ta aura kuka ta rushe dashi,gaba daya duniyar juya mata takeyi, ta rasa ina zata sa rayuwarta.
Anyi rarrashin duniya tai shuru amman taki shuru.
Da yamma aka turo motocin daukar amarya, dambe sosai aka sha da nana inda taki yarda adauketan.
Haidar na zaune shida fahad yana kara rarrashin shi,wayarshi tai kara.
Dauka haidar yayi,inda wani abokinshi usman ya shaida mishi abinda nana tayi.
Sosai yaji tausayinta amman dole ya tilasta mata.
Duban fahad yayi yana murmushi dan beso yayanshi yasan abinda nanar tayi.
Mikewa yayi da sauri yace
"Yaya prince ina zuwa"
Be jira amsar shi ba yadauki key din motar fahad ya fice.
Koda ya isa nanar nanan ta kame kan bazata ba.
Haidar da sallamarshi yashiga dakin.
Nana da gudu tayo gurinshi tana kuka tace.
"Yaya haidar kajisu ko,wai gidan yayanka zan tare shi na aura,don Allah kace su dena"
Wasu hawayene masu dumi ke kokarin fito masa ya maidasu.
Hannu ya mika yaja hannunta,ba musu ta bishi.
Motar daya zo aciki yasakata,yashiga yaja suka fice daga gidan.
Nasarawa Gra ya karasa da ita,jerin gwanon wasu gidaje masu kyau da tsari yabi da ita.
Kofar wani rantsatstsen gida yayi hon,megadi ya bude ya shige.
Suna shiga yayi parking ya fito ya kamo hannunta,suka shiga cikin gidan.
Sosai gidan ya hadu,ta koina,falo yamata gurin zama.
Bayan ta zauna yanadaga tsaye ya juya mata baya,yace cikin kausasshiyar murya.
"Nana khadija,kinsha fadamin kina sona kuma zakimin biyayya iya ranki,yau gaki a dakin dan uwana bani ba,dede da rana daya kika bari dan uwana yasan bakyason aurenshi dole nai miki Allah ya isa ban yafe ba,kidauki fahad amatsayin haidar,kisa aranki haidar be taba sonki ba"
Yana kaiwa nan yasa kai ya fice daga cikin gidan.
Kuka nana ta rushe dashi ta kife agurin se yanzu ta fahimci ashe gidan aurenta yakawota dataki zuwa.
Haidar kirkinshi dabanne,taya zata rayu babu shi,gashi yamata baki kan in ta ki nunawa dan uwansa so be yafe mata ba,
Dan uwan dako kammanninsa bata saniba se suna,wannan wacce irin rayuwace.
Tasake kifewa agurin tana kuka.
Shiko haidar dakyar ya iya karasawa gida sabida zafin da kirjinshi yakeyi.
Dakin fahad ya shiga yasameshi inda ya barshi.
Murmushi ya kakaro yasami guri ya zauna yana dariya yace.
"Naje ankai amaryane yaya prince,kaima ka tashi akaika sabida ita kadaice agidan"
Shuru fahad yayi yana kallon haidar din tausayin kanin nashi ya ratsa zuciyarshi.
Ajiyar zuciya yayi yace.
"A bari zuwa anjima mana,yanzu yayi wuri"
"Yaya,inda ace nine na auri nana,to ina me tabbatar maka sena rigata zuwa gidan dan kar akawota tai zaman jirana,yaya nana amana na baka,dede da rana daya ka bari nana ta fahimci cusa maka ita nayi ba sonta kakeyi ba,Allah ya isa ban yafe ba"
Yana kaiwa nan ya mike yanufi kofar fita daga dakin.
Yana kaiwa bakin kofar ta tsaya batare daya juyo va yace.
"Ina jiranka a motarka"
Yasa kai ya karasa ficewa daga dakin.
Fahad gaba daya haidar ya daureshi da jijiyoyin jikinshi,ya rasa gano mafita a lamarin.
Mikewa yayi ya dauki wayarshi yabi bayan dan uwan nashi zuciyarshi na bugawa,dan shi ko kamannin nanar ma be saniba.
A mota yasamu haidar yana jirashi,shiga yayi,haidar yaja suka fice daga gidan.
Haidar se tsokanarshi yake shiko yayi zugum kamar mejin kashi,har suka karaso gidan fahad kala bece ba.
Sosai tsarin gidan yayiwa fahad kyau,dole shima ya ginawa haidar wanda yafi wannan dan shi ya gina kayanshi da kanshi.
A bakin get haidar yayi parking alamun baze shiga ba,
Jiki asanyaye fahad yabude motar ya fice,hannunshi rike da ledar kaji da madara da haidar ya bashi,yana fita haidar yay kwana da motar yay masa hon ya wuce da mahaukacin gudu.
Tura kofar gidan yayi ya shiga,dan tuni me gadi ya bude masa kofar daga ciki.
Ahankali yake takawa,har ya isa bakin kofar falon,murdawa yayi yaji ta abude,dan haka ya tura kofar bakinshi dauke da sallama.
Nana nanan kwance akasa tana ta kukanta mara sauti,jin muryarshi yasa tai dif,dan seda gabanta ya fadi sosai dajin muryar tashi.
Ta amshi nasihar haidar dan haka zatai ayki da ita,zata nunawa mijinta so da kulawa.
Kan kujera ya zauna,yana karewa dakin kallo,ba laifi ya tsaru.
Tabbas ya amshi amanar haidar dan haka ya kauda komai ze rike nana fin yadda haidar yake fata.
Da yayi niyyar yay banza da ita to amman amanace aka bashi.
Hannu ya mika,ya dagota gaba dayanta,ya zaunar da ita kan kujera,ga mamakinshi a ido kamar zatai nauyi amman kuma ahannu yaji bata dashi.
Nana ko tsorone ya dabaybayeta gaba daya ta kara sunne fuskarta cikin lullubin dake jikinta.
Nana maganganun haidar ne ke mata yawo akunne,tabbas in haidar ne kusa da ita yanzu kanta zata dora kan kafadarshi dan ya rarrasheta.
Tuna hakan keda wiya ta kwantar da kanta gefen kafadar fahad dake zaune ya kasa magana.
Jin ta dora kanta kan kafadarshi ne yasa yasamu kwarin guiwa,
Hannu yasa ya daga kanta daga kafadarshi yasa hannu yacire mayafin data rufe fuskar dashi.
Jin anbude mata fuska yasa ta bude idonta da sauri.
Dukkansu alokaci guda seda sukayiwa Allah tasbihi abisa kyautata surarsu da yayi.
Kurawa juna ido sukai bame shirin cirewa acikinsu,nanace kunya ta kamata tai kasa da kanta.
Se alokacin tunanin fahad ya dawo,ahankali yasa hannu ya dago habarta,yace yana murmushi.
"Waya ce miki amarya na kuka yanzu,kode ni dinne bakyason zama dashi?"
Murmushi tayi ta sunne kanta.
Sosai ta saci zuciyarshi da salon nata.lalle haidar yayi gaskiya,nana mace ce.
Hannunta ya rike,yana duba jan lallen da aka mata,yace.
"Kinyi kyau sosai,wannan lallen ina son inci gaba da ganinshi"
Ita gaba daya nauyinshi takeji dan haka ta kasa sakewa.
Ledar daya shigo dashi ya mika mata yace ga abincinku amare.
Dukawa tayi har kasa tasa hannu biyu ta ansa,ta nufi hanyar kitchen,dan kitchen din me glass ne so ana hangoshi.
Juyo naman tayi a plate mekyau data dauraye,sannan ta dakko kofuna,ta dauko farantin kajin ta dawo gurinshi cikin takunta me daukar hankali.
Duk abinda takeyi yana kallonta,take ya fahimci tana da tsabta,inda watace haka zata juye kazar kan plate din batare data wanke ba,aganinta ay sabone.
Tana zuwa gabanshi ta duka ta ajiye,ta koma ta dauko musu gurin wanke hannu da ruwa ta dawo ta ajiye.ta zame gefen kafarshi ta zauna.
Sakkowa kasan shima yayi,yana mata murmushi yace.
"Sannu amaryata Allah yamiki albarka"
Akunyace nana ta amsa da amin.
Wanke hannu yayi sannan ya janyota jikinshi ya shiga bata naman da madarar,seda ya tabbatar ta koshi sannan ya kyaleta,yaci nashi shima.
Yana gamawa ya wanke hannu,nana ta kwashe kayan ta kai kitchen ta dawo.
Hannunta ya rike,suka fara laluben hanyar dakunan gidan.
Sama suka haura,wani madaidaicin falon suka tarar sannan dakuna guda uku.
Yana rike da hannunta suka gama zaga gidan,inda ya zaba mata dakin dayafi kyau,amatsayin nata.
Murmushi tayi ta dukar dakai tace.
"Wannan shi yafi cancanta da zama naka,kasancewarka miji,miji ko abune me girman daraja,"
Kureta da ido yayi sosai kalamanta sukai masa dadi.
"To nagode amaryata,na amsa sede ba ni kadaiba dukanmu namune,damu da yayanmu"ya karasa mgnr yana latsa cikinta.
Kamar wacce aka tsikara,ta fada jikinshi cikin jin kunya.
Daukarta yayi cak suka shiga dakin ya maida kofar ya rufe.
Kan gado ya ajiyeta,sannan,ya wucs toilet,
Brush yayo yayi wanka ya dauro alwala ya fito.daure da towel ajikinshi.
Agigice nana ta kife kanta kan gadon,dan bata tsammaci ganinshi ahaka ba.
Murmushi yayi ya wuce,gurin wayarshi.
Haidar ya kira.
Daidai lokacin haidar na kwance agadon asibiti,
Sabida daya kawo fahad dakyar ya isa gida.
Koda yaje gida bangaren mahaifinshi yayi,inda acan ya yanke jiki ya fadi,
Mahaifinshi dakanshi ya daukeshi da wasu dogaranshi suka nufi asibiti dashi.
Sin dan jima da kaishi kan asamu ya farka.
Sede dakyar yake numfashi,inda likitocin suka bada tabbacin ciwon zuciya ke barazanar kamashi.
Yana kwancen ne mahaifinshi namishi nasiha kan muhimmancin yadda da kaddara wayarshi tai kara.
Mahaifinshi ne ya daga wayar,dakyar yake magana.
"Haba yaya ina bacci ka tasheni me kakeso?"cewar hydar dakyar.
Fahad dagacan bangaren yace.
"Katashi ka kawoni gida batare da kayana ba,yanzu seka fadamin inda zan sami kayan sawa"
Dakyar ya bashi amsa da cewa.
"Ka duba kaf wadrof din gidan cike suke da kaya,aciki bazaka rasa ba,ni na kwanta"ya kashe wayar,wasu hawaye nabin fuskarshi.
Sosai mahaifinshi ke tausayinshi.
Dan haka dole ya fitar dashi waje ta yadda ze manta da duk damuwarshi.
Shiko fahad yana gama wayar yashiga neman kayan.
Ilai ko yana bude wadrof din yasamu kayan sawa aciki.
Doguwar riga yasaka,sannan ya waiga ga nana dake duke tunda ya fito.
Cike da kulawa yace.
"Je kiyo wanka kiyo alwala kizo muyi sallah"
Jiki asanyaye ta mike ta nufi hanyar toilet din,zata shiga tajiyo muryarshi yana fadin.
"Karki sake ki fito da kayan jikinki"
Da sauri ta waigo tana kallonshi,murmushi yay mata,da sauri ta shige toilet din.
Muje zuwa
Surbajo for life.[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:πππππππ
*DAN KARUWA*
πππππππ
*writen by zahra surbajo*
*page 8*
Jiki asanyaye tayi wankan tayi brush ta dauro alwala.
Towel ta dauro daurin kirji,da kadan ya rufe mazaunanta,se wani data yafo akai.
Tsayawa tayi bakin kofar ta kasa fitowa,tunaninta taya zata fita a haka,bayan tasan fahad na dakin.
Rasa abin yi tayi kawai ta bude kofar ta fito,
Kanta akasa ta karasa bakin gado ta zauna.
Fahad wanda tunda ta fito yake kallonta,murmushi yayi ya mika mata doguwar riga da hijab yace.
"Saka miyi sallah bacci nakeji"
Daukar rigar tayi ta zira sannan ta zare tawul din jikinta,tasa hijab din,ta mike tabi bayanshi.
Yajasu sallah rakaa biyu,ya jima yana adduoi,kamin daga bisani ya shafa ya dafa kanta yayi adduoi,atakaice yamata tambaya gameda addininta,kuma ba laifi ta bashi amsa .
Mikewa yayi ya cire doguwar rigar jikinshi,ya fada kan gado.
Nana mikewa tayi amman ta rasa abunyi,dan haka tsayawa tayi tana wasa da hannunta
Fahad binta yayi da ido,ganin ta tsaya atsaye kamar yar sanda.
Murmushi yayi,ya mika mata hannu daga kwancen da yake yace.
"To taho na miki iso,tunda jira kike nayi"
A hankali ta taka ta isa gurin hannun nashi tasa nata aciki.
Janta yayi ta fada jikinshi,ya mirginata ta koma kasanshi rabin jikinshi na kanta,
Hannu yasa ya zare hijab din jikinta,sannan ya fara mgn ahankali,yana yamutsa gashin kanta.
"Kisaki jiki dani nana,bazan taba cutar dake ba,haidar dan uwanane,yana sonki nasani,ya bani ke ne dan yana da tabbacin nagarta ta,ada na daukeki amatsayin amanar soyayyar dan uwana,amman tunda na dora idona akanki naji na kamu da sonki me tsanani azuciyata,bansaniba nana ko kema kina da wani abu game dani,uhm?"ya dan matsa kafadunta,gamida kwantar da kanshi gefen kafadarta.
Cikin sarkewar murya nana tace.
"Inason haidar matuka,sede yanzu barin sonshi azuciyata haramunne,sanin hakan ne yasa,na fara koyawa zuciyata son mijin da Allah ya zabamin,"ta karasa mgnr cikin hawaye.
Rungumeta yayi dakyau jikinshi ya dora bakinshi kan nata,
Ahankali yake kissing dinta cikin salon daukar hankalinta.
A hankali yayi nasarar cire doguwar rigar jikinta,
Wasa yashigayi da duk wata gaba ta jikinta.
A hankali ya fara karanta adduar saduwa da iyali,ya cilla kwallonsa araga.
Ihu nana tasaki daga bisani ta fashe da kuka me tsuma zuciya.
Rokonshi take tana dukan bayanashi tana kuka akan ya kyaleta amman ina,wanda yayi nisa bayajin kira.
Seda yasamu gamsuwa sosai da ita sannan ya kyaleta,ya mirgine gefe.
Kuka nana takeyi dan ita kadai tasan azabar datasha.
Hannu ya mika ya lalubota ya janyota jikinshi yana shafa bayanta,alamun rarrashi.
Nana ko se kuka take,ahankali yadunga rada mata kalamai masu dadi akunne,da godiya bisa zumar data shayar dashi me wuyar mancewa.
Wanka ya dauketa suka shiga tare,nana se kara narkewa take yana rarrashinta.
Dakyar ta bari ya taimaka mata tai wanka suka fito.
Kan gadon suka koma bayan ya sauya musu zanin gado.
Ajikinshi ya kwanta da ita yana shafa bayanta,har bacci yayi awon gaba dasu.
Basu farka ba seda gari ya waye,
Fahad ne ya fara farkawa,sosai yayi mamakin makarar da sukayi,dan shida da kwata ya tashi.
Mikewa zaune yayi bayan ya kwantar da nana ahankali akan gadon.
Toilet ya shiga ya dauro alwala yayi sallah sannan ya zo ya tashi nana.
Farkawa tayi ahankali ta bude idanuwanta da suka kumbura sabida kukan datasha jiya.
Koda takai dubanta fuskarshi ba ita yake kalloba,bin setin inda yake kallo tayi da ido itama.
Kan boobs dinta idonta ya sauka,wanda babu riga dama ajikinta,gashi ta yaye bargon gurin tashi a bacci.
Wata yar kara tasaki ta cukuikuyi bargon da hanzari zata rufe jikinta.
Rikewa yayi ya hanata aywatar da nufin nata.
Kuka tasa mishi na shagwaba kan ya kyaleta ta rufe jikinta amman yaki.
Seda ya gama kallon boobs din dan kanshi ya dagata zaune,sannan yafice daga dakin yana dariya.
Rasa abunyi nana tayi,ta zauna turus tana mamakin lamarin na fahad.
Mikewa tayi ta fada toilet tai wanka sannan ta sake gasa kasanta dakyau dan har yanxu zafi yake mata.
Alwala ta dauro ta fito.
Wadrop ta nufa ko zata sami kayan sawa.
Tana budewa ko taga kusan rabin kayan ciki na matane kuma english wears.
Wata doguwar riga ta zabo me hannun siriri,baka,fant da bra ta dauko ta zira.sannan tasaka rigar.
Sosai rigar tai mata kyau,dan ta bayyana suffarta dakyau aciki.
Hijab tasaka tai sallah,sannan ta tsaya gaban madubi tayi light make-up,
Sosai tayi kyau abunta.fesa turaruka tayi masu dadin kamshi sannan ta fito daga dakin bayan ta gyara gadon,yayi kamar baa kwanta akaiba.
Falon kasa ta sauka,cikin tafiyar daukar hankali.
Zaune fahad yake,a falon yayi wanka shima ya shirya cikin kananan kaya sosai yayi kyau.
Wayace akunnenshi alamun waya yake me muhimmanci.
Hannu ya mika mata alamun ta karaso gurinshi.
A kunyace ta karasa ta zauna kan cinyarshi,se alokacin taji dawa yake wayar.
Haidar ne.
Fahad taji yana fadin.
"Haba haidar karka tafi bamuyi sallama ba,"
Daga gefen hydar wanda ke kwance agadon asibiti yace cikin dauriya.
"Yaya prince hakuri zakayi,tafiyar ta gaggawace,nan da minta talatin zan wuce lagos,tacan zan wuce,ba jimawa zanyiba ay"
Hakade sukai ta ja in ja inda daga karshe dole fahad ya kyale hydar yayi tafiya zuwa india kamar yadda yace.
Yana kashe wayar ya rungumota jikinshi,yana shinshinata yace.
"Baby na kinyi kyau sosai,ya jikinki?"
Cusa kanta tayi kirjinshi tana murmushi.
Haka yayta janta da hira har aka kawo musu abinci suka ci,
Hydar ko tuni antafi lagos dashi,anjima ze wuce india neman magani.
Muje zuwa.
Surbajo for life[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:πππππππ
*DAN KARUWA*
πππππππ
*writen by zahra surbajo*
*9*
Hydar andaga dashi zuwa kasar india neman lfy.
Amman fahad beda labari gameda rashin lafiyar.
Zaman lfy da so da kaunar juna suke shida nana.
Duk abinda nana keso shi yake mata,sosai nana ta saki jiki dashi.
Anashi bangaren hydar yasamu sauki sosai,amman yana bukatar yadan huta kan ya dawo.
Me martaba bayajin dadi sosai,yau lfy gobe babu,hankali jamaa ya tashi sosai.
Yayinda hajiya babba,nata yafi na kowa tashi dan gani take yana mutuwa,fahad ze hau karagar mulki.
Ko kadan bata kaunar nana tunda ta ganta taji ta tsaneta,shiyasa tasha alwashi masu muni akanta da mijinnata.
Nana baiwar Allah ta dage da faran tawa kowa dan yarinyace me biyayya.
Hydar hankalinshi a kwance yake acan india,tuni ya mance da soyayya nana ya tungumi kaddara.
Yau nana tun safe ta tashi da zazzabi aikinta. Dan haka koda fahad ya matso yin kafi shayiπ tasa mishi kuka.
Rudewa yayi ya janyota jikinshi cike da kulawa yake tambayarta meke faruwa.
Jin jikinta da zafi ne yasa ya fahimci akwai zazzabi jikinta.
Lallabata yayi ya shiryata,suka tafi asibiti badan ranta naso ba.
Koda suka isa asibitin, basu sha wuya ba suka ga likita.
Bayan gwaje gwaje,likita ya basu tabbacin tana da shigar ciki na wata biyu.
Kunyace ta kama nana tai kasa dakai,shiko fahad godiya yay tayiwa Allah bisa niimar da yayi masa.
Ko a mota haka tai tajin kunyarshi,shiko se tsokanarta yakeyi har suka isa gida.
Rayuwa tayiwa fahad da nana dadi inkaga yadda suke renon cikin abun dole ya burgeka .
Fahad har gida yaje ya sanar da mahaifiyarsa batun cikin,
Sosai tai murna gamida fatan alkhairi ga nana da abinda ke cikinta.
Hydar tuni ya dawo nigeria,yanzu ma ana shirin bikinshi ne da wata budurwarshi zainab da suka hadu acan india.
Sanda ya samu labarin nana nada ciki sosai ya tayasu murna.
Inda ya shiga kasuwa ya ciko akwatuna da kayan baby kala kala.
Kai kace shi zaayiwa haihuwar sabida murnar da ya nuna,fahad har mamaki yakeyi.
Cikin nana nada wata biyar,mahaifiyar su fahad ta kwanta rashin lfy.
Hankalinsu in yayi dubu ya tashi,gashi ciwon nata da zafi yazo mata,dan gaba daya ko gane mutane batayi,hawan jininta ya hau sosai.
Me martaba shima jikinshi ba dadi amman dole tasa ya yi ta maza ya dunga duba matarshi,
Ganin ciwon ba sauki yasa fahad yimata duk shirin daya dace domin afita da ita waje.
Ana e gobe zaa fitar da ita,tace ga garinku,rai yayi halinsa.
Fadin tashin hankalin da suka shiga baze faduba,wanda sanadin jin mutuwarta me martaba ya yanke jiki ya fadi,daga haka yasamu ciwon barin jiki.
Nana ma ta firgita da mutuwar sirikar tata me matukar kaunarta.
Haka akai mata wanka aka sallaceta aka kaita gidanta na gaskiya.
Bayan rasuwar mahaifiyarsu,hankalinsu kan mahaifinsu ya koma,
India suka fita dashi,inda hydar da kaninshi ne agurinshi suna jinyarshi,se hajiya babba wacce ganin ido yasa ta bisu.
Watannin sarki biyu a india yasamu sauki suka dawo nigeria.
Sede dukansu ransu ba dadi rashin mahaifiyarsu.
.addua sukai taimata,dan ita tafi bukata.
Hajiya babba bayan sun dawo cigaba tayi da tsafe tsafenta wajen son ganin ta shiga tsakanin haidar da fahad.
Hakan yasa tai ta asirin da ta janyo fahad jikinta,suka fara shiri
Duk yadda hydar yaso nuna masa illar ta baya yarda karshe da fada suke rabuwa.
Kullum hajiya cikin kai sukar hydar take ga fahad,wanda tun fahad din be yarda har yazo ya fara yardar.
Har tana cemishi yasa ido tsakaninshi da nana,ita tana zargin wani abu.
Cikin nana yakai wata tara ko yaushe zaman jiran haihuwa akeyi,iyayenta sun so su tafi da ita gida amman fafur fahad yaki yarda,wanda dole suka hakura.
Yau tun asuba nana kejin bayanta na ciwo tana daurewa.
Dakyar taiya shan tea.
Fahad dake lura da ita rukota yayi yace cikin tausayawa.
"Nana ta lafiya kuwa,kode abun yazo ne"
Murmushi tayi na karfin hali tace.
"Inda sabo ay na saba da irin ya wash wash dinnan"
"To Allah ya saukeki lfy baby na,bari naje training nadawo,bazan jima ba"kiss yay mata akumatu ya fice.
Bayan fitar shi,ba jimawa ciwon ya turnuke,nana,tun tana daurewa har ta fara kuka.
Acan kuma cikin gida me martaba keson ganin fahad ya kira wayarshi akashe,hakan yasa ya kira hydar ya shaida mishi yaje ya kira mishi shi agidanshi.
Da hanzari hydar ya tafi ayken na mahaifinshi.
Sanda ya isa gidan sallama yay tayi akofar falon amman ba kowa daya amsa,
Da har ya juya ze tafi se kuma tadawo yataba kodar yajita a bude.
Se ya tura ya shiga gidan.
Falon ba kowa haka yay ta sallama amman shuru.
Can yadunga jiyo kukan nana daga falon sama,
Da gudu ya haura saman,akwance ya ganta,akasa zanin jikinta ma ya kwance sabida azaba,daga rigar jikinta se pant.
Jini ne ke bin jikinta,nana na ganinshi ta fara miko mishi hannu tana fadin.
"Yaya hydar kataimakeni,zan mutu"
Hydar agigice yayi kanta,be jira komai ba,ya kinkimeta ita da cikin yayo kasa da ita.
Suna sakkowa daga saman Fahad da hajiya babba suna shigowa,sabida fahad daya fita training din yana gamawa yaje yacewa hajiya su zo taga jikin nana dan yana tunanin ko haihuwace,to ya daukota kenan.
Yazo ta tarar hydar dauke da nanarsa ahannu,ya fito da ita daga dakin baccinsu.
Me hakan ke nufi.
Waya ba hydar damar hawa saman gidanshi.?
Muje zuwa
Surbajo for life.[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:πππππππ
*DAN KARUWA*
πππππππ
*writen by zahra surbajo*
*Duk wanda yasan ni yasan books dina,yasan zeyi wuya in gama batare da na jinjina ga wainnan jaruman zaratan matan ba,zeyi wuya sosai,ina sonsu har cikin raina,ina musu fatan alkhairi akoda yaushe.*
*Maman Gidado,Fatima Abubakar Radda,inna Ibrahim kime,Aunty jamila tayakasai,Aunty Halima,Aunty halilos,Billy shantali(hankarataπ€),Bilshop,Hassana da hussaina muhd lawal kano,Aunty Rumaisa lagos,etc*
*masu bin sabon salo kuyi hkr wasu cikinkune suka dan bata raina ta hanyar yada book din groups amman yau zan muku posting da daddare,ayi hakuri*
*page 10*
Hydar ko kallon inda suke beyi ba,
Da gudunshi yayi hanyar ficewa da ita.
Se alokacin ya lura dasu,cikin kidimewa yace.
"Yaya prince yi sauri mukaita asibiti,kaga mawiyacin halin da take ciki"be gama rufe baki ba Fahad ya daukeshi da wani wawan mari.
Agigice Hydar yake duban dan uwan nasa baki bude yace.
"Pls yaya kome nayi maka save her life first"
"Yimin shuru,munafiki,dama hajiya tajima tana fadamin kana neman matata bantaba amincewa ba se yau da nagani da idona,wato sickler din da aka guji ka haifa shine ni kakeso kasa ahaifamin amatsayin nawa ko,wlh hydar nayi danasanin hada jini dakai"fahad yayi maganar yana huci.
Hydar kanshi ke sarawa,bakinshi yayi nauyi maganar tamasa nauyi,rasa abun cewa yayi kawai se yasa kai ya fice dauke da ita ahannunshi,idonshi na zubar da kwalla.
Kai tsaye asibiti ya nufa da ita,yana zuwa kan ya fita da ita ya tube doguwar rigar shaddar dake jikinshi ya zira mata,sannan ya fito da ita zuwa cikin asibitin,inda likitoci suka rufu akanta.
Hydar kuka kawai yakeyi,kamar wani karamin yaro,likitocin sun dauka halin da matarshi ke ciki kesashi kuka,nanko bakin ciki kalamun dan uwansa ke sosa zuciyarsa.
Yana nan zaune yana jiran likitocin su fito,su hajiya da Fahad suka karaso gurin.
Fahad kan Hydar yaje yaci gaba da zazzaga masa masifa shide ya dukar da kansa kasa yana ta kuka,yana adduar Allah ya sauki nana lafiya.
Ana haka likitan ya fito da murmushi afuskarsa.gurin hydar ya nufa da faraa ya mika masa hannu yace.
"Ranka ya dade ina tayaka murna,matarka ta haifi da namiji,dukansu suna cikin koshin lfy,zuwa anjima kadan zaa baku damar ganinsu"cewar likitan dan shi atunaninsa hydar shine mijin nanar.
Godiya hydar yayima likitan.
Hydar yayi murna da haihuwar sosai,yayinda fahad ko alamar hakan babu atattare dashi.
Awa guda bayan haihuwar aka basu damar shiga dakin.
Nana na kwance tana ganinsu ta fara murmushi,dan duk bidirin da akayi ita batasaniba.
Hydar gurin nanar ya nufa,da faraarshi yace.
"Sannu nana,ya jikin naki,"
Cikin faraa tace.
"Jiki da sauki hydar"
Shiko fahad da hajiya kan gadon jaririn suka nufa,suna zuwa hajiya ta dago dan dake ta faman tsotsan hannu,ta bude fuskar yaron.
Daga hajiya har fahad seda suka firgita da ganin kamannin yaron.
Dan in ka kalleshi zaka dauka hydar ne yana yaro,sabida tsabar kamar da yake da hydar.
Salati hajiya ta farayi tana sallallami,gamida rushewa da kuka,tace.
"Kaico hydar kaci amanar dan uwanka,ka tozarta sunan gidanku,yanzu wannan abun kunya dame yayi kama fisabilillahi"ta karasa maganar cikin kukan munafurci.
Fahad afusace,ya fisgi dan yanufi gurin hydar da nana,wacce kanta gaba daya ya kulle,ganin yadda hydar ya dukar da kai yana kuka.
Yana zuwa ya cilla dan gurinsu da sauri hydar ya tara hannu ta cafke dan ya rungumeshi jikinshi,yaron ya riga ya firgita dan haka kuka ya shiga tsalawa.
Nana a hassale ta yunkuro zata rufeshi da masifa,hydar ya dakatar da ita.
Murmushi fahad yayi yace.
"Ay da ka barta tamin,ay dama ba kunyace gareku ba,dan duk me kunya bazeyi zina da matar dan uwansa ba,itama bazatayi da kanin mijinta ba,to kisani nana,wannan dan ba nawa bane,ki nemi meshi tun kan dare be miki ba,koda wasa karki sake ki jinginashi dani,kuma nasakeki saki daya,hakkina dakuka ci keda hydar Allah ya isa ban yafe muku ba,"yana kaiwa nan ya juya ya fice yana kuka,dan dukansu yana sonsu.
Hajiya ma cewa tayi.
"Karuwar banza da wofi,Allah ya tona asirinki to ba agidanmu ba,bakar munafuka,kai kuma yanxu base anjimaba zakaga hukuncin da me martaba ze zartar maka"tana kaiwa nan ta fice daga dakin ta nufi gurin fahad inda tasameshi yana yawa da mahaifin nana yana fada masa abinda nana tai masa,yadda yake fadin zaka dauka akan idonsa komai ya faru.
Mahaifin nana mutum ne me matukar zafi,hankalinshi in yayi dubu ya tashi dan haka mahaifiyarta yashaidawa kuma yabata tabbacin matukar nana ta waiwayeshi seyayi ajalinta..
Yana gama wayar hajiya tajashi suka wuce zuwa gurin me martaba.
Itako nana wacce kanta ya fara birkicewa,dafa hannun hydar tayi tace da kyar.
"Hydar don Allah ka gane me suke cewa,akan me suke mgn kuma akan wa,pls wacce nanar fahad ya saka,pls tell me"ta fadi cikin karaji.
Hydar ya kasa mgn,kuka kawai yake yana jijjiga yaron dake kuka.
Riko hannunta yayi tana tirjewa yajata suka fice zuwa mota,dan ya biya komai ba abinda ake binshi.
Mota yasata ta zauna sannan ya mika mata yaron ta rike,yashiga yaja da mahaukacin gudu,ya nufi gurin me martaba da su.
Sede kan yaje hajiya da fahad sun rigashi zuwa,dan har hoton daukar da yayiwa nana seda hajiya ta nunawa sarki,wanda ta dauka batare da sun sani ba.
Hankalin sarki in yayi dubu ya tashi ya rasa meke masa dadi,jin dan dayafi so cikin yayansa irin barnar daya tafka..
Hydar na shigowa dalon me martaba,yajiyo muryar me martaba na masa gargadi.
"Idan har ka kuskura ka sake bari fuskarmu ta hadu nidakai,Ban yafe maka ba hydar,kafice daga rayuwata da duniyata,ni ban haifi mazinaci ba,kaje duniyace hakkinmu se ya hanaka kwanciyar hankali,"me martaba ya karasa maganar yana share hawaye.
Hydar jiki asanyaye yayi baya,bece komai ba,yaja hannun nana suka fice.
Amota ya natsar da nana ya fada mata duk abinda ya faru.
Se alokacin nana taji dan sauki a zuciyarta ganin sharrine aka musu wanda tasan duk daren dadewa Allah ze tona asiri.
Hydar gidan su ya nufa da ita,dan dama gidan ay nashine yabarwa fahad.
Suna shiga gidan wayar nana dake falo ta fara ruri,koda ta isa gurin domin dauka numver mahaifinta ta gani,dan haka da sauri ta dauka.
Muryarshi ta katse mata hanzari.
"Naji alfashar da kika aykata,kanki kikawa,ba niba sede kisani,na yafeki niba ubanki bane,dede da rana daya kika kuskura kika tunkaro gidana ko rimin kuru,nine ajalinki,ko kuma ni na kashe kaina,ina danasanin haihuwarki"
Yana kaiwa nan ya kashe wayar.
Wayyo Allah.
Muje zuwa
Na raina comments
Surbajo for life.[9/26, 6:08 PM]