ya shigo ta washe Baki tana mishi sannu da zuwa
Ta mike ta SHIMFIDA Mishi tabarma ya Zauna suna gaisawa Nimra Kuma ta shiga dakin maman ta kwanta don hajijiya ke neman kayar da ita..
Mahaifin Nimra ya shigo daga masallaci ya iske anam ya bashi hannu suka gaisa Yana tambayar shi Aiki da Rayuwa .
Anam Yana da mutunci a idon iyayen nimra Domin kuwa ya nuna musu shi Dan halal ne Wanda Yake taimakon su da nuna musu sun Zama iyayen sa shiyasa maman Nimra take matukar Jin kunyar shi musamman da ta San Halin yarta . Shima baffan Nata Yana matukar mutunta Anam don Haka yake Dan gida a wurin su fiye da Nimra...
Baffan ne ya dubi anam Yana Fadin
"Anam in ce dai ba wata tsiyar yarinyar Nan ta antaya maka ba....
"Eh baffa wani Abu ne dai tayi Wanda har naji ba Zan iya zuba Mata ido ba gara Nazo na sanar da ku don gaskiya Nimra tana neman kure hakuri na Amma nauyin ku da kunyar ku zai Hana na dauki hukunci da hannu na Amma don Allah kuyiwa tufkar hanci....
Jikin su yayi sanyi kalau suka zuba mishi idanu ya soma Koro musu abinda Yake faruwa na ciki da Nimra tace ba zata iya Raina da haifewa ba sai dai a zubar Kuma mummy ta goya mata Baya har kawo yanzun da mummy ta hado su akan suje a zubar da cikin shi kuma baya Jin zai yarda idan har cikin Nan ya samu matsala...
"Shine baffa na dawo da ita Nan wurin ku don na kafa ku shaida Kuma na ke so na roki alfarmar zaman Nimra a Nan gidan har zuwa lokacin da zanga abinda ya Dace Nayi tukuna ....
Maman ta Rafka salati tana sanar da Ubangiji tana Fadin
"Ni hajara Allah kayi min jarabta ta yarinyar Nan wace irin bayahudar yarinya ce ne Wai ? To ko Ni Kuma wallahi matukar tazubr da cikin Nan Zan Mata Allah ya Isa tunda inda ana zubarwa da ita Bata budi ido a wannan duniyar ba ...
Baffan ya soma Bawa anam hakuri Yana Fadin
"Kayi hakuri don Allah don bani da bakin baka hakuri m tunda na San kana kan yi ma Amma kayi Hankali da ka nufo mu da maganar Nan Kuma in Sha Allah matukar dai tana son gamawa da mu lafiya to Dole tabi yadda kake so ni na San kana hakuri da yarinyar Nan wacce Bata aje kanta Nan kusa ba Kai ka ce Yar wani ce ta samu Allah ya Rufa Mata asiri shine take son yayewa kanta ...
Ya soma Kiran ta tana daga kwance tana Jin duk abinda Yake faruwa duk da tafi Jin ta mama akan baffa Wanda bashi da wani tsanani kamar mama Amma a yau sai gashi ta karyata kanta domin kuwa duk da ciwon da take ciki bai Hana ya saka mabugi ya Bata Kashi ba har sai da Anam ya kwacw ta
Tun daga wanna Rana zaman Nimra ya dawo Gidan su Abinda Kuma yayi matukar takura ta Domin kuwa ko da mahaifin ta Yake da Dan rufin asirin sa to gidan Anam yafi Nasu gashi Babu Shiga Babu fita
Mummy Nina Kuma da taji shirun Nimra yayi yawa ta tambaye anam Wanda ya ce Mata tana gidan su Kuma ya kafa iyayen ta shaida matukar ya nemi cikin sa yarasa to ba zai yarda ba ...
Ina wuta ta jefa shi ta soma auna mishi Ashar da tijara kala kala amma ya faske Yana Fadin
"Ni fa wallahi aure na zanyi mummy na huta da wannan Bala in dakika ja min Nimra Kuma jira kawai nake ta haihu na Karbe Dana ko Diya ta na sallame ta don Sam bamu da gami hanyar jirgi daban da ta mota...
A Ranar ne kuma mummy ta nufi gidan su Nimra da son ta mayar da ita dakin ta Amma baffan ta yace tayi hakuri mijin ta yace a Barta har zuwa lokacin da Yake ganin kamatar ta koma din .
Duk yadda taso tafiya da Nimra Amma baffan ya kafe Dole kuwa ta bar shi Amma fa cike take da takaicin anam akan wanna matakin da ya dauka Akan Nimra inda tayi nufin tata mishi Rashin kirki Mai daraja.....
To Kai Kuma anam kaga ta Kan ka wane irin Rashin daraja ne wanna ? Wallahi ka samu wata kawai kayi ciki da ita ka rabu da su mace Babu kula yaushe ta Zama mace? Nimra Kam tsautsayi ne ya Kai ka dauko ta duk da mun fahimci Dole akayi maka to samawa kanka mafita Yasin 🙄
✍🏻 Alkalamin GIDAN IKO💖
[8/20, 10:53 AM] Gidan Iko: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
🧆 *_LINZAMI DA WUTA_*🧆
Pages
2️⃣1️⃣/2️⃣2️⃣
GIDAN IKO💖
_Kirkirarren labari ne da Bai shafi Rayuwar kowa ba kuskure ne babba danganta kai ko wani dashi babu mafi cancantar suyi suka akan labarin irin taurarun cikin labarin Wanda kuka San Babu su a zahiri to kar wanda ba cikin jaruman labarin Yake ba yace don shi ko don wani akayi Hakan jaruman cikin labarin ne kadai suke da damar sukar marubuci akan don me zai fallasaww duniya sirrin su_
_Fatan Aminci ne ga Amina baiwar Allah wacce Allah ya jarrabe ta da bauta Kashi Kashi Ubangiji ya jikan ki ya Baki ladar jinya Hawa Hawa_
_Gaisuwa ne ga dukkan masoyan Rubutun gidan iko musamman Wanda suka fahimci manufar Rubutun nawa Ubangiji ya amfanar damu alherin Rubutun kuskuren ciki Kuma Ubangiji ya yafe Mana_
_MUGUNTA_
💖
.................Mayra ta iso gidan cikin hadaddiyar motar ta wacce kallo Daya zakayi Mata ka yarda kudi suna magana sai dai ga Wanda Bai fahimci ta yadda suke maganar ba.
Mayra fara ce kyakkyawar gaske wacce ta kallo daya zaka yarda Mayra Mai kyau ce . Fara ce Mai kyakkyawar fuska Mai dauke da idanu masu kyawun zubi ga dogon hanci da giraren idanu masu tsari sai Ramin kyau a gefen fuskar ta wato dumful sai Dan karamin Baki Mai dauke da jajayen labba tamkar ta shafa musu Jan Baki Amma Haka Halittar ta ce .
Mayra ba Yar garin katsina bace Yar garin kaduna ce kuma Diya ce ga tsohon gwamnan kaduna saukakke. Iyayen ta suna can kaduna Amma suna da gida a Nan katsina don Haka in Mayra ta zo katsina gidan su take sauka
Tun lokacin da Mayra taga Hakim ta Rikice duk da tarin maneman ta Ya'yan wasu masu Rike da madafun iko Amma Mayra babu ajandar aure a tare a tare da ita duk da ma tarin maneman Nata Bata ga Wanda yayi Mata ba Amma ganin Hakim ya tarwatse Mata tanadi taji duk duniya Babu wani in ba shi ba har ta Kai ta sanar wa anty Nina ta Kuma Bata tabbaccin in dai hakim ne damuwar ta to anyi an gama Amma har yau da ake shirin Shiga watanni uku cur Babu wani gamsasshen Bayani shine ta iso da son Jin inda aka kwana...
Ta faka motar ta fito cikin shigar doguwar Riga wacce Bata Boye Mata tsarin Halittar ta ba don in ka zuba Mata ido da kyau ma gaban Rigar Wanda Yake da raga raga zaka iya hango kirjin ta Wanda Yake saye da farar bra da sashi sashi na jikin ta Banda bra din ma da tsab zaka ga tsayuwar kirjin nata...
Sanye take da takalmi high Hil Mai madauri silver color sai Yar karamar jaka itama silver color sai siririn agogo Mai hannun sarka da Yake a farin hannun ta yayin da ta yiwa gashin ta dauri Mai burgewa duk Bata daura Dan kwalin ba yafa shi tayi kamar gyale hakan zai baka damar ganin gashin nata soasai
Kamshin turaren ta kuwa tamkar wacce akayi barin turaren a kanta don tun daga parking space na cikin gidan ya jiyo shi
Hakim Yana dakin sa Wanda Yake Dan da parking space din yajiyo kamshin wanda ya sa shi ya mike Yana dage labulen tagar dakin nashi da son yaga waye ? Duk da ya San ba Zai wuce shegun bak'in mummy ba Wanda ya tsana fiye da zaton Mai zato don ya Rasa makasudin zuwan Nasu tunda ya San ba wani kasuwanci take ba bare ace ko hajar ta suke zuwa siye
Yana dage labulen ya hangi Mayra wacce shigar ta ta Kara darsa Mishi tsanar ta....
"Don Allah dubi shigar yarinyar Nan Bata da maraba da tsirara
Ya fada ba tare da ya Shirya magana Akan ta ba don Allah yayi shi da tsanar mace Mai nuna tsiraici . Yana son ganin mace cikin shiga ta mutunci da kamewa . Mace wacce ta San ita mace ce Mai daraja sai yaji lallai duk Wanda ya Dace da mace kamammiya lallai yayiwa Ya'yan sa Uwa ta gari shiyasa yake tausayin brothe din sa anam Wanda ya Gama fahimtar mummy Kam sai a Hankali....
Yaja tsaki ya saki labulen ya koma Yana karbar Ruwan coffee Mai zafi ya soma Danna wayar shi wacce katon hoton Halimatu ya mamaye screen din wayar ya zuba Mata ido kafin ya sumbaci hoton ya Kuma Danna Mata Kira ....
Mayra ta shiga gidan tana taku irin na Mata masu aji..kamshin ta ne ya sanar da mummy zuwan ta ta Kuma fito tana Fadin
"Wannan kamshin Mayra Aisha ne Yar Halak kink'i ambato yanzu nake maganar ki a Raina Ashe kina tafe .....
"Kar dai har an kashe Boos anty?
Mayra ta tambaya cike da doki da ci da zuci ...
"Me kike ci na baka na zuba ne Mayra ? Ni fa nace Miki anyi an Gama ....
"Na kasa nutsuwa ne anty tun daga Ranar Nan na kasa Zama lafiya gayen ya tsaye min A Rai ne ko Babu komai yanzu Nazo muga juna naji Kuma irin yadda yake Sona....
"Uban yaron Nan fa a hannu na Yake Mayra sai abinda nace da shi bare Hakim da baya tsallake maganar Uban sa don Haka Bari na Kira shi yazo Nan ku gana tunda na kula dai Mayra kina Dab da zautuwa...
Mayra ta zauna akan kujera tree seater tana Dora kafar ta Daya Kan Daya tana kada su tana aje key din motar ta da Jakar ta s saman center table tana Fadin
"Ai anty bature yayi gaskiya da yace love at first sight wallahi Naga hakan don Allah Kira min shi ko kollon sa nayi na Rage radadin da Yake zuciya ta ....
Nina taja wayar ta tana kiran wayar hakim Wanda ta samu laying nashi Yana busy sai waiting Yake nuna Mata ..
Fiye da mintuna talatin Nina tana Kiran wayar hakim Yana ta busy...
"Yau dai bashi da Aiki to wayar ta mecece Haka ?
Ta mike tana Kiran Dan ladi Mai wanki tace ya Kira Mata Hakim a dakin sa
Hakim Yana Zaune Yana waya da Halimatu Wayar da ake kona kudi b kad'an ba wacce ake kwashe fiye da minti sitting ana yin ta Kai har wucewa ma...
Dan ladi ya sallama a kofar Yana Kara sallama
Hakim ya mike ya fito Yana duban Dan ladi wanda ya isar da Sak'on mummy na Kiran shi da take
Ya jawo kofar ya na Kare da wayar shi suna ta misayar Kalamai shi da Halimatu
Yana shiga ne yace ta Bari zai Kira in ya fito.
Ya shigo da sallama ya zauna Yana Fadin
"Mummy kina Kira?
Ya fada fuskar shi Babu yalwa don irin yadda yaga Mayra ta tsare shi da idanu shi kuma tun Ranar da ya iske su ya Kuma ga irin kallon da take mishi Yaji ya tsane ta matuka Gaya don Sam bai ji mutuniyar kirki bace bare Kuma shigar ta da irin adon ta na nuna tsiraici....
"Eh Hakim dama Mayra ce Zaku gaisa gata nan ...
Ya juyo ya kalli Mayrar da tsukakkiyar fuska Babu sassauci kafin ya mayar da kallon shi ga mummy Yana Fadin
"Wace irn gaisuwa Kuma mummy? Ya sake kallon Mayra Yana Fadin
"Ya kike?
Tayi murmushi tana Fadin
"Lafiya Lau ya kake,?.
Yana Gama fadar hakan ya mike zai wuce Nina ta tsayar da shi tana Fadin
"Kai bana son hauka kaji. Gaisuwa irin ta fahimta nake so kuyi don tuni muka magana da Daddyn ku ya ce na zaba maka Mata kamar yadda nayiwa anam shine na ce mishi ga Mayra nan ya San Uban ta tsohon gwamnan kaduna ne Kuma ta Dace da Kai shine nace tazo ku zanta na San dai irin choice din ka ce don Babu inda ba za a nuna Mayra ba ba tare da anji kunya ba dube ta da kyau zaka Gane ta Dace da Kai matuka Gaya don na San Kai Dan gayu ne shiyasa ma na zabo maka wacce zata Dace da Kai.....
Yayi murmushi Yana Fadin
"Ni mummy ai ba Dan gayu bane Dan islamiya dai ne Wanda Yake son yayi komai irin na islam don na Gane musulunci shine kawai karbabben addini wurin Ubangiji Amma wannan matar da kike magana ai matar Yan boko ce dube ta fa ?
Ya fada Yana nuna Mayra wacce ta kasa dauke idon ta daga Kan Hakim....
"Ni fa ban Kira ka don ka nuna min boko da Islam ba Mayra na Kira ka ka gani don na fita hakkin ka Kai da ba iya maka ake ba yanzu meye aibun ta to?....
"Ga aibu Nan kina kallo mummy dubi yadda ake iya ganin under din ciki Mana. A Haka kike so na aure ta tana yawo tsirara? Sam Ni ba na son irin wannan matan Wanda mazan duniya suka gama kalle su sai kace dai wani jaki na dauki abinda kowa ya Sani ? ....
"Zage Ni kawai Mana Hakim saboda nayi maka abin alheri...
"Ba abin alheri bane wannan mummy Ni fa ba Zan yarda ayi min auren da akayiwa Yaya Hakim ba tunda akan idona komai Yake faruwa Kiri Kiri shi da gidan sa an Hana shi yayi komai bare a bar shi yayi iko da gidan shi Ni Kan wallahi bana so mummy ki ma fadawa Daddy Ni bana son irin wannan auren a barni na zabi kalar macen da nake so Mai hjabi Yar islamiya iri na wacce Kuma zata yarda nine mijin ta ba Mai cikakken Yanci a hannun ta ba .....
"Ai kuwa ka San kayi karya wallahi ayi magana da iyayen yarinyar Nan Kai Kuma kace zaka mayar da Uban ka karamin mutum ba.....
"Ai ban ce a nema min auren Nan ba mummy Ni fa ina da wacce nake so wacce ta Zama irin yadda nake so Yar islamiya ba Yar boko ba wacce Bata bayyana jikin ta ga Kare da doki ko Ni sai nayi da gaske na iya ganin fatar jikin ta bare Kuma wurare masu daraja don Haka mummy ayi hakuri ba Ni ba wallahi ko brother ba Zan sake Bari ayi mishi irin auren Yan iskan can da akayi mishi ba Wanda Bai Kara mishi komai ba sai bak'in ciki Ni da na San hakan ma ai da ban yarda ya Karbe shi ba wallahi ....
Dr Anam ya iso gidan ya Sami wannan chapter ya dubi hakim Yana Fadin
"Kai Kar ka sake wallahi ka tsaya ka duba Yar mutunci don ni Yar gidan mutuncin ce Amma Babu mutuncin kawai mummy a fadawa Daddy Yana da wacce Yake so Amma ai naji Dadi shine garin ba na saba ba....
Nina mike a fusace tana Fadin
"Yanzy in Hakim ya wulakanta Ni Anam Kai zaka yarda Kai ma ka wulakanta Ni? ....
"A a mummy wallahi ba wulakanci bane yayi Miki ita yarinyar ta Rasa Mai so ne ko kuwa wahayi akayi sai Hakim ne zata aura? Don Allah mummy ki Rika duba abunda zai je ya dawo yanzu yadda na Rasa mutunci a idon Nimra ai ba Zan so Hakim ya kasance irin yadda na kasance ba don Haka ki Bawa yarinyar hakuri kawai ta nemi wani gaba shikenan....
Mummy ta fice daga falon yayin da tayi hikimar janye Mayra zuwa uwar dakin ta tunda ta fahimci boren da Hakim zai Mata ...
"Kai wallahi Kar ka yarda a cuce ka Hakim Ni wannan kyalkyalin Kar ya dauke ka cuta ce wallahi ka auri matar ace baka Isa ka saka ko ka Hana ba? Ni fa yanzu tana gidan su na mayar da ita na jingine ciki ne fa da ita Amma Wai mummy ce ke goyawa Nimra baya Wai a zubar kaji fa? To wallahi Kai idan ka sake suka jona maka wanna yarinyar Mai Kama da kilaki sai ka fini Shan wahala tunda ana takamar Yar wani ce Uban ta tsohon gwamnan kaduna ne kofar rago zasuyi maka ....
"Ni yaya ai na Kama wacce nake so ma Kuma Yar mutunci ba irin wannan da take yawo tsirara ba....
Mayra ta dubi Nina tana Fadin
"Na kula gayen Nan Jan wuya ne anty zai bani ciwon Kai...
"Wallahi yaci Uwar karya ya kwana da yunwa Mayra bari ki gani ai yayi sake da ya Bari na Riga shi zuwa duniya na Kuma fi shi makirci....
Ta jawo wayar ta tana Kiran Daddyn Nasu
Kara biyu uku ya dauka Yana Fadin
"Dearest Yaya ne?
"Distinguish nayi maka over talking fa na yanke hukuncin auren Hakim ban sanar maka ba sai da magana tayi nisa don Haka ina so manya su Shiga cikin maganar don ban yarda da yaron ba ya soma leke leke Ni Kuma abinda nake tsoro kenan idan ya waye da Hakan to likkafar neman matan shi zata wuce Haka don Allah manya su Shiga cikin maganar....
"An Gama my dearest a Ina ne ya Samo yarinyar?...
"Shi fa Babu maganar aure a gaban shi nice dai na sama mishi wacce kowa zai yaba Yar gidan a fakallahu na kaduna ai ka San shi ....
"Sosai kuwa to Bari ma na Kira shi mu yi magana kome kenan sai na tura su iliyasu suje mishi tambayar...
"Yauwa gara ayi a Gama da zafi zafi akan Daki karfe Nagode distinguish sai na shigo Abuja Zan maka surprised zuwan ba zata ...
"To Ina saurare..
Ta aje wayar yayin da Mayra ta jinjina Mata Hannu tana Fadin
"Kai anty wallahi kin iya Allon ki har anyi an Gama?
"Uhum ai yaron Nan sai na na fito mishi ta Bayan gida wallahi Yana bani ciwon Kai da yawa bashi da tsoro ko shakka tunda ya Gane wani Abu ya ke min Jan Ido Amma ki bar shege ya Shiga koma shima......
Ziyada ta daga waya ta tana kallo cike da mamaki kafin ta dube ni tana zaro idanu tana Fadin
"Kika ce farin mutumin Nan ya Baki ita Halimatu? Haba no wonder wallahi irin kallon da Naga Yana Miki na San an gamu Amma fa kun matukar dacewa wannan Zan so Naga Ya'yan ku Halimatu kyau cikin kyau kai Masha Allah Amma kin kuwa San tsadar wayar Nan? Wallahi in Kika ji kudin ta Zaki Sha mamaki don duk garin Nan masu ita zasu lissafu cikin sauri don ba Duka Kai ba sunan wata hula....
Nayi murmushi Ina Fadin
"Kai Ziyada kin San Abu Mai tsada amma Ni kin San ba tsdar wayar ne a gaba na ba irin tsadar Wanda ya bani wayar a zuciya ta? Wallahi Ziyada in dai Haka so Yake sai nace Babu abu Mai Dadi a duniya irin so musamman son Wanda Yake son ka wallahi Ziyada ina son Hakim irin son da in na Rasa shi Zan mutu....
Ziyada ta kame Baki cike da mamaki tana Fadin
"Tabdijan Nan Kam tun ba a tafssa ba za a kone ....
"Wallahi da gaske nake Miki Ziyada kwanaki fa Yan iskan matsiya tan mutanen can masu bakaken Kaya suka Kama mini shi suka kulle saboda lambar mota kawai ai ban tab'a tsanar Yan sanda ba sai da suka Kama Hakim wallahi....
"Ai fa Abu yazo ga masu iya shi to shi kuma Dan bawan Allah balange Kuma a Ina a ka Dora shi tunda na kula Hakim ya mamaye zuciyar....
Nayi tsaki ina Fadin
"Don Allah Ziyada bar tuna min wani balange da ko sunan sa ma yake Tayar min da zuciya ke in banda Rashin adalci nayi Miki Kama da irin matar balange? Ai matar balange tana kauyen su kamar yadda Nima nawa mijin yake Dan garin mu...
Wayar da take hannun Ziyada ta dauki tsuwwa ta duba inda taga hoton Hakim Wanda ya mamaye screen din wayar yayi kyau matuka Gaya har ita da kanta Ziyada taji wani Abu Akan kwarjinin Hakim da sauri ta Miko min wayar na dauka ina shigewa uwar dakin Dada muka balle da fira wacce yake fada min kalaman da suka sa naji duk duniyar ma Babu mace sai Ni . Muna kwashe fiye da awa muna waya har nayi ta Mamakin kudin d yake zubawa
Tun Ban goge da iya fira da Hakim ba har na Saba da mayar da martani abinda ya karawa soyayyar mu wani irin armashi Mai yawa muka Kara kullewa muna Jin tamkar zamu hadiye juna saboda kauna da soyayya...
Tun Ziyada na jiran na Gama wayar Nan har ta gaji Tayi tafiyar ta gida tana Fadin
"Wannan Kam in aka barsu kwana zasuyi suna magana Kai sabon shigar soyayya sai ka Rufe idon ka in kuwa ba Haka ba yanzu ne zaka Sha kunya............
To ko hakan ne Halimatu? Ko kuwa SHARRIN Ziyada ne? Amma dai Bari muga yadda za a kare wanna kitimirmira tsakanin Mayra da Hakim ga can dai za a Kai kudin neman auren Amma ango Bai Sani ba......
✍🏻 Alkalamin GIDAN IKO💖
[8/20, 10:53 AM] Gidan Iko: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
🧆 *_LINZAMI DA WUTA_*🧆
Pages
2️⃣3️⃣/2️⃣4️⃣
GIDAN IKO💖
_Hakkin mallakar ma na gidan iko ne kuma abin kiyayewa ne kowane Abu Yana da mamallakin sa Babu Kuma Mai son a daukar mishi kayan sa ba tare da izinin sa ba mu kiyaye hakkin juna sai mu Zauna lafiya_
_Gaisuwa ga dukkan marubutan mu masu kokarin kawo gyara ba masu son tarwatse tarbiyar yaran Al umma ba Allan ka Taya musu kayi Ruko da hannayen mu Baki Daya_
_Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da Aminci mara yankewa zuwa ga shugaban mu fiyayyen halitta ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam da ahalin gidan sa madaukaka da masu bin su da kyautatawa har izuwa Ranar Alkiyama_
_DANGIN SHAIDAN_
💖
...................Nimra ta iso gidan anty Nina a fusace tamkar mai shirin kamaww da wuta inda kuma aka hadu Mayra da nimra suka hadu haduwar bazata. aka yi kallon kallo cike da izza kowa najin zafin kowa nimra taja tsaki kafin kowace ta kawar da kanta cike da takaici da Jin tamkar ta shake Yar uwar ta.
Nimra ta wuce zuwa Dakin anty Nina yayin da Mayra tabi ta da kallon cikin jikin ta Wanda ya turo Riga taja wani tsaki Mai karfi tamkar zata tsunke harshen ta abunda ya fusata Nimra wacce taji tsakin Mayra Amma bata dawo ba ta shige Uwar dakin Nina
Nimra da Mayra ba a ga maciji tamkar masu ganin hanjin juna . Nimra dai tana yakar Mayra ne da kyawun da tafi ta baza capacity a ko ina ne kuwa kyawun nimra ya zarce na Mayra . yayin da Mayra kuma take yakar nimra uba da kudi da girman gida har da mahaifi Wanda Yake tsohon gwamna. Al Amarin Nasu dai dadadde ne Wanda ya Samo asali Kuma har yau din Bai Kare ba ba Kuma zai Kare ba _kun San dalilin wannan tsama kuwa? Ku biyo ni na fallasa muku sirrin_
Anty Nina ta fito daga wanka taga Nimra wacce duk ta fita a hayyacin ta yayin da laulayin ciki ya tasa ta a Gaba duk ta fita hayyacin ta tausayin ta ya Kama Nina duk da ta kula kamar a fusace Nimra take don har ta iso inda take tana Fadin
"Nimra me Yake damun ki ne duk Kika sauya Haka?
Nimra ta dago cike da fushi tana saukewa Nina wani shegen kallo tamkar zata kama da wuta tana Fadin
"Har ma za a dube Ni ace tambaya ta abinda ke damu na za ayi? Nifa nace ba Zan haifi cikin Nan ba Kuma Haka nake nufi amma saboda Rashin adalci kin San ya mayar da ni gidan mu ya Kuma zayyane musu komai har da gindaya sharuda Amma anty kuka banzatar Dani Babu ke Babu shi? A Haka