yarda ba'. Taja
sai yace koda Binta?" Rufa'i yace àai ko Binta ce ba yanzu ba,
kai akwai wata mafa bayan Bintan kasan mu 'yan
underground ne'. Taja yace ah! to! mu da muke da niyaryi
zoka rakani na sayo katin ma tunkun. Kafin mu sake zama".
Sai suka tafi lyani Stores neman katin Valentine saboda ranar
sha hudu ga watan biyu ne akan bayar da irin wannan kati a
kowace shekara. Itace ranar masoya. Suna tafiya ne Rufa'i
yake cewa, Ah! kaga dai wani katon Arne ya barmu da gadon
sa. Muna tayi kamar addini, Taja yace to ai shine shugaban
masoya na duniya. Rufa'i yai tsaki. Da isarsu, Taja ya sayo
guda daya har sun fito, sai ya koma ya karo guda biyu. Rufa'i
sai yace 'yar gata duk a'ita ne?
Taja dai sai yana dariya har sukai nisa. Suna tafe sai Rufa'i
yace kai wannan abu duk ya tsimani fa kaga yan zunnan
wallahi nidai ina tafiyane amma kwakwalwata ta tafi nesa,
amma in naje gida zan tambayi mama, ko tanada masaniya.'
Taja sai yace tunda Baba ya sani har ya kiraka to ai ita ma ta
sani. Ni dai yanzu ka tambayo mana muji wacece sai mukai
mata katin daya, wannan biyun kuwa na Žaliha ne da Binta'.
28
Juyawar da Rufa'i yayi sai ya daka masa harara kuma yai
turus ya tsaya. Kuma yace to siradi na dakai kenan nan kai
tafiyar ka'. Taja sai ya tsaya yana dariya sai ya juyo yace kai
zaki, maza masu daji, masu dagi da karfin kirji, a fuce, kowane
allazi, da nasa amanu. Dan-Baba. Allazin Ka nine Taja'. Sai ya
kama hannunsa zai ja, Rufa'i ya fisge kuma yana murmushi,
saboda kirarin yai masa dadi, kuma dama tunda suke tare in
Rufa'i ya tunzoro da haka, Taja kan kwantar dashi. Amma bai
taba masa kirari irin wannan ba. Dama Rufa'i haka yake
kamar talgen gari dayayi zafi sai ya taso. Haka dai suka kama
hanya suka tafi, ba magana sun iso bakin titin sardauna
wadda shine babba a garin kuma a nan zasu rabu saboda
unguwarsu daban. Rufa'i don ya nuna ya fuce sai yace, to sai
ka ganni da daddare ko gobe da safe zakaji kome'. Taja yace
to ina ganin hanya'. Suka rabu. ******************************29
KASHI NA BIYAR
Taja yana zuwa gida ya shiga daki har ya kwanta don ya futa
yana jin sauti wakar Brandy mai suna I wanna be down, sai
yaji karamar murya tayi sallama, kawai sai zuciyarsa ta bashi
cewa Zaliha ce. Sai ya tashi ya debe katinan nan ya boye karkashin filo, kuma ya rage sautin recorder sannan yace
bismillah waye? Sai yaji shiru, kuma ba'a shigo ba. Sai ya taso
ya leko sai sukai ido hudu da Binta. Sai tai murmushi shikuma
yace a'a lalle, Ranki ya dade shigo mana". Binta bakace doguwa mai kirar kalangu, kuma bata cika surutu ba, gata da fayau fuska da gashi mai yawa. Kuma takan danyi dingishi in
tana tafiya dan kadan, amma sai ta zamar shi kamar na
gaye. Dama sun saba zuwa tare da Zaliha, anan ne ma suka hadu da Rufa'i. Shike nan suka shigo, ta zauna a ta farko daga kujerun dakin. Taja yace "af ke dai kun kulla da wannan
kujera". Binta dai batace kome ba sai murmushi da take yi.
Bayan dan shiru kadan, sai sautin da ke tashi kadan kadan
Binta tana dan motsa fatar baki, ga dukkan alamu tana bin
wakar ne, Taja sai ya katse shirun da cewa Hajiya Binta yanzu
muka rabuda Rufa'i," sai tace nan yazo"? Taja yace eh! tun
safe ba, sannan muka fita sai yanzu na dawo'. Binta tace ka
ra kashi wani wuri ko?" Taja yace kamar ina?" tace ah! ku
kuka sani ai". Taja yace haba ai yadda kikasan nake da
mutumiyarki Zaliha, to ina mai tabbatar miki shima haka yake.
one for one kawai". Binta sai tace umh! kar kazama tsari
masta mana'. Taja sai yace to shikenan, wai ina ma wannan
mala'un take ne?" Binta sai tace eh! haka ma zaka ce mata?
To ai tare muke tana can waje tare da yar gida mai benen
can, Marliya, tana zuwa, in tazo ka kare kanka". Taja yace
kinga don Allah ki rifa min asiri itama uwar daukan dimice
30
kirabu da ita kawai", sai tace to abiya ni sai nai shiru', Taja sai
yace to wallahi zan biyaki da wani abu amma sai kin ganni
jibi" sai tace "to Allah ya kaimu. Amma fa wasa nake maka" sai
yace to ai ni nayi niya tun tuni dama".
Kwatsam sai ga Zaliha ta shigo ba ko sallama kamar wadda
aka jefota. Zaliha farace mai kiba, gata da cikakkiyar fuska
tana da dan faffadan hanci da lebe mai kauri, in tayi
murmushi, kumatun ta sukan taru su nutsarda idanuwanta,
kuma gata da ushirya da lobar kunci. Jib! ta zauna kan kujera,
ta yaye gelenta, ta kai hannu ta dan kara sautin recorder, duk
suna ganinta ba magana, Binta sai tace "haba sai kace ana
fati ki rage mana ko kwaji dadin yin zancen’. Taja yace "ah to!
ai Baba bayanan tayi haka man". Shikenan sai ta rage. Sai
tace ina Rufa'i'? Binta tace uhm! ta kauda kai gami da
zumbura baki. Taja yace yana gida kawo sakon', sai Zaliha
tace ga sakonnan" ta nuna Binta, taci gaba da cewa "dama
itace take son ganinsa". Rufa'i sai yace dir kashi, lalle shi
yanzu....." Sai yai shiru, Binta sai tace shi me? Rufa'i dai har
zaice tauraronsa tana haskawa, sai ya tire. To Binta dai abin
sai ya dan kulle mata kai ta nemi sai Taja ya mata bayanin
abinda yake so, ya fada kuma ya fasa.
Wakar da sukeji ta Brandy ta kare sai ta Boyz II men"Boyis tu
mer' ta shigo ta fara sai Zaliha ta kashe, Taja yace "yaya?"
Sai tace bana son su na fison ta mata kamar
Maria Carie da Dolly da, Taja yace,"to ga wannan sa mana,
ya miko mata wani kaset. Tasa shi sai ga karatun Addu'oin
Limamin Madina Abdur-Rahman Sudais. Binta tace don Allah
ku cire! Taja yace haba kuyi hakuri mana ai karatun yafi, ga lada ga
dadi, ga tsari daga sharrin aljannu. Binta sai tace to! amma ka
31
gayamin abinda zakace dazu ka fasa'. Taja yace kai! magana ta wuce sai tone tone, in wata ce sai in cemata tsofuwar kaza". Zaliha sai tace eh mana! mu ai tsofin kaji ne za'a zage mu a fakaice". Taja yace haba ginbiya Zaliha ai bakin Taja ba zai iya zagin kiba". Sai tace to ai kai fadin bakar magana ne dakai, sai kace dan kama. Taja yace to kin rama, daya da daya kenan.
Binta sai tace ai dama duk mai shiru shiru in ya shuka maka
magana daya sai ka gigice". Nan dai sukai ta hira har magriba. Ya rakasu, suka tafi gida. Da zasu rabu Binta ta miko
masa takarda don ya kaiwa Rufa'i.
Shikuwa Rufa'i dama daga yadda suka rabu da Taja sai da
yabi ta gidan kanwar uwarsa ya bata labarin abinda yake
faruwa. Sannan ya wuce gida. Ya isa gida dai kusan magriba.
Ya shiga gida an gama abinci ya dauka yaci sannan lokacin
Babansa ya shigo. To yaso da ya sami uwar amma ganin
uban sai ya fasa. Ya fita waje ya zauna kan dakali yana ta
tunani. Sai ga Alhaji ya fito zai je wazifa a masallaci sai yace
dashi kai kaje'? Rufa'i yace eh! naje" Alhaji yace to!* sai ya
wuce. Rufa'i sai yaji dadi rashin wani neman bayani akai, sai
ya tashi ya shiga gida, uwar kuwa tana daki. Daga shiga sai
tai murmushi tace "yaya kuka kare?" Rufa'i ya zauna, yabata
duk yadda sukayi kuma ya kare da cewa shi a ra'ayinsa babu,
bai yarda ba ko wacece. Sai Balki tace la! Zainabu ce dai yar gidan Daso mai kunu. kyakkyawar
yarinya irin wannan, gata da hali mai kyau, ga ilimin Arabbi".
Sai Rufa'i ya katse ta da cewa Nifa na Rantse babu. ipso
facto, ma'ana "bazai yiwu ba" uwar sai tace menene sipakjto?* Rufa'i sai yai shiru, ya manta akan cewa da uwarsa
32
suke magana. To dama akwai wurin da suke zuwa da wata
yarinya Quirana cikin tafiyar dare akwai yaren da sukeyi. Nan
take ake koya, da ansha ruwan rantsuwa, sai a zama
cikakken mamba. Nan dai ya tashi ya fita ba bayani ita kuma
uwar tana mai yarda da ra'ayinsa duk da cewa bai bata dalili
ba. Amma tana dan tunani akan sabon yarensa da yake yi jifa
jifa.
Mu hadu a littafi na Biyu
In da zamu cigaba da batun yadda Rufa'i ya tsinci kansa
cikin kungiyar Asiri mai suna KU KLAN KLUX ta
sanadiyar yarinya mai suna Quirana. Da yadda suka share
da sauran 'yan kungiyar da kuma irin halayensu gami da
mugayen dabi'unsu.
Allah ya tsaremu Amin.
33
Printed by
ADAMU NAMAAN PRINTING PRESS
173 IsaWasiri Rd., Brd Lane Off 2oo Rd..
P.0. Box 1595. Kano
IDO UKU
2
Suleiman El-Ahmad Azare
IDO UKИ
UTTAFI NA BIYа
NA
SULEIMAN EL-AHMAD
AZARE
GABATARWA
Wannan rubutu ba shagube, habaici koko ba'a ga wani, wata, ko wata kungiya bane, ko kuma tarihin rayuwar wani, wata ko wata kungiya bane. Kage ne kawai. Duk wani abu da yai daidai da na wani, wata ko wata kungiya to Arashi ne kawai. Ance kwa Arashi na rariya mai raba Auren wawa.
Hakkin Mallaka (H) Suleiman El-Ahmad 1996.
An fara bugawa 1996
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan littafi ga dukkan wadda ya karantashi
DOKA
Ba'a yarda wani ko wasu su juya wannan littafi, ko wani bangarensa zuwa wani yare ko gyarashi ta ko wace hanya
ba tare da rubucecan izini daga marubucin littafin ba; don
gudun batanci.
Wannan cigaban littafi na daya ne zai fi kyau a karanta na
farkon tukun.
i
GODIYA
Ina mai godiya ga Allah (S.W.T.) daya bani ikon farawa da
kammalawa na rubutun wannan littafi mai suna IDO UKU......
Sannan dole in godewa abokai na Adamu Musa Hiyo da
Abubakar Sule Itas wadda suka bani shawarar in rubutashi
tun muna makarantar C.O.E. Azare (1990). Sai na fara na
barshi sai a wannan shekara(1995) na kammalashi.
Sai kuma M. Garba Mohd. GBS Bookshop Kasuwar Sabon
Gari, Kano da Bala Annas Babin lata wadda suka duba shi da
kuma bada shawarwari, nagode.
Haka Alh. Dan Bala da ya bada shawara wajen sunan littafin,
Shi wannan littafi an rubuta shi ne don gargadi ga matasa
daga mummunan dabi"u, da kuma shukura ga kaddarori da
kan auku cikin rayuwarmu.
Ina fatan mai karatu zai same shi da saukin fahimta da
karantawa, Allah ya taimakemu amin.
i
KASHI NA SHIDA
To shidai Rufa'i sai ya shiga cikin wata iri dimuwa ta me ya kamata yayi a wannan halin na rayuwarsa. Wannan kuwa ya faru ne ta sanadin abotar da ya kulla tsakanin sa da ita yarinya 'yar kabilar Mbatsat mai suna Quirana din. Sun hadu da ita ne tun lokaci da suka je irin aikin budar ido da dalibai kanje daf da zasu kare karatu, wato Aftachement. Daga makarantar gine-gine da zane (Art and Craft College) ta zo
wadda take anan garinsu Rufa'in. Kuma suna aikin ne a
ma'aikatar Fili da Safiyo (Land & Survey).
Quirana mai matukar kyauce da farin jini ga kyakkyawar kira
kamar ita tai kanta. Bata da makusa. In tana tafiya duk wadda
ya ganta sai ya sake wai gawa ya ganta, ko don farin da take
da shi, domin tana yin kode fata" da irin man nan na wanke
fata, ga iya tafiya da made ga kuma kisi-sina da iya jan
hankalin wanda ya hankalta da ita. Da wannan dai taja Rufa'i
har suka kullu. Duk randa suka hadu sai kyauta da saye-saye.
Harma ya kan kai mata ziyara lokaci-lokaci gidansu. Wasu
lokuta kuma yana yawan yin mafarkinta. Kai harma ta taba
jansa a mafarkin wani wuri wadda anan Rufa'i ya fara shiga
wannan hali na rudani. Kai har takai tana zuwa masa gida ziyara a cikin kurwa tare da abokanta. Duk da wannan bata baiya na masa manufarta ba, sai wata rana da suka je gun da suka
taba zuwa dinnan, anan Rufa'i ya ga abubuwan mamaki da ban
tsoro da aľ'ajabi, amma cikin lokaci kadan sai ya zama masa jiki kai
kace shima dama haka yake. Ya zama dan kungiyar asiri sosai
kuma cikakke. Kwadayí mabudin wahala inji Hausawa.
To duk da wannan Rufa'i bai sanar da wani daga abokansa,
yan'uwansa da sauransu ba. Kuma suma basu ga wani
34
chanji tattare dashi ba. Ko da sunga wani chanji dabam ma
basa tunanin akwai wani abu. Kuma dama a kaidarsu ba'a
baiyanawa saboda nifaqa.
Shi Rufa'i sunyi alkawari da Taja kan cewa zaije to amma sai
bai jeba a wannan daren. Cikin daren ne ya tafi gidansu
Quirana don ya gayamata halin da yake ciki. Da yaje sai ya shiga dakinta ya sameta tana barci, ta tafi chan duniyar da
suke zuwa. Rufa'i ya dawo gida. A daren sai suka zo masa
cikin mafarki suna jaddada masa cewa kar ya taba yarda da
wannan auren sai in matar zata bi ra'ayinsa. bayan gari ya
waye sai shima ya shiga tunani yaya akayi suka sani? amma
sai ya manta. Bayan sun karya sai ya tafi gurin Taja yana
zuwa, Taja ya bashi takarda daga Binta ya bude yana
karantawa kamar haka.
Zuwa ga abin begena dare da rana, ina fatan ganin wannan
takarda bazai zama abin mamaki ba gareka. A gaskiya ya Habibina, ina cikin matukar damuwa wadda take cina dare da rana, na san kana dan sona, kuma ni ma ina matukar sonka, to amma tsorona kar ka basar dani, shiyasa nake cikin dimuwa, saboda naga bakacika zuwa ba. Gidanmu sun san komi, kuma tun sati guda daya wuce suka ce in gaya maka kafito, to amma ina tamtamar gaya maka, shine Zaliha ta ce
in rubuto maka, don inji taka maganar, don haka ya hasken zuciyata ina ganin hanyarka ko takurdarka.
Nice Binta Demar.
Da ya kare sai yace "dir kashi! ana dara, ga dare yayi", Taja yana kishingide sai ya tashi yace me ya faru'? Rufa'i sai ya jefa masa takardar, shima ya karanta sai yace Talle fa, kanwar 35
tawa ce, koko kanwar devil. Af ni ina ma yake ne?" Muntaqa
devil? Inji Taja, Rufa'i sai ya amsa masa rikin fushi banda
yana prison na 'yan fashi har sun samasa CC (Criminal
Condem), Taja yace chab! lalle wuyarsa yayi karfi. Ai dama
karshe tika tika tik. Kuma karshen alewa".Rufa'i yace "kasa".
Sukai dan shiru kadan.
Rufa'i yana cikin sake-sake kamar bayan buzun Mallam, yaло
ta tunanin yadda zai bullowa Binta, ga kuma yaya za suyi da
Babansa akan Zainab, sannan ga Quirana ta kungiyar àsiri.
nan sai Taja ya tsinka masa wannan tunani da cewd di
chabin ka ne sai ka zaba ka darje, Ido uku duk sai sut dill
domin a gane ta kwarai,Rufa'i yace Ido uku wane iri.? Taja
yace ah! sune zuciya, kunne kuma da kwayar idon gaba
daya. Amma ni a shawarta, ina ganin waccan tafi, duk d
ban san halinta ba. Zaben iyaye ai ko tayaya yafi zaben yaro
don ta yaro kyau take bata karko. Abinda zasu hango yaro
bazai hango ba ko ya hau dutsen shira". Budar bakin Rufa'i sai
ya ce ai ko kudus suka hango sun daba a kas“. Yaci gaba da
cewa ai mu a tsarin mu babu haka, kuma auren sai a
junanmu, kuma da amincewar Dios" Taja sai kansa ya kulle
ya kasa fahimtas wannan magana, a zuciyarsa, yace mene
kuma Dios? Sai yace Rufa'i yaya dai? me kake nufi kana zahce
kamar wadda ya sha giya ko kwaya?" Rufa'i yace "a'a zaqumiya na
sha. Abin da nake gaya maka na san abinda nake nufi in kai baka
sani ba“. Sannan ya tashi tsaye yace "ka rakani gidan su Binta Taja
yace to me zaka je kayi? yace zan gaya mata ta nemi miji tun dare
bai yiba ni ina da mata', Taja yace" wa cecé"? Rufa'i yace "baka sanla
ba kuma ba zaka santa ba sai in na aureta?* Taja yace"kai Rufa'i
lafiya kuwa? yanzu har zaka auri mata amma bazan santa, to a ina
zaka aurota, ai ko daurin auren, maje "ina! ba zaka iya zuwa
ba inji Rufai don kana cin albasa da tafarnuwa kuma, kana
36
yawan karatun Alkurani. Amma in har zaka, to zaka bar
wadannan har na tsawon wata guda, to sai muje". Taja sai
yace "umh! nace baka hankalinka, kace a'a, ai wannan
maganganun naka, kasha abinda yafi zaqumiya ma", yaya
za'ayi ina musulmi, in bar addini har na tsawon wata guda,
Allah ya sauwake. "Amma ina ganin maimakon kaje har
gidansu gara ka rubuta kamar yadda ta rubuto". Rufa'i yace
kai bana son commitment, gara baki da baki' Taja sai yace to
amma sai in gobe ko jibi, don sunce zasu je unguwa don za
aiwa Zaliha kitso saboda haka gobe in kazo sai muje. Har ma
na basu katinansu na Valentine, yana ta al'ajabin abinda
Rufa'i yayi. Yana tunanin ko aljannu suka buge shi.
A can gidansu Rufa'in kuwa Balki ta gayawa Alhaji mai Wake
yadda sukayi da Rufa'i, to Basu hadu ba shine uban ya sami
Alhaji Usamatu suka tattauna akai, kan to yanzu yaya za'a
sanar da Mallam Ibrahim, ko kuma in ma za'a tilasta Rufa'i ne
to yaya za'ayi. Shine Alhaji Usamatu yace ai munyi zai zo ya
same ni don haka ni na san yadda zan yi da shi" To uban
wato Alhaji Mai Wake kunyar Rufa'i yake dan ji, kuma yana
matukar sonsa. Kuma dama abinda ya ke gudu kenan. Gaba
daya sai ya shiga damuwa. Ga hannun kyauta ya miko
amma hannun karba yana rawa.
37
KASHI NA BAKWAI
Rufa'i bai zo gida ba sai da dare can, Balki ta tambaya, ko sun
hadu da uban? Yace a'a, ya ci abinci, ya shiga daki ya kwanta
har yai barci. To a barcin ya dauko wata irin fuska ta roba mai
alamar idon uku na mutum, yasa, kace ido uku gare shi.
Dama da ita ake zuwa duniyar da suke zuwa, ruhinsu yakan je
duk inda suka yi niya koyaushe. A kwai wani zane marar fasali
a manne a dakin daf da kansa a sama da gadonsa. An
rubuta The Land of?' a jiki zanen. Ita Quirana ce ta bashi shine
shaidarsu. Ya duba zanen yace Good Dios'- cikin irin yarensu
ma'ana Da kyau Dious, sunan irin abinda yake musu jagora
kenan akan wannan kungiya tasu ta asiri mai suna KU KLUX
KLAN'sai ya fita ya tafi gidan su Quirana, ya same ta a barcin
tana kuma shirin tafiya, ta gama shiri ta dauki tata fuskar tasa,
ta duba irin zanen dake dakin Rufa'i tace Good Dious' sai
suka fita sai kan dan wani dutsi dake bayan gari, suna sauri
suka hau kai.
Tace bamu makaraba, suka dafa kirjinsu. Sai duka suka ce
llamor' ma'ana kamar sallama ce a bakin kofar da suke
shiga. Sai wata murya ta amsa Hora?' wato waye? sai Rufa'i
yace Dunga'ita kuma tace Dena'wato sun fadi irin sunan da
suke amfani dashi kenan a gun. Sai akace "caida bajď" wato
ku fado, sai baki daya sukai tsalle, suka fada.Kawai sai suka
dinga tafiya suna iyo ba tsayawa kamar tsutsaye can sai ga
su a wani katon kogon daki mai fadin gaske ga haske na
Diamond ta ko ina a manne jikin kogon. Kogon ga kanshi
kamar na fire marar dadi ga kuma jama'a kowa cikin irin wannan
fuskoki daban daban. Ana ta mahawara, wannan yai nan, wancan
yai can. Ana ta wani irin yare mara dadi, kowa yana gai da kowa
da cewa Comrade dia dia wato aboki sannu sannu. Wasu kuma
38
suna ta fadowa.
Can sai wani ya dirko da wata irin alkyabba mai daukan
haske tana ta walkiya. Wani abin mamaki da ya shigo sai duk
hasken gun ya dauke duka sai suka ce "Hurra Good Dious"
Barka da zuwa da kyau Dayos. To ba shine Dayos din ba. Shi
wannan wadda ya fi kowa gajarta a cikin jama'ar kai kace
yarone karami, shine shugaban 'yan kungiyar. Shiko Dious
shine suke jin mai basu abin da suke so na Duniya na daga
arziki, sarauta, shugabanci, ilmi, farin jini, kwarjini da dai duk
irin abinda suke da niya a zuciyar kowannen su 'yan kungiyar.
Shiru suna tsaye cikin duhu sai wata kofa ta bude sai ga
haske ya koma can, shugaba sai yace: "kada boka centro
palour" wato kowa ya shigo cikin falon shiri. Duu duk suka
shigo. Daga nan duk abinda za'ayi, shi shugaba ke bada oda
ayi. Sai yaci gaba da cewa "kada tener'mala vestido
piernaless". Cewa kowa ya iya canza kayansa rabida rabi. Ya
cigaba 'vestido blanco piernaless Figuras difunto", wato
fareren kaya da takalmi daya, kuma mu dauka a mace muke.
Duk baki daya sai gasu sun shiga farin kaya amma gefe guda babu, rigar dai rabi ce kuma da takalmi daya. To shima
wannan daki na biyu harma yati dakin farko kawa domin shi
akwai tebura a jere da kofuna na zinare da tagulla a jere ga
kuma wata babbar gidauniya mai ado da zane a jikinta kusan
irin na dakin su Rufa'i, tana sheki, tana canza launi. Duk sai
suka zo kusa da ita shugaba sai yace "mezclar bloo de vinor"
wato ku gauraya jininku da ruwan jiri' kowa sai ya mika hannunsa
cikin gidauniya wadda take kusan cike da wannan ruwa na jiri. Yayin
da kowa yakai hannu sai kawai jinin jikinsu ta yatsunsu tsakanin
faratansu ya zuba cikin gidauniya, kuma tiriri na tashi daga cikinta,
abudai tsafi-tsafi sai shugaba yace "kada Vra Vaso" wato kowa ya dauki kofi. Suka dauka suna diban wannan ruwan jini.
39
Shugaba yace "Alegrar! Agua" wato a hada kofi irin yadda
turawa kanyi. To cikinsu ba wadda zai gane wani, hatta shi
Quirana ba tunda suka Rufa'i bai san waye shiga. Kuma
cikinsu akwai turawa, shikansa shugaban bature ne, kuma
akwai hatta mutanen da kanzo daga kasashen Larabawa,
Asiya da Amurka, kuma shi wannan kogo da suke ciki, can
yake a dutsin maumau' cikin dajin Nyamkpe' a kasar
Qutamala'. Shike nan duk sai suka sha ruwa tare suna cewa
Good Dious. Kuma shi wannan ruwan tsafin ana sha ne da
nufin duk an zama iri daya kuma kowa ya dau halin kuwa, da
dabio'in kowa ta jini da aka sha. Mai kashin arziki da mai ilimi
da masarauci da dai ko wacce irin baiwace kake da ita to kun
hada tare kun raba a juna. Suna shan ruwan nan, sai kowa
ya canza. Idanuwansu ya juye ja zur, gashi ya mike tsaye
hakora suka kara tsayi, fikokin nan suka fito waje sai gurnani
suke yi kamar damisar da ta haihu, farata suka kara tsayi suka
lankwashe, kai abin dai kai kace aljannun kasar Magrib ne ko
ko irin dodainin nan da ake labari Gongi da Bongi. Shugaba
sai yace "Nor kada alma kambiar Diabla"wato yanzu kowa ya
zama dodo. Yaci gaba da cewa "lete culquira cengre"ma'ana
to kowa ya iya waka. Sai suka dau waka gaba daya suna
cewa "kada comida willow hehe" kada Agua'ra baber heh
suna tafi suna zaga gidauniya suna cin abincin da ke kan
teburan. Duk abinda daya yadiba kafin ya kai baki ya zama
tsutsa sai kawai a kai baka a hadiye. Kash! duk abin da
mutum ke fadi in yana can duniyar, to anan gunda yake
kwance ana iya fahimtar abinda ke faruwa don mutum zaiyi
tayin surutai kadan kadan yana ta motsi. Kuma duk kiran da
za'ayi masa bazai tashi daga barcin ba sai in ya dawo daga
waccan duniyar. To abinda ya faru da Rufa'i kenan, lokacin da Alhaji
ya shigo sai ya wuce dakinsa yai kira, shiru kuma kofa a bode gàshi
yana barci, ada kuwa kira daya ya tashi, sai uban ya shigo yai kira
40
amma ina! ya buge shi inaļ sai yasa salati ya kirawo uwar
suka ce ai bashi da lafiya, shike nan suna ta tsaye a kansa.
Shiko gogan naka ina suna can duniyarsu suna shagali.
Shugabansu yana cewa "lete praya wisho ciego" wato muyi
addu'ar bu katammu. Yaci gaba "sacre Buenos" wato sai
masu sadaukar da abinda suke so fi ye da kome suyi. Sai
kowa ya rufe ido yaci gaba da addu'a a karshe sai ya fadi
abinda ya bayar aje a shanye jininsa. Wasu suce hamono'
wato abokinsa, wasu kuma Los' da; wasu suce marido
mata ko miji, wasu kuma hijo' uba; sannan wasu sukace
madre' wato uwa. To shi Rufa'i alkawari yayi na babansa,
saboda haka aka zo sai ya kasa karasa sunan wadda ya
bayar har yace Hijo'wato ubansa sai ya fasa kuma ya tuna
cewa ai Alhaji Usamatu shine ummul-aba'isin hadashi da yar
Mallam Ibrahim kuma gashi zai iya bayar da shi,kawai sai ya
karasa "hamond Usamatu", wato abokin ubansa Usamatu:
Anan sai Alhaji Mai Wake yaji an ambaci sunan Alhaji
Usamatu kamar daga sama sai yai mamaki yace da Balki
Kiji! tace nai"sai yace mafarki yakeyi", Balki tace zazzabi ne,
inda kauye ne sai muce mayu ne, bare aji ya kira sunan wani?"
Rufa'i dai har yanzu yana can duniyarsu ta 'yan kungiyar asiri.
Sai dai a duk lokacin da uban ko uwar sukai salati ko ta'auwizi
ko kuma Hailala sai Rufa'i ya zabura. Shike nan sai uban ya
gamsu akan cewa ko iskokine? Sai yake tayi masa topi. Amma
da uwar tayi ta kokarin ya yarda akan ba wani abu Rufa'i ya
sha ba yaki. Shi a gunsa Rufa'i kawai ya sha irin kayan shaye
shayen zamani ne. Kamar yadda Muntaqa dan gidan Mallam
Ibrahim ya shiga shaye shaye, yaki makaranta har ta kaishi ga
zama barawo zuwa dan fashi. A karshe suka shiga gidan
wani attajiri da makamai sukai masa fashi har da yin fade ga
41
iyalinsa da 'yarsa a gabansa. Allah ya tona asirinsu aka
kamasu aka rufe, shine ake kiransa devil wato shaidan', tun
yana yaro mugune dama.
Yayin da Rufai ya daga katarsa duka biyu sama sannan ya mayardasu yaraf, sai uwar ta kama kirji, tana cewa Allah Sarki, Allah ya sauwake maka. Shikuwa ina, ana shirin fita ne. Sanda ya daga kafar yanabin odar shugabane yayin da yace kada nadar gymnasia Domir wato kowa ya tashi sama ya makale kamar jemage ayi barcin fita shan jinin wadda aka bayar. Shine suka tashi suka makale jikin duwatsu daga sama da dakin can sama kai kasa kamar jemagu, suna reto kuma
hannu nade idanu rufe, baki