miyasa za ka yi min wulaƙanci irin wannan?
if you really want to break up with me, you should not follow this way Abba. Sai da ta fesar da wani kalan iska mai zafi daga bakinta muryarta yana rawa ta cigaba da faɗin "I know all this time I was the only one who loved you and you didn't love me ba ka sona Abba ina yaudara kaina ne kawai.
Ta ƙarasa magana hawaye yana bin kumatunta Abba bai ce komai ba sai komawa ya yi jikin kujera ya jinginar da bayansa tare da lumshe idanuwansa yana ji yadda kansa ke wani irin sara mishi kwata-kwata bai san abunda take magana akai ba kuma ko za su kai gobe ba zai iya buɗe bakinsa ya tambaye ta ba. Da ta gaji da masifarta ta nemi kujera ta zauna sun ɗauki tsawon lokaci ba wanda ya yi magana Rumaisa tasan waye AB ciki da wajensa, shiyasa ta saukar da fushinta cikin sanyi murya kaman za ta yi kuka ta ce
"Please Abba, talk to me, why did you humiliate me? Na je na ɓata lokaci aka yi min kitso da body waxing don dai kawai na burgeka ka soni ni kaɗai amma ka rasa kalma da za ka jefe ni da ita sai wannan.
Ta nuna masa wayarta duk da azababben ciwon kan da yake ji hakan bai hana shi bi text message ɗin ya karata take ya gane ko aiki waye.
"Idan ma baka so ina ƙara gashi sai ka faɗa min ta siga mai daɗi sai na daina duk abunda ba ka so Abba duk son da nake masa wallahi zan daina.
Rumaisa ta faɗa tana wani langwaɓar da kai.
"Rumaisa ki tafi gida za mu yi waya,
Ya faɗa kamar mai ciwon haƙora.
"Abb...
"Please go!!
Yai sauri tarar numfashinta ba tare da ta sake magana ba ta tashi ta nufi ƙofar fita tana sharar hawaye tana fita ya sauke naunnayar numfashi.
*MASARAUTAR KUDU*
Alh Aliyu na uku yana gani Hajiya Safiya ta fita ya miƙe ya nufi master bedroom ɗinsa kai tsaye wardrobe ɗinsa ya nufa bangaren da ya ajiye safe ɗinsa ya saka lambobin sirri (code) ya buɗe safe ɗin yana ɗauke da muhimman takardun sa wasu hotuna ya ɗauko ya nufi gefen gadonsa ya zauna hoton farko ya fara ƙurawa idanu na wata kyakkyawar baturiya tana tsaye jikin wata bishiya wacce samanta ke ɗauke da furanni ja da fari tana sanye ne da half blouse pattern gown red in colour rigar da kaɗan ta wuce gwiwoyinta, gashin kanta ya sauka har gadon bayanta, mace ce kyakkyawar gaske wacce kallo ɗaya za ka yi mata ka tabbatar da kyawon nata yakai maƙura. Ya ɓata lokaci sosai yana kallonta yana sauke numfashi a jere kafin ya aje hoton gefensa, idanuwansa suka sauka akan wanda suke tare manne da juna akan gadon asibiti da kyakkyawan Baby sun saka shi tsakiyar hannayensu tare da rungume shi, Baby yana naɗe cikin farin baby shawl fuskarsa ce kaɗai a buɗe. Alh Aliyu bai ankara ba ya ji wani abu mai ɗan ɗumi-ɗumi yana bin tattausan kumatunsa, bai damu da sai ya goge su ba ya rungume hoton a ƙirjinsa ya ɗauki lokaci mai tsawo a haka sai da ya ji wayarsa tana ringing kana ya tashi ya mayar da hotunan cikin safe ɗin, sannan ya ɗauki wayarsa dake ta faman ruri.
*ALH BASHIR MANSION*
Misali ƙarfe 4:15pm AB ya baro kamfani duk da yana da tarin muhimman ayyuka da ya dace ace ya kammala su kafin tashinsa sai dai ya zama mishi dole ya bar ayyukan duk da irin muhimmanci su agare shi, saboda yana so ya je ya haɗu da yarinyar da Daddynsa ya nema masa bedroom ɗinsa ya wuce ya cire kayan jikinsa ya ɗaura brown towel ya shiga wanka, bai wani ɓata lokaci a wurin wanka ba ya fito saboda har yanzu yana fama da migraine headache sai ma ji yanzu ya daɗa ƙaruwa fiye da ɗazu da safe. Ya shirya cikin farar shadda tasha aiki da zare blue shiyasa ya saka hula blue da blue color sandal irin wanda ake sakaɗa yatsa sosai takalmin suka yiwa fararen ƙafafuwansa kyau, duk da baya ciki yanayi mai daɗi hakan bai hana masa feshe jikinsa da tsadaddun turarunkansa, dama ƙamshi ya zame masa jiki ma'aɓoci so turare ne. Kai tsaye parking lot ya wuce ya shiga motarsa tuni maigadi ya wangale masa gate koda ya isa gidan Alh Habib Bichi ƙarfe 5:44pm bayan ya yi parking motarsa ya aika maigadi ya sanar wa da Mufeeda zuwansa.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
littafin nan 500 Naira only
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/1/2023, 6:53 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love story
#Gwagwarmaya
#Team tagwaye novels
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels