ashawo,ni zakice bazan kwanta dake ba se nasa kariya,kariyar uban me zansa bayan naga har da gareki a karuwancin,"
Kamar kibiya haka sultan yaji maganar ta sokeshi,runtse ido yayi yana ta kuka.yana jiyo sautin kukan mummyn tashi,har seda mutumin yagaji dan kanshi yazo ya wuce ta gabanshi sangam sangam. Bayan wucewar mutumin da dan jimawa ne sultan ya iya rarrafawa ya shiga dakin mahaifiyar tashi.
Kwance take akan kujera sanye da doguwar riga tana kuka.
A hankali ya dafata yace cikin kuka.
"Kiyi hakuri kinji mummy,Allah ze saka miki,kidena kuka"
Dagowa tayi ta dubeshi cikin kuka tace.
"Sultan kaji zafin hakan ko?"
Dukar da kai kasa yayi yana girgiza mata kai alamun eh. Sake rushewa tayi da kuka tace.
"Ba abinda naimasa ya dokeni sultan,"
Kasa bata amsa yayi illah kukan daya cigaba dayi.
"Kaji ka tsaneni ko?"
Da sauri ya dago kanshi ya ruko hannunta yace.
"Mummy inna tsaneki,dawa zan zauna,har gobe mummy ina sonki,ina kaunarki, ba abinda zaki aykata da zesa na tsaneki mummy"
Kuka taci gaba dayi me tsuma zuciya,cikin kuka tace.
"Why Fahad,me nayi maka haka ka jefa rayuwata cikin garari,me mukayi maka nida danka,me mukayi maka?"tasake rushewa da kuka.
Da sauri sultan ya matsa kusa da ita ya rukota yace.
"Mummy waye fahad kuma?meye alakarshi dake?"
Batare data dago kai ba ta bashi amsa.
"Fahad shine mahaifinka sultan,alakar dake tsakanina dashi tsohon miji nane,shine ya dandanami zuma at dsame time ya dandanamin madaci,fahad ya cutar da rayuwata da yawa sultan,ya cuceni,"ta karasa maganar cikin kuka.
Dakyar sultan yashawo kanta tayi shuru,sannan tace.
"Yau zuciyata ta aminta na baka labarin asalinmu sultan bayan shekaru masu yawa ko zanfita hakkin boye maka da nayi"
Mikewa tsaye tayi ta fara zaga daki tafara da cewa.
*FARKON LABARIN.*
*RIMIN K'URU*
wani karamin kauye ne a karamar hukumar kiru ta jihar kano.
Kauyene na fulanin asali shiyasa yawancin jamaar dake kauyen fulani ne.
Malam jibril dattijone ne nagari akauyen me tsoron Allah.
Bafulatani ne yana da mata daya inna hajjo,yar su guda daya aduniya,Nana Khadija.
Nana khadija tasamu kulawa daidai karfin iyayenta,basu rageta da komai ba,
Nana ta taso da kyau na fitar hankali,kasancewarta bafulatanar asali,tayo gadon kyau tundaga kakanninta.
Ko kadan Nana bata da hayaniya,yarinyace me hakuri da kauda kai,uwa uba tana da ladabi da biyayya ga kunya.
Kowa akauyen nason nana,gashi mahaifinta yasata makaranta boko da arabic,wanda sosai take maida kai,
Cikin garin kiru akasa ta makarantar da akwai nisa tsakaninsu da kauyensu amnan kullum nana seta je makarantar dan bataso tai fashin zuwa.
Tsawon shekaru nana ta kwashe tana karatun inda ahalin yanzu ta gama secondry school,islamiya kuma tuni tayi sauka.
Dakyar mahaifinta yabarta ta gama karatun sabida yawan manema aurenta.
Wanda ita nanar mutum daya takeso acikinsu,shine haidar,Sun shaku sosai da haidar,shi dan kano ne teaching practice aka kawoshi makarantar su nana suka hadu acan.
Nana nason haidar da duk zuciyarta haka shima,komai yasamu nana,bashida hira se nana.
Bayan ta kammala karatu ne,malam ya umarci nana tacewa haidar yanason ganinshi.
Sosai haidar yayi murna,be bata lokaci ba ya iso kiran na mahaifin nana.
"Malam aliyu na jima da sanin kana neman auren yata nana,dan haka na shirya aurar da nana yanzu,kaje ka turo magabanta dan mu tattauna"cewar malam jibril
"Baba nagode da wannan dama daka bani kuma insha Allahu,zan turosu cikin satin nan"
Daga haka sukai sallama haidar ya wuce kano cikin gaggawa.
Haidar dane ga masarautar kano,mahaifinshi shine akan karagar mulkin kano,amman koda wasa haidar be taba nunawa nana hakan ba,
Muje zuwa
Surbajo for life.[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*DAN KARUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Writen by zahra surbajo*
*@zahra_surbajo1 shine handle dina na instagram,nafi hira da fans tacan*
*Page 5*
Sarki hashim Aliyu shine mahaifin haidar,yayanshi hudu a duniya,
Matanshi biyu,hajiya hauwa ,itace ta farko,se amarya,Hajiya zainab
Hajiya hauwa y'arta daya mace,me suna husna,se hajiya zainab me yaya uku duka maza,Fahad shine na fari,se Haidar Se usman.
Idan akwai abinda hajiya hauwa ta tsana shine,ta bude ido taga hajiya zainab da ahalinta,kullum fata da burinta subar gidan duniya.
Bokaye da yan tsubbu kullum cikin binsu take,yayinda hajiya zainab ta rike Allah,wanda shi ke bata kariya.
Haidar na isa gida kai tsaye gurin mahaifinshi ya nufa me martaba sarki.
Kasancewar haidar sunan mahaifin sarkin akasa masa ne me martaba ke girmama haidar da bukatunsa.
"Babana ya akayine?"cewar me martaba bayan haidar ya gaisheshi.
Sosa keya haidar yayi kamin yace.
"Ranka ya dade,inda nake neman aurene aka bukaci ganinku"
Murmushi sarki hashim yayi sannan yace.
"Haidara zaki,yanzu aure zakayi yayanka beyi ba"
Turo baki gaba haidar yayi yace cikin shagwaba.
"Shi be shirya yi bane,ay"
"Kai kuma ka shirya ko?"me martaba ya tambaya cikin sigar wasa.
Gyada kai haidar yayi alamar eh.
"To bakomai a ina ne kasamo yarinyar yar waye?"inji.me martaba.
"Baba acan rimin k'uru ne,yar gidan malam jibril bafulatani,sunanta nana khadija,baba yarinyar nada tarbiyya kasa abincika ma"
Murmushi,sarki yayi,dan yasan haidar farin sani,ba ruwanshi da nuna karya aharkarshi,
"To badamuwa zan tura su galadima suje su gana da iyayenta"cewar sarki cikin walwala.
Godiya haidar yayi sannan ya mike ya wuce gurim ummanshi.
A dakinta ya sameta,karasawa cikin dakin yayi da sallamarshi.
Da faraa ta amsa tana masa sannu.
Durkusawa yayi ya gaisheta,sannan ya kwantar da kanshi kan cinyarta,cikin shagwaba ya fara mgn.
"Umma,Aure fa zanyi"
Jin maganar tayi kamar dirar aradu,cikin sigar tsokana tace.
"Ba kunya babana kake fadamin aure zakayi,wasa kakeyi nasani,inakai ina aure yayanka beyiba"
"Wlh umma aure zanyi,yanzu ma daga gurin me martaba nake,iyayen yarinyar suna bukatar iyayena suje"
Daga haka ya kwashe komai ya fada mata.
Dosai taji dadin bayanin nashi,
"To babana Allah yasanya alkhairi,yasa damu zaayi,yasa kuma abokiyar zamanka ce"
A kunyace ya amsa yana dariya.
Me martaba ya tura garin su nana,duk wani bincike angama yinshi baa sameta da wata illa ba.
Hakanne yasa ya tura wakilai su gana da iyayen nana.
Sosai nana da kowa na garin sukayi mamakin jin waye haidar.
Iyaye sunyi mgn ta fahimta da girmama juna,take suka biya sadakin nana,aka tsaida lokaci,watanni uku masu zuwa.
Bayan an saka ranar ne,hajiya hauwa tasamu labari,
Bata damuba,tunda bataji yar wani sarkin ze aura ba,sema dariyar mugunta datai musu.
Nana ko da haidar yazo gurinta bata nuna masa tasan koshi waye ba,haka shima be nuna mata ba.
Haka suka ci gaba da gudanar da soyayyarsi me tsabta.
Duk wani abun al-ada ankai shi gidan su nana,dan biki ya karato.
Lefenta nagani na fada aka shirya mata,kowa seson barka yakeyi.
Yau saura kwana biyu biki,haidar ne zaune adakin yayanshi fahad,
Cikin girmamawa yace.
"Yaya prince,ya kamata kaima fa kafito da mata kai aure ka huta,sabida yarima me jiran gado be dace ace beda mata ba har yanzu"
Murmushi yayi sannan ya yamutsa fuska yace kamar baya so.
"Matanne duk kwadayayyu,karasa gane mesonka domin Allah,ni shiyasa banda lokacinsu"cewar fahad
Murmushi Haidar yayi yace,
"Allah yabaka mace kwatancin nana ta prince,wlh bata da kwadayi gata da tarbiyya"
Dariya yayi ya kauda zancen da cewa.
"Ya kamata ku shirya akai motoci can garin su adakko su su dawo nan agama bikin gabadaya se su koma,zefi saukin zirga zirga,naji jiya me martaba yana mgn da mahaifin nana game da haka kuma ya amince."
Sosai haidar yaji dadin labarin,dan haka da gudu ya fice daga dakin yaje ya fara hado kan direbobin gidan nasu.
Fahad ko kwanciyarshi yayi yana tunanin shawarar kanin nashi,tabbas shima ya yaba da hankalin nana,in ze samu kamarta ze iya aura.
Kamin dare motocin daaka tura garin su nana sun dawo dauke da jamaa dangin nana,
Bangare guda aka ware musu,agidan sarki,a wadace,yadda zasu sake sosai.
Amarya nana tayi kyau bana wasa ba,dan me kwalliya ta musamman aka ajiye mata,datake tsarata.
Yau jummaa yaune ranar daurim auren nana khadija da haidar,wanda zaa daura a masallacin gidan sarki.
Tuni jamaa sun cika sun tumbatsa ana jiran adaura auren.
Muje zuwa
Surbajo for life.[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*DAN KARUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Writen by zahra surbajo*
*Page 6*
Liman kawai ake jira ya karaso,
Ba jimawa ya karaso me martaba ma ya fito.
Liman ya bukaci waliyyin amarya da wakilin ango dasu gabato.
Ba bata lokaci suka matso.
"Ina takardar gwajin jini dasukayi"liman ya bukata.
"Wacce irin takardar gwajin jini kuma,bayan dukansu lafiyarsu lau"inji madaki wanda shine wakilin ango.
"Bana daura aure se ankawo wannan takardu na shaidar tabbacin lafiyarsu,"cewar liman.
Ran madaki ne ya fara baci da batun na liman.
Me martabane ya katse hayaniyar inda yace.
"Wannan tsari liman abune me kyau,akira amarya da angon aje asibiti dasu ayimusu test din yanzu adawo adaura auran." Ba musu dogarai sukayi kamar yadda sarki ya bukata.
Mota aka kai har kofar gidan amarya nana ta shiga,sannan haidar shima ya shiga,se mutane biyu amintattun sarki suka bisu.
Ana zuwa asibiti baa bata lokaci ba,aka dibi jininsu aka shiga dashi dakin gwaji.
Mintuna kadan aka fito da sakamako.
Gwajin ciwon HIV duk basu dashi,gwajin ciwon hanta duk basu dashi ,genotype dukansu AS,AS
Kiransu office likita yayi yamusu bayani cikin natsuwa yace.
"Bawai baku da lafiya bane,aa,yayan da zaki haifa ake tausayawa,sabida dukanku as gareku wanda zaku iya haifar da me ss,azo ayta faman shan wahalar magani karshen inbaay daceba yayan sudunga mutuwa,"
Hakade yay ta musu bayani game da hatsarin dake cikin aurensu,daga haidar din har nana kuka sukeyi,me tsuma zuciya.
"Ashawarce ku hakura da juna domin samun kwanciyar hankalin kowa,kuma kun taimaki yayankune"cewar likitan cikin yanayin tausayi.
Haidar share hawayenshi yayi,yakamo hannun nana yace cikin rauni.
"Nana kinga kaddarar Allah ko,kiyi hakuri kidena kuka,Allah be kaddaro rabon aure tsakaninmu ba,ni musulmi ne na yarda da kaddara,nana, dole mu hakura da juna,kema kin yarda da kaddarar?"
Cikin kuka ta gyada mishi kai,ita kadai tasan zafin da zuciyarta ke mata,.
"Nana yaya fahad genotype dinshi ba AS bane,na rokeki da girman Allah ki amince adaura miki aure dashi,mutumin kirki ne,ze soki fiye dani na tabbata nana,kitaimakamin banason kibar zutiarmu dan Allah"
Nana ido kawai take ware mishi tama rasa mezatace jitake kamar tamutu ta huta,dan haka gyada mishi Kai kawai take batare da tasan tanayiba.
Hakan yasa haidar tunanin kota amincene.
Tahowa sukai zuwa gida.inda jamaa kecan ke jiran dawowarsu.
Suna zuwa gida da gudu nana ta shige cikin gida tana kuka.
Haidar dakin fahad yafada,ya birkico takaddunshi har ya dauko takardar genotype dinshi.
Da gudu ya juya zuwa gurin daurin auren,ana parking ya fito bayan yayi kokarin seseta natsuwarshi.
Gaban me martaba da mahifin nana yaje ya duka,yamika musa takardun duka,
Dubawa sukayi,wata zuface ta karyo musu me zafi cikin tausayi suke duban shi summa rasa bakin magana.
"Baba ku amince amaida auren kan fahad,nana ma ta amince,ga takardar gwajin jininshi ze iya auren nana baba"cewar haidar can kasakasa gudun kar wani yajiyo.
Me martaba,bece komai ba,mahaifin nana ne ya hada takardar fahad da nana,ya mikawa madaki yayi masa rada akunne
Madaki liman ya mikawa takardun yadan masa bayani atakaice.
Nan fa aka shiga daurin auren gadangadan.
Haidar kusa da fahad ya koma,fahad se tsokanarshi yake,shiko se yake yake masa.
Can suka jiyo sankira na fadin.
"ANDAURA AUREN YARIMA FAHAD HASHIM ALIYU,TARE DA AMARYARSA GIMBIYA NANA KHADIJA JIBRIN ABDULLAHI,BISA SADAKI DUBU DARI BIYU YA BIYA LAKADAN JAMAA KU SHAIDA"
Agigice Fahad ya zabura,yana fadin.
"Kai ba ni bane haidar ne,ku gyara sunan"
Rukoshi haidar yayi cikin hawaye yace.
"Don girman Allah yaya prince kamin rai,karkace komai har taron nan ya watse don Allah"yakarasa maganar dakar sabida kukan dake kokarin cin karfinshi.
"Taya zanyi shuru bayan badakai aka daura aurenba?"cewar fahad afirgice.
"Kayi shuru yaya inba so kake zuciyata ta fashe na mutu ba"cewar haidar yana haki.
Shurun dole fahad yayi kanshi na bugawa ya rasa abun yi.
Yanaji yana gani aka gama daurin aurensa da nana khadija.
Ana gamawa jamaa sukayo kanshi,ana taya shi murna,bebi takan kowa ba yaja hannun haidar sukai gida,dan yakosa yasan dalilin dayasa hakan ta kasance.
Suna shiga dakin fahad din,haidar ya rushe da kuka gamida yiwa fahad bayanin abinda ya faru.
Duk juriya irinta fahad seda ya rushe da kuka shima,rungumo haidar din yayi jikinshi,sukai ta kuka me tsuma zuciya dakyar sukai shuru.
Muje zuwa
Surbajo for life[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*DAN KARUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*writen by zahra surbajo*
*jiya naje wani tarone yasa banyi ba kuyi hakuri*
*page 7*
Bayan sunyi shuru ne,haidar ya dafa kafafum yayanshi yace.
"Yaya prince nana amanata ce na baka,na yarda dakaine yasa na baka nana,kayi hakuri ka koyi sonta nana bata da matsala,yarinyace me biyayya don Allah yaya"ya karasa maganar cikin rauni.
Murmushi fahad yayi ya dafa kafadar haidar yace.
"Haidar da ace in nasaki nana akwai yiwuwar aurenku wlh da yanzu zan saketa,amman hakan akwai matsala na amshi amanar nana haidar,Allah ya bamu zaman lfy"
Rungumeshi haidar yayi yana masa godiya.
Acan bangaren amarya nana kuwa sanda ta samu labarin wanda