komawa.
Bayan sun tafi washegari Nafisat ta tarkata
komatsanta, na dauke ta sai gidansu. A kofar gida muka ci
karo da Inspector Kabir. Nayi mamakin ganinsa matuka.
Bayan na tambaye shi dalilin rashin saduwarmu kwana biyu
ne ya sanar da ni cewa yayi 'yar tafiya ne. Daga nan na sanar
da ni cewa zuwansa kenan, kuma nan ne gidan iyayensa.
Take anan ni da Nafisat muka fahimci cewa shi ne Kabirun
da Hajiya Mai-Duka ta sanar da mu cewa shi ne babban dan
Hajiya: Ubaida wato shi ne babba a gidan. Bayan mun
rankaya mun shiga gidan ne ya tambaye mu abinda muka zo
yi gidansu. Kafin in sanar da shi, gida ya rude da ihun
murnar zuwansa. Bayan ya huta ne su Ahmed suke sanar da
shi labarin Nafisat. Shi ma yayi murna kwarai, sannan ya
hada da cewa "Ai nina san cewa biri yayi kama da mutum,
domin nauyin baki kawai nayi a ranar da aka kama su T.j.
idan baku manta ba na kura wa wuyanta ido wanda kuma ba
komai ne ya sa ni yin haka ba sai tsagun da na gain a
wuyanta wanda babu marabar tsinke da namu."
Take na lura da na shi wuyan, inda na ga wadannan
tsagu. Bayan mun yi 'yar hira nayi sallama da su nayi nufin
tafiya gida. Hankalina ya tashi kwarai da na lura Nafisat na
zubda hawaye. Ni da kaina ban so muka rabu ba sai don ya
m
a
B
S
68
zama dole, domin an ce kyan 'ya mace idan har ba aure ta yi
ba'ta KasanUe gatah iydyent
dud tabuds В dodee Lore
Kdawar Nafisal fidarda kwatia biyu londi fat iturman
thyi măna Kaurá ta koma wajen mähdifanti4lukadzaliká ita
ma na ga mugun tashin hankali kafinmubu daital Mon
rabu akan zah dinga ziyartar ta ko du. yaushe ina:Ma a duk
Iskacin da ta samu dama zata dinga zuwí wajenm st ro
suttBkpkuiha mun ziyarci Zariye bdyan shtindaya,
anan ma mur gaggaisa da dangin ialraitan Moda,isairkuma
MURd VOdEEdaidar wannani tikaci eiyilwe Moda canjin
atki zuwt hatr garih Hamu: Bahukwhnaiidu bamukayi
haramal gawewa gidal San daakal Mouaunyiraidaritá
akat thihta Bubi MAyRksariata ita üUn'sahanin kaunar datiko il um neanse elosрку
tin a muka dawolrdagnd Zamyabnatard isu
Uzarfat k ba ni shawarár yaddá zán juya wanmin dukiyata
sale da'ta banki Sun bachi shawarh cowa Rhdanmayiswaвана
taßa kudin banki n bab sfeantlaroi amniu kadin dhukee
safe sun bar slawarar cewa na bikde kanfaninda äke ganin
Zai-taimukawa tülakawa niatukasmakenagardshawarar
su, bayan haka sai da muka je dukkanin bunkumary da yayaria
Vakeajiya kudwBubátshákka nh rażdnataha biliyoyin
kudin da ya tara. Bayan mun koma gidasdadshigal dakinsa a BAcsanignenas t kito ida takárdar cak
dinsa na bankonan darakerdjiyär kunmede namon sb ulede ii an biyu da yinishwalamiinta"na samu
ih i uhguwa gada na siyld Bada jimasdal ha
"blikilo suka farä aikinsu. Bayan hákd-sai da naidadagiyan
anfadd nasuaka yiahtai kamfanin saidamotogi: Mr.
Klink ne ya faure mini gindi gurin samun hanya shigoida
ababbinfola sandrdannidowrd vikih wata mai
69
shisters agob slan
30
/JWa 7a:kanın da suke JAPAN domin ark mi sh
motoci sababbın amturt, dan haka na ware makulan kudi
na tura ta bankinsa na can domin ni ma na amu wadanda
zan bude kamfanina da shi. duk wannan abu da nake yi su
Uzaifat ba su da masaniya
Wata na zagayowa Mr. Klink ya buge mini waya ya
sanar da ni cewa motoci sun iso. Da ma ya zo a daidai
lokacin da na kammala wannan kamfanin, taken na ce a
zarce mini da su can ni ma ina tafe ba da jimawa ba
Take na dauki Moda tare da bebi Maryam muka nufi
gurin aikin Uzaifat ba tare da ta san abinda ke faruwa ba
Mun risketa zaune a ofis dinta, bayan na sanar da ita cewa
ina son ta raka mu unguwa ne, ta kinkintsa takardun da ke
gabanta sannan muka fito muka rankaya gidansu Nafisat, ita
ma ba tare da mun bata lokaci ba muka baro gidansu. Ba mu
zame a ko'ina ba sai a BEB MARYAM & CO. INT. LMT
sunan kamfanin kenan. Muna fita daga mota su Uzaifat suka
tsaya cirko-cirko suna kallon sarautar Allah.
"Yaya me zan gani?" Nafisat ta tambaya.
Bayan sun karanta sunan kafanin ne suka gane
dalilin zuwansu wajen.
"Kai yaya, shi ne kawai ka yi mana bazata?" Nafisat
ta kara fadin haka.
"A'a ba wai bazata nayi ne kawai kada ku ce na
ishcku da neman shawara." Na fada ina dariya.
"Uzaif Allah ya kara budi kuma ya sa anyi a sala.
Allah ya sa bebi Maryam ta amfane shi, kai ma kuma ka
amfane shi." Ta amshi bebi Maryam a hannun Moda. "Allah
ya raya mana ke kin ji." Ta fada a yayin da idanuwanta suka
yi raurau.
Moda-kuwa kasa fadin komai tayi hawaye ne ke
zuba daga fuskarta.
70
Da haka muka Karasa cikin kamfanin. Mun sadu da
Mr. Klink a farfajiyar kamfanin yana yiwa motócin kallon
tsaf, Motocin sama da saba in sun yi reras suna kelli. Bayan
na gaisa da Mr. Klink su ma su Uzaifat suka gaisa da shi.
Take ya ba ni Container din mukullen motocin yayi mini
sallama ya tafi. Yayin da muka kammala dudduba kamfanin,
sai nayi wa su Uzaifat tayin mota. Da farko sun yi mamaki
amma daga baya suka tuna cewa sun fi karfin hakan a
wajena, bayan na ce su fauki motoci daya daya ne. Nafisat
ta kella ido ta hangi B.M.W. 500 xl ta nufi wajenta tana
tsalle tana murna. Yayin ne Moda ta nufi wajen LAND
CRUISER ita ma tana murna. Gimbiyar kuwa ni ta barwa
zabi. Bayan 'yan dube-dube da nayi ne na hangi MAXIMA
JEEP wanda da gani kowa zata yi matukar dacewa da ita. Na
dudduba makullensu na ba su. Daga nan kowacce ta tashi
motar sai gida. Da isarmu gida suka yanke shawarar ayi 'yar
kwarya-kwaryar fati. Take muka sake shiga cikin gari muka siyi I.V. da sauran abubuwan da ake bukata. Muna dawowa
kowacce ta bugawa saurayinta waya tana gayyatarsa. Cikin
kwana biyu muka kammala rabon I.V.
Ana gobe za a yi fatin Dr. Aimana da Engineer
Ukasha suka diro mana. Ranar fatin kuwa gayu da ciku sun
hade sosai. Sannan kuma an saki sauti sosai, a yayin da
samari da 'yan mata suke cashewa. Lallai EXCELLENT
HOTEL ta debi kayayyaki.
BAYAN SHEKARA DAYA
Bebi Maryam ta taho a guje ta fado kan ruwan
cikina a yayin da nake kwance akan kilishin falon. Gaba
daya muka tuntsire da dariya da ita. "Waye ya koro ki haka?" Na tambaye ta.
71
"Wannan." Ta fada tana yi mini nuni da hanyar
dakin Moda.
"Rabu da ita sai mun yi mata duka ko?" Na fada ina
dariya
"Eh." Ta amsa tana dariya ita ma.
Ba zaka ta6a ganin Bebi Maryam ka ce shekararta
daya da wata hudu ba, don tsananin wayo da surutu.
Moda ta fito tana fadin "Au nan kika gudo? Ai da
kin tsaya ma ba dukanki zan yi ba marar jin magana kawai."
"Me tayi ne ake yi mata balbali bala'i?"
Ta kwashe da dariya sannan ta ce "Ji'ita man
shafawa ta kwáshe ta zubar akan Kafet sannan ta zazzagar da
hodar ta. Moda ta fada tana kallon ta.
Ai dai babu laifi tunda nata ne a siyo wani." Na
fada ina shafa kanta.
"Au- haka ma zaka се?"
"To me kike so na ce ko so kike ni ma na ruda ta da
fada?"
Ta tintsire da dariya sannan ta koma cikin daki.
Yau saura kwana biyar a daura mana aure gaba ki
dayanmu. -Domin kuwa iyayenmu wato mahaifiyar Uzaifat
da mahaifan Nafisat da kakar Moda duk sun ba mu hadin kai
a bisa soyayyarmu. Kuma ba tare da 6ata lokaci ba suka
bukaci su Doctor Aimana da Engineer Ukasha da su toro
magabatansu. Bayan 'yan kwanaki suka turo aka sa ranar
daurin aure bayan iyayen sun ce ba sa bukatar komai sai
sadaki, don haká muka yanke shawarar siyan makeken fili
domin gina gida. Mun sami filin a can G.R.A. inda muka yi
tagwayc.da ganbonsu a cikin haraba daya. A yanzun haka
ma mun kammala komai na game da kayan masarufi.
Sannan kuma mun kammala komai ma game da fatinan da
zamu yiyyi da irin ankon da mu maza zamu yi, da kuma
72
wanda mata za su yi, yanzun haka kuwa babu abinda muke
jira sai ranar farin ciki. Mun yi da su Doctor Aimana sai ana
sauran kwana biyu daura aure za su duro da danginsu 'yan
biki baki daya. Sannan an yanke shawara cewa dukkan
amaren a gidansu Nafisat za su tare har a kammala biki
kowacce ta tare a gidanta.
Sannan a ranar dfaurin aure za a yi Launching din
kamfanin garin masarar da na bude dan talakawa.
Daurin aure saura kwana biyu Uzaifat ta ziyarce ni.
Bayan mun gaisa ne ta ce da ni "Uzaif har yanzu baka
tambaye ni yadda aka yi na kubuta daga hannun su T.j. ba,
ko ka manta da alkawarinmu ne?"
Na nisa na ce "Ina sane Uzaifat kin san harkokin ne
suka yi mini yawa sosai, amma in babu damuwa kya iya ba
ni yanzun."
"To ba laifi, wai shin ina bebe Maryam ne?" Ta
tambaya.
"Sun tafi Zariya da Moda amma gobe za su dawo."
"Allah ya dawo da su lafiya."
"Amin" Na amsa.
"To in fada maka bayan mun hau sama da kanmu
mun tarar da Momi a kwance cikin maliyar jinni, kawai daga
sama sai na ji wani abu yayi mini dum akaina. Gaba daya
ban san lokacin da idona ya rufe ba. Kwatsam sai ganina
nayi a cikin wani faki bakikkirin da shi. Bana.raba daya
biyu ba na san cewa aikinsu T.j. ne. Take Momi ta fado mini
a rai banda kuka babu abinda nake sarba. Ina cikin kukan ne
na ji an bude kofar. Tsaye a kaina T.j. ne da Sussy suna
dariyar na zo hannu, sai dai mutuwa cc kawai ta rage mini.
T.j. ya zo daidai inda nake ya tsuguna ya kama habata kamar
zai yi kiss dina kawai sai ya kwashe ni da mari.
73
Haushin marin da na ji ne ya sa na aikata abinda na
gwammace da ban aikata hakan ba. Yawu na tofa masa a
fuska. Ai fa take ya sa kafarsa mai sanye da wani
kwankwamemen takalmi ya dinga dukana da shi yana
haurina, amma don tsananin taurin kai na ki bude baki na ba
shi hakuri har ya gaji ya daina da ya tabbatar na sume. Ban
ankara ba na ji wani irin sanyi ya ratsa ni fiye da yadda kake
zato. Ina cikin tunanin halin da kake ciki ne na sake ji an
bude kofa an shigo Sussy ce dauke da wake da shinkafa
babu ko manja bare man kuli akai. Ta turo mini gabana
kamar wata dabba, sannan ta ajiye mini ruwa a cikin wani
kazamin kofi tayi gaba tana zagina da turanci "Stupit girl,
idiot." Ta mayar da kofar garam! Ta rufe hade da kullewa da
makulli. Ban so cin abincin ba amma ganin ban san ko
kwana nawa zan yi kafin su kashe ni ba ya sa na ci don ban
taba zaton zan kubuta ba.
Lokacin da na gama cin abincin sai na ji takun sawu,
sannan kuma aka tsaya a daidai bakin kofar dakin. An fi
minti goma sha biyar ba a shigo ba, kai har ta kai na fara jin
sautin murya tana tashi kadan-kadan, don haka haka sai na ja
gindi har zuwa bakin kofar. Tabbas na ji muryar yayanka
yana magana ya ce "Well done, kun yi matukar kokari, ar
daman na san cewa in har zaku bi abin da na sanar da ku
zaku yi maganin dan iskan, yana can yana shan bakar
wahala, so nake yi sai na rataye shi sannan ita-ma ku gama
da ita, saboda haka kada ku sake ku bar ta ta kubuta. Shi ma
wancen shegen kuna lura da shi sosai ko?"
"Sosai ma kuwa." Suka amsa.
Ban taba sanin da mahaifina yake ba sai daga bayan
nan da ka kubuto daga wajen yayan naka ya 6oye shi. Kar in
kaika da nisa a haka na ci gaba da zama cikin wahala da
kunci, sannan ga dan karen azabar da T.j. ke gana mini ta
74
shorking dfin electric. Allah bai taba sa na kawo kubuta a
rayuwata ba, sai a ranar da zan kubutan, sai ranar na kawo
aka cewa tunda ba wai sun daure ni ba ne, me zai hana in
jarraba ganin ko zan yi dace.
Na fadi haka a zuciyata ne a 6oye, amma na san
cewa a zihiri wasa nake yi, sai kuma Allah ya sa a ranar na
dada sauraren hirarsu da yayanka in da yayi musu aike mai
nisa. Na ji dadin wannan aiken su da yayi matuka. Don haka
bayan tafiyarsu da kamar awa daya, sai na mike tsaye na fara
bin bangon dankin ina shafawa. A haka na dinga bi kusurwakusurwa, 6angare-Gangare ina neman makunnin wuta ban
samu ba. Na yi matukar jin haushin haka wanda hakan ya sa
na koma na zauna. Bayan 'yan mintina kadan sai nayi tunani
cewa ai ba za a rasa taga a dakin ba. Dan haka sai na sake
mikewa a karo na biyu na fara bin bango ina shafawa, ban
ankara ba kawai sai na ji na taßa katako, wanda hakan ya
sanar da ni cewa taga ce, nayi farin ciki matuka wanda ya sa
ba tare da 6ata lokaci ba na shafa dan na ji wajen budewa.
Take kuwa hannuna ya ci karo da sakata. Ban tsaya 6ata
lokaci ba na bude tagar, na leka tagar banda manyan
bishiyoyin da ke dajin ba ka ganin komai. Sai da fakin ya
waye da haske sosai, sannan na fahimci ba komai a dakin sai
wata 'yar guduma sai kuma tsani wanda duk gara ta cinye
shi.
Ba tare da 6ata lokaci ba na nufi wajen da tsanin
yake na dauka na nufi taga da shi. Bayan na zura tsanin da
kyar, sai na daka tsalle na dane tagar, take na fara takawa
tsanin ina sauka. Kafin na karasa sauka tuni tsanin ya karye
biyu wanda hakan ya sa na fada cikin wani tulin kara da aka
tara. Na fi minti biyar ban tashi ba, don tsananin tsami da
jikina yayi. Da kyar dai na kokarta na tashi na nufi daji
kuje ba tarc da na san inda na dosa ba.
a
75
Allah cikin ikonsa ya sa na lura da hanyar da
motarsu tayi sati don kai komon da suke yi. Da taimakon
Allah da taimakon wannan shaida na samu na fito har bakin
titi, inda na tsayar da wani dan tasi ya ki tsayawa. Wani dan
Асаба та na tsayar da shi, da har ya tsaya amma da ya lura
da ni sai ya kara gaba a guje. Haka dai nayi ta tsayar da
motoci da 'yan acaбa amma suka ki daukata, sai wani yaro
mai keke ne na samu na tsayar da shi ya dauke ni shi ma da
kyar ya yarda sai da ya ga wahala ce ta mayar da ni haka
sannan. To ka ji yadda Allah ya sa na kubuta daga hannun su
T.j."
Bayan da ta dakata, sai na ce "Lallai kin yi matukar
kokari, kuma Allah ya so ki da har bai hada ki da su T.j. ba a
yayin da kike kokarin gudu."
Ina gama magana su Moda suka iso ita da kakarta.
Murna ta hana ni ikon sanar da Uzaifat sauran labarina. Daga
bisani Magariba ta gabato daga nan Uzaifat tayi haramar
komawa gida, tayi sallama da kakar Moda. Bayan na rakata
inda tayi fakin din motarta Maxima a nan ma sai da muka
Bata lokaci sosai sannan muka yi sallama, sai da na ga
kulewarta sannan na koma cikin gida. Ina zaune akan kujerar
falo ina tunanin yadda zamu gudanar da soyayyarmu ni da
Uzaifat idan mun yi aure nan da kwańa biyu, sai karar Phone
ta katse mini tunanina. Na mike na nufi gurin na dauki
Phone din "Hello." Na fada ina gyara tsayiwuta.
"Uzaif ne?" Aka tambaya.
"Eh shi ne, wake magana?"
Dr. Idris ne ke magana daga NAGARTA, ana
bukatarka kayi maza ka zo." Yana magana cikin sauri da
garaje "kayi maza ka zo yanzun.."Ya sake maimaitawa.
"Lafiya? Me ya ...." Ban karasa ba ya ajiye kan
wayar.
76
Ina tsaye jikina yayi sanyi, hankalina ya tashi, ina
tunanin neman da ake yi mini. Ni dai na san cewa mahaifin
Uzaifat ya samu sauki sarai, kuma ya murmure, sannan
kuma Uzaifat yanzun ta bar nan, to neman me ake mini? Na
tambayi kaina.
Ina cikin tunanin ne ta bankado kofa ta shigo ta facd
kasa tana ihu tana kururuwa.
"Nafisat me ya faru ne?" Na tambaya
Maimakon ta ba ni amsa, sai wani ihunta saka, har ta
sa bebi Maryam da ke kwance akan kujerar ta farka daga
barcin da take yi. Take Moda ita ma ta fito tana magágin
barci.
mana.
"Haba Nafisat isanar da ni mana ko mene ne."
Ito It ina Moda ta sa baki "Mene ne Nafisat? Ki fada
Cikin matsanancin ha!i ta bude baki kamar zata yi
magana amma ina! Abin ya gagara.
"Wai yanzun mene ne amfanin haka ne? Shin ba
zaki sanar da ni ba?" Na fada ina mai daka ma ta tsawa.
Kaina kuwa banda sarawa babu abinda yake yi.
"Uzaifat ce tayi hatsari ta mutu."
"Me?" Na tambaya da ihu "Uzaifat tayi me? Ва
yanzun nan ta bar nan ba."
Haba ai tuni kafafuwana suka kasa daukata ban san
sanda na fadi kasa ina kuka ba.
Take Phone ya sake ringing, a wannan karon kasa
zuwa in dauka nayi, sai Moda ce ta dauka "Hello" Ta fafa a
sanyaye "Eh nan ne lafiya?"
"Daga asibiti ne." Aka amsa ta daya bangaren "Dr.
Idris ne.....
"What! Allah yayi mata rasuwa!" Take ta saki kan
wayar tayi kasa.
77
A daidai wannan lokaci ne ni kuma cikina ya bada
wani sauti wanda ban san abinda zan kamanta shi ba. Ban da
kuka babu abin da nake yi, ina fadin "Wayyo Allahna
shikenan Uzaifat kin tafi kin bar ni. Kai ban yarda ba Moda
ba ita ba се."
Take na mike nayi waje a guje na nufi motata. Su
ma su Nafisat suka biyo ni a baya. Ba mu tsaya a ko ina ba
sai NAGARTA. Muna isa muka ci karo da Dr. Idris tare da
mahaifin Uzaifat shi ma idanuwansa sun kada sun yi jawur.
Da ganin haka na saduda, na nemi izini gurin Dr. Idris ya bar
ni in je in ganta, ya kuwa_amince. Muna shiga dakin na ci
karo da gawarta kwance akan gado an rufe ta da zanin
atamfar da ta daura ta zo waje na. Na nufi wajenta ina kuka,
gaba daya na yaye mayafin na fara jijjigata ma fadin
"Uzaifat kar kiyi mini haka mana, ki bude idonki."
Da kyar aka fidda ni daga dakin.
domin akaita Bayan an suturta ta aka fauke ta
kushewarta, a lokacin na ga tashin hankalli domin ji nake yi
kamar na kashe kaina na huta. Addu'a kawai nake ta
kwararo mata, a lokacin da za a sanvata a cıkın kabarin
zuciyata ta sake karaya take na yunkura don kokarin kama
gawar wai kar a saka ta a cikin kabarin, jama'a suka rike ni
suna tayi mini nasiha akan in dangana domin ubangiji yafi ni
sonta kuma ya karbi ranta, saboda haka dai na hakura na
koma gefe ina zubda hawaye. Mahaifinta da kansa bai karasa
gurin ba, shi ma can gefe ya nema ya tsaya.
"Allah ya jikanki masoyiyata." Na fada yayın da na
fita daga cikin makabartar na nufi gida. Da ganin na shiga
gidan mata suka kaure da kuka domin gidan cike yake da
jamala: Sam ji nayi ba zan iya tsaya wa a wajen ba. don
haka sai na fita na nufi gareji na zauna ina tunanin tun tarkon
haduwata da ita. banda kuka babu abinda pakevi
78
"Ji wannan gayen har yanzun barci yake yi bai farka ba. Tashi ya isa haka barcin" Eng. Ukasha ya daka mini duka
a bay a.
Nayi firgigit na tashi ina fadin "Allah ya jikanki mdsoyiyata."
Gaba dayansu suka yi kasake suna kallona "Wanene
ta rasu kake yi imata addu'a har da su hawaye? Kai tashi dan
Allah kayi wanka mu wuce, ka san fa da zuwanmu kai da ya
kamata kayi sammako?" Dr. Aimana ya fada yana kallona.
"Af dan Allah Uzaifat ba ta mutu ba?""
Suka tuntsire da dariya "Uzaifat din da muka gani
yanzun ita da Nafisa zasu siyayya sagon Nasir mai Taba?"
Take nayi hamdala hade da godiya ga Ubangiji. Na
kwashe mafarkin da nayi na fada masu. Suka yi dariya. Dr.
Aimana ya ce "Ka kara mata tsahon rai ne kamar yaddä na ji
ana fada.
Na ce "To Allah yasa hakan ne."
Suka ce "Amin." Eng. Ukasha ya ce "Amma mu ma
da namu matan.
Allah ya bada zaman lafiya. A yau an daura auren
mutum uku, Allah ya sa sai mutuwa ka raba." Wani maroki
ne daga nesa yake wannan addu'a. Don tsananin jin dadin
wannan addu'ar sai da na sa aka yi kiransa na sanar da shi na
ba shi kujerar Makka. Daurin aure yayi albarka musamman
idan aka yi la'akari da dimbin jama ar da suka ziyarci wajen
kamar hawan arfa. Bayan an kammała ne muka zarce wajen
Lauching inda muka yanka cake. Anyi fati ya kai kala uku
hade da walima, sannan amare suka tare dakinsu. A ranar ne
ma muka kai ruwa rana da Moda akan sai ta ba ni baby
Maryanı amma sam ta ki, sai da na gaji na hakura na bar
mata, hade da fatan Alla ya raya mana ita.
Bayan mun yi sallah raka'a biyu ta neman zaman
lafiya, Uzaifat ta koma kan gado ta zauna, ni ma na nemi
gefenta na zauna. "Amarya kin sha kanhi." Na ce da ita ina
dariya.
Tayi murmushi ta ba ta ce komai ba.
"To kina son na baki sauran labarina da su T.j.?" Na
tambaye ta cikin tsokana.
"A'a ba na so.
"Saboda me?" Na tambayeta.
"Saboda zai tuna da azabar da ka sha, ni kuma ba na
son jin duk wani abu da żai daga maka hankali cos you are
special to me.
Na yi murmushi na ce "Haba?"
Ta ce "Honestly." Tayi shiru, can kuma ta се
"Kamata yayi ma daga daren' yau mu watsar da maganar su
T.j. gaba daya daga rayuwaru, sakayya sai ga Ubangiji."
Nayi ajiyar zuciyar na ce "Insha Allahu na daina
daga yau.
Tayi murmushi ta ce Thanks."
Bayan na nemi guri na kwanta, sai na janyo bargo na
lulluba "Taho nan ki ji wata magana mai zaki."
"Sai ka ce wata zuma. Ta fada a sanyaye kunya ta
hana ta motsi, har sai da na sanya hannu na janyo ta, ta zulle.
Na mike na nufi har inda take a tsaye, kan kace me na
ciccibo ta nayi kan gado da ita îna dariya, ita kuwa tana zillo.
Na janyo bargo na lullube mu zuciyata cike da farin ciki.
Karshe.
Mu hadu a littafi na gaba
KISHIYA TA CE.
80
"Wato duk abin da nake yi kana hura da ni,
kuma kanabina a gindi a gindi ko? To ka sani cewa ba
a ka kai labarı ba.” Ya yi huei tamkar wani rikakken
kumurci, ya ei gaba, "Tun da kagagari su T.J. Aini ba
za ka gagare ni ba, kuma ina tabbatar maka cewa idan
na kası eku na kashe banza.
Ina auне на кasa aiwatar da komai domin
tsoro duk ya bi ya ishe ni, addu a kiwum na ke ta
zubawa a zuciyatu, yayin da shi kuma yayana sai
kokarin daidaita bindigarsa yake yi domin ya harbe
111.
Nuifashina ya dauke a daidai lokacian da na
tsinkayi bakin bindigar yayana na bavazarar saitin
ruwan cikina...
Babu shakka Malama Binta ba karamin
kokari ta yi ba wajen ganin ta fitowa da al'umma
dimbin basira a fannin rubutunm zube na harshen
Hausa, ta kowane bangare, ta yi matukar taka rawa
a ladon soyayya fa gaskiya, salannan kuma
hannunksa mai sanda ne ga dukkan al'umma. А
gaishe da Binta Agege.
Reader Fagge
Marubucin KOMLAI RINTSI
AKARA CITY BOOKSHОР
08027614161
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This