wajenta da wajen
mahaitinta.
Duk wannan magana da yake yi banda hawaye
babu abunda ke zuba daga fuskarsa. "Nafisa ke ma ki
Xafe mini dan Allah. in Allah ya so zaki gane
mahäifinki ko da wannan tsagu da ke wuyanki ko da
sarkar hannun da muka tsince ki da shi. tana wajen
Hajiva ga shi kuma yadda al'amari ya kasance na
Bat Karasa ba ya fashe da kuka yana mai daga
muryat kamar fan yaro "Allah ka yafe min, ubangiji ka
yafe minı zunubaina. Üzaif dan Allah ku yafe mini. Ku
yafe mini Nafisa....
Banda kuka babu abinda muke yi, na kasa ua
bude baki in yi masa magana.
"Astagfirillah, Astagfirillah. Astagtirillah. Allah
ka yafe mini, Allah ka yafe
Bai Rarasa ba wani dan sanda ya shigo wajan.
Da shigowarsa na san cewa lokacin tafiyarmu ya ki.
Kan ka ce Kala tuni yavana ya mike tsaye yana,fadin
"Ku gafarce....." bai Karasa ba va fadi Kasa wanavas ran
yayi halinsa.
51
** *
Allah ya raya Maryam, da gama radin suna
bayan sallar Asuba sai aka nemo masu hada gawa.
Kamar Karfe bakwai na safe aka yi jana'izarsa. Bayan
"yan karbar zaman makoki sun taru a kayi masa addu
da sauran musulmi da suka riga mu gidan gaskiya, daga
nan jama'a suka watse.
Mun jima kwarai kafin juyayin mace-macen da
aka yi mana hade da fargaba ya sake mu.
Yau kusan wata uku kenan. Dukkan su suka futo suna
murmushi hade da fadin "La! har ka maida Hajiyar
gida?"
Na: amsa musu a yayin da suka zazzauna akan
makekiyar kujerar da ke falon "Tun dazu na dawo, ai in
fada muku kafin Hajiya Inna ta bar ni na taho sai da
nayi da kyar tukunna, ban da kuka babu abin da take yi
mini. Ta ce dai kun hana ta bebi Maryam."
Moda tayi dariya sanían ta ce "Haba Uzaif ya
za a yi mu ba wa wannan tsohuwar wannan tsaleliyar
yarinyar?
Uzaifat ta dauka "Wallahi gaskiyarki gara dai ta
zauna a wajenmu."
Nafisat da ke zaune a hannun kujera tayi ajiyar
zuciya hade da fadin "Ni wallahi duk rashin saduwa da
mahaifana shi ya dame ni, domin kuwa bacin yawon da
muke yi da ku a nemansu ni ma na yi har na gaji, kuma
na gane kwatançen da Hajiya tayi mini, na je har gidan
aka ce mai man kulin ta rasu, Sannan bolar bayan gidan
naku an yi gidaje a wajen. Wallahi ni ban san inda zan
sa kaina ba.
a
52
Na nisa na ce da ita "Kar ki samu damuwa Insha
Allahu zamu kasance masu kara baki kwarin guiwa
domin kuwa farin cikinki shi ne namu." Na lura cewa
maganata ta faranta mata rai, don haka sai na ci gaba
"Zamu sake komawa gidan mai man kuli mu yi bincike
akan ta dalla-dalla." Na mika hannu na amshi bebi
Maryam daga hannun Uzaifat. "Bebi Maryam how are
you today?"
Ta bamale baki tana dariya a yayin da nayi mata
wannan tambaya. Gaba daya muka kwashe da dariya.
"Kawo ta ka gani za ta yi dariyar da tafi haka
idan nayi mata rawa da waka."
Na mikawa Nafisa ita a yayin da na mike ina
mai tambayar Uzaifat lafiyar mahaifinmu.
"Eh, ya samu sauki kwarai da gaske har labari
fa yake ba ni." Ta amsa tana mini murmushi mai kara
kwarin soyayya.
* * *
Nafisat ta kalli 'yan tsagun da ke wuyanta a
madubi ta ce "Kun san wani ikon Allah? Wallahi ban
taba lura da wadannan tsagun ba fa."
Uzaifat ta ce "Haba ai ñi tuni na san da su,
domin suna daga cikin abubuwan da suka karawa
wuyanki kyau."
Tayi murmushin yabonta da aka yi.
Na ce "Sai mu hanzarta zuwa can gurin gaida
baban namu daga nan sai mu karasa gidan mai man
kuli."
Na sa hannu na amshi bebi Maryam wacce ta ci
ado da jeans complete sannan tayi bulbul abinta kamar
53
mai shan mama, ai dole tayi bulbul in ba haka ba kuwa
mene ne amfanin Dr. Uzaifat? Kana kallon ta ma ba
zaka ce da ita bakwai ni ba.
Bacin fitarmu daga gidansu Uzaifat ne muka
dauki hanya zuwa 'Faltinga'. Da isarmu gidan muka
riske wani tsoho a zaune akan tabarma. Bayan mun yi
masa sallama sai muka yi masa tambaya cewar muna
bukatar ganin daya daga cikin yaran da mai man kuli ta
rika. Ya sanar da mu cewa da daya kawai ta rika wato
jikanta.
"Baba dan Allah ko zamu san inda wannan jika
nata yake?"
"Eh to". Yayi tari hade da kaki. Bayan ya tofar
sai ya ci gaba "Shi wannan jika nata yana can Abuja da
zama, amma kuma ya kanzo nan duk bayan sati, domin
duba lafiyar mahaifiyarsa.
Bayan sauraron bayaninsa saia na yi masa
tambaya da cewa "Idan ba zaka damu ba dan Allah ina
son ka sanar da mu ranar da zai zo.'
Yayi tari mai tsayi sannan ya gutsiri goro ya
tauna "Gaskiya ba na ce ga ranar da zai zo ba, domin
kuwa ya kwana biyu bai bullo wajena ba."
Cikin garaje Nafisat ta dauka da "To yanzun
dan Allah idan zai yiwu kayi mana kwatancen gidan
יי mahaifiyar tasa."
* ** *
Mun yi fakin a kofar gidan wanda yayi matukar
dace wa fantin da akayi masa. Bayan sallama da muka
yi. mai gadin wanda a zahiri bahause ne amma yayi
kama då bafillatani.
54
"Don Allah Hajiya-Mai-Duka muke nema." Na
fada a lokacin da yake gyara tsaiwarsa.
"Eh babu mai duka sai Allah." Ya fada yana
dariya "To ta san da zuwanku ne ko kuwa?"
Nafisat ta gyara mayafin da ta rataya a kafadarta
sannan ta ce "Ba ta san da zuwanmu ba, amma ka iya
sanar da ita cewa daga gidan mahaifiyar mijinta muke
wato Faltingo."
"A sannunku da zuwa ku shigo mana, ai shi ma
Hafiz din ya zo dazun nan amma ya dan zaga gurin
abokai."
Mun yi farin ciki kwarai sosai da jin wannan
albishir. "Shakka babu wannan Hafiz din means alot to
us." Na fada a bayane wanda hakan ya sa mai gadin
yayi mini wani kallo wanda yake bukatar in fahimtar da
shi wani abu game da turancin da nayi. Nayi masa
kallon kai magulmaci ne, sannan na kau da kaina daga
kallonsa.
Mun zazzauna akan kujeru da aka shirya a falon
kasa, a yayin da mai gadi ya sauko daga matattakalar
"Ku jirata minti biyu tana zuwa."
Bayan godiya da muka yi masa ne ya fice waje.
Kyakkyawar kafarta ce ta fara yi mana sallama
sannan sauran jikinta. Fara ce gajeriya wacce goshinta
ya sha fashi siriri wanda yayi matukar kara mata kyau.
"Sunnunku bayan Allah." Ta fada tana kokarin zama.
"Yawwa sannu ina yini?" Nafisat ta fada tana
fadada bakinta zuwa murmushi.
Bacin sauran gaishe-gaishe, ta nemi ta san ko su
waye mu? Na nisa na ce da ita "Da yake abu mai wuya
55
(
ne ki kasa ganc bayaninmu in dai har kin sauraremu
sosai. Ba zamuce mun sanki ba, domin kuwa babu
wanda ya taba ganinki a cikinmu. Amma idan baki
manta ba shekaru ashirin da foriya da suka wuce kin yi
wata kawa Hajiya Ubaida wacce take kamar aminiya a
gareki." Na tsaya a lokacin da nake kallon kwayar
idonta.
Ta dan yamutse fuska wanda hakan ya sanar da
ni ta zurfafa cikin tunani. Ganin zata 6ata mana lokaci
yasa na kudiri niyyar fahimtar da ita cikin sauki.
"Hajiya kada mu saki a duhu, bari in sanar da ke abun
da ke tafe damu dalla-dalla. Kamar yadda na sanar da
ke cewa kin yi aminiya a da H.Ubaida wacce kika
canja mata suna da Kawas a wannanlokaci......."
Ban Karasa ba ta zaro idanu ta dakatar da ni
"Af! Kawas kake nufi matar A.M. Sadiku?"
"Shakka babu ita."
"Au ai Allah yayi mata rasuwa."
"Subhanallahi." Gaba dayamu muka fada.
A gaskiya ban ji dadin wannan zance ba, domin
kuwa na so a ce tana raye domin ta ga abinda Allah ya
maida Nafisat.
"Allah ya jikanta." Na fada, sannan na ci gaba
"ko da yake dama ba saboda ita muka zo wajen ki ba,
mun zo ne domin kiyi mana kwatancen gidanta. Ko da
yake ya kamata idan har da dama mu tafi tare da ke.
Nayi mamaki da ba ki tambaye mu wanda ya turo mu
wajeki ba, amma duk da haka zan yi miki bayani
yanzun. Idan ba ki manta da Hajiya Maryam sirikar
Alhaji Mubarak matar Alhaji Yusuf ba, to zaki iya tuno
56
da duk wani bayani da zan nema daga wajenki." Na ja
na tsaya, domin na ba ta damar magana.
Bayan ta nisa sai ta ce "Haba ni kuwa na san
Hajiya Maryam farin sani, dama tana nan garin?"
"Tana nan garin mana, amma ita ma Allah yayi
mata rasuwa.
"What" Ta fada a yayin da hawaye suka
bakunci kuncinta "Allah sarki matar arziki, kai Allah
ya jikanta da rahama." Ta fada tana sharar hawaye.
"To tun kafin ta rasu ta bar mana wasika mai
kunshe da yanayinki, sannan tayi mana-kwatancen
gidan sirikar ki wato mai man Kuli wanda tana ganin
cewa ta hanyar wannan mata zamu fi saurin saduwa da
ke. Tayi mana bayani cewa ke da Kawas aminan juna
ne, sannan kuma kuna mutunci dà ita kwarai da gaske.
Hajiya idan ba ki manta ba a baya dillanci kike yi
wanda hakan ya sa kike zuwa gidanta talla. Wanda
hakan yasa wata rana bayan zuwanki wajenta kika ci
karo da wata jaririya, a wannan rana kun yi rigima sosai
akan jaririyar sannan daga baya kun shirya akan wasn
makudan kudi da tayi miki alkawarin zata baki. Kafin
ta baki sai da kika shaida mata cewa wannan jaririya
'yar A.M. Sadiku ce sannan kuma Kawas ce ta sa danki
Hafis ya kashe ta a yayin da ke kuma kika hana shi
sannan kika sanar da shi cewa ya je bolar da ke bayan
gidan mahaifina ya ajiye sannan ya san yadda yayi ma
gadi ya fito ya ga wannan jaririya.
"Babu shakka anyi haka." Ta fada tana mat ba
da gaskiyar ta akan maganar.
57
Ba ni ba har su Uzaifat sai da suka ji dadin
rashin musawarta. Na ce "Ta sanar da mu ccwar da
farko ta ba ki Naira dubu dari uku sannan kika dada
dawo mata da nufin ta kara miki. Kafin ta ba ki sai da
kika kika yi mata alkawarin ba zaki kara dawo mata ba,
kuma ba zaki taba fadawa kowa ba hatta Kawas. Bayan
haka ne ta kara miki Naira dubu dari biyu. Daga sannan
ba ki kara dawo mata ba, ita ma kuma ba ta kara
ganinki ba, wannan sirri ne a tsakaninki da ita a wannan
lokaci, amma yanzun ya zama open secret domin kuwa
yarinya ta gane cewa ba mahaifanta ba ne, saboda haka
yanzun muke son dan Allah ki kai mu gurin
mahaifanta.
"Babu komai, yanzu ina yarinyar take?" Tа
tambaya.
"Gata nan." Na yi mata nuni da Nafisat.
"Sannu 'yan mata, ya sunanki?"
Nafisat ta kalle ta hawaye na zuba daga fuskarta
"Sunana Nafisat, na gode kwarai da taimakon da kika
yi mini a rashin bari a kashe ni."
Hajiya Mai-Duka ta tashi ta je gaban Nafisat
idonta na zubda hawaye ta ce "Don Allah ki gafarta
mini domin kuwa da ni aka hada komai, sannan kuma
cetonki da nayi ba wai tsakani da Allah na yi ba, nayi
shi ne domin na samu kudi wato kenan na butulcėwa
Kawas, kuma ba komai ya sa tayi miki haka ba sai don
tsananin kishin da ke tsakanin mahaifiyarki da ita.
"Ni kuwa mai ya sa kishin mahaifiyata ya shafe
ni?" Nafisat ta tambaya.
"Yanzun kuwa zaki ji komai."
58
* ** *
Bayan ta koma kan kujera ta zauna, sai ta fara
ba mu labari da cewa "Duk da zafina da iya kissata
wannan bai hana na ji tsoron H. Ubaida ba, domin kuwa
mace ce mai zaifin bala'i tare da saurin fushi. Ya
kasance cewa mahaifiyarki ita ce amaryarta. Mahaifinki
ya dade yana neman 'ya mace a sakamakon duk
'ya'yansa-maza ne. Ita Kawas ta haifi maza biyar amma
uku sun rasu saura biyu Haruna da Kabir, sannan
mahaifiyarki ta haifi 'ya'ya hudu duk da ke. To amma
kafin ta haife ki ta dade sosai har hakan ya sa
mahaifinki ya zata haihuwa ta tsaya musu ne. Kwatsam
sai ga mahaifiyarki ta fara laulayin ciki da ganin haka
sai gaba mai tsanani ta kullu a tsakaninsu har ta kai sun
daina wa juna magana.
Kawaş tayi-tayi ta zubda cikin amma abun ya
gaga, har Allah ya sauki mahaifiyarki lafiya. A ranar da
ta haife ki wanki wanda kike bi ya rasu a sakamakon
wawan marin da ya sha a wajen Kawas, don ya je da
gudu ya fada mata cewa an haifarwa baba yarinya
kyakkyawa. Tayi masa marin ne har sai da ya fada kan
tebir din da gilas da ke falon, fuskarsa ta yanyanke а
sakamakon farfashewar da gilas din yayi wanda yasa
hakan ya zo da karar kwana." Ta dakata sannan ta cі
gaba "Tun ranar da aka haife ki Alhaji ya dauki ransa
gaba daya ya dora kanki. Hakazalika ya rinka kashe
kudi kamar daga sama ya same su. Hakan ya
bakantawa Kawas rai sosai har ta neme ni da shawarar
yadda zata yi. Ban yi niyyar ba ta muguwar shawara ba,
amma ganin yadda take kallona kamar wacce na azurta
59
mahaitinki da 'ya mace ya sa na ji tsoron ta na ce da ita
a sace ki kawai a kashe. Hakan ya faranta mata rai
matuka har va sa tayi mini kyautar da ba ta taba yi mini
ba. Ana sauran kwana biyu a rada suna mahaifiyarki ta
Kamu da matsanancin ciwon eiki wanda ya sa ta fita
hayyacinta. Bayan an kaita asibiti sai aka ba ta gado.
Dan tsananin son da Alhaji ke yiwa wannan jaririya sai
ya ki bawa kowa ita ya rike a barsa. A wannan rana sai
da Kawas tayi kirana ta sannar da ni cewa wannan ita
ce damarta ta Karshe idan kuwa ta wuce ta to ba zata
samu wata damar ba. Dan haka muka yanke shawarar
cewa mu hada baki da Doctor din asibitin a karbi 'yar a
sanar da shi cewa idan ba tana kusa da babarta tana ba
ta nono ba to ita ma 'yar zata samu illa, jin hakan shi ya
sa Alhaji bayar da jaririyar.
Bayan barin mahaifinki asibiti ne Kawas ta bani
jaririyar ta ce na kaita da daddare in sa dana Hafiz da
abokan shashancinsa su kai ta can wurin katon kwalbati
su kashe ta su jefa ta ciki. Ta kawo kudi dubu talatin ta
ba ni, ta baiva likitan ma dubu ashirin da biyar bayan
yayi mata alkawarin zai bata motacciyar jaririya. Bayan
tafiyarta likitan ya ba ta jaririyar, take ta zarce gida ta
sai likkafani ta sanya yarinya a ciki ta ajiye gefe guda.
Da Alhaji ya dawo ya ji labarin mutuwar 'yarsa yayi
bakin ciki sosai kai har da kuka. Ni kuwa bayan na je
gida sai na nemi Hafiz da yake Allah ya hada ni da
sangartaccen da mugu marar jin Magana, sai na sanar
da shi abin da nake so yayi mini. To kin ji dalilin da ya
sa Hajiya Maryam ta same ki. Da ma sai da na yi masa
kwatance da gidan sosai, kuma na yi masa kashedin
60
kada ya kuskura ya bari ki mutu, kuma ya tabbata ya ga sanda ya dauke ki sannan ya bar wajen. Nayi haka ne domin samun wasu kudi daga wajen Hajiya Maryam sakamakon yawaita fadin tana sha'awar ta ga ta haihu.
Bayan ta gama sai ta kalli falonta sama da kasa ta ce "Ga shi kuma Alhamdulillahi kudin Hajiya Maryam ya zame
mini gata, ya canja mini rayuwa gaba daya, domin da su na
gyara dana Hafiz shi ma ya zama mutum sannan kuma ya
zama babban masana'anci a sakamakon makarantar da na
komar da shi da rokon Allah. Sannan da su ni ma na dinga
kasuwanci ina juya su har suka zama miliyoyi. Dalilin da ya
sa na kaurace mata a wannan lokacin shi ne kada ganina ya
dinga zame mata tashin hankali, Allah ya ji kanta, sb "Amin" Duk muka amsa.
Daga nan ta sanar da mu cewa tana zuwa ta raka mu.
Bayan hawanta sama da kamar minti hudu, ta fito hannunta
rike da mayafi. Tana saukowa aka yi sallama aka shigo
falon. Wani farin saurayi mai matukar kama da ita ne ya
shigo.
Af Hafiz har ka dawo?" Ta tambaye shi a yayin da
take kokarin yafa mayafinta.
"Na dawo Hajiya, baki kika yi ne?" Shi ma ya
tambaya.
'Ya'yana ne." Ta fada tana murmushi
Bayan yayi mana sallama sai muka gaggaisa, Baila
"Hafiz ba zama zaka yi ba, ina so ka kaimu gidan
A.M. Sadiku yanzun." Ta ce da shi.
"A.M. Sadiku dai wanda na sani a da? Ya tambaya,
"Ba shakka shi."
"Anya suna cikin gidan nan na shi har yanzun?" Ya
sake tambaya. s neb ainided ingеd "Ina zaton hakan." Ta amsa masa,
361
"Bakin naki za a kai?"
"Eh su za a kai, kai dai labari ne mai tsaho zan sanar
da kai sai mun shiga mota.
Mota Kirar Intergra ce keyi mana jagaba. Ta ja ta
tsaya daidai lokacin da muka isa gindin wani katafaren gida.
Bayan fitowarmu daga motocinmu Hafiz ya kwankwasawa
mai gadi kofa. Ya dauki tsahon wani lokaci kafin ya bude
Kofar. Bayan Hafiz yayi masa sallama sai ya nemi yayi masa
sallama da mai gidan.
"Wane mai gidan kuma?" Mai gadi ya tambaya yana
mai shakka.
"Wannan dai mai gidan mana A.M. Sadiku." Hafiz
ya sanar da shi.
"Ahaf, ka ce ba ka san ya kwanta cuta ba?"
Sai da dukkaninmu muka dubi juna a yayin da muka
ji wannan magana.
"Allah sarki yaushe kenan." Hajiya Mai-Duka ta
tambaya.
"Haba yau kusan shekara biyar da wasu 'yan
watanni." Ya fada yana sosa keya. "Amma ku shigo in kai
ku Bangaren matarsa.
Bayan fitowar matar A.M. Sadiku daga cikin uwar
dakinta sai muka gaggaisa. Tabbas duk hankalinta yana kan
Nafisat ne a yayin da ita ma sai tayi kuri tana kallonta.
Hajiyar a zahiri kyakkyawa ce ainun, domin kuwa zaka ga
duk da tsufanta ba ta da siffar Allah ya isa. Can daga baya
sai Hajiya Mai-Duka ta nisa ta ce "Hajiya baki gane ni ba
ko?"
Hajiya Yaha ta kalli H. Mai-Duka a tsanake, daga
bisani bakinta ya dan fadada zuwa murmushi take kuma ta
fara darıya tana fadin "La!! Mai-Duka ke ce kuwa a duniyar
62
nan?" Tana fadin haka ta mike ta nufi H. Mai-Duka ta
rungume ta.
Duk wannan abu da suke yi babu wanda ya ce
kanzil daga cikinmu. Su kuwa banda murna babu abin da
suke yi. Bebi Maryam kuwa tunda muka baro gida ba ta
farka daga barcin da take yi ba sai yanzun.
10
RANAR FARIN CIKI
Bacin mun nutsu H. Yaha tasa mai aikinta ta kawo
mana Five Alive mai matukar sanyi, kowannenmu ya
kurkurba. Daga bisani H. Mai-Duka ta nisa ta ce "To Hajiya
Allah ya kawo mu ranar farin ciki, ranar da ya cancanci in
nemi gafararki. Ina rokonki da Allah ki yafe mini akan
abinda nayi miki wanda ba ki san da shi ba. Ina san ki ba ni
aron hankalinki, sannan ki kai zuciyarki nesa. Idan ba ki
manta ba shekaru ashirin da doriya da suka shude kin haifi
'yarki mace kyakkyawa wacce a rashinta Alhaji ya kamu da
ciwon hawan jini kuma kuka fita daga kamanninku gaba
daya. Abun da ya faru ne.....
Takę ta fara ba ta labari kamar yadda ta sanar da mu
tana ba ta labari ita kuwa Nafisat sai kallon mahaifiyarta take
tana zubda hawayen farin ciki.
Gamawar H. Mai-Duka ke da wuya ta nuna Nafisat
ta ce "Yanzun dai ga Nafisat Allah ya raya miki ita, da fatan
zaki yafe mini."
63
Тарн даma fadin haka Hafiz ya durkusa уa се
"Hajiya dan Allah ni ma ki yafe mini kuruciya ce ta sa ni
nikata hakan."
"Haba babu komai ai hakan ma da kuka aikata kun
nikata alheri tunda baku dauki ran yarinyar ba, sannan kuma
rashi ne ya saku aikata hakan," Hajiya Yaha ta fada tana
sharar hawaye.
T'sam! Nafisat ta mike ta nufi mahaifiyarta, da
zuwanta ta fada kanta tana kukan farin ciki.
Lokacin da suka nutsu ne mahaifiyarta tayi mana
godiya Kwarai, sannan tayi ma Hajiya Maryam addu'a ta gari
da kuma yayana. Da gamawarta ta amshi bebi Maryam tayi
matn addu'a a kunnenta, sannan ta ci gaba da yi mata waки.
Jmmwa kadan da yin hakan ta nemi da mu je Bangaren
mabaitin Natisat.
Da zuwanmu dakin muka tarar da wasu maza su
hudu n zazzaune suna bira. Shi ma dattijon da ke zaune akan
gondo yana sahün hirar tasu, Hannun dattijon da ya dan motse
Endan a yayın da sauran jikinsa bai yi kama da na mai jinya
ba. Bayan mun gaisa dattijon ya kalle mu daya bayan daya,
yanp żuwa kan 11, Mai-Duka ya shaida ta "Kar dai a ce MaiDoka dillaliya ce wannan."
Ta fan yi murmushi yayin da take amsa tambayara
Athap or ye оanа."
Yayı murmushi shi ma ya ce "A'a ashe rai kan ga rai
Mm Duka? Yn fashe da dariya.
"IHakn abun yake Alhaji, wallahi ba na zama a garin
me osgt shн уn sа." Та fada tana kallonsa,
A'a wannan ba hujja ba ee Mai-Duka."
Lo Alhaji nayi laifi a gafarce ni, ya kuma aka jí da
bakmi
Mat yri snu ma'niki." Ya amsa ta'aziyyar,
64
Hajiya Yaha ta kalli mijinta tare da sauran samarin
da ke dakin, sannan tayi ajiyar zuciya,"Alhaji yau fa zaka ji
abun da zaka yi mamaki Rwarai da kuma farin ciki."
Ya daga kai ya kalle ta "Kamar me fa?" Ya
tambaya.
"Ga 'yarka mace tilo da kake da ita Allah ya dawo
maka da ita." Ta nuna Nafisat.
Gaba daya ya sukurkuce yana mai tambayar "Ban
gane manufarki ba."
"Zaka ji komai yanzun a bakin Mai-Duka, dan an ce
waka a bakin mai ita tafi dadi."
Ba tare da 6ata lokaci ba H. Mai-Duka ta kwashe
duk abinda ya faru a baya ta sanar da shi, sannan ta hada da
neman gafara. Mahaifin Nafisat tare da yayyenta musamman
ma wadanda suke uwarsu daya wato Isma'il da Ahmed sun
yi farin ciki matuka hade da mamakin faruwar hakan. Shi
ma Haruna yayi murna kwarai wato kanin Kabir. Alhaji ya
nisa ya ce "Amma kuma abinda mamaki yake ainun. Na
gode kwarai dillaliya kuma na yafe muku har ita Hajiya
Ubaidan Allah kuna ya jikanta." Sannan muma yayi mana
godiya tare da yiwa yayana da matarsa addu'ar samun
aljannatul-Firdausi. Daga bisani Hajiya Mai-Duka tayi mana
sallama da zummar zata tafi. Take Alhaji ya sa Haruna da
yake shi ne babba a cikin samarin da suke zaune ya dauko
masa takardar cak a daki. Take ya sa ya rubuta zunzurutun
kudi na dubu dari uku ya baiwa Hajiya Mai-Duka da danta.
Tayi godiya marar misaltuwa sannan suka fita, mahaifiyar
Nafisat na biye da su. A daidai lokacin da suka bar dakin ne
Nafisat ta dube ni ta ce da ni "Yaya dubi wuyansu yaya
Haruna ka gani."
Ina kallon wuyan su kuwa idona ya ci karo da tsagun
dake wuyansu. Tabbas sai yanzun na tabbata gadon gidansu
65
kenan. Hajiya mahaifiyarda ke thigia dakin fuskaz
cike da fara a. Nafisat ta tura Hn takana ta ciro ata
'yar karamar sarka mai kýélrkai tana daya d22
cikin alamomin da Hajiya Marym tsaka a čikin bakar
ledar da muka dauko a cikin dirowarta. Sannan ta senar da
mu a wasikarta cewa da ita aka tsinci Nafitata sakamakon
sa mata shi a hannu da aka yi, lezle anu1
"Momi kin t ta huna wa
mahaifiyarta.
Ta amsa tana nazarmtaWanhan ai kamar sarkar da
ka siyo daga umara Alhaji." Hajrya ta fada tana mai mika
masa
-Shakka babu ita ce, Kih
gaa
ba ia styanta nayi ba
wani balarabe ne da muka yi haji taleya ba ni ita wai in
kaiwa "yata, kin san kuwa baki haife'ta ba a lokacin." Ya
fada yana jujjuya sarkar
Muna isa gida muka tarar an yi manyan haki Dr.
Aimana ne zaune akan motarsa kirar HALA fare de
abokinsa. Mun yi farin cikin ganin juna hatuka ba tare da
mamakin ganinsa ba, domin kuwa ya yi manz alkawarin
ziyartarmu. Da yake Magariba ja kawo kai ba mu tsava bata
lokaci ba na bude kofar gida Bayar mun yr fakin đĩn
motocinmu a cikin garejin gidan, sai muka nufi cikin gidan.
Sai bayan da kowannenmu ya nutsu sannan muka
fara hirar yaushe gamo, sai bayan da su Kafisat suka yi
wanka sannan suka shiga kicin domii girka mana mana dina. Da
gama girka mana abincin suka kai dining suka shirya. Duk
wannan kai komo da suke yi idon Dr. Ailfiana na kan Moda.
RED
Sai da muka zazzauna akan dining din. sannan ygaba daya
muka ji Nafisat da wannan bako suh haga baki wajen cewa
"La!!"
66
Sannan Nafisat ta hada da cewa "Dama kai ne ban
gane ka ba tuntuni?"
Shi ma bakon ya amsa da "Ni ma wallahi ban ganc
ki ba ko kadan sai yanzun.
Nafisat tayi dariya ta ce "Ashe rai kan ga rai dan
Fulani ya ga furar gero.
Dukkansu suka kwashe da dariya. Mu dai mun yi
saroro muna kallonsu. Bakon ya kalli Dr. Aimana ya cé
"Gogan ga fa madam din da nake fada maka nan."
Dr. Aimana yayi dariya shi ma ya ce "Au Nafisat da
ma ke kika kusan sa aminin nawa gangarawa?"
Nafisat tayi murmushi kunya ta kama ta. Bayan wani
lokaci ne ta sanar da ni cewa shi ne mutumin da ya rage mata
hanya a lokacin da motarta ta mace a tsakiyar daji "Ka san
lokacin ina yawon neman Uzaifat."
"Ba shakka an yi haka, da ma shi ne?"
"Eh" Ta amsa.
Sannan muka ci gaba da cin abincin. Bayan mun
gama cin abinci ne Dr. ya tashi ya nufi kofar fita "Engincer
ina zuwa" ya ce da amininsa.
"Ba laifi" Ya amsa daga nan aka fara kallon soyayya
tsakaninsa da Nafisat. Dr. ya shigo falon hannuwansa rike da
ledoji wadanda ban taba ganin irinsu ba. Bayan ya zauna sai
ya miko mini daya ya ce "Sirikina ga taka tsarabar Holland
din."
Ban yi mamakin jin hakan ba, domin kuwa ko yaro
ne yake tare da mu zai fahimci cewa akwai so da kauna
tsakaninsa da Moda. Ya sake mikawa Uzaifat tata ledar,
sannan ya mikawa Engineer leda daya, da mika masa ya
kalli Nafisat ya ce "To Honey ga taki tsarabar."
Kunya ta hana ta karba har sai da ya mike ya je daf
da ita ya mika mata sannan ta amsa. Shi ma Dr. da kansa ya
67
matsa kusa da Moda yayi murmushi hade da cewa "Have it
my soul, wannan ita ce tsarabar da nayi miki, domin na nuna
miki kaunata a gareki a fili I Love U."
Moda ta sa hannu ta karba "Thanks alot." Ta ce da
shi.
"Don't mention." Ya fada yana kallonta a daidai
lokacin muka kalli juna ni da Uzaifat muka yi murmushi mai
karfafa zuciyoyin masana'love. Sai da suka kwana sannan
suka yi haramar