Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 11
karfe biyu saura kwata na Daren. Ya shafi sumar da take kwance a kanshi Yana Rintse idanu Babu abinda Yake hangowa face kyakkyawar fuskar ta da Kuma sassanyar muryar ta da take rero Kira ar ... Ya jima cikin shiru kafin ya mike saboda ya Gane ba zai iya Samun bacci a yanzu ba. Ya kawo farar jallabiya ya saka ya nufi kofar toilet ya tura ya shiga ya dauro alwala ya fito ya shimfida sallaya ya Tayar da salla Raka a hudu yayi ya Zauna tasbihi ya jima kafin ya Daga Hannu sama Yana ADDU A Mai tsayi kafin ya shafa tare da bude alkur Ani Yana karatu. Sai dab da asubahi ya ji BACCI na fizgar shi Amma sai da yayi salla kafin ya kwanta... Yana kwanciya kuwa bacci ya fige shi cike da mafarkai akan ta... Wayar sa ce ta Tayar da shi ya bude Ido cike da bacci inda yaga sunan mai Kiran abinda ya tuna mishi da Aikin da Yake hannun shi Dole ya mike ya shiga toilet yayi wanka. Ya fito ya shirya cikin Kayan Aiki Yana tsaye a gaban mirror Yana sharce sumar sa inda ta cikin mirror din Yake hango gizon yarinyar abinda yasa shi juyowa Yana kallon dakin Amma Bai ga komai ba. Ya Zauna cikin shiru kafin Kuma ya jawo farar takarda tare da kaloli irin na art ya soma zana fuskar ta har da kalar Rigar da ya ganta Mai stone. Kan kace me? Ya Gama zanen ya daga takardar Sama Yana kallo yayi murmushi ya sumbaci fuskar ta ya linke ya nufi fita ko kofar mummy din Bai duba ba ya fice ya Shiga motar shi ya fice daga gidan... Mummy din Ashe jiran shigowar shi take Amma sai Jin fitar motar shi tayi. Taja tsaki tana Fadin "Wannan yaron fa in banyi sannu ba zai bani ciwon Kai kamar yadda uwar sa ta bani..... Ina Zaune akan kujera tree seater a dakin Dada nayi shiru don tun lokacin da Goggo Dubu tayi min maganar Nan na Zama wata lazzy magana ma sai ta Zama Dole nake yin ta. Babu abinda nake tunani irin shin tsakanin Uwa da Uba na wanne ne Wanda yaja min bakin fenti da mugun tabon? Shin su waye ma iyayen nawa? Kuma Ina suke da har suka barni hannun dada wacce na jima da Gane kakata ce don Nasha Jin tana cewa mutanen da suke tambayar ta Ni din ta wurin waye? Sai tace ta wurin Hamza ce. Sunan hamzan kawai na Sani Amma ba Zan iya nuna shi ba. Cike nake da tarin tambayoyi Amma Kuma na San furta su daidai Yake da bacin Ran Dada shiyasa na hadiye kayana. Na mike da nufin na tafi gidan anty sa a yayar Ziyada wacce tace nayi Mata laifi ban Kai Mata Allon sauka ba shine nace zanje na Bata hakuri Na dubi Dada Ina cewa "Dada zanje gidan anty sa a Ziyada tace min wai nayi mata laifi ban Kai Mata Allo ba.... "To maza ki Shirya kizo ka kudin Napep ki tafi Kuma don Allah ki saki ranki bana son Ina ganin ki kinyi shirun Nan .... Na wuce bandaki na bar Dada tana magana akan shirun nawa. A Raina Kuma cewa nake to me Zan ce? Ai gara na koyi kame Baki na tunda in nayi magana ne ake neman mayar min da aibu na ko na Uwa ta ko na Uba na Wanda ban San me sukayi ba... Ina cikin makewayin ne naji zuwa wani mutum Wanda kamshin turaren shi ya iso har cikin ban dakin inda naji Dada na Fadin "Iko sai Allah Hamza Kaine? Gaba na ya Amsa da karfi duk da ban San dalilin hakan ba. Sai naji Ina son nayi na Gama na fito don Naga waye wannan bakon na Dada... Na Gama wankan na fito inda Naga sai shigowa ake da kayayyaki dangin kayan abinci buhuhuawa ana ta saukewa a kofar Dada Wani kyakkyawan yaro Dan kimanin shekara biyar na gani fari tas Yana tsaye bakin kofar dakin Dada da kwalbar lemu Yana Wasa da ita . Na samu kaina da zuba mishi ido Ina Jin wani Abu Yana fizgata zuwa gareshi har na kamo hannun shi ya dago Yana kallo na kallo irin na neman ba asi... Kukan dada shi ya saka Ni ajiye yaron na nufi kofar dakin Ina sallama ban jira an bani izinin Shiga ba na shige don inga abinda ya saka Dada ta kuka.... Wani kyakkyawan mutum ne fari tas Mai Kama da yaron Nan Yana durkushe a gaban Dada Yana Rike da Hannun ta shima Yana kuka fuskar shi Sharkaf da hawaye.... Ina shigowa Dada ta daina kuka shima ya zuba min Ido Yana kallo na inda Naga kamar na tab'a ganin shi Amma Kuma ba Zan iya tunawa ba.... "Kiyi min gafara dada Ni Mai laifi ne a wurin ki Amma Allah ya Sani ban San abinda ya ke dauke min Hankali da gida ba har dai na Gane mutanen Nan ba Haka suka barni ba don Allah kiyi hakuri Dada ki yafe mini ki saka Ni ADDU AR ki Allah ya yaye min abinda Yake kaina.... "Na yafe maka Hamza na Sani ba Haka mutanen Nan suka barka ba Kuma Ina ADDU A gashi Kuma Allah ya nuna min Yana karba mini tunda yau gaka gaba na Ina fatan dai kana Nan a musulmin ka Basu kafurta mini Kai ba kamar wancan lokacin? Ya gyada kanshi Yana Fadin "Ina Nan a Muslim dada Ya'ya na ma Haka itace dai nake ta kokarin jawo ta Amma mamar ta tana hanawa... "To alhamdulillahi Hamza wannan shima naka ne? Ya Amsa Yana Mai jawo yaron Yana Fadin "Ameer come great my mother.... Yaron ya jiyo Yana kallon dada Yana Fadin "Sweet Daddy this is your mother? Ya fada Yana nuna dada shi kuma ya kada mishi Kai sai yaron ya taho Yana mikawa Dada hannu Wai suyi Musabaha. Dada ta karba tana fadin "Yanzu Baku koyawa yaron Nan hausa ba sai yaren uwar sa? Yayi murmushi Yana Fadin "Ba yaren Uwar sa bane dada turanci ne Kuma ya iya hausa can inda muke ne galibi da turancin ake komai .... Na matsa Ina ce mishi "Sannu da zuwa Ya juyo ya Kuma zuba min Ido yana Fadin "Dada Halimatu wannan ? Ya fada Yana nuna Ni Dada tace "Itace.. Ya jawo Ni jikin shi ya rungume Yana Fadin "Halimatu ki gafarce Ni kinji ki yafe mini alhakin ku da Dada ya ishe Ni.... "Ai bana Jin ma ta San ka Hamza wata Kil dai sunan kawai ta Sani... Jiki na yayi Sanyi don na Gama Gane shine mahaifi na Amma meye nake Jin Yana fada?.... Ya jawo hannun Ameer Yana Fadin "Ga Dan Uwan ki Halimatu mahaifiyar ki tana cike da kewa da begen ki ta bada Sak'o na Baki ga Kuma Ameer Nan Dan uwan ki ne dauke shi kuji dumin juna... Na damke Ameer Wanda Yake cewe "Daddy how she it? "She is anty.... Kan kace me? Sai kofar dada ta cika da mutanen gidan ana tayiwa baba na barka inda baba Headmaster yake ta mishi fada sai ga yakumbo na mariya ta iso wacce itace karamar su a cikin Ya'yan dada . Goggo jauhara ta zubo taliya Mai yawa ta kawowa Ameer ta Kuma gaisa sa baba na tana tambayar shi iyali. Goggo Dubu ma ta shigo sun gaisa Amma ita Kam Bata tambye shi kowa ba ta juya Sai da dare yayi dada da danta suka sake Zama ya fuskance ta Ni Kuma Ina tare da Ameer Wanda ya like min ko ina Ina tare da shi inda naji abinda baba na Yake cewa Dada "Dada idan ba Zaki damu ba ina son Zan dauke ku ke da Halima mu tafi can ko shekara daya kuyi min in Kuma garin yayi muku shikenan sai kuyi zaman ku a can.... Da sauri dada tace "Cikin arnan? Ka manta yadda muka Rabu da iyayen matar ka akan Halima? Allah yasauwake ai Ni nayi zaton ma ka sakar musu Yar su ne ka dauko danka ka dawo arewa ?... "Hakan nake fata Dada Amma Allah ya Sanya abincin nawa a can Kuma Ina son na jawo matata ta Rabauta da addinin musulunci in Sha Allah sai nayi hakan dada .... "To mu dai ba zamu bika ba wannan yaron ma da kazo da shi ba Zan Bari ka koma da shi ba shima yazo kenan don na tabbatar idan har matar ka tana Nan a cikin kafircin Nan to Ya'yan ka ma gasu can sun Zama kafurai don Haka Kai dai ka koma Kuma wannan yaron shikenan ko a kwai wani ? Yace akwai kanin sa dada ... "To shima dauko shi ka kawo mini Ni Kuma zanyi ta ma mutanen can alkunut har Allah ya dawo min da kai Nan Amma Ni ? Yaushe Zan koma wannan garin ? Ai ba rantsuwa ba Baki gari duk kafurai... Washe gari Dada tayi ta Rabon kayan tsaraba ko Ina sai da ta aika har makotan ta sai da ta Bawa tana ta fadin baban Halimatu ne yazo Kwanan Baba na uku yace zai koma saboda Aiki inda dada tace sai ya bar Ameer Amma yafada Mata in ya koma Babu Ameer har kashe shi ana iyawa don Haka Dada tace "To yanzu sai yaushe? "In Sha Allah Nan kusa Dada ayi Mana ADDU A in dai Ina cikin Hankali na irin Haka Babu abinda zai sa na jima banzo na ganki ba. Da wannan sukayi sallama ya fuskance Ni yana Fadin "Halimatu Zan tafi ga kudi kiyi duk abinda kike so Dada ta ki muje kiga mahaifiyar ki .... "Zamu zo wata Rana Daddy a fadawa mama ta I love her... Ya tafi ya barni cike da wani irin rudani Wanda Yake kulle a cikin duhu Wanda nake son sanin ta Yaya akayi Hakan? Dada ta ce kawai Mai iya kwance mini bakin zaren ita Kuma bana son abinda zai Bata Mata Rai Amma na San da sannu komai zai fito a fili har naji na Kuma gani Amma wane irin Al Amari ne tsakanin mahaifiya ta da mahaifi na?....... Lallai Nima Ina son sanin hakan don ABIN DA MAMAKI Kam duk da bamu ji mamaki ba sai an baje komai a faifai...... ✍🏻 Alkalamin GIDAN IKO💖 [8/20, 10:53 AM] Gidan Iko: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 🧆*_LINZAMI DA WUTA_🧆 Pages 7️⃣//8️⃣ NA GIDAN IKO💖 *_Fatan alheri ne ga mahaifiya ta Haj Rabi atu abubakar magaji Yar adua Allah ya Kara lafiya da sutura_* *_Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da Aminci mara yankewa zuwa ga shugaban mu fiyayyen halitta ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam da ahalin gidan sa madaukaka da masu bin su da kyautatawa har izuwa Ranar Alkiyama_* _DA MAMAKI_ 💖 .............Kaya sosai Baba na ya kawo mini tare da Wanda mahaifiya ta bashi ya kawo mini. Tuni zuciya ta ta Shiga fasalta min mahaifiyar taww Wanda na soma shinshino ahalul kitabi ce wacce Kuma bana ko shakkar kasancewar ta ahalul kitabin ne ake goranta min bak'in fentin da Kuma mugun tabo. Zuciya ta ta Shiga laluben ta Yaya mahaifi na da Yake musulmi har ya auri ahalul kitabi? Sanin bani da wannan amsar yasa na watsar da komai na kuma ji a Raina ina kaunar iyaye na tunda Suma suna kauna ta ko ban shaida ta mahaifiya ta ba na shaida ta mahaifi na Wanda a cikin kwanaki ukun da yayi ya nuna min kauna matuka Gaya har ban so Rabuwa da shi ba bare Kuma ameer Wanda muka Rabu Yana ta tsala kukan ba zai bi sweet Daddy ba wurin sweet anty zai Zauna da mother Daddy. Kai kayan da mahaifiyar taww ta Aiko min kadai ya Isa ya nuna kaunar da take min Domin kuwa har da Yan kunnen gold masu daraja ga kuma suturu masu tsada duk da dai English wear ne Babu wata atamfa ko lass bare doguwar Riga. Amma na Daddy Kam kamar ya San Ina son dogayen riguna da after dress..... "Ikon Allah kenan bana fa shekara Tara kenan Rabon Hamza da garin Nan Kinga Allah Mai Amsa Rokon bayin sa ya karba min ADDU A ta har ya waigo gida. Allah sai yayi mini sakayya Akan mutanen can don ba Zan tab'a yafe musu ba in banda Allah yaga tsayuwar da nayi a darare mafi daraja da yanzu sun mayar min da shi kafuri ahalul kitabi wace asara ce tafi wannan ka haifi Dan ka musulmi Amma mishan Mai badda musulmi ya fidda shi daga musulunci ya mayar da shi kafurci ? Sai Kuma ta fashe da kuka tana fadin "Allah ka tsaya wa Dana kafi kowa sanin ahalin musulunci ne Kar ka Bari arna suyi nasara akan sa ka tabbatar da shi a musulmin sa ..... Na mike Ina ture Kayan da nake ta dagawa Wanda suka burge Ni na Kama Hannun Dada ina Bata hakuri.... "Kiyi hakuri Dada ADDU AR da kika tabbatar itace makamin ki itace kawai Zaki Rike in Sha Allah Babu abinda zai same shi Nima Zan saka shi cikin ADDU A ta.... "Sun tab'a fidda shi fa daga musulunci suka mayar da shi addinin su na kiristanci sai da Allah ya nuna min a MAFARKI na Kuma Isa can garin na Kuma ga hakan a zahiri shine Nazo na saka malamai aka yi ta Rokon Allah Har mukayi nasara.... Wani Abu ya tsikari zuciya ta naji Ina son sanin yadda wannan Al Amarin ya faru da iyaye na Amma na San Dada ba zata sanar min ba sai nayi wata hikima nace Mata.... "Wane gari ne Baba na Yake Dada? "Can ne kamaru ... "Me yakeyi a can to? "Aikin koyarwar yaren ingilishi da faransanci Yake yi Baki ga kudin da ya bamu duk sefa ce ba? Ai kin San kamaru tana daga cikin Rainon faransa . Kuma galibin Al ummar garin da Yake da yaruka kala kala mafi yawan su kiristoci ne Wanda Basu Faye musulunta ba . Shi kuma Hamza Allah yayi mishi baiwar ilimin yaruka ko da ya Gama karatun sa sai gwamnatin kasar ta kamaru ta dauke shi Aiki don su mafiya yawan Al ummar garin yaren faransa suke ji Basu Faye Jin na turanci ba shine aka dauke shi don ya Rika koyawa akan yarukan guda biyu to a can ne kaddarar sa ta fara har abinda ya faru ya faru.. "Wace irin kaddara ce ta same shi Dada?... "Barni Halimatu bana ko son tunawa kyale Ni kawai ke dai Taya Ni wurin ADDU A kawai Amma Hamza kam ai yana cikin tsaka Mai wuya Amma Allah shine gatan sa .... Dole na kyale tarin tambayoyin da suke Raina don na San ba Zan samu amsar su ba. Na dauki damin kudaden faransa da baba na ya bani na mikawa Dada ... "Ajiye su wurin ki Dada zan Kuma dauki Kaya kala biyu na Bawa Ziyada da iman Haka ma Zan Bawa fiddausin Goggo Dubu kala Daya ita Kuma Goggo jauhara zan Bata turare tunda Bata da mace cikin Ya'yan ta ... "Kar ki sake ki Bawa Ya'yan Dubu kayan ki Mai kaunar ka kake bawa kayan ka .... "Fiddausi Mai kauna ta ce Dada Kuma Bata daga cikin masu goyon Bayan abinda goggo Dubu take min ba don Goggo Dubu Zan baww fiddausi ba sai Donn ita kanta... Haka na ware kayan na kuma dauki turare Mai kamshin na nufi kofar su Goggo jauhara... Da fiddausi muka yi Karo na Bata kayan Ina Fadin "Fiddausi ga irin tsarabar baba na Ta karba tana murna tana duba Rigar da dogon wando tana Fadin "Kai Halimatu Amma kuwa na gode wallahi kinn fiddo Ni wannan kayan da gani masu tsada ne... Na wuce ta tana ta kambama kyan kayan.. Na nufi inda goggo Dubu take tuyar waina ina gaishe ta Amsa a watse na wuce wurin goggo jauhara "Goggo ina kwana... "Lafiya Lau Halimatu maza dauko kwano na zuba Miki taliya Kar ta Kare don Sai na sake dafa wata yau din ma duk da na so tafiya gidan sunan can... Na Mika Mata turaren ina Fadin "Goggo ga irin tsarabar da baba na ya kawo min duk kayan Mata ne bare ba Bawa abubakar Amma ga turare.... "Kai Aiko na gode Halimatu Allah ya amfana maza dauko wuri na zuba Miki taliyar Nan Kar ta Kare... Na dauko wuri ta soma zuba min har sai da nace ta Isa . Haka goggo jauhara take abin ta baya Rufe Mata ido . Duk Safiya in dai ta dafa taliyar Nan sai ta aikawa Dada Nima tace Nazo na karba. Kai hatta da Ya'yan Goggo Dubu sai tace musu suzo su karba Kuma in duka zasu Kai wuri sai ta zuba musu Kuma babu kyashi bare mugun ta. Amma Goggo Dubu in karamin Dan Goggo jauhara zaice waina Yake so sai goggo jauhara ta saka kudi kaifin a goggo Dubu ta bashi wainar . Haka kuma Dada in dai tana son waina sai ta siya bare Kuma Ni . Bata bawa kowa wainar ta Mai so sai ya saka kudin sa.. Na shirya cikin sabuwar Rigar da Baba na ya kawo min na dauko Rigar da zan kaiwa Ziyada na fito zuwa gidan su Inda na hango balange wanda ya taho da sauri Yana Fadin.. "Masoyiya ina zuwa ne Babu neman rakiya? "Na dube shi ina Fadin "Waye dan Rakiyar ? Yayi maza yace "Ni Mana.... "To koma shagon ka na hutar da Kai... "Yauwa dama don Allah Zan tambaye ki shegen Dan sandar Nan yazo gidan ku jiya ? Na dube shi ina Fadin "Yazo gidan mu yayi me? Ni a duniya ma akwai abunda na tsana irin Dan sanda? Shegu tsinannu ko hanya bana fatan ta hada ni da Yan sanda saboda Rashin gaskiyar su da munafuncin su? ... Balange yayi murmushi Yana Fadin yauwa don Allah ko yazo Kar ki yarda ki saurare shi don tun a Ranar na lura da sonki Yake.... "Wallahi Zan antaya maka Ashar balange Ni ko mazan duniya sun Kare sai Dan sanda ba gara na mutu a gwauruwa ta ba? Ai Ni da dan sanda sai dai nemawa shegu jafa I tunda sukayi abinda idona ya gani.... Da sauri Naga balange ya sulale ya koma shagon shi Babu ko sallama har nayi Mamakin abinda ya sa shi sulalewa . Na daga kafa Zan wuce naji anyi min sallama na juyo sai Naga farin mutumin Nan da ya bani Dubu biyar Ranar Nan da na Karanta mishi Allo.... Yana tsaye Rungume da Hannuwa a kirji... Na Amsa Ina gaishe shi ya dube Ni Yana Fadin "Mai babban suna ya gida? Na Amsa da lafiya Lau... "Ina zuwa ne Haka? Na samu kaina da Jin wannan abun Mai Kama da jan wutar lantarki har bana iya yi mishi musu. Na fada mishi gidan su Ziyada zanje... "To muje na sauke ki a mota ta Mana... A a Nagode ai Nan ne Babu nisa.. "To muje na Raka ki tunda Naga Baki yarda da Ni ba wata Kil kina tunanin ko Zan fille kanki Amma ko zanyi hakan Banda kyakkyawa irin ki kuma ko dukkan Mata zasu kasance Wanda Zan fillewa Kai to Zan ware Mai irin Sunan ki... Muna tafe Yana fada min yadda na shiga zuciyar sa da irin yadda yake Sona Al Amarin da naji shi har a zuciya ta don ban taba Jin Dadi Akan kalmar so ba irin ta bakin shi.. Har muka zo kofar gidan su Ziyada ban iya tanka mishi ba... "Baki ce min komai Halimatu don Allah say something to me? "To Ni me zance ? "Kice Ina son ka hakim ! "Hakim? Zuciya ta ta Kuma maimaita sunan nashi kamar ban tab'a Jin shi ba. "Bari na Baki lokaci Halimatu kiyi shawara Amma don Allah ki bani address din gidan ku Nazo na Samu su baba na nemi izinin zuwa wurin ki don ni ina son nayi komai nawa irin yadda musulunci ya koyar damu... Banja ba na bashi kwatancen gidan mu mukayi sallama Tun daga wannan Rana da ya furta min kalmar so ya Zama komai nake Hakim Yana zagaye da idaniya ta da zuciya ta . Ban tab'a ganin namijin da ya shiga zuciya ta tashi daya ba sai Hakim. Na yarda na Amince tun Ranar da na fara ganin shi son shi ya Shiga zuciya ta at first sight musamman idan Ina tuna Surar sa . Fari ne tas Kuma kyawun da Mata zasu so suna shi s cikin tsara tunda in ban manta ba Ziyada ce wacce ta soma kambama kyan sa... Babu abinda ke Amsa kuwwa a zuciya ta sai Amon sautin sa da yadda yake fadar na shiga zuciyar sa na Hana mishi komai NASA ya tsaya cikk... Sai dai wani ABIN MAMAKI har yau din Nan ban sake Jin duriyar sa ba inda nake Jin tamkar na fita neman sa Amma Kuma idan akayi Hakan ai aji ya zube kasa warwas....... A a Kar ki tsaya garin kallon ruwa Halima in dai kinji kin gani fita kawai kiyi yakin kwato kaunar ki in Kuma ba Haka ba yanzu ne Zaki Sha mamaki..... ✍🏻 Alkalamin GIDAN IKO💖 [8/20, 10:53 AM] Gidan Iko: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻 🧆 *_LINZAMI DA. WUTA_*🧆 Pages 9️⃣//🔟 NA GIDAN IKO💖 _Kirkirarren labari ne da Bai shafi Rayuwar kowa ba kuskure ne babba danganta kai ko wani dashi babu mafi cancantar suyi suka akan labarin irin taurarun cikin labarin Wanda kuka San Babu su a zahiri to kar wanda ba cikin jaruman labarin Yake ba yace don shi ko don wani akayi Hakan jaruman cikin labarin ne kadai suke da damar sukar marubuci akan don me zai fallasaww duniya sirrin su_ _ADDU A ne ga dukkan Al ummar musulmi da suke kwance karkashin k'asa Allah ta ala ya linka Rahama da afuwa a gareku ya amintar da ku damu da muke Kan doron duniya._ _Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da Aminci mara yankewa zuwa ga shugaban mu fiyayyen halitta ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam da ahalin gidan sa madaukaka da masu bin su da kyautatawa har izuwa Ranar Alkiyama_ 💖 ...............Hakim ya iso gida zuciyar sa cike da farin cikin yau ya samu ganin Halimatu har ya Amaya's Mata da abinda Yake sunke cikin zuciyar sa. Babu abinda Yake hangowa sai kyakkyawar fuskar ta da irin action din ta Wanda ya nuna mishi tana respect din sa Don Haka yaji lallai akwai nasara ba zai wahala wurin sace zuciyar ta ba.... Yana Zaune cikin motar Yana tunanin Halimatu Yana murmushi musamman da ya tuno kalaman da take fada Akan Yan sanda sai yayi dariya Yana Fadin "Halimatu kin tsani Yan sanda gashi Kuma Allah ya zubawa Dan sanda kaunar ki kuma alfarmar ANNABI da Al kur ani Zan sace zuciyar ki ba tare da kin Ankara ba. Halin Yan sanda wake Daya ne yake Bata gari Yaya zakiyi Ranar da na mallaki zuciyar ki Kika Kuma Gane Dan sanda ne Wanda kike so? Sai Kuma ya tuno kalaman balange Wanda ya Gane shima son Halimatu Yake har da yaje tambayar shi ko ya San gidan su Amma yace Bai Sani ba Ashe kishi Yake.. "Kayi hakuri balange nafi ka bukatar yarinyar Nan.... Motar ta shigo gidan inda yayi saurin katse tunanin sa ya fito don ya tarbi Yayan sa da yaga ya shigo kamar a fusace... Ya iso har motar tayi parking ya matsa ya bude mishi kyauren motar Yana Fadin "Yaya yau ka tashi da wuri ... Dr Anam ya dubi hakim fuska Babu fara a yace "Dole na tashi brothe yarinyar Nan ce ke neman haukata Ni Kuma Babu iko Babu zarafi nayi magana sai mummy ta k'ale min tana goyawa Nimra baya Ni na Rasa wace irin Rayuwa ce wannan? "Kayi hakuri Yaya Dr su Mata Haka suke sai ana hakuri dasu.... "Ba Haka Mata suke ba Hakim tawa matar ce dai Haka Kuma Daurin gindi ta samu shiyasa kullum wulakancin ta Yake yin gaba. Kullum mace kafar ta tana waje ? Kullum gida na cike yake da Mata kawayen ta da nayi magana tace min kawayen ta ne? Girki Nimra Bata da lokacin yin sa sai dai ta barwa Mai Aiki haihuwa ma tace Bata shirya ba. Idan kuwa nace Zan tab'a yarinyar Nan to yanzu ne zamuyi tashin Hankali don

Chapter 3 of 11