Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 10
boko. Matan kuma suma suna makarantar na jekaka dawo a kasan uguwar mu don bata wanke kowa ba tukun ita har yanzu amma naji tun anty safiya nada rai tace wai babban tayi miji data hada karatun secondary aure zatayi. Mama lanto dake amarya a gidan itama yaranta biyar yanzu a gidan mata uku maza biyu kinga ke nan gidan mu zurian yaya mata yafi yawa ke nan a gidan. Asalin iyayyen mu turankawane zuwa sukayi nema daga sokoto tun lokacin mulkin Frere minister lokacin kadunace zones center sokoto tana hade da naija. Har zama ya zaunar dasu a nan kaduna don haka mu din zubin fulanine ke nan na sokoto amma idan ba tarihi ya taliyo ba a yanzu mu din muna claiming cewa mu yan kadunane don bamu san garin sokoto din ba gaskiya haka duk matayen su baba yan asalin jahar kadunane su. Ina kallonsu kowa tana faman yan girke girkenta da yaranta da zasu kara bayan na gida da akayi da bai isa mama uwace da girki a ranan ina ji da kunnuwata ta kwalawa yarta kira da cewa yasir dauko min tsohon kwanon miyan sliver nan dake bayan gambon kofan shiga kuryata. Naga yarinyar ta fito da dan kwanon da uwar tayi mata kwatance ta dauko mata a dakin ta dan kyafato tuwan farar masara ta manna a can kasan kwanon ta kawo miyar busassan kubewa ta lema a sama ta aje agefenta. Saidata gama abinda takeyi kaf yarinyar tana kai mata dakuna tace wanan na wancan ne mama nakai mata naji tace rufa min asiri ban manta da dawainiyar cikin ba ai har yanzu yasira. Kul na ganki wurinta saina saba maki rai sosai wallahi ta mike ta dauko kwanan a wullakance ta dan garo min daga nisa tana fadin gashi don ni uwarki har ta bar gidan nan mussu kona baki bai taba hadani da ita ba donshi zanyi yar nisa danisa dake kada Allah ya kamani da alhakinta a kaina. Kallon tuwon nayi nace nagode sannu da aiki yadda anty safiya kance dani idan na hada masu abinci zataci zata juyo tace dani Bantu sannu da aiki. Ban kara kallon abincin ba inda ta garoshi a nan na barshi tunkan ya karaso naji muryanshi yana magana da yaranshi maza da suka hade a waje dasu. Duk da duhune a lokacin ba wuta amma haka bai hanashi ganenini ba lokacin da nace sannu da dawowa baba ya amsa da a,a wa nakw gani kamar fatimatu nace nice baba. Ikon Allah anzone ko an dawo gida ke nan nace na dawone baba Anty Altinece taje tazo dani aiko ta kyauta dan uwa ke nan to me mugun gado da a can kike son a barki ki zauna don kwadayi ko ? Kai kai haba meye haka don Allah yarinyace har yanzu yaushe wai Fatimatu tasan wanan maganan da kike nufi don Allah ni bani son hakan da kuke nunawa yarinyar nan ku barta taji mana da rashin yar uwanta da tayi wanan kadai koshi damuwane a gareta ai. O lalaima malam a bugeka a hanaka kuka bayan kowa yasan meke faruwa zaka kama wani boye boye yanzu sai baba yace yanzun dai inane zata zauna ni banson yawan magana don Allah. Ai sai ka fada don dai kasan badani ba ta isheni haka abinda nagani akan yar nan da uwarta in ba nawa rayuwan kuma kuke nema yanzu ba don Allah a barni haka ya isa ka kaita duk inda zaka kaita a yanzu tabon ya isheni hakana. Tabo tabon me don ni ban gane inda zancen ki yake zuwa ba akan fadimatu ba gaskiya sallamu alaikum hayyatudeen ne da hjy tace zai kawo min kayana ya shigo dashi yana fadin wai ance ga kayan Bantu a kawo mata inji hjy. Baba yabi katon akwatin da kallo yana fadin zo nan ka sauke kaji dan albarka iso in kamamakashi don baba ya kula lokacin da yake magana da maman biyu yaga lokacin da mama uwa ta turo kofan dakinta alaman ba a dakinta ba kan. Ita kuma mama Lanto yartace ta fito ta gyara masu labulen kofan dakin su din don haka ya gane me suke nufi da hakan. Bai kara bi ta kan maman biyu ba sai cewa yayi dani taso Fadimatu ki shigo nan daga ciki kinji hayatudeem ya kama masa katon akwatim aka shiga min dashi turakan mahaifin mu. Na shiga dakin baba din kamar yadda yace na zauna kasa a gefen kujera nakai zaune duk kokarina na son tare hawayen dake son zubo min a lokacin na kasa saida ya zubo . Alokacin baba ya shigo yana fadin ina dai kinci abinci Fadimatu sun baki abinci dai kinci ko a hankali na gyada kaina nace mama uwa ta bani amma yana nan waje na barshi ban ci ba. Fita naga yayi don dauko min abincin sai kuma ya dawo yana fadin wanan ne abincin da zasu baki din gara da bakici ba don wanan ai wullakancine. Shinfida yayi min da kansa a falon ya dauko babban bargonshi da filo har da zanin rufa ya aje min wanda zan rufa dashi don sanyi kafin mama uwa tayi sallama ta shigo dauke da abincinshi a jere cikin tire. Malam ka dawo sannu da dawowa ta fada ya amsa mata yauwa bayan ta aje abincin ne yace Fadimatu tashi ki wanko hannunki ungo ga ruwanan kizo muci abincin. Yana rage kayan jikinshi yake fadan wanan maganan nace to baba namike lokaci naji mama uwa na fadin a,a ya haka kuma aina bata abincin tundana kare dafawa dazun. Nasani wanan din dai da yanzu kika kawo min zamuci tare ba yadda ta iya tana kallo na zauna muka fara cin abinci da mahaifin namu a akwashi daya tare dashi. Yin hakan da baba yai min shine yasa mama uwa yin fushi bata kara leko dakin baba din duk da itace da girki a ranan washe gari tunda asuba ya tashi zuwa masalci . Ni kuma ina kwance nan falo ina ta sharan barci saida gari ya danyi haske na tashi na lalaba na fito nayi alwala na koma dakin na kwanta a inda na kwana din barcine ya kara daukana. Wanan karon hayaniyarsuce ya tayar dani don kowansu su uku fada sukeyi don baba shimfideni a dakin maman biyu sai fadi take ai sai mu barmata dakin taita kwana dashi. Sallaman baba yasa duk sukai shiru suna kallon shi ledace baka a hannunshi sunsan ya jisu don kallon da yai masu kawai zai nunama yana hake dasu lokacin sai ku gyara akwai wanda zai shigo yanzu ya fada cikin dakewa irin ta maigida ga matanshi fuska daure. Kallon juna sukayi suna mamaki ba wanda ya kawo cewa maginane zasu shigo gidan a lokacin saijin muryan baba sukayi daga dakunan su yana fadin sai a rufe nan a fasa kofa ta nan bangaren. Wancan kuma daga bayan ginan za a fasa a fitar min da ban daki daga bayan nan din ma,ane dai baba ya dauko masu gina su fasa dakinshi da yake ciki da falo a mayar daki guda guda ni zan zauna a cikin dayan ke nan yake nufi. Allah Allah sukeyi mazan su fita su hau bala,i sai baba ya shiga dakin ya sameni rakube yace Fadimatu tashi ga abin kari na sayo maki tunda ba lalai bane su baki naso don na fahinci nufinsu a kanki . Niko matukar ina raye a duniyan nan ba zan taba barin ki wullakanta ba ga kowa fadimatu kaina kada masa alaman gamsuwa da zancen yace. Tashi ki wanko baki a waje kizo ki zauna ki karya rana yayi yanzu namike jiki ba kwari zuwa wajen tsakar gidan cikin dari dari na fito dauke da butan baban mu a hannuna na wanke bakina da kyau na koma dakin na sameshi ya bude min dan kullin masan zaikai na dari biyu yace zauna kici ki koshi. Ki koma wurin hjy mairo ki zauna har a gama maki gyaran wancan barin nawa sai ki zauna a ciki yau ba zan fita ba saboda wanan aikin ina gida idan kina son wani abu kizo ki sameni. Zan zauna a din kada taga na dawo yau kuma ashe kina da hankali shiga bayin kiyi wanka da kin gama saiki sauya tufafin jiki ina dai kinyi sallah nace eh baba. Mama Lantoce ta daga labulen dakin daga waje baba ya zaune a saman kujera ya kurawa yadda nake cin masan kamar banso taunawa a bakina. Amma malam baka son fitina ya kare a gidan tunda ka fara nuna banbanci akan bintu su wa yancan yayan namu suba diyanka bane ke nan ka sayo mata abin karyawa ka zaunar da ita a daki ka bata ita kadai kayi muna adalci ke nan malam ? Kamar maman biyu dama jira takeyi ta fara magana sai gata waje tana fadin ai zamu gani wanan yar gaibun ake shirin fifitawa akan yayan mu ai naga gidan nan akwai manyan yan mata da suka fita girma amma haka ka barmu dasu a daki muna cudanya baka taba cewa zaka gyara masu daki kwanansu su kadai ba a gidan nan sai yanzu. Zakice baba baya gidan a lokacin kowa ke fadin albarkacin bakinta shidai yana zaune ya tsareni har in gama shiryawa. Na gama tsab na fito lokacin masu aikin suka dawo da yashi da bulo da zasuyi aikin sukai mashi sallama ya fita ya barni suna jifana da zagi ta uwa ta uba duk wai akan kishin uwata da ma ban sani ba suke min wanan abin laifin mahaifiyata shine ya shafeni a yanzu. Saukina guda ba wace tayi gigin cewa zata tabani daga cikinsu komai yasa haka oho ni dai ina zaune nasha jinin jikina har yakai baba ya dawo dakin ya sameni yake fadin fito ki zauna a tsakar gida zasu fara aiki a dakin yanzu . Ina fita naga baba yana kokarin fito da kaya dakinshi na kurya haka yasa na mike nima na taya shi kwaso kayan muna fitowa dashi waje. Duk ido suka saka muna suka koma gefe har muka gama kwasan kayan aka fara aiki zuwa karfe uku aiki yasha kashi nan da nan aka karasa muka mayar da kayan na baba a daki daya. Ni kuma ya sakamin kujeru kwara biyu a dakin da zan zauna din duk da tsofine amma naji dadin hakan sosai a raina ba gado sai tsohon katifa aka yar min akasa. Ranan a dakin na kwana ni kadai tunda na zama manya kowa na gudun hadani da dansa inciye masa shi a cikin dare. ZAINAB IDRIS MAKAWA [7/25, 9:24 PM] +234 803 434 1977: KARAN DAFI 🌾 YAFI DAN DAWA AMAFANI 🌾 ZAINAB IDRIS MAKAWA 🌾 🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾 4️⃣ GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , , Kwaran niyan iyalan baba ya falko dani da safe na tashi da sauri waige waige na farayi ina neman abinda zan kewaya dashi don bukitine wani tsoho na baba ya bar min a ban dakin nawa a lokacin. Kai dan tallaka naganin rayuwa a duniya tundai akacs uwarka bata gida kece ke daya a tsakiyan iyalan mahaifinki zakiga rayuwa iri iri tundai tawa rayuwan dayazo da kalubali a garesu. Gashini ban ko san fuskan uwartawa da suke muzanta min haka a kanta ba dazata zo ta tsaya ace wacece ita ba zancen na santa ba sai dai idan an fada min. Duk da ina jin wasu tarihinta a bakin su mama idan suna min gori hakan kuma baisa na taba tsarnarta daidai da rana daya ba a zuciyata saima son ganinta da nakeyi a rayuwata. Tunda ina goyene suka rabu su suka yayeni a tsakar gida a hannunsu na taso a cikin bakar wahala duka da zagi sai dai in fadawa wani badai a fada min ba yanzu . Har zuwa lokacin da ubangiji ya sauwaka min rayuwata ta koma hannun anty safiya da zama yanzu kuma Allah daya haliccemu ya karbi nata rayuwan na dawo a turketa mai cabo na zauna kuma ina ganin wanan ukuban acikin kwana biyu da dawona cikin su. Mikewa nayi na shiga bandakin dan ruwan dake cikin bukitin na samu nayi alwala dashi na fito na nemo zani da hijjab na dora saman rigata na tayar da sallah. Bayan na idarne na zauna a wurin ina sauraren maganganunsu dake zo min ta tagan dakin guda guda a kunnuwata lokacin na mike na fito don in gaidasu da kwana. Mama lantoce take aiki a tsakar gida da ita muka fara cin karo nayi mata ina kwana ta amsa min a dan darare a cikin shakku tana wuceni da sauri. Na nufi kofan mama uwa dana tsinkaya a zaune saman kujera dan tsugunno tana gyaran wani abu a cikin ture da ganin na nufo inda take a cikin tsawa da daga murya gareni tace ke dakata daga nan in dai gaisuwan kice na yafe daga yau din nan. Ba ruwana da ladabin dan maciji ban shiga tsabganki ba kada ki shiga rayuwata dana yayana don Allah ki zauna a inda aka ajeki a gidan nan . Dariya mama Lanto ta kwashe dashi don jin abinda take fada min tana fadin kai yaya tace ato ban daga kai na kalleta ba balle tazo min da gaisuwanta na gaibu sai an jaka a jiki an shige maka daga baya azo a cuce ka to ban yarda da hakan bama. Yaranta gaba daya suka fito daga dakin don jin abinda take fadi sun fito su gani don gidanmu ba wuya fada ya kaule a tsakanin su mama din har ya koma ta yara wani lokaci. Don ma mahaifin mu yana tsaye wai ke nan da gidan amma hakan bai hana komai ba a gidan wani tsawa ta juya ta daka masu tana fadin zaku kauce daga nan ku ban wuri kunzo kun baza mata cibinan ku kuna talla ko riga baku dashi mafarin a kwashe maku hanji a barni da salati. A lokacin ita hamshakiyar gidan ta fito watau maman biyu tana fadin wai meke faruwane kuma ina jin murya sama sama dan matsawa nayi na rukube a bangon dakinta ina fadin mama ina kwana an tashi lafiya ? Ta juyo ta kalleni a wullakance tace ke lafiya kada ki dameni fa sai mama uwa tace kema dai kya fada yaya shi ta kawo min nayi mata kashedin hakan ta rike gaisuwanta na cuta na yafe don ko kusa dani da yayana banson ganin wanan yar. Sallama hjy mairoce suka shigo su biyu da hjy Laraba kishiyarta sai jamal da jamila rike a hannunsu don yanzu sune yan gaban goshin gidan. Kinsan in aka rasu aka bar yaro yana jin dadi na kwana biyu a wurin mutane kowa na haba haba dashi a wuri yaran na ganina suka kwace daga hannayensu suka nufoni da gudu suna fadin anty Bantu ashe kina nan ? Rugumesu nayi a jikina nakai tsugune a inda nake rakube dasu muna murnan ganin junan mu dasu yayin da mama ke fadin an gudu ba a tsira ba ke nan nama a hannu. Su dai su hjy gaisawa sukeyi dasu suna dariyan mu tare da fadin munzo ganin yar gidan mune bintu muga ya tazo gida yarinyar tayi rashin yar uwa sosai don abin ya daki zuciyar ta. Amma kuma basu barta da abindake damun taba sai sheri da suka dauko suka dagwara wa wanan yar a yanzu suna kokarin aibanta min ya da sunan banza akan bakin kishi . Uwarta dai ta tafi ta bar maku gidan har abada amma ku har yanzu kishinta yana nan a zuciyar ku kuna kaya yanzu hjy ace wanan yar ta cancanci wanan ukubar da matan nan ke gana mata. Hjy tace asha wani abune ke faruwa malam Habu yace sosai hjy sunje sunyi kisisinar da yar nan ta dawo nan cikin su ba tare da sanina ba sun kawota nan yanzu kowan su yace ba zai zauna da ita wai manyace ita ta cinye yar uwanta . Subbahanallahi hjy ta fada tace aina dauka wurin ita Altine din zata zauna ma da naji haka keko maman biyu me wanan yar ta sani da zaku fadi haka a kanta don Allah. Mutuwa fa tana a kan kowan mu nan idan lokaci yayi tafiya zamuyi koda shiri ko ba shiri balle mutuwan safiya na ishara ga bawa mai tunane. Tunda mijin ta yace tun cikin dare ta fara ciwon ciki zuwa safe kuma taji sauki har ta tashi da kanta tayi masu abin karyawa ta sallami yara dashi suka tafi makaranta shiya wuce wurin sana,anshi. Yana can ta bugo mai waya tun fitanshi ciwon ya tashi gata tana amai ga shigan ciki kuma gareta baifi minti uku ba bayan sun gama waya aka kirashi wai ta rasu. Wanan kadai ya ishi bawa imani ga mai tunane to ita bata yarda yarta tayi mutuwan Allah da Annabi ba cewa tayi Fadimatu ce ta kashe mata ya ban sani ba ko wurin shige shigen su bokanta ya fada mata hakan . Wai wanan zancen shirmen dama harke kin yarda dashi idan Bintu muguwace ai ba uwar zata fara ciba da yaran nasu zata fara kawarwa kafin ta kai gareta ko dan kada ta dawo garin nan. Hjy mairo akwai yar kunya a tsakanina daku bayan hakan dana fada maki wani magana a yanzu ina nan gaban kowan ku kusan irin ukuban dana shiga kan uwar yar nan a gidan nan . To mukan zamu koma malam habu dama zuwa mukayi muga isanta gida don kula kuma mun ganta mungaida ku sai anjima ta kare da sawa yaran kira suzo su wuce don ko wanka ba ai masu ba a lokacin. Yaran sukaki baba yace ai a barsu yanzu inta hada saita kawosu gida don fita zanyi sai taje can ta gaidaku dama haka na shirya a raina don jiya ban fita ba muna aikin gyaran dakin da zata zauna tunda su sunki ta rabesu. Shine na kashe dakina aka fitar mata da kofa yanzu a nan take zaune ya nuna masu dakin da hannu duk suka juya suna kallon dakin da aka kira da nawa din karama dani. To malam Allah dai ya sauwaka mukan mun tafi maman biyu uwa lanto sai anjiman ku dama shiya kawo mu Alh yace muyi sammako muzo mu dubata don baya gari jiya ya dawo daga Ikko. Hjy laraba tace bintu kada ki dade dasu basuyi wanka ba karyawama sama sama sukayi muka fito dasu yanzu don basu yarda da uwayen su sai mu. Hjy agaida min maigidan ina masa sannu da zuwa nagode nagode zata shigo yanzu insha Allah inta hada ta kawo yaran shinema wanda ya raka mata donsu matanshi suna cikin bacin rai. Ya juyo garesu yace yanzu ku duba ku duba don Allah makwabtaka da dalilin aure ya hada mu dasu amma suka wanko kafa sukazo ganin yarinyar nan don sunsan darajanta na yar adam. Ba wace ta taka baba a cikinsu ganin hakan yasa yace debesu kikai dakin ku ki zauna dasu a can barin fita in samo maku abinda zakuci keda su. Muka shiga dakin saman kujerun nan kwara biyu tsofi na zaunar dasu na koma saman katifa nayi tagumi can bayan jamal ya karewa dakin kallo naji ya jefo min tambaya yana fadin . Anty yaushene mami zata dawo ta daukemu mu koma banson garin nan ba dadi daddy ma yabi mami bai dawo ba ya barmu a nan. Hawayene yazo min lokaci guda nace Jamal hakkuri zamuyi mami ba zata dawo garemu ba ta tafi ke nan daddy kadai zai dawo shi kadai banda mami kuka yaran sukasa min nace amma kila tare zasu dawo ai. Baba ya shigo gida da leda biyu saida ya miko muna babban ya fice da dayan ya kaiwa mama Lanto a raba a cikin gida ina jin suna sake habaici garemu muka gama na fito naje rijiya na debo ruwa nayi wanka na shirya cikin wani rigar yar kanti da ya habibi ya sawo min ta sallah bara nacewa yaran su fito mu tafi. Ban dadara ba nabisu ina sallaman su ban damu da amsarsu ba gareni muka nufi hanyar fita naji mama Lanto tace ai in ba kinyi da gaske ba ko yaran saita rabaki dasu hayyatan hayatan kinaji kina gani suce bake kika haifi uwarsu ba nina taba ganin haka don Allah ? Baba na wanka koda muka fita don haka bamu samu yin sallama dashi ba a lokacin muka shiga gidan su ya habibin yaran suna ganina suka fara fadin Lah ga Bantu ga Bantu. Zaune suke a falon daga ita sai kanwar nata tana fadin duk yadda zakiyi kiyi kiga kin shiga zuciyan shi wasila don in kika samu ya yarda ya aureki kin more miji a cikin tsara. Koni wallahi don ina da auren wanan dan iskane a kaina da bandashi ni zan makale masa da kaina ya aureni bake ba don gayen nan ya hadu wallahi. Ga kyau ga kudi kuma ga ilimi irin mijin da ko wace mace take son ta mallaka a rayuwanta zaki tsaya har ana ce maki ga Allah kina wasa . To anty ni ya zanyi kindai san halin wanan guy din ko gaisuwa baya amsawa sai yaga dama yar nata tace ko bai amsa ba ki gaidashi mana me kika rasa a matsayinki na mace a duniyan nan ? Kin mafi matarsa data rasu fasali da kyau gani ke nifa in baki iyawa na aika gida a turo min hafsat yanzu kiga aiki da cikawa tunda ke sanyin jikinki tayi yawa sosai. Ni ai bance bana son shi ba anty gayen yayi min sosai wallahi amma dai yadda baya kula mutane din nan shiyake damuna no way da zan iya shige masa bashi ya nuna min hakan ba. Amma wasila ashe ke banzace ke ba mace bace ki guda abubuwan dana fada maki yanzu kiga in bai afka maki a so ba waya fada maki mace tana duban wana ga abinda takeso. Ke in kika sameshi ai mun huta don yafi wanan wawan dake shirme waishi yana neman kudi a garin nan fa sukazo suka samemu ki duba yanzu ida matsayinsa yakai cikin layin nan. Baban baby yace min a yanzu kaf layin nan babu kamarsa a cikin su wurin kudi wama ya sani ko matarsa yai scicrefaying ya samo wanan kudin haka. Tsoro wasilan taji ta fito da ido waje tace anty shine kike son ni in shiga kuma bayan kin fara tuhumar haka wasila inma ita yakai yayi kudi shi da iyayyenta

Chapter 3 of 10