Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
biyayyar da ya keso nayi masa na zaman aure da yaya AB za ka yarda babu auren yaya AB akaina yanzu Hafeez ka daina shunning din soyayyata ko kwana ɗaya ban yi ba a gidan Ya AB ba kai ɗin nan shaida ne, idan da gaske kana sona mahaifina ya bani nan da sati biyu na fito da miji aure zai min. fashewa da dariya Hafeez ya yi yana buga desk da yatsa yake nuna kansa a fusace yace "Ni kike tunanin zan auri ragin wani ?" kin rainawa kanki wayau Sadiya ba zan ɓoye miki ba ba zan iya aurenki ba koda iyayena za su yarda ke kin san kishina, ma ba zai barni na aureki ba wallahi. wannan karon hawaye ke gudu sosai acikin fuskarta tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugawa ga wani irin zafi -zafi da zuciyarta taji tana yi mata. Ƙofa ya nuna mata yana faɗin "Allah ya sadamu da alkhairi. Sadiya miƙewa tsaye tayi ta nufi ƙofa bata ƙara waiwayen Hafeez Sale ba tana jin yadda yaja wani dogon tsaki adaidaita sahu kawai ta tare ba tare da tayi masa bayanin inda za taje ba. Sosai jikinta ke mugun rawa kalaman Hafeez ta ke ji cikin kunnuwanta haɗe kai tayi da gwiwa ta shiga rera kukan bakin ciki murya dan sahu taji yana bata haƙuri kafin ya tambayeta wacce unguwar zai kaita dakyar ta faɗa masa har ƙofar gida ya sauketa ko canji bata tsaya karɓa ba ta shiga gida, wannan ƙaron Aydah ce kaɗai a parlon zaune akan rug da uniform ajikinta wanda tunda ta dawo bata cire ba shinkafa da miya ce agabanta cikin plate da littafi a hannunta ,jin shigowar mutum cikin parlorn yasa tayi saurin tura Novel ɗin karkashin kujera ,dan kakaf gidansu babu wanda yasan tana karatun hausa novels ita ma wajen yar class ɗinsu take karbowa mai suna Zulaiha Kasim, tun basa bata sha'awa har ita ma ta fara karantawa tasan idan Mami, ta ganta da littafan soyayya a gidanta kasheta za ta yi hakama yaya Abba, mafi yawanci tafi karatunta da dare idan ta shiga ɗaki ta sakawa ƙofarta key, wannan karon ta kasa haƙura da karantawa sai da dare saboda daɗin da labarin yayi mata da kanta ta bai wa Zulaiha kuɗi ta siyomata daga na daya har na 4 kuma wai littafin yafi shekara goma Amma yadda Zulaiha ke zuzuta haɗuwarsa littafin sunansa wai (Tattalin so)har bata so ko na minti ɗaya ta daina karatun sai dai ganin yadda yaya Sadiya ta shigo a firgice kamar bata cikin natsuwarta yasa ta mayar da hankalinta sosai wajen yar uwartata da alamar idanuwa Sadiya a rufe suke ko sanin zaman Aydah ba ta yi a Parlon ba da gudu ta nufi stairs da kallo Kurum Aydah take bin ta har ta bacewa ganinta ɗan taɓe baki Aydah ta yi tana faɗin."duk bake kika jawo wa kanki abunda da ya sameki ba da yanzu kina gidan yaya Abba, hankalinki a kwance ana riritaki ana tattalinki kamar yadda yaya Aliyu na cikin littafin tattalin so yake yiwa zeee ,har hango fuskar Aliyu take kamar yaya Abbanta amma ta nacewa wannan Hafeez ɗin da bata san da me ya fi yaya Abba, dashi ba. Yayanta ya fi Hafeez komai da komai ba ma za a haɗa su ba Jawo novel ɗinta ta yi ta cigaba da karantawa abincin da ta keci har ya yi sanyi ya sandare tana gama cin abinci har ɗaki ta samu Mami ta marairaicewa Mami ,tamkar da gaske tace kanta na ciwo dakyar idan za ta iya zuwa islamiyya za ta je ta sha magani ta kwanta, mami ta bita da addu'ar Allah ya sawwake, tana shiga ɗaki ta sakawa ƙofarta key ta faɗa kan dan kyakkyawan gadonta tayi ruf da ciki ta cigaba da karatun ta... #Love story 2023/2024 #Jeeddah Aliyu #Asmy b Aliyu #Team tagwaye novels #Kurman Allo Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 [11/29/2023, 5:28 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO* (A beautiful Love Story) NA JEEDDAH ALIYU & ASMY B ALIYU #Love story #Gwagwarmaya #Team tagwaye novels 10... *RUBUTUN ƳAN TAGWAYE ZANGO NA BIYU.* *TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA* PAID BOOK #Love Story #Gwagwarmaya #Team Tagwaye novels *MASARAUTAR KUDU* Masarauta ce mai ɗimbin tarihi duk wani jinin sarautar da ya fito daga masarautar za kaga yasha bamban da normal mutane. Jinin masauratar suna da wata irin izza, taƙama, ƙasaita, za ka ga duk wanda ya fito daga wannan masauratar ɗabi'un da halayensa ba kamar na sauran mutane ba, ga su da girman kai da ɗagawa wayayyu ne suna da ilimin boko dana addini kuma gasu da wani irin kyau na ban mamaki da matuƙar wahala ka ga mummuna cikinsu sai dai abinda ba a rasa ba saboda mutum ɗan tara ne bai cika goma ba. Allah ya yi musu arziki sarauta da kuɗi gasu da mulki ga kuma tarin dukiya da Allah subhanahu wata'ala ya albarkace su da ita. A halin yanzu mai martaba sarkin kudu Mahmood Mustapha na uku shi ke mulkar wannan daula shine a matsayin sarkin kudu mahaifinsa Margayi Alhaji Usman Mustapha na uku shine Sarki bayan ya rasu aka naɗa ɗansa Mahmood Mustapha na uku. Sarki Mahmood su shidda mahaifiyarsu ta haifa wacce suke kira da mai babban ɗaki wato ita ce uwargidan sarki Usman, mai martaba sarki Usman ya mutu ya bar mata huɗu da sadaka uku tare da tarin 'ya'ya arba'in da bakwai a halin yanzu talatin da tara ke raye takwas daga ciki sun rasu. Kafin Sarki Usman ya rasu kan zuri'arsa a haɗe yake sai ya rasu ne aka fara samun rabuwar kawunan su wannan kuma ya samu asali ne daga wurin matarsa ta biyu Hajiya Kilishi, a dalili sarautar Sarkin sabon birnin kudu da margayi Sarki Usman ya bai wa Aliyu tun yana da rai kasancewar Aliyu shine ɗansa na shidda a ganinsu bai cancanci wannan sarautar ba tun da akwai na sama dashi. Wannan sarauta da sarki Usman ya ba wa Aliyu ita ce silar haddasa ƙiyayya tsakani yaran mai babban ɗaki da yaran Kilishi. Shi kuma Sarki Usman ya yi hakan ne a dalili fahimtar da ya yi Aliyu baya da ra'ayi sarauta ko kaɗan idan aka ɗora masa nauyi mulkin jama'a dole ya fara saka sarautar aransa. Dama shi Aliyu abarsa da kasuwanci domin kusan dukkan kamfanonin su shi ke kula dasu. Alh Aliyu yana baro bangaren mai babban ɗaki ya wuce gidansa kaitsaye ɓangaren sa ya shiga yana shiga katafaren parlorn sa ya nemi ɗaya daga cikin royal cushion da suka daɗa ƙawata parlornsa ya zauna, ya cire rawani kansa ya ajiye kusa dashi ya tsani rawani sai dai doka ce ga duk wani jini masarautar ya saka naɗi kafin ya shiga faɗa, shiyasa yanzu ma da zai shiga faɗa ya saka ba don haka ba da ba abinda zai haɗa shi da rawani. Hajiya Safiya ce ta turo ƙofa ta shigo cikin parlorn, ta hango mijn nata ya lafe jikin cushion idanunsa rufe tasan ba bacci yake yi ba kawai dai damuwar nan ce da ya ɗorawa kansa tasaka shi cikin irin wannan yanayi. Tambayar duniya nan idan za ka yi masa zai amsa maka ne da ba komai rana da baya ji so magana sai ya yi banza da mutum. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta nemi dab da ƙugunshi ta zauna tana matuƙar son mijinta irin son da fatar baki ba za ta iya faɗarsa ba, sai dai ta misalta. "Abbu! Ta kira shi da sunan da yaransa ke kira shi dashi, dama a wasu lokuta haka take kiransa dashi. Bai matso ba balle ta sa ran ya ji kira da tai masa sake lankwasa muryarta ta yi ta koma kiransa "Abbu! A hankali ya ɗage idonsa guda ya kalleta na 'yan wasu daƙiƙu kafin ya maida idonsa ya rufe, ya yi hakan ne don tasan ba bacci yake ba balle ta dame shi da kira. Sanin hali yafi sani kuma tasan halinsa fiye da yadda tasan yunwa cikinta muddin ba shi yaso yin magana ba duk nacinka dole ka kyaleshi don ba tanka ka zai yi ba. "Abbu har sai zuwa yaushe zan daina gani wannan damuwar akan fuskarka? Dan Allah Abbu ka faɗa min idan ni ce ba ka jin daɗin zama dani ko ina maka wani abu da ba ka so wallahi a shirye nake da na gyara. Shiru ya yi alamar ba tanka mata ba "A matsayina na matarka makusanciyarka ina da damar da zan san damuwarka idan ina da hali taimakawa Abbu sai na taimaka ma idan babu kuma sai na tayaka da addu'a. Ni da kai abu ɗaya ne damuwarka nima tawa ce hakazalika farin cikinka shine nawa matuƙar kana cikin damuwa ba yadda za a yi na kasance cikin walwala. Har ta kai ƙarshen zance ta idanunsa suna a rufe "Safiya ina buƙatar hutawa za ki iya tafiya. Ya yi magana still idanunsa na rufe. "Amma Abb.. "Safiya please. Yai sauri katse mata hanzari a wannan karo ya buɗe idanuwansa suka fara canza launi, jikinta a sanyayye ta miƙe ta baro ɓangaren nasa, ba tun yau ba take ayyana cewa gangar jikinsa ta aura ruhinshi yana wani gun daban. *RUMAISA MADAWAKI* Rumaisa ta fito daga cikin gida jikinta sanye da straight gown na lace pitch in color gaban rigar har zuwa ƙasanta an mata beads work, sosai shigar tai mata kyau hannunta riƙe da purse ɗinta wacce tayi match da heel ɗin ƙafarta ɗayan hannunta ke ɗauke da car key ɗinta. Fitar nan da za ta yi za ta je gyaran gashi da body waxing da take zuwa duk ƙarshen wata yadda take tafiya tamkar wacce bata kashi sai wani yatsine fuska take yi ga idanuwanta ta lulluɓe su da sunglass. Ta shiga motarta tare da yi reverse ta fito da ita daga parking lot kana ta daidai motar ta ja ta zuwa gate wanda tuni maigadi ya buɗe mata. Kai tsaye Aj beauty palace and spa ta nufa dama can ake mata duk wani gyaran jiki, tana shiga wurin ta haɗu da old friend ɗinta Aneesa Baffa wacce suka yi karatun sakandare tare tun daga lokaci basu sake haɗuwa ba sai yau da suka haɗu a Aj beauty palace and spa. Aneesa Baffa kyakkyawar matashiyar budurwa wacce ke ji da naira saboda mahaifinta Alhaji Baffa ya mutu yabar musu tarin dukiya wannan yasa ta fara business ɗinta tana da manya-manyan boutiques na siyar da expensive clothes na mata da maza har ma dana yara Aneesa Baffa she's independent woman wacce ke cin kashin kanta sai dai har yanzu bata yi katari da namiji da take gani ya dace da ita ba duk da tana da farin jini wurin maza. Cike da wayewa ta mata da idanuwansu suka gama buɗewa suka rungume juna ita da Rumaisa daga nan hira ta barke a tsakanin su daga nan suka yi exchange ɗin contact, da yake ita Aneesa har an kammala mata abunda ta zo yi saboda haka suka yi sallama tare da alƙawari kai wa junansu ziyara. *ALH BASHIR MANSION* Sosai Sadiya ke rera kuka kaman ba gobe Allah na tuba ko uwarta da ubanta suka mutu iya kukan da za ta yi kenan, wani kololon abu take ji ya danne mata zuciya saboda tsanani kukan da take yi she can't even breathe sai wani irin sheɗewa take yi tasha baƙar wahala kafin ta samu numfashinta ya daidaita a jikinta, she didn't think Hafeez would break her heart like this ta ɗauki soyayya da yarda ta bashi sai gashi ya barta da dafi a ƙahon zuciya, wani kalan mahaukaci so take mishi shiyasa ta kasa karɓa Ya Abba a matsayin mijinta sai gashi tayi biyu babu ta rasa Ya Abba shi kuma Hafeez Sale ya guje ta. *AYDAH* Hankali kwance take karanta novel ɗinta duk gun da ya yi mata daɗi sai tai wani lumsashe idanu, tana rausayar da kai kiran sallah magarib ya tashe ta ba don ranta ya so ba ta ajiye littafin sai lokaci ta cire uniform ɗin jikinta ta ɗaura light pink towel ɗin ta ta shiga wanka agaggauce ta fito ta zura plain cotton gown mai gajeren hannu tayi sallah bata tashi ba sai tayi sallah isha kana ta fito main parlor, babu kowa sai mai aikinsu da ta hango a dining area tana arranging table, saboda haka ta wuce ɗakin Siyama tana tura ƙofa Siyama was busy with her laptop turo ƙofar ɗakin nata da Aydah tayi yasa ta ɗagowa Aydah ta ƙaraso ta zauna kusa da ita "me kike yi ne yaya Siyam?" "Ina ruwanki da abunda nake yi? Siyama ta faɗa tana mayar da idanuwanta kan laptop ɗin. Sai da Aydah ta galla mata harara a fakaice ta wani turo baki tare da leƙa screen ɗin laptop ɗin ita a dole sai ta ga abunda Siyama take yi cikin sauri Siyama ta janye laptop ɗin tana faɗin "what's wrong with you? "I just want to see what you are doing in the laptop ko haramun ne don na ga abinda kike yi? Wani kallo Siyama ta wulga mata sosai iskanci Aydah ke sauri hasala ta kalli yadda tai mata magana kaman wata sa'anta "Get up and get out of my room before naci ƙarniyarki. Miƙewa Aydah ta yi tana gunguni ƙasa-ƙasa magana ne take mayar mata, rai ɓace Siyama ta kalleta taga sai da take da ɗan mitsitsi bakinta ko ba tambaya ba tasan maganganu banza ne take faɗa mata "Why don't you respect me, Aydah?, I am your sister ina gaba dake you have to respect me. "Haba dallah Yaya Siyam sai faɗa kike kina nanata wa sai kace wasu shekaru kika bani masu yawa. "Iyeee! Aydah yau kuma iskancin naki akaina ya dira? Kallo sama da ƙasa Aydah ta yi mata hakan ya ƙara harzuƙa Siyama ta zabura ta miƙe tsaye da zimmar idan ta kama Aydah sau ta yabawa aya zaƙinta, Aydah tana ganin yadda ta miƙe ɗinan da gaske za ta iya dukanta saboda haka ta juya da gudu ta buɗe ƙofa ta fita, ita ma Siyama da rashin haƙuri ta biyo ta da gudu suka sakko ƙasa dai-dai Sadiya tana fitowa kitchen hannunta riƙe da mug ta haɗo tea, ta gaji da kukanta na rashin dalili ta fito yunwar da ta dinga naniƙar hanjinta yasa ta fitowa babu shiri sai dai ta rasa appetite babu ɗanɗano ko kaɗan a bakinta wani ɗaci-ɗaci ma yake mata shiyasa ta yi deciding ta sha tea. Sai kuma ga waɗannan rigimammun siblings ɗin nata da basa gajiya da rigima, Aydah da ta zo da gudu bata lura da Sadiya ba tai bala'in bangaje ta mug ɗin hannunta ya subuce ya faɗi kan marbles ya tarwatse tea ɗin ya zuba a ƙafarta, duk dai bai da zafi sosai hakan bai hanawa Sadiya tsandara ihu tana kira ƙafarta sai tsalle take Siyama ta nufe ta, tana ƙoƙari kamata Aydah tana gani yadda jikin Sadiya ke motsawa sai kawai abin ya bata dariya ta fashe da dariyar harda su riqa ciki .a fusace su dukka biyu Sadiya, Siyama suka yi kanta ta sake kwasa da gudu ta fice zuwa compound tana dariya abinta, a bayyane ta ce "Cabdijam! Wallahi yaya Sadiya buhun banza ce dallah kalli yadda naman jikinta ke rawa dama za ta ɗauki shawara ta fara rage fat. Ta ƙarashe magana tare da kwatanta yadda Sadiyar ke tsalle sai kawai ta sake sheƙewa da dariya. Motar Ya Abba da ta hango yana shigowa ta nufi wurinsa tana ƙoƙarin haɗiye dariyarta saboda tasan halinsa ba kasafai yake son dariya ba. "Sannu da dawowa Ya Abba! Ta faɗa sa'ili da ya fito briefcase ɗinsa ta karɓa ya sakar mata yana faɗin "Me kike yi a waje Aydah?" "Yaya Sadiya da yaya Siyama ne za su yi min duka shine na gudu waje. Sai da ya ƙare mata kallo kafin ya furta "Hauka suke yi da za su yi miki taron dangi? Ban da mugunta me za su daka anan? Sai dai in kasusuwan ki za su karya. Ya ƙarashe magana yana nuna jikinta cunno baki tayi "A'ah! Ya Abba bangane ba wannan yabo ne ko zagi? Murmushi mai sauti ya yi tare da dungure mata goshi "bansani ba. Ya yi magana tare da nufar flat ɗinsa tayi tsaye tare da bin sa da ido tana kallon yadda yake tafiya cike da izza da ƙasaita a zuciyarta tace "Anya kuwa Ya Abba ɗinan ba daga royal family ya fito ba? OMG! ji tafiya irin na hamshaƙai sarakuna. Tuni AB ya yi gaba yabar ta tsaye tana sambatunta na shirme yana dab da isa entrance ɗin flat ɗinsa ta kwasa da gudu ta cimmasa tana "Ya aka yi yau yaya Abba ka yi saurin dawowa?" Bai bata amsa ba har sai da suka shiga parlornsa ya ce "Ko na koma ne? "Ni na isa na ce ka koma. Ya ajiye wayoyinsa kan centre table yana faɗin "Ki jira ni zan yi wanka. Ya ƙarasa magana gami da karɓar briefcase ɗinsa dake hannunta ya nufi master bedroom ɗinsa "A fito lafiya! Aydah ta faɗa tana mai zaunawa akan cushion. #Love Story 2023/2024 #Jiddah Aliyu #Asmy b Aliyu #Team tagwaye Novels #Kurman Allo Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 [11/30/2023, 1:53 PM] Jiddarh Aliyu 2: *KURMAN ALLO* (A beautiful Love story) NA JEEDDAH ALIYU & ASMY B ALIYU #Love Story #Gwagwarmaya #Team Tagwaye novels 011. Daya daga cikin wayoyinsa ta ɗauka wacce ta kasance ita ce babba iphone 14 pro max, ba ta tasha wahala wajen cire code saboda sunanta ne, yawanci dukka pics ɗin dake ciki nata ne, ta shiga nan ta fita nan sai kace ta bashi ajiya a wayar ne. Text message ya shigo daga habibty, ɗan ƙaramin tsaki taja tare da buɗe text ɗin "Habibi ka buɗe Data na tura maka pics ɗin kitso da aka yi min yau ka gani ko ya yi kyau. "Mtss! Aikin banza tsabar iskanci hatta da kitso tayi sai ta nuna masa. Aydah ta yi magana a bayyane sai kawai ta buɗe Data ɗin jim kaɗan sai ga pics ɗin sun shigo kusan guda biyar wanda har sun buɗe "mtsss! Ta sake jan tsaki har yafi na farko a dalili kitso da aka yiwa Rumaisa na attachment ne irin gana waving ɗinan ƙanana ya sauka har gadon bayanta, tsabar ɗaukar magana irin na Aydah sai kawai ta yi tagging guda daga cikin pics ɗin ta rubuta "Bai yi kyau ba ko kaɗan saboda ba da ainihin gashinki kika yi ba sai da kika haɗa da gashin doki kuma Allah ya la'anci mai ƙara gashi. Sai kawai ta tura mata tana gani text ɗin ya tafi ta kashe Data ɗin ta ci-gaba da sabgar gabanta. AB ya fito sanye da farar jallabiya sai zabga ƙamshi yake ya dubi Aydah ya ce "tashi mu tafi yunwa nake ji tun breakfast ban sake saka komai a cikina ba. Aydah ta tashi da sauri suka nufo flat ɗin Mami koda suka shigo hatta da Mami jiraye take da ita ganinta tare da AB yasa dole suka shafa mata lafiya saboda sun san in har yana wurin ba dakuwa za ta yi ba. Bayan sun kammala ci abinci AB ya wuce parlorn Daddy saboda tun a kamfani Daddy yace yana so su tattauna magana mai muhimmanci. Bayan ya yi sallama Daddy ya amsa masa kana ya ɗan runsuna ya gaida Daddy, ya nemi wurin ya zauna yana faɗin. "Daddy ka ce za mu yi magana. AB ya yi magana yana kallon Daddy wanda hankalinsa ke kan akwatin talabijin yana kallon news. Sai kawai Daddy ya tattaro hankalinsa ya mayar kan AB "Abba dangane da zance aurenka ne nayi magana da Alhaji Habibu Bichi akwai 'yarsa da ta kammala karatun ta na pharmacy yarinya ce mai cike da nagarta ka shirya gobe idan Allah ya kai mu ka je ku dai-daita bana so al'amari ya dauki dogon lokaci. Wani irin gumi ne ya karyowa AB a jiki ya kasa furta uffan sai bin Daddy da idanu yake yi, da Daddy ya ji ya yi shiru bai ce komai ba ya kuma san halinsa da kawaici da matuƙar wahala yai mishi musu saboda haka ya umurce shi da ya tashi ya tafi amma ya tabbata gobe ya je sun gana da yarinyar. AB ya baro parlorn Daddy tamkar zai rusa ihu, meyasa Daddy zai kafe lallai-lallai sai ya yi masa aure? Shi ba wani mummuna abu yake yi ba da zai sa Daddy ya matsawa kansa. Tun sanda aka fasa aurensa da Rumaisa aure ya gama fice masa arai Rumaisa ita ce zaɓinsa ita ce mace da yake ganin zai iya zama da ita a karkashin inuwar aure. Da wannan tunani ya dawo bangarensa ya cire jallabiya jikinsa ya hau gado ya kwanta ba don yana ji bacci ba sai don yana ji kaman kwanciya zai iya sassauta mishi halin da yake ciki a koda yaushe yana ƙoƙarin danne damuwar da yake ciki don gani ya farantawa Daddy yasani muddin ya bari damuwar da yake ciki tai tasiri za ta shafi makusantan shi da dama abunda baya fatan faruwarsa shiyasa yake pretending as yana cikin farin ciki alhali azahirance ne kawai amma badilinsa abu ba haka bane. Yana so sanin wani abu da ya danganci asalin iyayensa komai ƙanƙatarsa amma babu hali yin hakan saboda Daddy ya gargaɗe sa akan zancensu. Daren rana AB bai yi bacci ba sai tufka da warwara yake. Shiyasa washe gari ya tashi da wani irin azababben migraine headache, adaddafe ya je sallar asuba yana dawowa ya sake kwantawa sai lokaci ya sami bacci. Yau trouble maker Aydah an auna arziki ta shirya da wuri, yau su dukka uku za su fita Siyama da Sadiya dukkansu biyu lectures ɗin safe suke da. A parking lot suka rutsa Aydah kowane su da kalan muguntar da yai mata Sadiya ta fara kai mata rankwashi yayin da Siyama ta sakar mata mugun dundu saboda azaba sai da Aydah ta fasa ihu ido ya raina fata har ta isa school tana matsar idanuwa sai tsokana amma babu juriya. Sai misali ƙarfe 11:00am AB ya falka zuwa lokaci ciwon kai ya ragu sosai agaggauce ya yi wanka ya shirya ko breakfast bai tsaya yi ba ya wuce kamfani saboda yana da meeting da team members (employees) wannan meeting ɗin har da Daddy zai yi attending ƙarfe 11:40am dukkansu sun hallara a conference hall dake cikin kamfanin bayan AB ya gabatar da sabuwar motar da za su kawo bayan dogon bayani da ya ɗauke shi tsawon awannin yana yiwa team members dangane da mota ɗin wani abin burgewa kamfanin su shine kamfani na biyu da zai fara shigowa da irinta a Nigeria, cike da kwarewa ya kammala jawabin nasa, sannan ya zauna nan take hall ɗin ya kaure da tafi da sowa. Daddy sai gyaɗa kai yake yi cike da alfahari kasancewarsa mahaifi ga AB idan ka cire mutane biyu Alh Sanusi da Alh Umar dake ciki hall ɗin kowanne team member za ka hango fuskarsa lulluɓe da farin ciki domin nasarar kamfani nasarar su ce dukka. Bayan an watse daga meeting ɗin a jigace AB ya wuce ofishinsa wani irin jiri ke ɗibarsa bai daɗe da zama ba ya ji muryar Secretary shi Skyler a dai-dai ƙofar shigowa ofishinsa da alama akwai wanda take sa'in-sa dashi, da ƙarfi aka banko ƙofar ofis ɗin nasa ya ɗago yana dafe da forhead ɗinsa "Madam! Madam, I told you that you're not allowed because you do not have an appointment with him, Come back and wait. Lemme ask him first if he wants to meet you. Duk maganganu da secretary Skyler ke yiwa Rumaisa bai sa ta tsaya ba har sai da ta iso tsakiyar ofishin ɗin na AB alama AB ya yiwa Skyler da hannu ta juya tare da rufu ƙofa ta koma baki aikinta cike da jin haushin Rumaisa. "What's all this Abba? Na ce menene wannan

Chapter 6 of 7