bude da zage zagen hakora, sai shugaba ya sake bada oda da cewa "Animo Vuelo lo Cielo Willow ma'ana ruhinsu yai fiffike zuwa duniyar tsutsa dajini. Shike nan to fa duk wadda aka ambaci sunansa a daren nan
to babu shi sai in yana tare da abinda basa so kamar warin
albasa, tafarnuwa, ko kayan yaji, ko kuma ambaton Allah da
karatun Al-kurani. Sannan basu son dumin wuta da hayaki. Basu kuma son barkono da kamshin zaitun. Haka basu
samun wadda yake farke don idonsu bai iya ganin su. Suna ganin mai barci ne don shima ya shiga duniyar linkaya ta
mafarki. To anan suke haduwa a tsotse jini, shike nan sai
kaga mutum ya wuce ta can ko ya kamu da cuta, sukai ta
shan wadda suka samu a wannan dare.
To Rufa'i dai gudun mawarsa bata samu ba don sunje gidan Alhajin amma sai kamshin zaitun na carbin da Alhajin yake ja
a lokacin ya hana su shiga, gashi kuma yana ta lazimi domin abinda ya saba yi kenan kullum dare. Sannan yana da niyar addu'a ga Rufa'i akan Allah ya juyo zuciyarsa akan kar ya basu kunya. Badon kome ba sai don kawai son da yake masa, ya 42
A
dauke shi tamkar shine ya haifeshi don bashi da da. Suka
zaga suka zaga amma ina? Rufa'i ya leka ya duba babu
alamar Alhaji sai dai ya kan ga kamar ya wulga to sai ya bace
to ashe gyangyadi Alhaji yakeyi. Rufa'i kuma baiga iyayensa
ba, saboda ba suyi barci ba. Yai fushi, yai wani gunji wadda
uban har ya sunkuya zai masa tofi sai da ya tsorita. Mahaifiyarsa sai
idonta ya fara hawaye tana ta shafansa, tana al'ajabi.
To a ka'idarsu in akai fita uku ba'asha jinin abinda ka bayar
ba to za'a shanye naka ne. To Rufa'i anyi fita biyu da shi
kenan. Don haka shine yai fushi. Nan da nan sai shugaba
yace "vueta mundo"wato mukoma duniya. Nan da nan sai
kowa ya bode ido" shugaba ya ce kuma "Despido comrades
ir" ma'ana abokai sai wata rana sai an jima kowa sai yace
"Good Dious" sai ya fado daga sama, kamarsa kuma ta dawo
amma cikin wannan fuskar robar yana ta iyo a sarari kamar
tsuntsu, kan hanyar komawa daga yadda suka taso, suna
cewa ga junansu, "Diu Diu Onioly" wato hankali da albasa fa!
Kowa sai ya koma gurbin da yake fara tasowa, a ko ina ne
kuma kome nisa cikin lakaci kadan zai isa. To sai anan ne
Rufa'i ya gane Quiranan, shikenan sai suka sauko suka kama
hanyar gida, sai take ce masa haba Rufa'i yaya kake magana
biyu ne? da, kace babanka, kuma ka dawo cewa abokinshi,
wannan ya jawo maka faduwa fa, nan gaba in bamu kama
ba kaga zamu rabu da kai kenan, sai ya ce ba kome zamu
kama, Quirana tace wa din? Sai yace Usamatu, nan ma sai
uban yaji an ambaci Usamatu, sai yace, "Rufa'i! Rufa'i!!" ya
girgizashi sai akai sa'a Rufa'i ya dawo sai ya tashi firgigi sai
yaga mahaifinsa a tsaye a kansa da carbi, uwarsa kuma tana
zaune a bisa kujera tana gyangyadi, sai ya tsorita, zuciyarsa
ta yanke, idanuwansa sunyi jazur, sai uban yace 'yaya ka kara
ji? uwar tace dan nan ka bamu tsoro. Sannu, yace "sannu".
43
KASHI NA TAKWAS
Anan ne dai Rufa'i ya basu labarin irin halinda yake ciki tun
daga farko har karshe. Uban yai ta mamakin irin wannan
al'amari uwar ma ta tambayi ko menene kuma kungiyar asiri.
Dukkaninsu suka la'anci irin wannan ta'ada. A ka'idar wannan
kungiya ta su Rufa'i kuwa ba'a fada ma wani ko nuna alamar
al'amuran kungiyar, in kuma kayi daya daga ciki to a bakin
ranka ne. To sai gashi Rufa'i dangane da irin tambayoyi irin na
hikima da takurawa da mahaifinsa ya masa shine bai san
lokacin da ya fede biri har wutsiyarba. Saboda uban ya tsorita
kan cewa in mayu ne suka kamashi kamar yadda uwar tace,
to yaya zai rinka kiran Alhaji Usamatu? bayan haka kuma in
cuta ce ai jikinsa babu zazzabi, in kuma kwaya ya sha yaya
haka farat zai mike, kuma cikin hankalinsa? To wannan shi ya
baiwa uban damar sai ya tsaya ya bincike shi, nan ne sukai
tayi har akai assalatu ya tafi masallaci. To uwar ma ta gamsu
da taji yadda abin yake sai ta tuna cewa akwai lokacin da yaci
albasa yayi amai saboda haka fur ya hanata yin abinci da albasa.
Sannan kuma tana ganin yana kinyin salla akan kari kuma yakan yi
wani yare jifa jifa. Da dai abubuwa iri-iri, sukai ta al'ajabin wannan
al'amari. Sannan da tunanin hanyar da za'a fito ayi maganin hakan.
Rufa'i kuma sai zulumi, me zai faru dashi nan gaba yake yi,
tsakaninsa da jama'arsa. Duk abinda daya yayi a ko inane
sauran zasu sani, saboda sun sha jinin juna kuma sun zama
daya. Cikin daren sha hudu nako wane wata dama suke fita
don haka sai wani watan zasu zo mar ke nan.
Alhaji dai haka ya kwashe duk wannan labari ya kaiwa Alhaji
Usamatu. Shima yai mamaki kuma yai addu'ar Allah ya kawo
44
sauki. To sai dai kuma basu san raayin Rufa'i akan batun
auren ba, shi yasa Mallam Ibrahim bai ji ko duriyar su ba. Kuma shima bai tuntube su ba.
Wataran da daddare, Alhaji ya kira Rufa'i ya tursa shi kan sai
ya yarda da batun auren Zainab, shiko sai ya fito ya bashi
labarin tsakaninsa da Quirana da alkawarin da sukayi. Alhaji
ya shure wannan magana. Kuma yai masa tankiyar kar ya
sake alaka do ita har abada. Kuma in yayi to zasu sa kafar
wando guda, yai barazanar zai tsine masa. Rufa'i da ya ga
ran uban ya baci sai yace ya yarda. Amma a gaskiya zuciyar
sa bata yarda ba.
To a daren ne fa Quirana ta zomasa kamar yadda ta saba.
Rufa'i dai ga ci ga rashi, yana tuna managar uban kuma yana
tuna Quirana, da ya tuna cewa ai kuma yanzu ya zama nama
ga sauran 'yan kungiyar sai ya baiyana mata cewa yanzu tayi
hakuri don ya canza shawara. Jin haka sai Quirana ranta ya
baci ta juya kamar zata tafi sai ta waigo da wata irin
mummunar fuskar da Rufa'i bai taba gani ba koda a can
duniyarsu ta tsafi. Saboda hancinta da ya zazzabo kai kace
liko take furawa, kumatunta kuwa sunyi fulu fulu kamar
balobalo, sannan wuya kamar sillen kara; sai katon kai da yafi
tulu kuma ba gashi, tace ani ko'? Zaka gani! Kasancewar
Rufa'i bai shiga sulke ba irin nasu wato wannan fuska da suke
sawa a can duniyar sai ya tsorita. Wannan shi yasa yai lhu
mai tsanani, kawai sai ta juya ta tafi. Ihun da Rufa'i yai shi ya
tada uwar sai ta fito da sauri ta nufi dakinsa. Dama dakin
yana can kusurwar gidan ta barin yamma, kuma an kewaye
gaban da 'yar katanga wadda sai an za gaya ta sannan a
shiga dakin. Da 'yan shuke shuken fulawa da furaini irinsu biribis, Barbados da ros a gaban dakin. Balki da ta shiga sai
45
ta tarar da shi yana motsi bisa gado tai kira shiru sai ta tabashi sannan ya firgita, zubur ya mike. Uwar tace 'yaya, sai ya gaya mata abinda ya faru. To ashe uban ma yaji fitarta da Ihun sai yazo, sai yace da shi ya karanta Salatin Annabi uku, Inna Lillahi goma sha daya, La'ilaha Illa Lahu goma sha daya sannan ya karanta kula'uzai da qul huwa uku, ya kwanta. Kuma kullum kar ya rabu da karanta wannan abu iya gwargwado, kuma a ko'ina yake. To haka dai Rufa'i yai tayi, kuma sai ya shiga cin tafarnuwa da albasa lokaci, lokaci har ya saba. Zikiri kuwa kamar Liman. Shiko Taja da yaji abinda ya faru da Rufa'i sai yai ta masa Addu'a kuma ya bar abin a
cikinsa bai furtawa kowa ba shima. Haka dai har lokaci mai
tsawo. Tajan yana matsawa akan suje ido da ido gun Quirana
amma Rufa'i yaki.
Dangane da yardar Rufa'i akan auren Zainab sai aka sanar da Baban ta Mallam Ibrahim. Shikuma ya bada dama ga
Rufa'i akan duk lokacin da yaje zance to ya shiga cikin gidan
abinsa. Shiko Alhaji Usamatu tuni har ya fara tunanin gidan
da zai bashi a gidajensa dake kusa, to babu, don duk a gefen
garin suke, shima kuma Alhaji Mai Wake yana tunanin ko ya
gyara masa dakinsa ne koko ya saya masa wani a kusa
domin gina wani zai dauki lokaci, kuma ga dukkan alamu
Mallam Ibrahim a shirye yake. To akarshe dai suka zantu sai
Alhaji Usamatu ya hakura akan Mai wake ya sai gidan.
hakanne ta faru, amma sabon gidan da aka saya na da dan
nisa da ainihin gidan nasu. Gidane dan karami na maigida
daya da matarsa. Domin dakuna biyu ne kawai a hade, ciki
da falo. gami da bandaki hade da falo wadda kofarsa ta cikin
falon take, sai kuma 'yan zauruka biyu na kicin da dakin ajiya.
To amma a kwai fili mai dan fadi wadda za'a'iya gina wasu
dakuna guda biyu manya daidai da nada. Akwai fanfo, wuta
46
da kome na kawa, kai harda ma alamar mashukar fulawa kewaye da katanga. Sai kuma irin matarar ruwa (tanki obahed) da akan dora sama da daki domin amfanin cikin
gida da sarga irin ta sink da shawa ta wanka. Rufa'i bai san
da wannan gida ba, ammam mahaifiyarsa taji cewa an saya
masa.
Yana nan yana tunanin yadda zai fito wa wannan matsala,
ga shawarar Taja dai yaje gun Zainab yai ta zance kawai,
yayi yayi dashi suje amma yaki. Ga shawarar uwarsa kuwa ya
cigaba da zuwa amma zata san yadda za'a raba abin koda
malamai, kuma tana son Binta don shi Rufa'i ya bata labarin
Bintar da abinda ya faru tsakaninsu.
Rufa'i sai ya dauki ra'ayin uwarsa. Ranar nan da la'asar sai yai
tunanin da ya fara zuwa gun Zainab, ita ma ta san kome
dama. Tunda uwarta ta gaya mata cewa babanta yace ya
nema mata miji sai ta yarda. Harma tace da uwar ai akwai
Hadisin da yake cewa bazawara ita ke da Hakkin kanta,
budurwa kuma iyayenta. Dadin dadawa kuma dama ta gaji
da zaman gida, tana son auren amma Allah bai kawo shi ba.
Sannan kuma da taji Rufa'i ne sai ta amince Hani'an ba gardama, kuma sauraron zuwansa takeyi kullum amma shiru.
To da yaje sai yaki shiga kamar yadda akai masa izini ya tura
yaro. Zainab sai tace yaron yazo yace wai baza ta zoba. Rufa'i
da yaji haka sai yai mamaki, yace da yaron yakoma yace inji dai Rufa'i ne, sai ta aiko da cewa ai dama ta sani, bata da
lokaci ne kawai, Rufa'i yai shiru yace to! Wato wannan taji
nace bana sontane take so ta min walakanci, ko kuma taji
labarin da na shiga kungiyar asirine. Haka dai yana tunani,
sai ya ce "kai bata isa ba" sai ta soni sai ya kada kai ya
tafi. bayan kwana biyu ya koma Zainab dai bata canza
47
ra'ayinta ba, ta bada amsa irinta rannan. Rufa'i fa sai hankali
ya tashi, ya koma gida sai tunanin wannan al'amari yake yi. Yanzu ya manta da itane? to amma ai taci nasara akansa
kenan, to yaya zasu hadu ya ga karyarta yana ta tunani. Duk da haka bai sanar da kowa abinda ke faruwa ba. Duk kowa
na ganin cewa yana zuwa suna hira sosai da Zainab.
Rannan yaje unguwar su Taja gun da suke zama sai ga Zainab da wasu abokanta sun wuce, Rufa'i ya ganta amma
ita bata ganshiba saboda yana daga karshen kudune a
zaune. Shiko Taja bai santa bama sosai bare ya ganeta. Suna
nan har kusan magrib Rufa'i na cewa zai tafi gida Taja na
cewa ya tsaya suyi sallah tukun, sai ga can Zainab ta bullo ita
daya, Rufa'i da ya hangota sai yace da Taja ka ganta nan
tafe"Taja yace wace fa?" Rufa'i yace "Zainab din mana 'yar
yawa" Taja sai ya sake hangota yace kodai dan 'yawa, ai
wallahi wannan in kabarta kabar banza, hadaddiyar dem irin
wannan, ai ban san haka take ba. Don Allah kayi mata
magana', Rufa'i yace haba, ai bazata sauraren ba don naje
sau biyu ta bonsa ni. Taja yace To wallahi ni zammata".
Sauran abokansu sai dariya suke tayi, suna dan hangen
Zainab tana tafowa, Rufa'i zuciyarsa tana ta bugawa.
To ita ko kafin ta iso ta fahimci akwai wani abu don taga
kallon yai yawa, har ma tai sassarfa. Yuu da tayi da ido sai taga
Rufa'i sukai cul da cul sai ta kauda kai ta wuce. Dama ta can gefen
hanya take. Taja sai ya tashi ya bita Rufa'i ya biyoshi, yace Hajiya
Zainab"kamar dama tasan suna zuwa sai tace "a'a, Zainab din dai.
Sai ta tsaya. Su kuma sauran duk suna ta kallonsu. Taja yace ai im
ba busa sai a daga hannu", Zainab tace ana me? Rufa'i sai ya
karbe, yace ana zumunci, mutunci da kuma......"sai tace kuma me?
Fadi man muji, sai yace soyanci" Zainab tace "banga ne ba soyanci?
48
wani yare ne? ko karatu? Sai yace eh yare ne na soyayya
kuma karatu ne na biyayya? Sai tace, iunda yaren masoyane
ai sai a gayawa masoya? Anan Taja sai yace Hakika ai
masoyanne yan zuma suke yarawa?"Zainab sai tace uhm
makiya dai", Rufa'i sai yace sai dai inke ce mai ki ni masoyine!
Sai tace na wa"? Rufa'i yace naki' Taja sai ya ce "kwarai tunda
ya furta, Zainab tace to ai ni banga alama ba', Rufa'i yace,
eh! to! baki zoba shiyasa aida kingani kuma koda yau zaki zo
in rnunje, to zaki ga alamar? Zainab tai murmushi a ranta
tana cewa ha! kace ba kai ba, da saura ma tukun! Sai tace
Allah ya kaimu", suka ce amin'. Ta kama hanya zata tafi sai ta
juyo tace da Taja "Mallam baka gayamin sunanka ba, Rufa'i
sai yai farat yace eh don Allah kiyi hakuri, ban gabatar miki da
shi ba sunansa Tajuddeen Tijani ko kuma T.T" sai tai
murmushi tace sai an jima ta tafi. Su Rufa'i aka tafa hannu ana
dariya tuni kuma har anyi sallar Magrib suna hira. Sukai sallah
suka ci abinci ya dan afa tafarnuwa, kamar yadda ya saba.
Suka nufo unguwarsu Rufa'i tare.
49
KASHI NA TARA
Anan kofar gidansu Zainab, Rufa'i da Taja suna jiranta ta fito,
Taja sai yace da Rufa'i "ah! kaga da muntafo da katin nan,
koda yake ma ya wuce, kasan su Binta ma sai washe garin
Valentin din na basu?" Rufa'i sai yace "kai kuwa! ina ruwan kifi
da rigar ruwa? me ya hada eli da valentin? Ta san maka
amfanin katin? Taja yace "ai wai dan tukwici ne", Suna cikin
haka sai ga Zainab ta fito tare daʼyar yarinya, kafin ta nufo su
sai kamshin turaren da ta sa ya bugesu, Taja sai yace "uhm!
lalle!" Zainab dai sanin cewa zatayi baki, hatta kayan da tasa
da la'asar ta canzasu. Ta sako irin duguwar rigarnan mai
suna Hijab da kuma farin gyale ta yafashi a kafardarta ya rufe
kirjinta. Dan kwalinta kuwa tayi masa daurin kimar wato
hannayensa ta dauresu ta karkashin habarta. Sai ta nufosu,
tai sallama suka amsa. Ta zauna. Bayan duk tabi su da
daddaya sun gaisa sai akai dan shiru na dan lokaci. Can
Rufa'i sai yace, "mun cika alkawari?" Zainab sai ta amsa masa
da cewa kadan ba!" Taja sai yace "ea! Zainab yaya kadan?
Zainab tace "ah! kabarni da shi mana", Rufa'i sai yace "to ya
barmun mana, nidai nasan alkawari na na cikashi, sai dai
kece ma baki cikashi sosai ba". Zainab sai tace "to naji abar
wannan zancen". Taja sai yace to wane zancen za'ayidaya fi
wannan din. Haka dai sukaita zancen shega kai kaсе
calikawa ne irin na fin din Indiya. Ba suyi wani zancen
soyayyaba har dare yayi sukai sallama.
Rufa'i yai mata kyauta, sai taki karba, yayi, yayi taki, sai ya dan
baiwa yarinyar da ta rako ta. Yayin da Rufa'i ya dan yi tattaki
ga Taja sai suka tsaya suna tattaunawa, Taja yace "na tabbatar
wannan yarinyar tana sonka kwarai", Rufa'i yace "ai nima yanzu
naji kuma gaba daya tana shiga raina wallahi". Taja yace "ai kayi
50
스
sa'ar mata don agaskiya bata da makusa. Ga kyau, ga hali
ga ilmi to kuma me yarage? Arziki kuwa na Allah ne". Nan dai
suka rabu kowa ya tafi gida.
Haka nan dai Rufa'i yai ta zuwa gidan su Zainab suna hira
wata rana da Taja wata rana shi kaďai ko kuma da sauran
abokansa dake unguwarsu, har dai aka aiko gidansu Rufa'ї
cewa ambashi Zainab, amma za'asa ranar biki nan gaba,
saboda shi Mallam Ibrahim ya sanar da Alhaji Usamatu cewa
kar su aiko kome da ake yi. Bukata dai son yaro da yarinya, to
ga dukkan alamu sun shirya. Shiya sa aka aiko cewa am
bashi ita.
Ita ko Quirana, ganin Rufa'i ya shiga mata duhu saboda
tsabar tasbihi da Hailala da zikiri da yakeyi ga kuma dan
karen cin albasa da tafarnuwa da shike dama da niyar
hakan yake yi sai ta hakura. Suma 'yan uwanta sun rasa
hanyar da zasu fito masa, saboda foton da ke manne a
dakinsa ya cire ya kona, dama shine kamar shaidar
mambarsu., sannan kuma a zahiri ya kaurace mata baya
zuwa gidansu, dake unguwar 'yan sanda. Ita ma kuma sai ta
fara tsorita dashi. Allah gatan kowa. Kai in gajarce maka
labari Quirana dai barin garin Fatara tayi kwata-kwata,
saboda tasan abin zai komo kanta tunda itace musabbabin
shigar Rufa'i wannan kungiya. Haka ta kare, domin kashet.
za suyi. Rabuwar Rufa'i da muguwa Quirana kenan.
Labari ya bazu cewa Rufa'i zai auri Zainab, har ya kai kunnen,
Binta wadda ita bata san ma akwai wata mace da Rufa'i yake
kulawa ba. Da taji wannan labari tayi bakin ciki matua,
saboda burinta bai cika ba. Dama haka yake duk wadda yake
da mungun nufi ga wani, koda Allah ya bashi sa'a, a karshe
51
sai ya koma kansa. Ko kuma Allah ya kiyaye wadda aka nufa
din. To ita Binta dai ashe juna ne da ita. Tun lokacin da ta
tabbatar ta samu ciki sai ta gayawa shi Sekiap cewa ga halin
da take ciki. Dama tun lokacin da suka sadu a 'me and you
photo studio yayin da taje daukan photo lokacin sallar idi ya
sa aka dauketa kyauta, kai har ma ya bata damar duk lokacin
da taken son dauka kawai tazo ta dauka, a matsayinsa na
abokin mai daukan photon. To shi Sekiap wadda akafi sani da
eskep mutumin jihar Bayelsa ne dan yaren tsigira.
Dama Binta kan je gidansa. Ta fura zuwa gidan ne ta sanadin
karbowa photo da ta dauka, shi kuma ya karba da nufin in
tazo a turata gidan nasa. Tun daga wannan ranar eskep ya
san Binta 'ya mace, a takaice ma dai shine ya kawar mata da
budurci. Ya aza harsashi bata mata rayuwa. Kuda wajen
kwadayi akan mutu. Haka Binta ta dinga satan jiki tana zuwa domin
ta samo irin abinda yake bata na bajinta. Da ta gaya masa nefa
cewa tayi ciki sai yai mata alkawarin zai aureta, ina! kan kace me, ya
tattara'yan kayan gyaransa ya gudu. Dama bakanike ne na babur.
To daga nan ne fa Binta ta rasa makama, har taci karo da
Rufa'i. Ta so ta rufeshi. Mahaifiyarta ta sani amma uban bai
san kome a game da maganar ba. Zaliha ma tasan kome
amma saboda kunya, kawaici da zumunci irin na mata sai ta
bakam kuma ake hada baki da ita. Binta dai bakin cikin ta,
asirinta sai ya tonu, tunda shi kadai din da take gadara dashi
gashi ya kubuce A duk lokacin da tazo kwanciya sai tayi kuka
da hawaye tana mai nada mar abinda tayi. Kuma tana ta
sake saken hanyar da zata bi. Ta gudu ne! kashe kanta
zatayi? a'a zubarwane? duk abinda ta tuna sai taga ai tamkar
ta tona asirine da kanta.
52
Allahu Akbar, Allah mai yin yadda yaso, har an sanya ranar
bikin Zainab da Rufa'i, duk wadda abin ya shafeshi na dokin
lokacin yazo, shi kansa Rufa'i yama fi kowa dokin abin,
saboda dunbin son daya kwarara masa na Zainab cikin
zuciyarsa. Kash, abinda Allah ya kaddara hakika ya kaddaru,
cikin lokaci kankane sai masifar anobar wata cuta amai da
gudawa mai suna "Gastro entritis' ta barke a yankin gaba
daya. Duk wadda ya kamu in har ya wuce kwana uku to ana
tsammata masa tashi. Mutane da dama, manya da yara,
maza da mata an rabu dasu. Allah Sarkin kudura, Rufa'i da
aka gaya masa cewa Zainab bata da lafiya, waiyo, yadda
kasan an harbo masa kibyar da aka zaro a wuta ta soki
zuciyarsa. Tunda ya kamo hanya ya nufo gidansu Zainab bai
san da wa yake kiliya ba, har ya kutsa kansa cikin gidan.
Shigarsa na farko kenan gidan sai ya rasa inda zai nufa. Daso
sai tace dashi "shigo gata a daki", sai ya shiga bayan sun
gaisa, da uwar, ya ga Zainab, ya kura mata ido sai ta bude
ido ta ganshi sukai ido hudu sai tai murmushi ta yunkuro zata
dago ina! babu karfi duk ta zabge ta rame cikin awoyin da
basu kai ashirin ba. Rufa'i dai ya rasa ma me zai ce.
Idanuwan sa sun ciko da hawaye saboda yanayin da ya
ganta. Zainab tace da shi da sauki dai karka damu, to anan
ne fa yai mata magana da cewa "ai asibiti ya kamata aje" sai
Daso tana daga waje tace, ai anje, Mallam ya sayo mata
maganin kuma yai mata allura. Yanzu ma shi muke jira ya
dawo don a saka mata karin ruwa." Taci gaba da cewa, "ai
wannan al'amari sai dai mu barwa Allah, domin asibitin ma
cike yake da bayin Allah. Kuma ga babu maganin sai dai
saye." Rufa'i yace "sai a dinga bata ko dan kunu ma", sai
Zainab tace "bazan sha ba". Daso itama tace "ai ko ambata to
yanzu zai fito". Sai ta fashe ta kuka don tausayi. Haba zuciyar
Rufa'i sai ta kara bugawa idonsa yana zubda hawaye, sai yai
53
ta maza yace gwaggo hakuri zakiyi Allah zai sauwake mata.
Suna haka sai ga Mallam Ibrahim sun shigo da wani saurayi
da fararen kaya. Ga alamu nas ne, da yaga tana kuka sai yai
turus yace "ke ni halinki kenan, to ame kike yin kukan? inma
mutuwane, kullu natsin zayikatil maut ko? Kawai ki mata
addu'ar neman sauki, in ko ciwon ajali ne ki yafeta, Allah ya
yafeta, amma kya rinka kuka wadda ma bashi da kyau".
Wannan nas shima yace "ai sai hakuri, Allah ya sauwake
mata" duk suka ce amin.
Mallam Ibrahim suka gaisa da Rufa'i sai ya shige daki nas ya
bishi. Shiko Rufa'i ya ce zai je gida ya gaya musu, ya fita. Daya
isa gidansu magriba tayi, sai yai alwala yai sallah, yai ta yiwa
Zainab addu'ar neman sauki, sannan ya dauko abincinsa
yana ci sai yana tunani ko ya gayawa Balki ne. ko da
yake ma ita Balki bata cika son Zainab ba sosai, haka dai ya
samu, ya sanar da Balki, sai tai alkawarin in Alhaji ya shigo
zata tambayeshi taje ta ganta. haka kuwa akayi.
Shiko cikin daren ya tafi gidansu Taja ya tarar da shi da wasu
abokansu guda uku sunzo gunsa. Taja yace kaga ango sha
kanshi, Ruta'i sai yace yanzu kam sha wari ne, ai Zainab ba
lafiya Taja sai yace subhanallahi. meya sameta? Rufa'i sai
yace ah banda Gastro! sauran sai suka ce cab! Allah ya
sauwake mata, duk suka ce amin.
Taja sai yace "ai sai ku tashi muje mu ganta, a wane daki
suke?" Rufa'i sai ya ce "a'a, suna gida, ai kasan aľ'amarin
wani daga cikinsu yace "kai abinfa ya zama azimin sai dai
addu'a don ana matukar yin wannan cutar". Na biyun sai
yace "babban abin ma mutuwa", Rufa'i yace "ai nima yanzu
54
duk hankalina wallahi ya tashi ganin Zainab cikin irin halinda
take, duk fa ta zagbe Mallam". Suna al'ajabin abin har suka
iso kantin 'Jibo stores,' Rufa'i ya shiga ya sayo Treetop da
Ribena, da kuma gwangwanayen Madara da sauransu, suka
nufi gidansu Zainab. Duk suka shiga gidan. Tuni har
Mahalfiyarsa Balki itama, tazo nan dai sukai carko carko shiru
kowa na alĽajabin wannan abu. Suka gaisa sai Rufa'i ya mika
kayan. Zainab da taji muryar Rufa'i sai tai yunkuri zata tashi
sai uwartace a'a kiyi hakuri ki kwanta, Zainab ga dukkan
alamu tana son ta kira Rufa'i amma bakin ba zai iyaba sai ta
bude baki amma murya bata fito ba. Ta daga hannu ina' sai
ya koma. Da Balki ta lura da haka sai ta kiransa dama suna
daga waje ne, sai ya shigo cikin dakin. Dakin na da fadi kuma
falone 'yan kayan dake ciki ba wasu masu yawa bane dama.
Kuma an tare su gefe guda. Daso na rike da hannun Zainab
da aka daura mata Dirip wato karin ruwa a jiki, shi kuma
Rufa'i sai ya tsuguna kusa da Zainab, idonta yana rufe.
Daso sai tace da Zainab gashi nan yazo, Zainab dai bata
bude ido ba. Can sai ta bude ta dan waigo taga Rufa'i sai ta
sake yi mishi murmushi, Rufa'i yace da ita sannu Zainab, Allah
ya sauwake miki. Tai kamar ta dago amma ina babu, ta bude
baki ba murya, sai ta dan gyada kai a hankali Rufa'i dai ta
maza yake yi, amma abin kamar yayi kuka ne. Zainab ta dan
matso da hannunta don ta dafa jikinsa amma hannun bai iso
ba da Rufa'i ya lura sai ya miko hannun sa ya dora akan nata.
Taba jikinta na biyu kenan tun marinda yai mata tana yarinya.
Anan nefa ya tuna irin abinda ya faru da su a wancan lokaci,
arashi, ita ma mahaifiyarsa da taganshi yayi zugum a gaban
Zainab sai tana tunanın abinda ya faru tsakanin iyayen
akansu Rufa'i da Zainab.
55
Shiru ne dan loakci Zainab sai ta janye hannun ta, ta kuma yi
murmushi ga Rufa'i shima anan ne yai mata murmushi sai ta
rufe idonta. Mahaifiyarshi tace dashi ai sai ka tashi kutafi dare
yayi. Sukai sallama, suka tafi.
Balki tana nan wannan suzo, su tafi wancan suzo har wajen karfe sha biyu na dare bata tafiba tana tausayawa Zainab da kuma taimakawa Daso