turakarsa, sai ta
bishi, suka zauna ya cigaba "wato a gaskiya kinsan zuciya
wani lokaci zata yi zafi wani lokaci tayi sanyi. To ni a lokacin da
aka nemi muyi sulhu sai naji wallahi wani Imani yazomin,
saboda haka kawai sai muka yafewa juna shikenan zance
yawuce. Sannan kuma ina so ki manta da wannan magana,
kuma zan samu Rufai inyi masa fada. Balki dai bata ce kome
ba ta danyi shiru sai dai ta nisa tace "ba kome! ai duk wannan
mai sauki ne, hakuri maganin zaman duniya, inji Hausawa".
Alhaji sai ya tashi ya tube babbar rigarsa ita kuma tayi waje
sai yace da ita, ta kunna masa fanka. Dama makunnin yana
bakin kofar dakin. Sai ta kunna tayi waje shikuma ya kwanta.
Ta na fita sai ta fara shirye shiryen abincin rana. Rana ta fara
yin zafi sai ga Rufai ya dawo daga makaranta. Dama yana
makarantar jeka ka dawo ta koyon sana'a, kumama har yana
aji biyar, sauransa shekara guda ya hada.
A can gidan Mallam Ibrahim kuwa, matansa basu san ma
yaje kotu ba. Dama bai gaya musu ba don bai tabbatar akan
12
za a kaishi ba. To shima azahar ta kunno kai an tashi a aiki ya
tafo gida sai ya biya ta kasuwa ya sayo kayan cefanne abincin
dare. Ya iso gida sai ya taradda Zainab tana zaune akan
dakalin kofar gida sai ta taso ta karbi kayan ta wuce gaba,
shima ya shiga gida, to ranar dai yana dakin Da'ado ne sai ya
wuce dakin ta domin shi bashi da turaka. Shigar sa ke da
wuya sai ya cire fularsa da takalmi ya sanya silifas ya dauki
butarsa wadda kullum take cike da ruwa a bakin kofar daki,
ya nufi bandaki. Ya fito yayi alwala, ya fita. Da'ado kuma bata
mayi masa ko sannu da zuwa ba domin tana ta shirin abinci,
ita kuma Daso tana daki tana ta dinkin fula, dama takan dan
taba sana'ar dikin fula lokacin da ba ta yin kome.
Mallam Ibrahim ya dawo daga masallaci ya tarar Da'ado ta
kare abinci ta zuba masa nasa. Ya shiga daki ya fara ci, sai ya
kwalla kira Zainab! Zainab' sai ta amsa "Na'am" ta zo, ta
tsugunna ta ce "gani" sai yace mata "karna sake gani, ko naji
ance kinsake fada da wani yaron bare yaron Alhaji kinji ko"? ta
ce "eh! naji"! yace jeki. Ki kirawo min Muntaka, ta fita, ta kirawo shi, yazo shima Mallam Ibrahim ya gaya masa haka ya fita. Daga nan, basu sake fada ba.
13
KASHI NA BIYU
Mallam Ibrahim yana nan yana ta aiki shekara da shekaru
sannan kuma suna ta mutunci da Alhaji. Bayan kamar
shekaru uku sai Allah yayi wa Da'ado wato kishiyar uwar su
Zainab rasuwa. Alhaji Mai Wake dashi akai zaman makoki na
sati guda. Mutunci yaci gaba tsakaninsu shekaru da yawa.
Mata da saurin girma ake. Zainab dai tariga ta girma don ta
fara cika mace duk alamun girma sun baiyana a gareta,
sannan gata da tsabta. A takaice dai duk namijin da yakai
matsayin namiji in ya ganta, ya sota. Ta kara fari, ta cika so sai
ta ko'ina sai kyalli take yi. Ganin Zainab tagirma ba abin daya
dami Mallam Ibrahim da matarsa Daso illah auren Zainab.
Domin ta riga ta bar makarantar Islamiyar da take tun shekaru
uku da suka wuce, ta sauka. Ran nan Mallam Ibrahim suna
kwance a daki shi da matarsa Daso sai ya tuntube ta akan
yaya tagani akan ya aurar wa dan Alhaji Mai Wake Zainab
wato Rufai? Ko kuma? Daso dai sai ta yi 'yar dariya tace Alhaji
dai, akan wannan, ai yar kace. Kafini sanin kamantuwarsa ko
kuma rashin kamantuwarsa. Sai Alhaji yace "ke wato ba 'yar ki
bace ko"? Sai tace "ah! in kace ma ba tawa bace ai duk ta
zauna. Bari in gaya maka wani abu. Kai kanka kasan halin
yara a yau, in dai akace za a zaba masu wanda zasu aura to
ko suna so sai sun bijire don kawai dai kar a ce an sa su.
Amma kodayake mu tamu 'yar tana da dan hakuri munyi sa'a
kadan. Amma kaje ka tuntubi Alhajin tukun kaji".
Allahu Akbar, shi Rufai dama tun lokacin da wancan rikici ya
hadasu da Zainab kullum inya ganta sai ya tuno da abin
daya faru a unguwarsu. To a hankali sai yaji yafara sonta. To
amma bai ya tunanin cewa inya hada makaranta za'a yarda
14
ya aureta saboda babanta ba zai yarda ba.
Shi Rufai yana neman aiki, ya hada makaranta har yayi
diploma a harkar tsara birane, shekaru biyu kenan. Sai tsarin
gwamnati ya chanza aka sa dokar ba daukan aiki sai bayan
shekara biyu. To abin daya dada tsaida shi kenan bai samu
aikin ba. Amma sabuwar shekara anajin shugaban kasa zai
sauke wanan takunkumi na aiki.
Ran Juma'a Alhaji suka hadu a Masallaci da Mallam Ibrahim
sai Mallam Ibrahim ya tuntube shi da wannan magana, sai
Alhaji dai yace "to amma kafatuna da halin yara a yau".
"Amma ba kome. In Allah ya yarda Allah ya shige mana gaba
zamuyi iya bakin kokarin mu Allah Ya tabbatar". Suka rabu.
To daga masallaci dai shi Alhaji mai Wake bai koma gida ba
sai ya zarce kasuwa shagon wani Amininsa Mai suna Alhaji
Usamatu. Shi Alhaji Usamatu mutum ne mai hakuri, mai sanin
yakamata, kuma attajiri ne, yana da dukiya mai tarin yawa, ga
shanu da gidaje, sai dai kuma Allah bai bashi haihuwaba.
Sun dade tare da Alhaji Mai Wake suna zumunci, kuma duk
abinda daya zaiyi sai ya shawarci daya. Alhaji Mai Wake ya
isa shagon Alhaji Usamatu. "Assalamu alaikum"! "wa alaikas
salam" duk mutanen dake gun suka amsa masa. Ya bisu da
daya daya suna musabiha. Sunyi hanu da Alhaji Usamatu sai
yace da shi "Dan kwangila!" Alhaji Mai Wake ya amsa masa
da cewa "Dan kanzagi dai" ai 'yan kwangila kam masu bada
-ita, ga ten pasen (10%), ga cuwa-cuwar ofis, ga kuma
sallamar akawu masu payil." "Kadanma kenan" inji Alhaji
Usamatu "ai da zaka kama kasuwa gaba daya ni inaga yafi". "To naji! sai kaban kamar kwata miliyan kenan" inji Alhaji Mai Wake, "kwata miliyan ina almajiri irina zai sameta" yana dariya 15
Alhaji Usamatu yace to ba shi din bama, kai da ka shiryar da
dan naka? Ka shiryane? Gashi kana cewa ma bai samu aiki
ba, to, ko dayake aiki bashi zai mar auren ba sai dai ya dan
rage wahala 'yar kadan. Saboda haka "kasan abinyi"? "a'a"
Inji Alhaji Mai Wake. Usamatu ya cigaba "ka turo min Rufai ni
zan same shi. Ai ba a maida hannun kyauta baya ba, duk
wadda zai maka haka masoyinkane. Duk yadda muka yi
dashi, zakaji. Sannan kai kuma ka samu mahaifiyarsa ka
tuntubeta kaji. Alhaji Mai Wake yace to shikenan, hakan za'ayi.
Amma in har Allah ya tabbatar to shanun garma ta zasu tafi.
Nan da nan sai Alhaji Usamatu yace kai! Alhaji kar kafara,
kade bari muga yadda Allah zai yi, ni kadai ma ai mai yiwa
Rufai aure ne, yadda yake shi kadai a gunka ni ma haka yake
shi kadai a guna. Nan take sai jikin Alhaji Mai Wake yai sanyi
yatuna, rashin haihuwar Alhaji Usamatu, sai yace "Amin" ai
inaga ma la'asar tayi, sai Alhaji Usamatu ya daga ido ya
duba agogon dake makale jikin bango "eh! har hudu saura
kwata sai muje ayi alwala. Sukayi alwala, Alhaji ya rufe shago
suka karasa masallacin da ke kusa da gun akai sallah. Tun
daga can sai Alhaji Mai Wake ya wuce gida bayan sunyi sallama da Alhaji Usamatu shi kuma ya dawo ya bude shagonsa.
Shi kuwa Mallam Ibrahim tun daga Masallacin juma'a gida ya
wuce, dama daga wurin aiki ya zarce masallacin. Bayan ya
dan taba barci har magariba ta gabato yana gida. Sai yayi
alwala ya tafi masallaci. Anyi Sallah ya dawo ya zauna bisa
tabarmar da Daso ta shimfida masa a gun da ta saba, kuma
tariga ta kawo masa abinci da ruwa. Zamansa keda wuya sai
ya kira Daso ta zo ta durkusa kusa da shi, har ya fara cin abinci
sai ya ce da ta zauna bisa tabarmar, sai ta zauna. Ya cigaba da
cewa, "na samu Alhaji Mai Wake,kuma mun yi maganar hada
yarannan to amma yace zai waiwaiceni nan da kwana uku"
17
Saboda haka ke yaya kukayi da Zainab din? Daso sai tace "eh! to, na dan sha cikinta akan cewa in muka zaba mata miji
zata yarda? to a gaskiya bata fito sariri ta nuna min gamsuwarta ba sai dai kuma bata ki zancen ba. Domin sai da ta tambayeni kan cewa wanene mukeso mu zaba mata, to ni dai duk banyi mata bayani ba. Saboda kuwa ban san me zai kasance can wurinsu ba". eh! haka ne" inji Mallam Ibrahim yanzu dai muda kata muji daga garesu.
18
KASHI NA UKU
A gidan Alhaji Mai Wake kuwa cikin dare suna zaune a daki
sai Alhaji ya kada baki yace "ke baki san wani abin alheri ba",
sai Balki tace "na mefa"? "ince an biyaku kudin kwangilar?" "Sai
yace "ahaf! bar wannan magana, ina Mallam Ibrahim? na
can unguwar Tsakuwa, to dazunnan a masallaci ya tuntube ni
akan ko zamu yi zumunci a aure tsakanin Rufai da 'yarsa, ni
han ma san sunanta ba". Nan da nan sai Balki tace" aiki ya
z...na cakulet! Dan autan mu guda tun yanzu zaka fara yin
maganar aurensa. Ni kam nafison ya zama babban ma'aikaci
ko muma zamu dan sarara a rayuwarmu. Ko irin dan danne
muku kudi da akeyi ai kaga sai ka manta da shi". Sai Alhaji ya
kada baki ya ce "eh! nima kam nayi tunanin hakan, amma ma
ni nafi son ya cigaba da makaranta, to kuma da nayi la'akari
da yadda harkar karatun take a yau, ga kudi mai yawa, da
tsadar abinci, kuma ga babu karatun, kullum yajin aiki. Sai
muka shawarta hakan da Alhaji Usamatu. Kuma ya goyi
bayan ayi masu auren sannan ya bani kwarin gwiwa. Kuma
kinga shi aikin gwamnatin nan gashi ga kamarsa. Kudin
albashin ba zai isheka kaci abinci na wata guda ba, balle
magani da sutura, ba'a batun yima wani dan alheri. Saboda
haka mun shawarta da Alhaji Usamatu kan cewa inyi masa
auren shi yafi, sai kuma ya kama sana'ar da ya dan koya a
makarantar da ya gama. Tunda ya iya kafinta, ga walda, da
safiyo shikenan." Ko kuma yaya kikaga? "Tace" Ah! to, yanzu
kam me zance sai kuyi abinda kuıkai niyya". Sai Alhaji kuma
yace da ita "yanzu gobe zan sa Rufain yaje gun Alhaji
Usamatu shi zai gaya masa kome, kuma shima na san duk
bayanin da Alhajin zai masa zai gamsu kuma ya yarda. Allah
ya kaimu goben "tace" Amin. Suka kwanta.
19
Bayan da gari ya waye, Alhaji ya dawo daga masallaci kamar yadda ya saba. Gari yayi shaa hantsi ya fara fitowa, sai yai
kiran Rufai domin ya sayo kosai na karyawa. Dama kullum
haka akeyi, saboda gidan basu da yara kuma su ukun kawai
ke gidan. Amma a nayin kwakkon safen. Ita kuwa Balki tana
daki tana ta sana'arta ta dinkin hula. Bayan da Rufai ya dawo duk suka karya, bayan ya gama cin nasa abin karyawar, sai Alhaji yai kiransa. Ya amsa kuma yazo ya durkursa. Duk da
girman da Rufai yayi yana dabi'a kamar karamin yaro badon komai ba sai don shi kadai ne a gidan kuma ba'a sake haifan
wani ba shine na farko kuma shine auta. Kuma duk iyayen
suna sonsa sosai. To bayan da ya durkusa sai Alhaji ya се
masa, wajen karte goma kaje gun Alhaji Usamatu a gida, na
san bai fita kasuwa ba, sai kace gaka. In kuma baka same shi
a gida ba ka zarce kasuwa shagon sa. Kaji ko! To naji Baba
dama baba yake cewa uban ga Alhaji Usamatu kuma Baffa.
Sai ya tashi, ya tafi dakinsa yana ta zulumin da tunanin ko a
kanme zai je gun Alhaji Usamatu? Yana dai ta wannan tunani
ya saka wannan, ya warware, ya zaci wancan, ya rushe, haka
dai yai ta yi har can yai zubur ya tashi ganin karfe tara ta riga
ta wuce da wajen kwata. Ya je ya debi ruwa yai wanka ya fita tun kafin ubansa ya fita.
To bayan fitarsa sai ya tare Achaba' (babur na haya) ya hau
sai yace kaini unguwar matsango sai dan Achaba yace to
amma naira goma ne fa saboda unguwar da nisa. Rufai yace
ah! muje man zan dubo wani ne in baya nan ma sai ka dawo
dani, muje. Sai suka tafi.
To shi dai Taja saurayi ne mai matukar hankali ga kuma
hakuri, ga shi gajere kyakkyawa, sai dai bashi da wargi ko
20
sakin jiki a cikin abokansa. Ko da a majalisin da suke zama
suna hira anan unguwarsu baya cika surutu ko shiga duk
zancen da akeyi amma a gefe ya kanyi. Ayi ta musu akan
siyasa, ilmi da sauran al'amura na yau da kullum, amma bai
cika shiga ba sai dai ka ganshi yana ta murmushi. To anan
majalisin sun fi shakuwa da Rufai, kuma shine ma kawai
wadda Rufai kan kai wa shawara akan duk al'amuransa.
Haka shi ma Taja, shima ya kare karatunsa na N.C.E. yana
koyarwa a makarantar 'yanmata wato G.G.C. Govt. Girls
Collegeta nan garinsu.
Sun isa kofar gidan su Taja dama Rufai shi yai niyar dubawa.
Sai yace da dan Achaba "tsaya in dubo shi in ya nanan to sai
murabu". To dama dakin Taja yana daga zauren gidan, gidan
kuma a bakin titin nan mai suna Adandaya street yake. Farin
gida yasha fenti da yar Rumfa tana kallon yamma. Sai kawai
Rufai ya kutsa kai zaure, sa kansa ke da wuya sai yaji sautin
rikoda yanayi ansa kidan wani mawakin America Pin Kolins'
irin kida mai sanyi da akece dashi blues: Daga jin wannan
sauti sai Rufai ya raya aransa cewa Taja na nan. Amma dai
sai ya kutsa kai cikin dakin. Sai ya tarar Taja baya ciki amma
ga dukkan alamu yana kusa. Ko ma ya shiga cikin gida.
Domin a cikin gida ma yake yin wanka. Kuma ga kayansa nan
ya goge ga alamu dai yana shirin ya fita ne. Ganin haka sai
Rufai ya fito ya je gun Mai babur ya bashi kudinsa yace masa
"inaji yananan nagode". Dan Achaba ya karbi kudinsa ya
buga babur ya tafi.
Rufai ya juyo ya shiga zauren kenan sai Taja shima ya fito daga cikin
gida. Suka hadu a nan. A'a Yallabai' Rufai, inji Taja sai Rufai ya ce
"ku ay yallabai" mukam ai muna yallabai ne gashi kai sai yanzu ma
ka tashi daga barci. "Haba! sai kace har yanzu ina sakandare', inji
21
Taja! Ai tunda asubar nan in Baba ya kwankwasa min kofa in zai tafi masallaci, in na tashi to shike nan, bazan iya komawa ba', suka shiga, sun shiga kenan Rufai ya zauna bisa daya daga kujeru ukun dake jere ta barin gabar na dakin suna hannun riga da gadon wadda shi kuma Taja ya zauna a
kansa. To da yake ranar Asabar ce, Talabijin suna yin 'yan shirye-shirye kadan irin na karshen sati har zuwa sha biyun rana. Rufai ya mika hannu ya kunna talabijin din dake kan dan tebur gefen kujerar da yake zaune sai ya rage karar kidan da rekodar keyi wadda take a bisa shi talabijin din, lasifi kokinta kuma suna gefen talabijin din a kan tebur. Dama a
kan rabasu da ainihin uwar rikoda. Kunnawar sa keda wuya sai foto ya fara fitowa, sai gashi ana wani fin na Indiya mai
suna Firem Kaidi'. Taja sai yace kai niko na washi, wannan fin din wallahi sun same shi, duk sati sai shi! Rufai sai yace tab ai niko yanzu ma sai ya tunatar dani abinda ya kawo ni gunka. Da har na manta. Sai sukai shiru na dan lokaci ba wanda ya
ce uffan. Sunata kallon abinda ke faruwa a fin din.
Can sai Taja yace meya faru? dan na san kai uban shawarane. Kome sai kai shawara, sai kace dillalin awaki.
Rufa'i yace ah! ai ance aikin mai shawara baya baci, ko
kuma? Taja kuma yace "in batai yawa bako?" Eh! batai yawa ba saboda kai ne kawai wadda nazo don in shawarta." Taja
yace oh! ashe na kama, to shawarar tame cece. Me ya faru?"
Rufa'i yai shiru sai ya nisa yace "meye kake ci na baka na
zuba. Abin da ya kawo ni yau ban san cikin sa ba nima.
Babane yace inje wurin Baffa Usamatu, to bansan me zai faru
ba, ni dai bai taba gaya min haka ba. To shine kafin inje na
biyo ta nan. Ni ina tunanin ko aiki zai sama min". "Ko kuma jari
ba?" Inji Taja, ya katse shi, Haba! Jari, ai ko Baba zai ban. To
22
jariya fa? inji Taja menene jariya? ah! ka tunadai, bashi da
'ya ne? ya! ai shi bai taba haihuwa ba" Rufai ya amsa ya
cigaba. "Wallahi ina yimasa bakin cikin rashin samun da, ga
arziki amma babu magada". "Kash! nima sai naji wani iri", inji
Taja "dama bashi da da ashe? "Allah Sarki, Allah ya bashi
haihuwa". "Amin!" inji Rufa'i, Taja yace "yanzu yadda za'ayi
kaje kaji tukun in ma aikin ne ai duk alheri ne, kasan yadda
kasarnan take, takunkumin ya jawo matsala wallahi", "umh!
ba karama ba" inji Rufa'i. To shirya mu fita, ko ba yanzu zakа
fita ba"? "Ah! yanzu mana kayan nan kawai zansa. Ina so ma
inje lyani Stores, in sayo katin Nalentine) Balentin don in aika
wa mutumiyar inji Taja "wa? Zaliha"? Rufa'i ya tambaya "eh!
mana akwai wata ne bayan ita"? "Na sani ko kayi kari? mu dai
har yanzu bamu shiga fagen ba tukun". Inji Rufa'i. Sai Taja
yace "ina Binta? Ko dama tasha kakeyi?" Rufa'i ya mayar
masa da cewa "ai tashar ma bata mota ba, tashar jirgin kar
nakeyi. Kasan yanzu tashar jirgin kar ce bata aiki. Sai a
shekara jirgi bai zoba".
Taja yace "ka gayawa kajin gidanku ko sa yarda, amma ni
kam a'a". Taja tuni ya riga ya sanya kayan sa ya dauko turare
a karkashin filo ya fesa, sai Rufa'i yace "kai wannan wane irin
turare ne haka"? Taja sai ya juya gun sunan turaren yana
nuna masa sai Rufa'i ya karanta indifference' (indipirens),
wannan ai sunan ka ne, kai ne dan baruwana'. Taja yace ah,
to! sai me?" ya ajiye turare gun da ya dauko shi, Yace tashi
mutafi kaga yanzu goma saura minti biyar. Nan da nan sai Rufa'i ya tashi yace tab ai na makara, karfe goma akace inje
amma badamuwa. Zan isa dawuri ai'. Suka fita tare bayan da Taja ya rufe kofar dakin. Rufa'i yace "yanzu kai gabar za kayi, ko? ba yanzu zaka sayo katin ba? "Sai yace eh! amma muje dai tukun in rakaka kasuwar ai ba gaggawa nakeyi ba, zan 23
jiraka a shagon Tela Musa". Shikenan sai suka fara tafiya. To gun da dan rata kuma basu da abin hawa ga shi duk cikin garin babu Taxi ko bus isassu sai Achaba kacha, kacha. Suna tafiya sai ga mai Achaba, Rufa'i ya tsayar dashi, ya ce dashi don Allah zamu je kasuwa ne ko zaka saurara wani yazo sai ku kaimu. Mu biyu ne" Dan Achaba yace to'. Can sai ga wani ya fito sai suka tsayar da shi duka suka hau sai kasuwa. Suka biya su kudinsu. Sannan suka shiga kasuwa. To shi shagon Mallam Musa na bakin kasuwar sai Taja yace ni zan jiraka a
nan sai kadawo'. Rufa'i ya wuce shi kuma ya shiga shagon Tela Musa.
24
KASHI NA HUDU
Tsakanin shagon Mallam Musa da na Alhaji Usamatu nada
dan rata. Kusan ma yana a tsakiyar kasuwar ne kusa da'yan
goro. Isar sa ke da wuya sai ya tarar da Alhaji na zaune a daf da kofar shagon. Shi kadai ba kowa. Karfe goma kuwa ta
wuce da kimanin minti goma shadaya. Da Alhaji ya ganshi sai
ya ce dan-Baba ka iso? Dama haka yake kiransa dashi. Shi
kuma Rufa'i sai yace eh!' sannan ya durkusa, bayan da ya
riga ya cire takalmansa daga baya. Sai yaci gaba da cewa
Baffa ina kwana? Alhaji ya amsa lafiya' suka gaisa sosai
gami da tambayarsa ina Babarka? Rufai ya amsa masa cewa tana
nan lafiya'. Rufa'i dai yana ta zulumin me zai ce masa? Oho!
Bayan dan shiru kadan sai Alhaji yace "Babanka ya yi min
batun cewa yanzu gashi ka gama makaranta, kuma ba'a tafi
wata ba sannan ga aiki an sa takunkumi ko?' Rufa'i yace eh!"
Alhaji yaci gaba to yanzu me kake so kayi'? Rufa'i yayi shiru
na dan lokaci sai yace Ah! Baba duk abin da Allah ya huwace
shi za'ayi'. Alhaji sai yace to mun yi shawara tare da Baban
naka kan cewa a hadaku aure tare da 'yar Mallam Ibrahim,
sannan sai ka kama kasuwanci muga abinda kuma Allah
zaiyi yaya kaga? In kuma da wata shawara sai kayi sannan
kazo ka gaya min jibi musan abinda ake ciki Rufa'i duk sai
kansa ya kulle, zuciyarsa ta yanke, gumi ya keto masa ya
shiga tunani mai zurfi saboda bai zaci abinda za'a gaya
masa ba kenan. Alhaji dai ya zuba masa ido, sai yace dashi
yaya dai Dan-Baba? maganar tama nauyi ne naga kayi
zugum'. Rufa'i yace a'a', sai ya tashi tsaye zai tafi sai yace to
Baba sai jibin dai zandawo', Alhaji yace to Allah ya kaimu.
Yace kuma dashi Dan-Baba, ji!' Sai ya dan juyo, Alhaji yaci
gaba da cewa kayi shawara da abokanka mashawarta ba
25
mashashantaba'. Rufa'i yace to naji. Alhaji yace šai anjima,
Rufa'i ya tafi duk ya rude sai ya manta da maganar Taja
kawai ya bi wata hanyar yana tafe yana ta tunanin wannan
magana. Ya raya wannan ya warware ya kulla waccan ya
katse yana tafiya bai san inama zai tafi ba yana cewa a
zuciyarsa to wai shin wace yarinya ce ma 'yar Mallam
Ibrahim? Yaya take? To aure? makarantar fa? Kuma yana
batun kasuwanci ina jarin, kuma kasuwanci me zanyi? In ma
auren zanyi ai sai Binta, nan da nan sai Taja ya fado masa a
zuciya ya tuna cewa zasu hadu a shagon Tela Musa. Shi kuwa
gashi ya bar kasuwa abadan ma yayi nisa kuma bai bima ta hanyar
gida ba. Kawai sai ya juyo. Ya nufi shagon Tela Musa.
Isar sa ke da wuya sai Taja yace da shi Haba Rufa'i, haka
kawai ka shuka dusa ka manta dayi mata bayi', Rufa'i sai ya
kada baki yace 'an manta din', Tela Musa na cikin dinki riga
mai suna Jawaniya' sai ya dakata ya daga kai ya dubi Rufa'i
tukun, to akwai jama'a kamar mutum uku suma suna tadi a
gefe ta cikin shagon. Sai sukai shiru jin amsar da Rufa'i yayi.
Mallam Musa dai sai yai murmushi yace yallabai ai sai a dan
sassauto', Taja kuma shima yace To mai dai wukar, sauran
jama'ar shagon sai duk suka bushe da dariya duk tare da
Rufa'i da Musa da Tajan gaba daya.
Rufa'i sai yace haba ai kai din ne ma ko gaisuwa baka bari
munyi da mutane ba, ka tarbeni da kaskon tuya'. Taja yace to
a gaisa' Rufa'i yace Alhaji Tela Musa Salamu Alaikum gami da
mika hannu sukai musabiha, sai ya dan leka cikin yace da
jama'ar cikin Malamai salamu alaikum' duk suka amsa
wa'alaikas salam. To shi dai Rufa'i bai saba da kowa ba na
cikin shagon, sai dai ya dan san Tela Musa daya ke
unguwarsu kusa da kusane.
26
Yan boko da wayo, wai su boye abinda suke so suyi magana
akai sai, Taja ya tambayi Rufa'i cikin turanci what the hell's
cooking? ma'ana me yake faruwa'? Rufa'i shima dayake dan
boko ne harma yayi diploma a kan harkar town planning'
wato tsara birane) a makarantar (CABS) Poly-CABS dake nan
garinsu. Sai ya amsa masa dacewa The unexpected always
happens' ma'ana abinda baka tsammani kan faru. Taja yace
more clarification' (ma'ana ka kara bayani), Rufa'i sai yai tsuka
kuma yace let's get aside, it's a very long and dubious matter'
(ma'ana, kai muje gefe, al'amarin yana da tsayi, kuma mai
rikitarwa.) Taja sai ya tashi, yai waje, Rufa'i sai yace da Mallam
Musa, Alhaji don Allah zamu gana', Tela Musa yace
bismillah! bismillah!! ya cigaba da dinkinsa.
Suna tsaye a waje daga dungun shagon sai Rufa'i ya debe
labari ya baiwa Taja duk yadda sukayi da Alhaji Usamatu.
Yace kuma ni yanzu ban ma san yarinyar ba kuma ban nemi
karin bayani ba kuma yace in nai shawara jibi inje in gaya
masa. Na rasa ta ina ma zan fito. Taja yai shiru, to dama
gashi da shiru shiru ga hakuri sai yace to a unguwarku
Mallam Ibrahim na wane?' sai Rufa'i yace ah! waya sani
unguwar ai tawuce haka', Taja sai yace to kuna da dan'uwa
mai irin wannan sunan', Rufa'i yace ai ni duk danginmu har
ma na Saleri da Kwajalewa ban san mai suna Mallam
Ibrahim ba'. Garin kakaninsa na uwa da na uba kenan. Sai
yaci gaba da cewa na san wani Mallam Ibrahim suna dan
mutunci da gidanmu to amma 'yarsa ba yadda za'ayi na aure
ta saboda dalilai', Taja sai yace waye shi?' Rufa'i sai yace
hum! ance sabon maza fada ko?
To shi wannan Ibrahim din an.taba samun sabani ne a
tsakanin gidanmu da nasu, amma daga baya sai aka shirya.
27
Shine Baban Devil dai! Taja sai yace ah! Muntaqa devil?
Rufa'i yace shi, yaci gaba da cewa ai yana da ya wata illi,
saboda haka nasan babu ma yadda za'ayi ace wai itace
sam'. Taja sai yace umh!' yana 'yar dariya kai dai baka sani
ba', yaci gaba shin ta girmane ma? ko kuma?' Rufa'i yace
wannan ai har ta batse ma tsabar cika, wato da, na dan ji ina
santa ma amma haka kawai sai na ji yaya'. Taja sai ya kada
baki yace to yanzu misali ace itace yaya zakayi?" Rufa'i yace
ah! yaya kwa banda naki kawai. Taja yace chab, to kul!
wallahi kar ka fara, ba'a nuna kiyayya a miraran kaji'. Rufa'i sai
yace 'to yau in dai itace wallahi kaji rantsuwar musulmi to ba
za'ayi ba. Kai koma wacece a yanzu ba zan