Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 11
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ο»Ώ[8/20, 10:53 AM] Gidan Iko: _*LINZAMI DA WUTA*_ GIDAN IKOπŸ’– SHIMFIDAR LABARIN _*TURK'ASHI*_ ..........A Rikice take matuka Gaya saboda tashin Hankali tamkar wacce ta leko ta yadda zata mutu. Cike da tashin Hankali take duban mutumin da take a gaban shi tana Fadin.... "Ina cikin tashin Hankali malam don Allah ka taimaka mini ..... Ya yi saurin daga mata hannu kafin ya dago daga jefa wani Abu da yake q cikin wutar da take ci a gaban shi cikin wani kasko Yana Fadin.... "Kin cika wutar ciki Nina Haka ne sunan ki ai ko? Ta dube shi cike da Mamakin yadda akayi ya San sunan nata.... "Ko da Yake ba Nina ne cikakken sunan Zinatu shine cikakken sunan ko? Ya Kuma kashe ta da wani Mamakin kafin ta farko daga Wanda take ciki .... Ta Kuma sake gyada mishi Kai cike da sallamaww Aikin nashi na mamaki.... "Ni da kike gani nan Nina masu zuwa wuri na ba sai sun wahalar da Kan su wurin fada min damuwar su ko lalurar su ba Ni da kaina nake ganin ta don Haka na San abinda Yake damuwar ki don tun kafin kizo Rauhani ya fada min komai Akan ki ... Tsoro ya soma kamata ta soma karewa dakin malamin kallo don gudun Kar ace Rauhanin Yana dab da ita.... Ta Shiga karewa dakin kallo yayin da idon ta ya sauka a kusurwa hudu ta dakin ta Kuma ABIN MAMAKI. Kowace kusurwa Kan mutum ne da Karan taba sigari Yana fidda hayaki yayin da idanun Kuma suke zubar da wani Jan Abu Mai kamar jini Amma ABIN MAMAKI shine Kan kawai ta iya gani Amma Babu gangar jiki...... Malamin ya dube ta Yana Mai zuba Mata idanu kallo irin na kurullah har Yana lasar busasshen leben shi yana Fadin.... "Daina kallon su basa son kallo kin San Rauhani baya son kallo Banda ma Nan ne ai Baki Isa ki kalle su da idanu Baki makance ba. Tsoro Mai tsanani ya kamata ta soma kyarma . ya lura da firgitar da tayi ya Kuma yin murmushi Yana Mai maida Hankali Kan wutar da take ci a cikin kaskon gaban shi Yana Mai dauko wani nama ya jefa a cikin wutar. Sai Bayan da ya jefa Naman kafin ta Ankara da zuciya ce ya jefa a cikin kaskon wutar Amma Kuma Bata iya sanin ko zuciyar mecece ba.... Sai kawai ta jiyo Nishi daga cikin zuciyar da ya jefa a wuta.... "Ko baka kaunar Allah Musa sai ka so baraka mun hada soyayyar ku da tsiya ba da arziki ba don Haka zuciyar ka zata ci gaba da kasance wa cikin zafi da Rad,ad,i har sai ka kawo kanka wurin baraka ka so baraka irin son da zaka iya Rasa Rayuwar ka.... Ya soma watsa wani Abu Mai kamar jini a cikin kaskon sai kawai dakin ya dauki karar kuka da wani Sanyi kafin Kuma iska Mai karfi ta soma shigowa dakin duk da Rashin yalwar haske hakan Bai Hana Nina ganin giccin wani Abu ba kafin taji saukar wani yiff ya fado saman rufin dakin..... Ya ture kaskon Bayan da iska ya tafi da dukkan abinda Yake cikin kaskon wutar zuciyar nan da wutar da ke ci.... Ya juyo Yana fuskantar Nina wacce ta Gama mutuwa da mamaki a Zaune lallai duk Wanda yace ba asiri yayi karya...... "Nina Naga bukatar ki ko nace Rauhani ya fada mini kinzo ne akan mijin ki ya sake ki saki uku Kuma kina son komawa saboda wani Al Amarin da Kika baro gidan wanda Yake cikamakom farin cikin ki ko ? Ta muskuta tana Fadin "Haka ne malam don Allah a taimaka mini kamar yadda Naga ka hada zuciyar can son abinda ya Zama jazaman Don Allah malam a gasa min zuciyar Miji na fiye da Haka a Hana shi tab'a yarinyar da ya Aura Kar ya kwana da ita don in yayi hakan Zan iya Rasa Rayuwa ta malam Ina so a zabaro shi yazo wurjanjan yace ya mayar da auren mu..... Ya dube ta da kallon kurulla Yana shafa kasumbar shi Yana Fadin.. "Gaskiya Aikin ki Babu nasara a cikin sa Kar ma ki wahalar da ksnki don Ni bana yaudarar mutum Ina fada mishi gaskiya kawai don Haka gaskiya ba Zaki tab'a komawa gidan honorable ba don tun kafin shekara talatin da ta gabata muke da labarin ki Kuma a yau din ne aka nuna Mana Zaki bayyana gaki Kuma kin bayyana..... Cike da wani irin tashin Hankali take duban shi duk da lamarin yazo Mata a baibai . Ba don komai ba sai don Rashin nasarar da ya Kira Mata Akan Aikin ta ..... Tana Shirin bude Baki tayi mishi tambayar ya kashe ta da wani mamaki inda ya jawo madubin mai Rufe da fatar damisa ya bude wani haske ya fito wall ya shafi madubin sai ga Nina ta bayyana ya Kuma juyo da fuskar madubin Yana nuna Mata inda ta soma ganin hotunan ta da Kuma wasu daga cikin motsin ta tamkar dai ace majigi ko vedio ya kunna Mata...... "Malam ta Yaya Al Amari na ya zo gareka? Ta tambaya a Rikice.... Malam yayi murmushi Yana Fadin " Munyi yarjejeiya da Rauhanan da nake Aiki da su sune suka gindaya min wani sharadi na Kar na sake nayi aure babu Ni babu wata mace matukar Ina son tabbatar aiki na sai Nan da shekara talatin masu zuwa don matar da zata Zama tawa zata bayyana a gareni ne da bukatar son nayi Mata Aikin da zata koma gidan mijin da ya tafka Mata saki uku. Ba don komai ba kuwa sai don suna da wata bukata a gareta ita To matar tawa saboda tana da wata dabi a ne da sai irin ta ne suke son na aura don cikar Nasu burin. To gaskiya ba kowa bace matar Nan da Rauhani ya sanar Dani sai ke din Nan don Haka Babu wani miji da zai bayyana a gareki sai Ni Nan Kuma Babu ba Zaki tab'a auren wani ba sai Ni in Kuma ba Haka ba to Al Amarin ki zai Zama tsoro da tashin Hankali har ma ki ce gara mutuwa . Don Haka ki kwantar da hankalin ki Zan tabbatar Miki da mijijn da kike son komawa Bai fini komai ba in kudi ne ina da su duk da munga wata nufaka a ranki ba ta komai bace face matar da mijin naki ya Aura itace burin ki to Amma Alkalamin ya Gama Zane fashin mu don Haka nine mijin da da dama yake zaman jiran wancan mijin naki ya sake ki don na aure ki in ma Bai sake ki a wannan lokacin ba to hakika sai ya mutu Ina fatan ..... Cike da wani irin firgici da Jin Haushi da takaici take duban shi tamkar ta shake shi tana nuni da yatsar hannun ta zuwa kirjin ta tana Fadin "Ni kake maganar na aure ka Wai ? Ni ce wacce Rauhanan suke nufin biyan bukatar su a kaina? Dube Ni sosai Mana don Allah ka Kuma dubi kanka Ni Ni kake fadawa wannan maganar wofin don Uban ka? Kunci uwar Uban ku Kai da duk Rauhanan da suka Karanta maka wannan tatsuniyar.... Ta hada da auna mishi Ashar saboda Jin haushin maganar shi.... "Dube ka don Allah wani Baki mummuna kamar wani namun dawa . Babu wani Abu Mai kyau a tare da Kai komai naka Mai muni ne akayi maka kuma Mai arha kamar ahalin samudawa "Ni kike zagi Zinatu ? Kika zagi Rauhanan Nan? Kin kuwa San Bala in da kike Shirin daukowa kanki?..... Bai Rufe baki ba ta kwasa mishi Mari a faffadar fuskar shi dake cike da gashi tana fadin "An zage ka shege tsinanne la anannen Allah ma yaudarin banza da wofi Mai fakewa da malanta Yana sheke Ayar sa Uban Uban ku Kai da duk Rauhanin da ya daure maka gindi in Kuma ga abunda zai faru Allah ya tsine maka in ka Bari Naga Safiya Kai da duk Rauhanan da suke daure maka kunkuru. In ka cika hatsabibi inga ta gidan Uban da zaka Kuma gano ni bare ka nemi latsa Ni shege fasiki asharari.... Ta figi makullin motar ta da Yake gaban ta ta mike tana mayar da numfashi ta soma kwallo da duk wani Abu da ta gani a cikin dakin tana watsi da shi yayin da malan Kuma yake ta murmushi tamkar ba Mari yasha tare da bakaken maganganu ba.... "A yau Babu ke Babu bacci don ma Ina kaunar ki ne Amma da wannan zagin kadai ya Isa yasa nayi Miki tukwici da hauka Marar warkewa Amma ina son ki Kuma son ba zai Hana na firgita ki ba don Haka ki saurari aike na Nina.... Ta fice daga dakin tana Kara wanke shi da zagi da cin mutunci yabi ta da rakiyar kallon tausayi da jimantawa har ta fice. Yana ji taja motar ta a guje ta wuce inda ya dubi inda ta tashi sai yaga jakar ta wacce ya tabbatar da mantawa tayi da ita.... Ya jawo kaskon dake gefen shi Yana murmushi kafin ya tada wuta a lokaci Daya wata narkekiyar kyanwa Mai idanu tamkar touch light tare da wani shirgegen kadangare Mai kala irin jangwalagwada suka bayyana suna zubar da hawaye. Nuni kawai malam yayi musu da hannu suka auna aguje lamarin da zai tabbatar maka da lallai Wanda yace Babu asiri tamkar yace babu Allah ne.... Malam ya sheke da Dariya Yana shafa kasumbar shi Yana Fadin. "Yaro Bai San wuta ba..... Tana tafe a motar tana Kara Jin haushin maganganun shegen malamin can da Ramsy ta turo ta gareshi da tabbaccin in dai matsala tazo gareshi to an Gama tamkar yankan wuka Yake aiki Ashe Ashe shegen malami ne da Yake Shirin Tasar Mata Alkiyama da wuri. Ta Kuma antaya mishi Ashar tana tsine mishi albarka....... sai kawai taji fadowar wani Abu ya sauka akan gilas din motar yiff . Kafin ta Ankara sai kawai taga wani irin kartakeken kadangare kadangare kuwa Mai ban tsoro Mai kalar Nan wato jangwalagwada ya lafe a tsakiyar gilas din motar Yana wurga Mata idanun sa masu ban tsoro ainun...... Ta fasa wata razananniyar Kara don in akwai wani abu da take tsoro a duniya to kadangare Mai kala ne sai Kuma wahainiya.... Tana kokarin take burki ne don fice daga motar Kuma ta cikin mirror da ka iya hango Bayan ka ta hango wata narkekiyar kyanwa tana nufo ta tana dallare ta da idanun ta . Ba girman kyanwar ne abin tsoro ba sai idanun ta masu shekin kalar hasken touch light da Kuma nufo tan da take gadan gadan tamkar aike ko wahayi Babu shakka Babu tsoro shine abinda ya razana ta ya sa ta kwalla wata gigitacciyar Kara har da kururuwa har ta Bata iya control din motar ba ta soma rawa a titi kafin ta ci Uban burki a tsakiyar titi tana shidewa....... _Ikon Allah me ye a cikin tafiyar labarin LINZAMI DA WUTA ? kenan mun soma tsintar MAMAKI Amma mu nutsa a tafiyar_...... ✍🏻alkalamin GIDAN IKO [8/20, 10:53 AM] Gidan Iko: πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ» πŸ§† *_LINZAMI DA WUTA_*πŸ§† Pages 1️⃣//2️⃣ GIDAN IKOπŸ’– _*Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da Aminci mara yankewa zuwa ga shugaban mu fiyayyen halitta ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam da ahalin gidan sa madaukaka da masu bin su da kyautatawa har izuwa Ranar Alkiyama*_ *_Godiya ga sarki Allah Mai yarda da iyawa da ya Amince min na Kuma dawowa a cikin wata tafiyar Mai sunan LINZAMI DA WUTA Allah yadda kake tasrifin komai nawa Ina Rokon ka Taya min yadda na fara lfy na Kare lfy ka Sanya amincin ka a cikin tafiyar da shi kanshi littafin Duka_*. *_Sadaukarwa ne ga dukkan masoyan Rubutun gidan iko Allah ta ala ya amintar damu duniya da lahira love you all Ina sane da ku da soyayyar ku_*πŸ’–πŸ₯° Katsina ............Na shigo gida tun a soro nake kwalawa Dada ta Kira saboda farin cikin da nake ciki a yau din kasancewar Allon Zayyanar saukar Al kur ani Mai GIRMA da aka bani a makaranta Wanda yasha Zanen kaloli masu kyau da burgewa tare Da Rubutacciyar ayoyin bak'ara da fatihatul kitabi da aka Rubuce Allon gaba da baya.... "Dada ta Dada ta taho ki Taya Ni murna yau Halimar ki ta karbi Allon Zayyanar ta..... Dada tafito daga dakin ta tana daura Dan kwalin ta tana fadin.... "Kai madalla Halima ta Ina ma Ina da hanci in rangada Miki gud'a"?. Na iso Ina murna na Mika Mata Allon Wanda Yake cikin sabuwar leda Mai kyalkyali ta karba tana Fadin "Bismillahirrahamani Raheem na tab'a da hannun dama Allah ka Bamu ladar Al kur ani kasa mu cikin Wanda zai ceta Ranar Alkiyama.... "Bari na biya Miki Dada kiji don sayyadi yace muke biyawa mutane suji Dadin da ke akwai cikin Al kur ani... Dada ta Miko min Allon na soma fidda ledar dake ciki tamkar wacce take tab'a kwai har na zare ledar na soma karantawa dada cikin murya ta Mai Sanyi tana saurare har na Kare tace "Ikon Allah Halimatu Anya kuwa akwai wani Abu Mai Dadin saurare irin Al kur ani? Nayi maza nace Mata "Babu shi dada zancen manzon Allah ne kadai yafi shi Dadi.... "Wannan gaskiya ne Allah ya sada mu da manzon Allah ya Kuma sa Al kur ani ya CeCe mu Ranar Alkiyama taso kiyi wanka in fito Miki da sabuwar Rigar da nace Miki sai Ranar saukar ki Zan fito miki da ita in yaso ki kaiwa Yan Uwa da abokan arziki Allon Zayyanar ki Kuma Karanta musu zancen Allah suji Dadin da ke akwai a cikin sa.... Na mike Dada ta hada min Ruwan wanka na fito na iske Ziyada kawata ta iso tana Rike da Allon Zayyanar tana gani nayi murmushi Ina Fadin "Yar Halak Ina bandaki nake maganar ki Bari na shirya ki Raka Ni in kaiwa mama Allo ta Gani... Na shiga Daki na iske Dada ta fito min da doguwar Rigar da ta siya min wacce take da adon stone Kuma Mai daukar idanu . Kalar gwaiduwar kwai ce Mai hade da Dan kwalin ta . Ina saka kayan Ina jiyo dada da Ziyada tana tambayar ta Wai saura izifi nawa ta sauke? Ta fada Mata saura Sha uku Dada tayi Mata ADDU AR Allah ya nuna Mana da Rai da lafiya sai Kuma naji Dada na Fadin "Kaf din yaran gidan Babu Wanda ya sauke Al kur ani tun daga Wanda akayiwa auren har na yanzu sai Halimatu Kuma iyayen su Basu damu ba su dai barsu da boko itama ba wata tsiya suke tsinanawa ba.... Ina gaban madubi Ina daura Dan kwalin Rigar wanda nayi rolling din sa ya Zauna tsab na shafe fuska ta da kwalliya kamar yadda na saba ... Na fito Ziyada tana Fadin "Kai Halima kin hadu wallahi kamar ba ke ba wa zai ce Halim ce? Na harare ta Ina Fadin "Kema yau Halim din Zaki ce mini Ziyada?... "Yi hakuri kin San me na tuna? Nace "A a Tace "Balange Mai shago Anya in ya ganki zai Gane ki kuwa? Naja tsaki Ina Fadin "Mun kusa mu Bata Ziyada Ni Ina wani tunawa da wani balange ne? Don Allah tashi muje in kaiwa mama Allo na ta gani ... Dada ta kamo Hannu na tana Fadin "Baki fesa turare ba Halima ai kin ragewa kwalliyar armashi... Ta fito min da turaren ta tana fesa min kafin tace "Ki fara kaiwa mutanen gida Allon Zayyanar ki Kuma Karanta musu ko sa yi zuciya suke matsawa Ya'yan su zuwa islamiya Kuma duk Wanda ya Baki sadaka ki Amsa Nima kafin ki dawo Zan samu abinda Zaki kaiwa sayyadin sadaka yanzu Kuma Zan Kama kaza guda in Miki ragadada.... "Kai dada kina shagwaba Halima da yawa ai kuwa Zan dawo aci kazar Nan Dani. Cewar Ziyada. Na Rungume Dada Ina Fadin "Allah ka bar mini Dada ta ka Kara Mata lafiya da nisan kwana.... Muka fito kofar dada na nufi madafi inda goggo Dubu take tana tuyar waina goggo jauhara Kuma tana can Yara Yan makaranta sun yanyame ta kasancewar Yan Tara masu siyen abincin tara. Idanun goggo Dubu Yana Kan goggo jauhara da Yara suka Rufe kasancewar ita goggo jauhara taliya da manja take yi ita Kuma goggo Dubu waina da miya da Kuma Yar tsala da yaji duk da itama akwai yaran a wurin ta Amma na goggo jauhara sunfi yawa don Haka sai idon ta Yake Kan kishiyar ta goggo jauhara don ba wani zaman Dadi akeyi ba duk goggo Dubu ce Bata da son zaman lafiya ga tsegumi da neman fitina Amma sai tayi sa a goggo jauhara wayayyiyar mace ce Mai kawai ci da alkunya da Kuma nuna harkar ilimi a komai nata.... "Sannu da Aiki goggo Dubu. Na fada Ina rusunawa ta waigo tana min wani shege shegen kallo musamman da ta ganni cikin sabuwar Riga don Bata Boye Jin haushin ta Kuma Bata son ace Anfi ta komai ko Anfi Ya'yan ta don Haka a sheke ta amsa tana Kare min kallo tun daga sama har k'asa..... "Goggo ga Allo na karbo ku saka mini albarka.... "Wai na sauka? Ta tambaya da mamaki nace Mata eh... "Saukar izifi biyar ko na goma? "Izifi sittin dai goggo.... Ta kada kanta tana Fadin "Shararrar fayif ! Wai ke Nan izifi sittin Kika sauke? To madalla dama sai da asiya ta fada min karatun naki duk Zuk'u ne gashi Kuma na gani ... "Wallahi Babu Zuk'u goggo Allah ma shaida ne Kuma Bari na Karanta Miki kiji in Zuk'u ne..... Na soma Karanta Mata har na Kare Bata ma sake bi ta kaina ba tana ta hidimar sallamar Yara Yan siyen waina . Ziyada ta Kama hannu na mike Muka wuce zuwa wurin goggo jauhara wadda Yara suka yiwa sauki ta dube Ni tana murmushi tana Fadin "Kai Halimatu ba dai an kawo Allon ba? Na Duka Ina Fadin "Wallahi an karbo goggo sannu da Aiki .... Masha Allah Halimatu Ubangiji yasa anyi na tsoron Allah ya Kuma saka albarka kiji. Na Amsa da sauri abinda ke burge Ni da goggo jauhara kenan mace ce Mai fahimta da sanin Rayuwa akasin goggo Dubu... Ta bude bokitin da take zuba kudin cinikin ta ta dauko dari biyu tana Fadin "Karbi Halimatu Allah ya Rika .... "A a goggo ki bar kudin ki wallahi Nagode da ADDU A ma.... "Ke karbi kinji duk Wanda ya Baki karbi albarkacin Al kur ani ne Kuma ko A LAHIRA albarkar ANNABI da Al kur ani muke fatan samu duk Wanda ya Baki karbi abinki Kar ki ki karba... Na karba Ina godiya nace "Goggo Bari na biya Miki bak'ara da fatihatul kitabi.. "Ai kuwa Karanta mini Halimatu naji... Na Karanta Mata gaban Allon da Baya tana ta fadin "Masha Allah shukaran tabarakallah kinji . Na mike Ina Mata godiya muka fice daga gidan Ziyada na Fadin "Wallahi matar Nan tana burge Ni ta San Rayuwa ba kamar goggo Dubu ba Sam kamar Bata je makaranta ba Babu lissafi a lamarin ta... "Uhum Shi kadai na iya fada don ma Ziyada Bata San goggo Dubu bane Ni Kam na San ta Sani na hakika..... "Halimatu Aka Kira sunan muka juya tare da Ziyada saboda shaida Mai muryar wato balange.. "Muje Halimatu don Allah kar ki share shi yau fa Ranar farin ciki ce Ni fa banga aibun balange ba Halimatu Mai sonka kamar Bai kamaci wulakanci ba don Allah ki daina nunawa bawan Allah Nan Baki yin sa ki rabu da kowa lafiya .... Na kada kaina don na yarda da maganar Ziyada kwarai... "Kai masoyiya ta sauka kikayi? "Eh na bashi Amsa cike da wani irin Sanyi.. "Masha Allah Allah ya sa albarka biya min naji in dai ba Zuk'u kikayi ba ... Na kalle shi Ina Fadin "In ma Zuk'un nayi ai Allah shaida ne mala ikun Allah ma shaida ... Na soma Karanta mishi cikin murya ta har na kare shi Kuma ya Amsa da takbeeri Yana Fadin "Takbeer Sadak'ta masoyiya na yarda Allah yasa anyi na tsoron Allah ga wannan sai na kawo abin sadaka ko? Ya Miko min naira Dubu Amma na kawar da kaina Ina Fadin "Nagode ma da ADDU AR da kayi min... Ya mikawa Ziyada Yana Fadin "Rike Mata Ziyada sai Nazo har gida wurin Dada na kwashi gaisuwa Kuma na kawo wani Abu.... Muna Shirin wucewa ne na kula da shi tsaye gefen mu Yana sanye da hannayen sa cikin aljihun wandon sa ga Alama Kuma yaji abinda muke ... Idanun mu suka hadu a lokaci Daya yayin da naji wani Abu ya fizge Ni kamar Jan wutar lantarki. Fari ne tas Mai tsawo Kuma Mai Fadin kirji. Yana da manyan idanu da dogon hanci sai gashin Kansa Mai tsananin kyalli da sheki..... "Nima Azo a biya min karatun naji in Babu damuwa. Ya fada da wani Amon sauti Wanda ya Hana nayi mishi gardama.... "Babu ma wata damuwa Cewar Ziyada Na juyo Ina Jin idon shi a kaina Yana zagaye Ni Amma kamar ance dago muka sake kallon kuda ya saki murmushi Yana Fadin "Kece kikayi saukar ? Na amsa da gyada mishi Kai... "Ok to Allah yasa albarka malama Amma sunan malamar?.. "Halimatu na Samu kaina Ina Mai fada mishi sunan Kai tsaye Babu kwana abinda na tabbatar ban tab'a

Chapter 1 of 11