Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Sadaukarwa2 Naja'atu Haruna Saleh (Matar Nura Sada Nasimat KT) SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah SHEKARAR BUGU 2015 GODIYA na mika godiyata ga Ubangina, mahaliccin kowa da komai, wanda Ya ba ni dama da ikon rubuta wannan littafi nawa ba don iyawata ba, sai don kudirarsa na tabbatuwar rubutuna alkali a cikin al'umma. GODIYA TA MUSAMMAN Ga Mijina abin tinkahona, wanda ba ya gajiya da bukatuna, ina fatan Allah Ubangiji Ya saka masa da gidan aljanna Firdausi, Ya daukaka, Ya kiyaye shi daga dukkan sharri, Allahumma Amin. SADAUKARWA Wannan littafi nawa SADAUKARWA ne ga mahaifiyata Marigayiya Rukayya Na'iya, ina fatan Allah Ya kai haske a kabarinta, Ya şa aljanna Firdausi ce makomarta. 2 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah JINJINA GA:- Alhaji Haruna Sale (Abbana) Alhaji Sada Isah Mani (Babana) Alhaji Ibrahim Na'iya (Kawuna). YABON GWANAYE Makaranta littattafaina a duk inda ku ke. bisa kokarin da ku ke yi na duba littafina, Allah Ya saka muku da alkhairi. Ya bar kaunar da ke tsakaninmu har zuwa aljanna Firdausi, amin MUN HADE HAR KULLUM Aisra Wada Abdullahi (Jini da tsoká) Maimuna Idris Sani Beli2 Li Sadiya Garba Yakasai Fauziyya D. Sulaiman Ummulkhairi Kabir-Aliyu Khadija Sharubutu Zulfa'u Jabir Abdullahi Zulfa'a Aliyu Zango A'isha Ali Dambatta Farida Ado Gachi 3 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah Hauwa Abubakar Lawan Maiturare Bilkisu Yusuf Ali Nafisat Tasi'u Moh'd Lu'ubatu Isah Lawan Da sauransu, duk ina mana fatan alkhairi. JINI DA TSOKА Dana Kwallin Kwal Yusuf Nura Sada (Faanah) Allah ya raya ka tare da sauran 'ya'yan musulmi bisa tafarki na gaskiya, amin. KA CANCANCI YABO Yahaya Mahi, Bookshop, da ke wurin 'Yan Awaki, Bakin Kasuwar Kauran Namoda, Zamfara State. TA'AZIYYA Ga 'yan uwana musulmai wadanda hatsarin rikicin addini ya rutsa da su suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka rasa muhallansu da rashin nutsuwar zuciya. Allah ya jikan rayukan da a ka rasa, Ya mayar da abin da 4 R SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah a ka rasa da mafi alkhairinSa, Ya zaunar da kasarmu lafiya, allahumma amin. TSOKACI Don Allah ina son a tsaya a fahimce ni, kar ai saurin yanke min hukunci kamar yadda wasu suka soma yi akan tallar littafin kawai da suka gani kafin ma su karanta, wasu har kafirta ni suka dinga yi. To ina neman alfarma a yi hakuri a kammala labarin sannan ai sharhi. Baya da haka, ina rokon duk wanda ya ga kuskure a cikin littafi na daya da na biyu bayan wancan maganar da na fada ną sakin aure ga da uba ya aura, to a sanar min don kiyayewa. Na gode. GARGADI Daukar wani 6angare na wannan littafi ko sarrafa shi ta wata hanyar, laifi ne babba, kuma hakan yana iya gurfanar da mu gaban kuliya. Neman izinin marubuciyar shi ne abu mafi dacewa da samun salama a tsakani. 5 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah SADAUKARWA-2 afiz. ya yi shiru bai ce komai ba da zan yi maka, shin da gaske kake aure zaka yi? da cewa. Bai ba shi amsa ba, Habib din ya ci gaba "Na tambaye ka ba ka bani amsa ba". "Idan tambayar taka tana da amsa ai da na baka". "Ke nan kana nufin ba ka shirya aure ba?" Inji Habib. "Wannan kuma kai ta shafa". Ya ba shi amsa cikin kulewa. Ya jinjina kai, sannan ya ce. "Ba laifi, ka ga tambaya ta biyu ba ta da amfani, sai dai abin da zan yi maka matashiya da shi shine, ka daina sanya kanka shirgin da ba naka ba, a sanina kai ba mayaudari ba ne, to don me yanzu za ka fara yaudar..." Ya sake tare shi, wannan karon rai a бace, "Wai wa ya ce maka ni mayaudari ne 6 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah kake ta dauko wannan batu kana dora min? Ko na yi maka kama da irin samarin'nan 'yan shan minti ne?" Murmushi Habib ya yi sannan ya ce. "Ai ba ni na ce ba, tambayarka na yi ka ce min kuma ni ta shafa, ni kuwa a tunanina duk mutumin da kyakkyawar niyya cе zuciyarsa idan har aka tambaye shi ba ya maido irin amsar da ka maido min ba". Hafiz ya jinjina kai, ya ce. a "To ni ba haka nake ba, tun da nakе rayuwata ban taßa duban wata 'ya mace da wannan sigar ba, idan kuma ba aurė zan yi ba babu dalilin da zai sanya ni shiga shirgin mata bare na wahaľar da kaina har na dorawa kaina hawan jini". 2F Habib ya sake yin murmushi, ya ce. "Idan na fahimce ka ka bani amsata ta farko, don haka tambayata ta biyu a gare ka, shin zaka iya aure 'yar talakawa wadda ba su da cin gobe a ajiye, kullum sai an fita an nemo? Kuma diyar malamin makarantar allo, wadda ba su waye da wayewar boko ba?" 7 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanoh Ya kasa fahimtar inda wannan tambaya ta sa a gaba, don haka sai ya zubawa Habib in ido kawai yana nazarin ta inda zai kamo hax y fahimci me yake nufi da wannan tambayar tasa mai harshen damo. Kamar Habib din ya fahimci abin da Hafiz din yake tunani, sai ya murgina kai ya ce "Kar ka rikita kanka mana, game da matar auren da Allah Ya jarrabi zuciyarka da so ne". Daram! Gabansa ya kuma faduwa, ya dai yi shirun yana kallonsa. Habib ya gyara zama ya ce. "Ka yi hakuri abokina na ruda tunaninka kwanaki hudu da suka wuce, ba komai ya sa na yi hakan ba, illa don na tantance wane irin so ne kake wa Batula, kuma alhamdu lillah na fahimta, amma maganar gaskiya Batula ba ta da aure, budurwa ce 'yar talakawa diyar malamin zaure... Zuciyata tana raya min kamar don ba ka san wace ce ita ba shi yasa ka ce kana sonta, sai na kasa samun nutsuwa, hakan ya sa na ce 8 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah maka tana da auren don mu samu mu rabu lafiya da kai. Na farko Yayanta abokina ne, kai ma abokina ne, ga shi akwai sanayya dukkanmu sai na ke ganin tarin kalubale a duk lokacin da ka ce ba zaka aure ta ba don tana 'yar talakawa bayan kuma ka sa ni a tsakiya, ka ga zan ji kúnya a gidan su. Sannan kai ma za mu iya samun sabani a tsakaninmu, ka ga anyi badi ba rai ke nan. Wannan shi ne dalilina, to amma daga shekaran jiya kawo wa jiya na yi istihara sai na rasa gane kan lamarin, domin ina ganin alkhairi a tarayyarku, haka ina ganin wani rudani da ban san daga inda zai fito ba, saboda haka kawai na ga dacewar na sanar da kai gaskiya, na kuma tayaka da addu'a Allah Ya tabbatar da abin da ya fi zama alkhairi a tsakaninku". Hafiz ya rasa kwatanta irin dadin da ya ji ya shige shi, fuskarsa ta yalwatu da fara'a sosai, wai Fadima ta tabbatu ba ta da aure? Mamaki? Al'ajabi? Farin ciki? Murna? Ko doki ya kamata ya yi? Habib ya mike tsaye daga inda yake 9 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah zaune, ya dawo gaban teburin da ya gilma tsakaninsu, yana murmushi ya ce. a "Ka san me? Har na yi azarbabin sanarwa Batula, kuma ta nuna min amincewarta, sai dai kasan gidansu akwai a'idoji da duk wanda yake neman 'yar gidan ya ke bi kafin ya soma tunkarar mace, don haka ta bayar da wannan damar. Ma'ana kana da damar da zaka sami mahaifinta ka sanar da shi cewar, kana sonta idan ya amince da kai zai ba ka damar tsayawa da ita, idan kuma ya yi mata miji ne duk zai sanar da kai". Sai ya ke ganin kamar abin a mafarki ne. amma yadda ya ga Habib yana maganar ya samu yakinin hakan take. Shi ma mikewa tsayen ya yi suna fuskantar juna ya ce. "Don Allah da gaske ka ke Habib?" Gira ya daga masa ba tare da ya yi magana ba. "Idan dai har da gaske ka ke, ina so ka fada min me ya hanata zuwa nan kwanaki hudu tun ranar da ka dauke ta?" Ya yi murmushi, tukunna ya ce. 10 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanoh 3 "Allah Sarki! Wato ka yi tunanin mijin nata ne ya hana ta zuwa? To sha kuruminka, ba ta jin dadi ne tun daga ranar da na dauke ta, yau ma da safe na shiga na duba ta". "To yanzu ya za a yi ke nan?" Habib ya dafa kafadarsa ya ce. "Abin yi ya rage gare ka, sai ka fidda lokacin da zamu je ga mahaifin nata idan har zaka iya aurenta a bisa mizanin da ta ke kai". Da fara'a a fuskar Hafiz ya ce. "Kar ka damu Habib, wallahi ba ni da wannan burin na cewar ba zan auri 'yar talakawa ba sai 'yar masu kudi, domin a rayuwar aurena babu abin da nake fata illa Allah Ya hada ni da abokiyar zama ta gari. Fadima kuwa ba na hasashen rashin dace a tare da ita. Tun ranar da na soma tozali da ita, na san ita kyautar Allah ce, wadda suka yi karanci a wannan zamanin. Zuciyata na raya min idan na samu nasarar aurenta na yi dace da mace ta gari duk da dai su din ba tukwane ba ne bare a kwankwasa a ji wacce ta fi kwari, amma ka san 11 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah an ce daga ganin juma'ar da zata yi kyau tun daga Laraba ake gane ta. Fadima tana da nutsuwa, hankali kai har ilimi Fadima duk ta hada, yadda ta ke da kamewa da kuma kwalwa na san ba zata rasa wadataccen ilimin addini ba sai ga shi kuma yanzu ka sanar da ni daga gidan da ta fito, wato gidan da aka san alkur'ani ciki da bai, gidan da koda yaushe rahama ta ke ziyartarsa. Alhamdu lillah, ina matukar godiya ga Allah da Ya hada ni da Fadima, kuma ina fatan Ya mallaka min ita a matsayin matar aurena ПАПЧЕ nitnoa janye hannun Habib da ke saman kafadunsa, sannan ya zauna. Shi ma Habib din ya zauna yana kallon yadda Hafiz duk ya cika da farin ciki, nan da nan ya ji shi ma farin cikin ya kama shi, saboda dukkansu ya san su, yasan kuma sun dace da juna. Hafiz ya сe. "Yanzu ya kake ganin za a yi?" un Habib ya dan yi murmushin jin dadi ya ce. "Ba sai mun tsawaita lokaci ba, kamar yadda na sanar da kai Fadima diyar malami ce, 12 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah ३ ka san kuwa dole zaka same su da dokoki da sharudda, don haka da zafi-zafi akan bugi karfe, sai ka shirya anjima da daddare mu je gidansu mu nemi izinin ganin mahaifinta mu isar da muradinmu a gare shi". Hafiz ya girgiza kai, yana fadin. "Da wannan dan wannan wai an tura tsohon banza biko ya ce idan ba a mayar masa ba ina wa dana riko... Amma me zai hana mu bari sai jibi Laraba, kasan duk abin da aka soma shi ranar Laraba zai wahala bai zo da nasara ba, manzon Allah (S.A.W) Ya yi mana nunin, dumbin darajar da ranar Laraba ta ke da ita, har ya yi mana hani da fifita ranar juma'a fiye da Laraba, saboda Yahudawa sun dauki Asabar mafificiyar rana a gare su, Nasarawa kuma suka dauki Lahadi, ka ga ke nan idan mu musulmi muka dauki juma'a a matsayin mafificiyar rana a gare mu, mun koma su ke nan, ma'ana mun bi sahunsu. Saboda haka ina ganin mu je ranar Larabar". Habib ya ce, "Lallai kam ka yi tunani mai kyau, da a ce mutane da yawa za su dinga 13 LADANLAFWA; ataha uma 31 hutur 2 253ght dи123 21а 7кabа ta at SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah tsinkaye irin naka su soma neman aure ranar Laraba da sun ji dadi, to amma an biyewa Yahudawa da Nasarawa wai hatta da daurin aure sai a ce sai ranar Asabar za a yi shi, ba kuma don komai ba wai sai don ranar ce ranar hutun ma'aikata, shin a islamance wace rana cе ranar hutu? Ina ce Alhamis da Juma'a sune ranaku hutun musulmi, me yasa ba za a dinga daurin aure a irin ranakun ba a matsayinmu na musulmi? Duk da cewa yin daurin auren ma Asabar ba aibu ba ne, amma kowa ya bar gida, to kuwa gida zai barshi. Ba Karamin jin dadi Yahudawa suke ji ba da wannan tsarin nasu da muka dauka wai na daurin aure ranar asabar" Da wannan shawarar suka rabu akan jibi ranar laraba za su je wajen mahaifin Fadima. *** *** Kwance ya ke akan gadonsa yana bacci bayan ya taso daga wajen aiki ke nan, wayarsa ta ishe shi da tsuwwa, amma baccin da ke idonsa ya hana ya kai hannu ya janyo ta. Kiran ya katse, wani ya sake shigowa har 14 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah sai da aka kira ya fi sau biyar bai daga. Karfe uku da mintina sha biyar ya farka daga baccinsa, wayarsa ya soma dubawa don ya ga karfe nawa, sai ya tarar da kiran da aka rasa guda shida (6 missed calls). Ya mike zaune yana dubawa, lambar Rufa'atu ya soma gani mài kira biyar, sai daya lambar da babu suna. Ya yi tsai da idanunsa akan lambar Rufa'atu yana tünanin makasudin kiransa, domin ya san tunda abin nan ya faru ta daina amfani da layinta, a cewarta mahaifinta ne ya amshe wayar gaba daya, yanzu kuma ga shi ta kira shi da layin. Kafin ya lalubo abin yi rubutaccen sako (text massage) ya. shigo masa. Ya duba da bakuwar lambar da aka yi masa missed call ne aka turo sakon. A hankali ya soma karanta abin da sakon ya kunsa. Farin cikin rayuwata, da fatan ka wayi gari cikin koshin lafiya. Bayan haka ina mai sanar da kai zuciyata ta kamu da matsanancin Kaunarka sai dai na 15 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah kasa sarrafa kaina ta yadda zan iya hakura ba tare da na tuntube ka ba... Iya abin da sakon ya kunsa ke nan, karo na farko babu wadda zuciyar Hafiz ta hasaso tana mallakar wannan rubutaccen sako sai Rufa'atu, domin ita ce tauraruwar da ta ke sonsa fiye da tunanin mai tunani. Bayan ita babu wata budurwa da ya taba tunkara ya ce yana sonta, don haka koda yaushe, zai ga irin wadannan kalamai yasan daga gare ta ne, ko ba ma don haka ba, yanzun nan ya gama duba missed calls dinta guda biyar sai daya da bakuwar lambar, ke nan hakan na nufin ita се mallakar bakuwar da aka yi missed call da kuma rubutaccen sakon. Bai yi kasa a gwiwa ba, tunda zuciyarsa ta gama yi masa amanna Rufa'atu ce, sai ya soma kiran lambar da ke da sunanta, amma ya tarar da ita a kashe. Ya bi waccan bakuwar lambar, ita din ma a kashe ta ke. Ya jingina da filo yana mai lumshe idanunsa, hakika har kullum yana tausayin Rufa'atu, yasan son da ta 16 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah ke masa ba irin wanda zai yi fitar burgu ba ne a gare ta, amma shi a ganinsá son da babu aure me ye amfaninsa? Ita da kanta ta fada masa zata yi hakuri da shi don ta taya shi biyayya ga mahaifansa, kuma ita ma ta yi tata biyayyar ga mahaifinta da ya'ce ba ta ba shi, to ammá ya lura Karfin son da ta ke masa žai haifar da raunin yin hakan a gare ta. Abin da zuciyarsa ta ayyana masa idan har yana son zama lafiya, ya kuma yi biyayya ga mahaifinsa har ita ma ta samu damar yin tata biyayyar ga nata mahaifin dole ne ya saúya layi don su yi nesa da juna. Ya yi amanna da wannan shawarar dari bisa dari, sauya layi shi ya fi dacewa a gare shi. Bayan ya yi wanka ya shirya, kai tsaye cikin gida ya shiga, ya tarar da Hajiya Asiya zaune akan doguwar kujera, fuskar nan tata a daure. ga dukkan alamu wani abu ne ke damunta. Ilai kuwa Hafiz na zama a kan kujera ko gaishe ta ba ta bari ya yi ba ta hau furta munanan kalaman da ta kunsa. 17 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah "Haka kawai ina hakuri da mutum ba ya gani, to wallahi alo tsiya alo danja. ba a isa a kawo min wata bankadaddiyar yarinya ba". Jin wannan furucin nata ya sa Hafiz ya dago dalilin fushin, wato Abba ya sanar da ita zai kara aure, shin maganar har ta tabbata ke nan? Rashin dacewar magantuwa ya gani shi yasa ya mike tsam zuwa bedroom din mahaifinsa, ya tarar da shi yana kidaya kudi. Ya nemi guri ya zauna kusa da kafafun Abban nasa, yayin da Alhaji Atiku ya dago kai ya dube shi, ya ce, "Ka shigo?" A' yanayin fuskar Alhaji Atikun bai ga wata damuwa ba game da halin da Hajiya Asiya ta ke ciki, ya san hakan ba ya rasa nasaba da maganar Hausawa, inda sabo kifi ya saba da ruwa. Ya се. "Eh, dama game da maganar da muka yi da kai jiya ne, yau da daddare za mu je gidan su yarinyar wajen mahaifinta". Alhaji Atiku ya tsayar da nutsuwarsa akan Hafiz fuskarsa cike da yalwa ya ce. "Na yi murna matuka, Allah Ya sa a fara 18 SADAUKARWA-2 neman a saa Hafiz ya ce, "Amin" Mummyn Faanah Alhaji Atiku ya ce, "Bude lokar can ka dauki daurin 'yan hamsin guda biyu ka yi dük abin da ya dace". Ya ce, "To Abba, na gode Allah Ya kara girma". Ya mike ya bude lokar ya dauko kudin, dai-dai lokacin da yake shirin fita Hajiya Asiya ta shigo dakin, tana fadin. "Magana fa nake maka ka kyale ni, mene ne manufarka a Kaina?" Hafiz ya sa kai ya fice daga dakin, ita kuma ta karasa shiga ciki tana zuba ruwan masifarta, shi dai ya yi shiru ya kyale ta tamkar bai san da zamanta a gurin ba. Kai tsaye Hafiz na fitowa daga gidan, motarsa ya shiga ya zauna sannan ya kira lambar Larab, ba jimawa ya dauka. "Hello Larab kana ina ne?" Larab ya ce, "Uhummm! Na san arina, yanzu kuma ta nan ka billo wai kidan farauta a kasuwa". 19 SADAUKARWA-2 Hafiz ya yi dariya. yaа се. Mummyn Faanah "To nuna min kana digiri a fannin Hausa, ni ba wannan ne sanadin kiranka ba. Kana ina ne? Ina so zaka yi mana rakiya ni da wani abokina zuwa gaido surukai". "Surukai?" Larab ya maimaita cike da tsananin mamaki, zuciyarsa kuma na isananta bugawa. Yaushe ka samu surukan har da zamu gaishe da su?" Maimakon Hafiz ya amsa masa tambayar da ya yi masa, sai ya се. Kai dai kana ina ne, ina sauri karfe biyar muka yi zamu je" eer Larab ya ce, "To'yanzu dai ga ni nan gidanmu". Ya ce, "To ka jira nina karaso". Yana kashe wayar ya nuti gidan su Larab din. Tafiyar mintina ashirin suka sadar da shi gidan, lokacin ana ta haramar shiga masallaci sallar la'asar, don haka gaisawa kadai suka yi da Larab ko cikin gidan bai shiga ba sai suka wuce masallaci, ya yi alwała a can sannan suka 20 SADAUKARWA-2 gabatar da sallar. Mummyn Faanah Suna gamawa suka nufi cikin gidan. Umma ta gama tata sallar sai Bintu ce ke yi. Ya durkusa kasa ya gaishe da Umman, ta amsa cike da jin dadi. Ya ce, "Ya mai jiki?" Ta kyabe baki tana fadin. "Ai ciwon Bintu yadda ka san ciwon jinnu, yanzun nan za ka ji ta da lafiya an jima ka ji ba lafiya. Tun dai da muka dawo asibiti lafiya kalau babu wani abu da ya ke damunta, illa rashin kuzari na wanda ya tashi daga ciwo". Ya ce, "To Allah Ya kara inganta mata lafiya, amma ni kaina ciwonta na ba ni mamaki, ko dai har da aljannun ne?" h Larab ya yi karaf ya сe. "Ba wani aljannu, illa jarabar soyayya da ta saka wa ranta... Sai kuma ya kasa karasa fadar abin da ya ke shirin fada, ya sunkuyar da kansa kasa. Shi kuma Hafiz ya yi saurin duban Larab din yana maimaita kalmar. "Soyayya? Da ma soyayya ce jigon 21 SADAUKARWA-2 rashin lafiyarta?" "Yaya barka da yini Mummyn Faanah Wannan itaice amsar da ya samu daga bakin Bintu wadda ta sallame. sallar tana murmushi. Ya juyo yana kallonta ya amsa mata. "Yauwa Bintu, sannu da jiki" Ya maida kallonsa ga Larab yana fadin. "Laifinka nake gani; domin kai ne ka cе Bintu ba zata tsayá da saurayi ba wai ta yi Karanta, yanzu wa gari ya waya?" Ya dubi Umma ya cс. "Wallahi Umma kar ki yarda Larab ya nakasa miki 'ya, kiobar yarinya ta kula wanda ke sonta, wannan takurar ta Larab ban san inda ya koyo ta ba, sammutum ba ya uzuri da duban abin da ya dace saboda mugun son kai". Su duka biyun Umma daLarab suka yi dariya, yayin das Bintu ta sunkuyar da kai Kwalla na zubo mata cikin idanu. Hafiz ya lura da kwalan dansuka zubo mata a kumatu, tausayinta yaokama shi, ina dalilin wannan zalunci da Larab ya yi mata? 22 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah 3 Shi kam a yanzu ya san zali da radadin rabuwa da masoyi. don haka a duk inda masoya suke suna ba shi tausayi, dole ne kuma ya Karfafa musu gwiwa rike junansu bisa gaskiya da amana, an ce ruwan da ya dake ka shi ne ruwa. Larab yana dariya ya CC. "Soyayya ko shirme? In bącin hauka me ye a cikinta?" Sai Umman ta mike ta fita ta ba su guri, jin sun tabo shafin da ya girme tunaninta. Hafiz ya auna masa harara yana fadin. "Kai ka ga hauka a soyayya, ni kam ina ganin muhimmancinta da darajarta, shi yasan kake ba ni haushi Larab, wani lokaci kai mugu ne, ba ka da tausayí sam a rayuwarka Larab ya tamke fuska, ya сe. "Tausayi? Ai kana tausayawa masoyan da suka san me ye soyayyar har suke yinta, wadanda ba su santa ba me ye amfanin ka tausaya musu? Kai ni fa wallahi duk wanda ya ce zai jawo kansa azal to ba ya ba ni tausayi..." Hafiz ya katse shi da fadin. "Me ye azal? Kuma idan ba a koya an 23 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah samu Rwararru? Ko ka manta duk wanda ya shahara a soyayyar sai ya fara zama falibi kafin ya zama shahararren?" Bintu dai Kwallanta ta ke shara. Hirar kuma tana burge ta, a kalla zata samu sassaucin matsin lambar da yayan nata ya mata. Larab ya girgiza kai, ya сe. "Da kake wannan hakilon, shin me ye amfanin SON MASO WANI?" A nan sai Hafiz ya yi jagale yana kallon Larab, a fahimtarsa son maso wani koshin wahała ne, domin ba lallai wanda kake son ya tausaya maka ba har ya kulaka ya tallafe ka da muhalli ko da na wucin gadi ba ne, duk da dai ba duka aka taru aka zama daya ba, wasu suna da adalcin musamman idan suka dubi wanda ke son nasu yana cikin halin kunci da damuwa mai tsanani... "Ba ka ba ni amsata ba" Larab ya katse masa tunani. Hafiz ya kai dubanshi ga Bintu, sannan ya dawo da duban ga Larab, ya сe. "Ba shi da amfani kam, amma ya kamata 24 SADAUKARWA-2 Mummyn Faanah duk wanda ya samu kansa a wannan gurbi a tausaya masa, zafafa masa ba shi zai kawo maslaha a gare shi ba..."" Larab ya daga masa hannu. "Don haka ne ba na jin tausayinta, tunda ta dorawa kanta dala da gwauron dutse ba sai ta nemi mai sauke mata su ba, na me mu kullum zata sa mu dinga asarar lokaci da kudadenmu a wajen nema mata magani? Ni fa wallahi kullum ji nake kamar na kamata na yi ta jibga don takaici..." Bintu ta dago kai ta dubi Larab, mamaki ta ke na rashin tausayinsa. Harara ya auna mata, sai ta maida kan kasa. Hafiz ya ce da shi. "To ba sai ka maida niyya ba, tunda kai ka haife ta? Ah! Ji ni da mutum da karfin hali... Amma na san. maganinka, addu'a zan ta yi Allah Ya sa ka hadu da wadda kake tsananin so amma ba ta sonka" Larab ya ce, "Ba bakinka ba, sai dai kai دو zan yi addu'a kar ka dace da samun... Sai kuma ya sauya zancen da fadin. "Ka ga na sha'afa, ya kamata mu san na 25 SADAUKARWA-2 yi kada lokaci ya kure mana ko? Mummyn Faanah Hafiz ya ce. "Eh, tunda ka san ba ka da hujja ba". Suka yunkura su biyun, Bintu ta zuba musu idanu kawai har suka fice daga dakin, suka yi wa Umma sallama sannan suka fice zuwa inda Hafiz ya ajiye motarsa. Bayan sun soma tafiya ne, Larab ya dago kai ya dubi Hafiz yana fadin. "Ka ce gaisuwar surukai za mu je, shin ya maganar ta ke ne?" Hafiz ya yi murmushi cikin zumudi, ya ce da shi. "Haka zancen ya ke, na samu matar da zan aura ne a unguwar su wani abokina Habib, to ya fada min

Chapter 1 of 6