Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 11
lamarin yaci tura. Duk sati jauhara tana hanyar gidan kaso kaiwa salisu kayan masrufi inda Kuma ta kudurce ba zata yi aure ba sai ta jira salisu ya fito. Suna Zaune a benci tana ta kuka Yana Rarrashin ta har Yana Fadin ta Bawa masoyan ta dama tayi auren ta Amma ta tabbatar mishi da zata jira shi abinda ya tabbatar da ba me yuwuwa bane. Duk yadda yaso ta yarda Allah Bai zana aure a tsakanin su ba ta kafe zata jira shi har ya fito Da ya Gane da gaske take sai ya Barta Amma da baffan Nasu yazo duba shi shine ya ke bashi shawarar a fiddawa jauhara miji Mai mutunci tunda Ni ga yadda Allah yayi baffa ba zai yuwu ace jauhara ta jira Ni har shekara ashirin da biyar ba Ni da ita zuwa lokacin ai Rayuwa ta tafi... Haka akayi ta juyi da jauhara ta kafe akan zata jira salisu. Sa adu malamin makarantar su ne tun a primary Yake son ta Amma Bata yarda ta bashi fuska don ta San tana sa salisu shine fa ya kafa naci musamman da ya samu labarin Halin da saurayin jauhara Yake ciki Duk da Bata Boye mishi yadda take son salisu ba da Kuma jiran da take cewa zatayi mishi hakan Bai sarar mishi da gwiwa ba ya kafa naci har dai Allah ya kaddara shine mijin Kuma Uban su abubakar da Usman Umar da aliu. Hauka Babu irin Wanda Dubu ba tayi ba lokacin auren jauhara don ta Gane sa adu ya mutu a Kan jauhara. Amma sai jauhara ta nuna Mata ita mace ce Mai ilimi Bata biye Mata Akan komai sai fa Ranar da Dubu ta Rufe kofa Wai zata baka Kashi inda jauhara ta lakada Mata dukan Shan gishiri har tayi barin ciki to daga Nan ne Bata Kuma gigin cewa zata dake ta ba. Shekara daya da auren jauhara Allah ya wanke salisu ya Kuma fito gaskiya tayi Halin ta Al Amarin da ya gigita jauhara kenan ta Tayar da tsiyata ku kala kala don sa adu ya sau ta ta koma ga salisu Amma ina sa adu ya Kama igiyar ya Rike ya Kuma ji a duniya bashi da babban makiyi irin salisu da har gobe ya tabbatar da Bai bar mishi zuciyar jauhara ba . Gane Bata da yadda zatayi yasa ta hakura shima salisun Bai jima ba yayi aure da wata matar wacce itama take cike da Jin zafin jauhara don salisu Bai Boye yadda yake son jauhara ba shiyasa matar salisu Bata yin jauhara ko sabga aka hadu Sai suwaiba matar salisu ta yadawa jauhara magana koma ta ganta ta dauke kanta. Yayin da Baba Headmaster Kuma Kuma ko sanga ake gidan salisu baya barin jauhara taje Wai Kar taje su hadu da salisun Asiya Tasha yawon ta ta dawo babu cinikin kirki yayin da fiddausi dake waje ta Dan siyar Babu laifi Goggo Dubu ta dubi dukan cinikin abun Haushi da takaici tamkar ta fashe da kuka cike da bak'in ciki... Goggo jauhara tana ta kadin taliyar ta don injin gareta ita ke kada kayan ta Usman ya dawo dauke da geron da goggo jauhara ta bashi ya surfo Mata don har da gero take son fara dafawa a gobe don yaran sunce take dafa musu zasu siya Kamar Wasa ta fara dafa gero da manja shima yara suka dafe kowa ya shigo gero ko taliya yayin da Goggo Dubu Kuma waina Taki sai ma Dan Karen bashin da ya Haye Mata har ta Kai a cikin kwanaki biyar kacal Babu jarin da zata Dora har ta Kai wainar ta gagara Tana Zaune bakin kofar dakin cike da bak'in ciki tana kallon yadda yara suka Rufe jauhara suna siyen gero da taliya yayin da hafsa karamar Yar goggo Dubu take kukan taliya take so goggo Dubu ta make Mata Baki saboda Jin Haushi ta Rufe yarinyar da sababi da tijara... "Taliyar uwar ki yarinya sai cin tsiya ba yanzy Kika Sha Koko ba shine wani taliya? Uwar ki ke da Mai taliyarπŸ˜‚ Goggo jauhara tayi murmushi don tana Jin komai ta zuba taliya a Roba ta dago kanta tana Kiran hafsa.. "Taho ki Amsa kinji hafsa? Da sauri hafsa tanufi Goggo jauhara ta karbi taliyar.. "Yauwa to Zauna Nan kici kinji.. Hafsa ta zauna tana cin taliyar yayin da Goggo Dubu taji bak'in ciki na Shirin shake ta ta mike ta fada Daki don ta gaji da ganin kayan takaici Kuma wani arashi a yau din da batayi wainar ba sai tambaya ake shine abinda ya Kara fusata ta... Tabawa ta sheko sallama ta shigo inda taga bakin madafin Dubu babu ita bare tuyar waina sai madafin jauhara ne dankam da Yara suna siyen gero da taliya... "Ikon Allah Haka abun ya Zama Kuma? Cewar tabawa inda jauhara ta dago tana Mata Sanny da zuwa.. "Kai Amarya ludayin ki Akan dawo Masha Allah Ina Dubu ne Naga yau Babu waina? Goggo jauhara tayi murmushi tana Fadin "Allah dai tabawa Dubu tana Nan D'aka... Tabawa ta afka dakin goggo Dubu tana Fadin "Lafiya dai Dubu zaman D'aka ana wannan kakar ta Yan makaranta? Ina wainar ne? Meye ya faru Naga ban ganki a madafi ba?..... To munji wanna Bari muji meye next chapter? Amma tabawar Nan anyi munahika duk da ban Gano ta ba Amma bakin ta fall Yake da tsegumi..... ✍🏻 Alkalamin GIDAN IKOπŸ’– [8/20, 10:53 AM] Gidan Iko: πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ» πŸ§† _LINZAMI DA WUTAπŸ§†_ Pages 1️⃣3️⃣/1️⃣4️⃣ GIDAN IKOπŸ’– _Kirkirarren labari ne da Bai shafi Rayuwar kowa ba kuskure ne babba danganta kai ko wani dashi babu mafi cancantar suyi suka akan labarin irin taurarun cikin labarin Wanda kuka San Babu su a zahiri to kar wanda ba cikin jaruman labarin Yake ba yace don shi ko don wani akayi Hakan jaruman cikin labarin ne kadai suke da damar sukar marubuci akan don me zai fallasaww duniya sirrin su?_ _Sadaukarwa ne ga dukkan Al ummar musulmi da suke Rayuwa a wannan yanayin Ubangiji Allah ka shiga cikin Al Amarin musulmi ka Hana cewa ya zamuyi a Raye ko a kwance._ _Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da Aminci mara yankewa zuwa ga shugaban mu fiyayyen halitta ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam da ahalin gidan sa madaukaka da masu bin su da kyautatawa har izuwa Ranar Alkiyama_ _MUNAFUNCI_ πŸ’– ..............."Me nake Shirin gani Haka Dubu? In dai lafiya ma ai da sauki.... Cewar tabawa wacce take Raba idon duban aminiyar tata Dubu... Goggo Dubu da ta tashi daga kwancen da take tana daura Dan kwalin ta tana Fadin "Ina fa lafiya tabawa? Wace lafiya ce zata kunshe Ni a Daki a irin wannan lokacin .... "Ince dai ba zazzabin Nan bane ba? "Ai Ni ko zazzabi baya Hana Ni tuya tabawa nayi sake ne dai kawai har anyi nasara a kaina kasuwa ta k'i Ni tamkar Mai bakin iyaye Sana a Babu ci gaba kullum cikin asara nake waina kullum nayi ta sai dai su salamatu suyi ta watanda da ita maganar na siyar Bata taso ba bare na ga haske ko wata Riba. Ba ma wannan ne abinda yafi Tayar Min da Hankali ba sai bashin hatsin duduwa da ya taru ya Haye min yanzu Haka kudin duduwa sun Tasar ma Dubu Sha biyu Kuma Ni bani da Dubu biyu cikakkiya tabawa.... "An kuwa yi nasara Akan ki Dubu Amma banji Miki zafi ba Baki da kaico tunda tuni nake fada Miki duk Ranar da aka tashi saka Miki hannu Zaki ga abinda zai faru gashi Kuma kina Kan gani yanzu jarin ya lalace kenan? Tabawa ta tambaya... "Ya Rasa lalacewa tabawa? Kullum nayi waina kwantai nake sai dai na Bawa Yara Amma ita har da gero ta ke hadawa yanzu Dubu kiga yadda gidan Yake cike da Yara da ta siyar ta sake maida tukunya Ni Kuma gani makure a kuryar Daki na Kame hannu na Rungume Ni ba salati ba ba istigifari ba sai bak'in ciki ke ta nanuka ta ... "To kuma Haka Zaki ci Gaba da zaman D'aka kamar wata Mai danyen jego ko amaryar mugun Abu? ... "To Yaya Zanyi tabawa? "Ai Ni kinji abunda Yake bani takaici da ke wallahi Dubu Baki da dabara bare fiddawa Kai mafita. A wannan Halin da in Allah ya kawowa fiddausi da hadiza miji za a ce fito shine har kike tambayar ya zakiyi?... "Ai wallahi tabawa na Gama tayarwa kaina hankali akan sabgar aure tabawa. Abinda Uban su yayi ya wadatar Dubu bataliyat da take gaba na in ma wasu sun tafi ga wasu Nan to abunda ya samu da shi za ayi amfani wallahi Yar Sana ar da Zan tattali wani Abu an kassara Ni... "Tashi kawai zakiyi mu nufi wurin malam Mai gafukka ki samo Dan dafa I ko kya Dan Rika motsawa Amma yaushe matar malamin makaranta irin ki Mai Ya'ya Mata turus har biyar a gaban ki Zaki ja ki Zauna ko kudin Jan Baki da hoda da Dan man shafawa sun ishe ki ba?.... "Tabawa in munje wurin malam Mai gafukkar shekaru na Zan zube mishi yayi mini Aikin? Tuni nake ta auna zuwa wurin nashi Amma sai na tuna kudin motar zuwa da dawowa kadai na mallaka gashi Kuma kince Aikin shi tsadar tsiya ne da shi ga bashin da ke kaina na tabbatar da duduwa ta tabbatar da Babu kudin Nan a k'asa sai tayi kamar ta tura wuta da Raina.... "Kuma ke Baki da Dan Kama sayar Wanda za a Kama wasu Yan kudi Nan? Cewar tabawa da ta katse Dubu... "Adashe Kuma Ni ake bi bashin zubi bare nace ina jiran kwasa na dauki ta takwas duk na zuba cikin Sana ar Nan Amma duk a wofi aka ce kad'an ma kenan ai na tsinewa Ranar da sa adu ya kyallo min matar can har yaji Yana son ta wallahi nayi Allah ya Isa yafi sau Dubu.... Tabawa ta kyalkyale da Dariya tana Fadin "Kya ma Kara wata dubun dubulliya Amma dai yanzu ki San abunyi Amma Zama Kam Bai Kama ki ba... "Ni yanzu in akwai kudi a wurin ki tabawa ki aro min na koma waina na gani.... "Au wainar Zaki koma ba zuwa wurin malam Mai gafukkar ba? Lallai Baki ji wuta ba to Ni Ina Zan ga kudin Baki Dubu ? Ba fa wata Sana a nake ba miji ba wata Gama ba bare na kwantalo Miki a jikin shi .... "Duk ba wannan ne damuwar ba tabawa Wai kin San fa duk jarin shegiyar matar can sa adu ne ya Bata har da na gero Amma Ni na tambayi aro ma yace tun kafin albashin yaxo Wai mun cinye shi shima wurin jauhara Yake aro Wai nayi Mata magana ta Ara mini?... "Ta Ara Miki ? Ai kuwa da kinci baya wallahi ace jarin da kake juyawa kishiya ce silar sa ai ko albarka ma ba zaiyi ba ... "Yo ko nayi hauka tabawa yaushe Zan kalli kudin jauhara bare nace ta Ara mini? Ni fa duk gidan Nan ya fita a Raina wallahi ji nake kamar nayi tafiya ta jibia... "In Kika tafi jibia ko ai Aikin malami yayi Dole a biya shi. Ni fa ina ganin idan babu kudin da kema Zaki motsa to Ina ganin ta Bayan gida kawai Zaki fito ma ana ki nemi hanyar kassara sa ar tata da tuggu da makirci kiyi ta lalata kayan Sana ar har itama ta Rasa in yaso ku taru ku Rungume Hannuwan Baki daya.... "Kamar Yaya tabawa? Goggo Dubu ta tambaya a zak'e don taji tafi yarda da Hakan ... "Ai idanu Zaki fakaita ki samu wani Abu da zai lalata kayan Sana ar Kamar in ta Dora geron ko taliyar sai ki ambama Mata wani Abu da Dole zata zubar da shi Rariya Kinga Dole ba zai ciwu ba sai dai a Kai tsari a Kai kwatami.... Goggo ta kyalkyale da Dariya suna tafawa ita da tabawa... "Shikenan kalas Kinga daga Nan sai jari yayi kasa in Kuma Yara sunci sunji Babu Dadi gobe ba sa komo ba... "Yo Eh Mana in an Hana ihu ai ba za a Hana aha ba shiyasa nake ganin wautar ki Dubu Baki da hikimar kwatar Kai sai Uban kishin kawai Kika iya Amma Baki da tuggu da makirci .... "Ai wallahi yanzu Dole nake koyar su tabawa tunda na Gane kisan mummuke ake Shirin yi min macijin kaikayi sari ka noke kenan.... Goggo Dubu ta leka waje inda goggo jauhara take ta siyar da kayan sana ar ta ta waigo ta yafuci tabawa tana Fadin "Duba ki gani hatta da manja yanzu jarka take siya Bata ma jiran Mai gidan in dai girki ne sai dai tayi nata dama Ni nace sai an Raba girkin an Kuma Raba kowa nashi Yake to Ni gashi yanzu ba harka .... "Ai sai kiyi kokari ku dawo Daya itama ta Zama ba harkar Amma in ba Haka ba ai ita zata Rika digawa Ya'yan ki abinci a faranti Kuma ta Daki kirjin cewa itace take ciyar da gidan tunda har Mai gida Yana aron kudi hannun ta ai Kuma da gayya ma zata yanko magana.. Tabawa ta mike tana Fadin "Ni Kam na wuce dama yau Haka muka tashi gidan Babu komai nace Bari na yo Nan ko waina na samarwa su Fati Ashe Rabon nayi mugun ji Amma dai kiyi kokari Dubu mu samu mu fiddo jaki daga Duma... Suka fito tabawa tana Kara kallon Goggo jauhara da yaran ta Yan Tara. Bata Kuma duban inda take ba tayiwa goggo Dubu sallama *** *** *** **** Na dubi yaron da Yake sanar Dani Wai ana Kiran Halimatu a waje... "Waye ?. Na tambayi yaron yace "Wani ne a cikin mota... "Jeka kace Bata Nan Na fada mishi don ban San Mai motar da Yake magana ba... Dada ta tsayar da yaron tana Fadin "Kai ce tana zuwa Na dubi Dada wacce take duba na tana fadin "Haba Hali Dubu Rai goma Kika Sani ko shine surukin nawa da nake ta fatan ya iso tunda kince Baki son yaron Nan balange Mai shago? Tashi kije ita mace da kike gani Allah ne kadai ya San mijin ta Kuma su maza ba a musu Haka ka Rabu da kowa lafia shi yafi... Na mike Ina Jin Hakim Bai min adalci ba da ya faku tsawon wannan lokacin don Babu Ranar da zata fito ta komawa Ubangiji ban tuna bawan Allah Nan ba.... Ina fitowa Naga abunda ya saka Ni murmushin da ban shirya ba Yana tsaye cikin Riga sheet da jins Wanda suka Kara fito da haibar sa... Yana jingine jikin motar shi ya tako zuwa inda nake tsaye... "Shikenan Babu cigiya Halimatu? Na dube shi kamshin turaren shi Yana karade kofofin hanci na in Fadin "Nayi cigiyar ka fa har a BBC Amma shiru bace ko baka Nigeria? Yayi murmushi Yana kallon Ido na kafin yace "To kalle Ni Mana sai muyi magana? Na juya cikin gida na dayko FARAREN kujeru na kawo mishi a soron na Aje Ya Zauna Yana Fadin "Ina can ina ta fatan na Samu na kubuto Nazo Naga kyakkyawar fuskar ki Halimatu ai wannan Dan sanda ba Zan yafe mishi ba wallahi ... Da sauri na dube shi Ina Fadin "Me yayi maka? Yaja tsaki kamar gaske ya soma Fadin "Kama Ni yayi Wai don bani da lamba a motata Kuma bawan Allah Nan yaki Jin Rarrashi.... "Uhum ai Kai dai kaga Yan sanda ba kirki ne da su ba wallahi suna sane da gaskiya suke take ta in dai ba kudi gareka ba wurin Dan sanda duk gaskiyar ka Sai ya cuce ka shiyasa Ni ba wani son su nake ba Allah dai ya sa ba kulle ka sukayi ba? Yayi murmushi Yana Fadin "Kulle Ni sukayi tsawon wannan lokacin da Baki ganni ba sai jiya na fito.... "Allah ya kyauta gaba ya tsare wallahi ban sani ba ai da na jajanta maka... "Ba komai na gode Yaya maganar mu Halimatu? Nayi shiru kunya Hana Ni nace mishi tun Ranar da ya furta min kalmar so naji a duniya Nima wata ABA ce Mai daraja Kuma gare shi .... "Kar kice min bana daga cikin maxan da suke burge ki Halimatu Amma zanso ki sada Ni da Baba na fara gabatar mishi da kaina na fara neman izinin sa.... "Sai dai na fara kaika ga Dada ta don Baba na baya garin Nan... Muka shiga Dada ta Karbe shi da karamci ya zube Yana gaishe ta ta Amsa tana ta saka mishi albarka kafin ya gabatar Mata da kanshi da son neman auren Halimatu... Dada ta soma sanar dashi Halimatu jikar ta ce wacce ta haifi Uban ta Kuma ta yaba da tunanin shi da har ya iya fara neman auren sa irin yadda musulunci ya koyar da musulmi don Haka ta bashi Halimatu Babu wani ja tunda har Yana da Hankalin tsare Shari a to shine mijin Halimatu Allah ya Taya mishi Godiya sosai yayiwa Dada kafin ya aje Mata kudi masu afki ya mike zuwa soro "Allah Nagode maka Halima ni din ina da sa a daga kallo Daya Dada ta bani ke sai dai ban San yadda kike kallon kyautar Dada ba... "Dada ta Isa tayi gaban Haka Dani don bani da Wanda yafi ta itace komai nawa ban tab'a sanin Dada kakata ce ba sai daga Bayan Nan don da ita na dube Ido na zaci ma itace mahaifiya ta don Haka Babu Mai Tayar da kyautar Dada.... "Alhamdulillahi Halimatu Amma naso naji irin matsayin da Kika bani don na San na Kai a so ... "Kar ka damu Zan baka matsayi Mai GIRMA don Ni a gareni duk Wanda ya ce Yana Sona Ina bashi matsayi na musamman bare Kuma Kai... Mun Jima muna fira Yana fada min yadda nake a zuciyar sa har zuwa Kiran sallaar magaruba inda yayi nufin tafiya ya Kuma aje min kwalin waya Yana Fadin "Ban Sani ba ko Ra ayin ki ne ba kya son Rike waya Halimatu Amma dai ayi mini alfarma ko sau daya ne nake Kiran ki Ina Jin muryar ki Ina fatan ba dokar manya Zan karya ba? Na kada kaina Ina Fadin "Kawai dai nice bana son rikewa Amma in kana son hakan Zan yi .... "Yauwa to Nagode akwai layi a ciki har da kati nayi karambanin sakawa Zan Kuma Kira anjima ... Mukayi sallama ya tafi na Shiga gida da waya Ina nunawa Dada wacce take cewa "To kin gani arzikin Yana Kira da tsiya zata Hana ki zuwa gashi Nan kin samo galleliyar wayar ai Ni wallahi yaron ya burge Ni tunda Yana da sanin auren musulunci ta sama ake fara neman sa ba taka Haye irin yadda yaran yanzu suke ba sai dai kawai kaga mutum a kofar gidan ka tsaye da yarka don Allah meye ba zai faru ba tunda ya san gidan su Babu Wanda ya San da shi? Sai Naga maganar Dada gaskiya ce kuma Ni Kam yadda naji zuciya ta akan Hakim gaskiya in har Haka so Yake sai nace Babu abinda ya Kai so Dadi a duniya... Da dare kuwa na kunna waya na saka chaji sai ga Kiran shi ya shigo n dauka. Tun daga wannan Rana Hakim ya dasa min wani irin so Mai wahalar mantawa har nake Jin Babu Dadi idan Bai Kira ba. Goggo jauhara tun asubahi take tashi ta soma Dora sanwar kayan Sana ar ta musamman gero da Yake yafi taliya wuyar dahuwa. Kuma a cikin gidajen Makota ma Akan shigo siya don Haka manyan tukwanen ta masu lamba 20 da Mai 25 sune take dorawa kafin garin ya waye ta Gama sai dai dakan yaji da Kona manja da albasa Kamar kullm yauma bayan an sallame sallar asubahi ta Dora sanwar ta ta tada wuta ta Shiga bandaki tayi wanka yayin da Goggo Dubu take ta faman fakaitar idanu harta samu jauhara ta Kandami Ruwa ta Shiga bandaki sai kawai goggo Dubu ta soma waige da neman abinda zata gani a dakin taje ta zuba a tukunyar gero ko taliya. Idon ta ya fada Akan omon kilin irin na aune din Nan sai kawai Goggo Dubu ta figi ledar ta sadada ta ambamawa goggo Dubu shi a cikin tukunyar taliya ta koma Daki abinta... Goggo jauhara ta fito ta shirya har ta soma dakan yaji taga tukunyar taliya Tana ta kumfa da sauri ta matsa ta bude inda kumfa sai fita Yake abinda ya Bata mamaki Bata kawo komai ba in ma da akwai abinda ta kawowa Ranta to Bai wuce fulawar ce bata da kyau ba don tun a wurin kadi taga Bata son Ruwa... Da sauri ta sauke tukunyar daga wuta ta dauko matsami ta soma fidda taliyar tana zuba ta cikin Ruwa duk Bata kula da abinda Yake k'asa ya cure ba. Ta wanke taliya tas ba tare da ta San asara aka so jaza Mata ba Amma da Yake Al Amarin Yana Nan cikin kaulasan Allah Bai zana Mata wannan asarar ba sai ga taliya ta shige tas Babu Mai cewa akwai wani abu a ciki sai dai Dan gishir gishiri shima sai ya hade da yaji Goggo Dubu da ta fito bakin kofar dakin ta tana jiran taga ana Kai taliya Rariya sai taga ana Shirin mayar da tukunya Kan murhu hatta da geron ya Kare sai an sake dafawa Wurin wankin tukunyar ne jauhara taga abu ya taru gefe daya ya dunkule Bata kawo komai ba ta wanke ta zubar ta mayar da tukunya... Wannan ta wuce goggo Dubu Bata samu yadda take so ba inda ta Kuma kulla makircin ambama kalanzir Shima kamar waccan lokacin da asubahi ta fakaici Ido ta auna Uba kalanzir a cikin Ruwan sanwar Shi ma da Yake Allah Bai dorawa jauhara wanna asarar ba kafin ta zuba geron ta taga kyallin maiko a saman Ruwan inda ta soma yad'ewa Amma tuni zarnin kalanzir yaje hancin ta ta kuwa sunsuna sai ga Abu zau Dole ta zubar da wannan Ruwan ta Kuma sake tukunyar sanwar Sai da Goggo Dubu tayi Karo uku Duka Babu nasara Amma Kuma zuciyar ta Bata rusuna ba A cikin Karo na hudu ne Kuma Allah ya tona asirin ta dama Rana Dubu ta barawo Rana guda ta Mai Kaya inda Baba Headmaster ne ya kamata tana madacin da Dole ya haramtawa Al Umma abincin. .... "MENENE Kika zuba Mata Haka Dubu? Yayi tambayar a lokacin da Goggo Dubu tayi zaton a cikin duhu Babu Mai ganin ta tayi muguntar ta .. Goggo jauhara ta fito tana kallon su inda Baba Headmaster ya tsare Dubu Yana tambayar ta... "Ban Gane me nake zubawa ba? Kai ma SHARRIN zaka ja min?... Ya juyo Yana duban jauhara Yana Fadin "Duba kigani meye ta zuba a cikin tukunyar can ta farko? Da sauri Goggo jauhara ta bude tukunyar sai ga Ruwa ya rune da kalar Abu.... "Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un menene wannan din? Cewar Goggo jauhara Allah ya kiyaye shima Bata Kai ga zuba hatsin ba.... "Wai Dubu me kike daukar Rayuwa ne? Yanzu ke hakan shine yayi Miki daidai ki cutar da abokiyar zaman ki... "A a Kar fa kace zakayi min sharri sa adu. Wace burgewa kake sonyi wurin matar ka da kake neman b'ata Ni a idon ta don kayi bajinta? Kai Kuma Haka naka salon Yake ? Yau ga wani ikon Allah Mai gida da haddasa husuma a gidan sa. ai ba sai kayi Haka ne Zan gane kana neman Shiga ba .... Goggo jauhara ta dubi Baba Headmaster tana Fadin "Don Allah kaje ka shirya kana Shirin makara fa... Ya juya Bai cewa Dubu komai ba abinda Kuma yayi matukar Kona Ran goggo Dubu akan yadda jauhara tayiwa sa adu magana cike da kinaya da kissa ya Kuma bi Babu musu to wannan yafi komai bak'in ciki a wurin ta .... Goggo jauhara ta zubar da Ruwan sanwar ta sake wasu ta mayar a wuta Tun daga Ranar goggo jauhara in zata Dora girkin ta zata Zauna a wurin har sai ta sauke . Sai ya Zama komai nata ma ta daina barin sa Haka nan tana ta kaffa kaffa da koman ta yayin da kasuwar ta Kuma take ta hab'aka tana ci gaba tana ta Samun Yan kudaden ta . Kuma Bata fasa zubawa Ya'yan Goggo Dubu kayan Sana ar ta ba. Sai ma ta tambaye su abinda suke so taliya ko gero Kuma in zata zuba batayin na kwauro yadda zai ishe ka don Bata yarda kyauta na Hana samu ba. Kuma ita a gareta biyan bukata yafi dogon buri . Shiyasa Allan ya Daga Al Amarin

Chapter 5 of 11