An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
REAdeN's Media FagGe
Rashin MutunciBinta Rabi'u Ali
Laraba Agage
Copyright : B.A.R.A. Agege.
Hakkin Mallaka (m): B.A.R.A. Agege.
Shekarar Bugawa2007.
BUGAWA A COMPUTER
B.T.H. COMPUTERS
080-62218701
GODIYA DA MANUFA
Alhamdulillahi Rabbil Alamina. Wassalatu was
salamu ala Asharaful Mursalin Sayyadina wa
Nabiyyina Muhammad S.A.W. Godiya mai yawa ta
tabbata ga Ubangijina mai kowa mai komai, wanda
yayi ni yayi ku, sannan ya kwararo mana da manufa
daban-daban a zukatanmu. Ina godiya ga Ubangiji da
ya nufe ni da rubuta ci gaban wannan littafi mai suna
RASHIN MUTUNCI wanda kuka dade da karanta na
dayansa, a dalilin wata 'yar matsala da na samu wanda
nake fatan Ubangiji ya tsayar da ita kenan.
Bayan haka manufata ga rubuta littafin nan yana
da yawa, to amma wanda yake shakiki a ciki shi ne, ba
wai na rubuta shi ba ne saboda wani ko wata, sai dan
kawai abinda ke faruwa a al'ummanmu 'A YAU'. Na
rubuta RASHIN MUTUNCI nc domin fayyace gaskiyar
abinda ke faruwa a tsakanin 'yan'uwa kai hatta
wadanda suke ciki daya wanda kansu na wallafa
wannan littafi. Kar jama'a su ta'allaka akan cewa sai
lallai 'yan'uba ne ke bakin cikin junansu, wanda sam!!
ba haka ba ne. Saboda haka jama'a sai a lura a gane
cewa zumunci ya fi gaban wasa, in ba a yi sa anan
duniya ba, to wallahi ża'a yi sa a lahira. Da fatan duk
wanda ya karanta littafin nan zai dauki abubuwan da zasu yi
masa amfani a ciki yayi aiki da su, ya watsar da wanda ba su
da amfani, domin kuwa no one is perfect no matter how
expert you may be. Sannan kayi tunanin karshenka in har ka
kasance mai irin halin Alhaji Yusuf.
TUKUICI GA:
Kannena Zainab, Hafsat, Sani, Salis Tahir Mande.
SADAUKARWA NE GA:
Kannena Amina Rabi'u, Sagir (M.S), Yakub,
Muhammad, Hassana, Husna Tahir Mande.
KYAKKYAWAN FATA GA:
Iyayena H.Binta Tahir Mande(Asabe), A. Tahir Mande, da
A.Bashir Mande, dawana Auwal Tahir Mande.
KYAUTARWA NE GA:
Hajiya Hauwa'u Bashir Maude (Naira Power), da
amarvarta Anty Amina, da yaransu gaba daya, Allah ya raya
mana su, aminMUSAMMAN DON:
Yarana Tahir A. Rabi'u (MD), Ibrahim Rabi`u
Halilullahin Furera: Rabiu (lhsan Smatt Eondoner), sannan
mahartinsu Alhagi Rabr'u Ali Usman (Sweetheart).
GODIYA TA MUSAMMAN GA:
Kawayena Shafiya Alhaji Tanko Mai Rago (Mrs
Bakure), Hadiza A. Lawan (Maman 'yar Baka), Hadiza Sani
Shuaibu (Hajiyayye), makociyata Hajiya Nana A. Papi
(Maman Ummita). Bana iva suya na manta da albasa Hajiya
Binta Sani Shuaibu ilnnan Fahad) babbar yaya kenan, Allah
ya bar mana ke amin. Ubangiji va kara zaman lafiya
Sakanınkr da kishiyarki Hajiya Binta Sani Shu`aibu (Inna
Haw Ya raya maku zmyarku. Hajiya Binta Rabi'u
Shu athu Innai bán mnua da ke ba. t bangin ya Kata miki
hakur kkka yi. Ya sa kuma ajanna ce
akomarsa)
3
5
ogi hade da radadin da suka addabe ni ne yа Z
sanya ni na farka daga wahalallen barcin da nake
yi, sam na kasa bude idanuwana saboda nauyi da
suka yi mini, sannan hankalina gabaki daya a tashe
yake a dalilin mummunan mafarkin da nayi. Tabbas
mafarkin ya firgita ni ainun, domin ganin yadda
mutanen biyu da suke tsaye a kaina suke shirin zare
robar da aka sanya mini a baki hade da hancina ta
oxygen domin taimakawa numfashina. Kuma suna
sanye ne da kayan likitoci. A zahiri na farka amma
zuciyata ba ta daina dukan uku-uku ba. A hankali na
fara kokarin bude idanuwana da tuni na dan fara jin
saukin nauyinsu, ga mamakina sai kuwa na ga mutaen
nan biyu a tsaye a kaina fuskarsu a Taure. Baki dogon
ciki yana rike da sirinii In, yayin da gajeren ya mika masa
wata yar karamar kwalba mai dauke da ruwan magani.
Gabana ya yanke ya fadi, na kasa motsa ko'ina a jikina
saboda tsananin razana. Zuciyata kuwa ta kasa tunato
komai na game da addu'a, sai salati kawai na ke yi.
Gajeren ya matso daidai kaina ya yaye mayafin da aka
lullube ni tun daga iyaka wuyana har kafaduna, sannan
ya karbi sirinjin ya daga sama yana matsawa, ruwan ya
dan yi tsartuwa, sannan ya nufo wuyana yana kokarin
danna mini.
Cak! Ya tsaya hade da kallon dan'uwansa,
lokaci guda suka faďa wata kofa dake cikin fakin suka
rufe. Lokaci guda na ji an murda kofar shigowa dakin
4
マ
hade da sallama. Dr Idris ne ya shigo fuskarsa cíke da
fara'a yana murmushi. Na ja wani gwauron numfashi
na ajiye hade da hamdala. Ya lura da yanayina, saboda
haka sai na tsince shi yana fadin "Uzaif ka farka? Ya
jikin naka?"
Na kalle shi na kauda kaina. Ya zauna a gefen
gadon ya ci gaba da magana "Komai fa sai a hankali
kar ka ce zaka dinga damun kanka, in sha Allahu Every
thing will be o.k."
Ni dai hankalina duk yana can kofar da
wadannan mugayen mutane suka shiga, domin ba ni da
tabbacin ko ina ne kofar da suka shigan, dan na fahimci
kofar da Dr Idris ya shigo an rubuta Special Ward,
sannan ta bandaki an rubuta Toilet, ita kuwa wannan
kofa da suka shiga babu komai a rubuce a jikinta. Take
na daga hannuna ina yi masa nuni da kofár.
Ya kalle ni ya ce "Fitsari zaka yi?"
Na girgiza kaina.
Ya sake cewa "Bayan gida zaka yi?"
Na sake girgiza kai hade da nuna masa kofar ina
yunkurin mikewa.
Yayi saurin maida ni izuwa kwanciya hade da
mikewa, ya ce "In shiga wannan kofar kake nufi?"
Na yi saurin kyada kaina.
Take ya bude kofar a hankali hade da tura ta, ya
shiga ciki ya maida kofar ya rufe, ya kusa minti biyar
da shiga sannan ya fito yana share gumi da farin
hankicin da ke hannunsa, bai ce da ni kala ba ya nufi
Computer da ke ajiye akan karamin tebur din da ke
5
gefen gadona yayi 'yan tabe-tafensa sannan ya zare
mini robar oxygen din.
Cikin kaguwa na ce da shi "Dr kashe ni za su yi,
su biyu ne sun shiga wannan kofar."
Ya kalle ni ransa a bace ya сe "Ka kwantar da
hankalinka Uzaif insha Allahu babu abinda zai sami
rayuwarka anan. Tabbas na shiga, amma kafin na
karasa garejin tuni sun tashi motarsu sun yi gaba." Ya
dan yi shiru, sannan ya ce "Nayi mamaki kwarai domin
kuwa wannan kofar ba a bude take ba, don ba a amfani
da ita, haka ta sauran Special Ward din da ke asibitin,
domin kuwa na tabbata duk cikin mu likitocin da ke
aiki a asibitin babu wanda yake rike da ko wane dan
makulli na kofofin dakunan da ke cikin asibitin. Ita
wannan kofa tana leading ne izuwa gareji saboda
inmajensi (Emergency), kenan da an taho da marar
lafiya cikin gaggawa za ayo nan da shi Special Ward;
sannan a take a ba shi treatment ingantacce kamar
yadda akai maku. To a tsammanina bayan kawo ka ne
aka manta ba a rufe kofar ba, ko kuwa mukullina aka
samu ta hanyar maciya amana da ba su san darajar
aikinsu ba, amma dole ne in sanar da M.D. domin a
dauki mataki na musamman.
Duk wannan bayani da yake yi, yana yi ne
idonsa kur a kaina yana mai nuna tsabar tausayawa. Ya
danyi gwaje-gwajensa ya mike yana mai yi mini Allah
ya kara sauki hade da nufin barin dakin. Cikin sanyin
murya nai kiran sunansa, ya waiwayo hade da tsayawa
cak sannan ya amsa. Na yi shiru kamar in fasa
tambayarsa abinda nayi niyya. Ganin haka ne ya sa ya
6
juyo sosai ya sake nufo ni, ya sa hannu ya shafa kaina "Haba Uzaif na ce da kai babu komai Insha Allah za
mu nemi taimakon 'yan sanda ma in har hakan zai faranta ma rai." Ya dan yi shiru.
Shi a tunaninsa ko har yanzun tsoro nake ji, bai
san gaba daya tunanina ya koma kan masoyiyata ba "Dr
wallahi ni ba wannan nema yake damu na ba." Na dan
yi shiru.
"Come on Uzaif talk mana.
Na kalli gefe guda sannan na ce "Dama tunanin jikin Uzaifat kawai nake yi, don ban san a matsayin da
takc ba."
Ya ja numfashi ya ce "Babu komai jikin nata da
sauki kamar naka, kuma tana Next Ward."
Nayi farin cikin jin haka "To kana ganin zan iya ganinta?"
Yayi murmushi ya ce "Ka kara hakuri dai
Uzaif, domin ba ku gama kwari ba duk kanku, ina so
sai ka fara taka kafafunka sannan." Ya kare maganarsa
da murmushi, sannan yayi waje.
* **
Tun fitar Dr Idris zuciyata ta nutsu cikin tunanin
Uzaifat take na fara tunanin tun daga ranar da na bupi
ido na ganta a NAGARTA HOSPITAL har zuwa ranar
da yayana ya ritsa ni a dakina. Tabbas an ce ka so mai
sonka ko ba komai rayuwa tai maka dadi. Uzaifat ta
zama wani bangare na jikina wanda ba za a taba gani ba
ballantana a yanke a yar "Zuciya" kenan. Ta yi risk din
rayuwarta a kaina, ta sadaukar da ranta a kaina, tayi
mini abinda ba kowa ne zai iya yi mini shi a rayuwan
7
nan ba. Uzaifat ta cika mace a cikin mata, kuma ta
cancanci yabo. Tabbas da lafiyata lau ba yadda zan
yarda in wayi gari in tsinci mai kaunata na mawuyacin
hali in kasa agaza mata. Sallamar da na ji ce ta yanke
mini tunanina, na daga kaina hade da amsa sallamar.
Ta nemi guri ta zauna jikinta na rawa, jefi-jefi
kuma ta kan yi ajiyar zuciya mai cike da nuna alamun
tayi kuka har ta gode Allah. Ganin ba ta da niyyar yin
magana ne ya sa gabana dukan uku-uku, zuciyata kuma
tuni ta dauki haramar bugawa. "Nafisa, lafiya kuwa?"
Tayi shiru ba ta amsa ba.
"Haba Nafisat ya zaki zo mini da wannan suffa?
In wani abu ne ya faru ki sanar da ni mana."
Shiru ta sake yi ba tare da tace da ni kala ba.
Na yunkura zan mike, na kasa. Ganin haka ne
ya sa ta ta tashi ta matso kusa da ni idanunta na zubda
hawaye, sannan ta ce "Ka yi kwanciyarka yaya, da ma
tambaya ce na zo in yi maka, amma dan Allah you have
ta tell me the truth." Ta yi numfashi mai zafi wanda
tururinsa ya daki fuskata "yaya please tell me su waye
iyayena?"
Kaina ne ya fara sarawa sannan gabana ya ba da
gudunmawar faduwa, zuciyata kuwa sai da tayi wani
irin bugu wanda ba ta taba yinsa ba. Tambayar ta
girgiza ni ainun, saboda ban taba tsammanin wannan
tambaya a rayuwata ba.
"Yaya ka sanar da ni kawai, saboda 6oyewar ba
ta da wani amfani tunda tuni Daddy ya sanar da ni cewa
in nemi iyayena a gaba in bar masa gidansa......" Ba ta
8
Karasa maganarta ba ta barke da kuka mai ratsa zuciya.
na dangana yaya, wallahi na dangana!!!
Jikina gaba daya yayi sanyi na kasa katabus. Da
na ga kukan nata sai ci gaba yake yi ne na bude baki da Kyar ina fadin "Haba Nafisa, wane irin zance ne
wannan? Idan zuciya ta bata ina ce hankali ne kc nemo
ta? Ni dai ban sån wasu iyaye naki da suka wuce Hajiya
da yayana ba domin kuwa.....
Kallon da tayi mini mai cike da rashin
amincewa ne ya sanya ni dakatawa.
"Ni dai yaya ni na san abin da kunnuwana suka
jiye mini, wallahi ko ka sanar da ni gaskiyar al'amari
kamar yadda Daddy ya umarce ni da in zo ka sanar da
ni. ko kuwa inna tashi daga nan in bi uwa duniya in
huta da wannan bakin ciki da ya addabe ni."
Jin haka ya sa ni daka mata tsawar da ban yi
niyya ba "Ba ki da hankali ne Nafisa? Ki bi duniya
kamar yaya? To koma mene ne ki bari sai na samu
sauki mun koma gida."
Ba ta tanka ba kuka kawai ta ci gaba da yi.
*
Ni da kaina na tabbatar da cewa Dr Idris ya
dauki tsattauran tsaro a kaina, domin kuwa duk wanda
ya zo dubiya gurina sai da amincewata zai shigo, idan
har kuwa na ce ban san mutum ba to ta zauna sai dai ya
hakura ya koma, in ba haka ba kuwa ya fuskanci tashin
hankali. Hankalina har yanzu bai yi daidai ba domin
matsaloli biyu da ke addabar raina. Na farko sam Dr
Idris ya ki bari in ga masoyiyata daidai da minti daya
balle in san halin da take ciki ko zuciyata ta yi sanyi.
9
Duk sanda na tuntube shi sai dai ya kawo mini Excuse,
Na. biyu kuwa Nafisat, domin ban san yadda zan yi da
ita ba in na koma gida, domin kuwa tashin hankali ne a
tare da mu gaba daya in sanar da ita cewa ba su yaya ba
ne iyayenta, to shin ina zamu nemo nata iyayen?
Tabbas yaya yayi kuskure da ya sanar da ita wannan
Magana, dan kuwa laifina bai kamata ya shafe ta ba.
Sallamar da na ji ce ta yanke ni daga tunanin da
nake yi. Dr Idris ne ya shigo wannan karon su biyu ne
shi da wani mutum mai kirar 'yan ibo amma a zahiri
bahaushe ne. Bayan yayi gwaje-gwajensa ne yayi
introducing din Sa'id Muhammad a matsayin sabon
likitan da suka sake yi a asibitin, ya sanar da ni a
yanzun haka ma yana kaisa Ward-Ward ne domin ya ga
tsarin asibitin da yadda suke gabatar da ayyukansu.
Sa'id Muhammad mutum ne mai fara'a hade da
barkwanci, wanda hakan ya sa har muka dan saba a
tsakankanin wannan lokaci.
Har sun juya nai kiran Idris na ce da shi ina da
magana. Yayi murmushi hade da fadin "Malam Uzaif
kenan ni dai na san zancen gizo baya wuce na koki."
Ya kwashe da dariya a daidai lokacin da suka fice daga
dakin.
- Bayan dawowar Dr Idris sai da muka dauki
wani lokaci muna fafatawa akan ya bar ni in je in ga
Uzaifat amma ya ki, sai da ya ga na nace ne yake sanar
da ni cewa "Ba wai ba na son ka ganta ba ne Uzaif,
dalili kuwa shi ne tunda aka kawo ku sai da Uzaifat ta
kwashe kusan kwana uku ba ta cikin hayyacinta а
sakamakon buguwa da kanta yayi, sannan ko da ta
10
lartado da sunanka ta budi bakr. Ita ma haka ta damu
akan tana son ganinka, sar da na tabbatar mata da ce%2
kana nan lafiya sannan ta hakura, Da ma tunanina bzi
wuce in ga duk kun samu sauki vnai ba, domin in har
zaku fuskanci junanku a cikin yanayin da kuke lo fa
tashin hankali zai zame muku, amma tunda kon amu
sauki zan sa Nas ta kawo ta nan wájenka tunda kafarka
har yanzun da sauranta.
Na ji dadin maganarsa kwarai na yi masa
godiya. Ya mike yanayi min dariya.
Fitarsa ke da wuya na ji an bude kofa da
sallama. Nas ce ta riko hannunta suka shigo, ta nemi
guri ta zauna a bakin gado. Bayan Nas din ta fita ne
muka kalli juna zuciyarmu cike da farin cikin ganin
juna. Tabbas Uzaifat ta ji jiki in ka yi laakari da bandejin da aka daura mata aka da kafafunta. Na tashi
zaune ina mai tausaya mata.
"Czaif sannu yaya jiki?" Ta tambaya-muryara
na rawa.
"Haba Czaífat ai ni zan tambaye ki jiki."
Ta yi hishiru tana kallona fuskarta duk a
kumbure. Ta fashe da kuka a lokacin da ta kurawa
kafafuna da suka sha bandejí ido. "Ba komai Ľzaif
Allah zai yi mana sakayya."
"Da ma kin san Any disappointment is a
blessing." Na fada ina kallonta ido cikin ido. ban
ankara ba na tsinci Dr. Idris a bakin kofa.
11
Mun samu wata-uku a asibiti sannan aka sallamé
mu a sakamakon warkewar da aka tabbatar mun yı. Bük
tsawon wannan lokaci babu duriyar Hajiya balle na
yayana. Ko da yake Nafisa ta sanar da ni cewa bayan
sun dawo daga asibiti yayana ya tare su ya sanar da ita
cewa ba shi ne ya haife ta ba ta je ta nemi iyayenta,
sannan kar ta kuskura ta tunkari gidansa. Ita da kanta
Hajiya garin ba da hakuri sai da ta shå wawan mari.
Abun farin ciki kuma shi ne Nafisa ta sanar da ni ceWa
Hajiya na da juna biyu a sakamakon zuwansu asibiti.
Na taya Hajiya farin ciki da fatan Allah ya sauke la
lafiya ganin cewa shekararsu ashirin da 'yan kai"da
yayana amma sai yanzun ubangiji yayi musu arzikin
haihuwa.. Muna kan hanyarmu ta komawa gida Nafisa
ta sanar da ni cewa gida ba kowa daga ita sai Baba
Musa, yayana tun a ranar da abun ya faru ya dauki
Hajiya suka bar gida.
"Faduwar gaba asarar namiji." Na fada ina
murmushi.
Sai a lokacin ne na sanar da su yadda na danawa
yayana tarko, da yadda ya ritsa ni. "Amma ga shi komai
ya tashi a banza, tunda komai ya koma hannunsa."
Uzaifat ta ce "Ba dai komai ba, domin tabbas
lokacin da na riske-ku har ya make ni, kafata ta buği
wani abu kamar rikoda kamar camera yayi Rarkashin
firij.
12
Dadi ne ya mamaye mini zuciya hade da fatan ubangiji ya sa yayana bai ga lokacin ba ya dauke. Bayan ham din da muka yi baba Musa ya bude mana
Gate muka shiga. Ya karaso yana murmushi hade da yi
mini sannu "Ban sami damar komawa ba tun da na je
sau biyu na tarar kana bacci. Barayi ne suka takurawa
unguwar yanzun, shi ya sa bana fita ko'ina, jiya ma sai
da suka shiga gidan malam Muttaka."
Nayi salati na ce "In ce dai ba suyi masa komai ba ko?"
Baba Musa ya fada dakinsa yana fadin "Haba
Uzaif ai malam Muttaka ya ga ta kansa, domin su yi
masa wulakanci wai dan ba su samu kudi mai yawa ba
suka harbe masa yara biyu har shi kansa ba su bar sa ba
sai da suka harbe sa a kafar dama."
Labarin ya girgiza ni, nayi wa yaran addu'ar
Allah ya jikansu, shi kuma Allah ya ba sa lafiya, sannan nayi nufin shiga ciki wanda dama tuni su Nafisat sưn
shige dan sun san surutun baba Musa baya karewa. Kira
na da baba Musa yayi ne ya sa ni na dawo, hannunsa rike da Brown din Envelop yana murmushi ya miko
mini "Ga shi wani yaro ne matashi ya kawo, kuma ya
sanar da ni cewa in ba kai ba kada in bawa kowa hatta Alhaji."
Na karba hade da tambayar "Wai in ji wa?"
"Bai fada ba, amma ya ce akwai muhimmin bayani a ciki."
Nayi masa godiya na shige ciki. Na tarar da su Uzaifat a zaune akan kujera kowacce da kofin ruwa a
hannunta. Na nemi waje na zauna ina jujjuya Evelop
13
din hannuna. Nafisa ta mike a yayin da ta nufi kicin
gami da tambayata ko ina na sami sako? Nayi shiru ina
kallon Envelop din har ta fito daga kicin din ta sake
neman waje ta zauna. Na kalle su na ce "Wallahi
wasika ce baba Musa ya ba ni, amma har shakkar bude
יי
ta nake yi saboda ban san me zan tarar a ciki ba."
Uzaifat tayi hanzarin cewa "Akan me za kai
shakka? Ko fargaba kake yi kar irin ta Dele Giwa ta
kasance maka?"
Muka tintsire da dariya, sannan na ce "To in dai
wasika ce aka kawo ba tare da wanda ya aiko ya fadi
sunansa ba, shi ma dan aiken ya ki fadawa baba Musa
wanda ya aiko.
Haka dai na daddage na bude wasikar na fara
karantawa.
Daga wacce take a matsayin mahaifiyarka.
Bayan gaisuwa da fatan alheri, ya bayan
saduwa? Ka san ce mai karanta wannan wasikar. Sauki
ya tabbata a gareka, Allah ya sa hakan amin. Ya su Nafi
da Uzaifat, ita ma ya nata jikin? Ubangiji ya baku lafiya
tare da kara muku juriyar hakuri.
Bayan haka Uzaif ba komai ne ya sanya na
rubuto maka wannan wasikar ba, illa in ba ka hakuri
kuma in tausasa maka zuciyarka akan abinda yayanka
ya aikata gareku. Uzaif abu daya nake son ka sani cewa
fa shi ubangiji ba azzalumi ba ne, duk abinda da mutum
ya aikata imma hairan ko sharran to ubangiji yana kallo,
kuma zai yi hisabi a ranar da dan'adam ba shi da wata
katabus sai aikin alherin da ya aikata, saboda haka
Uzaif kuyi hakuri ubangiji zai saka maku saboda ni da
14
kansab yaneh Hа bыdarda dewayayüika shi ne
kd gindinedakanfbddk&afkiwaa gard ka har a
thasoy4yarkaliewato Uzalfatsaboda haka Uzaifkakakа nki wani mata Ka
barwa abangijn koihđi đon Shi ne'ntai sakayya domin in
HiarsA hajioyifuskanci kid Shitih aikata wahi abti gare
shi, to wallahi ka san ya tara 'yan iska wadanda zasu
iya ikand komiai saboia bamun abur duani kuma
rayuwarku ita ce muhimmiye gare i! Hakurl Shi ne yaskartneu kaihadeda adit'a a kowanne lothei!
Magana ta biyu kuwa ita ce akan Nafisa konmai
runtsi kar ka sanar da ita komai akan Background dinta,
doino yinrhakanař zome makd babbah thstin hankali. A ranar daA ajt onyi mhne Wayau ya tirar nlagi hartyalaikata malk annan hummuhar abu, y ae achanyalya eiwa Naft mitunel ya kama faf körhkr ganet Ua Kiahtl WandaakalJ
ARUBISHI sherara
batantanaus o arna, unihdiana itsanfP haka
ku Abufa nay tiik haP Th en Gidansa nacwbuja a aaska sahi Han üah ajiye shananvya Nanga thasugadikapy i fita,
hunzafta zuwa Rathoya Uwo
Yath ANANRila he is fi nabig sbud sat asy a
Taku har abada Hajiya Maryam.
a
15
Ina kammala karantawa na mayar da wasika na
mike ina shirin maida ta cikin Envelop gudun kar
Nafisa ta ga ma ke ciki. Amma kafin na aikata hakan, ta
wurgo mini tambaya "Yaya wane ne ya aiko da ita?"
Ni da kaina na san cewa 6atan basira ne ya
sanya ni na ce da ita "Hajiya ce ta aiko mana da
gaisuwa."
Ai nan take ta mike ta nufo ni tana dariya "La
wallahi sai ka ban na karanta ni ma."יי
Kafin na ce me tuni ta firge takardar daga
hannuna.
** **
Mun lallashe ta ne da kyar bayan mun daukar
mata alkawari zamu ziyarci Abuja very soon, tare da
alkawarin cewa duk inda iyayenta suke sai mun
taimaka mata wajen nemansu. Na tashi na nufi dakina
ina taka matattakalar bene hade da yiwa Hajiya addu'a
domin a rayuwata ban taba ganin mace mai hankali da
nutsuwa hade da sanin ya kamata ba irinta. 'Ubangiji ka
sauke ta lafiya, hade da raya mata abin da zata haifa."
Na fada a raina a lokacin da na murda mubudin dakin
na shiga. Gabana ya fadi lokacin da na riski anyi wa
dakin tsinke duk an hargitsa shi, amma cikin ikon Allah
ba a taba firij ba, dan haka na sunkuya na leka
karkashi, ga mamakina can na hango ta kwance tana ta
walkiya kamar ba ta shafe wadannan watanni a wajen
ba. Na sa hannu na dauko ta lokacin da fuskata ta
fadada izuwa murmushi, nayi godiya ga ubangiji.
Bayan na bude gidan Film din na tarad shi ma yana nan
16
a mazauninsa yana shakatawa. Na bucfe akwatina na jefa ta ciki hafe a hargitsa lambobin.
*
Sautin amon wakar shahararriyar mawakiyar
nan Celine Dion ne ke tashi wato Think Twice sannu a
hankali, falon yayi tsit duk sun nutsu akan nazarin
mujallar da ke hannunsu ta Daily News Paper illa ni
kadai kawai da ke rike da littafin Hausa na Hajiya Binta
A. Rabi'u Ali Agege wato Tsautsayi ko Kaddara? Na
fara jin dadin littafin ainun, amma saboda matukar son
wakar ya sani ajiye littafin na nutsu wajen saurare.
Kaset fin ya kare na tashi na nufi wajen redio domin
juyawa izuwa daya bari. Uzaifat ke tambayana inda na ajiye mata Mixmac dinta maganin ciwon cikin da take
amfani da shi in ya murda mata. Na ajiye kasct akan
redio ba tare da na sa ba, na nufi bayan babbar kujera
na dauko ina fadin "Ya fara yi miki ciwo ne cikin?"
Ta amsa da "Yana dai so ya fara ne, shi ya sa
zan yi