musamman irin nata na SON
MASO WANIDY ana tausaya mata yadda ta ke
cikin komar makauniyar soyayya da ba a sani
ba za a haife ta da rai ko matacciya ce? Ya dan
yi murmushi, ya ce.
"Kanwas; ya dai?HS CL
Ba tare da ta saki fuska ba ta tura masa
78
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
takardun da ke hannunta a gabansa, ta cc.
"Da ma assignment din da ka ba ni jiya
ne na shigo kawo maka".
Sai ya ji ba dadi a ransa, yadda ta yi
masa maganar. Ya sa hannu ya dauki
zungureriyar takardar yana magana cikin sigar
zolaya.
"Da kyau kanwas, himma ba ta ga raggo!
Haka na ke son falibi da maida han..."
Bai Karasa maganarsa ba ganin ta mike
ta soma tafiya, ya ce.
"Ah! Saurin me ki ke yi ne haka?"?
A takaice ta amsa masa da cewa.
"Zan koma gida, Umma za ta
unguwa".
je
Ya dago kai ya dube ta sosai, tare da
dora hannayensa a saman tebur ya ce.
"Ga shi yau ina son mu tattauna wasu
muhimman maganganu game da lamarin
bikina, ya ke nan?"
Ba tare da ta juyo ba ta ce.
"Kada ka damu, za mu tattauna idan an
samu lokaci".
79
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
Ya lura tana cikin damuwa, watakila
masoyin nata ne ya hado mata zafi. don haka
sai ya kyale ta, ya се.
"Shi ke nan, ki gaishe min da Umman.
kwana biyu ma ban je na gaishe ta ba.
Karashe maganarsa Karashewar ficewar
Bintu daga ofishin nasa. Ya yi zugum cike' da
nazari, wace irin yarinya ce Bintu da ta dauki
rayuwa da zafi haka?
Ya jima yana nazarinta kafin daga bisani
ya soma duba aikin da ya ba ta. Kokarin Bintu
na kayatar da shi. da a ce ba ta da damuwa da ta
fi gaka hazaka.
Da yammaci ya kai gyaran motarsa da ta
ke dan ba shi matsala, yana tsaye ana gyaran,
wayarsa ta yi kara kafin ya ciro ta daga aljihu
kiran ya katse, don haka sai bai bi ta kanta ba,
ya ci gaba da kallon bakaniken. Zuwa can
kuma ya ji kara alamar sako ya shigo wayar.
Wannan dole ya duba don ya san sakon ba zai
wuce daga Rufa'atu ba. Cikin nutsuwa ya ciro
wayar.
"Yar halak!" Ya ambata a ransa lokacin
80
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
da ya tabbatar da ita din ce a sabuwar lambarta.
Murmushi ya soma yi kafin ya soma karanta
abin da sakon ya kunsa kamar haka:-
'Da zan iya da na tsaga kirjina na cire
soyayyarka a raina ko na huta da azabar da na
ke sha. Amma sai dai kash na makara, ba ni da
jaruntar da zan yi amfani da karfi na tsaga
kirjin nawa, watakila rashin tabbaci ne da na ke
da shi idan na tsaga Kirjin zan iya cire soyayyar
ko ba zan iya ba, shin a kirjin ma kadai
sovavyar ta ke da muhalli ko a gabadava
gangar jikina ce? Amma dai tabbas Kokari yana
bude kofar da ke rufe, don haka zan yi wani
yunkuri ko da zan kusanta da kushewa, kai da
mutanen duniya ku tabbatar an taba yin wata
mahaukaciya a soyayya, ko na ce mai yin
mataccen so a rayuwarta'.
Iyakar nan sakon ya tsaya. Matukar
damuwa Hafiz ya shige ta, shin wane yunkuri
Rufa'atu ke son yi? Ta shiga duniya ko ta kashe
kanta duk a kan soyayya? Lallai cikin biyu
81
SADAUKARWA-2 Múmmyn Faanah
daya zai iya faruwa idanthaka ne mene ne abin
yi? Yaushé zá tá yi yunkurin? Yanzu? Anjima?
Gobe? Ko har ma ta yi-bayan tà turo da sakon?
Ya fan ja tsaki, a sarari ya furta.
Soyayya mä ba ta yi ba à rayüwa".
Daidai kunnen danfulanin bakaniken da
ke fama da sifanu, ya yi murimüshi ya cc. sde
"Yahaj, ai kuwa soyayya ta yi sošaina
rayuwa".
SKHafiz ya dan kafe shi da idanu yayin da
bakaniken ya bude bakin famfon koro jawabi. o
"Yahaj. soyayya fa ita ce jigon zamän.
lafiya isakanin alumm. kowace arin al ng
kuwa. Da soyayya ake Raunar juna har ayi aure
a zauna lafiya. Da soyayya a ke kulla abota Da
133 ...soyayya ل
Hafiz-ya katse shi lura da ya yi, watakila
bakaniken yana cikin inuwar yan ga-ni-kashenin soyayya, ya ce.
Ni ma ai ba zagin soyayya na yi ba,
cewa na yi ba ta yi ba a rayuwa". aDH awrn
Bakaniken ya bangare da dariya yana
carafke da sifanu уа сe.
22
SIHE
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
Bakaniken ya bangare da dariya yana
carafke da sifanu ya cе.
"Ai Yahaj kanin zagin soyayyar ka yi".
Hafiz ya yi tunanin da alama zai iya
samun wata shawara daga bakaniken, tunda ya
yi zurfi a kare hakkin soyayya, don haka ya ce.
"Yauwa to, tunda na lura kana kare
hakkin soyayya, ko za ka taimake ni da
shawara?"
Yahaj".
Bakaniken ya ce, "To, ina saurarenka
Hafiz ya mirgina kai da fadin.
"Misali, budurwa ce na ke so ta ke sona,
sai wani shamaki ya ratsa tsakaninmu da ba za
mu iya aure ba, ta bangaren kin amincewa daga
magabatanmu. To sai budurwar ta ci alwaşhi
idan ban aure ta ba, za ta kashe kanta ko ta
shiga duniya, a shawarce ta wace hanya zan bi
na rabu da ita lafiya ba tare da ta aikata abu
daya cikin biyun ba?"
Shiru bakaniken ya fara yi, hatta da aikin
da ya ke a gaban motar sai da ya dakata, da
alama yana zanta abin da zai fada wa Hafiz ne
83
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
a zuciyarsa. Zuwa can ya yi dan malalacin
murmushi, ya ce.
"E to, a hakikanin gaskiya idan ni ne kai
hanyoyi biyu zan bi. Hanya ta farko, zan iya ce.
mata zan aure ta domin na samu ta dakatar da
aikata wa kanta daya daga cikin biyun da ta ke
yunkurin aikawata. Inyaso sai na dinga janue
jikina daga gare ta, na yi kokarin cusa mata
tsanata a zuciyarta, ta yadda za ta ji ba ta
sha'awar aurena sam. Ko kuma na bi hanya ta
biyu, wato na ce mata mu je a yi gwajin jini,
idan har ya kasance ni da ita babu mai dauke da
wasu kwayoyin cuta to za mu yi aure. Ka san
hikimar yin hakan?"
Yadda kalaman bakaniken suke ratsá
zuciyar Hafiz, hakan ya sa shi zakwadin son jin
karashen fatawar tasa, don haka da sauri ya
girgiza kai. Bakaniken yana dan murmushi ya
се.
"Hikimar ba ta wuce ta za a dasa wa
budurwar zargi a zuciyarta ba, ta yi tunanin ko
da ma kana bibiyar wasu matan banza ne,
watakila kana dauke da kwayar cutar kanjamau
84
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
ma ka rasa hanyar da za ka bayyana mata, shi
ya sa ka 6illo mata da hakan. Ko kuma ta yi
tunanin kana zarginta da bibiyar wasu mazan.
Ka ga ke nan wasi-wasi zai shiga zuciyarta, a
hankali sai ta dinga jin sonka yana ficewa a
zuciyarta".
Hafiz ya dinga gyada kai cikin gamsuwa
da jin dadin bayanin bakaniken. Yana rufe baki
ya dora da cewa.
"Lallai matambayi ba ya bata, haka ilimi
kogi ne idan ka shige shi sai ka zama kamar
allura a cikin ruwa. Don Allah ya sunanka?""
Bakaniken ya fashe da dariya, ya сe.
"Sunana Nura Baban Soyayya".
Hafiz ya yi dariya da gyada kai, ya ce.
"Tabbas ka cancanta da sunanka. Don
Allah a ina ka koyo soyayya haka?"
Nura yana dariya har yanzu ya ce.2
"Tabdijan! Ai labarin mai tsawo ne,
amma ka sa a ranka duk fadin duniyar nan ba ni
da malami a bangaren soyayya da ya wuce
sahibar raina Naja'atu. Ita ce mafari da jigon
zamana zakwakuri a soyayya. Ai in gaya maka
85
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
Yahaj, har ranaku na ware wa masoya don
kawai su zo su kwankwadi romon
dimokaradiyyar soyayya"
Su duka suka yi dariya, Hafiz ya dora da fadin.
"Kai dai dan ban dariya ne, in ban da
haka ga abubuwa nan da yawa da suka addabi
mutane, yaushe za a tsaya daukar wani abu wai
darasin soyayya?"
Nura ya hangame baki yana kallon Hafiz
jin yana neman ya raina fasahar da ya ke
tinkaho da ita. Ya ce.
"A tunaninka soyayya ba ta cikin
abubuwa masu muhimmanci da suka damu
al'umma a wannan marrar da muke ciki? To
wallahi ba ka bi na bashin rantsuwa ka zo nan
garejin duk ranar lahadi da yammaci ka ga
yadda samari da 'yammata ke taruwa... Kai
Yahaj, soyayya fa hm!"
Murmushi Hafiz ya yi, ya ce.
"A takaice dai kana yi min tallar
makarantar soyayyarka ko?"
Daidai lokacin da Nura ya ke rufe gaban
86
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
soyayya, ina ku ina karamar makaranta irin
tamu da ba ta wuce cikin cokali ba?"
Hafiz ya ce, "Na yi digirin zan tambaye
ka abin da na tambaye ka? Yanzu ba ga shi ba
ka ba ni shawara, wanda dole a ciki zan yi
amfani da daya?"
Nura bai tsaya- sake yin wata magana ba
ya shiga cikin motar, ya tayar ya ba ta wuta,
sannan ya ja ya yi gaba. Ya je karshen garejin
ya juyo, yana fitowa ya сe.
"Yahaj, mota dai ta gama kammaluwa"
Hafiz ya ce. "Alhamdu lillahi malamin
sovayya. Nawa ne kudin gyaran?"
ne?"
Ya yi dariya ya ce.
"Dubu biyu da dari biyar".
Hafiz ya ec. "Kudin form kuma nawa
Nura ya zakuda kafada, ya ce.
"Wani ikon Allah, kwandalar mutum ba
na karba in dai zai zo daukar darasina, ni dai
burina a daina ha'inci a soyayya, a dinga
wanzar da zaman lafiya da yalwata zukata da
annashuwa. Saboda ina takaici inga namiji ko
87
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
mace wani na babakere da nuna zamba a
lamarin soyayya. idan na ga haka har zubar da
Kwalla na ke, na dinga jin tausayin mai wannan
hali a raina"
Hafiz ya dinga Kyalkyala dariya, ya ciro
Jubu biyar ya ba shi. ya се.
"To na gode, ka rike sauran canjin ka sha
rüwa, don na sani makoshinka na bushewa
saboda bayar da darasi. Allah ya Kara yaukaka
Kwalwa. Ya sa kuma daliban suna amfani da
abin da suke koya".
Nura ya cê. “Amin. ni ma na gode Yahaj.
Allah ya kyaija geba
Hafiz yana tafiya don shiga mota ya cc.
"Amin Ya Allah".
Da haka suka yi şallama. Yana tafe cikin
mota yana zanta maganganun Nura Baban
soyayya mai dumbin hikima da zalaka. Ya so
matuka su yi rabuwar arziki da Rufa'atu, yana
sonta tana sonsa ba tare da yin wani yunkurin
da zai wanzar da kiyayya a zukatansu ba kamar
yadda suke yanzu, sai dai dole ne ya dauki
hanya daya a cikin biyun da Nura Baban
88
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
Soyayya ya karanto masa, domin ba ya so ta
rinjaye shi ya bijire wa umarnin mahaifinsa.
Har ya isa gida yana zanta wannan
kudiri.
*** *** ***
Da ya ke yau ranar hutu ce, kamar yadda
ya saba more baccinsa a irin ranakun, yau din
ma hakan take. Yana kwance daidai a kan gado
yana sharbar baccinsa, kiran da a ka yi masa a
waya ne ba gaggautawa, da kiran ya katse wani
ya sake shigowa shi ya tayar da shi. Cikin
magagin bacci ya kai hannu ya rarumi wayar.
ganin lambar Abbansa ya sa shi mikewa zaune
yana murza idanu, tare da kara wayar a kunne.
Bayan ya yi sallama, Alhaji Atiku ya ce.
"Hala kana wannan sababben baccin ne?
Na ga ranar da ka yi iyali, haka za ka kwance
mata a gida kamar kasa?"
Duk suka yi dariya, sannan Alhaji Atiku
ya ci gaba da cewa.
"Yauwa, ka je maza-maza ka ciri kudi
dubu hamsin ka kai wa Alhaji Umar, suna jira
89
7
SADAUKARWA-2
za su tafi sa ranar aurenka
Mummyn Faanah
Mamaki da farin ciki suka lulluße shi, ya
сe.
"Yau za a sa ranar ne?"
Alhaji Atikú ya ce, "Mai garinku! Ko
kunyata ba ka ji?"
Sannan ya farga da rashin alkunyar da ya
yi, yana dariya mai bayyanar da kunya ya ce.
"Ка yi hakuri Abba...
Ya katse shi da fadin.
"Ka yi sauri fa, kada ka wuce minti
talatin, domin sha biyun rana za a sa ranar".
Bai ma jiraci cewar Hafiz din ba ya
kashe wayar. Baccin da bai sake komawa ba ke
nan, da sauri ya shiga bandaki ya watsa ruwa
tare da yin brush ya fito.
Bai Gata mintina goma ba ya gama
shiryawa tsaf, ya saka fararen kaya, ya yi kyau
ainun. Manufarsa idan ya je kai wa Alhaji
Umar kudin sai ya bi su a sa ranar a gabansa.
Kai tsaye banki ya nufa bai damu da rashin
karin kumallonsa ba, ya ciri kudin sannan ya
nufi gidan Alhaji Umar.
90 C
SADAUKARWA-2 Mummyn Faangh
Ya tarar da su su uku duk sun shirya, đa
alama "shi kadai suke jira. Bayan ya gama
gaishe da su ya ba su kudin. Da za su tafi bai
nuna binsu zai yi ba don kada su ga rashin
kunyarsa, sai ya bi su a baya yana tafiya a
hankali har suka isa unguwar, ya samu guri can
inda ba za su hango shi ba ya lafe.
A gaban idonsa a ka yi komai, yau dai ta
tabbata an sa ranar auren Hafiz, amma ba da
Rufa'atu ba, da Fadimar da ke lugwigwita masa
zuciya. Wani irin sanyin dadi ya dinga ji yana
kwarara a kalbinsa. Ya daga hannu murya cike
da nishadi ya ce.
"Ya Ubangiji, yadda Ka nuna min
wannan rana Ka nuna min ranar da za a daura
aurena da Fadima lafiya".
A take ya dinga kiran abokansa yana
shaida musu sa ranar, amma duk wanda ya
tambaye shi yaushe ne bikin sai ya ce sai an
jima ya sanar da su, saboda bai ji da kunnensa
lokacin da a ka sa ranar bа.
Sai da ya ga iyayen nasa na haramar baro
kofar gidan su Fadima din tukunna ya tayar da
91
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
motarsa, da ma sun yi waya da Habib ya kuma
shaida masa ba ya cikin unguwar, Larab ne ma
ya yi ta neman lambarsa ba ta shiga ba, shi ya
sa da ya bar nan kai tsaye unguwar su Larab
din ya nufa.
Daidai lokacin da ya kashe mota zai fito
daga motar shi kuma Larab ya danno layin
hannunsa rike da bakar leda. Cikin murna da
doki Hafiz ya fito daga cikin motar yana faman
fara'a ya doshi Larab wanda yanayinsa ya nuna
kamar bai kula da shi ba.
"Larab! Larab!!
Hafiz ya ambata ganin da gaske bai lura
da shi din ba. Larab ya dan juyo a kaikaice
fuskarsa kadaran kadahan ya cе.
"Ah Malam Hafiz ya garin ne?"
Yadda ya yi maganar ya shayar da Hafiz
matukar mamaki, sai ya yi saurin duban hannun
Larab din, haka nan ya ji bai gamsu ba, duk
yadda a ka yi akwai wani kulli a kasa, ma'ana
akwai wanda ba shi da lafiya wanda ya zautar
da Larab din har ya sauya masa haka. Cikin
rashin kuzari ya ce.
92
SADAUKARWA-2 Mummyn Faunah
"Alhamdu lillahi. lafiya ina ta neman
Jay inka a kashe?
Suna tsaye a Rofar gidan su ba su shiga
ba. haka ba su yi baya ba: Larab ya dan yatsina
fuska yace.
"Wallahi tun da safe na yi cilli da ita ban
Kara bi ta kanta ba
Sai ya jure damuwarsa a kan sauyawar
yanayin abokin nasa. ya dan washe fuska ya сс.
To albishirinka. vau fa an sa ranar
aurena da Fadimatu
Wani irin bahagon kallo Larab va watsa
"Aure kuma? Ashe har maganar ta nuna
haka ba ni da labari?
Ganin kamar labarin bai yi masa dadi ba
sai Hafiz ya dan yi dariya tare da dáfa
kafadarsa duk da shi din yana kokarin ture
hannun nasa, ya ce.
"Ka yi hakuri abokina, wallahi ni ma ban
san maganar ta yi karli haka ba, ka san Abba
yana Lagos sai Baba Umar ya wakilta a kan
komai, saboda haka ba ni da masaniya a kan
93
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
abin da suke ciki, ni ma sai dazun da safe
Abban ya kira ni ya ce na je na kai musu kudi".
Larab ya ce. "To Allah ya sanya alkhairi,
Ya kuma kai mu lokacin lafiya".
Tun kafin Hafiz ya amsa masa tuni ya
juya zai shige ciki, Hafiz ya dan tako da nufin
binsa cikin gidan. Larab ya juyo fuskarsa babu
fara'a, ya се.
"Don Allah ka fan yi hakuri Hafiz,
maigidan ya ce kada wani baligi ya Kara shigar
masa gida idan ba 'ya yansa ba".
Mamaki va gama kashe Hafiz. sai va vi
tsave fuskarsa da damuwa va ce.
"Wai don Allah mai ya faru ne?"
Larab ya ce, "Me fa? Umarnin maigidan
ne dai wannan, ka san kuma da ma hakan ya
kamata ko a addinance, tunda akwai 'yammata
a gidan?"
Hafiz ya girgiza da kalaman Larab, bai
yarda ba akwai abin da ya ke faruwa. Larab zai
shige cikin gidan. ya yi saurin riko hannunsa ya
juyo da shi suka fuskanci juna, ya ce.
"Don girman Ubangiji ka tsaya ka fada
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
juyo da shi suka fuskanci juna, ya cе.
"Don girman Ubangiji ka tsaya ka fada
min gaskiyar abin da ya faru. Wani abu na yi
maka ne?"
Larab ya girgiza kai, ya сe.
"Na fada maka babu abin da ya faru".
"To ina Bintu?"
Ya tambaya bayan ya yi zargi biyu a
zuciyarsa, wato ko ita ya yi wa laifin, ko kuma
ta rasu ne, watakila mutuwar ce ta zauta Larab
din har ya koma haka.
Larab ya cuna masa baki.
"Tana ciki mana
Ya ce, "To don Allah taimaka ka kira
min ita".
Wani rudadden kallo ya sake watsa
masa, kafin daga bisani ya ce.
"Ba ka da labarin Baba ya hana ta fita
gabadaya, saboda za a daura aurenta ranar
asabar mai zuwa?"
Wani irin lugude kirjinsa ya yi. Ya zaro
idanu waje alamun mamaki zayyane a fuskarsa,
tabbas wannan dalilin ne ya sa Bintu ta je
95
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
ofishinsa cikin rashin sukuni. Wannan dalilin
nc ya sauya Larab daga yadda ya sanshi tunda
ya san akwai. shakuwa da soyayya tsakanin
Larab da Bintu. Da kuma wannan dalilin ne zai
gamsu cewa mahaifin su Larab din ya kafa
dokar hana shigar masa gida. Kafin ya samu
abin fada, tuni Larab ya shige ciki ya barshi
hangame da baki da dumbin mamakin yadda a
ka mutu a ragaya.
u Ya jima yana jiran tsammani ko Larab
zai sake fitowa, amma shiru. Yana kokarin
shiga motarsa ke nan ya hango Alhaji Shu'aibu
mahaifin su Larab ya doso kofar gidan, don
haka sai ya dakata har ya karaso. Ya risina yana
gaishe da shi, Alhaji Shu'aibu ya amsa cikin
yalwar fuska yana fadin.
"Ya kuma na ga ka tsaya a kofar gida?"
Wannan shi ne hagu da dama! Yanzu ba
jimawa Larab ke maida masa martanin
mahaifinsu ya hana maza shiga gidansa, amma
ga shi mahaifin ya dawo yana mamakin rashin
shigarsa cikin gidan. Ya kai 'hannunsa ga keya
bai yi magana ba, Alhaji Shu'aibun ya sake
96
SADAUKARWA-2
cewa.
Mummyn Faanah
"Ko ba dubiya ka zo ba? In ce Larabi ya
fada maka dalibar taka ba ta lafiya?"
Ya ji maganar ta sake shigarsa, ya girgiza
kai ya ce.
"Wallahi bai fada min ba".
Alhaji Shu'aibu ya ce, "Ayya, ai tun jiya
da ta dawo gurin darasin ta ke haraswa, mu
shiga ciki".
Ya karashe maganar tare da dosar gidan.
Hafiz ya mike ya bi shi a baya.
A tsakar gida suka ci karo da Umma tana
matse kayan da ta wanke. Ta amsa sallamar da
maigidan nata ya yi, tare da yi masa sannu da
zuwa. Ganin Hafiz a bayansa ya sa ta daure
fuska, hka nan sai ya ji ya tsargu, me ya yi wa
wadannan bayin Allah suka dauke shi da zafi
haka? Ya dan risina yana gaishe ta, fuska babu
walwala ta amsa masa.
Alhaji Shu'aibu ya ce, "Na dawo ke nan
na tarar da shi a kofar gida, ashe bai samu
labarin Bintu ba ta lafiya ba?"
Ta basar kamar ba ta ji abin da ya ce ba,
97
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
ta soma dauraye hannunta yayin da Alhaji
Shu'aibu ya soma tafiya yana fadın.
"Zo mu shiga dakin".
Jiki ba kwari Hafiz ya bi Alhaji Shu'aibu
yana nazartar laifin da ya aikata wa Umma da
Larab.
Turus Alhajin ya ja ya tsaya bayan ya
shiga dakin sun yi ido hudu da Larab, ya ce.
"Da ma kana cikin gidan amma ba ka san
abokinka na waje ba?"
Larab ya hade fuska sosai, ya ce.
"Ban san ya zo ba".
Hafiz ya dube shi da mamakin furucinsa,
amma sai ya basar ya mika masa hannu kamar
da gaske ba su hadun ba. Larab ya miko masa
nasa hannun don babu yadda zai yi, suka yi
musabiha..
Bintu na kwance idanunta a bude, amma
ta ki duban inda Hafiz ya ke. Alhaji Shu'aibu
ya ce.
ki".
"Ke Bintu, ga malaminki nan ya zo duba
Ta dan motsa jikinta kadan alamun ta ji
०२
SADAUKARWA-2
ba?"
Mummyn Faanah
Ba ta amsa ba, Alhajin ya cc.
"Yana yi miki magana fa?"
Larab ya yi karaf ya се.
"Baba ta ji fa, ka san yanayin ciwon dole
sai an yi mata uzuri"
Alhaji Shu'aibu ya dubi Larab da Bintu,
sannan ya dubi Hafiz sai kawai ya girgiza kai,
ya fice daga dakin.
Hafiz ya yi tsuru-tsuru, ya rasa ta inda
zai kamo don shigar da tuhumarsa. Bayan 'yan
mintoci da fitar Alhajin, Larab ya dubi Hafiz ya
ce.
"Hafiz. ka san dai ni ne abokinka a gidan
nan ko? To don Allah daga yau ba na bukatar
ka zo gurina, abotar ma na yanke ta!"
Gaban Hafiz ya sake hauhawar faduwa.
"Larab, don Allah me na yi maka?"
Wani dogon tsaki ya ja, kafin daga bisani
ya girgiza kai, ya ce.
"Babu bukatar jin abin da ka yi min,
amma ka sa a ranka kusantarka a gare ni bala'i
ne mai mugun muni, don Allah ka taimake ni
99
SADAUKARWA-2
ka janye jikinka daga gare ni
Mummyn Faanah
Babu yadda Hafiz zai yi, tunda shi ma
mutum ne mai jini a jiki da zuciya, yasan ciwon
kansa bai kamata ya tsaya a ci zarafinsa ba a
kan abin da bai sanaya yi ba, saboda haka ya
gyada kai ya ce.
"Shi ke nan Larab, na gode. Amma
wallahi ban taba tunanin akwai abin da zai faru
tsakanina da kai ka kasa zaunar da ni ka fada
min don mu fahinci juna ba"
Larab ya kyabe baki. ya ce.
"Ai da ya ke kai makaho ne sai ka tsaya
nå rike hannunka na vi maka jagora ka dinga
fahintar lamuran duniya!"
Kwarai Haliz ya shaka, duk da bải
kasance mai saurin fushi ba. ko duban inda
suke bai kara yi ba. ya juya ya fice daga dakin.
Daidai lokacin Umma ta fito daga dakin
Alhaji Shu'aibu, ta auna masa harara ko amsa
sallamar da ya ke yi mata ba ta yi ba, ta wuce,
shi ma ya fice.
Da ya ke ranar yau din ta kasance ta farin
ciki a gare shi, saboda hawa mizanin da ya jima
100
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
yana fatan hawa, sai ta kasance mai sirkin abu
biyu, wato farin cikin sa ranar aurensa da kuma
damuwar abin da ya faru tsakaninsa da su
Larab, wanda har zuwa yanzu ya kasa canko
abin da ya haddasa wannan jin zafin nasa da
suka yi. Ya yi kokarin ture abin amma ya kasa.
Da yammacin washegarin ranar Alhaji
Umar ya zo gidan ya kawo wa Hajiya Asiya
kayan sa ranar Hafiz, ya kuma sanar da ita an
sa za a yi bikin sati biyar masu zuwa, Ta vi
farin ciki sosai, don tana son a aurar da Hatis
saboda tana sane da har yanzu bai dayaye daga
radadin rasa Rufa atu ba.
Hafiz na shigowa gidan. da wannan
albishir din ta tare shi, don ta yi tunanin bai
samu labarin halin da a ke ciki ba. Ya zauna a
kujera ya dinga kyalkyala mata dariya, ya ce.
"Haba Aunty, ai a gabana a ka yi komai,
ranar ce dai kawai ban ji ba sai yanzu".
Та се, "То alhamdu lillahi, tafiya Dubai
da Saudi hado lefe ya kama mu"
Ya ce, "Wane lefe kuma bayan wanda
Abba ya hado tun tuni?"
101
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
Ta yatsina fuska, ta cс.
"Ai na zaci nasa ne. ko ba ka san da nasa
auren ba?"
Ya yi murmushi, ya се.
"Aunty ke nan! Ba na tsammanin fa
akwai maganar auren nan".
Та се, "Мe ya sa ka fadi haka?"
Ya ce, "To ni dai tun kafin ya koma
Lagos bai sake yi min maganar ba, har gara
wancan zuwan da ya yi na dan tuntube shi,
amma dariya kawai ya yi bai dora ni a kan
komai ba. Kin ga kuwa da akwai maganar ai da
va ce wani abu ko?"
Ta sake kyabe baki ta ce.
"Hmn! Kai dai a yi sha'ani wai dogari ya
mari. Sarki, amma in ka ga Alhaji ya fasa auren
nan to mutuwa ya yi".
Ya dube ta da mamaki, zai yi magana
wayarsa ta yi kara alamar shigowar sako, ya
ciro ya duba, ya ga lambar Rufa'atu ce, kai
tsaye abin da ya fara fado masa a rai shi ne,
shawarwarin da Nura Baban Soyayya ya ba shi,
wanda tuni ya yanke hukuncin yin amfani da
102
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanáh
shawarwarin da Nura Baban Soyayya ya ba shi,
wanda tuni ya yanke hukuncin yin amfani da
hanya ta farko. Cike da karsashi ya soma
karanta sakon.
'Yau na nutsu na yi wa kaina tambayoyi,
wai shin ni wace irin mace ce da na kasa tsayar
da alkibla ta a guri daya? Me ya sa na ke son
abin da bai dace da ni nawa ra'ayin ba? Amsar
da na samu ita ce, da ma can ni Allah ya halicce
ni da zazzafar jarabta shi ya sa ba ni da juriyar
kauda kaina ga abin da na ke so. Babban dalilin
ankarar da ni hakan shi ne, cin zarafin da
magabatana suka yi min, ya hada da kafa min
sharadin idan ban cire ka daga zuciyata ba za
su bar rayuwata ta kare a wahalce. To na amsa
musu na hakura da kai, amma sonka da
kaunarka har abada ba za su taba tumbuke
jijiyoyinsu da suka kafu a raina ba in ba Allah
ne yà cire min ba.
Daga yau, ina yi maka albishir zan koyi juriyar rashi, ba zan sake kiranka ko turo maka
sako ba. Ba za a sake samuna a duniyar waya
103
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
ba, zan yi gangami domin binne mataccen sona
da ya dade da mutuwa a cikina ban sani ba. Zan
jarraba nesanta kaina da kai watakila na samu
sauki daga radadin da na ke ji. kada ka manta
da an taba yin mahaukaciya a makauniyar
soyayyarka! Sai watarana!!
Ya yi shiru yana kallon madubin wayar,
batutuwan da ta zana mafita ce a gare shi
wanda ba sai ya yi amfani da waccan hanyar ta
Nura Baban Soyayya ba, sai dai fa zuciyarsa ta
cunkushe da tsananin tausayin rayuwar
Rufa'atu, wato bayan wahala da soyayyarsa da
ke nukurkusar gabban jikinta, ba ta huta ba a
6angaren mahaifanta?
Hajiya Asiya tunda ya soma karanta
sakon wayar ta ke binsa da ido, kafin ya gama
kuma ta shige dakinta yin wasu bukatun. Ba ta
fito ba har ya gama zamansa ya fice.
*** *** ***
Bai yi mamakin daina zuwan Bintu
daukar darasi ba saboda tana fama da rashin
104
1
SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah
lafiya, da kuma abin da ya faru tsakaninsa da
yayanta, wanda shi ya kawo ta kamfanin. Don
haka ya cire ta a cikin jerin daliban da ya ke
tunanin kaifin kwalwarsu ya kai tsaikon da zai
dauke ta aiki a kamfanin nasa. Yanzu abin da
ke gabansa bai wuce shirye-shiryen aurensa da
Fadima ba, wanda saura mako biyu kacal.
Duk wata bukata ta kudi Hafiz ba shi da
matsalarta, domin bayan nasa kudin da ke cikin
asusunsa na banki wanda a ké samunsu ta
6angaren