tsarin gidan ba a fara zuwa gurin
'yar gidan sai an nemi izini daga maigidan, shi
ne za mu je gaisuwa da rokon iri".
Larab ya yi shiru yana wani tunani, kafin
daga bisani ya yi murmushin yake, ya ce.
"To me ka shirya game da zuwan?"
Hafiz ya dube shi, ya сe.
"Ban gane me na shirya ba?"
26
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
Larab ya cc, "Ah, kana nufin hannu
rabbana za mu je?"
Hafiz ya yi dariya, ya сe.
"To me za mu kai musu?"
Larab ya amsa masa da cewa.
"Kamata ya yi mu sayi ko dan lemo da
abarba ne ko?"
Hafiz ya ce, "Ba matsala".
Kafin su isa unguwar suka tsaya wajen
mai sayar da kayan marmari suka cika ledar
viva da su lemo da ayaba, sannan suka doshi
unguwar. Gidan su Habib suka fara zuwa, don
shi zai yi musu jagoranci.
Habib ya dinga dariya, ya ce da Hafiz.
"Kai mutumina akwai ka da zumudi, to
ai Malam din ba ya zama a irin wannan ranar'
Hafiz ya dan harare shi.
"Tsiya ta da da kai kenan ba ka cika ba
wa komai muhimmanci ba, don Allah ka daina
wannan halin naka, sam ba shi da kyau wallahi".
Habib ya de, "Daga fadin gaskiya sai ka
yi min wannan fassarar? To shi kenan mu je
27
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
idan an tarar ba ya nan kai ka jiyo
Hafiz ya ce, "Eh, na ji mu je".
Suka doshi gidan a motar Hafiz, da yake
layi daya ne a tsakani shi ya sa ba su bata
lokaci ba suka isa. Yaro suka samu ya yi musu
sallama da Malam Abdullahi, jim kadan ya fito
yana ganin Habib fuskarsa ta yalwatu da fara'a,
yá ce.
"A'ah malam Habibu ku ne tafe?"
Su duka suka rusuna don gaishe da shi,
ya amsa musu cikin jin dadi. Habib ya ce.
"Malam wani sha'ani ne ya zo da mu:
game da wannan abokin nawa mai suna Hafiz"
Ya Karashe yana nuna Hafiza da ya
sunkuyar da kansa kasa. Malam ya ce.
"To, ina zuwa"
Ya shiga cikin gida ya sa Tahir ya
shimfida tabarma a soron gidan, sannan ya
dawo waje ya ce su shiga. Suka shiga suka
zauna a ladabce.
Malam ya ce, "Ina jinka malam Habib".
Habib ya gyara zama ya soma da cewa.
"Malam wannan abokina ne, ko kuma na
28
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
ce aminina, domin mun dade da shi, na san
halinsa da yawa sunansa Hafiz, to shi ne Allah
ya hada shi da Batula a inda ta ke koyon na'ura
mai kwakwalwa, ya ji yana sonta da aure. Ya
same ni da maganar na sanar da shi ka'idar
gidan nan, shi ne muka zo maka da zancen"
Malam Abdullahi ya yi shiru idonsa a
kanCELERT Hafiz, tun da ya ga yaron ya ke jin ya
kwanta amasa a rar domin a kallo daya ya
gamsu da kamewarsa, sai kuma ga shi ya
gurfana a gabansa da sunan ya zo neman izinin
tsayuwa da yarsa, wannan ya isa shaidar da Ka
gaske yana sonta. Domin a wannan zamanin ba
a cika samun matashi kamarsa ya amince da
zuwa neman izini don yana son yarinya ba.
Amma duk da haka bai yi garajen yanke
hukunci ba, illa ya nuna jin dadinsa da faruwar
hakan, sannan ya doara da fadin.w sD
"Na ji dadi kwarai da wannan karamcin
naka, amma wani hanzari ba gudu ba, zan ba
Hafizu damar tsayawa da Fadimatu ya nemi
soyayya a gurinta don ba na yi wa ya'yana
aure da wanda ba sa so, amma hakan za ta
29
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
tabbata bayan bincike da zan gudanar na nasaba
kamar yadda ma'aiki (S.A.W) ya koyar da mu"
Hafiz ya ji tsananin dadi ya kwaranya a
zuciyarsa, domin alamu dun kara tabbatar masa
da ya yi dace da 'yar kwarai, wadda Hausawa
kan ce mai son IRI NA GARI ya duba gidan
Kwarai.
Haka suka baro gidan da alkawarin
Malam Abdullahi zai tuntu6i Habib lokacin da
ya gama bincike a kansa, ya karfi cikakken
adireshin mahaifinsa. Da za su tafi suka ba shi
dubu biyar, da farko ya ki karba saboda ya
nuná musu ba don kudi zai ba su Fadimatu ba.
Larab ya nuna masa su ma ba don haka suka ba
shi ba, kyauta ce suka yi masa a matsayinsa na
mahaifinsu. Ko bai ba su Fadimatu ba a yadda,
ya karbi lamarinsu ma ya gode.
Da wannan farin ciki Hafiz ya shigo
gidan, ya sami Alhaji Atiku a falo yana kallon
labaran kasa. A gefe guda kuma Hajiya Asiya
na zaune tana ta hura hanci alamun har yanzu
ba ta huce ba. Hafiz ya zauna a kusa da kafafun
mahaifin nasa, yayin da Alhaji Atiku ya rage
30
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
sautin talabijin din ya dubi Hafiz ya ce.
"Ĝa dukkan alamu an samu nasarar abin
da aka fita nema ko?"
Murmushi ya kara bayyana a fuskar Hafiz ya cе.
"Kwarai Abba, an dade. Amma ya сe mu jira shi ya gama bincike".
Alhaji Atiku ya dafa kan Hafiz ya ce.
"Ina tayaka murna Hafiz, hakika alamu
na nuna ka dace da surukin kwarai, Allah ya tabbatar da lamarin"
Hafiz ya amsa da, "Amin Abba.
Ya ce, "To ni yaushe za a kai ni na gaida
surukin nawa?"
Kunya ta kama Hafiz ya kasa magana. Alhaji Atiku ya ankare da hakan, ya ce.
"Ko don da ya ke a bari sai nan gaba idan
tafiya ta yi nisa, wato idan ya gama binciken ya
ba ka damar tsayawa da yarinyar... Wai mene
ne sunanta ma?"
Murya kasa-Kasa Hafiz ya ce. "Fadimatuz Zahra"
Alhaji Atiku ya yi dariya ya ce.
31
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
"Ka ga mun yi anko ke nan, don ni ma
sunan sabuwar uwar taka ke nan
Hajiya Asiya ta ja dogon tsaki tana fadin.
"Sabon salo busa usur da asuba".
Ba wanda ya kulata yayin da Alhaji
Atiku ya ce da Hafiz.
"Sai ka dage addu'a dare da rana kana
neman zabin Allah, ka kuma yi tawakkali duk
abin da ya same ka daga Allah ne, idan ya
hukunta matarka ce falillahi hamdihi, idan ma
akasin haka aka samu don Allah kar ka zafafa
ka yi tawakkali kamar yadda ka yi game da
Rufa'atu".
Ya salam! Da Alhaji Atiku ya sani bai
tabo wa Hafiz zancen Rufa'atu ba, domin da ya
koma dakinsa kasa sukuni ya yi. Sakon da ta
turo masa dazun ya yi masa tsaye a zuciya,
wanda ta ke nufin har yanzu ba ta hakura da shi
ba, tana hangen wani sanadi zai dauwamar da
su a inuwa daya. Da damuwa ta yi masa yawa
ya kasa jurewa sai ya dau wayarsa ya dinga
kiran layinta ana sanar da shi a kashe wayar ta
ke. Karshe ya tuna da sabuwar lambar da ta yi
32
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
amfani da ita wajen turo masa sakon ya kira, ita
kuma ya yi nasarar samunta a kunne amma har
ta karaci kararta ba a daga ba.
Ba a jima ba kuma sai ga rubutaccen
sako ya shigo wayarsa da lambar. Ya soma
karantawa kamar haka.
"Hafiz ina sonka sosai fiye da yadda baki
zai furta, sai dai na rasa yadda za a yi ka gane
irin son da nake maka. Wannan dalilin ke sa ni
fargaba a duk lokacin da na ji muryarka. Ka yi
hakuri ba zan iya daga wayarka ba, ka dai sani
ina sonka har karshen rayuwata".
Ya sauke ajiyar zuciya lokacin da ya
gama karanta sakon. Tausayi mai tsanani ya
shige shi, sai yaushe ne Rufa'atu za ta gane ba
laifinsa ba ne? Ya takarkare shi ma ya rubuta
mata amsa.
"Na yarda da kina sona, domin ko halin
da ki ke yanzu a ciki na kasa juriya ya tabbatar
min da zurfin Kaunarki. To amma ya za mu yi
33
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
da ikon Allah? Mu yi tawakkali mu mikà
lamarinmu ga Sarki Allah, idan da rabon za шп
zauna a inwa daya sai ki ga wani sanadi ya
assasa hakan, domin Allah ba Ya bacci, ba Ya
mantuwa a kan komai. Don Allah ki daure ki
sanyaya zuciyarki kin ji? Yawan damuwarki na
daga min hankali matuka".
Bayan ya tura sakon ya dade yana kallon
wayar, a bangare daya kuma yana jin kaunarta
na kara shiga jinin jikinsa.
Har kullum yana hango wa kansu zama a
muhalli daya, yana hango Rufa'atu a wani
matsayi na rayuwarsa marar gushewa. Samun
Fadima a gare shi hanya ce ta kawo sassauci ga
dumbin damuwar da ya ke cikina rashin
Rufa'atu har ya kan yi kokarin goge shafin
soyayyarta a zuciyarsa,amma a wannan
lokacin komai ya kunce wa Hafiz, burinsa bai
wuce ya ji zazzakar muryarta tana ambata masa
yawan kaunarta a gare shi. Burinsa bai wuce
yau mahaifinsa ya ce ya amince ya koma wa
Rufa'atu domin kulla mu'amalar aure ba.
34
C
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
Haka Hafiz ya yi ta juyi yana kallon
hotunan Rufa'atu da fatan maido bara zuwa
bana.
Washegari ya shiga gaida mahaifinsa
bayan sun gama gaisawa, Alhaji Atiku ya dubi
Hafiz a nazarce ya hango damuwa a tare da shi,
tausayinsa ya kama shi. Ko kadan ba ya so ya
ga Hafiz cikin halin damuwa yana ji a jikinsa
duk lokacin da Hafiz ya shiga damuwa, to
Allah zai kama shi da laifin hakan, domin yana
ganin kamar ya tauye wa Hafiz hakki ne, amma
dole tasa ya hana Hafiz.mu'amala da Rufa'atu.
Cikin nutsuwa Alhaji Atiku ya ce.
"Hafiz me ke damunka?"
Hafiz ya yi malalacin murmushi ya сe.
"Ba komai Abba, jiya ne dai na kwana da
ciwon kai".
Alhaji Atiku ya ce, "Hala ka yi tunani
ne? Don Allah Hafiz ka daina sanya damuwa a
ranka, kar ka so ka ji yadda nake kasancewa a
duk lokacin da na ganka cikin damuwa, sai na
ga kamar na kasance mugun uba...."
Da sauri Hafiz ya ce.
35
:
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
"Ko daya Abba, ka daina tunanin ba ka
yin adalci a gare ni. Wallahi babu hukuncin da
za ka yanke min ya zamo cuta".
ka ji?"
Alhaji Atiku ya ce, "To ka daina damuwa
Ya ce, "Insha Allah".
Alhaji Atiku ya ce, "Yauwa, da ma ina
son sanar da kai an kammala ginin kamfanin
nan yaushe za ka je ka gani?"
Hafiz ya dago kai da murmushi ya ce.
"Kai amma aikin ya yi sauri. Ina ga ko
zuwa gobe sai na je ko?"
Alhaji Atiku ya jinjina kai ya ce.
"Eh hakan na da
:
na da kyau, amma fa na yi
abin da ba ka so, wato na mallaka maka shi
halak malak, ba ya cikin kadarorina da idan na
mutu za a raba gado da shi"
Hafiz ya dan daure füska ya ce.
"Kai Abba, wai me ya sa ka ke haka ne
komai mai muhimmanci sai ka ce ka mallaka
min shi?"
Alhaji Atiku ya yi dariya ya ce.
"To ai kai ma din mai muhimmanci ne
36
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
shi ya sa na ke SADAUKAR maka da duk abu
mai muhimmanci"
Ya ce. "Duk da haka Abba ka daina. ka
dinga barin kadarorinka a hannunka..."
Alhaji Atiku ya tare shi da fadin.
"Saboda me? Ka sani ko yau na fadi na
mutu 'yan uwana su yi sama da fadi da
dukiyata? Amma idan tun ina raye kowa ya
shaida na ba ka kadarorina ka ga ko da ta Allah
ta kasance bå mai tunanin ya yi sama da fadi da
su.
Hafiz ya ce, "Haba dai Abba, ai su Baba
Aliyu ba za su yi haka ba, don Allah ni ka ma
daina kawo mutuwa kusa, ba na son na rasa ka.
don idan na rasa ka zan yi kukan gatana ya
Kare".
Alhaji Atiku ya kai hannu ya dan bugi kafadar Hafiz ya ce.
Dan lelen Abbansa. Allah ya sa mu yi
tsawon rai mai amfani".
Hafiz ya amsa, "Amin"
Yana barin gurin Abban nasa wayarsa ta yi kara, ya duba sunan Habib ne ya gani. Cikin
37
SADAUKARWA-2 Muňmmyn Faarlah
zumidi ya fauka don yana kyautata zaton
bayani ne zai ji game da abar kaunarsa.
"Habib. va a ke ciki?"
Habib ya ce. "Zumudi sarkin tabargaza
ke nan, wato ko gaisuwą ba za ka barimu yi ba.
anya Hafiz yarinyar nan ba ta soma zautar da
kai ba?"
Hafiz ya ce. Tolsarkin jayc-jaye, don
Allah kai min bayanin abin da keda akwai, kar
ka bata min lokaci.
Habib ya ce, "Ah to shi ke nan sai
anjima. don ni'ma ina tattalin nawa Hokacin
kamar baturen ingila..
Da sauri kuma cikin sarewa Hafiz ya tari
numfashinsa da fadin
"Kai fa matsalata da kai ke nan. komai
sai ka vi masa waśar don Alah be serious. me
ka ke son fada min?
Habib ya yi dariyayá ce."Ja'iriCidan ba
da irin wannan damarBasyausher (zaka
langwabe min kamar marayathaka?
Hafiz ya yi dariyar da ba tá kai har ciki
ba, ya ce.
38
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
"O.K, shi ya sa ka ke gara ni? Mhm, to ni
dai na ji na zubda makaman, yauwa Yaya
Habib ina saurarenka".
Habib ya kyalkyale da dariya, ya сe.
"To ai ka san gwamnati ta hana aikin
banza, don haka ka kira ni tunda ka san kudina
a ke ci ba kuma kai ke turo min katin ba, ko..."
Kafin ma ya karasa doki da gajiyawa ya
sa Hafiz ya datse kiran, ya kuma bi shi da nasa.
Yana dauka bai tsaya jinkiri ba ya ce.
"Albishir zan maka, dazun surukinka ya
kira ni ya sanar da ni ya ba ka damar ka zo ka
nemi soyayya a gurin Batulu..."
Dadin da ya shigi Hafiz ba don yana
jingine da bango ba hakika da tafiya ya ke ya
fadi, idan tuki ya ke da ya kai wa abin hawan
da ke gabansa karo. Farin ciki ya sa shi fashewa
da dariya sosai.
Habib ya ce, "Kai dan tsaya mana, kar ka
kashe min dodon kunne, ba auren a ka ce an
daura ba. Dama kawai a ka ba ka ka nemi
soyayya, idan kuma ba ta amince ba yaro sai a
rungumi na Annabawa".
39
SADA
SADAUKARWA-2
Cikin dariyar Hafiz уa сс.
Mummyn Faanah
"Wannan albishir din ya fi daura auren
ami gardi a gare ni, domin na san tunda na samu
ayar amincewar mahaifinta, samun soyayyarta ma
zai zamo abu sassauka, ko ka manta bayanin da
ka yi min da ya fitö daga bakin Fadima?"
e na
iya
ai b
Allal
a 6:
njin
ám
Habib ya ce, "Ban manta ba, saura goron
albishir don ungulu ba ta jewar banza".
Hafiz ya yi dariya, ya сс.
"Oho dai, ai aikin gama ya gama, da dai
ba ka fara sanar da ni ba ne ka zo da wannan
fatawar, wata kila ka samu 1,500 recharge
card...
Habib ya katse shi da cewa.
Wallahi yanzu ma ba ka isa ba, ko na
750 ne ka turo min, ai na yi kokari ma a haka
da na bata lokacina, da kudina na sanar'maka"
Hafiz ya ce, "Hmm! Sai ka gan ni anjima
ai da daddare..."
Ka
341
Habib ya ce; "Tsaya, su fa gidansu ba a
tadin 'yan shan minti ato, sai a zo da yamma
Ja. idan ba haka ba murna sai ta koma ciki"
an Hafiz ya се, "Ко da asuba ma a ka
ba
40
3
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
kayyade min zan zo karshen yamma"
Yana Karashe fadar hakan ya kashe
wayarsa.
Ya dade tsaye a gurin yana maimaita
kalmar godiya ga Allah da Ya kawo masa
lamarin a saukake.
Bai san son da ya ke wa Fadima ya kai
girman mizanin kasa fasaltawa ba sai a wannan
lokacin. Tabbas bayan Rufa'atu bai so wata 'ya
mace kamar yadda ya ke jin karfin son Fadima
na kutsawa da karfin gaske a cikin zuciyarsa.
Ana gama sallar la'asar Hafiz ya shilla
wanka, ya murza mai akwai wani dinkinsa da
ya karbo jiya na wani farin yadi, tunda yau rana
ce mai muhimmanci ya zabi ya saka shi, da so
ya yi sai juma'a mai zuwa, to amma zuwa gurin
Fadima da kayan abu ne da zai faranta masa
rai, a kalla duk ranar da zai dubi kayan zai
dinga tunawa da su a ka soma ginin tubalin
soyayyarsa da Fadima, Bintu Zahra, Batulu
Abdullahi.
Da farin ciki sosai ya saka kayan, ya
kawo hular zanna bukar wadda a ka yi dinkinta
41
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
da farin zare da baki, haka takalman kafarsa
bakake ne, da ya ke aikin jikin tagguwar fari da
bakin zare ne, sai komai ya yi cas a jikinsa, ko
da ma Hafiz ba daga baya ba wajen faukar ado,
ya ko hadu ainun.
Hummer Jeep ya dauka daya daga cikin
motocin da Abbansa ke ji da su.
Gidan su Habib ya fara zuwa, a kofar
gida ya tarar da shi zaune a majalissar da sukan
zauna shi da abokansa duk yammaci.
Habib na hango Hafiz ya mike da sauri
ya ba shi hannu suka yi musabiha ya ce.
"Yau shi ne farko kuma karshe, ka dai
san Zahra kanwa ce a gare ni, ba zan juri zuwa
tadi gurinta ba".
Hafiz ya ce, "Na ji, mu je don Allah".
Suka shiga mota suka zagaya baya zuwa
gidan su Fadima. Suna tsayawa da motar,
Malam Abdullagi ya fito daga soron gidan da
alama wani gurin za shi.
Habib da Hafiz suka rusuna suna gaishe
da shi, ya amsa tare da cewa.
"Malam Hafizu ka samu sakona ke nan?
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
と
Na bincika nasabarka, alhamdu lillahi na tarar
da mahaifinka mutum nc kamili da a ka ba da
shaidarsa, don haka na yarje maka ka cí gaba da
zuwa gurin Batulu har ku daidaita junanku"
Hafiz ya ji dadi da wannan bayani, su
duka suka yi wa Malam Abdullahi godiya,
sannan ya koma cikin gidan don sanar da
Fadima tana da baki.
Suna nan tsaye, wani yaro ya fito daga
cikin gidan dauke da tabarma, ya shimfida a
kofar gidan sannan ya ce su zauna. Suka zauna
jim kadan Fadima ta fito cikin yalwatacciyar
shigarta ta kamala. fuskarta kadaran-kadahan ta
gaishe da su. Habib ne gaba wajen amsawa,
sannan ya се.
"Malama Fadima, kamar yadda" na yi
miki bayanin abokina, ga 'shi nan na rako shi.
na kuma fada masa yadda muka yi da ke, don
haka daga yanzu din nan ba zan kuma zama
dan rakiyarsa ba".
'Fadima ta yi murmushi ba tare da ta ce
komai bá. Hafiz ya ce.
"Wallahi ko me za ka ce godiya dai ce
43
SADAUKARWA-2
tsakaninmu".
Habib ya mike. ya ce.
Mummyn Faanah
"Idan ka gama ka same ni gida".
Bayan tafiyarsa sai duk su duka suka yi
shiru, Hafiz yana kallonta cikin shauki, ita
kuma kanta a kasa kunya duk ta lullube ta
saboda wannan ne karo na farko da ta taba
tsayawa da saurayi tunda ta ke.
"Malama Fadima, ina fatan Baba ya yi
miki bayanin abin da ke tafe da ni?"
Ta yi shiru, ya ce.
"Ko da yake bai kamata ma na vi miki
wannan tambayar ba tunda shi ya turo min ke.
Don Allah ina rokon alfarmarki, kada ki 6oye
min sirrin zuciyarki game da ni, idan kin
aminta da ni zan yi farin ciki, haka idan akasin
haka ma aka samu zan yi farin cikin".
Ta dai yi shiru ta kasa magana.
Ya ce, "Don Allah ki yi min magana,
bana so na shiga hakkinki, ni dai Allah ya sani
na kamu da matsananciyar kaunarki, wadda na
ke fatan ta kai mu ga aure ban sani ba ko ke
kina da wani ra'ayi game da aurenki".
44
SADAUKARWA 2
Cikin sanyin muryarta ta ce.
Mummyn Faanah
"Ba ni da wani ra'ayi a game da aurena.
sai abin da Allah ya za6a min".
Ya ce, "Ke nan kin aminta da ni?"
Та сс, "Ko da ban aminta da kai don
ra'ayin zuciyata ba, zan aminta da kai don cikar
nasabarka wadda mahaifina ya bincika ya
tarar
Ya girgiza kai, ya ce.
"A'a Fadima, na fi so ki fada min
gaskiya, kar ki so ni don dole, idan kina sona
har cikin zuciyarki ki fada min. wallahi ba zan
ji haushi ba idan kin ce ba kya sona, sai dai ba
zan yi fatan hakan ba, don a zahirin gaskiya ina
miki kaunar da ba zan so ki kubuce min ba".
Ta dago kai kadan ta dube shi cikin
sanyayyen 'kałlonta, kafin daga bisani ta maida
kan Kasa saboda ba ta iya jurewa kallonsa, ta
ce.
"Bayanin ke nan, na amince da kai da
zuciya daya bisa dalilai guda biyu da na
hanga".
Ya gyara zama yana kallonta ya ce.
45
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
"Ina jinki, fada min dalilan".
Ta yi shiru kamar ba za ta yi magana ba,
Ya lura halayyarta ne haka, kafin ta yi doguwar
magana tana sararawa. bai takura mata sai ta yi
maganar a dole ba, illa kafe ta da idanu da ya yi
yana jin farin ciki sosai a ransa.
Ta ce, "Dalili na farko da na amilnce
maka shi ne, cancantarka. Don a rayuwata ina
son namiji kamili wanda a kallo daya da na yi
maka na fuskanci haka.
Na biyu, ka cika sharuddan da Ma'aiki
(S.A.W) ya koyar mana, wato idan saurayi ya
ga budurwa yana so kafin ya tunkare ta ya
soma zuwa gurin mahaifinta neman izini.
Wadannan dalilai su suka sa na amince da
soyayyarka a gare ni".
Tana kammala fadar haka ta yi shiru tana
murza yatsun Kafarta. Ya yi murmushi ya ce.
"Na ji dadi, kuma na gode da wannan
karamci da ki ka nunan. Allah ya barmu tare".
Can kasan makoshi kamar ba tason
maganar ta fito ta amsa, "Amin".
Ya ce, "Kin san wani abu, da gaske fa na
46
SADAUKARWA-2
shiga rudani a kanki".
Mummyn Faanah
Ta dan dago cikin rashin fahimta ta ce.
"A kan me?"
Yana murmushi ya се.
"Ai na yi zaton wanda ke kawo ki
mijinki ne, sai da Habib ya ke sanar da ni
yayanki ne".
Ta yi murmushi, ta се.
"Auho! Yaya Isma'il ne, shi ne babban
yayanmu".
Ya ce, "Haka Habib ya fada min... Yanzu
Fadima yaushe ki ke ganin ya dace na dinga
zuwa?"
Та сc, "Eh to duk lokacin da ka zo ma
daidai ne".
Ya ce, "Na dauka kina zuwa islamiyya?"
Ta ce, "A gida malam ke biya mana duk
bayan sallar asuba da isha'i".
Ya jinjina kai cikin jin dadi, ya се.
"Masha Allah, gobe ai za ki je daukar
dárasi ko?"
Ta ce, "Insha Allah".
Sun tattauna cikin fahimtar juna kafin
47
SADAUKARWA-2
daga bisani su yi sallama.
Mummyn Faanah
Abin da Hafiz ya lura game da Fadima
mace ce mai zurfin ilimin addini, da nutsuw
sosai. Wannan ya armasa masa zuciya, yakuma
sa shi tunanin ya yi dacen samun mace ta gar
ba kwashi kwarab irin wafanda mahaifinsa ya
aura ba.
WACE CE FADIМА?
Malam Abdullahi mai almajirai haifaffen
garin Bauchi ne a karamar hukumar Jama'are,
neman ilimin addini ya dawo da shi cikin birnin
Bauchin, inda daga nan ya soma yin dako a
kasuwanni yana dan samun abin kashe, lokacin
da ya girma zaman Bauchi ya kama shi
tsakaninsa da Jama'are sai dai ziyara.
Ya samu ilimin addini mai zurfi, na
bokon ne ko A.B.C.D bai taba zuwa koyo ba.
Zurfin iliminsa ya sa malamin da ya ke zaune a
gidansa tun yana yaro ya wanke 'ya sukutum ya
ba shi, wato Hajara ya kuma hada masa da inda
za su zauna a cikin gidan nasa, don gidan babba
ne akwai bangaren da irin Abdullahi ke zama,
48
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
za su zauna a cikin gidan nasa, don gidan babba
ne akwai bangaren da irin Abdullahi ke zama,
wato sabbin aure za su zauna kafin Allah ya
hore musu nasu, ko kuma su samu karfin kama
gidan haya su tashi a saka wasu.
s sbbe Tun can baya malam Abdullahi ya kan
aTID E) Б
zauna wa malaminsa a makaranta, ma'ana yana
koyar da daliban makarantar idan malamin na
da wani uzuri, don Abdullahi tuni ya sauke
alkur'ani da sauran littattafai, don haka ko
bayan aurensa ma bai yı kasa a gwiwa ba ya
kan yi hakan, sannan ya kan fita neman dari da Sobab ups ase dub na etisd si so a sma
182 a haka Hhar Allah ya albarkace su. da
sd wudisd st sd isd dsIIA
samun da namiji, wanda suka sa wa Isma'il. USTSU Kudin sunan da Hajara ta samu suna da yawa,
ta damkawa mijinta su, lokacin yana da wasu
kudın da ya ke tarawa, ya hada ya sai musu (2SIKI fili.LUST
sionsIdan ya samu sa faragar kud kdi ya kan je da sun 20 synnisy SS Su almajiran Malam su dan taba ginin gurin har ya ssisM рт ву li s kammala. Lokacin da suka koma gidan da
shekaru biyu Hajara ta kuma haihuwa, wannan
karon ma namiji ne ta haifa Sablu, bayan shi a
49
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
ハ
k
al
ká
A
ki
dl
ki
1
k
P
la
b
ka haifi Fadima. Tana da wani cikin ne ciwon
sankarar mama ya kamata, wanda cikin lokaci
Kankani Allah ya yi mata rasuwa.
Wannan rashi ba karamin tashin hankali
ya jefa zuri'ar Malam Abdullahi ba, babu
wadda a ke tausaya wa kamar Fadima wadda a
lokacin ba a jima da cire ta daga mama ba, ga
shi Allah ya sako mata kwallafar uwa.
Bayan an yi sadakar arba'in a ka wanke
Kanwar Hajara mai suna Baida'u a ka ba wa
Malam Abdullahi aurenta. Ita ma din dai mai
hakuri ce kamar 'yan uwanta, ta rike su Fadima
kamar ita ce ta haife su, duk wani abu da uwa
ke yi wa 'ya'yanta Inna Baida'u na yi musu, sai
dai ita Allah bai ba ta haihuwa ba har kawo wa
yanzu.
Fadima ta samu tarbiyya sosai, tun tana
;yar shekaru goma sha uku ta sauke alkur'ani
mai tsarki. Ta yi karatun firamare da sakandire.
Da ya ke yarinya ce mara kula samari don haka
da Isma'il ya roki Malam Abdullahi alfarmar a
barta ta yi difloma a Gangaren na'ura mai
kwalwa bai hana ba, sai dai ya kafa sharadin da
50
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
ta samu miji za ta yi aure, ko ba ta kammala
karatun ba, kuma a haka a ke har yanzu.
*** *** ***
Kafin mako daya soyayya ta kankama
tsakanin Hafiz da Fadima, sun fahinci juna
sosai duk da dai zuwansa biyu a gidan nasu,
amma dai sukan zanta idan ta zo daukar darasi.
Abota ta kullu tsakaninsa da Isma'il ta haka ne
ma Isma'il din ke dan daga musu kafa idan ya
zo daukarta ya tarar suna hira, sai ya jira su
zuwa mintoci kafin daga bisani su tafi.
Farin ciki na kama Hafiz duk lokacin da
ya kasance da Fadima, yanzu ya ture batun
Rufa'atu, ya sa wa zuciyarsa dangana don
samun lafiyarsa da kwanciyar hankali, duk da
ba ta tsagaita da yi masa atisayen sakonnin
jaddada ba za ta iya daina sonsa ba har abada.
Alhaji Atiku na zaune a falonsa, Hajiya
Asiya na gefensa fuskarta ba walwala ta ce.
"Alhaji, don Allah ka tsaya ka saurare
n1.
Ya dago kai ya dube ta, ya ce.
51
S
11
a
kc
an
ka
A
ka
al
ki
11
S
k
d
la
از
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
"Karshen tsayawa ma a zaune na ke. Ina
saurarenki sarkin korafi".
Ta ce, "Maganar auren da ka ke shewar
za ka kara, da me na rage ka da ba za ka iya
hakurin zama da ni kadai ba?"
Yana murmushin yake ya ce.
"Da abubuwa da yawa Asiya. Idan zan
zayyano miki illolinki ke kanki sai kin ji kunya
bare ni”.
Ta ce, "Lissafo su".
Ya ba da nutsuwarsa gabadaya a kanta.
"Kin ga na farko kina da matsalar yawan
korafi, wanda kin sani ba na son haka amma
kullum bakinki ba ya hutawa. Sannan ga ki
kazama ke kanki kin san ba Kazafi na yi mi"
ni ba?"
Ta katse shi cikin jin haushi.
"Idan ni Kazama ce to ba sai ka rabu da
Ya ce, "Ai na so yin hakan da ki ka kasa
gyarawa, amma da na tuna Manzo (S.A.W) bai
yi mana umarni da yawan saki ba shi ya sa na
kyale ki. Kullum