yi wa wannan ranar ba ne
shi ya sa ki ke fadin haka".
ooti Wani ciwo mai zafi ya mintsini Fadima,
har wayar ta kusa kubuce mata. Ta daure tana jin
ciwon ta ce.
Hum! Haka dai ka ke fad..."
Ta kasa Karasa maganar sakamakon fizgar
cibiyarta da a ka yi, ta sa salati tare da sakin
wayar.
Yana ta faman hello-hello bai ji amsarta
ba, sai salatin da ta ke yi. Hankalinsa ya yi kololuwar tashi, ya kashe wayar ya sake kira,
amma ta kasa kai hannu ta dauka, sai madodowa
131
1
1
SADAUKARWA-2
ta ke.
Mummyn Faanah
Daidai lokacin Ladi mai dakin ta shigo da
niyyar daukar wani abu ta tarar da halin da
Fadima ke ciki, ta nufe ta da sauri tana jera mata
tambayoyin me ke faruwa? Tuni Fadima ta fita
hayyacinta, don haka da sauri Ladi ta tallabe ta
suka fito daga dakin tana kwalawa kawayen
Fadiman kira.
Duk suka fito, ganin halin da ta ke ciki ya
kidima su, suka yi dafifi kowace na fadar
albarkacin bakinta, kafin daga bisani Jummai
daya matar gidan ta lulluba hijabinta ta shiga
gidan Malam Abdullahi ta sanar da su halin da a
ke ciki.
InnaBaida'u da wasu mata suka shigo
suka tafi da Fadima, a na jiran karasowar Isma'i!
wanda Malam Abdullahi ya kira a waya ya zo a
kai ta asibiti, sai ga Hafiz a sukwane. Tun bayan
gama wayar da ya yita kira ba ta dauka ba ya
biyo hanyar gidana Ya iso gidan cikin kidima
yana tambayar abin da ke faruwa, tausayin
Fadima ya narkar da zuciyarsayen
tvAllah ya sani yana jin tausayin wannan
yanayin da ta ke fuskanta da ya san fokacin
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
al'adarta ya yi da tuni an matso da bikin don ya
magance mata matsalar kamar yadda likita ya fada masa.
Bai bata lokaci ba ko jin kunya, tunda
yanzu ta zamo mallakinsa, halaliyarsa da ya ke
ikon yin komai da ita, haka ya runtse ido ya
dauki matarsa a kafada ya sa a mota. Fuskantar
da Malam Abdullahi ya yi Hafiz kokarin tafiya
da Fadima shi kadai ya ke yi,ya sa da sauri ya ba
wa Inna Baida'u umarnin ta shiga motar.
Ba don haka ba kuwa da sai dai su shafa su
ji ba komai, don yana shiga cikin motar da gudu
ya ja ta, bai zame ko'ina ba sai Najnoor Private
hospital, nan da nan a ka karbe ta a ka ba ta gado
saboda fita hayyacin da ta yi.
Wannan rashin lafiya ta Fadima ita ta rusa
komai, domin har magariba ana kanta don samun
saukin ciwon marar da ta ke rakin zai zamo
ajalinta.
Hafiz na zaune ya rafka tagumi cikin
yanayin damuwa da fargaba kada Fadima ta rasa
ranta a dalilin wannan ciwon marar, wayarsa ta yi
kara.
133
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
Yana dubawa ya ga lambar mahaifinsa ce,
ya kara a kunne. Alhaji Atiku ya ce.
"Wai ina ka shiga ne, tun dazu ina
nemanka?"
Hafiz ya ce, "Muna asibiti, Fadima ce ba
ta lafiya".oi
Alhajin ya ce, "Assha, me ya same ta?"
sils) Ya ce, "Ciwon eiki ne"
d BY "To Allah ya ba ta lafiya, ba maganar
daukar amarya ke nan a yau?"
uaa Tambaya ce mara bukatar amsa, amma sai
da ya ba shi amsar da cewa.
oseE tunda har yanzu ba ta cikin
hayyacinta
Ya ce, "Kuffia wane asibiti ne?""
zrHafiz ya ce, "Najnoor private hospital.
Ya ce, "To ga ni nan zuwa
om Bayan an gama sallar isha'i ne Alhaji
Atiku ya iso asibitin, lokacin Fadima tana bacci,
an samu al'adar ta zo mata don haka ciwon cikin
ya lafa mata.
i Tana kwance a kan gado dankwalinta ya
dan zame, ana iya ganin daukar kitson da a ka yi
134
SADAUKARWA-2 Mummyn Fagnah
mata, idon Alhaji Atiku a kanta zuciyarsa ta
soma luguden uku-uku, wani irin yanayi ya dinga
dawainiya da shi. Da kyar ya yi kokarim jan
kafafunsa yay fita daga dakin da ta ke kwancе
saboda zuciyarsa da ta ke karanta masa kada ya
yarda da kaddarar rabuwa da matar da ya ke
tsananin Kauna,led i as in ise shet"
Walwalarsa ta gushe ya ki yarda ya hada
idanu da Hafiz, domin yana ganin kamar idan sun
yi musayar kallo Hafiz din zai ga zanen kaunar
matarsa rado-rado a kan fuskar mahaifin nasa.2
Murya a cushe ya yi masa sannu da mai jiki,
sannann ya yi masa sallama ya tafi gida,Н"
Wani abin rudani da tashin hankali da yad
riski Alhaji Atiku a wannan dare shi ne rashin
nutsuwa, shaidan ya yi kane-kane azuciyarsad
yana Kawata masa kyau da cikar halittar matar
dansa BWAB0 ned Bb mi Ads saitim sb seeb shis sun s
Yana zayyana masa bai dace ya hakura da
matar da ta dace da shi ya bar wa dansa ba! Sam
wannan ba mai yiwuwa ba ne, shi ya cancanta da
auren Fadima. Sai dai anya bakin alkalami bai
bushe ba? An fa taru daruruwan mutane kowa yaA
shaida an daura auren Hafiz da Fadima, wane
135
a
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
yunkuri zai yi don kwatar matarsa daga hannun dansa?
Kwance ya ke a kan gado lokacin da
shaidan ke masa wannan kidan shan kabewar a
kunnuwa, ya tashi zaune ya zuba tagumi da
hannaye biyu, a sarari ya ce.
"Hafiz, sai dai ka yi hakuri. Allah ya
jarrabe ni da kaunar matarka!"
Ya ci gaba da cewa.
"Idan dai kai dan halak ne ya kamata ka
sadaukar min da matarka, ta zama matata!"
Ya karfafa zuciyarsa da wannan kudiri.
"Hafiz da ne na halak, mai dumbin
biyayya, zai iya yi min komai don ya san na yi
masa kowace irin SADAUKARWA, tun daga
haihuwarsa zuwa yanzu".
Ya janyo wayarsa, ya fara duba lokaci da
ya nuna karfe daya da mintina arba'in da bakwai
na dare, kawai sai ya lalubo lambar Hafiz ya
matsa masa kira.
Hafiz yana zaune a gefen matarsa, sam ya
kasa sukuni, addu'a kawai ya ke kwararowa
Allah ya ba ta, lafiya.
Tana kwance idanunta a lumshe tana
136
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
Bai amsa masa ba, ya ci gaba da cewa.
"Hafiz. ina son ganinka da safe".
Hafiz ya ce, "Lafiya Abba?"
Kashe wayar da ya yi ba tare da ya ba shi
amsa ba ya tayar masa da hankali.
Haka ya kwana cikin was-wasi, ko lokacin
da bacci ya fauke shi mafarkai ya dinga yi masu
razanarwa duk a dalilin kiran da mahaifin nasa ya
yi masa da daddare, irin lokacin da bai taбa
kiransa ba.
Da safe bai bar asibitin ba, sai da a ka ba
shi saliamar Fadima. Ya mayar da ita giuan
mahaifinta da zummar sai bayan sallar isha'in
ranar za su zo daukar amarya.
Lokacm da ya shiga gidansu ya tarar da
Abbansa zaune a falo, duk da akwai bakin biki.
Kallo daya za ka yi masa ka gane yana cikin
matsananciyar damuwa, domin fuskarsa ta
zayyana yanayin da ya ke ciki.
Hafiz ya karasa ya nemi guri ya zauna, ya
gaishe shi. Alhaji Atiku ya dubi idanun Hafiz ya
gå yadda suka yi jajir alamar bai samu
wadataccen bacci ba a daren jiya, ya ce.
"Wai a asibitin ka kwana ne?"
137
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
Haka nan sai faduwar gaba ta samu Hafiz,
tunda ya ke da mahaifinsa bai taba jin ya yi masa
magana da irin muryar da ya yi masa magana da
ita yanzu ba. Kunya ta kama shi ya kasa amsa
masa a can asibitin ya kwana.
Alhaji Atiku ya gyada kai, ya ce.
"To, je ka ka kwanta ka rama baccin
tukunna ka zo ina son magana da kaі”.
Musu ba dabi'ar Hafiz ba ne, don haka jiki
ba kuzari ya tashi ya nufi sashensa da zai yi masa
baccin bankwana a safiyar yau din.
Sai dai sam baccin da ya kamata ya yi ya
faskara, nazari kawai ya ke, me ya ke faruwa ne?
Karfe sha daya daidai ya fito daga sashen
nasa, har yanzu Alhajin na falo, sai dai babu
mutum ko daya a tare da shi.
Abu na farko da ya fara dasa masa zargi
shi ne, rashin ganin Hajiya Asiya daga dazu
zuwa yanzu, to ko sun samu sabanin da ya
sauwake mata din ne ya haifar masa da wannan
sauyin yanayin?
A darare ya zauna a kan kafet ya yi masa
sannu da hutawa. Su duka suka yi shiru na.wani
lokaci, kafin daga bisani Alhaji Atiku ya
138
A
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
in
a
Sa
Ba
a
la
ra
m
ка
Ke
a
e.
yi
a
0
sa
jagorance su su koma can bedroom dinsa, bayan
sun zauna ya ambaci sunan Hafiz har sau uku, shi
kuma yana amsawa cike da kaduwa. Alhajin ya
dora da fadin.
"Hafiz, na san a iya tsawon rayuwata na yi
kokarin sauke nauyinka a kaina ko?""
Hafiz ya gyada kai.
"Ko akwai abin da na kasa da shi?"
Ya tambaya idonsa kafe a kan Hafiz.
"Babu, ka yi mini komai Abba".
Ya fada muryarsa na rawa.
"Duk da haka ina yi maka albishir. Anjima
zan saka maka kudi naira miliyan biyu a
asusunka, sannan na mallaka maka gidajena guda
biyu sun zamo SADAUKARWA a gare ka. An
zuba komai na aiki a sabon kamfaninka, zan yi
dauki nauyin albashin ma'aikata hamsin daga
lokacin da suka fara aiki, zuwa wata biyar!
Zuciyar Hafiz ta raunana, ba mamaki
mahaifin nasa yana jin alamun kamar zai mutu ne
a kwana kusa. Ya dago kai da niyyar yin magana,
Abban ya riga shi cewa.
"Duk abin da zan yi maka ba faduwa ba
ce, domin kai kadai ne dana da na mallaka a
139
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
fadin duniyar nan, na san kuma kai mai biyayya
ne, duk abin da zan bukata a gurinka za ka yi min
shi, haka ne??"
Da sauri Hafiz ya ce.
"Abba alkawari ne babu abbin da za ka sa
ni na kasa yi maka shi, muddin bai tsallake
shingen addinin musulunci ba".
Alhaji Atiku ya gyada kai yana jin dadin
samun makamin da zai yaki dan nasa ya kwaci
matarsa, ya сe.
"Ka tabbata ina da wannan alfarmar?"
Hafiz ya ce, "Ko alkur'ani zan iya dalawa
a kan haka".
Shiru Alhaji Atiku ya yi yana kallon Hafiz
tare da nazarin ya dace ya biye masa ya kafa
rantsuwakafin yá bayyanamasa Kudirinsa,
domin abu ne mai nauyin gaske. A hankali ya
tashi ya isa ga durowar da suke ajiye littattafan
addini, ya dauko kur'ani ya ajiye a gaban Hafiz
yana dan murmushi, ya ce.
"Ba wai ban yarda da kai ba ne Hafizu, ina
so dai kawai ka dauki alamarin haka Allah ya
kaddara, ka dauki alkur'anin nan ka yi min
rantsuwa da shi za ka yi duk abin da na sanya ka.
140
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah ASRANUAGA?
"Ba wai ban yarda da kai ba ne Hafizu, ina
so dai kawai ka dauki al'amarin haka Allah ya
kaddara, ka dauki alkur anih nan ka yi min
rantsuwa da shi za ka yi duk abin da ha sanya ka.
Ka dai san matsayinsa a gare ka, da kuma illa
kauce wa rantsuwar abin da za ka yi da shi"
Jikin Hafiz ya yi sanyi kalau, tsoro yarle
kama shi sosai, me ke shirin faruwa né da
mahaifinsa zai gifta wannan shamakin? Sai kuma
ya tuna duk duniya ba shi da kamar mabaifin
nasa, haka yana da tabbacin ya yi zurfi auilimin
addini, ba zai taßa sanya shi aikatas abin da baab
daidai ba, don haka ya matsa ya sa hannu yans
dauki alkur'anin yana kallon mahaifin nasa ya
cё.
"Na rantse da tsarkin mulkin Allah, da
darajar da ya yi wa alkur'ani mai tsarkizansw
dauwama ina bin'umarnin mahaifina muddin baiм
saba wa Allah baoio utnla iy sy xtsH Alhaji Atiku ya gyada kai cikin gamsuwa
da rantsuwar dan nasa, sannan ya се твпет в nseuk
"Na gode da ka kasance dan, halak Ina sb
rokon Ubangiji ya ba ka juriyar abin dai zan
umarce ka da shi, Ya kuma musanya maka shi
141
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
da mafi alkhairi daga cikin alkhairanSa"
Hafiz ya yi shiru jikinsa na kara sanyaya.
"Shin jiya a ina ka kwana tsakaninka da
Allah?"
Kai tsaye ya yi masa wannan tambayar,
shi ma ba tare da jinkiri ba ya amsa masa.
"A asibiti wajen Fadima".
Ya ce, "Wani abu ya gilma tsakaninku na
auratayya?
Duk da tambaya ce mai shayar da kunya
da mameki, amma a hakan Hafiz ya ba shi
arma
"Wallahi babu abin da ya shiga
tsakaninmu".
Alhaji Atiku ya ce, "Za ka iya tuna
watarana da muka je unguwar su Alhaji
Mande?"
Hafiz ya yi shiru cikin nazari. Tabbas ya
tuna, a ranar ne ya gane unguwar su Fadima,
kusan a ranar ne ma ya kafa tubalin soyayyarsa
da ita bayan ya rasa masoyiyarsa Rufa'atu. Ya
gyada kai da fadin.
"Na tuna ranar".
142
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
Alhaji Atiku ya ce, "To a ranar ne na fara
ganin yarinyar da na fada maka zan aura,
wadda na sha yin istihara ina ganin alheri
tattare da ita. Sai dai matsalar da a ka samu
lokacin da na tura a bincika min mahaifanta, sai
a ka sanar da ni an bayar da ita ga wani..."
Dukan kirjin Hafiz ya tsananta.
"Duk da yadda na ke jin damuwar
rashinta na daure na hakura, amma wani
al'amari mai shayar da mamaki, sai ga shi ashe
ba wata ba ce wannan yarinyar face matar da ka
aura! Hafiz ba zan boye maka ba idan na rasa
auren Fadima zan rasa abubuwa da yawa masu
muhimmanci na cikar farin cikin rayuwata, don
haka a matsayina na mahaifinka da ka fi kowa
sanin rashin dacen da na yi na matan aure da ya
sa a ke kirana AURI-SAKI, ina rokonka da
girman Allah ka.daure ka sadaukar min da
matarka. Ma'ana ka saki Fadima na aura!!!"l s
Yadda maganganun suka razana Hafiz
haka ya mike tsaye a razanen, yana maimaita.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un
A umarnin da mahaifin nasa ya yi masa
143
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
bai saba wa shari'ar ubangiji ba, tunda bai
kwanta da Fadima ba, ga shi ya gifta ransa da alkur'ani, sai dai fa abu ne mai matukar rudani
ya saki matarsa mahaifinsa ya aura! Shi tunda
ya ke bai taba jin jarabtaccen al'amari
kwatankwacin wannan ba..
Nan da nan gumi ya karyo masa ta hanci
ta goshi, har cikin riga ma, jirin da ke neman
dibarsa ya tilasta masa komawa ya zauna jabar,
yana jin kirjinsa kamar zai tsage saboda
tsananin dukan da zuciyarsa ke masa!
Tammat!
Mu hadu a littafi na uku don jin
warwarar wannan kullin, SADAUKARWAr za
ta yiwu? Idan ta yiwu mene ne makomar
hakan?
Wace ce mai sakonnin wayar, da gaske
ba Rufa'atun ba ce?
Da ma wasu sauran tambayoyin duk sura
cikin ci gaban labarin.
Mai kaunarku koyaushe.
Shagwaba6biyar Daddyn Yusuf
144
Littattafan marubuciyar:
RASHIN JINI
SADAUKARWA
INA HUJJAR TA KE?
KAZA DA HATSI
WUTAR DAJI...
SUNANMU DAYA
BAHAGON HUKUNCI
Bugawa da yadawa
MADAKIN GINI BOOKSHOP
Kasuwar Kurmi, Kano City.
08036527328, 07068361426, 07037690966. 08104059156
F
Cover Graphics
Anka-Graphics fagge 07030319787
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels