Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 10
A can kasan nakaisu sukayi na daukosu na dawo dasu lokacin ya habibi ya shigo gidan ana masa gaisuwa ya wuce zuwa dakin mahaifiyar nasa kai tsaye. Abinci hjy tace a bamu na dan zuba kadan ina ba yaran sukaci sukace sin koshi nan kuma sukai kwance saman jikina sai barci dama haka muke ko can bamu wuce tara bamuyi barci a gida. A nan dakin hjy muka kwana dasu washegari nice na tashi na gyaro ko ina na gidan har kwanoni mutanen gidan kafin su fito na tsabtace komai na koma daki na tayar da yaran nayi masu wanka nima nayi kamar dai yadda muke a can ko kuma idan munzo nan erewa ganinsu. Don tun da anty tayi aure tana da cikin farko ta daukeni nake a wurin ta duk da mahaifiyan anty din watau maman biyu yadda suke kiranta dashi bata so haka ba amma anty safiya taki yarda tace ita ta yarda da kaddara amma tana sona hakana . Har wurin su baba taje ta nuna tana son daukana a lokacin ina walagigi a tsakar gidan mu wurin mutanen gidan dake nuna min bakin hattara yasa a lokacin na taso kamar wata tababa mara hankali wagila wagila dani haka saboda rashin wani babba a tare dani da zai koyar dani wani akidar alheri kamar yadda duk uwa ko wanda kake tare dashi zai doraka akai sam ni na rasa wanan a rayuwata. Don kawai ya kasance ban tashi tare da mahaifiyata ba a gidan mu tun rabuwansu da mahaifin mu babba yar mahaifina ta kwaceni a bayanta da karfi da yaji fushin hakan yasa tun bayan tafiyan ta ba kara jin duriyanta ba kuma har yau din nan. Saidai komawata wurin anty na a yanzu zakice bani bace a wancan lokacin don anty safiya da mijinta habibi sun gyarani tsab ba kazanta na koyi tsabta na iya na iya komai na gyara a yanzu wanda mutane kewa ganin matsi da tsangwamane a kaina yadda anty din take ban tarbiya. Sai gashi da rana tsaka mutuwa yazo ya rabani da mutanen da suka daukeni da zuciya daya kuma suke kaunata da zuciya daya don banda matsala a tare dasu ko kadan. Ban rasa ci ba ban rasa sha ba a gidan anty sai abinda naga dama nake girka muna muci haka kuma uwa uba sutura duk yaya habibi zai sayowa yaranshi sutura da nawa a ciki. Bantu ke bantu wata kanwar ya habibice ke kwala min kira a inda nake zaune ina wanan tunanen jjn kiran a wullakace yasani na dago kai ina kallonta tace ke kizo ana kira kina kyale mutane. Mu kizo ki karya ki tashi ki koma gidan ku kada kuma kizo nan ki sauke muna bala,in naki da yan uwanki ke kira maki bamuci bamusha a kan mu. Na mike da kyar ina daga jamila a kafafuna zuwa dakin ina tunanen abinda nai mata take fada min magana haka duk da karancin shekaruna amma na gane nufin ta. Kodana sa kai zan shiga dakin na samu mahaifiyarta na mata fada sosai tana fadin wallahi duk na kara jin wanan banzan kalamin a bakin wanin ku a dakin nan saina batawa maishi rai fiye da tsamanin ku. Na fada maku kubar wanan bakin camfin da baida dalili haka kawai mutum ya daukarwa kansa zunubi kan abinda bai shafeshi ba ya ara ya yafa son nemawa kai masifa. Hakkin makwabtaka ya hada mu dasu haka kuma yar uwantace karin hadin mu da ita har kuma ta kwanta dama ba abinda ya taba shiga tsakanin mu da ita na asha don me mu yanzun zamuki bayanta data bari kuma ? Aiko idan munyi hakan munzamo a cikin butullan duniya ke nan ganin na karasa shigowa dakin yasa matar yin shiru tana fadin Bintu zo zauna nan ki karya kinji. In kin gama sai a kaiki gida wurin yan uwanki kiyi hakkuri ki rungumi kaddara haka Allah ya nufa da rayuwanki ba zaki taso tare da yar uwanki mai kaunan ki ba . Ki daure ga duk abinda wani zai fada maki na mutuwae yarki ke dai ki bita da adduan alheri shi kadai ya rage yanzu a tsakani ku kuma nan dama gidane a gareki kome kike so kika rasa kizo nan ki sameni kinji. Hawaye na bakin ciki da nadaman dawowa na gida a wanan lokacin ya cika min zuciya har ban iya daukan hakan dole saina sako da hawaye ko zan danji sarari kasan zuciyar tawa a lokacin. Dan tsankwaran abincin nayi kadan nake fadin na koshi a marairaice ina kallon hjy tace to kin gama bari yayan naki ya shigo muyi magana dashi sai a kaiki gidan kinji tana min magana a cikin lumana da sanin ciwon kai. Ni ba zan koma ba hjy a nan zan zauna tare dasu jamal na fada a sanyaye tace Allah sarki Bintu nima ai banki hakan ba amma nasan halin yan uwan ku da tsegumi ai bamu rabu ba danan da can kamar gida dayane ai. Ina nan zaune a dakin sai tan gaisuwa ke faman shigowa don ta,aziya tayinda basu dadewa suke mikewa su fita zuwa dakin mama Laraba daga can kuma zasu tsaya su miko sai anjima ai masu godiya ta angode Allah bada lada. Ya habibine ya shigo shida abokinsa sani da mukazo tare dasu sai wasu abokansa na nan din a take aka fara mai gaisuwa ga wanda basu samu yi masa gaisuwa ba a lokacin. Har dai ya samu ya shigo dakin har lokacin damuwace karara a fuskanshi na rashin matarsa dayayi ni kaina duk da karancin shekaruna a lokacin nasan ya rasa mace tagari a rayuwansa don anty safiya mutum ce ta bugawa a jarida halinta na alheri ya bita inji manya. Mahmoud dama zancen yarinyar nan bintu ce wai ta tafi gida kada kuma suga rashin hankalin mu ga hakan ko wata yar uwar hjy din ta fada daga gefenta. Ya dan jiyo inda muke zaune har lokacin yaran dani kawai suke yarda yace haba mama hauwa kamar abin kora yanzu in ma nace ta tafi yanzu ku kanku ba zaku gane kan yaran nan ba ai don ko can da ita suka saba sosai komai itace meyi mata don ita safiyan ba damuwa tayi dasu ba tunda yarinyar ta dauka tana kuma yi tsakani da Allah. Yanzu ana rabasu wani fitina ne zai taso ba zaku gane kansu ba kuma to dama ai hakane idan uwa ta rasu tabar yaro kafin a saba sai ansha wahala sosai dasu balle su din daba zuwa gida kukeyi sosai ba dasu. Yace a dai barta har komai ya lafa tunda yanzu itama ai nan din ta saba dashi sosai fiye dacan a kaita yau din nan ya zama kamar kora gaskiya. Ai ina nan zan kwana biyu a garin nan in komai ya lafa sai a zauna ayi magana zaifi nan wanan maganan mayar dani gida ya mutu a lokacin har na dan sake jikina a gidan nasu ya habibi din. Akai sadakan uku na sati ya kewayo kowa ya watse ya zauna a gidansa cikin hakan naje gidan mu sau daya koshi da mahaifin mu ya shigo yiwasu hjy ta,aziya har cikin gidane ya ganni yace. Fatima kece nan aiko don ni kyaje gida ki ganmu indan ji sanyi a raina ko shine hjy tace kaganta nan ko a gidan nan daga dakin nan sai nan kofan daka ganta . Duk da yarinyace Bintu amma mutuwan nan ya daki yarinyar nan sosai wallahi wanan maganan ta baba shine mafarin zuwan mu gidan ni da yaran anty safiya din. Aiko ranan nayi dana sanin shiga gidan don duk yaran maman biyu suna gidan a lokacin ina shiga naga sun fara ja baya suna fita a dakin tare da fadin WATSAYYAHU ya tsaya a kanki . Naji anty Altine tace nace a raba yaran nan da bakar manyar yar nan suki koda yake yanzu aiba hasaransu bace idan ta cinyesu suba hasaransu bace tamuce muda zamu rasa abinda zamu gani mu tuna da yar uwan mu. Wasu hawaye ne masu dumi suka zubo min lokaci guda dama haka na tashi a cikin su zagi rankwashi da dundu ba irin wanda ban shashiba a wurinsu a baya yanzune da anty safiya ta daukeni komai ya rage. Sai lokaci maman biyu tayi magana tacw humm nidai ba inajin Mahmoud bane kawai dawai yake fadin sanadiyar ciwon cikine na ulcer yayi sanadin yata ba tunda ba yar dakinsu akaci ba. Nan kwana biyu zamuji ya kara aure muna kallo wata zata zo taci arzikinshi har ta mayar muna da yara marayu meye maza basu iyawa yanzu. Nidai da aka kashewa ya aini nayi hasara bashi ba ba uwarsa ba tun farko abinda nayiwa yarinyar nan ke nan gudu da zama da bakar dagan yarinyat nan mugun iri . Haka muka zauna da uwar yarinyar nan a gidan nan muna ganin bala,i iri iri saida su yahasu sukayi mata banga banga tabar gidan nan dama an sani a lokacin abar mata mugun abinta wai ya yanzu gashi ta zama muna mugun dahi a gida. Wanan da kuke gani watarana itace karan dafi a gidan nan don kisan karan dafi yafi dan dawan kashi amfani don zata zama maku ciwon ido a rayuwan ku tun yanzu ki duba yadda ta koma balle nan gaba idan ta girma. Kanwar maman biyu ke fadin wanan maganan tana kallona sai daga can anty Alawiya tace wanan abin banzan mama aiko idan ita karan dafi ce mu sayen ya banyane sai mu zuba dake mu gani manyar banza kaqai mai bakin gado. Haka zaki zauna yar banza kamar mujiya a cikin mu keda farin ciki har abada a rayuwan ki yadda uwarki tasa uwarmu kuka da hasara sai mun famshe haushin komai a kanki yar banza. Zaki bar kallona da idon nan naki kamar ta gwalaje yanzu na taso na halakaki a wurin nan kowa ya huta dake yar banza mai jinin banza kawai shegu jikan maya tsintattun mage . Sai maman biyu ta amsa da fadin ko magen ma na daji irin mugaye din nan da ake kira da magen daji masu mugun siffa dan Allah sake muna yara kar suma ki kama masu kurwa subi uwarsu inda kika aikata keda uwarki data baki mugun gado. A, a Fatima zahra yar ma,aikin Allah Allah ta nufa kin hakkura kin shigo gidan yau kai yaro dai yarone wai ita yar nan gida take gudu yanzu kamar an fada mata nan mutuwar take zaune. Kaiya dago ya bar kallo lokaci daya ya kallesu a cikin dakin saidai babu mai sauraren shi a lokacin ciki bandama bata rai da maman biyu tayi ta daure fuskanta tamau kamar bata taba dariya ba a duniya. Ganin hakan yace yaki Fatima zo nan zo kinji zo yar baba zo muje can wurina inji damuwan ki da sauri na tashi nabi bayan baba suma yaran suka biyoni a shimfidan da muka samu anyiwa anan muka zauna harshi. Baba ya kara min ta ,aziyan rashin anty safiya da mukayi inda ya nuna min ita kadaice mai tausayin shi ita kadai tasan damuwan shi a lokacin haka dai yayi tayi min bayaninta a cikin tausayi har idon shi yana tara ruwa yace badon komai sai daukan mike da tayi lokacin da nake cikin damuwa a kanki duk da nasan bada yardan uwarta dama ta daukeki ba fin karfin uwar kawai mukayi a lokacin. Tau fatima Allah bai nufi zaki rayuwa da yar uwanki ba a duniya nasan data share min hawayena a kanki yanzu dani dake duka sai muyi hakkuri don zaki komawa turkenki mai cabo da kika baro a baya. Duk da yanzu zakiga abin ya dawo maki sabo a rayuwan ki dana dauka zaman ki a wurin yar uwanki zai wanke komai azuciyar mutanen gidan nan amma yanzu na fahinci abin yana nan ba inda yaje a ransu ashe kanki. Fatima sai kin jajirce kin zama jaruma sosai a yanzu zaki ji dadin zama a tsakanin iyalina nasan kulba jima kulba dade zaki gama guje gujen ki ki dawo da zama gidan nan dole. Sai dai ina son kiyi hakkuri da duk wani sheri da zasu dagwara a kanki don kowan kansa ya sani da dansa keko a yanzu baki da kowa saini sai Allah don haka nake son , , , , baba wai ana maka sallama a waje inji malam liman shida wasu mutane. Wanan yasa ya katse fadin abinda zai fada min a lokacin ya tashi zuwa wurin su malam liman din dake masa sallama ya barni a zaune ganin furrow an maman Abida daga dakin ta ta watso ruwa kusa da inda muke zaune. Yasa nacewa yaran su tashi mu tafi gida muka fito babu sallama ga kowa a kofan gida na sallami baba muka wuce ya bini da kallo yana min addua a kasan ranshi. Satin ya habibi biyu a kaduna yayi shirin komawa wurin neman kudinshi inda yake black market na mai a can tsakani fatakwal da worri . Ana gobe zai komane ya samu baban mu da magana bayan sun gaisane da baba din yake fadin to baba ni zan koma wurin sana,ata amma nan zanbar yaran a wurin su hjy don bamu gama yanke shawara ba a kansu. Sai zancen Bintu kamar yadda marigayi taso riketa har aure nima insha Allahu haka nake son na karasa cika mata burin ta akan Bintu. Baba nayi alkawarin daukan nauyin karatun Bintu har zuwa aurenta don Allah baba a taimaka a barmin komai nata na rayuwa kai haba basai ka rokeni ba ai don wanan aikin ladane saboda kwadayin da matarka tayi ke nan da farko don fatima bata da maraba da maraye a duniyan nan sunan dai ni mahaifinta ina rayene kawai a duniyan nan. Nagode baba insha Allahu zan rika aiko da duk wani abin bukatunta a nan da yardan Allah kamar yadda zan dinga kula dasu jamal da yar uwanshi. Godiya sosai baba yai mashi ya habibi yake fadin na fadawa hjyn mu cewa ta dawo gida don ance su anty Altine sun fara korafi da rike ta can da mukayi a yanzu dama na bartane har yaran su saba dasu hjy don suji saukin rike min su har zuwa wani dan lokaci. Sosai baba yaji dadin wanan albishir da yaya yazo mashi dashi din muna barci yaya ya bar gida ya koma can Fatakwal shi kadai wanan karon ba tare damu ba. Saida muka tashi hjy ke fada muna tafiyan shi ta ban kudi me yawa bansan ko nawa bane dai a lokacin tace shiyace a bani na samu na zuwa makarantan da zan fara anam kaduna. ZAINAB IDRIS MAKAWA [7/25, 9:24 PM] +234 803 434 1977: KARAN DAFI 🌾 YAFI DAN DAWA AMAFANI 🌾 ZAINAB IDRIS MAKAWA 🌾 🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾 3️⃣ MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KUMA KIRAN WAYA AKIRA DA WANAN LAYIN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN AMANA A WURIN ALLAH , , , , , , , , Tafiyan yaya da kwana biyu Anty gajiye tazo gidan hjy ta sakani gaba zuwa gida dama kamar hjy tasan za ai hakan ranan da yaya ya tafi da yamma muna gyaran daki hjy ke fadim waini Bintu ? Saina juyo tace a ina dama kayan ki suke da kuke can nace da sauri nace lah hjy aini kayana a cikin ghana most go suke dama ssbbinne nake ajewa a wardrobe din dakin mu a kasa tace Allah sarki. To barin baki wancan tsohon akwatin nawa sai ki dinga saka dukkan tarkacen ki a ciki gashi yana da key dinsa da security kinga hakan ai yayi maki ko ? A cikin murna da jin dadi na zube kasa inawa hjyn godiya kamar yadda anty ta horar dani komai kankantan alheri gareni zanwa mutum godiya mai yawa sosai akan abinda ya bani. Haba dai Bintu kamar wace naba wani abu mai girma haka kike zabga min wanan godiyan nace anty tace wanda ya damu dakaine yake ma alheri a duniya don haka ka gode masa idan yai maka. Sai ta kara fadin lalai anty ki tayi gaskiya dama a can ajinki nawane nace biyu nake a inda nayi primary nan nake karatu saboda su Jamal yanzun da akasa tace. Amma dai karatun nan naki yayi sauri wallahi nace ai haka ko malaman mu suke fada a can amma idan sun gwadani sai suga ai zan iya su barni tace Allah sarki. Irin wanan tambaya da manya keyiwa yaro a cikin hikima don su fahinci wani abu a dangane da rayuwan yaro shi hjy ta dinga min lokaci lokaci a dan zamana a gidanta inda har ta fahinci irin rayuwan da mukeyi da yayyun nawa a can saidai nakan lura idan na bata amsa zatayi guntun murmushi tace Allah sarki Allah dai ya jikan safiya ko a hakan ai tayi kokari dake Bintu. Niko don jin adduan da takewa antyna din yasa kome ta tambayeni sai in dauka mekyau ne kai tsaye zan fada matashi don tayiwa anty din addua. Har yakai ranan da yamma kwatsam anty altine tayi sallama suka gaisa da kowa na gidan tace hjy gurinki nazo jin hakan yasa muka bar dakin bayan fitan mune tace nazo daukar Bantuce ta koma gida. Tunda nan din abinda ya kawota cikin ku Allah ya raba tsakani yanzu sai ta koma gidan ubanta ta zauna itama dan murmushin nan na hjy tayi tace. Allah sarki aida nan da can din duk dayane a wurin Allah Allah dai ya raya muna su yajikan yar uwarta da Rahama Amin dama kayan ta a shirye yake duk da ai da gidan ubansa yake takama kota koma can din ma aiko don yaran nan dake nan nasan zamuyi ta ganinta a nan ai saboda sun saba da juna sosai. Ni dai yanzu daukanta nazo ba wani magana ya kawoni ba aban ita in mayar da ita gidanmu shike nan kowa ya rike nasa da irin halinsa ai. Bintu kina inane hjy ta kwala min kira daga waje inda muke mugun wasa da sauran yaran gidan nasu da yanzu na saba dasu sosai. Na amsa na shigo ina sone kai don irim hararan da anty Altine take watsa min tun shigowanta gidan kafin hjy tayi magana tace. Ke kwaso kayanki mu koma gida tunda nan ba gidan ubanki bane yar iska mara zuciya mai bakin kwadayin banza kawai ke adole ga yar birni ko yanzu gudun gidanku kikeyi. Waike a dole kinje birni kinci jan miya to tsiyarki yasa mugun nufinki ya kashe mai baki jar miyan yanzu sai kwaso mu koma wanan gidan da kike gudu din nanne dai gidan naku yar banza mara zuciya. Ikon Allah Altine meya baku tunane kafin ku furta abu yanzu wanan yar ina tasan wanan maganganun da kike mata yakama ku sauwakawa rayuwan yar nan hakana don Allah. Bafa ita ta kawo kanta cikin ku ba Allah ne ya nufa saita fito a tsatson ku jini ya gauraya da anta hjy wanan bawai kake bane ko wani abu nake fadi abune da kowa ya sani a unguwar nan. Allah ya sauwaka bintu dauki kayanki gayancan ku tafi aiba a rabaki da yayanki ba ko yaushe ana tare da nan da can duk dayane ga Allah kiyi hakkuri kinji Allah yaiwa yarki rahama nace amin. Na dauki katon akwantin roban ja da yafi karfina a lokacin ina kokawan dorawa a kaina tace jeki in anjima dare yayi zanba su hayyatundeen su kawo maki akwatin har gida dauki dai wanan ledan ki tafi dashi. Haka muka fito da Anty Altine data sakani gaba da zagi na cin mutunci har gida muna tafe ina sharan hawaye. Muka shiga gidan naso ace baba na gida a lokacin saidai lokacin dawowanshi daga kasuwa baiyi ba don haka bamu sameshi a gida ba muna shiga tayi sallama take fadin ga bakar kaddaran nan naje na dawo da ita nan gidan yar banza kwadayayya. Su sun gujemu da nasu sai kece zaki likewa mutane a gida waike a dole kin samu wurin zama to dawo nan nan din shine gidan ubanki na yanka yar isa ita hjyn me tace dake ? Meko zatace min tunda ba ita ta haifeta ba itama ai munafunci yasa ta rike ta tunda sun rainawa mutane zaku hana muna yara kuma ku rike muna yarinya tunda yar banza bakin kwadayine gareta bata san ciwon kanta ba ko kadan ita ala dole ta bude ido da dadi yanzu. Sai yanzu na gane dalilin daukoni a cikin zafim rai da anty Altine tayi saboda sun roka a basu yaran anty safiya sun hana sunce diyansu ba zasu taso a gidan da babu tarbiya ba hjy ce zata rikesu duka . Haushim hakan yasa tayi min daukowan wullakanci tana dangwarana da kaya saman kai tana zagi har zuwa gidan mu din . Kowa na gidan yana tsaye waje a tsakar gida yana saurarenta kafin ta sauke numfashi tana dan waige waige tace a ina zata zauna ke nan a nan gidan. Da sauri mama uwa matar baba ta biyu ta juya zuwa dankin ta ta sake labulen kofanta na yadi mai launin pink colour tsofo tana gyarashi daga ciki. Daga bayana naji mama Lanto amaryansu a yanzu tace ina kuwa zata zauna banda dakin yaya don a nan ya dace ta zauna ai da ita tunda dama hannunta take ko can kafin a dauketa. Wa ni maman biyu ta fada da sauri tace Allah ya tsari gatari da saran kashi haka kawai zan dauki mugun abu na aje a dakina na halaka kaina da kaina da gangan ta shani yanzu nayi hankali ku barni da wanda akai min ya isheni miki a zuciyana. In ubanta ya dawo yasan inda zai sakata don ni nawama ya isheni yanzu to gata nan dai ni zan tafi inya dawo din kwasan yadda zakuyi da ita ni dai na dauko ta a can tunda ba gidan ubanta bane can din. Ganin sun barni tsaye sun fara tsabgansu yasa naja dan ledan dake hannuna na koma gefen turakan baba na zauna a saman ledan nawa baka dake dauke da yan sauran tarkacena a ciki ina kallon yadda rayuwan mutanen gidan namu ke tafiya a yanzu. Ita maman biyu itace uwar gida a gidan babana din itace me manyan diya shida mata Anty Altinece babba a dakinta sai Anty Atika sai antyna safiya sadiyan sai su yan biyun da yanzu basuyi aure ba suna makarantar kwanane su. Sai mama uwa dake da yara biyar da babana uku maza biyu mata mazan basu zama a gida tunda suka fara wayau suke fita koyon sana,an hannu idan sun dawo daga

Chapter 2 of 10