ina ganin za ki gyara wannan
matsalar shi ya sa na ke zaune da ke".
b つ
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
"Malam! Kawai kana son labewa da
guzuma ne ka harbi karsana, ka rasahujjar da za.
ka kafa gudun kada a maimaita sababben sunan
naka na AURI-SAKI shi ya sa... To ina yi maka
albishiri wannan karon ba 'yar iskar yarinyar da
ta isa ta shigo gidan nan ta raina min hankali...
a bar ni ma da zafin rashin ganin kwaina a
duniya ba za a yi ba, sai an kawo min annoba".
Ya dinga murmushi jin ta hau sama, ita
kuma abin da ya kular da ita ke nan, ta ce.
"Sannan maganar tafiyarka Lagos, na ji
kana cewa wai a nan za ka bar ni. Ban gane
wannan wankan kura da sabulun ba?"
Ya ce, "Asiya matsala! Asiya mita!
Asiya korafi! Ni yanzu na zauna don na huta a
cikin gidana amma kin hana ni".
Cikin tsiwa ta ce.
"Ai kai ne ba ka so hutawar ba. A bugi
kuturu a hana shi zuciya?"
Ya ce, "To yanzu me ki ke so a yi?"
Та се, "Ка fi ni sani!"
Ya yi dariya yana gyada yatsa.
"Hmn, aure dai babu fashi in Allah ya
53
SADAUKARWA-2 Mummyn Faangh
711
ha
S
ke
an
ka
A
ka
:
ka
111
3S
ki
di
la
bi
yarda. Lagos kuma ni kadai zan je idan kin ji za
ki iya zama a nan ki zauna, idan ba za ki iya ba
ki yi duk abin da za ki yi".
Ta ce, "Kana nufin ko tafiya gidanmu na
yi ba damuwarka ba се?"
Ya zakuda kafada cikin tabbatarwa.
"Kwarai kuwa, don na fita hakkinki. Don
zan tafi Lagos wajen aiki saboda ni ne lalle
sarkin aure sai na ce sai na tafi da ke?"
Ta mike tsaye tana sobare baki.
"Da ma na sani ba sona ka ke ba, bakin
zalunci ne ya hana ka sauwake min..."
Ta kai kofa za ta fita ya daka mata tsawa
ransa a matukar Gace, dole ta ja ta tsaya.
Ya ce, "Idan kina cin kasa ki kiyayi ta
shuri Asiya, bari ganin ina biye miki za ki raina
min hankali. Ki fada min kin gaji da zama ki
gani idan ban sauwake miki ba, sakaryar banza
kawai, ana hakurin zama da ke amma sai kin
kai mutum bango? Bace min da gani".
Ya Karashe cikin hasala.
Ta wuce dakinta tana jin takaici a ranta,
wannan danniya ce kawai a ke nuna mata, sarai
54
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
4
ya sani zaman hakuri ta ke da shi. amma bai
duba hakan. bai nuna mata kulawar da kowace
mace ke muradi a gidan aurenta, ta yi hakuri ta
zauna da shi a hakan amma zai dinga gasa mata
maganganu yadda ya ga dama?
Kudinsa ne ya sa ta'ke zaune da shi har
kawo wa yanzu, ba don haka ba da a yau za ta
nemi takardarta ko ita ma ta je ta haihu a wani
gurin kamar yadda ta samu labarin Hajiya
Suwaiba ta haihu a inda ta yi aure.
Bayan fitarta ya ja wayarsa ya lalubo
lambar Alhaji Mande. ya kira ringin biyu va
dauka: Suka gaisa. sannan ya cc.
"Alhaji Mande, game da maganar
yarinyar nan ne. Ina fatan ka samu zama da
mahaifin nata?"
Alhaji Mande ya ce, "E, jiya na je na
same shi. Amma an samu matsala, domin
bayanin da ya yi min a cikin satin nan ya karbi
bakuncin wani yaro da ke sonta, har ya ba shi
aurenta"
Alhaji Atiku ya ji maganar kamar saukar
mashi a zuciyarsa. Da sauri ya ce.
55
ce.
SADAUKARWA-2
"Subhanallahi".
Mummyn Faanah
Alhaji Mande ya kwantar da murya, ya
"Wallahi abin babu dadin ji, ga shi na
san shi mutum ne kaifi daya, ba don haka ba da
יי
mun bi ta wata hanyar..."
ya ce.
Alhaji Atiku cikin bayyanar da dauriya
"Kada ka samu damuwa, Allah ya sa
haka shi ya fi zama alkhairi, amina kwarai na
so auren yarinyar nan saboda na hangi alkhairai
da yawa a tare da ita. Kuma tun ranar da na fara
ganinta na ke istihara a kanta, alkhairin dai na
gani".
Alhaji Mande ya ce, "Ai ko yanzu ba
fidda rai za mu yi ba, domin ba a aurar da ita
ba. Addu'a za a dage yi idan da rabon aure a
tsakaninku sai ka ga Allah ya tabbatar".
Alhaji Atiku ya ce, "Na gode, gobc idan
Allah ya kai mu zan yi fakin Lagos din fa".
Alhaji Mande ya de, "Tow! Ashe tafiyar
har ta zo? Allah ya sa alkhairi, Ya sa kana
dawowa a ba ka damar yin ritayar
56
SADAUKARWA 2 Mummyn Faanah
Alhaji- Atiku ya yi murmushi, ya cc.
"Amin dai".
Ya kashe wayar damuwa ta dabaibaye
shi, tun ranar da ya soma ganin Fadima ya
kasancecikin fata da burin ta zamo matar
aurensa, saboda a kallon da ya yi mata ya
hango abubuwan da ya rasa a sauran matan da
ya aura. Yanzu shi ke nan ya ga samu ya ga
rashi? nes
Har dare yana cikin wannan yanayi,
Hafiz ya same shi a harabar gidan suna magana
da maigadi. Alhaji Atiku ya dubi Hafiz cikin
damuwa. ya сe.
"Yauwa Hafizu, ka kai masa sakon?"
Hafiz ya ce, "E, na kai. Amma ban tarar
da shi ba sai da na jira shi ya dawo. Ya ce a yi
maka godiya, Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya. foskod
Alhaji Atiku ya ce, "Amin... don Allah a
shirya min mota don da wuri zan tafi". s
Hafiz yana sosa kai ya се.
"To Abba, kuma..."
Sai ya yi shiru.
57
SADAUKARWA-2
cikin gidan, ya ce.
Mummyn Faanoh
Alhaji Atiku ya senm aaku don nuf
"Kuma me? Zo mu jesesciki ka fada min",
Suka karasa cikin falonAlhaji Atiku ya
zauna a kan kujera, yayin da shikuma ya zauna
a kan kafet kansa a kasa.
"Ina saurarenka"
Cikin sanyin murya ya се.
"Da ma cewa na yr no yi zaton kafin ka
tafi za a tura gidan su Fadima
Alhaji Atiku ya ji gahonse ya fadi saboda
tunowa da ya vi da tasa usalar. ya dan kafe
Hafiz da ido, ya ces
"Sun bukaci hakan ne?"
r.Hafiz ya ce, "A'a, gani na yi daí ya daçe
a tura din ba sai sun nema ba". Ee dz se
Alhaji Atiku ya ce, "To shi ko nan.
Lokaci ya kure min, amma zan wakilta Alhaji
Umar ya bincika min nasabar yarinyar kafin a
.tura وو
Hafiz ya yi mamaki kwarai, don ya san
wancan lokacin tare da Alhajin a ka je Katsina
gidan su Rufa'atu neman aurensa, kodayake
58
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
yanzu bai kamata ya yi mamaki ba idan ya yi
la'akari da Alhajin zai tafi Lagos ne, kuma
babu lokaci saboda aiki ko ya dawo ba zai
wuce hutun karshen mako ba, sai dai duk da
haka ya yi tunanin zai ce sai ya dawo din zai
bincika da kansa.
Alhaji Atiku ya katse masa tunani da
fadin.
"Na so a ce ni zan yi wannan binciken,
domin ina son ka auri 'yar gidan kwarai, 'yar
manyan mutane da suka san mutuncin kansu da
wanda ya rabe su, amma yanayin tafiyar da zan
vi dole zan wakilta Alhaji Umar din..."
Hafiz ya tare shi cikin girmamawa.
"To Abba, ko dai a bari sai ka dawo?"
Da sauri Alhaji Atiku ya girgiza kai.
"A'a. Kada ka damu, na san insha Allah
yadda zan yi binciken shi ma zai iya. Allah dai
ya sa a dace da wadda a ke nema".
Murya kasa-Kasa Hafiz ya ce, "Amin”. Alhaji Atiku ya ce, "Sai ka je ka same shi
ka yi masa bayanin gidan nasu".
Yadda ya yi maganar kamar cikin 6acin
59
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
rai ya daga wa Hafiz hankali, sai ya ga kamar
ya yi masa abin da bai dace ba, wato rashin
alkunya! Har ga Allah bai yi masa maganar don
rashin kunya ba, illa kosawa da ya yi Fadima ta
shigo gidansa, yana tsoron jinkirin ya haifar da
rashi kamar yadda ya rasa Rufa'atu. Cikin
sanyin murya da rashin kuzari ya се.
"Don Allah ka yi hakuri Abba idan na
ata maka rai".
Alhaji Atiku ya yi murmushin yake.
"Me ka gani?"
Hafiz ya ce; "Na ga kamar ranka ya
Басі".
Alhaji Atiku ya girgiza kai ya ce.
"Ko daya Hafizu, ba ka fata min rai ba.
Ai ni babban farin cikina na ga ka yi aure.
Wallahi ba zan iya fasalta maka murna ta a kan
wannan lamarin ba... kaina ne kawai ke ciwo
shi ya sa ka gan ni haka".
Hafiz ya yarda da abin da mahaifin nasa
ya fada, saboda ya sanshi da fadar gaskiya.
Duk abin da Hafiz ya yi masa cikin kuskure ko
rashin sani kai tsaye ya ke zaunar da shi ya
60
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
nusar da shi. Sai ya yarda ciwon kan ne ya
sauya shi haka, ya ce.
"To Allah ya ba da lafiya
Alhaji Atiku ya ce, "Amin"
Ya mike tsaye alamar yana son Hafiz din
ya ba shi guri. Fahintar hakan da ya yi ya sa tun
kafin Alhajin ya soma taku ya yi saurin mikewa
ya ce.
"Bari na fara shirya kayan"
Alhaji Atiku ya ce, "Ba laifi".
Don kada Hafiz ya gane korarsa ya yi sai
ya nufi dakinsa.
Hafiz yana cikin shirva kayan mahaifin
nasa wayarsa ta yi kara. Ya ciro ta daga aljihu
ya ga sabuwar lambar Rufa'atu ce wadda
yawan turo sakon da ta ke masa ya sa dole ya
adana ta a cikin jerin lambobin da ke kan
wayarsa. Yana kallon wayar yana tunanin ya
dauka ko kada ya dauka, har kiran ya katse.
Yana kokarin mayar da ita aljihu wani
kiran ya sake shigowa, ya danna malatsin
amsawa, sannan ya kara a kunne tare da yin
sallama. Ba a amsa masa ba illa shesshekar
61
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
kukanta da ya jiyo. Hankalinsa ya yi matukar
tashi, komai ya kunce masá, nan da nan ya
kidime yа се.
"Don girman Allah ki daina kukan nan
haka, wallahi kina daga min hankali. Ya
kamata mu yi hakuri mu mika wa Ubangiji
lamarinmu".
Ya dan saurara don jin ko za ta ce wani
abu, amma ba ta ce din ba, ba ta kuma daina
shesshekar kukan ba. Ya buda baki zai yi
magana ta ji ta kashe wayar. Rufa'atu tana da
babban matsayi a rayuwarsa. ba ya iya tsallake
uzurinta. don haka a take va bi ta da nasa kiran.
Tana ta kara wayar ba a daga ba, ya kira
ya fi sau hudu ba amsa. Ransa ya baci, yana
mamakin halinta, ta kasa hakuri da shi, idan ya
kira ta kuma ba ta daga wayarsa, ta ya zai
shawo kanta? Ya ja tsaki ya mayar da wayar
cikin aljihu ya ci gaba da aikinsa. Yana jin
Karar, wayar tasa alamar shigowar sako ya yi
biris, don ya san daga Rufa'atun ne.
Sai da ya kammala komai ya shiga
dakinsa, ya sauya kayan bacci ya zauna a gefen
62
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
gadonsa, ya janyo wayar ya duba. Lambar ce
dai tata, kamar ba zai karanta ba sai kuma ya
daure ya soma karantawa.
'Na rasa yadda zan sanar da kai son da
na ke maka Hafiz da ke tafiya a duk wata gaba
da ke jikina. Ka yi hakuri ka daina damuwa da
damuwata, domin na san ni kaina ban yi wa
rayuwata adalci ba da na kasa cire ka a raina.
Ka yi hakuri! Ka yi hakuri!! Ni na san sonka
shi ne ajalina! Don Allah ka yi min addu'a
Allah ya sa na yi kyakkyawan karshe, don ina ji
a jikina kamar ni ba mai sa'a ba ce a duniya!"
Ya ji zuciyarsa ta karye matuka, tsananin
tausayinta ya lugwigwita masa zuciya, ya kasa
jurewa sai da ya mayar mata da martani.
'Ko ba ki fasalta min a fatar baki ba na
sani kina sona matuka. Kuma ni ma din ina
sonki fiye da yadda ki ke tsammani, sai dai
shamakin da ya gilma a tsakaninmu shi za ти
dinga hanga. Kada ki damu, dole ne damuwarki
63
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
ta dame ni don idan na ce ban damu da
damuwarki ba, ban yi wa so adalci ba Insha
Allah sona ba zai zamo ajalinki ba, ke dai ki
dage addu'a Allah ya kawo mana mafita'.
Ya tura sakon tare da tsura wa wayar
idanu kamar ita ce a gabansa, dole ne ya samu
lokaci ya je Katsina duk da shamakin da ke
tsakaninsu, to amma ba soyayya ce za ta kai shi
ba ballantana a ce ya tsallake umarnin mahaifin
nasa. Yana cikin wannan hali ta sake turo masa
sakon.
'Hafiz, ba ka gane abin da na ke nufi ba!
Ba za ka gamsu da uzurina ba a lokacin da na
bayyana maka sirrin zuciyata, wannan shi ke
damuna da sa ni fargaba. Wallahi na sadaukar
da raina a kanka, don gabadaya rayuwata babu
wani da namiji da na ke so da Kauna, na ke
kuma fatan ya zamo mijina sai kai. Na sani duk
namijin da zan aura bayan kai sai dai na yi
biyayya, amma ni da shi za mu takura, don ba
zan taba dubansa a matsayin masoyi ba, sai
64
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
wanda ya yi soyayya ta karan tsaye'.
Ya dauke idanunsa daga kan wayar, abin
da ba ya so na son tabbatuwa, wato ya sauya
layin waya a dalilinta, ya kwana da wannan
kudiri. Sai dai kafin safe komai ya subuce masa
na son sauya layin, musamman dogon nazarin
da ya yi, idan har ya sauya layin bai zama lallai
ya samu lambobin wasu mutanen da suke
mu'amala ba. Bayan haka lambar tasa da ita ya
ke amfani ga wadanda ya ke koya wa ilimin
na'ura mai kwalwa. wanda tana like a takardar
shaidar karbar dalibi "(form), don haka ya
hakura kawai, zai ci gaba da amfani da layin,
amma zai yi kokarin isa Katsina a dan tsukin
kafin Abbansa ya dawo daga Lagos.
Lokacin da ya fito falon gidan, ya tarar
da mahaifinsa ya gama karin kumallonsa,
Hajiya Asiya na zaune cikin tattara fuska da
Kawatata da tsantsar damuwa. Haka ta kwana
jiya cikin kunci tana, ganin mijin nata mara
adalci, don a ganinta ya daina sonta shi ya sa ya
ke mata kora da hali.
65
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
Hafiz ya gaishe ta bayan sun gama
gaisawa da mahaifinsa, ta amsa masa ba yabo
ba fallasa, sannan ya dawo da dubansa ga
Alhaji Atiku yana fadin.
"Abba, yanzu za ka tafi ko sai anjima?"
Alhaji Atiku ya ce.
"Yanzu zan tafi, da ma kai na ke jira ka
fito".
Ya ce, "To, ina waje ina jiranka"
Ya fito zuwa harabar gidan ya barsu
zaune don su yi sallama a nutse. Cikin kwantar
da murya Alhaji Atiku ya ce.
"Asiya. don Allab ki kwantar da
hankalinki, wannan tafiyar fa ba wadda ya
kamata mu rabu a haka ba ne, idan ki ka yi
la'akari da tsayin kwanakin wata daya zan yi
kafin na dawo hutu. a kalla muna bukatar
rabuwa cikin salama don ba mu sani ba ko
rabuwar ke nan"
Ta ce, "Ni ba tafiyarka ce ta dame ni ba,
maganar aurenka ita ta dame ni
Ya yi murmushi yana duba agogon
hannunsa, ya ce.
66
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
"Lokaci ya kure ballantana na tsaya mu
yi wannan maganar, sai dai ina tunatar da ke,
tun can baya ba ke kadai ce a gidan nan ba, ya
kamata yanzu ma ki kwana da sanin zan iya
kara aure koyaushe".
Ta tattaro wani korafin, amma kafin ta
samu damar saukewa ya rigata magantuwa
bayan ya mike tsaye.
"Don Allah a bar maganar nan, ki yi
mana addu'ar sauka lafiya. Duk abin da ki ke
bukata na sauke miki shi, bayan haka ga Hafiz
nan ko da akwai wata bukatar a uzurce.
Ta kyabe baki, murya a cushe ta се.
"Allah ya kiyaye hanya".
Bai damu da rashin rakiyarta ba ya fice,
ya tarar da Hafiz yana jiransa.
*** *** ***
Larab ya dago kai ya dubi Hafiz ya ce.
"Malam, ni fa ba hirar Fadima ta kawo ni
gurinka ba, za ka wani dame ni da zancenta. Na
zo ne musamman don sayen form".
Hafiz ya yi murmushi, ya ce.
67
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
"To na ji, wa zai yi training ne?"
Kai tsaye Larab ya amsa masa.
"Kanwarka Bintu, wai tana son koyon
na'ura mai kwalwa".
Hafiz ya gyada kai, ya ce.
"E, hakan yana da kyau, ta warware ke
nan?"
Larab ya се, "Е".
Hafiz ya ce, "To, ai ba sai ka saya ba.
Tunda kanwa guda ce ai ko bude kwalwarta sai
a yi a zuba mata".
Su duka suka yi dariya, Hafiz ya dora da
fadin.
"Koyaushe ta shirya zta zo za ta zama
cikakkiyar daliba".
Larab ya ce, "Ai ita a shirya ta ke, ko
yanzu a ka ba ta umarni da gudu za ta zo. Hmn
yadda Bintu ke son karatun nan, ina jin ko
lokacin da ta samu gurbin karatun sakandire ba
ta yi dokinsa ba".
Hafiz ya yi murmushi, ya ce.
"Ai karatun kwamfita dadi gare shi...
yaushe za ka raka ni Katsina?"
68
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
"Ai karatun kwamfita dadi gare shi...
yaushe za ka raka ni Katsina?"
Ya jefo masa wannan tambayar gatsal,
Larab ya yamutsa fuska, ya ce.
"Katsina? Me kuma za ka yo?"
Hafiz ya ce, "Zan je wajen Rufa'atu ne,
wato tun rabuwarmu har zuwa yanzu fa ta kasa
kwantar da hankalinta, koyaushe cikin turo min
sakonni ta ke, wai ba za ta iya rabuwa da ni ba,
shi ne na ke son zuwa".
Larab ya yi shiru na wani lokaci, kafin
daga bisani ya girgiza kai ya ce.
"Kada ka yi wannan gangancin Hafiz, ka
bi umarnin mahaifinka ka rabu da sha'anin
Rufa'atu..."
Hafiz ya tare shi da fadin.
"Wallahi na hakura da ita, kawai ina son
dai na je na kara kwantar mata da hankali ne,
don ba na so a dalilina ta shiga wani hali, ka
san mata rauni ne da su musamman a sha'anin
soyayya".
Larab ya ce, "Ka san Allah ka rufa wa
kanka asiri, duk halin da Rufa'atu za ta shiga
69
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
bai kai naka ba don na tabbata ba karamin
6acin rai mahaifinka zai yi ba idan ya samu
labarin ka bijire wa umarminsa ka je gurin
Rufa'atu, ka yi mata addu'a da kuma ci gaba da
kwatanta mata muhimmancin yarda da
Kaddara".
Hafiz ya yarfa hannaye ya ce.
"Ai inda matsalar ta ke ba ta daukar
wayata, idan ma ta dauka ba ta ce min komai
sai kuka. Ni kuma abin da ya ke ci mini rai ke
nan, shi ya sa na yanke hukuncin zuwa can
Katsinan"
Larab ya yi shiru na wani lokaci.
"Ka yi hakuri Hafiz, ni dai ba na ba ka
goyon bayan zuwa Katsinan nan, sai dai zan yi
maka addu'ar Allah ya kai ka lafiya ya dawo da
kai lafiya. Daga karshe ina tunasar da kai,
mahaifa ba ababen wasa ba ne, umarninsu
muddin bai shiga shingen shari'a ba binsa ya
zamo lazim, ballantana ga bayanin da
mahaifinka ya yi maka game da nasabarta.
Wallahi ka gode wa Allah da ka samu uba mai
sonka da zai guje maka auren macen da za ka
70
SADAUKARWA-2
dawo kana nadama".
Mummyn Faanah
Sam bai ji zafin maganganun Larab ba,
bai kuma ji haushin rashin samun rakiyarsa ba,
haka suka rabu yana ayyana wa a ransa zuwan
shi ne mafi a'ala, domin ko daren jiya ta kira
shi tana kukan, ta kuma turo masa sakon tana
cikin wani hali na kunci a dalilin kaunar da ta
ke masa. A lokacin sun yi musayar sakonni,
amma yadda ya lura ta yi zurfin da zuwan nasa
Katsina ne kadai zai rage mata radadi.
A bangare daya kuma ga lamarin Fadima
da ya tunkaro shi gadan-gadan, tun bayan
zuwan Alhaji Umar gidan su Fadimanya dawo
da fadin dumbin karamcin mahaifinta, wanda
kai tsaye Malam Abdullahi ya ce ba ya bukatar
komai daga gare su illa sadaki, kuma idan yau
sun shirya ma su zo a daura aure, don da ma
koyaushe cikin jiran aurar da Fadiman ya ke.
Tun ranar da a ka yi hakan a ka dakatar
da Fadima zuwa daukar karatun, amma dai
yana samun damar ganinta idan ya je gidan. Abin da ya sa shi damuwa shi ne, da a ka sanar
wa Alhaji Atiku abin da suka ce, kai tsaye ya ce
71
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
a jira shi dai, ba za a yi gaggawa ba. A ganin
Hafiz kamar jinkitin ba zai yi fa'ida ba, tunda
sun nuna halin dattako bai kamata a jinkirta ba
nidan dai su ma suna son su dauke su manyan
smutanevil ns ok ni
gtsi noKamar yadda Alhaji Atikun ya sanar da
shitzai dawo bayan wata daya, yau saura mako
daya, don haka ya ke cikin zumudin dawowar
tasa don cikar burinsa, sai kuma ga sha'anin
Rufa'atu da ya ke hauhawa farashi a zuciyarsa,
ba dai yana son dawo da bara bana ba, ko nuna
karfi ya kwato soyayyar da ya ke ganin an yi
wa karan-tsaye ba, illa tausayin halin da ta ke
ciki a dalilinsa, wanda ya ke ganin shamakin da
a ka shata musu ya yi tsauri, akalla dai a barsu
su dinga haduwa har Allah ya zaba mata miji.
sm sb Bayan barin Larab ofis din nasa ya dade
cikin saka da warwara, a wani bigiren yana
tauna bayanan Larab a mahangar hankali da
kyautuwar a yi amfani da su don kore wancan
tarnakin, sai dai raunin da dayan bigiren ya ke
da shisyana sa shi rudani, har ya ji kamar yana
ci gaba da zalunci ne! Tun kusan wata daya da
721
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
lokacin ba, sai don bai san dalili ba.
Bayan ya tashi daga aiki ya koma gida ya
yi wanka ya dauki hanyar gidan su Fadima
kamar yadda ya saba duk bayan kwanaki biyu
ya kan jc. Yana isa kofar gidan ya tarar da abin
da ya kada hankalinsa., Fadima ce a ka fito da
ita ranga-ranga cikin halin fita hayyaci, gefe ga
mai tasi ya bude kofa yana jiran a sakata.
Hankalin Hafiz ya yi kololuwar tashi, da
sauri ya fito daga mota ya tunkari Malam
Abdullahi da ya ke ba da umarnin a saka ta a
: ciki, ya cе.
ne.
"Malam lafiya?
Malam Abdullahi ya ce, "Ba ta jin dadi
Hafiz ya ce, "To ku shiga motata mana".
Kafin ma Malam Abdullahin ya yi wata
magana tuni Hafiz ya isa ga mai tasin ya ba shi
dari biyar, sannan ya hanzarta bude wa su Inna
Baida'u motarsa, a ka sa Fadima a ciki, Malam
Abdullahi ya shiga motar suka nufi asibiti.
A kan hanyarsu ta tafiyar ne Hafiz ya ke
tambayar ba'asin rashin lafiyar tata. A dunkule
73
SADAUKARWA-2
Malam Abdullahi ya сс.
Mummyn Faanah
"Kada ka samu damuwa, da ma tana yin
haka duk karshen lokacinta, sai dai na yanzu ne
ya yi muni".
Sam Hafiz bai gane abin da ya ke nufi
ba, amma ba ya son tsawaita magana a
tsakaninsa da surukin nasa saboda kunya.
Sai da Karin suka isa asibitin ya samu
bayanin, duk lokacin da za ta yi al'ada tana
shan wuya. Tausayinta ya kama shi ainun.
An ba ta gado saboda ta sha wahala sosai
a wannan karon. Hafiz ya dinga zarya tsakanin
harabar asibitin saboda an yi mata allura ta
samu bacci. Yadda ya kidime ya rasa
kwanciyar hankali ya sa Malam Abdullahi ya
gamsu lallai ba karamin so Hafiz ya ke yi wa
gudan jininsa ba.
Har magriba ba shi da niyyar barin
asibitin, sai da Malam Abdullahi ya ji
tausayinsa sosai ya сe.
"Malam Hafizu, ya kamata ka tafi haka
nan, na san kana da sabgogi, ga shi sun yi mata
allura muna sa ran zuwa anjima idan ta farka su
74
SADAUKARWA-2
sallame mu
Mummyn Faanah
Kansa a kasa cikin girmamawa ya ce. "Ko da ta farkan a yi hakuri ta kwana
Malam, za ta fi samun sauki"
Malam Abdullahi ya ce, "E, ai dama ba
mu za mu nemi sallamar ba, sai yadda jikin ya
bayar. Kada ka damu, Bintu za ta tashi da
yardar Allah".
Hafiz ya ce, "Allah ya sa"
Kai tsaye ofishin likita ya nufa ya yi
masa bayanin ko da Fatima ta farka kada ya ba
su sallama. ya barta ta kwana a asibitin. sannan
daga bisani ya tambayi likitan wại dole ne duk
lokacin da za ta yi al'ada sai ta yi wannan
ciwon ba wani tallafi da za a yi mata don
rigakafi? Likitan ya ce.
"Akwai tallafin mana. idan za a aurar da
ita, namiji ya kusance ta ai abin zai zo da sauki.
Akwai irin nau'in mata da suke kasancewa a
haka yayin al'adarsu, da zarar an yi musu aure
suna samun sauki".
Ya bar asibitin da wannan maganar ta
likita, wato idan a ka aurar da Fadima ana da
75
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
yakinin za ta tsira da wannan wahalar? Idan
haka ne lallai ya kyautu a gaggauta yin aurensu.
don ba zai iya jure ganinta cikin wannan azabar
ciwon ba.
Báyan an sallaci isha'i wajen tara saura,
ya sake komawa asibitin ya tarar ta farko,
ruwan da a ka sa mata saura kadan ya kare. Ya
dan zauna ana jimamin da shi, sannan Karfe
goma ya bar asibitin.
Rashin lafiyar Fadima shi ya dauke masa
hankalin zuwa Katsina, musamman da ya
kasance a kwanaki ukun ba tà turo masa sakon
da zai iva tunawa da shä'aninia ba.
An sallami Fadima daga asibitin a
washegarin da a ka kawo ta, ba laifi ta dawo
hayyacinta, sai dai kana kallon fuskarta ka san
ka ga mara lafiya. A kullum Hafiz ya zo gidan
sau biyu ko sau uku, ban da kiran wayar Isma'il
da ya kan yi don jin yanayin lafiyarta. Ita kanta
Fadiman ta yarda da ba karamin so Hafiz ya ke
yi mata ba, duba da yadda hankalinsa ya tashi
game da rashin lafiyarta, barin ma irin
dawainiyar da ya ke yi musu, duk zuwan da zai
76
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
yi sai ya shigo mata da ‘ya'yan itatuwa, wani
abin ma sai a dalilinsa ta taba cinsa, misali inibi
da suturo beri.
Yana zaune a ofishinsa cike da nishadi
saboda wayar da ya ke yi da Fadima ta wayar
yayanta Isma'il suna more hirarsu cikin shauki
da kaunar juna.
A hankali a ka kwankwasa kofar, ba tare
da ya damu da ko waye ba ya ba da umarnin a
shigo, bai sauke wayar daga kunnensa ba.
Bintu ce ta shigo sanye da yaluwar
atamfa ta sha kwalliyarta mai kayatarwa, komai
iri daya (too much) ta saka kalar ja da fari, sai
shigar ta kayatar da ma abu ga fara sol.
Ya yi mata nuni da yatsa ta zauna kujerar
da ke gabansa, yana ci gaba da cewa a wayar.
"Allah ba ni da wani burin da ya wuce na
faranta miki, don haka kada ki damu da duk
wata hidima da zan yi a gare ki. Ba na duban
hakan a matsayin takuwara illa fita hakkinki a
matsayinki na wadda za ta maye min guraban
da ke tattare a zuciyata da ma rayuwar
gabadaya".
77
SADAUKARWA-2 Mummyn Faánah
Ya tsagaita da maganar da alama raddi
ya ke saurare, yadda fuškarsa ta sake washewa
da murmushi alama ce ta yana jin dadin abin da
à ke fada masa. Bintu ta ci gaba da zuba masa
idanu, yayin da ya fora da fadin!
"Hmn, Fadima ke nan, ke dai Allah ya
raya min ke mu yi tsawon rai, kuma Ya kai mu
ranar aurenmu...
Bayan ya yi shiru na wani lokaci, sannan
ya ce.
"To shi ke nan, sai na sake kiray amma fa
ki kula. kin san tukin tiwo akwai wahala"
Ya sa dariya tare dà kashe wayar ya
dawo daodubansa ga Bintu wadda ya ga
yanayinta babu walwala, koyaushe ya ganta
cikin yanayin damuwa tausayinta kan kama shi,
ya san zafin so