wajen juya Zainab da goje irin abinda ya fito daga gareta na Amai da Gudawa. Kai saida Mallam İbrahim yace da ita ta tafi kar Alhaji ya ga shiru bai ganta ba hankalinsa ya tashi. Sukai sallama ta tafi. Da ta isa, ta baiwa Alhaji labarin halin da Zainab ke ciki, yai Aľ'ajabi da niyar da safe zai je ya gaisheta.
Da gari ya waye sai ga Mallam Ibrahim yana sallama a gidan Alhaji Mai Waken, Allahu Akbar, Alhaji daga jin muryar sai ya saida, to amma yau ba sarka aka zo karba ba kuma ba tankiya aka zo yiba, Alkawarin Allah ne ya cika. Bayan da
Alhaji ya fito suka gaisa Mallam Ibrahim ya sanar mar da
cewa niyarsu kyakkyawa dai yanzu Allah bai yi ba saboda
kuwa Zainab Rai yai halinsa misalin karfe hudu na dare.
Yanzu ma am fara taruwa don jana'iza.
Mallam Ibrahim ya koma, shi ko Alhaji ya shiga cikin gida ya
kira Rufa'i ga Balki tana zaune ya sanar da su, haba nan da
nan sai Balki ta fashe da kuka, sai daki, ta dauko zani, Alhaji
yace da ita to haka zaki bi titi kina ihu sai kace wadda kura ta
koro, mutuwa fa kowa zai dandanata, na menene zakirinka
haka. Kije sai munzo. Ta tafi.
Shiko Rufa'i Alhaji yace dashi kayi hakuri kar ka daga
hankalinka. Duk abinda Allah yayi shine daidai, mahaifiya kan
56
1
α
e
iyilaια이
ih
mutu tabar jaririn da bai ko shekara ba, miji kan mutu ya bar
matarsa da ciki da 'ya'ya masu yawa, Sarki kan mutu ya bar
sarauta, don haka kayi hakuri, ka dinga yi mata addu'a, Allah
ya jikanta ya yafeta. Kuka kuma kan kara tsanani ne ga
mamaci, don haka kar ma ka fara kana namiji. Sai ya umarce
shi da ya tafi gidan Alhaji Usamatu ya sanar da shi. Yaje ya
biyo ta gidan kanwar uwar ya gaya mata.
Shiko Taja tun a unguwarsu yaji saboda akwai kanin uban
Zainab din acan don haka sai ya tafo. Nan dai aka taru aka
sallaci gawa aka je makabarta aka sitirta ta. Rufa'i na daga
cikin wadda suka sanya gawar Zainab cikin kabari. Aka dawo
zaman makoki. Duk wadda ya san Rufa'i sai yai masa taziya
ta musamman saboda rashinda yayi baya ga iyayenta. Akai
zama har na sati aka watse.
Anan ne Taja yake gayawa Rufa'i cewa Quirana ta bar garin.
Rufa yaii yoi murna da haka. Kuma ya fara tunanin Binta. Ita ko
Binta jhar ta riga ta yanke shawarar tafiya can gun wata
kanivar warta da ke aure a wani gari. Saboda kar asirinta ya
tond in thje can in da halin zubarwa sai a zubar. To duk Rufa'i
da qja basu da labarin haka. Amma Zaliha ta san kome.
Bayan lokaci mai tsawo, sai Alhaji Usamatu ya kira Rufa'i don
ya tun tube shi batun yarinyar da yaji labarin yana nema ada,
wato Binta. To a nan ne Rufa'i ya sanar da shi cewa sai ya zo
ya bincika.
To da yazo ya sanar da Taja batun wannan magana sai suka
je gidan su Zatiha saboda tun da tazo tai masa ta'aziyya basu
sake sadpwa ba, bare ma suyi zancen. Anan ne suka ji cewa
57
Binta tayi tafiya. Taja ya tambayi Zaliha batun auren Binta da
Rufa'i, sai Zaliha tai ajiyar zuciya, wannan sai ya baiwa Rufa'i
wani irin tunanin ko menene ya faru? Zaliha ta nuna babu
kome amma dal akwai wani abu a yadda suka fahinceta.
Sukai sallama akan sai in Binta ta dawo. To labarin dai da
Rufa'i ya sanar a gidansu kenan cewa sai Binta ta dawo.
58
KASHI NA GOMA
Daga cikin wadda suka zo ta aziyyar Zainab har akwai wani
abokin Rufa'i wadda yake can wani Birni na Uku mafi girma a
kasar, yana aiki a wata ma'aikatar harkokin kasashen waje.
To shine yake tun tubar Rufa'i batun kome yakeyi yanzu? Ya
bashi duk labarin halin da yake ciki na rashin aiki, sai shi
abokin nasa ya nemi da ya rubuta takardar neman aiki ya
hada da takardunsa na shaidar kare karatu don ya tafi dasu.
Don akwai wani kamfanin gine-gine da sauran aiyuka, na
kokarin kara ma'aikata saboda wata kwangila da ya samu ta
gina tagwayen hanyoyi a kasar. Haka akayi, Rufa'i ya rubuta,
ya bashi, shi kuma ya tafi dasu.
Rufa'i dai na nan yana jiran dawo war Binta, sai wata rana
Taja yake dan tsokala masa labarin da yajikishin kishin dinsa
a cikin gari game da Binta. Cewa Eskep ya gudu ne saboda
caiki da yai wa wata yarinya, har ma ya tafi da wasu kayan
jama'a. Taja da yai bincike sai yaji ashe Binta ce. To amma bai
yarda ba, akan sai ya tambayi Zaliha. Rufa'i da yaji haka sai
ya tuna lokacin da suka je gun Zaliha, wannan magana ta sa
Rufa'i cikin zulumi da tunanin yaya matsayin rayuwarsa ne?
Menene rashin nasararsa akan aľamuransa ne? Yanzu me
zai fada a gida in har an tabbatar Binta tayi ciki, wace hanya
zai bi, yana cikin irin wannan tunani, sai Taja yace dashi "yau
muje gun Zaliha!' Rufa'i ya yarda, Sai Suka tafi dare
yayi suje gidan su Zaliha. Da isarsu kofar gidan su Zaliha sai
sukai sa'a ga mahaifin ta ya dawo daga unguwa zai shiga
gida, to dama yana ganin Taja a wurin da suka gaisa sai ya
shige ciki. Kawai sai ga Zaliha ta fito ya turo ta.
59
Suka gaisą aka fara tadi kamar yadda aka saba. Can sai Taja ya ce "Zaliha a gaskiya, ranar wanka ba boyon cibi,kuma duk
mutumin daya taka ka gaya mar cewa ka takani, to abinda nake so dake, tunda tsakaninmu akwai cin amana da rufa, to fa ba zamu je ko ina ba. Kuma tsakanin mu sai dai sakayyar Allah". Zaliha sai tai farat ta dafa kirji tace me ya faru? Rufa'i ya sa baki yace "Batun Binta ne kuma kin san kome amma kika rufe mu, to amma alhamdu lil lahi tunda Allah ya buda
mana mum ji, kuma mun gani", Taja ya kara da cewa "kuma bamu.baku".
Zaliha kanta ya kulle duk ta fahimci manufarsu. To amma sai tai tawili ta dage tace, "kash! ana dara ga dare yayi, ni baku cemin ga irin abinda mukai muku ba kawai sai fada haka, ai sai kuce munyi muku kaza da kaza amma kuna magana a
fakaice sai kace kuna tsoro. Taja sai ransa ya baci ya ce a
fusace "Tsoron wa? Allah ya sauwake, saya wa ne kawai muke yi saboda kin san kome duk abinda muke nufi, amma bari ai miki gwari gwari; Binta cikine daita tun wata uku da suka wuce, shiya sa ma ta bar garin yanzu. Kuma munsan wadda yai mata. Kuma in gayamiki gaskiya, tunda abokin barawo, barowo ne to ni kema gari zamu raba, Rufa'i sai yace "a'a ba za'ayi haka ba. Kai dai tunda mun nuna mata laifinta sai ai hakuri". Binta tace "to wai ni ina ma zansan wannan
abu, ba gaya mun za tayi ba, ba gani nayi ba, to ina zan sani?"
Taja sai ya kauda kai yace "kya gayawa yaran gidaku ko zasu yarda. Amma ba mu ba! Nan dai sukai sallama, suka tafi.
Suna tafiya suna mahawara Rufa'i yace da Taja na tabbatar
ta sani, saboda ai kaga bata karya ta ba, sai kawai ta nuna
60
bata sani ba. Kuma ba tai mamakin jin cewa Binta tayi ciki ba.
Kuma abinda nake so da kai kar ka kuskura kace zaka rabu
da ita in ma tana iskancin dai to ya rage nata, duk tsuntsun da
kaja ruwa shi ruwa kan doka, kuma wannan ya isheta ishara,
in kace wata zaka nema ma to duk dai gautar jace, matsalar
wahalar auren nan saboda tsarabe tsarabe da kage kage da
sai nayl irin na wane suke hana auren, rashin auren kuma ya
haifar da zinace zinacen, Allah ya sauwake", Taja yace "Amin",
sukon
tun daga nan dai Rufa'i yai ta ko karin sasanta tsakanin Taja
da Zalita har ya ci našara. Shikuma ya sharar da batun Binta,
kai koma tunanin ta baya yi. Kuma ya sanar da mahaifiyarsa
labarin itama tai bakin ciki da wannan al'amari.
Shi kuma Rufai ya kudiri aniya ba zai sake neman aure a
wannan gari nasu ba, sai ko in kar yai auren kwata kwata.
Bisa wannan ra'ayi ko niya ta Rufa'i sai Taja yai ta bashi
shawara da Nasiha kan cewa ya dau hakuri da duk abinda
ya faru saboda yárda da kaddara wani rukuni ne na imani.to
duk da haka dai kuttum tunanin Rufa'i Allah ya kawo hanyar
da zai bar garinma, kullum yai sallah bayan yayi addu'a ga
iyayensa, addu'arsa, wani alheri yazo ga fiddashi daga garin,
kuma ya sami wata matar a can ta gari.
Allah maji roko a karshe dai wannan kamfani da aka kai
takardunsa suka nemi da yaje ganawa linterview). Bayan
kamar wata biyu sai ga takardar daukan aiki da albashi mai
tsoka. lyayen sa, 'yan'uwa da abokan arziki sukai ta masa
murnar samun aiki ya tafi. A karshe dai a can Rufa'i yai
aurensa da wata mai suna Sa'a cikinsa'a.
61
TSOKACI
Kai! kai! a'a kada kai haka mana ai rayuwa ta yau hakuri akeyi da ita....... Rufa'i sai bai kai marin ba ya kyale. To amma
ina ita Zainab bata daina zagin saba....... Nan da nan bai san lokacin da ya wanke ta da mari gaba da baya ba.
Rannan Mallam Ibrahim suna kwance a daki da matarsa Daso sai ya tuntube ta akan yaya ta gani akan ya aurar wa dan Alhaji Mai Wake Zainab wato Rufa'i.?
To shi dai Rufa'i sai ya shiga cikin wata irin dimuwa ta me ya kamata yayi a wannan hali na raguwarsa.
Shiko Dious' shine suke jin mai basu abin da suke so
na duniya na daga Arziki, sarauta, shugabanci, ilmi, farin jini, kwarjini, da dai duk irin abinda suke da niyya a zuciyar
kowannen su 'yan kungiyar.
...Shiga kungiyar sai an sadaukar da wani abu da mutum
yafi so fiye da kome. Kamar Uba, Uwa, da ko kai ko kuma
mata.
α
a
U
li
C
C
ג
1
62
ב
느
FASSARAR YAREN DA KUNGIYAR ASIRI TA KU KLUX KLAN KE Y
Ilamor
Hora
Dunga/Dene
Dia Dia
Caida Bajo
Hurra Good DiousDious
Kada boka centro palour
Kamar Sallama ce
Wanene?
Inkiya ce
Barka dai
Ku shigo
Barka da zuwa da kyau diyos
Sunan babban abinda suke wa biyayya
-
(jagoransu)
Kada tenermala vestido piernaless
Kowa ya shigo ciki falon shiri.
Vestido blanco piernaless figuras difanto
Mezclar bloo de vinor
Vinor
Kada Vra Vaso
Alegrar! Agua
Nor kada alma kambiar Diabla
Lete cualquira cengeri
Kowa ya canza kaya rabi
da rabi
Fararen kaya da takalmi
daya, kuma mu dauka
muma mace.
Ku gauraya jininku da vinor
Ruwan jiri (kamar giyace rin ta wiski)
Kowa ya dauki kofi
Hada kofi da na dan uwanka ana
shewa in za'a sha wani abiu
(turawane kanyi) wato fos.
Yanzu kowa ya zama
dodo (abin tsoro)
a iya wake gaba daya, kada
comida willow hehe, kada Agua
ra baber hehe'-'Kowa yaci
tsutsarsa da farin ciki, kowa ya
sha abinshan sa da farin ciki (waka ce) Lete praya wisho Ciego - ma iya addu'a ido rufe (ta abin da muke so) Secre Buenos A bayar abin sadaka (cikin addu'ar) kenan Madre - uwa, Los - da, Marido - mata, hamono - aboki hijo - uba
63
Kada nadar gymnasia domir - kowa ya makale (kamar jemage) ayi
barci (barcin fita shan jini).
A mino Vuelo lo cielo willow - Ruhin (kurwa) ya fita zuwa duniyar jini
Vueta mundo - Mu koma
Despido comrades ir
Diu Diu onoinly
da tsutsa
Abokai mu watse sai wata rana
Hankali da Albasa fa.
Mu hadu a littafi na uku
In da zamu ji yadda Rufa'i ya kare da sauran rayuwarsa a
can Abuja da abokanan aikinsa gami da iyalansa da sauran
mutanen da ya saba da su a Abujan. Da yadda a chan
garinsu ya share tsakaninsa da su. Dadin dadawa da
kuma tsohuwar dangantakarsa da 'yan kungiyar asiri.
69
Printed by:-
ADAMU NAMAAJ PRINTING PRESS
173 Ita Waziri Rd., Brd Lane Off Zoo Rd.. P. O. Воx 1395. Kano.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels