Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 10
a kasa kafin ta dago kai daga inda take zaune tana fadin. Kun rage abinci kubawa Bintu taci hjy na koshi saida na biya shagon baba ya saya min abinci naci kafin in dawo tace oh to kubarshi inda dane hjy din zata matsa min akan naci amma yanzu ba wanan. Ganin irin wanan sauyin yasa na fara jan jikina dasu don koda nake yarinya a yanzu ina fahintar wasu abubuwa na game da rayuwata don hakane nake son in nemawa kaina mafita tunda yanzu baba ba kullun yake dashi ba balle yayi ta bani. Ban dade a gidan ba nayi masu sallama na fito bayan tasa na bude mata dan abinda nasayo din ta gani dan murhune karami na kwalfot sai dan tukunya da kwadon roba da abin tsama. Dasu wake da mangyada sai roban yaji ta dandana yajin take fadin wanan yajin da dadi yake a ina kika sayo zan banda kudi ki sayo muna idan zaki koma kasuwa sayayya nace to hjy ki dibi wanan ki fara amfani dashi mana. Tace a, a wanan na sana,arkice bintu kada a fara da hakan tasa nakai kayan store dinta na aje na fito zuwa gida kodana shiga nasamu har babana ya dawo gida yana dan dakinsa zaune na gane hakanne ta hasken fitalanshi dana gani a kunne. Dakina na nufa na tura kofan ya bada kara lokacin baba ke tambayan waye a wurin dakin nan nace nice baba yace to to fadimatu kece ashe daga ina kike yanzu haka.? Jin hakan yasa na matsa zuwa dakin nasa nace baba daga gidansu hjy nake nakai kayan dana sayone ajiya a can yace to to to hakan nada kyau dkn tsara aisai in saya maki dan makuli gobe idan na fita zaifi maki saukin yawan jigila a can din. Nace to baba nagode Allah ya kara arziki yace amin yar baba kin dai dauko halin uwarki wurin godiya haka take komai kadan din abu idan ka bata sai tayi ta zubama godiya. Ire iren wanan halaiyan natane kikaga wa yan nan sakarkarun sunawa hassada har yanzu daga waje mukaji muryan maman biyu na fadin wai ikon Allah. Gadin kofan kuma malam ya koma yanzu don kada ayiwa yar gwal sata a gidan nan tunda ga barayi an tara ko ? Washegari ina Allah Allah in dawo daga school da sauri ana tashi na kamo hanya zuwa gida ina ta sauri don inje gida baraka na karbo kullun wakena dana kai mata aikinsa can. Ita Baraka sana,ansu ke nan su karbi wakensu su jika su nika makashi su dafa ka basu kudinsu su shine kawai sana,ansu a unguwar tamu. Banshigo gida saida na biya na dauko abina na wuce gidansu hjy na kwaso sauran kayana na hada a kusa da dan shagon isa dake kallon gidan namu don tun saura kwana biyu in fara na tambayeshi yaban wuri inyi. Kawai shigowa nayi cikin gidan mu na kwabe tufafin makarantana na shirya abu dayane ya kawo min cikas shine kujeran zama don haka naje gun mama lanto na make murya nace don Allah mama ki ban aron kujerar ki dan rsuguno na soya awara a waje. Tace kuma dai yau awara za a soya muna wajen gidan kuma nace eh mama ki min addua Allah ya ban sa,a na sayar. To bintu nayi maki addua Allah yasa ayi a sa,a nace amin kije ki dauka gaya can saidai ki kulamin dashi don Allah don shine kadai gareni kada ya halaka a can zan kula mama na fada. Na dauko zan fitone naji muryan maman biyu na fadin ana dai munafunci a gidan nan kan wai munafunci harda karamin yaro ya iya koda yake ai dole tayi don ta gadane a wurin uwarta indai munafuncine kan . A daibi a hankali kada aga kamar ana mata don miji yaso mutun idan maitan ya motso ta kama yaron mutum ko uwar taci muga karshen makirci ai mudai an shamu munyi hankali ban taba yarda da ladabin sheggu a cuceni nisa da nisa da a gidan nan yanzu. Ni dai ban tsaya ba ban kuma ji amsan da mama Lanto ta bata ba ina dai zaune nayi nisar suya naga ta aiko wai in bata kujeranta zatayi aiki akaine. ZAINAB IDRIS MAKAWA [7/26, 2:40 PM] Maman Aslam: KARAN DAFI 🌾 YAFI DAN DAWA AMAFANI 🌾 ZAINAB IDRIS MAKAWA 🌾 🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾 6️⃣ GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI A GAREKI, , , , , , , Ba yaran ba har uwayen nasu saida suka dinga lekoni suna jifana da bakar magana amma ban dago na kalli ko inda suke ba don inda sabo nasaba da halin yan gidan namu. Harkan gabana kawai nakeyi Allah ya taimakeni na samu ana saya sosai a wurin kinsa shi awara farin jinine gareshi sosai ga mai ga albasa da kabeji da yaji da nake zubawa mutum a sama idan ya saya. Nan da nan na sayar har ana nema na kashe wuta na fara hada kayana don in koma gida tunda na sayar ko gashi da yake ranan farkone wanda na fara soyawa na diba na zubawa isa mai shago hayyatun hjy yana wirin na zuba masa na kula wani daban yakaiwa su hjy din a gida. Haka kannena duk wanda ya fito ya tsaya zan dan saka mai in barbada kayan hadi in mikawa mutum su lamshe saidai ban aikawa uwayensu dashi ba yadda na aikawasu hjy dashi su saka min albarka. Amma nayi dabaran kullawa mama Lanto naba yarta Samira nace kiba mama idan kin shiga don Allah amma kada ki bari su gani don zasu zargeta ta karba tace angode na dauka idan ta shiga dashi zata dawo min dashi sai gashi naji shiru bata dawo dashi ba. Kayan suyan kaf na hada a wuri daya na dauki murhun da tukunya nakai cikin gida dakina na nufa dasu na aje daga gefe daya na koma na kwaso sauran na dawo lokacin an fara kiran magariba nasan lokacin dawowan baba gida ke nan yayi. Ganin gabatowan magariba baisa sun tashi a inda na samesu zaune ba kowa ya kafa kujeranshi ana gulmata ga yayansu zaune gaba daya zakace wani kasuwa akeci a lokacin gidan yawa ke nan. Dan Buta na dauko wanda baba ya saya min lamba 2 na fito nayi alwala nagama na dago mama uwa tace amma yar nan kinkai yar rainin hankali yanzu bahon nawane kika kasa kawarwa kina watsa min ruwan bakin nan naki mai dafin gado a cikin bahon? Bin bahon da kallo nayi naga ko kusa da inda bahon yake banje ba yasa na shura takalmina zuwa bakin famfo na kara cika butar da ruwa na juyo zuwa dakina da aka ban wanda babu komai a cikinsa sai tsohon katifa da labulen da hjy ta bani kwara biyu na kofa dana windoor dakin sai dan tarkacen kayana can gefen katifa dake aje min a wuri daya. Sallah na tayar har lokacin tana tsaye tana kare min zagi tare da aibantani a bakinta muryan baba naji yana fadin yaya yaya wai yane meya faru haka muryan ki har waje duk mai wucewa yana ji. Banda wanan yar taku yar rainin hakanli tazo tana zuba min ruwan bakinta ga baho kamar shi kadai ta gani a wurin kallon wurin ya juya yayi yace kai jama,a Uwa yadda kika san yar nan bata hanaki zama gidan nan to haka kema kuma ba zaki hanata zama gidan ubanta ba don nan dai shine gidan ubanta na asali da kika sani. Da baki son tarabi roban naki aisai ki kawar dashi a wurin baki zauna kina aibanta min ya ba haka akan roban ki kenan roban yafi rayuwan yata muhinmanci a wurinki. Karki manta inba rabuwa fa akwai mutuwa shi nake son ki gane, bari ganin kina zaune da kowa lafiya a yanzu da zaran ance babu ke a gidan nan ki tabbatar irin rayuwan da diyan ki zasu fuskanta ke nan a cikin gidan nan. Tunda kun riga kun saba da hakan an cusa maku ra,ayin yin hakan ga dan wani kunaku diyan waliyaine daba za,ayi masu hakan ba ? Baki kake min malam a kan diyana yace a,aaha hanya dai na haska maki in kina da ganuwa ki gane akwai rai dai akwai mutuwa don rayuwan mu ba a hannun mu yake ba. Malam kace kada yar nan ta bari in kai safe kace ta cinyeni a nan inda nake don Allah yace a,a yata ba manya bace kema kin sani don bakiga ta taba cin kowa ba inko kin gani ki fadi muje ki rantse. Don ni nan da kike gani da kaina zankai karan duk wani wanda yace wa yata manya saiya fada min wanda taci a garin nan bake ba duk mai niyar fadan hakan a shirye nake yanzu inyi shari,a damaishi. Nan kowa yai shiru ya barta dashi suna sa,insa a tsakar gida daga dakin mama lanto samira dake kwance tana karatun novel ta dago tana fadin kinji ko mama kinji abinda nake fada maki dazun ko. Wanan abin kusan duk sherin maman biyu ce amma kuka hau kuka zauna a kai wallahi kubi sannu halan koke maman biyu tana sonkine damu a gidan nan kowa bata bari ba ita sai diyanta. Amma ina magana kika rufe ido kika aika ta baki kujeranta data ara ke kadaice fa take dan dafawa taji sanyi a gidan nan duk da bata jin dadin ki kema don kina biyewa sherinsu kullun. A daidai lokacin baba ke fadin haba ni wanan abin ya isheni hakana abu dai babu marmari a cikin sa yarinyar nan baku san ajiyan da Allah yayi ba a kanta amma rashin hankali da tunane ya hanaku natsuwa ku fahinci hakan. Kinji ko mama samira din ta kara fada tana kallon fuskan uwarta tace ai gaskiya baba ya fada mama ke da kika san yadda yan uwanki suke har kika tsaya kina wanan shirmen duk mai cewa wani abu ya fadi ki dai fitar da kanki a cikin zancen nan don Allah. Ida ace ni akewa haka mama yaya zakiji a ranki buta uwar ta dauka ta fita tana fadin malam sannu da dawowa wanan gaisuwan natane ya sarewa baba gwiwa ga abinda hake fadi din don suna gaisawa ya shige dakinshi ya barsu a nan bai kara magana ba kuma. Rokan baba nayi ya ban wani tsohon gwagwanin fenti dake kofan dakinshi aje yake tambaya me zanyi dashi nace ina son in samu abin zama don kudin baikai har insai kujeran zama ba. Nan ya ke fadin duk kujerun gidan nan sai kin zauna a kwanko nace baba a dai bani don Allah don banson na dauki na wani kuma mama lanto ta aramin amma ina tsaka ga ciniki ta aiko in bata kujera. Kai wanan rayuwan ina zata kai matan nan ne amma ba komai ki dauka ki fara amfani dashi zan siyo maki kujera a kasuwa. Abu ga yar tallaka haka baba yake dan lalabani don dai kawai yaga farin cikina a lokacin don yasan ni nada kaina na saka kaina yin hakan gashi kuma ya dawo ya samu ko magariba ban kaiba a waje ranan dana fara din . Sai hakan yayi mai dadi sosai don haka ya kara kaimin taimaka min ga sana,an sosai saida zancen matanshi a kaina shine ya tsaya masa a raina yasan hakan balaifin kowa bane duk makircin maman biyune hakan don itace ta saka uwarta a gaba saida ta bar gidan nan. Kosu wa yan nan don tagansu kamar marasa kan gadone duk inda ta juyasu suna binta yasa suka zauna har wanan lokacin a gidan don da ba haka ba data aikasu suma waje ko. Sabon Gidan ya habibi yasha gyara da kayan alatu na zamani iri iri ta ko ina gidan sai walkiya yakeyi irin dai rayuwan da suke mafalkin shifidawa kansu da anty safiya a baya ke nan. Babu abinda ya rago gidan a yanzu sai macen aure mazauniya a cikin gidan shine abinda yanzu gidan baidashi. Yasan burin iyayyensa a kanshi nakin auren wata bare sai yar kusa da gida donsu ko a arewa din sunfi son diyansu su auri yan cikin kaduna wace aka san asalinta da kowa nata. Wanan shike saremai gwiwa a yanzu kan halakan shi da wasila da yake jin a yanzu bai iya rabuwa da ita gashi a yan kwanakin nan aure yakeso sosai a rayuwan shi donshi ba iya zinaba dako ace shi nazinacine da yanzu yakai jikin wasila din yadda shakuwan nan nasu tayi karfi atsakaninsu. Tunanen hanyan da zai bullowa Alhsu yakeyi don yasan na hjynsu mai saukine ba zata taba kin abinda ya zabowa rayuwansa ba amma Alh shine abin ji a yanzu gareshi don yasani yasha fada masu wanan maganan tun suna yara. Don ko yayyanensa biyu sunso gwadawa ya hana dole suka hakkura karshen wanan watan kan dolene ya ziyarcesu don tun hjy na kiransa tana mashi fadan rashin zuwa gida ya dubasu lokaci lokaci har yakai yanzu ta daina ma kirasanshi ga baki daya. Sai kuma ga mafalki yayi da mahaifinsu wanan ya tayar mashi da hankali sosai don haka washegari ya kira wayan yan gidansu har mutum uku bai samesu ba sai hankalinshi ya daga. Sai zuwa yammane ya kira layin yaya Hamza ya samu ya dauka saida suna gaisawa shima din ya haushi da fada baiko bari yayi magana ba ya kashe wayarshi hakan shiya daga masa hankali sosai a lokacin . Bai kuma kara kiran wani dan gida ba yaji kome ke faruwa a gidan lokacin saidai hankalin nasa gaba daya ya koma gida don haka yasa a ranshi cewa zai tafi gidan daga can zaisan yadda zai fito da zancen aurenshi. Amma kuma tunda yana da acount dinsu yai amfani da wanan daman ya turo kudi zuwa gida hjy da Alh sun wayi gari da sakonshi a waya amma dukkansu ba wanda ya kirasa yadda suka saba idan yai masu aike sukanyi godiyan cewa sunga kudi sun gode. Wanan karon ba amsa sai hakan ya kara daga masa hankali saidai shima bai kirasu ba so dai yake su ganshi kawai ya dira a garin duk da yasan suna da labarinsasu. Maman baby da wasila kanwartane gurfane a gaban bokan ibo kowansu yayi shiru yana sauraren abinda zai fada masu a lokacin. Farin kudi irin na da can baya currencies ya watsa a kasa gabanshi yana yan tofe tofen su na tsubo can ya jawo wani allon madubi a cikin wani tarkacen kayansa yana shafansa . Ya dago kai ya kalli wasila yace yarinya aikin ki akwai wahala sosai don jinin yaron yana da karfi sosai ba duk asirine zai iya kamashi ba a yanzu don iyayyensa na tsaye sosai a kansa. Baba Oracle ka taimaka muna yarinyar nan ta samu ta auri mutumin nan ta kuma mallakeshi da komai nayima alkawarin ko nawane zamu baka. Ya dago hannu tare da fuskanshi me rabi duk an fente da farin kasa ya kallesu yace hakan ba zai gagara ba a yanzu sai dai nan gaba akewa duba abinda zai iya biyo bayan hakan. Idan an fara samun shi a yanzu daga baya sai a magance wancan matsalan maman baby ta fada cikin tare masa numfashi sai yace hakane . Yanzu ki karbi wanan don naga shi mutum ne mai tsare ibandashi ya dauki addinin shi da karfi sosai don haka ki karbi wanan zaki shafa a idanunki wanan kuma a dukkan jikin ki da kinyi wanan kin gama dashi. Amma sai kin tabbatar da ranan fa zaku hadu dashi idan har kun hadu daga ranan sai yadda kikayi dashi kuma sai dai nan gaba din idan mun hadu zan baki sauran bayani. Godiya suka fara yi masa maman baby ta ciro kudi a cikin jakkarta masu yawa ta aje masa a gabansa sukai godiya tare da sallama suka dawo gida tun a mota wasila ta fara nuna tana tsoron hakan da bokan ya fada. Nan yar ta balbaleta da fada tana fadin in ansamu wa zaifi jin dadin hakan a cikin mu ana nuna maki hanya kulun kina bultsewa. Ina dai kin gane duk bayanin da yai maki komai dai kin haddace yadda ya fadi kiyishi tace nagane anty. To ki kiyayye in ya shigo hannu kinga sai yadda kikayi dashi kenan nan wasilan taji dadin kalamin yar nata har tana dan washe baki tare da fadin. Wallahi anty in haka ya samu gareni sai na rabasa da kowa nasa ya manta dasu sai mu kadai zamu morewa rayuwanshi ko garinsu ba zan yarda yaje ba balle su karamin maganina da adduan nan nasu A wai wasila tun yanzu kin fara fadin haka ashe nan gaba komu ba zaki tuna damuba ke nan tace nina isa anty ince zan manta dake. Yamma nayi maman baby tace ki kirashi muji idan zai samu shigowa wasila din ta dauki waya ta kirashi cikin kashe murya ta fara gaidashi da aiki ya amsa take fadin yau zaka samu shigowa erean mu kuwa ? Yace yanzun nan dana tashi nan nayo don yau ina son abincin gargajiya a cikina tace angama sar wani kala semo ko tuwon shimkafa yace idan ba zan wahal daku ba tuwon shimkafa nake so miyar kuka tace angama. Suka dan taba hira ta kashe wayan ta kalli anty nata sai suka kwashe da dariya lokaci guda barin tashi in dora masa ke kuma sai ki fara shiri. Karfe takwas da rabi ya iso kofan gidan nasu waya ya bugo mata don yanzun ya daina yawan shiga gidan don ya kula mutane sun fara sa masu ido dom unguwace da mafi yawanta hausawane zaune a cikinta dama. Yana buga mata dama ta gama shiryawa ta mike tana fadin gata nan fitowa yana zaune cikin motarshi ya hangota tafe dauke da basket din abincin tana rangwada ido ya kafeta dashi har ta iso gareshi. Ya bude motar ya fito yana amsan abincin daga hannunta nan ya fara shakan kamahin wanan sihirin da bokansu ya basu ji yayi wani iri a lokacin . A motan ya zauna suna hira yana cin abincinsa hankali kwance har ya gama suka dora da fira yana ji a ranan kamar kada ya tafi ya barta don yada yake jinta a zuciyarshi. Tun daga ranan wani irin son wasila din yake fisganshi har yakai yanzh yana jin in bai aureta ba zai iya samun matsala a rayuwanshi. Don haka ya shirya tafiya zuwa gida inda zai tunkari iyayyensa da wanan zancen jirgi ya biyo na yamma zuwa kaduna din don yana son idan yazo ya sayawa mahaifinsa sabon mota tunda yanzu kofan arziki ya budu gareshi. Baije gidansu a ranan ba don dare yayi lokacin don haka ya tsaya a wani hotel ya kwana washe gari ya kira wani abokinsa da suke sana,a tare dashi. Wanan abokin nasa shiya daukeshi da mota sukaje wure har wurin sayar da motoci ya sayowa mahaifinsa sabon mota dal da sauran kayan abin da sayayya su hjy dana yaransa. Da yaya Hamza ya fara cin karo ya fito daga cikin gidan nasu zaije ya sayowa mahaifinsu magani kafin ya fita zuwa cikin gari . Su yaya Usman ma da yaya hamza na tsaye wuri mashin din ya ibrahim suna magana bin motar gaba dayan su sukayi da kallon don sani waye a ciki yazo kofan gidan nasu kuma. Gaba daya duk kallonsu ya dawo kan motar ya dan dade bai fito ciki ba kafin can ya bude ya fara sako kafanshi daya nan suka gane shine ashe. Kallon mamaki suke mashi don gaba daya wana karon ya sauya sosai ya zama wani cele mai jin lokaci ga kamshi da jan aji a tare dashi. Shima murmushi yake masu kamar yadda suma fuskansu a sake yake da ganinshi a lokacin daga can makwabcin su malam Tanko da yanzu ciwo da tsufa yasa a gaba yana zaune yace a, a yau Mahmoud ne a garin namu lale marhabin . Hakan yasa ya fasa nufar yan uwan nasu ya nufi inda tsohon yake yana gaidashi cikin girmamawa da akewa mahaifa a nan yan uwan nasa suka sameshi suka gaisa. Yaran dake wurin suna wasa ya kira sukazo don su shiga masa da kayan tsarabanshi cikin gida inda sauran yan uwan nasa maza suka jera suna masa ya hanya inka debe ya hamza daya wuce zuwa inda zai tafi. Kafin su shiga yara sun shiga da kaya sun fara sanar masu zuwan shi din lokacin nan gida ya dauki murna suka garzayo zuwa kofan gida inka debe jamila da tayi zaune taki tashi saboda yanzu ta fara mantawa da mahaifinnasu. Sun hade dasu zasu shigo har hjy laraba ma ta nufo kofan gidan tana fadin maraba da baba karami kai tafe yanzu amma dai a hanya ka kwana ko tana tambayansa. Hjy mairo na daki taki lekowa don hjy Laraba tayi mata kara ko ko banza kuma fushi takeyi dashi llokacin don haka ba zata fito ba. Alh ma dake dakinsa zaune yaji gida ya rude da ihun yaya Mahmoud hakan baisa ya leko ba don ya nunawa dan nasa bacin ransa na sharesu wata da watanni da yayi kamar baida iyayye a raye. Hjy Laraba sai fadi takeyi haba baba anya ko zamuyi maka sannu da zuwa ka sheremu haka kamar bamu raye a duniyan nan ? Cikin dan sosa kai yace a gafarceni mummy wallahi abubuwane suka tsayar dani wanan karon amma wallahi kuna raina. A,a jamila ba zaki taso kiyiwa daddy welcome ba ya Ibrahim ya fada yana kamo yarinyar dake wasa a kasa zaune tayi saurin make hanninta alaman bata zuwa. Kai kardai ace har kin manta da daddy din naki da kike damun mu da kirasa a baya kaiko ai dole ta manta sau daya fa yazo garin nan tun zuwan yaran nan kagako dole ta manta dashi yanzu ai. Kallon kofan mahaifiyarshi yayi ganin ba alaman zata leko don jin muryanshi a gidan yasa yace hjy na nan kuwa dariya hjy laraban tayi kafin tace duk sunan har Alh kwanan nan baya jin dadin jikinsane. Da sauri yace asha subbahanallahi amma ba wanda ya buga min waya ya fada min da sauki ko ya tambaya ya kallon fusksn mummy din tace a,a da sauki ai kasan ciwon tsufa ai. Dakin mahaifin nasu ya nufa ya shiga da sallama yana zaune a kasa saman kafet dagashi sai babban riga a jikinshi yana fitara ya amsa mashi sallaman ya shiga dakin. Sun gaisa sama

Chapter 5 of 10